Showing 75001 words to 78000 words out of 212491 words
haihuwan don nayi tunanin nima irin inna tace haihuwa d'aya zanyi sai ga cikin Amadu to tun daga kanshi ne ban sake haihuwa ba kuma yana shekara biyar babansu ya rigamu gidan gaskiya sakamakon had'arin mota da suka yi"d'an dakatawa tayi alamar jimami,
"Allahu kakana,Allah ya jikanka da rahama yasa ka huta,yanzu to ina ita Habiban gwaggo" Gwaggo ta amsa da "Ameen,ita ma yanzu kusan shekara bakwae da rasuwarta sakamakon jinya da tayi,sai dae ya'yanta da muke ta zumunci,ai kinsan zaliha ko ta kopar k'aura?" kai fatuu ta daga alamar eh,"to ai diyarta ce,da shehu dake zuwa gidannan..."katseta fatuu tayi bayan ta d'ago kanta"Baba Shehu?"Gwaggo tace"eh shi,to shima d'an habiban ne,yaranta shida",
"Allah ya jikansu gaba daya" fatuu ta fad'a,
"Ameen" gwaggo ta amsa.
Shiru sukae na wani lokaci gwaggon nata gyara mata gashin,can fatuu tace"Amman gwaggo ya akai to Innata tayi Aure a Yola?" fatuu ta tambaya,Ajiyar zuciya tayi kafin ta d'aura"bayan mungama takabar kakanku Abdullahi dole na koma daura don bani da kowa anan,alokacinne kuma kawu shi6ado ya matsa aima Aisha aure acewarshi tayi girma da yawa kuma dae da gaske yake don lokacin duk yankinmu ba babbar budurwa kamarta don shekararta 17 gashi tubarkallah sam jikinta ba irin na ainihin yanmatan fulani bane hakan kuma ya samu asali ne daga mahaifinta da yake cikakken bahaushe dama fuskarta sak shine,yana da kyau da dogon hanci amman baki ne,ita kuma Aisha sai ta daukko haskena don harma ta fini fari sosae kuma batada tsawo ba kuma gajera bace,sannan Allah ya hore ma Aisha kugu tun tana yar k'ankanuwarta ya fara bayyana lokacin da take shekara sha bakwae d'innan in ka kalli kafadunta bazakace k'ugun nata bane don ya bude sosae harda shi kesawa ana ganin tayi girma da yawa,kema naga alamun jikinta ne zaki daukko don sam baki da tsawo gaki nan yar dumurmur...."kyalkyacewa da dariya fatuu tayi"kice nima zanyi hips,ai kaman ma ya fito fa,innasa skirt yana nunawa, Allah shiyasa nike son sa skirt",
Yar harara gwaggo ta wurga mata kafin ta d'ora"lokacin da ake ta maganar ayi mata aure ita bata so karatu take son taci gaba da yi don a katsina tana makaranta harma ta shiga Sakandire,amman fir kawu shi6ado yace baisan zancen wani karatun nasara ba,kan kice mi samari sukayo mata ca bayan komawarmu amman ita bata son kowa ganin tak'i fiddo miji ne yasa kawu yace shi zai za6a mata duk wanda yayi mashi,ana haka sai ga Muhammadu wanda abokin wani yarone makwabcinmu shi kuma yaron abokin dan wajen kawu ne,Muhammadu Dan jahar Adamawa ne,manyan kasuwannin yankin Katsina suka fara kawu shanaye to shine ya fara sauka a wurin abokin yaron kawun dama kuma yan uwansu ne,yana ganin Aisha Allah yasa mashi sonta itama kuma ta amince dashi don tubarkallah ko ni lokacin na yaba dashi ga kyau ga biyayya ba 6ata lokaci akayi bikinsu,to kinji yadda mamanki ta auri baffanki,bayan shekara guda da auren ta haifi yayanki Kamalu nayi murna sosae ganin ba'a dau wani lokaci ba,Kamalu na shekara ukku ta Haifeki kar kiso kiga Murnar da nayi don na fahimci ita bata gado ni ba,ashe duk salesalin Ajali ne....",dakatawa gwaggo tayi fuskarta a yamutse,
