Showing 195001 words to 198000 words out of 212491 words

Chapter 66 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

982

sambal kita tafiya ba sai kin sha wata kwana ba zaki ganki har Katsinar" maimakon ta tafin sai ta tsaya tana tura mashi baki yace ta tafi ta bashi wuri ta juya Mutanen dake kusa dashi na mata dariya ganin tak'i ta tafi a k'afan ta koma ta zauna. Da kyar aka samu ta gyaru don da har direban ya fara tunanin buga waya a turo masu wata duk da hakan ba k'aramin dare zaisa suyi a hanya ba tunda yaushe Motar tazo har suka tafi, Hamdala Mutane suka shiga yi suna Addu'ar Allah ya kaisu lpy yasa kada ta k'ara lalacewa, ba tare da 6ata lokaci ba suka ci gaba da tafiya saidai direban bai yin gudu kaman da lalla6awa yake su samu su isa Lafiya, Allah sarki gwaggo tana can hankalinta duk ya tashi jin abunda ya faru da ta kira Amadun ya sanar da ita dama akai akai take kira tana jin sun iso ina haka ma can inda suka baro Mahaifin Fatuu da yaya Kamalu suma duk bayan d'an lokaci suke kira suyi masu ya Hanya, Alhamdulillah sai ana sallar isha suka k'araso duk sun gaji likis Fatuu kallabinta a hannu ta fito daga Motar kitson fulanin da yadikko tayi mata nata reto, suna sauka gwaggo ta kira lokacin Amadun na niyyar kiranta ya sanar mata ai koda taji sun sauka nan take ta hau yin hamdala harda yin sujjadar godiya ga Allah, ce ma Amadun tayi bari tazo ta taho dasu yace ta barshi kawae tunda sun shigo gari zasu k'araso lafiya lou, within some minutes suka iso gidan lokacin gwaggo na tsaye jikinta sanye da Hijab tana dakon isowarsu Keke Napep d'in na tsayawa ta nufeta tana masu Oyoyo, saida ta taimaka ma Fatuu ta fito cike da tsantsar farinciki ta rungumeta don tayi missing d'insu sosae duk sai gidan yayi mata ba dad'i saukinta ma tana zuwa aiki, bayan an sallami mai adaidaita sahun tare da gwaggo da Bello daya dawo daga Masallaci ya taimaka masu suka shiga da kayayyakin yay masu sannu da zuwa kafin ya fito lokacin tuni Fatuu ta baje a d'akin gwaggo don akwae wutan nepa atare suka shigo ita da Amadu ya zauna kan kujera ita kuma ta nufi gefen gadonta tana yi ma fatun sannu sam fuskarta ta kasa 6oye farincikinta sai faman tatta6a Fatun take tana yi mata sannu ita dae kai kawae take d'aga mata, mik'ewa tayi ta tafi kitchen ta fara kawo kayan abinci Amadu nayi mata sannu tace ai su keda sannu bayan ta gama kawo komae tace to su saukko suci Abinci, mik'ewa Amadu yay yace shi yafi bukatar yayi wanka kafin Abincin tana jin haka tace to bari ta had'a mashi ruwan wanka yana ta barshi zai had'a tace yay zamanshi, Allah sarki uwa mai dad'i ya ayyana a ranshi kafin ya koma ya zauna, bada jimawa ba ta had'a mashi ruwan dama akwae ruwan zafi a electric kettle data jona saboda su don garin a d'an kwai sanyin damuna, bayan ta dawo d'akin tace gashi can a bandaki yaje yayi yace to, kallon Fatuu tayi tace "to taso auta kici Abinci ko sai nazo na daukeki ne?" girgiza mata kai tayi alamar a'a tace "to daure ki tashi in kika ci abincin zaki ji karfin jikinki" tana jin haka ta yunkura ta fara kokarin saukkowa don tana bukatar karfin jikin saboda taje gidan Hajiya, zuba mata Abincin tayi ta zauna kan darduma ta fara ci ita kuma gwaggo ta hau kan kujera tana kallonta da Murmushi tana k'ara yi mata sannu, ta d'an ci ba laifi ta mik'e gwaggo na har ya isheta tace gidan Hajiya zata je ta fad'i mata sun dawo,

