Showing 48001 words to 51000 words out of 212491 words
daga hannu ita ala dole bata da laifi.
"Nima kenan laifi nayi maki don na raba ku fada shiyasa kika fasa man glass din?haisam ya tambayeta yana k'ara kur6ar lemun,
"a'a ni badon ka rabamu fada ba,ba gaura mun mari ka yi ba,wllh har saida fa naga wuta" ta turo baki tana sussunar da kai kasa,jinjina kai haisam yayi,da alama dai yana enjoying hiran ko kuma kilan har yanzu akwae sauran abunda yake son sani game da ita ne.
"Shi abun da kika jefan ya mutu mi yayi maki shi kuma?ya jefa mata tambaya,kallonshi tayi har lokacin akwae kwalla a fuskarta tace" wai akuyan jibo? dage mata gira yayi alamar eh,durkushewa tayi don ta gaji da kneeling d'in tace"ba a makarantar bokon mu ne aka koya mana yadda ake shuka abinci ba,shine fa na had'a yar gona a gefen gidanmu na shuka gero da masara inason in sun fito in saida insamu kudi saida suka fara fitowa watarana kawai naje gonar naga an tuge su duka wllh ranar naji bakin ciki,kasan mi? ta d'age ido sama,a hankali haisam ya girgiza mata kai alamar a'a,taci gaba"harfa kuka nayi,naita birgima gashi abun haushin ma bansan waye ya tugen shukan ba,Yadikko nace taita bani hakuri da Baffana ya dawo ya sake bani wasu yace inje in shuka yace insamo k'ayoyi na rufe wurin in ta fara fitowa,shine fa na hakuri amman duk da haka na dau alkawarin inna gano ko waye wllh bazan kyale shi ba,bayan wani lokaci da shuka su suka fara fitowa nayi yadda baffana yace inyi sosai nike kula da gonata kowa yasan gonar fatuu masifa ce ba mai zuwa wurinta,abun bak'in ciki...." tasa hannu tayi tagumi cike da damuwa,haisam dai still yayi yana kallon Mental fatuu,
taci gaba"wai fa sai da shukan nan suka fara yin tsawo sosai watarana yadikko ta aikeni in debo ruwa a bayan tudu na dawo d'auke da tulu na akai tun daga nesa na hango kaman an bude man gona da sauri na nufi wurin tun kan na isa na hango yar iskan akuyar nan duk ta cinye shukan saura kad'an ta gama,Allah kun bansan lokacin dana saki tulun nan ba na rarumi dutsi na jefa mata bai sameta ba ta fara kokarin guduwa cikin sa'a kayoyi suka tokareta ta rasa yadda zata gudu nikam ina ganin hakan na dau icce na ritsata naita dukanta sosai hardai tasamu ta fice da kyar take gudu saboda kafafunta dana doka sosai,hakan bai ishe ni ba na sake rarumar wani k'atoton dutse na jefa mata aikam basai ya sauka akan cikinta ba kuma dama ciki ne fa da ita nan take ta fad'i a kasa tana birgima idanuwanta na haka...." ta langwa6ar da kai ta kakkafe idanunta tana displaying yadda Akuyan tayi,Haisam couldn't help it but laugh,da farko tausayin akuyan yaji don shi mutum ne mai tsananin tausayi amman yadda tayi yasa shi yin dariya har hak'oransa suka bayyana,yana ganin zata bude idanun ya yi saurin d'aure fuska.
