Showing 123001 words to 126000 words out of 212491 words
da yake matanne yasa ta k'ara shan jinin jikinta,
" Zaraah..."taji ya kirata,aikam tun kafin ya rufe baki ta durkushe a inda take ta fara cewa"Wallahi Ya Handsome kaji na rantse maka tun bayan dana fasa maka gilashin mota ban k'ara yi ma kowa laifi ba, ba ruwana da kowa ko Malamin math da ya ban Assignment d'innan ai na fad'i maka ni bansan rashin kunya bane da bazan fad'i mashi hakan ba amman ni ba abunda nayi ma Uncle Bash wllh tun dae can da dad'ewa ne ya ta6a cewa nayi mashi tsoki kuma dae gaskiya nayi mashin amman ya bugeni kuma tunda na shiga English club ma muke shiri dashi don shine shugaba amman wllh in dae ce maka yayi nayi mashi wani abu to karya yake man kawai sharri yake son ja man" cikin karyewar murya ta k'arasa Maganar nan da nan idanunta suka kawo ruwa ta duk'ar da kanta k'asa,still yai yanata sauraranta har ta gama kafin ya d'an girgiza kai had'i da yin guntun Murmushi aranshi yake ayyana ita dae kuka bai mata wuya,a yadda halinta yake bai kamata ace tana da saurin kuka ba ko kuwa shi take ma hakan saboda yarjejeniyar dake tsakaninsu ta glass oho,
Sigh yayi kafin calmly yace"Zarah sit down"da sauri ta d'ago ta kalleshi ya d'an lumshe ido alamar eh,maimakon ta hau saman kujera sai ta raku6e agefen kujeran ta zauna kan Carpet,shi dai kallonta kawai yake bai dai yi mata magana ba,
"Why zaki ce malaminku yayi maki k'arya kinsan mi yace man ne?"
Da sauri ta d'ago tana zare ido ta dan girgiza kai alamar a'a, yaci gaba"kar ki k'ara cema babba yana k'arya ba teacher dinki kadae bama"da sauri tace"toh"idonta akanshi,shiru yayi kaman bazai k'ara cewa komae,
"shi teacher d'in da kike magana akwae wani list na textbooks da ya ta6a baki right?" jinjina mashi kai tayi alamar eh,
"Ok,ina list d'in?"
"Paper d'in na wurin gwaggo tun lokacin da aka bani nakai mata nace ance asiyo wad'annan littattafan to sai ta ba kawu Amadu tace ya tambayo mata kudinsu lokacin da zaije kasuwa to daya dawo ne yace mata duk shagon daya je babu su sai da aka mashi kwatancen wani Babban Bookshop acan ne aka samu wasu acikinsu wasu kuma suka ce sun k'are amman za'a kawo ita kuma gwaggo data ji suna da d'an kudi don akwae ma wani na English dubu biyar yake shi kadae sai tace gaskiya bata da kud'in da zata siye su lokaci guda amman akwae adashe da take yi wanda zata siya ma kawu Amadu freezer saboda azumi daya kusan zuwa ya rinka saida kankara in ta kwashi kudin zata siya mansu duka shi kuma sai ta nemi ciko ta siya mashi,to ita nike ta jira fa kuma shima Uncle Bash d'in in ya tambaya ai inace mashi ance za'a siyo"ta k'arasa tana ta nishi sai kace ya tambayeta duk wannan bayanin,shi dai yayi shiru yana sauraranta har ta gama,
Gently yace" je ki amso man paper d'in",
Bud'a idanu tayi"siyo man zakayi?"
d'an k'ank'ance idanu yayi"ko baki so?"
A shagwa6e tana tura baki tace"to amman ai tsada garesu fa sai a saka ka kashe kudinka hakanan,shima ba ance za'a siyo ba",
"Shine ai yanzu za'a siyo d'in ko saboda kina bukatansu"
"Ni dai gaskiya banso kaita kashe kudinka fa,in kuma suka k'are fa", d'an Murmushi yayi jin abunda tace,d'an gyara zama yayi ya jingina sosae yana kallonta,
" bazasu k'are ba inada su da yawa so don't worry about dat, yanzu kije ki kawo man and daga yanzu duk in kina bukatar wani abu game da karatunki ki sanar man" zaro ido ta k'ara yi a d'an rud'e tace "kai kuma ba gwaggo ba?"
