Showing 27001 words to 30000 words out of 218703 words

Chapter 10 - Sakayyah 2 Hausa Novel Complete

tana da wanda take so, to bansan ya ake ciki ba dai. Ni dai tsoro na kaddai Nasseru take so?”.
Gyara zama Amina tayi tare da Girgiza kai kana tace.
“Ba dai Uncle Naseer ba Dan ko magana bata mishi, sai in shi ya mata, shima kuma baya mata magana sosai da nace masa bana so.
Sai dai ko ina wani can daban wayasan mata”.
Cikin jin daɗi Hajia Bunayya tace.
“Ato da sauƙi”.
Ita ko Amina gyara zama tayi tare da cewa.
“Uncle Naseer Kam yanzu ma wayar da muke yine, ya hanani fita.
Kuma cewa yayi anfara hada kayan lefe sannan kuma idan an tashi da kayan lefe da kayan gishi da goro da sadaki da kayan rufi duk za ahaɗa rana ɗaya za akawo”.
Murmushi Hajiya Bunayya tayi tare da Jinjina kai.
Ajiyar zuciya Amina tayi kana ta cigaba da cewa.
“Kuma yace nan da wata ɗaya za'a ɗaura Auren mu sannan ana gama bikin a Abuja zamu tare baza mu wuce wata biyu ba in yayi yawa ne uku zamu wuce India sannan zai nema min admission In cigaba da karatuna”.
Dariya Hajiya Bunayya tayi tare da ran gaɗa guɗa kana tace.
“Alhamdulillah burina ya cika haka nake son ji da ace mun na cewa batun wannan yaron Jameel gashi ƴan Kidnapping sun kashesa a wofi”.
Kai Amina ta gyaɗa tare da cewa.
“Ai dai kam Umma Allah ya rufa mnaasa asiri da na nacewa batun Malam Jameel da yanzu na zama matar Mamaci ina takaba”.
Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa tare da faɗin.
“Aikam Allah ya tsareki yaje can Allah ya jikansa da Rahma”.
Cikin sanyin murya Amina tace.
“Ameen dai tun da yana da kirki Allah ya jikansa Allah yasa ya huta amma dai na kama dahir dana kama Uncle Naseer”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Kin kama dahir kam”.
Asiya ce da bata cika shiga mgnar suba, tunda Hajia Bunayyah tace mata zata tsine mata in tana damunta da batunsuji tsoron Allah, a hankali ta ninke hijabin da tayi salla dashi tare da miƙewa ta fito falo tana maiyi musu addu'ar shiriya.
Ita kuwa Amina da baki ta nunata.
Shashar uwa sai dariya tayi.
Suna cikin hiran wayar Hajiya Bunayya ya hau ruri tana dubawa taga Hajiya Lami cikin sauri tayi Picking tare da kaiwa Kunnenta Hajiya Lami najin tayi Picking batare da tayi Sallama ba ta fara kora mata jawabin abinda Samira ta faɗa mata.

Zare ido tayi cike da damuwa tace.
“Subhanallah toh Meyesa haka?”.
Cike da damuwa Hajiya Lami tace.
“Ban saniba amma ki shirya da daddare bayan sallar Isha'i ki rakani”.
Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh nima zanje dama in Faɗa masa maganar Amina don tuni anfara hada kayan lefe, Gishiri, Goro, kayan rufi, da sadaki duk lokaci ɗaya za'a kawo kinga hankali ya kwanta”.
Jinjina kai Hajiya Lami tayi tare da faɗin.
“A hankali ya kwanta kam bari sai nazo ɗin dai”.
Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa kana tace.
“Toh sai kinzo ba komai ki kwantar da hankalin ki”.

Aɓangaren Innayi kuwa har maghariba bata ji motsin Moddibo ba sosai hankalinta ya sake tashi.
Wunin ranan yini tayi tana kuka wanda lokaci ɗaya zazzaɓi ya kamata baki daya tunaninta ya ta allaka akan idan ta mutu ya Moddibo zai kasance awannan gari ya zaiyi.
Wasa-wasa har aka Idar da maghariba da Isha'i har misalin goma ba Moddibo ba labarinsa cikin sanyin jiki da tashin hankali ta miƙe ta nufi sashen sa tun kafin ta ƙarasa hawa barandar ta jiyo sheshsheƙan kukan sa cikin sauri ta ƙarasa hawa barandar tare da Murɗa Kofar falon tashiga kan Sallaya ta hangosa yayi Sujjada yana sheshsheƙa.

