Showing 18001 words to 21000 words out of 212491 words

Chapter 7 - Asanadin Makwabtaka Book 1 Hausa Novel Complete

27 Dec 2024

954

"In kika tsaya yin fad'a yanzun nan kinsan za'aje a fad'i ma gwaggo gara ki rabu da ita kawai" A hankali Fatun ta juya suka fara tafiya amman ba haka taso b..,can ta tuna ai gwaggon ma ta tafi aiki tunda ta tabbatar mata bazata dawo ta iske ta ba,da sauri Fatuu ta mika ma haulat jakarta tace"Ki tafi man da ita gidan ku,da safe sai kitaho man da ita Islamiyya",
"Ina zaki kuma?" haulat ta tambaya fatun tace"Na manta ne gwaggo ta aike ni..." Haulat tace "to mutafi tare man....da sauri Fatu tace"A'a kije kawai ni kad'ai zanje" Haulat ta girgiza kai tace "ba wani aiken ki da akai fad'an dai zaki tsaya ko...?da tsiwa Fatuu tace "Eh d'in fadan zan tsaya ina ruwanki" haulat tace"Don Allah fatuu kiyi hakuri mana"
"Inyi hakuri? Kinajin yadda take gaya man maganganun banza zaki wani ce inyi hakuri, to wallahi bazan yi ba" Haulat tace "haba fatuu,Allah fa yana tare da masu hakuri..."
"To ni banda hakurinn ehe" Fatuu tace,hannu haulat tasa ta rufe baki, jin abunda Fatun tace.
Ganin haka yasa fatuu ci gaba da magana"Ai ba haramun bane in anyi ma mutum abu yaji bai iya yafewa ya rama,ke komai akai sai kice ma mutum yayi wai hakuri shikenan so kike a raina ni,inzama sakarya kamar ki ko" cikin sanyin murya Haulat tace"Ni babu wanda ya raina ni,kinga wani na tsokanata ne? Kuma yin hakuri ba sakarci bane,wani lokacin rashin hakuri ba abunda yake ja ma mutum sai dana sani mara Amfani,gara ma kayi hakurin tunda Allah da kansa yace yana tare da masu hakuri,in kayi hakurin sai kiga ya saka maka ta inda bakai zato ba"daga haka ta mik'a ma Fatu hannu,ta bata jakar,ita kuma ta juya don tasan ba lalle ta iya hanata yin fad'an ba,
cikin d'aga murya Fatuu tace "In ma k'ara ta zaki ki kai to gwaggon bata nan tana wajen Aiki" girgiza kai kawai Haulat tayi batare da tace mata komai ba bare ma ta juyo.

Wani gida dake kallon jikin gidan da Murja ta shiga nan Fatuu ta shiga ta 6oye a bayan k'aure tana lek'o waje ta tsagar jikin kofar jira kawai take taga fitowarta,Aikuwa bata fi minti biyar ba sai ga murja ta fito tana yarfe hannunta da alama ruwa ne a hannun,da sauri fatuu ta cire hijabinta ta d'aure ta tamau a k'ugu ta k'ara gyara d'aurin kallabinta,sai da ta bari murjar ta wuce kofar gidan data 6uyan ta fito cikin sand'a tamkar mage na shirin kama k'adangare da gudu ta shak'o murja ta baya cikin sa'a ta kada ita k'asa ta fara bugu dama Fatuu badai karfi ba gashi takai mata hari ta baya sai faman bugunta take,tana fad'in "kafin kiyi magani na ni zanyi naki" cikin wahala murja tace "Don Allah kiyi hak.....bugu Fatuu takai mata a baki nan take bakin ya fashe tace "hak'urin uwarki zanyi,badai ni kike ce ma yar kauye ba, aikam zaki ga yar k'auye,
Lokaci guda yara suka kewaye su suna kallon fada,yawanci duk d'alibai ne masu dawowa daga makaranta had'i da Almajirai ba wanda yayi yunk'urin raba su don yaran sun san halin Fatuu.