"Ki bari ki huta gajiyar mana zuwa da safe ba sai kije ba" tura baki tayi tace ita dae yanzu zata je ba dad'ewa zata yi ba, d'aga mata kai tayi alamar taje da sauri ta nufi kayansu ta bud'e jakar kayanta ta d'aukko wata bak'ar leda dake k'ulle sai kuma ta bud'e ta tsarabar da suka yo ta kalli gwaggo tace "don Allah gwaggo kina da bak'ar leda yar babba?" tambayarta tayi mi zata yi da ita tace "zan d'ibar ma Hajiya tsaraba ne" gwaggon tace "to ki bari da safe ba sai akai mata ba ko",

"To ai tsarabar Ya Handsome zan kai mashi tana iya cewa ita ina tata shiyasa zan fara kai mata wannan goben sai akai mata sauran" jinjina kai gwaggo tayi alamar gamsuwa ta mik'e ta samo mata ledan ta bata dama tasan duk zumudin na son ganin Haisam ne, bayan ta zuba abubuwan da zata d'iban tace ma gwaggo sai ta dawo ganin tana niyyar fita ko kallabi babu ta mik'e ta d'aukko mata kallabin ta bata tace ta yafa akanta tunda babba ne daga haka ta fuce.

Lokacin data isa gidan kaman an jefota ta fad'o cikin falon Hajiyan kallabi a hannu ga ledoji a hannu tana ta zare idon son hango Haisam don taje part d'inshi bai nan kuma tasan yau ba ranar zuwa gym bace, Jidderh ce zaune a falon kan sofa 3 seater tana yin chat da wayarta ta d'aura duka k'afafunta saman kujeran jikinta sanye da jallabiya milk colour kanta ba kallabi tayi parking gashinta da yake bak'i sosae mai santsi sai twins dake gefenta suna yin game da ipad, atare suka d'ago suka kalleta kaman yadda itama ta kafesu da ido tana yi masu kallon rashin sani ko kyaftawa batayi, sai faman kallon juna suke an rasa wanda zai tanka ma wani can Mubeen ya kai bakinshi saitin kunnan Mubeena ya rad'a mata wata Magana ai kuwa a firgice ta kalleshi ta kuma kalli Fatun atare sai kace an latsa masu remote suka diro daga kan kujeran bayan sun aje ipad d'in suka ruga hanyar Bedroom d'in Hajiya suna kwala mata kira cike da razana sai kace kaji broilers yadda suke gudun, a daidai Corridor sukayi kacibus da ita ta fito jin kiran da suke mata jikinta sanye da hijab da casbaha a hannunta tun kafin tace wani abu atare suna haki suka ce "Ha...Hajiya a genie has appear" waro ido tayi tace "a genie?" da sauri suka jinjina mata kai alamar eh,
tace"where is d genie" da hannu suka nuna mata cikin falonta, kama hannuwansu tayi tace "Ok let's go and see d genie" suka nufi cikin falon har wani sand'a suke tun kafin su k'arasa ta hango Fatun tsaye k'ikam har lokacin kuma Jidderh bata ce mata komae ba don ganin su twins sun ruga yasa ta d'an ji tsoron Fatun ya kamata, lokacin da suka k'araso cikin falon Hajiya na dariya tace "Lallai kuwa k'atuwar Aljana ce ta bayyana" da sauri Jidderh ta kalleta jin abunda tace amman ganin tana dariya yasa hankalinta kwanciya nan take kuma ta fara hasashen anya ba itace Fatun da Hajiya ke basu labari ba yar gidan ya haisam mai ce mashi Handsome don duk in suna fira sai ta sako masu labarin Fatun, kallon Hajiya su twins sukae suka nuna mata Fatuu wai ga Aljanar tana dariya ta zauna idonta akan Fatun tace "Manyan gari saukar yaushe?" tana tura baki tace "yanzun