Showing 69001 words to 72000 words out of 212491 words
don kyautatawa da nuna damuwa kuma hakan na sasu farinciki sosae,baki ga iyayenmu in zasu kaima manyan mutane ziyara ba sai su kai masu yar kuka dasu daudawa ba kuma kiga suna ta farinciki duk da sunfi kafinsu nesa ba kusa ba,to shima ina tabbatar maki in kika kai masa zai yi farinciki sosae yaga kindamu dashi hakan kuma zai k'ara dankon kauna a tsakaninku" wani kallo tayi mashi kaman zata kai masa bugu da sauri yace"ina nufin kaunar yan'uwantaka fa",
Ajiyar zuciya ta sauke,ta bud'e jakarta kudi ta fiddo yan hamsin hamsin,ishirin,goma harda naira biyar biyar ta mik'a masa"gashi kaban na duka kuma cika man leda zaka yi komae ka zuba"kar6ar kudin yayi yana fad'in"wannan kudi haka hajiya fateema,nawa ne da har za'a cika leda"fara k'irga kudin yayi kafin ya kalleta"dari biyar ne"daga masa kai tayi alamar eh,
"To amman d'ari biyar har acika leda,za'a dae zuba na iya d'ari biyar din" da sauri tace"a'a nidae komae zaka zuba man"tayi maganar tana tura baki,shiru yayi hannunsa rik'e da kudin yana mata kallon mamaki"taya zan zuba maki komae na wurin nan a d'ari biyar,kayan nan fa ba wata riba ce dasu ba don sunyi tsada yanzu,in ban ci riba ba ai bana fad'i ba ko,kinga wannan yankin kankanar naira dari take zansa maki ita,sai lemu da ayaba,sai in had'a maki da wannan yankin abarbar shima dari ne...."
katseshi fatuu tayi"harda Apple zaka sa man" d'an bude ido yayi"Apple!taya zan had'a maki da shi abunda duk d'aya 300 yake,to kuwa saidai abaki apple d'in sai yankin kankanar nan sai asa maki lemu..",
"to ayaba da abarbar fa" fatuu ta tambaya,
"To indae harda su kike so gaskia sai kin karo kudi,ki k'aro wata dari biyar din asa maki komae,a cika maki ledar"
"To ni ina naga wata d'ari biyar din,wannan ma kasan ko kudin miye na baka,nidae ka zuba man yadda kace din da farko sai ka saka man Apple d'in" shiru mai kayan marmari ya yi,lokaci guda ya fahimci rigimamma ce yarinyar,yar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"kingane ko hajiya fateema kar6i kudin nan,ki d'an k'ara gaba can gaban wanccan wurin wankin motocin,akwae wani mai saida kayan marmarin k'ilan nashi su fi nawa sauki don ni gaskiya ban iya baki yadda kike so,fad'uwa zanyi",
k'in amsar kudin tayi tace"tabb wllh ba inda zani,ai kai ka kirani kace inzo za kai man sauki ko sai kuma kace wai inyi gaba ba inda zani sai kaban yadda nike so...."a fusace yace"to na fasa saidawar kije wani wurin,kar6i kudinki" turo baki tayi ta juya masa k'eya tana fad'in "Allah ko kaban ko in tara maka mutane ehe" zaro ido yayi"ki tara man mutane akan me,ana dole ne a kasuwa,yau naga karfin hali ni Rabi'u,fitsara zaki man nida kaya na" juyowa tayi ta kalleshi"ba wata fitsara,in mutanen suka taru ai sai suyi mana sharia aga wanda baida gaskia atsakaninmu,tunda dae kai ai ka kira ni ko"shiru yayi yana tunani cikin ranshi,anya yarinyar nada cikakken hankali kuwa,gara ya lalla6ata su rabu lpy,
"Yanzu kingane to ki k'aro d'ari biyu sai in baki harda Apple d'in,ai kema nasan bazaki so in fadi ba ko hajiya fateema ki tausaya mani mana,nima sai nayi ciniki nike samu ina ma iyalai na cefane"lalla6ata ya shiga yi,ta k'ara bud'e jakar tana fad'in"ni bani da wata d'ari biyu naira d'ari ta rage man itama ajewa nayi don kar in rasa ko sisi" sababbin yan ishirin ta fiddo da gani kudin da hajiyar Sanata ta bata ne,mik'a mashi tayi bayan ta zare naira ashirin wai bazata zauna ba ko sisi ba,girgiza kai kawae yayi ya kar6i tamanin d'in ya fara kokarin zuba mata a leda bayan ta matsa masa saida ya kara lullube su kankanar da leda bayan wacce ke a jikinsu,yana zubawa tana masa korafin masu kyau zai bata don d'an gidan hajiyar Sanata ne zai sha in yaga ru6a66e bazai sha ba,
Dakyar aka gama wannan ciniki ta juya ta tafi mai kayan marmarin ya d'an d'aga murya cike da tsokana"to yar fillo sai kin k'ara zuwa ko,Allah ya ba masoyinki lpy ki gaida man shi don Allah" juyowa tayi cikin fushi tace"ban k'ara zuwa siyan wani abu wurinka"daga haka tayi gaba,
Dariya mai kayan marmarin yayi a fili yace"in kana sana'a kaga mutane kala kala".