"Kina shekara ukku Allah ya kar6i ran Aisha,ba lokacin aka fara man mutuwa ba amman naji mutuwar Aisha nayi kuka su kenan gareni su biyu ita da Amadu,ba yarda banyi ba alokacin amaido man ita nan amman sai kakanki ardo ya hana yace wai ba ciwon Asibiti bane to sanin Aishar nada iska ne yasa na amince da Maganarshi ashe ashe cutace kunshe acikinta....",
Dan ta6e baki fatuu tayi kaman zatayi kuka"Allah ya jikan mamata yasa tana Aljanna"gwaggo ta amsa da Amin ya Allah,kafin ta d'aura"Aisha ba ruwanta tana da halin kirki,har yau ina jin radadin mutuwarta sai dae ba yadda zanyi Allahn daya fi ni sonta ya d'auke abunshi,Wani lokacin sai inta ganin hada sakaci yasa ta rasu,da tun wuri an kaita asibitin angano cutar dake damunta k'ilan da ta rayu,amman Wannan nasan kawae rudun shaidan ne,ko ankaitan in Allah ya k'addaro a ciwon Ajalinta yake nasan dole sai ta mutu,baffan ki ma yaji mutuwarta wllh don yana son Aisha duk soyayyarta ce ya maido kanki,tun lokacin da ta rasu naso ya bani ke,amman duk kunya irinta fulani haka ya dinga rokona yana hawaye akan na barki acan,lokacin duk da halin da nike ciki ya bani tausayi hakanne yasa na kyale mashi ke kawae don nasan zai kula dake yadda ya kamata,"
Dago kai fatuu tayi"to gwaggo ki k'ara yin aure mana ba sai ki haifi wasu yaranba"harara ta wurga mata,fatuu ta fashe da dariya"Allah gwaggo baki tsufa ba sosae da anyi maki makeup aka nad'a maki gwaggwaro zaki koma kaman Yar budurwa,kinga sai muyi baba anan gidan",banza gwaggon tayi mata,
"Amman to ya akai kika dawo nan garin?",
"wai tambayoyin na miye fatuu,sai kace wata yar Jarida komai sai kin sani",
"Don Allah ni dae ki fad'a man,kinga ko tambayana akae watarana nasani",
"Akwae wani d'an uwan kakanki likita ne sunan shi Doctor Kabeer anan katsina yake,to watarana muka kawo mashi ziyara daga Daura ni da Amadu lokacinne yayi mun tayin aiki yace in inaso zai samarmun don insamu abunda zanci gaba da kula da rayuwarmu,nayi matukar farinciki nan take nace mashi inaso na bashi duk wani bayani da yake bukata,bayan komawarmu da yan kwanaki sai gashi ya kirani ya sanar dani nasamu aikin,lokacin da nazo na iske shi yake tambayata ya na tsara fara yin aikin don bai yuwuwa ince zan rinka zuwa daga daura nan nake sanar dashi zan samu gidan haya in zauna,sai yace in ba damuwa to in fara zama a gidanshi kafin wani lokaci,nan nayi ta mashi godiya naji dadi sosae,cikin sa'a na fara zuwa aikin lokacin Amadu nacan daura amman duk cikin sati sai nasamu lokacin dana je na duba shi,da tafiya ta fara mikawa sai na fara fuskantar matsala da matarshi Rukayya Wanda farko ba haka take mun ba muna zaman lafiya tana jin dadin yadda nike kama mata ayyuka da yake itama lokacin tana aikin koyarwa,amman daga baya duk irin hidiman da nike mata bata yabawa,don lokacin indai banje Aiki ba nike share mata gida,inma yaranta wanka har girki yi mata nike amman duk da haka sai tayi ta wani shan kunu gashi tayi ta nuna man iyaka da wasu abubuwan nasu Abinci ma sai in dafa amman iya wanda taga dama zata zuba man,ta hana yaranta guda biyu Mace da Namiji zuwa wurina da kuwa haka zasu zo muyi ta hira ina masu wasa har Assignment dinsu suke zuwa dashi suyi d'an abunda na sani in fad'i masu dayake lokacin na d'an iya karatu don lokacin da Aisha ke karatun boko tana koya mun,wata rana mai gidan ya aiko wani yaro lokacin tana a d'aki tayi bakuwa,wata aminiyarta ce tazo shine na nufi dakin don in sanar mata sai naji suna wata