Showing 120001 words to 123000 words out of 212491 words
da sauri Amadu yace"Wllh ta rigada ta tafi,dazun ina brush anan waje ta fito ta tafi yanzun ma ina ganin ta isa makarantar",
lumshe ido yayi ya dan jinjina kai,a tunanin Amadu wucewa zaiyi hakan yasa ya dan ja da baya amman sai yaji yace mashi ya shiga Motar,
"Yaya Haisam da kaje kar na 6ata maka lokaci zan hau aca6a" cike da girmamawa yayi Maganar harda dan rankwafowa,
"No problem ka shiga" cikin cool voice dinsa ya fada amsawa yayi da toh ya nufi d'ayan 6arin Motar,gaba ya bude ya shiga ya zauna wani ni'imtaccen sanyi hadi da sanyayyan kamshi suka kai ma hancinshi ziyara har saida ya dan lumshe ido bayan ya rufe kopar haisam yaja suka tafi,tsit kake ji idon haisam na akan hanya shi kam kawu Amadu yayi shiru yana kallon gefen hanya wani irin nishadi yake ji har dan murmushi yake saki,bayan sun hau hanya ne haisam ya tambayeshi wane school yake ya fadi mashi nan take ya gane Makarantar don acan wurin Airport take wato kambarawa,bayan d'an lokaci suka iso Amadu yace ya ajeshi a bakin gate sai ya shiga hannu kawai haisam ya daga mashi alamar ba wani abu ya shige dashi ciki,har gaban Admin block ya kaishi yana kokarin fita ya mika masa kudi 2k yace yayi break, da tsananin mamaki Amadu ya kalli kudin kafin ya kalli haisam,yana so yace mashi ya barsu sai dai sam ya kasa don wani irin kwarjini gareshi gashi ko kallon Amadun ma bai yi ba,hannu ya kai ya amsa hadi da yi mashi godiya daga haka ya bude motar ya fita daidai wasu Abokansa sun taho suna ganinshi suka ja suka tsaya suna kallonshi da mamaki ganin had'addar Motar daya fito wanda a iya saninsu ba'a ta6a kawo shi makarantar a Motar gida ba,tsaye yayi saida haisam din yayi reverse ya juya ya nufi gate kafin ya tunkari abokan nashi yana wani bouncing suna ganin hakan suka sa sowa suna kuranta shi,saida suka gama shegantakar tasu irin ta dalibai sannan suka nufi class.
*** **** ****
Lokacin da su Fatuu suka isa class dinsu Mutum biyu suka iske aciki wurin zamansu suka nufa don su zauna dayake a layin tsakiya suke kuma seat dinsu ne na farko,suna zama Fatuu ta fiddo Assignment dinta tana kara bitar shi haulat dae nata saurararta don ba gane inda ta dosa take ba,a hankali dalibai suka cigaba da zuwa nan da nan ajin ya cika period din farko ta shiga shiru Malamin lissafin bai shigo ba Fatuu duk ta kagara bunu bunu ta kalli kopar shigowa ajin,
"Fatuu gashi nan" Haulat ta fada tana gyara zamanta da sauri fatuu ta kalli kopar daidai malamin ya shigo cikin ajin,wani murmushi ta saki tana kallon haulat,sanye yake da blue jeans da riga mai dogon hannu ya dad'e da bak'in glass,yana shigowa yan ajin suka mike suna gaidashi,seat din farko na layin karshe ya nufa ya d'aura textbook da Allin dake ruke a hannunshi sannan ya kalli Students din fuskarsa ba yabo ba fallasa ya amsa masu gaisuwar kafin yace su zauna,bayan sun zaunan ya juya ya nufi blackboard ya rubuta subject din da yake yi da date yaja layi kafin ya rubuta sabon topic din da suka shiga jiya ya juyo ya dauki textbook din math ya rubuta wasu misalan bayan ya gama ya juyo ya fara masu bayani,itakam Fatuu ganin bai tanka mata ba yasa ta fara tunanin ko ma ya manta da Assignment dinne,saida ya gama yi masu bayanin misalai guda ukku yace in akwae wanda bai ganeba ko mai tambaya yayi,wasu suka fadi abunda basu ganen ba wasu sukayi tambayar saida ya gama dasu kafin ya kalli Fatuu fuska a matukar d'aure yace"where is my Assignment?",