**** **** ****
Fitowa Haisam yayi daga cikin Bedroom ya nufo cikin falo yana d'aura agogo a wrist d'insa,da gani alwala yayi,wurin da laptop dinsa take ya nufa don ya kashe ta,turo kopan da akai ne yasa shi dakatawa ya tsaya yana jiran ganin wanene ke k'okarin shigowa,bakinta d'auke da sallama ta shigo,tana ganinshi ta saki Murmushi shima d'an murmushin ya yi mata,tsaye tayi tana kallonshi tana ta kunshe ledan hannunta cikin Hijab,bangaren da armchairs suke ya nuna mata"get seated"ya fad'a gently,
Shigowa ta k'arasa yi ta nufi wurin kujerun ta zauna saman d'aya,shima zaunawa yayi kan L-shape d'in,sai faman Murmushi take saki tak'i cewa komae hakan yasa shi cewa"har an tashi" kai ta d'aga masa alamar eh,shima jinjina kae yayi kafin ya juya yana k'okarin kashe laptop din,
juyowa yayi ganin tana ta nuku nuku da abu cikin hijab yace"ba aiken ki akai bane,kije ki kai ni zanje masallaci" jin haka yasata fiddo ledan ta aje saman carpet kafin tasa hannu ta rufe bakinta tana k'umshe dariya,kallon ledan yayi sai kuma ya kalleta"What is it?" ya tambaya,
"Abun ciwon ne na kawo maka"ta fad'a har lokacin hannuta na rufe da bakinta,he was speechless,cike da mamaki Haisam ke kallonta jin abunda tace wai abun ciwo ne ta kawo masa,cire hannun tayi ganin kallon da yake mata"ba d'azun kace ban kawo maka komae ba,shine yanzu na kawo" tayi maganar tana turo baki,
d'an Murmushin mamaki yayi yana jinjina kai"Open it let me see what's inside",
hannu tasa ta bud'e ledan ta d'an turata gabanshi,bin fruit din yayi da kallo,tunani ya shiga yi cikin ransa yana fad'in wani irin yarinya ne wannan,d'agowa yayi ya kalleta"baki san wasa bane,ni wasa nayi maki ai ba ina nufin ki kawo man wani abu ba...."katseshi tayi"ai yakamata dae in kawo d'in tunda dama saboda ni kaji ciwon ko"dan ta6e baki ya yi kawae,in ya biye mata haka zasu yi ta jan maganan"a ina kika samu kudi haka?"ya tambaya yana ci gaba da kallonta,
d'an langa6ar da kai tayi tace"Kud'in adashe ne da muke yi nida kawayena yan makarantar bokonmu,to ni ce ke yin tari don ban yarda ba in ba wata kudina ta cinye",
"amman ai ke gashinan sun yi trusting dinki sun baki kuma kin kashe masu,
"ai zan biyasu dama d'ari biyar ce kawae ta adashen naira d'arin tawa ce hajiyanka ta bani,itama d'ari biyar d'in dama nida wata za'a ba kwasa yanzu,to rabi nawa ne rabin ne nata"
"Yanzu ina zaki samu rabin ki biyata da kika kashe mata?" yar dariya tayi"zan samu mana ai gwaggo na bani kudin break kuma sai nayi kalaci nike tafiya makarantar kaga sai in tara kudin,kuma hajiyanka ma na bani,ga kawu Amadu ma in nace ya ban wani abu zai ban duk sai in had'a in bata"shiru Haisam yayi yanata kallonta,
"ko bazaka sha bane"ta tambaya jikinta a d'an sanyaye,girgiza mata kai yayi"zan sha,amman karki k'ara yin haka,ni wasa nike maki" dan ta6e baki tayi"kenan ni baka son in baka abu?"
