Showing 132001 words to 135000 words out of 212491 words

Chapter 45 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

1006

ya bashi amsa da eh kafin yace yazo su sauke, da taimakon wasu mutane aka sauke freezer d'in suka nufi cikin gida da ita, Gwaggo na zaune asaman tabarma a inda ta saba zama in ba wuta taji anata kiciniyar shigo da abu, sakin baki tayi tanata kallon ikon Allah har suka samu shigowa da ita suka nufo cikin gidan a gaban gwaggon suka ajeta, tun kafin tayi magana Amadu dake ta faman washe baki yayi mata bayani, abun bana zama ne, mik'ewa tayi ba shiri tana kallon kwalin freezer d'in cike da mamaki, maida idonta tayi kan Tk dake tsaye gefe tace ya tabbatar nan akace ya kawo, tambayar tata har saida ta bashi dariya kafin yace mata eh, ita mamakinta yadda yasan da Maganar zata siya freezer d'in har ya aiko, wanda yau bai wuce saura yan kwanaki bama ta siyo ma Amadun ba donma kud'in sun samu gi6i ba da tuni ta siya mashi, suna cikin tsayuwar Fatuu ta rafko sallama ta shigo jikinta sanye da uniform d'in islamiyya, baki bud'e tabi kwalin itama da kallo cike da mamaki ta furta "kai,wai Gwaggo harkin siyo ma kawu Amadu freezer d'in?"
Wannan Maganar yasa gwaggon tunanin ko ita tayi ma Haisam zancen hakan yasa ta tambayeta ko tayi mashi zancen siyan freezer d'in, da farko cewa tayi ita batayi mashi Maganar ba gwaggon tace ta dai tuna, don ita abun yasata al'ajabi indae ba wani ya gaya mashi ba taya zai sani tunda gashi ance Amadu aka siya mawa, can Fatun tace ta tuna lokacin da Uncle Bash yayi mashi maganar littattafan nan daya ta6a siya mata, to lokacin ne ta gaya mashi gwaggo ma tace zata siya littattafan amman bata da kud'i sai ta kwashi kudin adashen da take wanda zata saima kawu freezer, jin hakan yasa gwaggo sauke nannauyar ajiyar zuciya tama kasa cewa komai don Al'amarin Haisam akwae d'aure kai, ko acikin mutane masu yin Alkhairi shi na dabanne, tambayar Tk tayi ko Haisam d'in na gida yace mata a'a yana can wurin exercise shima kiranshi yay awaya yace ya d'aukko mota ya iskeshi a wurin, jinjina kai gwaggo tayi kawae tk d'in yayi mata sallama zai tafi ta shiga yi mashi godiya harda cewa don Allah ya tsaya abashi tukuici, wata yar iskar dariya yayi yace "haba dae Kakus" dayake shima d'an barkwanci ne, bayan ya tafi tsaye sukai su duka farinciki duk ya cikasu sai fara'a suke Fatuu kam harda rawa tayi,

Da daddare bayan sallar isha suka d'unguma zuwa yin godiya lokacin Haisam na a part d'insa hakan yasa suka je can, karo na farko kenan Gwaggo da Amadu suka shiga sashen nashi, ba k'aramin burgesu wurin yayi ba suna ta yabawa acikin ransu, lokacin da suka shiga falon bai ciki yana can cikin bedroom d'inshi saida kawu Amadu ya kirashi a waya ya sanar dashi zuwansu sannan ya fito, fuskarshi a sake ya gaida gwaggo shikuma Amadu ya gaida shi ya amsa, wuri ya nuna masu yace su zauna kowa ya zauna saman armchair d'aya, bayan sun zaunan gwaggo ta fara mashi godiya tana cewa anga abun arziki angode Allah ya saka da mafificin Alkhairi ya albarkaci rayuwa yasa agama da duniya lafiya, sosae take mashi godiya had'i da Addu'a har saida sautin muryarta ya d'an karye kaman zatayi kuka, shidae abu d'aya yace shine ba wani abu, sai kuma Addu'ar daya rink'a amsawa jefi jefi, tana tsagaitawa kawu Amadu ma ya shiga yin godiya, kallon Fatuu yay data zauna akan carpet gefenshi yay mata alama da kanshi nan take ta gane abunda yake nufi don yanzu da yayi mata alama da kai ko da ido take ganewa, mik'ewa tayi ta kalleshi k'asa k'asa tace "Lemu ko ruwa?" wani kallo yayi mata kafin ya k'ara mata alama da kai ta juya ta nufi Fridge d'in, lemu da ruwa ta d'aukko ta kawo ma gwaggo kafin ta juya ta kalleshi ya lumshe idanunshi hakan yasa ta juya ta k'ara d'aukko wasu ta kawo ma kawo Amadu,