Wata mota ce 406 maroon ta shigo cikin lungun,ba kowa bane cikinta face Haisam,a hankali motar ke shigowa har yazo gab da yaran,dole ya tsayar da motar ba tare da ya kashe ta ba,don ba hanyar da zai wuce yara duk sun rufe hanyar,shiru yayi yana tunanin lafia,don bai hangen su fatuu dake fad'an,Horn ya latsa amman sam hankalin yaran na akan fad'an basu ma ji ba bare su bashi hanya,Wani magidanci ne ke k'okarin fito da wani tsohon mashin daga zauren wani gida acan gaban inda ake fad'an,adaidai lokacin da ya fito waje yace"Bismillahi,mun fito da sunan ka ya Allah,ka matso mana da rabon mu na alkhairi kusa Albarkacin wannan rana,bud'e tankin mashin d'in yayi ya d'an girgiza yace "tabb ashe ma ba man,Allah gamu gareka yan canjin da suka rage man su kenan na bada cikin gidan a samu a harhad'a,yanzu kuma anfito za'a neman gashi ba isashshen mai ma a mashin d'in ,kai rayuwar nan tayi tsanani Allah ka dafa mana",daga haka ya maida murfin tankin yana rufewa,
A daidai nan kuma Haisam ya k'ara yin Horn mai karar gaske nan da nan yaran suka shiga darewa ya rage sauran su fatuu dake ta faman tumurmusa a k'asa,da sauri mutumin nan ya juyo jin Horn d'in,sai a lokacin ya lura da meke faruwa a hanyar da sauri ya jingine mashin d'in ya nufi wurin masu fad'an da dan gudu gudu don ya samawa mai motan hanya,k'okarin rabasu ya shiga yi saidai sam fatuu tak'i ta rabu da yarinyar,duk abunda ke faruwa kan idon Haisam,yana kallon yadda mutumin keta kokarin 6am6are fatuu daga jikin d'ayar yarinyar amman ya kasa,saboda ta kafe,tak'i ta saki yarinyar,nan take ran Haisam ya 6aci,bud'e motar yayi,da karfi ya maida kofar ya rufe har lokacin motar na akunne,ya tunkari inda suke fad'an,yau ba suit ne a jikinsa ba,riga ce longsleeve shirt maroon color sai wando jeans bak'i ma6allan rigar ma bak'ake ne,takalmansa kuwa daga saman su maroon din fata ce,shimfid'ar takalmin zuwa kasan shi kuma baki ne,sumar sa tasha gyara sai salk'i take ba k'aramin kyau yayi ba, yauma dai da alama Too match din yayi da motarsa wadda take maroon.
Yana isa wurin yasa hannu guda ya fizgo Fatuu ya turata gefe guda sai gata a k'asa wanwar,sauran yara suka sa dariya ganin yadda ta wani wuntsila,juyawa yayi ya kalleta,da dogon dan yatsansa ya nunata yace"You Again..!" da ganin yadda yayi maganar ya ganeta ne,da sauri Fatun ta mik'e tana mashi wani irin kallo ta turo baki cike da tsiwa tace "To ina ruwank....bata k'arasa ba ya wanka mata mari ji kake tasss,da tsananin firgici Fatuu ta dafe inda ya mare tan sai faman zare ido take........,

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*


*BY OUMMU IMAM📲*

*Paid Book*

*Free Page1️⃣1️⃣*

Su kam yara mi zasuyi in ba daria ba suna fad'in yau anyi maganin masifaffa,hakan ba karamin fusata fatuu yayi ba,Tsawa Haisam ya daka masu yace"kowa ya bar nan!" nan da nan kuwa suka kama gabansu banda Fatuu wadda har lokacin tana dafe da kuncinta sai faman hura hanci take tana mashi wani irin kallo mai kama da harara,
cikin yar tsawa yace mata"C'mon leave this place kafin in k'ara maki wani" ya nuna mata hanya da yatsansa,daga jin yadda yake magana zaka fahimci ba mai hayaniya bane,A hankali ta fara tafiya tana yi tana waiwayensa har Lokacin kuma bata cire hannunta daga kan kumatun da aka maran ba,da alama taji zafin marin.

Juyowa Haisam yayi cike da takaici bayan Fatuu tasha kwana,kallon murja yayi wadda jini ke ta zuba daga hancinta da bakinta tasa hannu ta dafe hancin,jinin har ya 6ata mata brown hijab din ta,ya ma kasa cewa komae sai mutumin nan ne keta faman girgiza kai yace "kai jama'a yanzu ina Amfanin haka,kuna ya'ya mata kunzo tsakiyan hanya kuna fad'a ji yadda aka raunata ki,ina amfanin haka,cikin sheshshekar kuka murja tace "Wallahi ba abunda nayi mata,ni bama bangare d'aya muke ba a makaranta kawai don tace in....bata k'arasa bayanin ba Haisam ya katseta ta hanyar yima mutumin magana don a tunaninsa komai yarinyar zata fad'a game da Fatun gaskia ne,