Cikin sauri ta zauna gefensa Muryanta na rawa tace.
“Subhanallah haba, Aliyu!, Haba Aliyu!!. Meyesa haka Aliyu ka ɗauki dangana mana kuka shine abinda zakayi ta raka Jameelu dashi arayuwar ka wannan soyayya itace zaka nunawa Jameelu kenan?”.
Anutse ya ɗago daga Sujjada tare da yin tahiya kana yayi sallama yana sheshsheƙa kana ya daga hannunsa biyu sama cikin raunin murya yace.
“Ya Allah Ubangiji kasa mafarki nake, Allah kasa in farka daga wannan hautsinennen mafarkin da nakeyi”.
Ahankali Innayi ta matsa kusa dashi tare da Kallonsa cikin sanyin murya tace.
“Haba Aliyu Meyesa kakeyi yin haka? ka kwantar da hankalin ka babu abinda ya gagari lamarin Ubangiji”.
Domin Ita batasan cewa yaji maganar da sukayi da Hajja Nana ba.
Ahankali ya ɗago idanunsa da suke kada sukayi jawur tamkar garwashi cike da mamaki take kallon yanda idanunsa suka sauya launi Muryanta na rawa tace.
“Aliyu lafiyar ka kuwa?”.
Kai ya Girgiza tare da cewa.
“Bakomai”.
Ya faɗa tare da lumshe Idanunsa domin ya rasa ta yaya zai fara tambayarta shin inane asalinsa shin waye mahaifinsa su waye ne tushensa, yanaso ya tamyan amma ya najin tsoro da fargaba da taraddadin ya tambaye, ya zama cewa kalaman da Hajja Nana ta faɗa da kuma zarginsa na tsawon shekaru ya zama gaskiya hakan yasa yaji tsoron tambayarta kamar yadda ya saba, haka ya meda tambayar cikin ransa, sunkuyar da kansa ƙasa yayi.
Innayi kuwa cikin sanyin murya ta cigaba da rarrashin sa domin duk azatonta mutuwar Jameel ya tuna cikin rarrashi ta cigaba da cewa.
“Aliyu kayi haƙuri kowa da irin ƙaddarar da Ubangiji yake masa Addu'a zamu masa”.
Sunkuyar da kai Moddibo yayi hawaye ya cigaba da kwaranya daga Idanunsa.

Innayi kuwa cikin sanyin murya ta cigaba da cewa.
“Kada kayi kuka Aliyu ko wani irin matsala ka shiga arayuwar duniya kada ka butulcewa Ubangiji da irin wannan kukan, babu abinda zai kawo maka banda tashin hankali da damuwa”.
Ta ida maganar tana zubda zafafan hawaye, kukan abubuwa biyu ne suke haɗe mata alokaci ɗaya kalaman Hajja Nana da kuma halin da taga Moddibo aciki yayi masifar ɗaga mata hankali.
Anutse Moddibo yasanya tafin hannunsa yashiga share hawayen fuskarsa muryarsa na rawa yace.
“Toh shikenan Innayi nayi shiru dan Allah kema ki daina kuka Ubangiji Allah yarufa mana asiri”.
Cikin muryan kuka tace.
“Ameen ya Allah”.
Miƙewa tayi tare da fita ba daɗewa ta dawo hannunta riƙe da Warmers din abinci ta ajiye masa agabansa kana tace.
“Gashi kaci abinci”.
Kai ya Girgiza kana yace.
“A'a Innayi bazan ciba aƙoshe nake”.
Jinjina kai tayi tare da miƙewa ta dawo hannunta riƙe da wani bowl dake ɗauke da Fruit ta ajiye masa kana tace.
“Toh kaci wannan”.
Kai ya gyaɗa kana ya fara ci ahankali.
Ganin ya fara ci yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa.
“Toh sai da safe”.
Sannan ta fice domin bata da nutsuwa atare da ita.