shiru tayi tana binshi da ido hakan yasashi ce mata ta fito gaban Allo,mikewa tayi littafinta a hannu ta fita,
" Who is the class monitor?"ya tambayi yan ajin,
"Malam itace monitar" wasu suka fad'a, jinjina kai yayi ya tambayi ina mataimakiyarta aka nuna mashi Haulat,umarni ya bata taje Staff room ta daukko mashi kujera ta amsa da to kafin ta mike ta nufi hanyar fita,bada jimawa ba ta dawo hannunta ruke da kujerar ta kai mashi inda yake jingine da window ta aje agefenshi kafin ta koma ta zauna,gyara kujerar yayi ya zauna daga haka ya nuna ma Fatuu Allo da hannunshi,
"Ki rubuta Question din dana baki da kuma amsar danace ita zaki samo"amsawa tayi da to,yadda ta amsan a dan sanyaye sai kace batayi Assignment din ba,bayan ta rubuta ta juyo ta kalleshi tun kafin tace wani abu ya tambayi yan ajin sun gama kwafar rubutun tsakiyan allon suka amsa da eh,nuna mata wurin yayi yace ta goge rubutun tayi ma yan ajin bayanin aikin da ya bata har ta gano amsar,shiru tayi tana kallonshi ya dan daka mata tsawa" baki ji mi nace bane!" dan tura baki tayi tace"naji" juyawa tayi ta kalli yan ajin da kowa idonshi na akanta sunyi mata tsuru ba wanda yake tunanin zata iya don sam yanayinta bai nuna ta iyan ba ta galla masu harara,hada ido sukai da haulat ta tura mata baki itakam haulat din dariya tayi ta girgiza kai kawai don halin Fatuu sai ita,shidae math teacher din sai girgiza kafa yake ya dan kya6e baki cikin ranshi kuwa ya tabbatar bazata iya ba hakan yasashi cin alwashin sai ya koya mata hankali,littafinta ruke ahannunta ta fara rubutu a allo bayan ta goge rubutun jikinshi,tambayar ta fara rubutawa kafin ta fara fiddawa tana juyowa tana ma yan ajin bayani,tun tana yi ahankali har ta daga murya ta zage sai uban bayani take kai kace malama ce ke yima dalibai bayani,shin ina malam yake ne?yana dai azaune yayi tsitt sai bin ta da ido yake cike da mamaki abun ya matukar daure mashi kai don bai ta6a tunanin zata iya ko kusa da yadda take yi ba,gashi abunda ma yafi bashi mamaki shine yadda take bayanin ba tare da tana kallo a wani wuri ba da kai take yi,lokacin data zo karshe ta gano irin amsar tashi sai ta juyo ta kalli yan ajin da suka yi sototo suna sauraranta wasu bakinsu a bud'e saboda mamaki,
"kun gane ko asake yi maku bayani?"ta tambayesu tana murmura idanu had'i da sa hannu guda ta dafa kugu,gaba daya suka ce sun gane,juyawa tayi ta kalli malam da har lokacin idonshi na sanye cikin gilashi tace" Gashi nan na fidda har na gano amsar irin taka,nayi daidai ko?"ta tambaya da d'an Murmushi tana d'age ido,farko shiru yayi yana ta kallonta har saida ta k'ara tambayar tayi daidai sannan ya daga mata kai alamar eh,
"To tunda nayi daidai kace a tafa man ko" ta fad'a tana tura baki,d'an jinjina kai yayi yai wani guntun Murmushi da alama ta kashe shi da mamaki sai kace ba mai laifi ba har wani neman atafa mata take, ganin haka yasa tace"yanzu duk wannan uban aikin da nayi malam baza'a tafa man ba" ta k'arasa tana ta tura baki,kallon yan ajin yayi yace su tafa mata aikam kaman da gayya suka fara uban tafi kilan kuma murna suke Allah ya raba su da alakakai,
"Malam shikenan inje in zauna ko tunda dai nayi daidai ae ba batun punishment ko?" ta fad'a tana gwalo ido,d'aga mata kai yayi alamar eh, har ta juya ya tsaidata don ya kasa hakuri so yake yaji yadda akai ta fidda Assignment din don shi kanshi yana a shekararshi ta k'arshe aka basu Assignment d'in wanda ba karamar wuya yasha ba wurin fidda shi,