"Don Allah ko za'a samu chemist nan kusa?" ya tambaya fuskarsa sam ba walwala,da sauri mutumin yace"Eh akwae,sai dai yana ad'an can gaba in an fita bakin titi" duba agogon hannunsa yayi kafin ya kalli yarinyar "Muje" yace mata fuska ad'aure,
juyawa tayi zata nufi inda motarshi take,da sauri mutumin yace "Yalla6ai in sauri kake ka kawo sai in kaita" d'an dakatawa Haisam yayi yana duban girman mutumin,d'an murmushi mutumin yayi don ya fahimci kallon da yake masa yace "kar kaji komai yalla6ai zan kaita,tunda ga mashin d'ina can ajiye,dama hanyar zan bi,kaga ba sai kasha wahalan komawa ba",
Sigh yayi"Ok,nawa ne kake ganin zai isa a duba ta? ya tambaya,
Mutumin yace "ai ina ganin dressing ne zasu yi mata,k'ilan su had'a mata da maganin kashe rad'ad'i duka dai nasan bai wuce naira d'ari biyar haka,da Alama mutumin yana da kyan hali duk da halin rashin da yake ciki bai fad'i fin abunda yake tunanin za'a kashe ba,hannu Haisam yasa cikin aljihun jeans dinsa ya ciro wallet maroon mai kyau,kudi ya k'irgo dubu biyu yau ma sabbi fil dasu,ya mika ma mutumin gently yace"Ayi abunda ya dace" da sauri mutumin yasa hannu ya kar6a yana fad'in"to,to.." yana shirin juyawa Haisam ya sake mik'a masa wasu dubu biyun,da d'an zare ido mutumin yake kallon kud'in yace"Yalla6ai su kuma mi za'ai dasu? Cikin girmamawa yake maganar duk da kuwa ya girme masa nesa ba kusa ba,amman girman ya koma kan Haisam tunda shi mai kud'i ne,Allah kai mana Arziki mai Amfani,Amin,
"kasa fuel" haisam yace daga haka kuma ya juya,godiya mutumin ya shiga yi yana fad'in"Allah yasa kagama da duniya lafia,Allah ya jikan magabata,Allah yasa kafi haka,ya Albarkaci iyali...." ko a ina iyalin suke.

Hannu kawae haisam ya d'aga masa bayan ya nufi inda motarsa take,acikin zuciyarsa kuwa yanata amsa Addu'oin da mutumin yake masa,
bud'e motar yayi ya shiga dama a kunne take a hankali ya fara tafiya mutumin nata d'aga masa hannu,horn yayi mashi lokacin da zai wuce shi,

juyawa mutumin yayi ya nufi wurin mashin d'in don ya saukko dashi bisa hanya don yana da tabbacin zai kaisu bakin hanyar,sai faman washe baki yake yana godema Allah yanzu yanzu ya gama rok'on Allah da ya matso masa da rabon sa na Alkhairi kusa sai gashi ya samesa a kofar gida Allah kenan,ita kuwa Murja mutumin taso ya kaita don Yan kwanakin nan suna yawan ganinsa ita da kawayenta da safe in zai tafi Aiki,su kuma zasu makaranta,suyi ta santin kyawunshi har Addu'a suke Allah yasa watarana ya rage masu hanya,yau dai ga dama ta samu sai kuma rashin rabo ya gifta.

Juya kan motar yayi lokacin da yazo karshen lungun ya hau mik'akkiyar hanyar da zata kaisa har gida,Wata irin k'ara ce ta ziyarci kunnuwansa,A hankali ya d'aga idanuwansa ya kalli Rear view mirror din motar don daga bayansa yaji k'arar,lokaci guda yanayin fuskarsa ya canza zuwa tsananin mamakin abunda idanuwansa ke gani a bayan motar,nan take kuma ya tsaida motar ya bud'e kofar ya fito cikin tsananin mamaki,bayan motar ya nufa ya tsaya yana kallon Glass din bayan wanda yai tartsatsa duk ya tsatstsage wani wurin ma ya 6ule alamun wani abu aka jefo ma glass din,juyawa yayi ya kalli d'an can gefe dashi gaban wani gida,Fatuu ce atsaye ta rik'e kugu ta turo baki tana huci har lokacin hijabinta na d'aure a k'ugunta,
kallonta yake ba ko kyaftawa ya had'e girar sama data k'asa,ganin irin kallon da yake mata ne yasata juyawa ta ruga da gudu cikin lungun dake opposite da wanda Haisam din ya fito.