"Ki kawo cups ko" Haisam ya ya fad'a, tana juyawa ya mik'e ya fara kokarin matsar masu da c-table don a hannun kujerun ta d'aura ma kowa, gwaggo na ganin hakan ta mik'e tace ba sai ya wahala ba tafiya zasu yi ma hakan yasashi dakatawa, Fatuu na ganin sun miken ta dawo ba tare da ta dauko kofunan ba, ganin duk basu d'auki lemun da ruwan ba yasa tace" Gwaggo kin bar lemunki da ruwa fa" banza tayi mata ta fice Haisam yace ta d'aukar masu,
tace "to nima in d'aukko" yana niyyar fita yace "wani ya hanaki ne" daga haka yabi bayansu, daukowa tayi itama ta zubasu acikin hijabin jikinta daga haka itama tabi bayansu niki niki da abu rungume, bayan sun fito gwaggo tace mashi don Allah ya koma don part d'in hajiya zasu je, sallama yay masu suka shiga k'ara yi mashi godiya ya juya kawae Fatuu na cewa "saida safe Ya Handsome" ya d'aga mata hannu daga haka ya shige, itama dai hajiyar godiya sukai mata tace ita batama san anyi ba ai, sosae gwaggo ta shiga mamakin hali irin na haisam wannan shine kyauta da dama ba tare da hagu ta sani ba, masu yi don Allah kenan, yar hira suka ta6a kafin suka yi sallama da ita suka koma gida, bayan sun koma ne suka shiga kiciniyar bud'e sabuwar freezer din don su had'a ta, a cikin d'an ginin d'akin da ba'a k'arasa ba dake gefen na gwaggo suka yanke shawarar ajeta don ta rinka samun isashshiyar iska amman sai anyi mata yar baranda asama saboda rana wannan kuma duk sai gobe in Allah ya kaimu suka yanke shawarar za'ai hakan.

Ana saura kwana ukku a fara Azumi ranar laraba kwatsam sai ga Mahaifin Fatuu yayi masu zuwan bazata, wannan ne zuwanshi na biyu tun bayan da ta dawo nan ba kuma don baison zuwa ba sai don kunya da kawaici irin na Fulani, da farko lokacin data dawo ya fara turo masu kudi akai akai gwaggo ta dakatar dashi tace bata d'auki Fatuu don yaci gaba da kula da ita ba, d'aukar d'awainiyarta bazai gagareta ba in sha Allah, sosae yaji dad'i amman duk da hakan lokaci bayan lokaci yana masu aike ta hanyar yan garinsu dake zuwa manyan kasuwannin yankin Katsina tunda shi yanzu ya daina zuwa sai dae k'annanshi da y'ay'an yan'uwanshi, haka kuma yana yawan yin waya da fatun don ko bai kiraba ita tasa gwaggo ko kawu Amadu wani ya kira mata shi, Mahaifi mai dadi (Allah ka jikan namu da suka rasu, Amin), Jama'a kuzo kuga Murna agun Fatuu duk tabi ta kankameshi shidae sai dariya yake, fari dashi mai kyau har yafi Fatuu fari saidai daka kalli fuskarshi zaka ga kamanninshi da Fatun yayi shigar dogayen kayan yadi mai kyau kanshi sanye da hula tsaf tsaf dashi kaman ba daga k'auye yake ba, amman daka ganshi kaga cikakken bafullatani, A d'akin Amadu aka sauke shi fatuu sai faman tambayoyi take mashi tana tambayar yan'uwanta yana bata amsa da muryarshi mai sanyi daga ji baida hayaniya kuma ya iya hausa sosae don Fatun da hausa take mashi Magana koda yayi mata da fullanci amman sam basuyi hausa ba da gwaggo da ta shigo don su k'ara gaisawa, sam Fatuu tak'i barinshi ya huta yaci abinci sosae, tunda ta kawo mashi ta tasashi gaba tana ta bashi labarin Ya Handsome da duk Alkhairan da yake masu kuma har labarin yadda akai suka saba dashi saida ta bashi wanda ko gwaggo batasani ba har yake cewa ashe har yanzu baki daina rashin ji ba inna wuro (sunan da yake kiranta dashi kenan wato uwar masu gida don sunan Mahaifiyarshi ne aka sanya mata), rantsuwa ta hau yi mashi kan ta daina rashin ji kuma ma ya tambayi gwaggo, atare suka ci abincin gwanin burgewa har abaki take bashi, bayan sun gama ya d'an kishingida don ya huta ita kuma tace mashi zataje ta dawo, kopar gida ta nufa wurin kawu Amadu don tunda yaje suka gaisa ya dawo shagon, rok'onshi tayi wai ya kira mata Ya Handsome yace bai kira, Magiya ta fara yi mashi ta hanashi sakat har saida ya kira mata shi, cikin murna ko gaidashi bata yi ba ta sanar dashi Babanta yazo tana ta faman dariya, cemata yay yana tayata murna in ya dawo zaizo su gaisa tace mashi to,