nan muka dawo Mota ta lalace mana a hanya" da mamaki su twins ke kallon both of them ganin suna Magana, Mubeena ce tace "Granny u know d genie?" kallonsu tayi tana dariya tace "she isn't a genie, she's d Fatuu i ave been telling u about" a tare suka zaro ido suka had'a baki suka ce "Fatuuuu!" kai Hajiya ta d'aga masu lokaci guda suka saki dariya suka nufeta aikuwa ta d'aure masu fuska tana yi masu wani kallo hakan yasa suka ja suka tsaya a gabanta suna kallonta itama kallonsu take da yar harara kawae sai suka fara ta6e baki irin na shagwa6a66un yara alamar zasu yi kuka hannunsu cikin na juna suka juya zasu koma Hajiya tace "ah Fateema ya da haka kuma?" tana tura baki tace "ba sune suke ce man Aljana ba"
"To ai basu sanki bane baki ga bak'i bane gashi sun ganki da wata kalar shiga ga kanki a bud'e shiyasa suka tsorata ai" kallonsu tayi tace suje su bata hakuri a yadda suke ba tare da sun raba hannuwan ba suka koma,tsayawa sukae a gabanta sannan suka saki hannuwan kowa ya kama kunnanshi a tare suka ce"Sis Fatuu we're sorry" kawae sai gani sukae ta kece da dariya don yadda sukae ba k'aramin dariya suka bata ba dama ga uban kumatu tubarkallah suna ganin tayi dariya suka k'ank'ameta suna yi mata welcome, Jidderh da Hajiya ma dariyar suke, Hajiya ce tace ta zauna mana ta nemi wuri kan 2 seater suka zauna, gaida Hajiyar tayi kafin ta maida idonta kan Jidderh dake mata Murmushi itama ta gaidata ta amsa tace mata "an dawo lafiya" tana Murmushi tace "Lafiya lou amman munsha wahala tun Asuba sai yanzu muka iso fa" cikin sanyin muryarta tace "gaskia, sannu ko" amsa mata tayi da yauwa kafin ta kalli Hajiya tace "Hajiya su waye wad'annan?"
tana dariya tace "ai kuwa ya kamata ace kin ganesu basai an fad'a maki ba, ki kallesu da kyau zaki gane ko suwaye" jin haka yasa ta k'ura ma jidderh dake Murmushi ido sai kuma ta maido kallon kan su twins tana k'are masu kallo can tace "wad'annan kumatunsu yayi yawa na kasa ganewa" hajiya tace "to ki kalli wannan da kyau" tayi Maganar tana nuna Jidderh, zuba mata ido ta k'ara yi ganin kaman tana yanayi da Haisam yasa tace ta daina yin dariya zata fi ganowa dariyar ta k'ara yi sosae jin Maganar Fatun kafin ta dakata suna kallon juna can ta kalli hajiya da sauri tace "yan gidansu Ya Handsome ne ko?" aikuwa gaba d'aya harda twins suka sa dariya jin tace Ya Handsome din, bayaninsu Hajiya tayi mata daga baya tace bayan bata nan suka zo, Ledar dake ruke a hannunta su twins suka fara ta6awa suna tambayar miye a ciki tace masu tsaraba ce,
"Za mu ci" suka fad'a suna kara ta6a ledar da sauri ta janyeta tace"kai ba irin abunda kuka saba ci bane wannan shak'e ku zai yi" k'ara had'a baki sukae suka ce zasu ci koma minene tace "kai kuji man yara, so kuke ta shake ku kuja akaini gidan yari ko" kafewa sukae kan su dae ta basu suci su Hajiya na masu dariyar drama d'in da suke can Hajiya tace "miye a ciki ne?" da sauri tace "su goriba da kurna da magarya da aya ne fa na fara kawo maki sai gobe za'a ida kawo sauran tsarabar" kafin Hajiya tace wani abu Jidderh tace "ki basu ai sun iya cin su" da al'ajabi ta kalleta tace "ni ai nazata a Abuja ba'a saida irin wad'annan abubuwan don ance kaman kasar waje take" Jidderh na dariya tace "No