Showing 165001 words to 168000 words out of 212491 words

Chapter 56 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

1010

Najeeb yay kafin yace "look dude in ana magana irin wannan just keep ur mouth shut, kai dama ai bakasan mi Duniya ke ciki ba kai da H,Zakee har gara ma shi yana da d'an dalili kai ko in ba cutar kanka ba ba abunda kake sam baka san miye dad'in duniya ba, to ni naga abunda nagani atattare da girl din can..." tun kafin ya rufe baki Abbas ya bushe da wata yar iskar dariya hakan yasa Najeeb ya maida idonshi kanshi "Yauwa My Man kai nasan kaga abunda nagani ko?" jinjina mashi kai Abbas yay alamar eh,

"Obviously, Wannan yarinyan ta samu kiwo ba k'aramar Mace za'ai ba wllh so H,zakee in son Mom d'innan naka pls ya za'ai?",
sai lokacin Haisam ya kalleshi don tunda ya fara Maganar idonshi na akan wayarshi amman yana jin duk abunda yake fadi,
"Zatayi karatu ne" ya bashi amsa a takaice,
"Daidai kenan, kaga sai kawae in wuce da ita Canada tana karatunta nima ina aiki na" dan ta6e baki Haisam yay sai kuma yace " ita wife en naka fa?"
"Ita ai dama kaga ta gama karatunta kuma ta matsa tana son yin aiki yanzu zata zauna nan ne ba kowane lokaci zamu kasance tare ba kaga ita Mom d'in naka inna tafi da ita shikenan bani ba maraici sai taita karatunta acan......"

"Ta kuma yi karatunka ba" Abbas dake ta dariya ya katseshi, shima Najeeb d'in wata yar iskar dariya yasa yace "yauwa My Man dad'ina da kai ganewa, ai dama dole ne wannan" yana kai Maganar ya mik'a ma Abbas hannu suka tafa,
Sigh Saleem yay ganin da gaske Najeeb d'in yake yace "But kai can't u see she's young?"
"Ba wata young tsaf zata dauki d'awainiya na, kai bakasan abun ba'a nan yake ba" d'an ta6e baki Saleem yay bai ce mashi komae ba,

"Pls zaki am Serious wllh ni zan reneta indai zaka sa abani",
sauke 6oyayyan ajiyar zuciya Haisam yay, sarai yasan halin Najeeb mugun son mata gareshi kaman Abbas gwara ma Abbas shi abunshi a bakine shi kam Najeeb d'an sharholiya ne banda neman mata har shaye shaye yana yi, sunsha zama su bashi shawara kan irin wannan mummunan halin sai yace masu ya bari amman kuma ba barin yake ba, koda ace Fatuu ta isa aure bai ta6a yarda Najeeb ya aureta balle kuma a yadda take d'innan, ganin ya kafeshi da ido alamar dae shi yake jira yasashi d'an tamke Fuska yace "She's young so she can't get married now, Period!" daga haka ya maida idonshi kan wayarshi yaci gaba da daddanata, d'an ta6e baki Najeeb yay bai k'ara cewa komae ba don ya lura kaman bai son ma Maganar,

Fatuu na zuwa part d'in Hajiya ta iske sunata shirin tafiya Abuja don karfe 4:30 jirginsu zai tashi, Saude ma ta shirya tsaf da sun tafi zata wuce Daura dama yar can ce acan tayi aure har ta haifi yaranta biyu kafin auren nata ya mutu sanadiyar kishiya shiyasa take bama aikinta muhimmanci don ko tunanin ma k'ara aure bata yi don bataji da dadi ba agidan mijin nata, Hajiya ta had'a mata sha tara ta arziki kaman yadda ta saba yi mata, tayi ma yaranta dinkuna harma da Mahaifiyarta tun jiya take fama da ita akan ta tafi tayi salla acikin yan uwanta yaranta su ganta suji dadi amman tace sai taga tafiyar Hajiyar, tana shiga suka hau yabon kwalliyarta Saude na fad'in su Fateema an zama yan Mata har barka da salla Hajiya ta bata amman duk da haka saida tayi mata fad'a sosae kan d'inkin data sa akayi mata tace mata sanya matsattsun kaya sam baida kyau karta k'ara sawa ai mata d'inki irin wannan ta amsa mata da to,