magana da ta d'aga man hankali,wai ashe dama kawartata ce ta zugeta take man abubuwan da take man alokacin,taci gaba da zugata tana fad'in"yanzu kike yin abunda ya kamata,don wllh da kinyi sake sai dae kiji ana shafa fatiharsu tunda ba wasu shekarune da ita sosae ba gata da kyan jiki,yanzu kamata yayi ki fara yi mata kora da hali har ta gaji ta tattara tabar gidan" jiki a sanyaye na shiga na fad'i mata an aiko wani,daga haka na fito suna bina da wani irin kallo..."dan dakatawa gwaggo tayi tana sauke numfashi,
"Tun daga ranar na fara tunanin barin gidan don kuwa kora da halin ta fara yi man,in suna kallo ita da yaranta dana shiga zata kashe kayan kallon tace kallon ya isa,haka zan fito Jiki a sanyaye,duk wannan abun Dr bai sani ba don bata yi man wulakancin agabanshi,watarana ina zaune a d'aki da daddare inata tunanin yadda zan bar gidan ba tare da Dr din ya tuhume ni ba don banson in haddasa masu fitina,can na tuna da wata tsohuwar gona da muka gada ta marigayi kakanku dake can gefen gari wanda alokacin inda gonar take ya d'an fara shigowa cikin gari don akwae yan gine ginen gidaje da aka fara yi a wurin,gari na wayewa na tafi daura wurin kawu shi6ado don kar6o wasu kudadena dake awurinshi anan nake sanar dashi inason zan gina koda d'aki daya ne a wannan gonar in koma,ya tambayeni dalili na kwashe komae na fad'i masa nan take ya goyi bayana yace daman bai kamata in yi masu zaune agidansu ba,shima ya k'ara man kudi na had'a harda na aikina dana d'an tara,ta hanyar wata Abokiyar aikina na samu wadanda suka gina man daki daya da kewaye aka kuma katange gidan,sai da aka gama ginin nasamu Dr kabeer A asibiti na sanar dashi cewa zan koma gidan,anan yake tambayana ko anyi man wani abu ne,nace mashi a'a inason zan daukko yaro nane nasa shi a makaranta to banson na k'ara d'aura mashi nauyi ne gana iyalinshi kuma,ya fahimce ni sosae yayi man fatan alkhairi ya kuma bani kudi masu yawa wanda zan sa Amadun a makaranta,Matar Dr na Zaune a falo ita da yaranta ba zato ba tsammani ta ganni d'auke da jakar kayana nayi mata godiya na sanar da ita zan bar gidanne daga haka nayi mata sallama na fito yaranta nata yi mun bye bye harda yar kwallarsu,wannan shine dalilin dawowata wannan gidan da muke zaune",
"Lokacin dana dawo na d'an shishshiga makwabta don agaisa in kuma gabatar masu da kaina amatsayin sabuwar makwabciyarsu,alokacinne nashiga gidan Hajiyar Sanata wanda ada bai kai yadda yake yanzu girma ba da k'ayatuwa,hannu bibbiyu ta kar6e ni ba kamar da ta ji ni yar daura ce don itama Asalin yar can ce tana ma da dangantaka da Masarautar Dauran,daga nan muka fara zumunci da ita sosae tamkar uwa haka na dauketa don ta haifeni,koda na daukko Amadu nasashi a makaranta kusan duk dawainiyar karatunshi ita keyi,banda damuwar inda zan barshi in zan tafi aiki don da ya dawo bannan zai tafi gidan hajiya daga baya tukur ya zama d'an gidan suka fara abota tare ma suke tafiya makarantar allo da yamma,rashin sa Amadun makaranta da wuri ne yasa tukur d'in ya wuce shi don duk tsararraki ne amman Amadu ya dan girme mashi,kinga shi tukur yanzu yana makarantar gaba da Secondary shikuma Amadu har yanzu a sakandiren yake,A hankali ahankali da Kud'in da nike samu na albashi naci gaba da ginin gidan nan har yanzu ya koma haka,to Hajiya Fatuu yar Jarida,yanzu kinji komae ko?"