Bayan sallar la'asar yazo gidan yana sanye cikin jeans da t-shirt gaba dayansu navy blue ne, hannunshi sanye da agogo bak'a hakama takalmanshi bakake ne sai sakin kayataccen kamshi yake, Amadu ya shigar dashi wurin Baban Fatun lokacin tana like dashi sai faman zuba take mashi ko islamiyya tace bata zuwa, bayan Amadu ya shigo ya sanar mashi cewa zasu gaisa da bako ya juya waje yace ma Haisam ya shigo, fatuu na jin muryarshi yayi yar sallama ta wani zabura ta tashi zaune, ganin shine da gaske yasa ta washe baki tace ma babanta to ga Ya Handsome d'in da take bashi labari nan, ganin ba abun zama yasa Amadu cewa bari ya d'aukko mashi kujera acikin gida haisam yace ya barshi, d'an duk'awa yayi suka gaisa cike da mutuntawa anan yake mashi godiya yace inna wuro ta fad'i mashi abun arzikin da yake masu, to shi d'inma dai cemashi yay ba wani abu, daga haka shiru ta biyo baya don gaba d'ayansu ba gwanayen Magana bane kai kace bashi ne Mahaifin Fatuu ba ta wannan fannin, muryarta kawai ake ji sai zuba take tana zuba uwar shagwa6a da shirme kala kala kanta na akan kafafunshi,

" Baffa na gaya maka Ya Handsome dinnan yana da motoci, in kana so sai ya kaika kaga garin nan" Fatuu ta fad'a,shiru baice mata komai ba hakan yasa ta d'aga idanunta tana kallonshi tace "ko baka son ganin garinne?",
fuskarshi da fara'a yana kallonta cikin harshen fulatanci yace mata ai ba dad'ewa zaiyi ba gobe da safe zai tafi, tana jin hakan ta fara bori tana tittirza k'afa akan katifar cike da shagwa6a tace " kai da ka dad'e baka zo ba kuma sai kace wai gobe zaka tafi, ni dai ban yarda ba Allah kwan",
Still Haisam yay yana kallonsu fuskarshi a sake shi kuma mahaifin nata sai murmushi yake da gani dai yana da fara'a sosae, ganin yadda take ta zuba shagwa6a ne yasashi cemata yaso zuwa tuni Ardo ne yay jinya shiyasa bai zo ba kuma har yanzu bai idasa warwarewa ba shiyasa bazai zauna ba don shi ke kula da harkokinshi da yawa acan, da bud'ar bakinta sai cewa tayi " Allah yasa ma ciwon mutuwa ne yakeyi kowa ya huta da masifa " tana yin Maganar suka had'a ido da haisam ya d'an harareta shi kuma baban nata kama kunnanta guda yay ya d'an ja ta saki yar k'ara tana fad'in " wad' muyal baffa, ba ya tsufa ba",
murmushi Haisam ya danyi kafin ya mik'e yay mashi sallama ganin yana kokarin tashi shima yace yay zaman shi da mota yake zai wuce ne, mik'ewa Fatuu tayi tana sanye da riga da skirt na shadda kanta ba kallabi tace ma babanta bari ita ta raka shi waje yanzu zata dawo,