*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*
_A heart touching love story_
_*BY ZAINAB LALUH📲*_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
27⃣
......Bud'e idanun tayi taci gaba"ina ganin haka na watsa da gudu gida,ashe wani yaro gidado ya gan sanda na jefi akuyan ina jinsa yana fadin sai ya gayo ma jibo,aikuwa d'an banzan yaron nan ya falfala aguje yaje ya gayo ma jibo abunda nayi ma Akuyarsa,ina tsaye gaban yadikko tana ta tambayana ina ruwan,miya faru ta ganni a firgice gashi na shigo a guje,ban kaiga bata amsa ba sai ga yaron yayan baffana sun shigo da Jibo rungume da Akuyar......,
kyalkyacewa ta sake yi da daria wannan karon har tafi ta d'azun tace "kai,wllh Jibo baida hankali,kasan wai ko wando fa bai sawo ba don masifa daga shi sai yar riga" d'aure fuska Haisam yayi yana d'an harararta,ganin haka yasa da sauri tace"banfa ganin mashi jiki ba,a'a wllh haram ni ba abunda nagani ai rigan jikinshi ya sauko har gwiwa fa,kama duba a computer ka zaka gan ba k'arya nike ba ni banga komai ba" ta daga hannu,
Haisam da yai zugudum yana sauraranta tamkar ya kunna Redio yace"uhum.."alamar taci gaba,tace"masifa da bala'e yazo yayi tayi yana cewa wllh sai an biyasa akuyansa in ya yarda shege ne shi,nan dai duk yan gida suka fito suna tambayan ko lafiya da yake gidanmu babba ne duk yayyu da kannen Baffana anan suke da iyalansu,ganin haka yasa Yadikko ta kira Babana a waya da yake lokacin yana kasuwa,ai yana jin abunda ya faru ya dawo da sauri don yana masifar sona baison wani abu ya same ni su kuwa sauran yan gidan duk sun tsane ni,kowa ya bud'e baki fatuu bata ji,fatuu bata da kunya,fatuu ka za,fatuu yen-yen....,kana ji ko?" daga mata kai yayi kawai da alama al'amarin nata yafi karfin tunaninsa.
ta cigaba"gaba daya aka kwasa aka tafi wurin Ardo don yayi shari'a,karshe dai ardo yace za'a bashi wasu yan kudi yayi hakuri,yace bai ganin ni yarinya ce,kuma suma wai fama suke da ni,Jibo kam ya rantse da kwarankwatsi gajimare Akuyarsa za'a biyasa kuma daidai girmanta harda cikin ma,kaji fa don bala'i,shi kuma Ardo yaji haushin jibon yak'i jin maganarsa amatsayinsa na shugaba yace har kudin ma ba'a bashi,aikuwa yace to ko daga nan gari ya nufa yan sanda zaije ya fada mawa,baffana yayi ta ba ardo hakuri yace ya bashshi ya biyasa acikin akuyoyinsu,saboda baison aje wurin polisawan ai man wani abu,da kyar fa aka biya jibo akuyansa,ai yana fita Ardo yace akamo ni da gudu naje na 6uya a karkashin gadon yadikko amman mugun yaron nan Jauro da yake ya tsane ni shima saida ya jawo ni aka zane ni don dama ardo baison abunda zaisa a ta6a masa dabbobi,bayan an doke ni kuma yace a d'aure ni daga ranar ban sake fita ko makaranta ma ban k'ara zuwa,kuma ko aike na ma kada a sake yi wai aure za'a man ya gaji da hali na,na dinga kuka, ni d'aure nin da akayi ma bai dame ni ba don nasaba,jin za'a man aure shi yafi damu na,don ni bana son auren karatu nike son inyi in zama likita,kwana na biyu a d'aure sai dare ake saki na inje in kwanta da rana kuwa ina a daure don karna fita,kaga ni aka maida Akuyan ko,Baffana ba yadda ya iya saidai yayi ta bani hakuri yana man fad'an in daina rashin ji in natsu don Allah,sam baijin dadin yadda ake maganganu akaina,ana cikin hakan rana ta ukku kawai ba sai ga gwaggo ba....."
