Showing 45001 words to 48000 words out of 212491 words
kopan ta turata kad'an sannan ta turo kanta tana leken cikin falon,a iya hangenta bata hango mutum ciki ba sai computer da ta gani ajiye saman table hakan yasa tayi tunanin ko ya shiga cikin d'aki ne,fiddo kanta tayi waje ta shiga tunanin ko har yayi bacci ne,to yanzu ya zata yi ita?wata zuciyar tace anya kuwa yayi bacci,ai da ya rufe kopa,can kuma tace k'ilan kuma bai rufe kopa tunda akwae jami'an tsaro a bakin gate.....a daidai lokacin haisam ya shigo cikin part din har ya iso bakin balcony din bata ji motsinsa ba,k'ara tura kopan tayi tana sake lek'en cikin falon taga ko ya fito,cike da mamaki haisam ke kallon bayanta yama rasa tunanin da zai yi akanta babban abunda ya d'aure mashi kai shine mike kawo ta part d'insa?miye hadinshi da ita,sannan yama akai tasan inda yake,fuska a matukar d'aure tamkar bai ta6a daria ba ya tattaka stairs din ya haye"Excuse me!"yace mata,
a firgice fatuu ta juyo don sam bata ji motsin shi a bayanta ba balle tasan dashi a wurin,a tsananin tsorace take kallonsa ganin ya daure fuska tamau,wani irin bugu zuciyarta ta shiga yi lokaci guda ta fara ja da baya,atunaninshi rugawa zata yi kaman yadda tayi dazun hakan yasa a kausashe yace"kina guduwa zan sa aje har gidanku a kamo ki,gida mai kiosk right?" hannu fatuu ta shiga yarfawa jin abunda yace,kenan da gaske ne duk abunda Gaye ya fada mata,don dama yace mutumin ya tambayeshi kwatancen gidansu,lokaci guda ta rude ta kid'ime ta shiga fadin"innalillahi....nashiga ukkuna"tana ta faman yarfa hannu kamar wadda wuta ta kona.
*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*
_A heart touching love story_
_*BY ZAINAB LALUH📲*_
*Paid Book*
*2️⃣6️⃣*
kama handle din kopan yayi ya tura kafin ya juyo fuskan nan ba wasa ko kadan yace"biyo ni! a hankali ta fara jan k'afafunta kaman wadda kwai ya fashe mawa a ciki tabi shi ciki kaman yadda ya bata umarni,haisam na shiga ya wuce saman kujera wurin da ya zauna d'azun da Abbas yazo,ita kuwa fatuu tana shigowa wani ni'imtaccen sanyi had'i da daddad'an kamshi suka kai mata karo,zaro idanu tayi baki bud'e ta shiga bin ko'ina na falon da kallo,ba komai yafi dauke mata hankali ba face chandalier(fitilan sama) yadda take d'auke da sarkoki masu kyau,tunda take bata ta6a ganin irin fitilan a zahiri ba sai acikin film din yan kasashen waje,ita bata ma ta6a tunanin akwae irinta a Nigeria ba,gaba d'aya ta saki baki tana ta kallonta har gyalenta ya zamo ya tsaya kan tudun gashinta dake fake,
Ganin bata k'araso cikin falon ba kuma yaji lokacin da ta shigo yasa haisam waigawa ya kalleta,tsayawa yayi yana kallon ikon Allah kaman ba itace ke kerma ba,bai ce mata komai ba ya juya yai powering laptop up ya jingina da kujera ya jira tagama booting kafin ya fara daddanata kuma har lokacin fatuu bata daina kalle kallen da ta ke ba,ganin bata da niyyar shigowa ga dare nayi shi kuma yana son yaji abunda ke kawota part din nasa yasa shi daukan wayarsa ya d'an bubbuga gefenta a saman c-table,aikuwa firgit fatuu tayi ya juya ya dan kalleta ya had'e giran sama da ta kasa,hakan yasa da sauri ta nufo cikin falon can gaban red armchairs ta wuce tana isa gefensu kawai ta zube saman gwiwowinta tayi kneel down,