"Ina so,amman ba wanda zaki ta6a ma mutane kudi ba,understand?"jinjina mashi kae tayi tace"to ban k'arawa Yaya handsome,da ai abinci ma zan kawo maka kace bazaka ci ba,shiyasa ma na siyo wannan din",
"Na koshi ne,da zan ci ai" ya fad'a da d'an murmushi,itama Murmushin take tana kallonshi,
k'okarin mik'ewa ya fara yi"nafa yi wankan" fatuu ta fad'a,
d'aga mata kai yayi yana kallonta daga tsaye,ta ci gaba"wllh nayi,ina komawa gida kafin na tafi islamiyyar nayi kawae ban shafa turare bane shiyasa baka ji kamshi ba"ta k'arasa tana d'an sunsuna hijab dinta "miyasa baki sa turaren ba"haisam ya tambaya,
"ai bandashi yanzu,dama gwaggo ke siyo man a wurin abokiyar aikinsu irin wanda ake sawa a yar kwalbar nan irin ta fiya fiya,ka santa?" kai ya daga mata alamar eh,taci gaba"to irinshi,wanda garan rannan ina cikin shafawa ya fad'i ya fashe,amman tace zata siyo man wani"jinjina kae yayi alamar toh,cikin cool voice d'insa yace"yanzu zanje masallaci time yayi" da sauri fatuu tace"to su kankanar fa bazaka sha ba?",
"Zan sha mana,amman yanzu kinga sallah zanje,abunda za'ai ki tafi man dasu part d'in hajiya in nagama zanzo sai in sha,kema sai kiyi sallan ko" kai ta d'aga alamar toh ta mik'e bayan ta d'auki ledan,harta nufi kofa ya tsaidata"Zarah"juyowa tayi ta kalleshi,"wait,am coming"d'aga haka ya juya ya nufi bedroom d'insa,bai jima ba ya dawo,mik'a mata wani had'add'an kwalin turare yayi yace"kiyi amfani da wannan baida karfi sosae,za'a samo maki wasu" zaro idanu waje tayi ganin tana niyyar yin magana ya rigata da fad'in"ba rokona ki kai ba" dariya ta saki tace"ya akai kasan abunda zance Yaya handsome"shima yar dariya yayi"amsa kisa a bag d'inki" kar6a tayi tace"thank you Yaya Handsome" kai ya d'aga kawae daga haka suka nufi hanyar fita tana gaba yana bayanta.
Suna zuwa daidai fence door d'in fita daga part d'in nasa ta juyo da sauri da yake shi a hankali yake tafiyan saboda kafansa mai ciwo,ad'an rude tace"akwae matsala Yaya handsome,in na kae maka wannan fruit d'in part d'in hajiya kuma ta gane abunda ya faru fa ko ka gaya mata ne??"ta kai maganar tana ta zare ido,d'an lumshe ido yayi ya girgiza mata kai alamar a'a kafin Calmly yace"don't worry ur self bazata gane ba"jinjina kai tayi harta juya sai kuma ta sake juyowa "Yaya handsome ko ka dafa kaina mutafi naga dakyar kake tafiyan"da'n bude idanu yayi da murmushin da iyakarsa saman lips d'insa yace"sai dae in rankwashi kan" dariya ta kyalkyace da ita ta juya,
A harabar gidan ta tsaya tana yima dawisu wasa can ta d'aga kai ta kalli haisam da ya kusa isa kopan shiga masallaci ta kware murya tace"Yaya Handsome,don Allah kai man Addu'a Allah yasa in zama likita" hannu ya d'ago mata ba tare da ya juyo ba daga haka ya shige cikin masallacin lokacin ana cikin tada ik'ama,saida ta gama shiriritarta a harabar gidan kafin ta nufi part din Hajiya.