"Yeah"ya bata amsa fuskarshi still da Murmushi,
" to saboda me?"ta sake tambaya,
"Saboda na fita kudi kuma abubuwa sunyi mata yawa kinga sai in rage mata burden ko",
d'age kai tayi gyalen ya idasa sa6ulewa ya tsaya kan kafad'arta a shagwa6e tace "to amman kai ai ba d'an gidanmu bane kuma sai ka d'aura ma kanka nauyi"
"Yanzu ai nazama ko baki so?"
"To ai sai ka dawo gidanmu zaka zama d'an gidan"
"Ok sai in dawo in kin tanadar man inda zan zauna",
" sai ka dawo d'akina ni kuma sai in koma na gwaggo,tunda akwae gado sai ka d'auki wannan kujeran daka fi zama tunda d'akin bazai isa asa dukkansu ba"still da Murmushi akan fuskarshi da alama yana enjoying hiran ne,
"Ok zanyi hakan,sai ki fitar man da ranan da zan dawo but ki fara sanar da Grandma d'inki",
Wani kallo ta bishi dashi baki bud'e alamar mamaki sai kuma tace" wllh nasan karya...au wasa kake ba dawowa za kai ba,tabb yama za'ai kabar wannan Aljannar duniyar ka koma gidanmu d'an kut dashi kaman zuciyar talaka,ai zafi da sauro ma kadae sun isheka ka gudu sai dai mu farka muga Ya Handsome ya tsere"ta k'arasa tanata dariya shima dariyar yake har hakoransa sun bayyana sosae ba kaman da tace wai gidansu kaman zuciyar talaka ko a ina ta iya wannan Maganar ya fad'a aransa,
"Yanzu dae kije ki kawo man abunda nace" ya fad'a bayan ya gama dariyar,amsa mashi tayi da to kafin ta yunk'ura ta mik'e tsaye har zata juya sai kuma ta juya da yar damuwa a fuskarta tace"to kuma Ya Handsome in Gwaggo tace ni na fad'i maka Maganar littattafan fa,tana iya duka na fa don tace kar na rok'e ka abu",
Shiru ya dan yi kaman mai tunanin wani abu sai kuma yace"ki fad'a mata shi teacher dinne yayi man magana"still da yar damuwa akan fuskarta tace"to Allah yasa ta yarda" har ta juya zata fita ya kirata ta juyo,tambayarta yayi Uncle d'inta nada waya tace mashi eh,yace tasan number dinshi tace eh ta sani yace ta karanto mashi dama wayarsa na aje akan kujera tun bayan da ya dawo,bayan ta bashi lambar wayar kawu Amadun yayi dialing kira yana jin ta fara ringing yace mata taje gidan kawai za'a bata ta kawo mashi,
Lokacin da ta isa kopar gidan Amadun bai acikin kiosk dinshi,tana shiga gidan ta ganshi atsaye shi da gwaggo abakin kopar d'akinta, k'arasawa tayi ta tsaya agefe tana ta faman zare ido,
"To shi bai gajiya ne yai ta faman hidima" gwaggo ta fad'a yayin da ta maida idonta kan Fatuu da sauri fatun tace "Uncle Bash ne yayi mashi Maganar d'azun daya kaimu Makarantar shine yanzu yace wai in kawo mashi takardar",jinjina kai kawae gwaggon tayi kafin ta k'ara cewa wani abu Amadu ya rigata da fad'in" to wai duk minene na damuwa da jan Maganar ma tunda dai ba rok'onshi mukai ba shi yace abashi ki bata ta kai mashi kawae",
"Hakane amman dai wai kar abun yayi yawa aita d'aura ma Mutum hidimar da ba tashi ba" gwaggon ta fad'a da yar damuwa,
"Ba wani abunda zaiyi yawa tunda yana da hali,ki d'auka kawai Allah ne ya dubi duminiyarki kinsan in bawa ya dogara ga Allah sai ya bud'a mashi ta hanyar da bai ta6a zata ba,kuma kinga dama ni da ita duk marayu ne haka kike ta kula damu,to ki d'auka sauk'i ne Allah ya kawo maki ta hanyarshi don haka ki d'aukko takardar ki bata ayi mashi godiya kawai",
jin hakan yasa da sauri Fatuu ta kar6e" haka ma yace wai duk in ina buk'atar abu game da karatuna in sanar mashi,da nace saboda mi sai yace wai ke abubuwa sunyi maki yawa zai rage maki nauyi",
Da sauri Amadu yace"Kinji ko,kar ki wani damu",
jinjina kai tayi cike da gamsuwa"shikenan,Allah ya saka masu da mafificin Alkhairi,yasa ya gama da duniya lafiya ya biya masa bukatunshi na Alkhairi" gaba d'aya suka amsa da Amin,daga haka ta shiga ta d'aukko mata takardar dake d'auke da sunayen littattafan ta bata ta kai mashi.