Bayan angama Sallar la'asar atare Haisam dasu Najeeb suka shigo cikin harabar gidan daga Masallaci, Parking space suka nufa don zasu raka Haisam Airport ne dalilin dayasa ma suka tsaya basu tafi ba tun dazun, wucewa Haisam yay part dinshi don daukko abu su kuma suka jingina da Motar Saleem wadda take Jeep Toyota Prado Land Cruiser dama acikinta suka zo su duka, suna tsayen yayinda Saleem ke daddana wayarshi Fatuu ta fito daga part d'in Hajiya janye da trolley, tunda ta fito Najeeb ya kai idonshi kanta yanata kallonta yayinda ta tunkaro parking space d'in har saida ta sadda kanta k'asa don taga kallon da yake matan, a gefen Jeep d'in Hajiya ta tsaya sai Saude itama ta fito da kaya inda Fatun take tazo ta aje ta koma ta d'aukko wasu don harda kayanta saboda daga Airport itama zata wuce tasha ta tafi daura, tana cikin tsayuwar a parking space d'in ta hango Haisam ya fito daga part d'inshi hannunshi guda janye da madaidaicin trolley don ba wasu kaya masu yawa ya d'aukka ba saboda acan ma yana da wasu kayan, a d'ayan hannunshi kuma jakar laptop ce ya ruko, Fatuu na hangoshi ta nufeshi cikin sauri, jin rigar tata bata barinta yin saurinne yasa tasa hannu d'aya ta d'an d'age ta sama, Najeeb dake ta kallonta ganin ta nufi Haisam yasa ya kalli Abbas da shima ita yake kallo yace "My Man tell me d truth, kodae h,zakee yana son girl dincan ne?" juyowa Abbas yay da d'an murmushi ya kalli Najeeb yace "No ba haka bane kaima ai kasan komai game dashi",

"Yess, but is possible ai k'ilan shiyasa yak'i bani goyon baya" dariya sosae Abbas yake ganin yadda Najeeb d'in ya zauce kan k'ank'anuwar yarinya,

"No ka fahimta dude wllh ba wani abu tsakininshi da yarinyan kawae dai he's like a guadian to her...." nan Abbas yaba Najeeb labarin yadda Haisam d'in yasan fatuu, d'an ta6e baki Najeeb yay kafin yace "if dat's it why bazai goyi bayana ba tunda kaman ma taimakon girl d'in zanyi kenan ai",
"Serious Najeeb yarinyan can k'aramar yarinya ce sosae gaskia bai kamata ai mata aure ba"
"Ba tagama sec skul ba?" girgiza kai Abbas yay "Ko Junior secondary bata gama ba" d
d'an bud'a ido Najeeb yay alamar mamaki kafin ya waiga ya kalli Fatun ya furta "amman dae akwae wani abu"
"What?" Abbas ya tambaya idonshi akanshi, juyowa yay ya kalleshi ya d'an yatsina fuska had'i da d'age gira yace "Shape, wato yarinyan nada k'ira ba k'araman Babe za'ai a wurincan ba wllh" dariya sosae Abbas ke yi hada dafe ciki kafin ya tsagaita yana kallon Najeeb d'in "wato kai indae mace tayi maka baka da sauran zaman lafiya ko?"
d'age mashi gira yay "kaga laifina ne ai don mu akayi su ko, cikakken jin dadin duniyar nan ai bai samuwa saida su Mutumi na"

"Hakane, amman nan dae saidai kayi hakuri toh aje aci gaba da samun jin dadin wurin ta gidan"
cike da iskanci Najeeb yace "ita kadae ai bata isana" waro ido Abbas yay "Don't tell me har yanzu Najeeb ba ka daina womanizing ba?" wani d'an iskan kallo yay mashi kafin yace "Yea nabari since wannan d'in baka ji nace aurenta zanyi bane" daga haka ya kawar da kanshi shi kam Abbas girgiza kai kawae yay don yasan ba lalle in gaskiya ya fad'a ba, ba kamar yanzu da ba zaune yake anan kasar ba,