dakatawa tayi ta rike ha6a tana kallonshi tace"kasan wace gwaggon? da farko shiru yayi yanata kallonta kaman bazaice komai ba sai kuma yace "Grandma dinki attender i guess" da sauri tace yauwa ashe kana ganewa,
"Aikuwa tana zuwa ta ganni a d'aure ta tambayi dalili aka fad'a mata ai sai tasa kuka,tace yanzu yar jikan tawa mace kwallin kwal ce ake ma wannan horon kaman wata dabba,tace to wllh kafanta kafa na,ina jin haka nima naita kuka nace eh zan bita don ni banson ayi man wani aure,shi Baffana baison rabuwa dani to amman shima baison ayi man aure a lokacin,duka fa ban dade da fita shekara goma ba,shi da gwaggon suka sami Ardo suka roke sa akan ya bada izini gwaggon ta tafi dani zanci gaba da karatu a wurinta,a tunanin ka mi zaice? ta k'ara jefa ma Haisam tambaya,
gyara zama yayi yadan bud'e dogayen yatsun hannunshi yace"zaice ki tafi kawae tunda kin dame su...." da sauri ta katse shi "haka fa wllh,cewa yayi Dille,dille Allah yaru on djam...wai kutafi,kutafi Allah ya kiyaye,kwana ukku gwaggo tayi lokacin na tattara komae nawa,muka taho Baffana kaman zaiyi kuka,nima banso rabuwa dashi ba dasu yadikko da yayana Kamalu don su kad'ai ne ke sona,wai kaga yadda aka rako ni kusan duka yan rugan fa kaman an rako wata diyar gwamna amman nasan duk murna suke zan tafi su huta" ta k'arasa sai faman nishi take dama kuma saman skirt dinta ya matse mata ciki saboda ta takure.
Sauke ajiyar zuciya yayi"shine da kika dawo nan kika dasa rashin jin instead of ki natsu ko" gyara gyalenta tayi dake ta faman zamewa tace"wllh naso fa in natsu in koma ba ruwana da kowa ko gwaggo ma tayi man fadan haka,to su yan birnin nan sun cika tsokanan fad'a,wai fa don lokacin da nadawo nan banjin hausa sosae duka abu kad'an na iya wani lokacin ma ba daidai nike fadan wanda na iyan ba shine sai suyi ta tsokana na suna ce man yar fillo,ni kuma banso,tun dai ina hakuri har na gaji na fara nuna masu nima yar banza ce" ta k'arasa tana jinjina kai,
haisam dake kallonta yace "ya akai kika iya hausa sosai?"
"ai nafa kwana biyu anan,shekarana ukku yanzu,kuma acan lokacin dana zo saboda tsokana na da ake shine k'awata wadda gwaggo ta hada mu da ita haulat ta rink'a koya man da kawu na Amadu,gwaggo ma in bata komai tana koya man,ban dade ba na iya,yanzu ma ni mantawa nike da ni fulani ce,duk da gwaggo nayi man wani lokacin wai karna manta gaba daya,kuma ma wani natan ni ba ganewa nike ba"
"While,thank u for dat,kinga yanzu kin ban leakage na yadda za'a ban shanun ba wani 6ata lokaci,tunda shi mai akuyan cewa yayi zai kai wurin police,ni yanzu in na tashi sai inje da armies nasan dole za'a bani ko? zaro idanu tayi a firgice tace "Sojoji! dage mata gira yayi"yeah,ko ahakan ma baza'a bani ba?" jiki asanyaye tace"dole ma a baka,amman nasan dole Baffana shi zai biya ardo,kuma ni shikenan zama na anan wllh ya k'are aure za'a man kuma ni wllh likita nike son zama...."kasa k'arasa maganar tayi saboda kukan da yaci karfinta,ganin haka yasa haisam cewa"hey,miye kuma na kuka haka,in kina ganin hakan da matsala sai mu canja wata shawaran ai" jin hakan yasa ta dakata da kukan ta d'ago tana kallon shi,
"What about your mom,wannan da kike kiran sunanta a story dinki ita ba sai ta bani ba,kinsan mothers normally sunfi tausayi" cikin muryar kuka tace"wai yadikko? daga mata kai yayi alamar eh,da mamaki take kallonshi tace"kai baka san mi yadikko ke nufi ba? banza ya mata,hakan yasa tace"au yi hakuri na manta kai dan indiyawa ne ba fulani ba,to yadikko ba mamana bace kishiyan mamana ce,kuma ita ina taga wasu shanu goma,ko fa baffana na gaya ma baida shanu goma ballantana ita",