baice mata komai ba yaci gaba da operating laptop d'in hakan yasa ta samu daman cigaba da kallon fitilar da alama ba k'aramin daukan hankalinta tayi ba,a hankali ya d'ago idanunsa ya dan kalleta sai kuma ya mik'e ya nufi bedroom dinsa tabi bayansa da kallo har ya shige kafin ta maida kallonta kan fitilar dai,
bai dau lokaci ba ya fito hannunsa dauke da wani k'aramin kwali,daidai bakin corridor ya tsaya ya kai hannu ya latsa wani switch lokaci guda hasken fitilar da fatuu ke kallo ya dauke,sai kuma ya k'ara latsa wani lokaci guda hasken wasu fitilun ya gauraye gidajen dasu T.V suke ko wane gida na pop cast din na d'auke da fitila hakan ba k'aramin kawata wurin yayi ba,ai kuma sai ta maida kallon nan wurin har wani dan dukar da kai take,ita mamakinta daga ina hasken ke fitowa don ba'a ganin fitilun sai dai hasken kawai,komawa yayi ya zauna ya fara kokarin bude kwalin da ya fito dashi hakan yasa fatuu ta maido hankalinta kanshi tana so taga minene a ciki,screen glass ne ya fiddo wanda yake sawa in zaiyi aiki da dare don yai protecting idanunsa daga illar hasken screen,binshi da kallo fatuu tayi lokacin da yasa glass din don ba karamin kyau yayi masa ba tamkar fashioned glass haka yake,kasa d'auke idanuwanta tayi sai kallonshi take tun daga saman kanshi har kasan kafafunsa cikin ranta tana ta mamakin yadda akai hajiya ta haifi mai kama da yan kasan waje ita da take bak'a kuma ba wani kyau ne da ita sosae ba,shikam ji kyau kaman shi yayi kansa ta ayyana a ranta,ga dogon hanci ba kaman na hajiyan ba d'an mai fadi dashi,ji yayi a jikinsa tana kallonsa hakan yasa ya yi mata kallon kasan ido suka had'a idanu,da sauri ta sadda kanta kasa don sai taga kaman harararta yayi,tana ta wasa da yatsun hannunta gabanta na cigaba da faduwa.
"mi kike zuwa yi apartment dina? Ta ji ya jefo mata tambaya,
Da sauri ta d'ago ta kalle shi tana faman zare ido,ci gaba yayi da magana ba tare da ya kalleta ba"ina sauraranki,ki gaya man abunda ke kawo ki nan don dazun ma naga kinzo" gabanta ne ya cigaba da bugu da sauri da sauri,sai faman motsa baki take ta rasa ma ta ina zata fara,mi zata ce mashi,d'agowa yayi furiously yace"am i not talking to human being? ganin yadda yayi maganar yasa da sauri ta fara magana cikin in'ina tace"d...da...dama..." sam ta kasa magana saboda kafeta da yayi da ido sai faman kerma hannuwanta ke yi,ya fahimci ta tsorata dashi hakan yasa yadan sassauta daure fuskan da yayi yai lowering voice d'inshi yace"uhun dama what?"
"dama zuwa nayi na baka hakuri don Allah kayi hakuri ka yafe man laifin da nayi maka,na tuba Allah bazan k'ara ba" ta k'arasa maganar tana dan ta6e baki alamar zata fara kuka sai kace k'aramar yarinya lokaci guda hawaye ya fara sauka daga idanuwanta tasa gefen gyalenta tana gogewa,
"wonder shall never end.." abunda haisam ya fada cikin ransa kenan,shi mamakinsa wai hakuri tazo bashi,shi da tunda tayi masa laifin yama manta da ita,to miyasa zata zo bashi hakuri?ya jefa ma kansa tambaya lokaci guda kuma ya tabbatar ma da kanshi dole akwae dalilin yin haka,wannan bayin kanta bane don bai tunanin tana da cikakken hankalin dama zata gane tayi laifi har ta bada hakuri,amman koma miye dalilin he will find out now.