Tana zuwa gaban Haisam ta tsaya tana mashi Murmushi hakan yasashi dakatawa yana kallonta fuska a sake, hannu ta kai ta kama trolley d'in tace "Kawo na ja Ya handsome" sakar mata yay batare daya ce komae ba suka nufi parking space d'in,
"Ya Handsome yaushe zaka dawo?" ta tambaya had'i da d'an kallonshi,
"I won't stay long" ya bata amsa ba tare daya kalleta ba, "Tk zai kai ki duk inda kike so" taji ya k'ara fad'a, kai ta d'aga mashi alamar to sai kuma tace "in ina son yin waya da kai fa?"
"Ba Auncle d'inki nada phone no dina ba, ki amfani da wayanshi" turo baki tay "to ai shi wani lokacin sai yayi man wulakanci yake bani wayarshi" "Grandma dinki fa batada waya ne?"
"Tana da ita amman yar k'arama ce ni kuma so nike muyi Vedio call don in nuna maka sauran gayun salla na" sai lokacin ya juyo ya kalleta suka had'a ido wai kuma sai tasa tafin hannunta wanda bada shi ta ruk'e trolley d'in ba ta rufe idanunta alamar kunya, d'an Murmushi yay kafin ya juya yana fad'in "in kinyi gayun ask Tk to call me" bud'e idon tay tace to lokacin kuma suka k'araso parking space d'in, amsar trolley d'in Abbas yay ya bud'e boot d'in Motar ya saka alokacin Hajiya da Saude suma suka k'araso wurin, k'ara gaidata sukai duk da dama da suka zo sunje har part d'inta sunyi mata barka da sallah,
"Wai ina Tukur ne" Hajiya ta fad'a idonta akan Saude kafin ta bata amsa sai gashi ya taho daga baya yana k'arasowa ta bashi umarnin saka kayayyakin cikin Jeep dinta,

"Yar Bafullatana zaki raka Yayanki ko?" fatuu dake tsaye taji an fad'a a gefenta hakan yasa da sauri ta waiga ta kalli wurin Najeeb ne zaune a back seat na Jeep d'in Saleem kafarshi guda awaje, Murmushi ta d'anyi mashi kafin tace wani abu Abbas dake a kusa dashi yace "ai dole ta raka Ya handsome d'inta ko?" jinjina mashi kai tay alamar eh,

"Fateema taho to ki shiga mutafi kar mu makara jirgi bai jira, in kuka raka mu sai ku sauke Saude a tasha" Hajiya ce tai Maganar tana mik'o ma Fatuu hannu, shiga gaban Motar tayi Hajiya da Saude na a baya sai Tk da zai tuk'a daga haka ya fito da ita cikin harabar lokacin suma su haisam Jeep dinsu ta fito shida Saleem ne agaba sai Najeeb da Abbas a baya, Motarsu ta fara nufar gate da aka zuge masu suka fice sai ta Hajiya ta rufa masu baya bayan ta tsaya sun k'ara yin bankwana dasu Officer ita da Saude dama ita Gwaggo tun kafin su fito ta kirata tayi mata sallama har tana cewa bari tazo tayi masu rakiya tace tayi zamanta taji da bak'in Salla.

A sauka lafiya Hajiyar Sanata 🛫.