"Ita mom din naki fa" ya tambaya,ai kaman jira take ta idasa durkushewa ta langa6ar da kai cikin muryan kuka tace "Mamana ta rasu tun ina yar yarinya,ni marainiya ce wllh,ance tunda ta haife ni bata k'ara lpy ba,har dai bayan wasu shekaru ciwon yaci karfinta sannan fa aka kaita asibiti akace sai anyi mata aiki a cikin cikinta,haka suka dawo da ita gida wai sai an had'a kudin,da kyar Baffana ya samu ya harhada kudin sai da ma ya amshi aron shanayen ardo ana gobe za'a tafi kaita ayi aikin ta rasu...." kuka tasa sosai hakan kuma ba karamin sanyaya ma haisam jiki yayi ba,yayi shiru yana ta kallonta ta kife kai ajikin c-table,can ta dago tana goge kwalla da tissue taci gaba"shiyasa nike son in zama likita don banson in kara rasa wani nawa don wannan dalilin,don Allah kayi hakuri yaya handsome karkasa ayi man aure"
Shiru yayi yana cigaba da kallonta kaman yana nazarin wani abu,ita kuma sai sunnar da kai take yi kasa,sigh yayi "kinsan ke marainiya ce,kuma kina da wannan ambition din amman kuma kika kasa natsuwa ko..,while gaskia bazan iya yafewa ba don ba k'aramar asara kika man ba..." ta6e baki ta fara yi zata dasa kukan da sauri yace"karki fara wannan kukan! bake da bakinki naji kince ba haramun bane in an maka laifi kaji baka iya yafewa ka rama ba...." idanu waje take kallonshi ta rasa bakin magana,yaci gaba"kin tuna ko a story dinki da wadda ta 6alla maki kaza ne or what,so is the same da in anyi maka asara kaji baka iya yafewa kace a biya k..." tun kafin ya k'arasa yaga ta mike zumbur,don tun dazun take jin fitsari take rikewa yanzun ko tsabar rudewa tasa bata iya rikesa don gab yake da ya zubo mata,kallonta yayi sama da kasa ganin yadda take ta kerma gashi ta hade kafafunta sai tura hannu take tana dudduk'ewa yasa shi tambayar"lapia..."da sauri tace"fi..fitsari nike ji don Allah,zai zubo" kwalla ne suka fara gangaro mata,da sauri ya daga yatsansa pointing at d door opposite to him,yace"kije ciki akwae kofa by your right ki shiga" da sauri ta juya ta kalli kofan da yake nuna mata kafin ta nufeta da dan gudu-gudu,saboda kafafuwanta da suke a hard'e daidai bakin corridor gyalenta ya silalo kasa ta juyo kaman zata dauka sai kuma ta juya aguje ta tura kopan da alama fitsarin ya fara zubowa ne,sosai taba shi daria yana yi yana girgiza kai a fili yace"Silly Girl,
Duk wannan abun gwaggo na can tayi nisa a baccinta,dama tunda ta dawo tace ma fatun ta gaji sosae,ko lokacin da fatun ta tambayeta zuwa gidan hajiyan gab take da fara baccin,shi kuwa kawu Amadu yana shago mutane nata zuwa siyayya kasantuwar gobe Monday akwae aiki ga yan zuwa makaranta kuma,hakan yasa ake ta zuwa siyayyar abun bukata da safe,sam baima san fatuu bata gidan ba.
________________________
Waya Haisam ya dauka ya duba time,karfe 9:30 sauran yan mintuna dama lokacin da ya baro part din hajia tara bata k'arasa yi ba,shiru yayi yana dan tunani sai kuma ya d'an ta6e bakinsa kafin ya Kwantar da kanshi jikin kujeran yasa hannu yana shafa suman shi baya,lokacin ta fito ta duka bakin corridor din ta dau gyalen kafin ta nufo cikin falon tana yafa shi saman kanta,inda ta tashi ta koma tayi kneel down tana kallon shi,dagowa yayi suka hada ido wannan lokacin bata janye idanun nata ba a marairaice take kallon cikin idanunsa sun dan dau lokaci haka kafin calmly yace"hope baki 6ata man toilet ba..." da sauri ta daga masa kai"ai a cikin yar farar tukunyar nayi,a wurin hajiyar nan gidan na koyi yadda ake amfani da ita" dan bude ido yayi"wani hajia?",