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_*(Love and Destiny)*_
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D2Y0l2ZoRx8FLdjdi2Te0F
_*BY ZAINAB LALUH📲*_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
*3️⃣6️⃣*
Lokacin da fatuu ta shiga parlon ba kowa,deep freezer dake a Dining area ta nufa ta bud'e ta saka ledan fruit d'in kafin ta nufi corridor d'in d'akunansu,bedroom d'in hajiya ta fara zuwa ta isketa tana yin salla hakan yasa ta fito ta nufi d'akin Saude itama sallan ta taras da ita tana yi, shiga ciki tayi ta aje jakarta a gefen k'atuwar katifar sauden ta nufi toilet ta d'auro alwala itama tazo ta kabbara sallan,
Juyowa fatuu tayi ta kalli Saude dake zaune tana yin lazimi bayan ta gama sallan tace"ina yini Aunty Saude "fuskarta da fara'a ta amsa" lafiya lou fatima yar gidan hajiya,ya makaranta? "Lafiya lou" ta bata amsa,daga haka ta mike ta fita,bata jima ba ta dawo har lokacin sauden na a zaune,kallonta fatuu tayi bayan ta zauna"Aunty Saude kin daina koya man abincin yan gayu",
Yar dariya tayi"ai ba lokaci ne fateema kinga kullum kina zuwa makaranta ga kuma islamiyya ki bari in aka sake yin hutu sai in ci gaba da koya makin ko kuma tunda Azumi ya kusa ma kinga sai mu yi a lokacin don an fi yin abubuwa da yawa"jinjina kai fatuu tayi, Saude ta ci gaba"wai ina kawar nan taki ne kun rabu da zuwa tare",
"wai Haulat,tana nan,sai azumi yazo za ki ganta tana lalla6owa shan A.c"dariya saude tayi, fatun ta sake mik'ewa ta fita bata jima ba ta sake dawowa,ganin tana ta zarya yasa Saude fad'in"Hajiya kike jira ne,kinsan in tayi magriba sai ta yi isha'e take fitowa... "Fatuu ta katseta"a'a ba ita nike jira ba,Yaya hansome ne yace in jira shi anan" ba tare da saude taji sunan da ta kira shi da shi ba tace"ai kuwa shima wani lokacin sai anyi isha'in yake shigowa" d'aga kai fatuu tayi"to bari inje in gaisa da mutumina Aku kafin ya shigo"ba tare da ta jira abunda sauden zata fad'i ba ta juya ta fice,
Hajiya ce ta shigo cikin parlon bayan angama sallan isha,zama tayi akan kujera 2 seater ta d'au remote tana kokarin canja channel Haisam ya shigo da sallama 3 seater ya nufa ya zauna,hajiya ta juyo tana kallonshi da d'an murmushi, shima murmushin ya mayar mata"hope u'r ok sweethrt", "lafiya kalau nike" hajiyar ta bashi amsa tana shirin k'ara yin magana fatuu ta shigo cikin falon da gudu ta kofar baya,juyawa hajiya tayi tana kallonta har ta k'araso ciki a gefen hajiyar ta zauna tana ta dariya"ke kuma yaushe kika shigo?" hajiya ta tamabaya, maimakon ta bata amsa sai cewa tayi"wllh hajiya wancan Akun ya raina ni na kusa in mashi jan bugu"ta k'arasa tana nuna yadda zata buge shin da hannu,
hajiya tace"toh,yau kuma miya hada ki da mutumin naki ne?"
"wai daga nace Aku mai fitsari a tsaye shine yace man fatuu mai kashin kwance" hajiya tace"ah laifinki ne don mi zaki ce masa mai fitsarin tsaye a ina kika ga yana fitsari a tsaye"turo baki tayi"to ai ni wasa nike masa ko" hajiya tace"ai shima wasan yake maki nasan,ina Dije ko tana wurin aikin?",
"Eh tana can tana faman share-share da goge goge" hannu hajiya tasa ta d'an bugi kafad'arta"ja'ira aikin nata kike ma tsiya,ai da share sharen take biya maku buk'atunku ko,ita dije yanzu ai saidae ma tasa ayi don babba ce ita,ta jima tana aikin gashi har ta iya allura ciwo ma in bai tsanani ba tana fad'in maganin da za'a ba mutum.... " fatuu ta katseta"har k'arin ruwa ma tana sa ma mutane"hajiya ta jinjina kai"to kin gani,ai dije akwae kwazo",
Juyawa tayi ta kalli haisam dake danna wayarsa ya d'an kishingida hadi da mikar da kafafunsa saman kujeran sai kuma ta saci kallon hajiyan ganin ta maida hankalinta kan tv yasa ta mik'e taje gabanshi a hankali kaman mai rad'a tace"in kawo maka fruit d'in?" ba tare da ya kalleta ba ya d'aga mata kai alamar eh,juyawa tayi ta nufi hanyar kitchen,sai da ta bud'e freezer ta fiddo ledan kafin ta shige cikin kicin din,a saman plate mai dan fad'i ta jero mashi bayan ta cire bawon su ta yayyanka amman bata yanka Apple d'in ba,yadda ta jera su sunyi gwanin sha'awa.