Tsayawa yayi yana kallonta kaman mai nazarin wani abun sai kuma ya janye idonsa yaci gaba da abunda yake yi ita kuma sai faman murzar ido take ita ala dole kuka take kaman yadda haulat tace tayi,"wani laifi ne ma kika man? ya jefo mata tambaya ba tare da ya kalleta ba,da sauri ta d'ago tana kallonshi kaman ba itace mai murzar idanu ba,mamaki ne ya cikata aranta tace"kenan ma ya manta abunda nayi masa,dama banzo b...." ya katse da cewa"sai na maimaita maki ne? da sauri tace "a'a,d..dama nice wadda ta rotsa maka gilashin mota,amman na tuba bazan k'ara ba"tayi raurau da idanu alamun zata yi kuka tana ta6e baki,
D'agowa haisam yayi ya had'e hannuwanshi ya daura ha6arshi a sama yana kallonta hakan yasa ta sunnar da kai ya lura bata son had'a ido dashi ajiyar zuciya ya sauke yace "miyasa kika zo bani hakuri?" da sauri ta sake d'agowa tana kallonshi sai faman zare ido take sam bata so ta sanar dashi yadda sukai da Gaye don kada yace ashe ba don Allah tazo bashi hakurin ba sai don taji gilashin nada tsada kaman yadda haulat ma ta gargadeta,lokaci guda ta fara tunanin karyar da zata fada masa...kaman haisam yasan abunda take tunani yace"mark u!ba'a man k'arya,da zaran kika fad'a man karya yanzun nan zan gane karya ki ke and I hate people who're telling lie kinga laifinki zai kara yawa kenan" wani irin kuka cikin fatuu yayi ta had'iye miyau da kyar, shikenan ba daman tayi masa karya don ta yarda sosai da abunda yace ta k'ura ma computer din gabanshi ido tana tunanin ko tanan yake ganewa in an masa karyar don taga wasu abubuwa jone ta gefenta.
"baki ji mi na tambaye ki bane?bana son maimaita magana" fuska a d'aure yayi maganar hakan yasa fatuu gyara kneeling dinta ta fara motsa baki cike da fargaba tace"d..daman Gaye ne yace wai...wai gilashin motan nada tsada sosae,wai bazaka ta6a yafewa ba sai an biya ka,duk da ni naga kana da kalan masu kirki,am..amma shi yace wai in ba'a biya kaba gidan yari za'a kaini...."ta kwashe duk yadda sukai da gaye ta sanar masa tana ta d'age baki tana langa6ar da kai ita irin yaji tausayinta d'innan",
Sigh haisam yayi cikin ransa yace "exactly my thought,cire hannuwansa yayi daga k'asan ha6arsa ya maida kallonshi kan laptop din gabansa "wanene Gaye? Kaman jira take da sauri tace"wani mara jin magana ne anan unguwar d'an shaye-shaye yace wai yaga sanda na jefi gilashin motan ka kuma wai shi ka tambaya kwatancen gidanmu" d'an guntun murmushin gefe yayi jin abunda tace ga kuma k'aryar da gayen yayi masa don ya gane wanda take magana akai,kallon k'asan ido yayi mata"kice mai irin halinki kawai" da sauri tace"ai ni bana shaye-shaye kuma ma ni yanzu na shiryu na bar rashin ji daman shaidanu ne suka yiman fitsari a kai haka kaka na ke cewa" ta k'arasa tana ta6e baki alamar zata cigaba da kuka,
Danna wani key haisam yayi da karfi da alamar dot yayi kafin ya d'ago sosai yana kallonta on a serious note yace "While,duk abunda guy din ya fada maki gaskia ne,bcos i see no reason just don na raba ku fada zaki man asara irin wannan,dama abunda yasa ban dau mataki tun ranar ba lawyer na bai gari don bani son ai wasting time dina shiyasa ban reporting wurin police ba,gara muje court kawai a biyani hakkina,but luckily enough ya dawo yau so gobe zamu tafi can don already yasa anyi filing case din" ai ba fatuu ba ni kaina saida gabana ya buga don ba alamar wasa a fuskarsa yayi maganar,ita kam fatuu tsananin tashin hankali ta shiga,kuka na kirki ta fara tana masa magiya,