"Hajiya mamanka,ai ta sanni kuma tana sona sosai har dinki take man,ko kayan nan na jikina ita ta siya man su hadda ma uniform din makaranta ita ke siya man da littattafai....don Allah yaya handsome kayi hakuri ka yafe man,wllh in taji wannan abun da nayi maka 6atawa zatayi dani dama tana tace man nabar rashin ji,wllh daga yau na daina,zan koma kamar haulatu ita ba ruwanta,nima dama don kar a raina ni adauke ni sakara shiyasa in aka man abu ban kyalewa amman tunda kowa haka yake so in koma zan koma Allah kun"
"Wa yace maki in baka yin fada raina ka ake ko a dauke ka sakarai? ai yawan fadan kesa ana insulting mutum,kuma shiyasa ma mutane ke tsokanarki,ni bana fada kuma ba wanda ya raini ko kallon banza ba wanda ya ta6a attempting yi man" baki sake take sauraranshi tana kallon bakinshi,jin yayi shiru tace "kai yama za'ai a raina ka,ai da an kalli fuskarka ansan baka wasa da mutane" dan ta6e baki yayi"yanzu ya kike so ayi" da sauri tace"kayi hakuri da abunda nayi maka,kace ka yafe ba sai an biya kaba don Allah yaya handsome" gyara zama yayi sosai ya d'an k'ankance idanunsa"who told u sunana haka?",
A hankali ta d'aga yatsanta ta nuna rubutun dake agaban rigarsa,wanda yake baki sai walwali yake,kai dubansa yayi inda ta nuna ya kalli rubutun wanda akayi in italic font an rubuta "*_Call Me Handsome_*,
Dagowa yayi ya kalleta cike da mamakin yadda ta iya karanta rubutun duk da style din da akayi ma rubutun bai mata wuyar karantawa ba,hakan ya tabbatar masa da tanada kokari kuma har turanci tana fahimta don in anmata tana ganewa"Ajin ki nawa a school? ya tambayeta,yatsun hannunta ta daga masa guda ukku,hakan yasa ya dan daure fuska da sauri tace"J.s 3 nike"
"dama a garinku kin gama primary school ne kafin kizo nan? Tace "a'a aji na hudu zanje biyar na dawo nan da farko ma ba makaranta nike zuwa ba acan gangare wani dan yayan Baffana da yayi karatu yake koya mana kafin yace ma baffana wai ina da kokari akaini makaranta,to lokacin dana dawo nan kawu Amadu nayi man lesson shine yace ma gwaggo basai an maida ni primary ba,akaini secondary kawai" jinjina kai yayi kafin yace"now sit properly zamu yi magana dake" da sauri ta mik'e tsaye ta dan tattare skirt din sama sannan ta koma ta zauna kaman wadda zata ci tuwo ta zuba masa ido tana jiran taji abunda zaice mata gabanta na dan bugawa amman ba sosai ba saboda ganin fuskarsa adan sake,
"Zan yi hakuri,in kuma yafe kaman yadda kika roke ni,amman on one condition,dole akwai abunda zansa ki.." da sauri ta katseshi"to wllh koma miye zanyi indai bai sa6a ma addini ba,koma ya sa6an zanyi sai na roki Allah ya yafe man" sosai ya daure fuska yace"nayi maki kama da wanda zai saki hakan??" da sauri tace"a'a yaya handsome don Allah kayi hakuri wllh bansani ba na fadi hakan...",
"karya kike,u said it intentionally yanzu ke har Allah kike sa6a mawa don kar ayi maki hukunci!"
Ganin yadda yayi maganar a kausashe yasata rudewa tsoronta kar yace ya fasa yafewar,lokaci guda ta fara kokarin kara yin kneel down baki na kerma tace"na rantse da Allah ban ta6a sa6a ma Allah ba don a yafe mani,kwarankwatsi kaji na rantse,ni ai bamma ta6a yin irin wannan laifin ba tunda na dawo garin nan" gaba daya ta rude jikinta sai faman rawa yake,alamu yayi mata ta zauna da hannu,komawa tayi ta zauna,
"to amman yanzu miyasa kika za6i ki sa6a mashi don kawai a yafe maki?"da sauri tace"daman naji malamin mu na islamiyya yace shi Allah mai hakuri ne yafi kowa hakuri,indai kayi masa laifi ka roke shi ya yafe maka to zai yafe makan"ta k'arasa maganar tana ta dage baki,
Girgiza mata kai yayi"You didn't get him right,banda laifin da akayi masa da gangan,in kinsan