Kyalkyacewa da Dariya fatuu tayi tace"Amman wannan matar Dr din shegiya ce,daman kin Aure shin muga yadda zata yi,Oh da yanzu muna gidan Dr shine kakana kuma kinga da cikin sauki zai taimaka man in zama likita,Allah ya isa na matar Dr",Dariya gwaggo tayi tana girgiza kai jin shirmen fatuu"bana hana ki zagi ba,ni sam banga laifinta ba wllh kishi take akan mijinta ba wani abu ba,duk da hakan bai hana ayi mata kishiyoyin ba har ma guda biyu,yana nan yanzu shi Medical Director ne",
Fatuu tace"Allah ya kara,yasa ma ya cike ta hud'un",girgiza kai kawae Gwaggo tayi,
Hannu fatuu ta kai ta shafo kanta da sauri tace"Gwaggo ya naji kamar kina man kitso kuma",
"Eh wai in rage hanya,bana fulani kika ce kina so ba,na gaban ne nike yi maki goben in Allah ya kaimu sai in k'arasa maki",kai fatuu ta daga alamar toh,
Shiru sukae na wani lokaci kafin fatuu tace"Gwaggo kinsan Yaya Handsome?",
"yaya Handson kuma wani abu ne hakan?" gwaggo ta tambaya,kyalkyacewa da dariya tayi"kai gwaggo mutum ne fa,d'and'an Hajiyar Sanata nike nufi fa" ta6e baki gwaggo tayi"Haisam dinne wani handson,kuma waya fad'i maki d'and'an Hajiya ne,ke ko fadi maki akae ita ta haife shi kya yarda,Jikanta ne,Senator d'in da kika ji ana cewa shine d'an hajiyar shikuma Haisam d'an Senator dinne",waro ido fatuu tayi"haba ashe shiyasa kwata kwata basu kama,ni wllh dana ganshi zaune Agidan nayi zaton danta ne ashe anko muka yi dashi shima kakarshi ce ita",
"Itama Hajiya yaranta biyu a Duniya,amman ita ba kamar ni ba tana haihuwar kawae tana samun matsala ta yawan 6ari,wani cikin kuma inta samu har sai ta haihu sai d'an yazo ba rai,to daga baya ma sai aka juya mata mahaifar kawae,Shi Senator d'in shine babban d'an hajiyan daga shi sai Hajiya Maryam tana lagos tana aure Bature ne take aure,Allah cikin ikonsa su duk suna haihuwa sosae shi Senator Ali bansan ainihin yawan yaranshi ba,amman ita hajiya Maryam din tana da yara biyar yanzu,yaranta tubarkallah suma kaman turawan suke don duk farin ubansu suka daukko ga gashi kwayar idanunsu kala daban daban,da suna yawan zuwa amman yanzu sun rage zuwa ita Hajiyar ke zuwa can ta d'an kwana biyu......",
Cike da mamaki fatuu tace"Bature mai jan kunnuwa,Gwaggo ina ta same shi har ta aure shin?",
"Oho bansani ba,amman kya iya zuwa ki tambayi hajiyan"cike da gatse tayi maganar,
"To shi Yaya Handsome d'in Gwaggo waya biyo ne,naga shima kalan yan kasan waje ne",
"Senator Ali mai Kud'in gaske ne,Don a yadda naji yafi duk wani Senator d'an Arewa kudi,yana da kamfanoni iri iri har a kasashen dake makwabtaka damu,yana da gidajen Mai,da kamfanonin saida Motoci,Wanda wasu ya gaje sune daga Mahaifinsa,Mahaifiyar Haisam ba yar nan kasar bace Asalinta yar kasar Ethiopia ce...." katseta fatuu tayi"Wace k'asa ce kuma Ethiopia Gwaggo?",
"Kasar Ethiopia tana a cikin nahiyar Africa,kinsan akwae nahiyoyi bakwae a Duniya,Akwae Nahiyar turawa,Larabawa,Indiyawa....." da sauri Fatuu ta katse mata hanzarinta"Continent ake cewa gwaggo an yi mana shi a Makaranta guda bakwae ke akwai",
"Yauwa to Contilet d'in..." wata Mahaukaciyar Dariya fatuu ta saki"kai Gwaggo wayace maki Contilet yake,kalli bakina kiga yadda nike fad'i,CONTINENT" ta dashe
baki tana nuna ma gwaggon,
d'an guntun tsoki taja"to ban fad'in yadda kike cewan ki kyale ni da yanda na iyan" Fatuu dake ta dariya tace"Aikam wllh in turawa suka ji ki garkameki zasu yi a gidan yarin kasan teku kije kita cin gabza",
"Tunda Sarauniyar Engila na zaga ba" gwaggo ta fad'a fuskarta ad'an daure,
"To ci gaba kice Contilet d'in..." a harzuke gwaggo tace"banci gaban",
"Haba Kakus,kinsan fa wasa nike don Allah kici gaba da bani labarin Yaya Handsome d'in" ta hada hannuwanta tana rokon gwaggon,
"Zanci gaba,amman wllh kika kara katseni na gama"d'aga kai fatuu tayi alamar ta yarda,