" Waya koya maki?" yayi tambayar fuskarshi ba wasa,d'age gira tayi tace"Assignment d'in?"kai ya daga alamar eh,d'an murmushi tayi da bud'ar bakinta sai cewa tayi"wani Aljani ne acikin Aljanuna yazo ya koya man",tashin hankali!hannu ya kai ya cire gilashin idonshi yabi ta da wani irin kallo mai kama dana wanda ya razana duk da ya d'an dake,ganin irin kallon da yake mata ne yasa taci gaba da cewa"ba kaji yan ajin nan jiya sunce ina da Aljanu ba,to cikinsu ne ai wani yazo ya koya man har na iya",
ba iya malam d'in ba har yan ajin sun razana da jin abunda take cewa don duk d'aukar mai Aljanu kowa kema Fatun ita kanta Haulat in Fatuu tayi wani abun takan yi kokonton anya ba da gaske tana da Aljanu ba tunma farkon kawota garin amman yanzu tasan k'arya take ma malamin nasu tunda ta gaya mata wanda ya koya matan kawae iskancinta ne,
"Dama Aljanu suna zuwa wurin mutum in yana dasu ne" malam da yayi sototo yana kallonta yayi tambayar,
"Eh baka ga ko bokaye a film ba suna magana da Aljanu kuma suna ganinsu to ai a fili ma hakane,ni dama in dae raina ya 6aci to suna zuwa ko in wani ya ci zalina,to daka ban Assignment d'in naje gida nayi nayi na kasa shine raina ya 6aci har nayi kuka aikuwa sai ga wani cikinsu ya bayyana da suffar saurayi baka ganshi ba kyakkyawa ne sosae kamar balarabe gashinshi liya liya shine ya rarrashe ni ya koya man nan da nan na iya" ta k'arasa tana wani dashe baki ita ala dole dariya take shikam malam din was completely speechless bin ta kawae yake da ido daka kalle shi zaka fahimci hankalinshi ya tashi Haulat dai sai faman girgiza kai take don ta fahimci ya yarda da Maganar Fatun dama kuma shi bak'o ne bai dad'e da zuwa ba balle yasan halinta da cikin tsoffin malamansu ne ta fad'i ma wani hakan ba lalle su yarda ba tunda sun san halinta,
"Ko in ce mashi kana son ganinshi ne?" ta tambayi malamin ganin yanayin fuskarshi,
"Waye?" adan rud'e ya tambaya,
"Shi Aljanin da yayi man Assignment d'in" wani kallo yabita dashi irin kallon mahaukaciya ce ke kafin yace"ni bance maki ba"daga haka ya d'auki littafin shi da sauran allin daya rage ya nufi hanyar fita ko uffan baice ma kowa ba ya barta atsaye,tana ganin ya fita ta nufi seat d'insu tana kyalkyatar dariya ta fad'a jikin haulat,
"Wllh baki da hankali Fatuu shine kika tada mashi hankali ko",
Murguda baki tayi tace" to da ba mugunta yaso yayi man ba daga na fad'i gaskiya",
"Amman ai ta sigar rashin kunya ki kai mashi magana ko",
" ni wai komae nai sai ace rashin kunya kuma ni ai bansan ita nayi ba ko"tayi Maganar tana tura baki,girgiza kai haulat tayi kafin tace"yakamata dai ki bari wllh kinsan fa komae kayi kaima sai anyi maka ba kamar malamai su tamkar iyayenmu suke abunda kasan bazakai ma iyayenka ba bai kamata suma kai masu ba,don Allah Fatuu ki natsu duk abunda kikasan zaisa ayi maki surutu ki bari kinji yar kawata kuma kanwata"ta k'arasa hadi da dafa kafadarta,
"Ai nace ma Ya Handsome da Hajiya na bari in sha Allahu bazan kara ba",
"yauwa yar gidan Ya Handsome Aljani ko ke fa",zaro ido Fatuu tayi ta kalli Haulat d'in kafin tace wani abun Haulat ta rigata"ko bashi ne Aljanin da kika suffanta ma Malam yayi maki Assignment ba",tana jin hakan ta kyalkyace da dariya itama Haulat din dariyar take tace sai ta fad'i mashi Fatun ta fara mata magiyar tayi hakuri daga haka suka ci gaba da hira don dama period d'in malam mai lissafi bata kare ba Fatuu tasa shi ya fita ba shiri,