Duk ranta ba dad'i suka baro Airport d'in, su Abbas sun wuce su kuma suka nufi tasha don sauke Saude, suna zuwa ba 6ata lokaci ta samu mota sukai mata sallama daga nan Tk ya bazama dasu cikin gari, yawo sosae yay da ita don har gidan abokansa ma Makaranta ya kakkaita harda gidansu budurwarshi, sosae Fatuu ta samu barka da sallah don har jakarta ta cika da kud'i ga kayan kwalama da aka babbata iri iri ba kamar agidansu budurwar Tk d'in, basu suka dawo gida ba sai da akai Magrib lokacin tuni su Haisam sun sauka Abuja don har tayi waya dashi, lokacin data dawo gida ta nuna ma gwaggo kud'ad'en data samu sosae ta girgiza da ganin uban kudin ta hau tambayar a ina ta samu kudi haka nan ta kwashe duk inda ta samun ta fada mata harda wanda abokan Haisam suka bata karshe dae gwaggon taba kudin bayan ta ciri yan kad'an wanda zata ruke gwaggo kuma tai mata fadan banda rokon Mutane kudi ta rantse mata kan bata rokon kowa kuma in aka bata ma sai tace abarshi in aka matsa ne take amsa, tsakar gida ta baje tanata cin abubuwan data samo tanata zuba surutu gwaggo nace mata ta bi ahankali da ciye ciyen nan, karshe saida gwaggon tace in cikinta ya lalace ai taga yadda za'ai tayi yawon sallan sannan ta lafa da ciye ciyen don ta gaya mata Ya Handsome yasa Tk ya kaita duk inda take so.

Washe gari tun 9 ta shirya cikin riga da skirt na lace dinta, tayi kyau har ta gaji kuma suma sun kamata sosae hakan yasa koda ta gama shiryawa bata shiga dakin gwaggo ba tai ficewarta dama kuma bacci take, gidan Hajiya ta nufa bayan sun gaisa da Officer dake zaune shi kadai yana ta yabon gayun data yi, ce mashi tay wurin tk tazo zasuje kallon hawan bariki yace ta shiga ta duba in ya tashi, tana shiga ta nufi Bq can bayan part d'in Hajiya don acan yake da zama, koda taje kopar dakin nashi a rufe take hakan yasa ta hau kwankwasawa shiru ba'a bud'eba har saida ta k'ara sautin bugun sannan taji muryarshi yana tambayar waye, ce mashi tay itace sannan yazo ya bud'e da ka kalleshi kasan daga bacci yake, yana ganin Fatun ya d'an buda idanunshi cikin muryar bacci yace " ya mukai dake jiya, ba sae goma nace zamu fita ba?" gaidashi tay tana tura baki tace " to ai goman ya kusa ko tunda yanzu tara fa ta wuce ba sai ka tashi ka shirya ba" d'an jujjuya kanshi yay alamar baccin bai isheshi ba,
"Kije to in nagama shiryawa zanzo"
"To ka kira man Ya handsome" amsa mata da ok yayi kafin ya juya cikin d'akin, hannunshi ruk'e da wayarshi ya dawo bakin kopar ya fara kokarin kira mata Haisam din, "Vedio call zaka kira shi" ta fad'a cike da zumud'i,
"No bari dae in kirashi in ya d'auka sai kice ya kira ki Vedio d'in don bamma tunanin ya tashi bacci yanzu" sau biyu ya kira ba'a d'aga ba hakan yasa yace mata gaskiya bai tashi bacci ba amman tace wai a k'ara kira har ya tashi jin hakan yasashi bata wayar yace taje ta kira da kanta in ya fito zai amsa cike da murna tace to, gida ta koma ta shige d'aki tana ta kira dama tun kan hanya take kira bai d'aga ba sai can yai picking call d'in lokacin tana zaune gefen gadonta, da sauri ta kara wayar a kunne ko sallam bata yi ba ta kira sunanshi,