Haisam da har ya nufi mota ya juyo sakamakon kiran sunanshi da tayi, tsayawa yayi ta k'araso tana ta dariya ta kasa ce mashi komae,
" U'r Happy Dad yazo ko" jinjina mashi kai tayi sai kuma ta kwa6e fuska tace " bacin ma wai gobe da safe zai tafi",

" yana da uzuri ne" ya fad'a yana kokarin juyawa,
" gida zaka koma?" ta tambayeshi, kai ya girgiza alamar a'a,
" To ina zaka?"
"Gym" ya bata amsa yana nufar mota,
" ko in zo in raka ka?" sai lokacin ya tsaya yay mata wani kallo ta kyalkyace da dariya,
" ina Aunty Anah?" ta tambayeshi bayan ta daina dariyar,
" tana tambayarki" ya bata amsa a takaice,
" wayyo, don Allah zaka k'ara kaini in ganta, wllh tana da kirki",
girgiza mata kai yay alamar a'a aikuwa ta fara d'an bubbuga kafa tana jujjuya kai, kai kawai ya d'an girgiza ya kai hannu ya bud'e motar ya shiga kafarshi guda awaje, ganin tak'i daina abunda take yasa yay mata alamar tazo da hannunshi, sealed Popcorn da tuwon madara ya mik'o mata ta amsa sai kuma cewa tayi "Ya Handsome na gane wayonka, ina yi maka rigima shine kaban wad'annan abubuwan don inyi shiru ka maida ni karamar yarinya ko",
d'an cije peach lip dinsa na kasa yay da alama ta kashe shi da mamaki, murya can kasa ya furta "kinsan ma rigima ne kike man ko Zarah?" jin haka yasa ta 6oye a gefen motar tana dariya, d'an leko da kanshi yay ya kalleta aikuwa da sauri ta kife fuskar, girgiza kai yay yace "ki koma kin bar dad shi kadae" yana fad'in hakan ya maida kafarshi ciki ta lek'a kanta tana kallonshi yay mata alamar taje da hannu, har saida ya tashi motar ya tafi tana ta d'aga mashi hannu, lokacin data koma cikin d'akin kawu Amadu Babanta har yayi bacci, bawan Allah tun karfe hudu na asuba ya taho ya sauka a Kano kafin ya hau motar Katsina, ya kwaso gajiya don akwae nisa tsakanin Katsina da Yola kusan fin awa goma yana hanya yazo kuma ta hanashi hutawa, Allah yaso yan hankali sunzo mata ta kyaleshi ta nufi cikin gida, tare suka ci abunda haisam ya bata da gwaggo amman fa sai da ta rage ma Baffanta, da daddare aka aiketa gidan hajiya ta kai mata tsaraba ananne tasan baban nata yazo tace ta tayata murna in Allah ya kaimu sa gaisa dashi, bayan ta dawo rigima tasa wai awurinshi zata kwana dole saidai Amadu ya tafi dakinta ya kwana,