fad'i take"Don Allah,don soyayyar ka da manzon Allah,don hasken goshin manzon Allah kayi hakuri,in kana son ga kabarinka gana manzon Allah,in kana so ka gaisa da manzon Allah(S.A.W) yaya handsome kayi hakuri ka yafe man na tuba Allah bazan k'ara ba...." cike da mamaki haisam ke kallonta ganin yarda duk ta tashi hankalinta tana masa wani rokon da shi tunda yake bai ta6a jin kalarsa ba ga wani suna da ta kira shi dashi wai handsome,jingina bayansa yayi da kujeran yasa hannu daya ya rike ha6arsa had'i da bakinsa yaci gaba da kallonta kaman mai nazarin wani abu,ita kuwa har lokacin kuka take ga majina dake ta zubo mata sai faman sa gefen gyalenta take tana gogewa,hakan da take yasa haisam jin kyankyami don ya tsani majina bama ita kadai ba sam baison abun k'azanta,tsam ya mik'e daga inda yake ya nufi fridge dinsa don tun d'azun yake jin kishi saboda da yaci abinci baisha ruwa ba,ya bude ya d'auko lemun gwangwani tare da wani glass tumbler mai kyau ya rufe fridge din ya dawo cikin falon ya aje su a gefen laptop din sannan ya sake juyawa ya nufi wurin tv cikin wani gida ya dauko silver tissue box mai shegen kyau sai kyalli yake ya dawo ya zauna dashi a hannunsa ita dai fatuu sai binsa take da ido tana murzar idanunta da gyale tana cigaba da yin shesshekar kuka ga wata ajiyar zuciya mai k'arfi da take yi,
d'ago kanta tayi suka hada ido yayi mata alamar tazo da hannunshi,mikewa tayi ta nufi inda yake a gefen center table din ta durkushe idanunta sunyi jawur har sun fara kumburi,miko mata d'an akwatin yayi tasa hannu biyu ta amsa tana kare mai kallo don ta rasa mi zata yi dashi duk da tissue din ta leko,ganin haka yasa ya d'an duku ya kar6i abun ya jawo tissue din ya 6allo mata kana ya mika mata ya aje box din a saman c-table ya koma ya jingina yana cigaba da kallonta ahankali ta kai tissue din hancinta tana sunsunawa saboda wani sanyin kamshi da take kaman daga sama taji yace"abunda na baki ki da ita kenan?"cikin sauri ta fara goge fuskar tata sai murzar fuskar take still kallonta yake a hankali ta saci kallonsa suka had'a ido hakan yasa a hankali ta cire tissue daga fuskarta ta rike a hannu gyara kneel down din tayi taci gaba da rok'onsa,
cikin marairaicewa tace"don Allah yaya handsome kayi hakuri,kwarankwatsi kaji na rantse bazan k'ara ba,don Allah yadda Allah ya rufa maka asiri kake a aljannar duniya kada kasa akai ni gidan yari,ka barni inci gaba da kwana ad'an gidanmu ina cin abincin gwaggota,don wllh ko munje kotun bani da kudin da zan biya ka Allah kuwa" tana maganar tana d'an jujjuya kai lokaci guda wasu hawayen suka gangaro,
Shi abunda yafi daure mashi kai yadda yarinyar ta tashi hankalinta akan maganar biyan kudin,koda su talakawa ne bai yi tunanin zata tashi hankalinta har haka ba,nan take ya fara tunanin ko ana maltreating yarinyar ne,cike da son gano hak'ikanin gaskia cikin cool voice yace"ai bake zaki biya ba,dama duk in yaro ya nemo rigima ai parents dinshi ne a ciki in abun biya ne su zasu biya ke ai nasan bazaki iya biyana ba" kaman jira take ya gama maganan ta kar6e"ai ni a wurin kakata nike kuma bata da kudi talaka ce ita"takai maganar tana sauke ajiyan zuciya,
"Amman ai guy din nan yace tana aikin asibiti kuma nasan ana samun kudi a aikin..."da sauri fatuu ta saka salati"Innalillahi... Wallahi gaye bai tsoron Allah,na rantse karya ya fad'a maka",