_____________
A ranar da yamma bayan ta fito zata tafi islamiyya ne Kawu Amadu dake cikin kiosk dinshi ya fadi mata yau Yaya Haisam yazo tafiya da ita Makaranta ya iske bata nan sai dai ya daukeshi yakaishi har Makarantarsu,jin hakan yasa washe gari da safe taje har gidan Hajiyar suka tafi tare bayan an biya an dauki Haulatu,bayan Haisam ya aje su a gaban Admin kaman yadda ya saba yana kokarin juya Motar ya tafi wani Malami ya tunkaroshi yana dan d'aga mashi hannu alamar tsaidashi,tsayawa Haisam din yayi bayan malamin ya k'araso ya zuge glass d'in motar kasa,gaidashi yayi haisam din ya mik'a masa hannu don su gaisan,bayan sun gama gaisawa ne yace mashi in ba damuwa yana son yin magana dashi haisam yace ba matsala,ganin yana kokarin fitowa ne malamin yace yayi zamanshi ba wata magana bace mai tsawo jin hakan yasa haisam cewa ya shigo daga cikin motan amman nan ma yace ba matsala zai tsaya daga waje wanda yayi hakanne gudun surutun mutane da basu raina abun magana yanzu ayi masa wata fassarar ta daban ba kaman in aka ga ya shiga motar,lokacin su Fatuu har sun kai wurin Hall dinsu don yana aje su bayan ya bata kudin break yau harda irin Popcorn din daya ta6a bata tai ta santi ya basu yace su wuce class,kamar ance Haulat ta waiga ta hango malamin tsaye gefen kopar driver ya d'aura hannunsa guda asaman motar,
"Fatuu ji Uncle Bash a wurin dan gidan hajiya" haulat ta fad'a bayan ta ja ta tsaya,da sauri Fatuu da har tayi gaba ta juyo a sukwane jin abunda Haulat ta fad'a,a d'an rude tace"kai,to mi yake ce mashi,ko ya sanshi ne?"hannu Haulat ta yarfa alamar bata sani ba sai kuma tace"Allah yasa dai ba wani abun yake fad'i mashi ba game dake,kinsan yanzu kowa kallon d'an uwanki yake mashi" jin hakan yasa fatuu zaro ido a rud'e tace"to ni mi nayi mashi kuma in ba sharri zai ja man ba,bari inje inji mi yake ce mashi" ta k'arasa Maganar tana niyyar nufar bakin gate d'in da sauri Haulat ta kamo hannunta,
"In kin je kice mashi mi,kika sani ko ya sanshi ne yanzu kuma kije ki fad'i wani abun aga kinyi rashin kunya ki kyalesu kilan wani abun suke tattaunawa ba lalle in abunda ya shafe ki bane" jin hakan yasa ta fasa zuwan Haulat tace mata su tafi kawae suka juya suka nufi aji saidai sam zuciyar fatuu ta kasa samun natsuwa sai faman waiwayensu take har suka kai
aji tana ta sak'e sak'e acikin aranta.
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔
*Mallakin*
⬇️
*🌹ZAINAB LALUH*📲✍
_~(Oummu imam)~_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
5️⃣2️⃣
........Sosae Haisam ya fahimce shi,bayan sun gama Maganar yayi mashi godiya shima Uncle Bash d'in yace ya gode da saurararshi da yayi ya kuma fahimce shi daga haka suka yi sallama da juna glass d'in Motar ya rufe yajata dama akunne take ya tunkari gate ya fuce
,
Har aka tashesu bata bar tunanin mi Uncle Bash yace ma Ya Handsome ba,bayan ta koma gida ma abun na ranta saidai bata yi tunanin zuwa ta tambayeshi ba saboda zullumin ko wani abun ya fad'i mashi game da ita gashi ma tasan ba lalle in ya dawo daga wurin aiki ba,wuraren karfe ukku da wasu mintuna suna zaune atsakar gida saman tabarma ita da gwaggo ita ta kwanta tayi shiru gwaggo kuma na sauraren radio,ganin Fatun tayi shiru ne yasa gwaggon tambayarta ko bata jin dad'i ne tace mata a'a lafiyarta lau kawae ta gaji ne,suna cikin zaman Amadu ya shigo gidan yana hango su azaune ya dakata a bakin kopar zauren yace"ke kije Yaya Haisam na kiranki"daga haka ya fara k'okarin juyawa zai fita gwaggo ta tsaidashi da fad'in"gidan kaje ne?"