Lokacin data koma bai cikin parlon hakan yasa tayi tunanin ko ya koma cikin Bedroom ne,nufar corridor d'in tayi ta d'an shiga daga ciki ta rafka uwar sallama,
"Assalamu alaikum Ya Handsome ga takardan" jin shiru yasa ta sake maimaitawa still bata ji yayi Magana ba hakan yasata k'ara d'aga murya tace"Ya Handsome na dawo ga takardan ko in shigo in kawo maka ne?"
"Tunda d'akin ki ne ba sai ki shiga ba"
ba zato ba tsammani taji daga bayanta ya fad'i haka,aikuwa a furgice ta juya ashe bai cikin d'akin fita yayi ya d'aukko abu a Mota,hannu tasa ta rufe baki tana gumtse dariya shi kuma ya d'an harareta ya nufi inda ya tashi ya zauna bayan ya aje abunda ya d'aukko kan c-table, nufo shi tayi tana zuwa gefenshi ta mik'a masa takardar kafin ta zauna kan carpet,dubawa ya d'an yi itama ya d'aurata kan c-table din,
"Kasan inda ake saida su?" kai ya d'aga mata alamar eh,
"To yaushe zakaje ka siyo?" shiru ya d'an yi sai kuma yace"After Asr prayer",
"Kai wai yanzu ma ba dadewa kenan,to yau bazaka je d'aga karfen bane?" wani kallo yayi mata ba tare daya ce komai ba hakan yasata gwalo ido don a tunaninta ko tayi laifi ne da sauri tace"haka naji Hajiya tace rannan shiyasa nima nace",
D'an lumshe ido yayi calmly yace"ba sunanshi kenan ba exercise ne,kinsan mi kenan ko?"da sauri ta d'aga kai tace"to bazaka je exercise d'in ba?"
"Zanje amman sai na dawo"
"To kullum kake zuwa exercise din?"
Girgiza mata kai yayi"bani zuwa weekends but nakan yi saturdays wani lokacin, sundays dai bani yi"
"Yauwa to tunda baka zuwa ranar lahadin ka bari sai ranar sai kaje ka siyo man kaga ranar Monday ba sai inje dasu ba kawai"
Kai ya k'ara d'an girgizawa"No,tunda yayi Magana gobe yakamata ki shiga dasu,lafiya lou har naje na dawo ai",
kai ta d'aga alamar gamsuwa sai kuma tace"to don Allah zan raka ka Ya Handsome "
Shiru ya danyi sai kuma yace"Ai ba wani dad'ewa zanyi ba zan dawo",
" to ba sai mu wuce wurin exercise d'in ba in ka gama sai mu dawo ko",wani kallo ya bita dashi,
"Pls don Allah kaje dani,wllh ni da kake gani na kifin rijiya ne duk bansan wurare ba in baya ga kasuwa sai asibitin da gwaggo ke aiki sai wasu yan wurare kad'an fa" still kallonta yake,yana ganin k'okarinta intayi wata Maganar just cikin 3 years ta iya hausa sosae bacin ko agida tace wani lokacin Grandma d'inta fulatanci take mata,
"Pls don Allah Sweetheart ka tafi dani" Fatuu ta katse mashi zancen zucinshi,tunani ya shiga yi ina zaije da ita in ya tafi da ita,yana da register da gym ukku so baisan wanne zaije da ita ba duk da mata na zuwa amman ba kamarta ba,
"Don Allah Sweetheart Ya Handsome ka tafi dani inga gari" ta k'ara fad'a a shagwa6e,
sigh yayi idonshi akanta yace"in matana taji ki kina ce man Sweetheart d'innan zata fasa maki baki fa" yayi Maganar fuskarshi a sake kaman zaiyi dariya,
"Nasan wasa kake,Kai da ma baka da ko budurwa balle mata kuma",
jinjina kai kawai yayi sai kuma yace" to mi zaki fad'i ma grandma d'inki?" da sauri tace"yo zance mata zan bika siyo littattafan daga nan zan raka ka wurin exercise in ka gama sai mu dawo",