Washe gari da safe Haisam ya parker akopar gidansu lokacin zai tafi wurin aiki, kiran Amadu yayi a waya yace ya d'an fito waje, bayan ya fito ya gaidashi cike da girmamawa, amsawa yay yace ya bud'e back door akwae sako ya kaima bako, wata katuwar leda ce mai hannu ya fiddo saida yay mashi godiya kana ya shige gida shi kuma ya tafi, gwaggo ya kaima sak'on yace inji Yaya haisam yace aba Baffan Fatuu, jinjina kai kawae tayi tana Murmushi ta jawo ledan ta bud'e, kaya ne ciki sosae, shaddoji dinkakku guda biyu daya mai babbar riga daya kuma dogayen riga da wando ne, sai guda daya da ba'a dinka ba sai kuma manyan yadi kala biyu, takalma da huluna kala bibbiyu sai agogo ma guda biyu sai kwalin turare guda ukku, duk yadda gwaggo taso kin yin mamaki saida tayi shi haka Amadu ma sai faman jinjina kai yake don Haisam ya iya yin kyautar ban Al'ajabi, lokacin da aka kai mashi kayan shima saida ya d'an rude ba kamar dayaga duka fa jiya ya sanshi gwaggo tace mashi haka halinshi yake, koda ya buk'aci zuwa yi mashi godiya Amadu ya sanar dashi ya tafi wurin aiki saidai ya kirashi awaya, koda ya kira bai d'aga ba almost 3 times gwaggo tace ya kyaleshi kawai in ya gama shiryawa ya kaishi wurin hajiya su gaisa sai yay mata godiyar,

Lokacin da suka je gidan cike da mutuntawa hajiya ta kar6e shi tana ta fara'a don bata ta6a ganinshi ba sai yau sai kuma a wani hoto da Fatun ta ta6a kawo mata can da dad'ewa shida mahaifiyarta, har Saude da Tk saida Hajiya ta kirawo tace suzo su gaisa da Baban Fatuu, suma cikin girmamawa suka gaidashi yana ta dae fara'a Fatuu na lik'e dashi har hajiya na tsokanarta tana cewa to ko zata bishi ne, ta mak'e kafad'a tace in taje aure za'ai mata gaba daya suka sa dariya,sosae yayi mata godiya lokacin da zai bar gidan, kud'i hajiya ta ba Amadu abashi acikin envelope ba tare da saninshi ba, har Amadun zai yi mata gaddama yak'i amsa tace yaushe ta fara yin wasa irin wannan dashi dole ya kar6a, bayan sun koma yay sallama da gwaggo alokacin Amadu ya bashi kudin da hajiya ta bashi yace suyi amfani dasu amman gwaggo taki amsa tace shi aka ba adole ya amsa don bai iya yin jayayya da ita, Fatuu da Amadu ne zasu raka shi tasha don anyi hutun Azumi shiyasa basuje makaranta ba, har kopar gida gwaggo ta rako su tana yi mashi Allah ya kiyaye Amadu na ruke da jakar da gwaggo ta zuba mashi kayan da aka bashi don yar jakarshi da yazo da ita bazata dauki ko kwatan kayan ba don yar k'arama ce iya kayan da zai canja ya sako a ciki hakan yasa ta bashi babba mai zip wadda ta d'auke duka kayan harda jakar da yazo da ita, akan hanyarsu ta zuwa bakin hanya don hawa keke napep ne ta tuna da Haulat, rokon Kawu Amadu tayi su bi ta lungun gidansu don Haulat d'in ta gaisa da babanta, bai mata musu ba suka bi ta lungun lokacin da suka karasa, da zata shiga kiran haulat d'in yace mata kar ta 6ata masu lokaci tace yanzu zata fito, bada jimawa ba kuwa sai gata ta fito da haulat d'in tana sanye da hijab har k'asa ta duka ta gaidashi tana ta murmushi ya amsa mata shima yana murmushin, ce masu tayi bari taje ta tambayo innarta sai su rakashi tare, lokacin da ta dawo wajen harda innar tasu itama ta lek'o don su gaisa, atare suka durkusa suna gaida juna kafin tayi mashi Allah ya kiyaye hanya, k'arasawa sukai bakin hanya suka hau Napep don zuwa tasha, lokacin da suka sauka Haulat taba kawu Amadu dubu dayar da innarsu tace abashi har yana cewa ai da bata bada ba, Motar Kano ya hau lokacin bai fi saura mutum biyu ba ta cika, Fatuu tace bazata tafi ba sai sun tafi yanata cewa su tafi tana mak'e mashi kafada saidae yay Murmushi kawai don ya fahimci har yanzu da sauran rigimarta amman acan k'asan zuciyarshi ba k'aramin farinciki yake ji ba da ganin yadda ta koma gaba d'aya ta canja daka kalleta zaka san tana cikin jin dad'i, ba'a dau wani dogon lokaci ba mutum biyun suka samu motarsu ta tashi suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login