akwae kasuwar da ake saida irinsu kuma cikin maids din mu akwae wata Iya yar Daura ce so in tazo tana kai mana tsaraban su har Dad ma naci yace suna Magani" cike da jin dad'i Fatun ta washe baki jin an yaba tsarabar tata, bud'e masu ledar tayi kowa ya d'auki goriba biyu yasa a cikin riga suka rungume sannan suka d'ibi magarya a hannu suka fara sha Hajiya dake kallonsu tace "wai bani aka kawo ma tsarabar bane to a mik'o man mana kuke ta kwashewa" mik'ewa Fatuu tayi ta kai mata ledar ganin tana ta mak'ale d'ayar a hammata tace to ita wannan miye aciki tace ba nata bane tsarabar Ya Handsome ne, bud'e ledar Hajiya tayi ta aje masu suka fara shan magaryar ita da Jidderh su twins suka ba Fatuu goribar wai ta cirar masu dama haka ake masu in kuma irin wadda aka 6an6are ce sai a jika masu tayi taushi sannan su ci suna cikin ci Fatuu ta tambayi Hajiya ina Saude tace tana d'akinta mura ke damunta ne tasha magani ta kwanta tace to ina Ya Handsome yake tace sun fita amman tasan sun kusa dawowa, Hajiya na rufe baki Nameer da Farha suka shigo hannunsu cikin na juna kowannansu na sanye da k'ananan kaya ta zame gyalen kanta ya dawo saman kafad'a, nufo cikin falon sukae Nameer na Fad'in "kai kai wato abun dad'i kuka samu kuna ta shagali shine ko ku tuna damu ko" yana rufe baki Mubeen ya nufe su yana nuna masu Fatuu yace "Ya Nameer guess who she is" d'aga ido yay ya kalli Fatun da itama shi take kallo da mamaki ganin tsananin kamarsu da Haisam, k'uri yay mata ya d'an k'ank'ance ido alamar yana son gano ko wacece d'in duk suka bishi da ido da Murmushi ita kuwa Farha kujera ta nufa ta zauna itama idonta na kan Fatun tana mata wani kallon rashin arziki don dama ita shirgin Mutane bai dameta ba,

"She must be Fatuu yar gidan Ya Haisam" Nameer ya fad'a yana nunata da yatsa gaba d'aya suka sa dariya Mubeen na Fad'in "U guessed right" itama Fatun murmushi take mashi ya nufi hannun kujeran da take ya zauna yana mata Murmushi yace "saukan yaushe yar fillo" d'an tura mashi baki tayi yasa dariya dama yaji bata son sunan tace mashi bada dadewa suka dawo ba,
"To ya rugar kuma ina tsarabarmu" yay Maganar ya d'age gira kaman yadda haisam ke yi, nuna mashi ledan abubuwan dasu Hajiya kesha tayi tace "ga tsaraban can" kallonsu yayi kafin yace "yo nida zanga Fura da Nono sai inga wanccan tarkacen" tace "ai suma za'a kawo su sai gobe" jinjina mata kai yay yanata dae yi mata Murmushi, Mubeena ce ta nufi Farha da tunda taji cewa itace Fatuu ta sadda kanta tana latsa wayarta tana zuwa wurinta tace "Sis Farha this's Fatuu we ave been told about" banza tayi mata kaman bata ji abunda tace ba har saida ta k'ara maimaita mata tana ta6ata aikuwa ta daka mata tsawa tace "leave me alone twin" yadda tayi Maganar har saida suka kalleta gaba d'ayansu, ta6e baki Mubeenar tayi sanin halinta yasa Hajiya tace mata ta kyaleta ana haka Haisam ya shigo shima k'ananan kaya ne jikinshi kafarshi na sanye da wasu slippers masu kyau da alama ba nisa sukae ba fuskar nan tayi wani Fresh ai twins na jin Muryarshi yayi sallama suka nufeshi atare da gudu suna cewa "Ya Haisam Fatuu has came back" sukae Maganar suna nuna mashi Fatun da itama idonta na akanshi ta guntse dariya da tafin Hannunta, kamo hannuwansu