nodding kai yayi"Ok kije ki fad'a mata,if she agrees sai kizo in an gama salla",
Yar k'arar murna ta saki ta fara mashi godiya daga haka ta mik'e ta nufi kopar fita da sauri,har zata kama kopar ta bud'e ya kirata ta juyo,
" Ki fad'i mata exactly as u said,in kikai man karya....." kafin ya ida maganar ta katseshi ta idasa mashi ".....in kika man k'arya ina zaune zan gani" tayi Maganar tana kwaikwayon yadda yake Magana harda wani d'age gira daga haka ta fuce da gudu Haisam bai san lokacin da kyalkyace da dariyar da bai tunanin ma ya ta6a yinta, arayuwarshi ba mai mashi irin abunda Fatuu ke mashi haka kuma bai ta6a sake ma wani mutum 6are kaman yadda yake mata ba ko k'annenshi bai sake masu kaman yadda yake ma Fatuu ayanzu,wato ashe ta ruke Maganar da yayi mata lokacin da tazo bashi hakuri ta dau alkawarin ta daina fada da kowa yace inma tayi yana zaune zai gani kar tayi tunanin zata mashi wayo,girgiza kai yayi a fili ya furta"ZARAH".
Tana komawa gida cike da farinciki ta sanarma gwaggo kaman yadda tace zata fad'i matan sai dai da farko nunawa tayi bata yarda ta bishi ba kawai salon taje ta takura mashi,magiya ta shiga yi mata tana rantsuwar bazata takura shi ba,da kyar gwaggon ta amince bayan taja kunnanta sosae,cike da zumud'i ta nufi bandaki don yin wanka tana cikin yi aka fara kiran sallar la'asar da sauri ta gama ta fito tayi walwala kafin ta nufi dakinta ta fiddo sabuwar maroon jallabiyarta mai ratsin brown ta zumbula bayan tasa undies sannan ta duddungura sallar shaf shaf tana gamawa ko addu'a bata yi ba ta mik'e ta nufi gaban mirror ta fara yin kwalliya dama ta jere kayan shafan da Haisam ya siya mata,kwalliya tayi simple ba mai hayaniya ba ga powder din ta kwanta mata sosae tayi wani fayau,dama yanzu fatarta ta k'ara yin smooth saboda mayukan da take amfani dasu,ta shafa maroon janbaki wow,jama'a kuzo kuga Fatuu yanmata,fita tayi taje wurin gwaggo tace ta bata takalmanta na sallar bara dama ita ta 6oye su don Fatuu in tana son abu bata san ta kyaleshi ya huta ba yanzu ya tsufa,ba don gwaggon na adanawa ba shima takalmin da tuni ya tsufa koma ya lalace,d'aukko mata tayi da yar jakarshi bak'a shima bak'i ne mai tudu nan da nan ta idasa fitowa a yar budurwa,sark'a da yan kunne harda d'an agogo golden gwaggo ta fiddo mata harma ta tayata sakawa,tana niyyar juyawa ta fita gwaggo tace"wannan kitson na gaba ki maida shi baya ki hade ki kulle kar ki fita haka dashi",amsa mata tayi da toh daga haka ta koma dakinta tayi yadda gwaggon tace ta feshe jikinta da turare harda bakinta ta fesa mouth freshner dama tayi brush da ta shiga wanka,tsayawa tayi tana kallon kanta a madubi,kayataccen Murmushi tayi a fili tace"Fatuu kinyi kyau kaman sarauniya" tuntsirewa tayi da dariya daga haka ta fita daga d'akin ta d'aga murya tana fad'in "Gwaggo sai na dawo" lek'owa gwaggon tayi tana kallon bayanta har ta fita bayan tace mata adawo lafiya,d'an girgiza kai tayi ganin yadda Fatunta ta fara zama Budurwa.