Wani bak'in matashin saurayi ne da tunda ya taho daga d'an nesa yaga lokacin da fatun ta jefi bayan motar da dutsi ya karaso wurin,sam ba natsuwa tattare dashi gashin kansa duk yayi cibir cibir yana sanye da kod'addun kaya t-shirt da wando 3-qurter wanda duk ya farfashe,ya d'an sa6ulo ana hangen boxer din ciki la66ansa sun yi baki sosae alamun dai yana shaye shaye,tafa hannuwa ya shiga yi yana salati ganin yadda glass din yayi"La'ilaha illallahu,Muhammadu d'an Abdullahi,tayi tsiyar da ta saba,wannan yarinya anyi yar Akuya wallahi" yayi maganar yana wani ciccije baki irin yadda yan shaye shaye keyi,shidai Haisam still yayi yana ta kallon ikon Allah,matashin ya cigaba"Wallahi Oga haka take bata jin magana ko kad'an eeh duk tabi ta hayyaci mutane tamkar Aljana haka take,toh wallahi Oga ko ni duk iskanci na bazan yi kwatankwacin wannan aika-aikar ba don nasan mizai je ya dawo eehh" ganin yadda Haisam d'in ke masa wani kallo yasa yace "koda yake Oga ba wani iskanci ma nike ba fa,kawai ina nufin yar k'iriniyar mu ta samari" yana maganar yana wani janta,
"Amma Oga sam bai kamata ka kyale yarinyar nan ba,inba haka ba zata ci gaba da wannan Akuyancin ne ya kamata kadau k'wakkawaran mataki" nodding kai Haisam yayi alamar to,kawae ya juya don ya gaji da saurararshi,

cigaba da magana matashin yayi yana bin bayan Haisam d'in lokacin har ya kama k'ofar motar zai bud'e "Oga in maka kwatancen gidansu ne?" juyowa haisam yayi hannunshi d'aya rike da kofar ya bisa da ido sai da yadau yan seconds yace"Ina jinka" da sauri matashin ya fara magana harda gyara tsayuwa za'ai zuga"Yauwa Oga idan ka mik'e wannan hanyar da zaka bi,ka shiga ciki ina kasan gidan Hajiyar Sanata? Kai Haisam ya d'aga masa alamar "Ehh" ya cigaba"Yauwa to kafin ka kai gidanta ai kasan akwai wata yar kwana da ta raba gidanta da sauran gidajen 6arin tunda ita gidanta kaga tangameme ne yad'an shigo ciki kuma katangar gidanta akwai tsawo....,kowa ya tambaye shi wannan bayanin oho,ya cigaba "to ai gidansu ita waccan Aljanar yarinyar na nan daga shi sai wani sai ita kwanar akwae ma d'an kiyos a gaban gidan,In ma baka gane ba Oga da ka tambayi gidan DIJE ATTENDER,za'a nuna ma da yake awurin kakarta take kuma ita kakar aiki take a asibiti irin masu.....bai k'arasa ba Haisam ya dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu yace "na gane" yana k'okarin juyawa matashin yace "ko nazo na raka ka ne Oga?"
"No Thanks" Haisam yace lokacin kuma ya shige cikin motar,da sauri matashin ya rufe masa kofar yana fad'in "Allah ya tsare Maigida,Sauka lapia maigida" yana d'aga masa hannu kai da gani kud'i yake son ya bashi,shi kam Haisam jan motar yayi yai gaba abunsa don ya fahimci d'an shaye shaye ne,
Rik'e kugu saurayin yayi a fili yace"Hakanan a banza na wahalar da kaina ma ashe wurin yi masa kwatance,ko yar asi bazai ban ba,mtsww.." yaja tsaki,kafin ya cigaba"ni har nasa ran zan samu na kayan harka,wasu mutanen dai sun cika mak'o wllh" daga haka ya juya saida ya harbi k'asa irin yaji haushin nan kana yai gaba yana ta wuwwurga k'afa shiga niga,Allah ya shirya.