yay suka shigo cikin falon fuskarshi a sake da d'an Murmushi, mik'ewa Jidderh tayi ta nuna mashi kusa da Hajiya yaje ya zauna ita kuma ta koma saman hannun kujera tana facing inda Fatuu da Nameer suke Hajiya tace "ga Mutuniyarka fa an dawo sun dae sha wahala wai mota ta lalace masu a hanya tun Asuba sai da daren nan suka k'araso" d'an jinjina kai kawae yay kafin ya kalleta calmly yace "kun dawo lafiya?" tana ta sakin murmushi tace "Lafiya lou" nan ma jinjina kan yay kawae, Mubeen ne ya nufi wurin Fatun ya jawo ledar data k'ank'ame ta hana kowa ganin abunda ke ciki yace "ki bashi to" d'an harararshi tayi Hajiya dake dariya tace "atoh tunda ya dawo ai yanzu sai abashi muga abunda ke ciki ko, wai tsarabar kace tun d'azun ta kankame ta hana kowa gani" ta k'arasa idonta kan Haisam d'in shidae d'an Murmushi kawae yay, ganin Mubeen d'in yak'i kyaleta yasa ta mik'e taje gaban Haisam d'in ta mik'a mashi ya amsa ya furta mata "thanks",

"Ya Haisam open it let's see what's inside" twins da suka k'agara su ga mike ciki suka fad'a, a nutse ya bud'e ledar ya fiddo abunda ke ciki, kayan fulani ne riga da hula kala biyu farare da kuma Navy blue kalan na jikin Fatun sun sak'u sosae da gani masu kyau da kud'i ne, d'an Murmushi yay ganin kayan duk suka hau cewa ya gwada don Allah suga yadda zasu yi mashi, shiru yay kaman bazai gwadan ba can ganin sunata rok'onshi yasa hannu ya cire rigar jikinshi k'irar karfinshi ta bayyana muraran don ma akwae farar singlet a ciki, masu duhun ya fara sawa lokacin da ya d'aura hulan akanshi wani ihu da sowa suka sa suna fad'in wllh yay bala'en kyau Nameer yace "gaskiya da sakel wllh ban yarda ba nima dole a bani irinsu" Fatuu dake dariyar jin dad'i tace" to ai bansan kana nan ba shi kadae na kawo mawa" yace dole tasan yadda zata samar mashi shi dae ya d'auki wayarshi iphone yace bari yayi mashi hotuna, da farko k'in yarda yay saida Hajiya tasa baki sannan ya bari ya fara yi mashi hoton suka ce ma Fatuu ta zo ayi masu tare tunda kayansu iri d'aya ne ta matsa akayi masu, Wow shine kowa ke fad'i don ba k'aramin kyau pic din yayi ba ba kamar da yake kan Fatun ba kallabi kitson fulaninta sun zubo, hotuna suka ci gaba da yi harda su twins da Jidderh da Nameer ita dae Farha ko ci kanku bata ce ba amman ta kan d'an d'ago ta kallesu, bayan ya cire masu duhun yasa fararen suma dae sun amshe shi sosae hakan ba k'aramin dadi yayi ma Fatuu ba tana cikin yin d'an tsallen Murna kawae taji an tadiyota tayi baya ta fad'i da6ar a kasan Carpet ba karamin buguwa tayi ba har saida ta yarfa hannu tace washhhh, tsit kake ji wutar kowa ta d'auke duk suka maido hankalinsu kan Fatuu daketa faman yarfa hannu sai kuma suka maida kallon kan Farha data d'aure fuska tamau tana hararar Fatun,
"What's that Farha!" Hajiya ce tayi Maganar da d'an tsawa don daga kallon da Farhan kema Fatun suka fahimci abunda ya faru, jin Farhar tayi shiru ne yasa Hajiya maimaita Maganar Farhar tace "ta take man k'afa" a fad'ace tayi Maganar had'i da mik'ewa tana yamutsa Fuska ta nufi hanyar Bedroom walking slowly ita ala dole kafan ciwo take mata, bud'a ido Fatuu tayi alamar mamaki baki bud'e jin abunda Farhar tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login