Gefen kujeran da haisam yake ta aje kafin ta juya ta kinkimo sofa table hakanne yajawo hankalin hajiya kanta ta bita da ido ganin abunda take,gaban Haisam ta aje table d'in ta daukko plate din fruit din ta d'aura,fuskarta d'auke da d'an murmushi bayan ta mik'e tace"Yaya handsome gashi nan"sai lokacin ya juyo ya kalli fruit din kafin ya d'aga kai ya kalleta shima murmushin yayi ahankali yace"thanks",
hajiya da ta saki baki tana kallonsu tace"ina aka samu fruit ko Tk ya dawo ne?shi naba sakon ya taho dasu d'azun da nace Saude ta had'a man fruit salad take sanar dani sun k'are",
juyowa fatuu tayi ta dawo wurin hajiyan ta zauna"ba shi bane wannan na Yaya handsome ne",
"toh yaya handsome kuma?" hajiya ta tambaya,kai fatuu ta daga mata alamar eh,juyawa tayi ta kalli haisam wanda gabadaya hankalinshi na akan wayansa da alama chatting yake sai faman Murmushi yake tace"kai ka zo da ftuit dinne?" Kafin ya bata amsa fatuu ta amshe"ni na kawo masa abun ciwo ne,baki ga bai lpy ba" da mamaki hajiya ta kalleta"ke kika kawo masa?" jinjina mata kae fatuu tayi alamar eh sai kyakkyafta idanu take hajiya tace"daman kinsan Haisam ne?",
"Eh mana baki ji har sunanshi na fad'i ba" dan ta6e baki hajiya tayi sai kuma tace"amman baki ta6a ceman kin sanshi ba,shi dae nasan magana bata dame shi ba daman ba lalle ya fad'a man ya sanki ba..." da sauri fatuu ta tari numfashinta"to nima ai ina da sirri ko" bud'e idanu hajiya tayi cike da mamakin maganar fatuu tace"ah lalle kam ni shaida ce,amman yaushe kika san ya samu raunin ne?naga jiya da dare ya hadu da tsautsayin" wuki wuki da idanu fatuu tayi ganin kaman hajiyan nason ganota,turo baki tayi tace"kai hajiya bafa kyau zurfafa bincike nasan kin sani,nace maki na sanshi baki ji ma yaya nike ce masa ba,ai d'azun bayan na dawo boko nazo shine naga bai lafiya to ban shigo nan ba saboda lokacin islamiyya yayi shine fa na tafi" jinjina kae hajiyan tayi alamar gamsuwa,
Kallon Haisam tayi ganin hankalinshi na akan waya bai shan fruit din tace"Yaya handsome kasha mana" ta6e baki hajiya tayi"uhmm karma ki wahalar da bakinki...." maido idanunta tayi kan hajiya"bai shan fruit ne?"ta tambayaa,
"Yana sha amman shi fa komae sai an matsa masa yake ci kaman wani k'aramin yaro,kwata-kwata baison cin abinci ina ga dae tsukakkun yan hanji ne dashi" zaro ido fatuu tayi ta juya ta kalleshi har lokacin idonsa na kan wayar tamkar bai jin abunda ma suke cewa,hajiya taci gaba"kinga dae yadda yake k'ato tubarkallah, kamata yayi ace yana cin abinci hannu baka hannu kwarya,amman sam baison cin abinci k'irar tasa duk bogi ce ta k'arfe ce,yanzu fa inda zai sha fruit dinnan to wllh kina iya ganin ba lalle ya k'ara cin wani abu ba da daren nan,k'ilan sai dae ko tea da biscuit ko snacks,yafa iya yan ciye ciye maras amfani shi ga bature", ta k'arasa tana turo baki, daman rashin cin abincin nashi na damunta,ita kam fatuu tsura mashi ido tayi tana tunani cikin ranta"ashe abubuwan da ya bata d'azun sune abincin shi bai son cin abinci.."ji yayi ajikinshi idanu na yawo akansa hakan yasa ya juyo ya d'an kalleta tana ganin sun had'a ido tayi masa alamun ya sha fruit d'in da hannu tana yamutsa fuska,wani kallo yayi mata mai kama da harara ya juya yaci gaba da lallatsa wayansa.
A hankali yasa hannu ya d'auki Apple d'in ya kai bakinsa ya gatsa,lokaci guda fatuu dake kallonshi ta saki Murmushin jin dadi dama tasan zai so Apple d'in tunda shi d'an gayu ne shiyasa ta matsa sai da mai kayan marmarin yasa dashi,juyo idanunsa yayi ya kalleta, washe baki tayi tana dariya hakan yasa ya d'an mata side chuck kafin ya mayar da kanshi