yace"kenan bata aikin? tace "A'a ai kai ba'a yima karya, tana yi amman fa attender ce a asibitin,kasan miye attender din? ta tambayeshi,a hankali ya girgiza mata kai alamar a'a, "masu fa share-share da goge-goge har jinin haihuwa su ke gogewa" ganin ya d'an yamutsa fuska yasa da sauri tace"ai sai sun sa safar hannu suke yin aikin kuma in sun gama suna wanke hannuwansu,kuma ma ita gwaggon tsafta gareta kullum da ta dawo aiki take yin wanka kuma ta wanke kayan aikin" d'an yamutsa baki yayi yace"kyauta take aikin ne" tace"a'a ana bata albashi amman basu da yawa abinci take siya mana bama su isa mu rinka cin shinkafa kullum sai an had'a da tuwo",
"Ina Dad dinki?ya tambayeta,tace" ba a garin nan yake ba yana Yola acan jimeta anan kauyenmu yake sunan shi rugar baffa ard'o",
"ku fulani ne kenan? daga masa kai tayi alamar eh,yace"kuna da shanu?" batare da ta kawo komai a ranta ba ta k'ara daga masa kai alamar eh,dan guntun murmushi yayi" shikenan sai abani shanun madadin kudin gilashin,ni kuma nan yan kud'adena da nike saving sai in bada a gyara man glass din,tunda na fahimci cash bazasu samu ba"
tunda ya ambaci shanu gaba daya ta k'ara rikicewa ta wani zazzaro idanu tana kallonshi lokaci guda tasa tafin hannunta na dama ta rufe bakinta tana girgiza masa kai da sauri,shi dai sai kallon ta yake yana k'ara mamakin yadda ta kara rudewa don yace abashi shanu kuma,dan daure fuska yayi yace"kina nufin shanun ma bazai samu ba duk da akwai? baki na kyerma tace"kwarankwatsi kaji na rantse ard'o bazai ta6a yarda ya bada shanu goma ba akan laifin dana aikata,ai ko baffana ya aikata bazai bayar ba balle ni...."waye shi" ya tambayeta,da sauri tace"kaka na ne wanda ya haifi baba na kuma shine mai garinmu" ta6e baki haisam yayi"ni ai dama bani da case da shi,shi ina ruwanshi Dad d'inki shine zai biya ba grandpa ba" cije le6e fatuu tayi alamar bazaka gane ba,hawaye suka gangaro mata tace"ai shi Baffa na baida shanu goma yan kad'an gare shi ko biyar ma basu kai ba kuma duka ard'o ne ke iko dasu,basu isa suyi wani abu dasu ba batare da ya bada izini ba,nasan wallahi bazai bayar da shanun ba koda harbeni za'ai a gabanshi kuwa..." muryarta ce ta karye ta fashe da kuka,
d'an murmushi yayi ba tare da ta gani ba yace"bai ga za'a harbe kin bane" tsayawa tayi da goge kwallan da take,
"wallahi ni nasan bazai bada ba,ko fa Akuyan Jibo dana jefa ta mutu da kyar ya yarda aka biya shi..."kawai sai gani Haisam yayi ta kwashe da daria tana fad'in"wllh ranar yakin badar akai..." ganin yadda haisam din ke kallonta yasa ta shiga daidaita natsuwarta tana fadin"kayi hakuri wllh abunne dariya yake sani in na tuno ko banyi niyyar yin dariyar ba" tayi maganar tana turo baki,shi dai kallonta kawai yake can cikin ransa kuwa mamaki yake wai wadda ke cikin wani hali ce haka take daria lokaci guda yai assuring kansa cewa yarinyar is Mental,
Hannu ya kai ya d'auki lemun gwangwanin daya daukko ya bud'e hadi da tsiyayawa a cup ya dauka ya kai bakinsa,tunda ya fara tsiyaya lemun ta tsaya cakk cike da mamakin wane irin lemu ne wannan take binsa da kallo har yakai bakinsa ya dan kur6a sau biyu kana ya aje"kice dama kinsaba jifan abun mutane ki kashe masu and the worse of it shine da har abu mai rai kike jifa ki kashe",
"Wllh ita kadae ce babban abu mai rai dana ta6a kashewa,sai su 6era,kyankyaso,da kadangare su kuma ai kaga suna cutarwa ko....yauwa na tuna na ta6a karya ma Altine k'afan kazarta amman wannan ramawa nayi, nima take man kafan d'an kaza na tayi kuma ai ba haramun bane in an maka abu kaji baka iya hakuri ka rama ko,ko ita akuyan jibon ba hakanan na kasheta ba laifi tayi man kuma ma wllh bada niyyar kasheta na jefetan ba" ta karasa sai faman nishi take tana