Tana niyyar shiga part d'inshi ya 6ullo daga corridor d'in da zai kai ka cikin harabar gidan,tana ganinshi ta tsaya,suna had'a ido ya d'an buda mata ido alamar mamaki hakan yasa tasa tafukan hannayenta ta rufe fuska alamar kunya,
"Nayi kyau?" ta tambayeshi bayan ta bud'e fuskar,kai ya d'aga mata alamar eh kafin yace taje parking space ta jira shi,amsa mashi tayi da toh tabi ta gefenshi ta shige cikin gidan shi kuma ya ida shigewa part din nashi,tana shiga ta nufi part d'in hajiya don ta gaidata Saude ta sanar da ita Hajiyar bata nan bayan ta gama yabon gayun nata hakan yasa ta juya ta fita,tana isa wurin aje motocin Haisam ya fito ya nufo parking space d'in yana sanye da Sportswear ya ratayo jakarshi a hannu guda,k'ura mashi ido Fatuu tayi tana kallonshi don shi komi yasa kyau yake k'arawa,ganin kallon da take mashin yasashi sadda kanshi k'asa har ya k'arasa cikin wurin,back door na mota ya bud'e ya saka jakar,yana k'okarin bud'e gaban motar Fatuu tace"Ya Handsome mu hau wanccan mashin din" juyawa yayi ya kalli bike d'in da take nunawa kafin ya juyo yana kallonta, imagining ya fara abunda zata iya yi mashi in ya hau bike d'in da ita hakan yasashi girgiza mata kai yace"zamu a Mota",turo baki tayi tana d'an yamutsa baki alamar ba haka taso ba,ganin hakan yasashi cewa"wani lokacin" ya jaddada mata da kanshi itama ta d'aga mashi alamar toh daga haka ya bud'e Motar ya shige yace mata ta zagaya ta shiga,bayan ta shiga ya fiddo motar cikin harabar daga haka yajata suka fuce.
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔
*Mallakin*
⬇️
*🌹ZAINAB LALUH*📲✍
_~(Oummu imam)~_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
5️⃣3️⃣
Wani Babban Bookshop ya nufa dasu, a gefen wurin ya parker motar, da har zaice mata ta jirashi sai kuma yace ta fito sakamakon tunawa da Maganar data yi na cewa ita kifin rijiya ce duk bata san wurare ba, suna shiga ciki Fatuu tabi wurin da kallo don an tsarashi sosae gashi k'ato ne akwae duk wani abu da Mutum zai iya bukata a Bookshop, wani k'aton Alhaji ne zaune saman kujera acan ciki yana ba yaran shagon umarnin d'aukko ma Mutane abubuwa hannunshi ruke da calculator da littafi da alama lissafi yake, yana hango Haisam ya fara washe baki yana mashi dariya,
"Barka da zuwa yalla6ai" Alhajin ya fad'a lokacin da suka k'arasa,
"Yauwa Alhaji,ya kasuwa" ya fad'a cikin cool voice dinsa,
"Kasuwa Alhamdulillah gamu cikinta" Alhajin yayi maganar still da fara'a a fuskarsa, maida kallonshi yayi kan Fatuu data k'ura mashi ido tanata kallon tumbinshi cikin ranta kuwa tunani take wai ko dai ciki gareshi ne,
"Sannu yanmata"Alhajin yace mata, saidai sam hankalinta na kan tumbinshi har saida Haisam ya kira sunanta sannan ta maido idonta kanshi yay mata nuni da ana mata Magana, kallon Alhajin tayi dake mata Murmushin yake don ya fahimci abunda take kallo ya sake ce mata sannu sai lokacin ta gaidashi ya amsa mata, d'aura takardar yayi saman wurin dama ya fiddota daga cikin pocket d'in wandonsa yace ma Alhajin wannan yake so, da sauri ya kira wani matashin saurayi acikin yaran shagon yace ya mik'o masa takardar, bayan ya duba ya d'ago yace ma Haisam duk akwaesu nan take ya nuna ma saurayin inda zai d'add'auko su, bayan an fiddo mashi su duka Alhajin ya tambayi shikenan, Haisam yace a d'aukko mashi Calculator guda biyu da Math Sets, da sauri Fatuu ta kalleshi tace" Ya Handsome guda biyu biyu ai sunyi yawa kuma ma ina dasu don dai sun tsufa ne wasu abubuwan maths set d'in duk sun 6ace, amman dai guda d'aya ya isa" shiru yayi mata duk idanun mutane suka dawo kanta dama kuma tunda suka zo wurin tun a waje aketa faman kallonsu,(dama abu