"A'a yanzu ina shago yazo zai wuce cikin Mota shine ya tsaya yace in kira mashi ita",
"yana wajenne?" gwaggo ta tambaya,
"Ya wuce gida" ya bata amsa daga haka ya juya ya fuce,jin Fatun tayi shiru yasa gwaggo cewa"Fatuu ko har kinyi bacci ne?"daga yadda take ta girgiza mata kai alamar a'a,
"To kitashi kije baki ji ana kiranki bane", shiru tayi kirjinta na d'an bugawa tsoron zuwan take don yanzu ta tabbatar da kyar in ba wani abu Uncle Bash ya fad'i mashi game da ita ba,
" Fatuu baki ji bane wai"gwaggo ta fad'a da d'an d'aga murya hakan yasa ta yunkura ta tashi zaune,ganinta sukuku yasa gwaggon tambayarta"lafiya?ko wani abu ya faru shiyasa yake nemanki ne?"da sauri ta girgiza mata kai tace itama bata sani ba,
"To tashi kije,Allah yasa dai lafiya" mik'ewa Fatuu tayi ta shiga cikin d'akinta ta d'aukko d'an bak'in gyalenta ta yafa asaman kanta kafin ta fito zata tafi gwaggo ta bita da ido bata dai tanka mata ba ganin doguwar rigar atamfa ce ajikinta.Tana fitowa ta nufi kiosk din Amadu a sanyaye tace"Kawu ina Ya Handsome din?"wani kallo ya bita dashi mai kaman harara yace"A'a Ya Ugly,yar rainin wayo kawai Haisam dinne bazaki iya cewa ba"tura mashi baki tayi kawai bata ce komai ba,
"Saurayinki ne shi da zai tsaye yanata jiranki,ya wuce gida sai ki iske shi can",
Juyawa tayi ta nufi gidan Hajiya jikinta duk yayi sanyi sai faman zurfin tunanin ko tayi wani laifi a Makaranta kwanannan banda na Malam mai Maths take yi har ta iso part d'in nashi,tura kopar tayi ta shiga da yar sallama,abakin kopar ta tsaya ganin ba kowa a parlon,tunanin ko yana wurin Hajiya ne ta shiga yi har zata juya ta hango kopar Bedroom d'inshi a d'an bud'e bata idasa rufewa ba hakan yasa tayi tunanin ko yana ciki,d'an shiga tayi cikin falon ta tsaya gab da corridor ta k'ara yin sallama har sau biyu,
" Who's there?"ta ji muryarshi can ciki ya tambaya,
"Fatuu ce" ta bashi amsa,
"Ok,am coming",
jin hakan yasa ta koma can bakin kujerun tayi tsaye tana jiranshi,after some minutes taji ya bud'e kopar Bedroom d'in da sauri ta kai idonta gareshi,sanye yake da wando 3 quarter ruwan madara sai farar riga armless irin mara hannuwa ta mashi cif cif kirar karfinsa ta bayyana ba kamar damtsen hannuwan dake a murd'e ga suma duk ta kwanta luf a hannun nan da nan kamshin turaren jikinshi ya k'ara karad'e falon banda wanda dama falon ke saki,bai kalli inda take ba ya nufi kujera 6arin daya saba zama ya zauna ya d'an jingina,sai lokacin ya kalleta suka had'a ido da sauri ta gaidashi, maimakon ya amsa sai ya zuba mata ido kawae yana nazarin yanayinta don yaga kaman ba yadda ya saba ganinta ba,ita kuma ganin kallon