Ko ta kan kwatancan da akai masa bai bi ba,straight gida ya nufa yana karya kwana Officer ya tashi don bud'e masa gate Haisam ya dakatar dashi ta hanyar yi masa horn,juyowa yayi ya nufo wurin motar a hankali ya d'an sauke glass d'in yace ma Officer d'in "I will park it here" daga haka ya maida glass din ya rufe sai daya dan d'auki mintuna kafin ya bud'e kofan ya fito hannunsa d'auke da laptop da charger dinta,Officer yace "You're Welcome Sir" "thanks" Haisam yace kafin ya shige ta k'aramar kofa direct part d'insa ya nufa.
Yana shiga palor ya cire takalmansa a gefe saman desk ya nufa ya aje laptop da charger din,ya wuce saman kujera L-shape ya zauna ya jinginar da bayansa had'i da d'age kansa yana facing sama da gani abunda ya faru yake tunani,don makamancin hakan had never happened to him,hasali shi yara ma tsoron sa suke ba abunda ke hadashi da su,shiyasa da yaga fatuu zata yi masa rashin kunya ya mare ta don tun a jiya ya fahimci bata da kunya,shi da har manya ma shakkarsa suke sai gashi yau Fatuu ta aikata masa wannan d'anyen aiki.

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*


BY
OUMMU IMAM

*Free Page 12 &13


D'agowa yayi after some minutes yasa hannu gefensa ya d'auki wayarsa wadda ya aje lokacin da zai zauna Contacts ya shiga yayi searching wani suna Iro Mechanic yai dialing kira,bugu biyu aka d'aga speaker ya kunna ya aje wayar a hannun kujeran ya koma ya jingina daga d'ayan bangaren aka fara magana"Assalamu Alaikum" kafin Haisam ya amsa aka cigaba da magana "Allah ya taimaki babban Engineer" amsawa Haisam yayi da fad'in"Malam Iro ya aiki" on the other hand aka amsa "lafia lau wallahi ranka ya dad'e,barka da juma'a" haisam ya amsa"Barka dai,mota ce zaka zo ka d'auka tana nan na parker ta a waje",
Iro yace"toh yalla6ai badai matsala ta samu ba ko? d'an murmushin gefe yayi yace "Malam Iro ku da an nemeku ai kasan matsala ce ko" Iron yace"Hakane yalla6ai,to Allah yasa ba babban matsala bace," hannu haisam yasa ya dan shafi fuskan shi kafin yace"Eh,Widescreen din baya ne yayi damage,so it needs to be changed" Salati Iro ya saka yace"yalla6ai garin yaya,wacce ciki ta samu matsalan? Haisam daya fara k'osawa da maganar amsar k'arshen kawai ya bashi "406,in ka lissafa komae let me know" yana niyyar latse kiran da sauri Iro yace "to yalla6ai sai a sanar ma da Jami'an nan zanzo d'auka tunda kace tana a waje duk da sun san mutum sai....." Haisam ya katse shi da fadin"zan fad'a masu" daga haka ya katse wayan.

Mik'ewa yayi walking slowly ya nufi gaban desk ya dauki telephone yai dialing numbers sannan ya kara a kunne daga can bangaren daya kira aka d'auka"Security" shine abunda aka ce,shi kuma yace"Somebody will come and take the car I parked out there" daga can bangaren akace "His name sir?"
"Iro Mechanic" Haisam ya fad'a daga haka kuma ya kife kan Telephone d'in ya nufi bedroom d'insa,da alama bautar jikin zashi yi inji dai hajia.

Bai dade sosai ba ya fito, sanye da wani lallausan farin Voile ana hangen farar vest d'in ciki sai dai ba sosae ba anyi mashi dinkin Senator style,irin style d'innan wanda rigar ke tsayawa a rabin cinya sai dogon hannu wanda ake matse k'asanshi da link yasa links d'in silver da ratsin bak'i,kafafunsa na sanye da takalma plain half cover bak'ak'e masu kyaun gaske kai da gani kasan zasu yi tsada ga wata Hadaddiyar agogo silver,sai hula da ya sa itama bak'a sai dai bata rufe duka kan ba ana ganin gashin kansa daga gefe gefe haka ma na k'eyarsa ya turo,tana da d'an karamin kulu a tsakiyar ta,irin hular nan ce da ake cema Igbo cap amman da ganin jikin wannan mai tsada ce.

Part d'in hajia ya nufa tana zaune saman kujera one seater jikinta sanye da jalbab fara sol ga glasses mak'ale a idanuwanta ta d'an duk'a tana karatun Qur'ani wanda ke a saman table,da sallama ya shiga a kujerar kusa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login