"Mahaifiyarshi Fateema Fulanin Ethiopia ce,yayin da Mahaifinta yake Balarabe wato Kakan Haisam din na wurin Uwa,a yadda Hajiya ke ban labari Aiki ne ya kaishi kasar Ethiopian har ya Auri Kakar Haisam d'in wadda yar sarauta ce acan,suka haifi Mahaifiyarshi Fateema wadda yan biyu ne su,Wani taron Yan kasuwa ne yakai Senator Ali kasar Ethiopian anan ya had'u da Mahaifiyar Haisam din,shi da Abokinshi suka Aure su ai na fada maki yan biyu ne su,Fateema da Zainab,ita Zainab d'in yanzu haka Mijinta shine Gwamnan Jahar Nasarawa,ita kuma Fateema tana Abuja Gidan Senator Ali,da farko kafin ya zama Sanata din anan Katsina suke zaune a G.R.A,nan yake da katafaren gida,Hajiya ta ce lokacin da ta dawo Katsina don da a Abuja take lokacin Mijinta na Minister a gidan ta fara zama,to lokacin da shikuma zai koma Abuja yaso ta Zauna a Gidan don tace bazata bisu Abujan ba Amman taki acewarta yayi mata girma,shine aka gina mata wannan wanda kusan rabin Unguwar nan duk filayenshi ne da ya saida ma mutane,Allah yasa ma Hajiya kaunar Haisam tunda aka haifeshi Wanda hakanne yasa ta roki abata shi har yayi Primary da k'aramar Sakandire awurinta acan Abuja kafin ta dawo nan ya karasa Secondary d'in anan daganan kuma ya tafi kasar waje yayi Degree dinsa na farko bayan ya gama bai dawo wurinta ba ya fara aiki a Abuja sai dae yana yawan zuwa daga baya ya sake fita wata kasar yayi Degree na biyu shine da ya gama ya dawo nan,to kinji game da Haisam din",ta k'arasa tana kallon fatuu,
"Ohh,yanzu nagane dalilin dayasa bai ceman Fateema kamar yadda Hajiyan ke kira na shi saidae yace man Zarah,ashe sunan Mamanshi ne" fatuu tayi maganar tana jinjina kai,
"To gwaggo wannan Sojan na d'akin Hajiyan waye shi??"
",
kai gaskiya fatuu na gaji da wadannan tambayoyin haba,wannan dama yar Jarida kawae kika zama,shi d'in Mijin Hajiya ne General Adamu Zakee,Asali d'an nan Katsina ne kuma Soja ne tun Zamanin turawa,bayan ya kai matakin janar yayi retire daga nan aka bashi Ministern tsaro wanda yana ruke da mukamin ne ya rasu Sakamakon had'arin Jirgin Sama da ya rutsa dashi anan kasar....."katseta Fatuu tayi"Allahu Aikuwa nasan lokacin da yayi hadarin wll....."bata k'arasa ba sakamakon bugun bakinta da Gwaggon tayi tace"in buge bakin mai karya kawae,Mutumin da ya rasu kusan Shekaru Goma Sha biyar yanzu shine zaki ce wani kinsan lokacin,ashe har yanzu baki daina wannan muguwar k'aryar ba",
Turo baki Fatuu tayi"wllh ba karya nike ba,nayi zaton sune suka yi wani had'ari da akace Jirgi ya fad'o a Yola" Gwaggo dake harararta ta ture mata kai"d'aga ni in tashi inyi Sallah anata kira,kinga naso ma ki daka man daddawa wllh gashi har an kira Sallah,yi sauri kiyi sallar sai ki d'an kwankwatsa man ita"Wani kallo Fatuu ta bita dashi ta cuno baki"kai Gwaggo,kai gwaggo,wai an gama hiran yan gayu kuma zaki wani ce a daka daddawa,maimakon kice inje in kama kaza daya a keji in yanka",
Ruke ha6a gwaggo tayi"Waye zai wani baki ki yanka masa kaza,ance maki na manta kazan da kika matsa kwanaki in baki ki yanka kika gutsire ma kaine,ba wata kazar da za'a yanka sai Azumi in Allah ya kaimu,Nama dae ai daidai gwargwado ina siyowa,kuma inma tuwo kike tunani zanyi to bashi bane taliyar hausa ce za'a dan 6ararraka"Lokaci guda Fatuu ta washe baki"Yauwa Kakus yanzu naji magana,ni zan dafa to",
"To tashi kiyi sallah sai ki dafan"da sauri ta mike jelar kitson da gwaggo ta fara yi mata nata reto agaban kanta ta saukko har wurin kirjinta.
Bayan sun gama Sallan a gefen kitchen ta fiddo Gas d'in ta fara dahuwar taliyan gwaggo dake zaune kan tabarma tana nuna mata yadda zata sa abubuwan,lokacin da ruwan ya tafaso gwaggo tace ta d'aukko taliyar a kicin,ta dibar mata wadda zata dafa,fatuu tace"ki k'ara Gwaggo zan kaima Hajiya" ba musu tace toh,sai dae acan kasan zuciyarta ba hajiyan zata kaimawa ba Haisam zata kaimawa,Tashin Sense,Mutumin da Hadaddan Abinci ma bai dameshi