"Ya handsome " shiru bai amsa ba har saida ta k'ara kira sannan cikin murya mai tattare da bacci ya fara Magana "Zarah hope u'r ok" maimakon ta bashi amsa sai cewa tay "tun d'azun nike kiranka amman kaki ka daga",
"Wayan yana vibrate ne, any problem?"
"A'a dama kwalliyata ta yau zan nuna maka ka maida Vedio call kaga uban gayun dana yi",
ba tare daya k'ara cewa komae ba ya shiga maida kiran Vedio, yana kwance akan wani katafaren gado ya lullube rabin jikinshi da wani lallausan katon bargo blue don yanayin weather d'in can akwae d'an sanyi saboda samun ruwa da suke ba kamar Katsina ba gashi ya saba da Ac indae ba sanyi yayi tsanani sosae ba to bai zama ba tare da ya kunnata ba, Fatuu na ganinshi ta waro ido had'i da washe baki tana mashi dariya shima Murmushi yake mata yana daga kwance kanshi saman farin pillow haka rigar jikinshi kimono robe ce fara sol,
"Ya Handsome wannan gadon kane?" kai kawae ya d'aga mata alamar eh,
"To ina Hajiya da sauran yan gidanku,?" lumshe ido yay kaman bazai bata amsa ba da gani still da sauran bacci a idonshi a hankali kuma ya ware idon slowly yace "suna apartment nasu"
"Kenan anan ma bangarenka dabanne?" kai ya d'aga mata alamar eh,
"da an shigo bangaren naka yake kaman gidan Hajiya?" kai ya girgiza mata kafin cikin muryar bacci ya furta "Upstairs", zaro ido tay da mamaki tace "kai, gidanku na nan Abuja kenan benene tunda kace a Saman bene kake" kai ya sake d'aga mata ya fara kokarin tashi zaune don wani irin bacci ne ke fuzgar shi gashi sam baijin dad'in Vedio call d'in a waya don yafi sabawa da yayi a laptop, jingina bayanshi yay da kan gadon ya ruk'e wayar kan cinyoyinshi dake lullu6e da bargo, yana tashi zaunen da mamaki Fatuu ta kira sunanshi "Ya Handsome" bud'a mata ido yay ba tare daya amsa ba,
"Ashe yadda kake da gashi a hannunka har anan ma kake dashi" cike da al'ajabi tay Maganar tana nuna kirjinta alamar inda take magana akai, a hankali ya d'an duk'ar da kanshi ya kalli kirjin nashi dake abude sakamakon rigar dake jikinshi haka take bata rufe kirji in ba'a sa wata a ciki ba ga gashin nan liya liya a kwance saidae baida yawa sosae don yana rageshi, d'agowa yay ya kalleta ganin ta kafe wurin da ido tanata kallo yasashi kai hannu ya idasa jawo bargon sama, kallon fuskarshi tay suka had'a ido don kar ta sake yin Magana kan gashin yasashi cewa "kince zanga kwalliyanki" da sauri tace eh tare da saukkowa daga kan gado ta mik'e tsaye tun daga kan k'afafunta ta fara nuna mashi har saman fuskarta tana ta dariya,
"Nayi kyau sosae ko?" ta tambaya, fuska a sake ya furta "Yeah" shiru sukae na wani lokaci tana ta kallon fusakarshi tana dariya don dad'in Vedio Call din take ji shi kuma sai faman lumshe ido yake can yace "bazaki je yawo sallan ba?" da sauri tace "zanje, yanzu ai naje wurin Tk d'in don mu tafi kallon salla na iskeshe bai shirya ba amman yace yanzu zai shirya sai mu tafi" kai ya jinjina mata,
"Kai bazaka kallon Sallan ba",
" ba'a yi anan"
"Hawan barikin?" d'aga mata kai yay,
"Ai da yake ance Abujan duk yan gayu ne k'ilan baku zuwa kallo shiyasa ba'ayi, yanzu saidae kaita zama a gida kenan?" d'an Murmushi yay "No zan fita ba yanzu ba" gyad'a kai tay sukae shiru ita dae tana ta Murmushi shima fuskarshi a sake take yana cigaba da lumshe ido alamar dai har yanzu baccin yake ji can ya d'an langa6ar da kanshi da alama baccin yake, tsuru Fatuu tay tanata kallon fuskarshi,

"Wllh Allah Ya Handsome kanada bala'en kyau" yaji Maganar ta doki dodon kunnanshi, a hankali ya bud'e idanun akanta yana kallonta tana ganin ya bud'e idon taci gaba da cewa "bakaga da ka rufe ido ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login