Washe gari Da safe Ganin Moddibo bai zoba yasa Abba yashiga motarsa kai tsaye gidansu Moddibo ya nufa yana isa yayi Parking ya fito daga bakin gate ɗin farko ya tsaya yayi sallama Innayi dake Alwalan sallar Walha ta miƙe bayan ta ida ta nufi ƙofar tare da amsa masa Sallamar.
Bayan sun gaisa Abba ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.
“Dama Moddibo ne nake son ganinsa kuma bai zoba”.
Cikin sanyin murya Innayi tace.
“Hmm Moddibo ai jiya wuni yayi aɗaki yana kuka babu inda ya fita”.
Cike da alhini Abba yace.
“Subhanallah ni kuwa dama al'farma nazo nema Aliyu yamin taimako”.
ya ida mgnar cikin alamun neman al'farmar.
Haka yasa Innayi ta ɗan juyo ta kalleshi da kyau kana a hankali tace.
“Alhji Bashir ai ka wuce haka, kawai Umarni zakiywa Aliyu, kamar yadda kakeyiwa Jameelu da izinin UBANGIJI kuma zai cika maka umarninki. Aliyu ɗan ka ne, kadama kacemin komai kawai ka bashi umarni yamaka duk abinda kakeso ni kam na amince duniya da ƙiyama”.
Cikin jin daɗi kara da kawaicinta gareshi yace.
“Nagode da mutuntaka Allah ya bar zumunci”.
Amin tace tare da juyawa
tayi gaba.
Abba na bin bayanta zuwa falon Moddibo tsaye Abba ya gansa afalon yana ƙoƙarin fita.
Cike da ladabi yace.
“Ha'a Abba kazo ne?”.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Eh naga shiru-shiru Aliyu ba kazo ba tun jiya”.

Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da faɗin.
“Eh dama yanzu nake shirin fita zan biya ta gidan Ummi sannan na ƙara so wajenka”.
Ahankali Abba yace.
“Allah sarki to zamu tafi tare”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.
“Toh”,Sannan suka fita.

Cikin sanyi da
disesshiyar murya yace
“Abba na rasa ta ya zan gayawa Innayi batun
tafiyar nanfa”.
Juyowa Abba ya ɗan yi
ya kalleshi na second uku kana yace.
“Munyi mgnar da Innayi tace, babu matsala duk abinda ya dace in saka kayi min ta amince”.
Cike da mamakin amincewar tan yace.
“Ta yarda”.
Ka Abba ya gyaɗa mishi yana mai ci gaba da tuƙi.

Acan gidan Lamiɗo kuwa tun bayan tafiyar Hajja Nana Mommy ta fita sabgar Khausar da zaran ta gifta gefen da Mommy take Mommy zata kawar da kanta tare da dauke Idanunta akanta kana Uffan bata ce mata ba ko da safe da Mommy ke haɗa breakfast Khausar na shiga da niyyar tayata ta batare da tace mata Uffan ba ta nuna mata hanyar fita cikin rauni tace.
“Dan Allah Mommy kiyi haƙuri na tuba”.
Cikin fushi Mommy ta nuna mata hanyar fita ba tare da tace komai ba.
Da gudu Khausar ta juya tare da nufar Bedroom ɗinta tana shiga ta faɗa kan gado tare da fashewa da matsanancin kuka.
Haiydar ne yashigo falon jin sheshsheƙan Kukan ta a Bedroom yasa ya nufi Bedroom Cike da kulawa yace.
“Adda Khausi Meye sameki?”.
Ɗago Idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye tayi tare da Kallonsa tace.
“Haiydar Mommy fushi take dani”.
Cike da Mamaki yace.
“Fushi kuma? to me kika mata?”.

Kai ta girgiza still tana kuka tace.
“Nima ban sani ba amma Mommy fushi take dani”.
Ajiyar zuciya Haiydar ya sauke tare da cewa.
“Toh Addah Khausi muje kibata haƙuri kinji ko?”.
Nunfashi me zafi ta fesar tare da Kallonsa kana tace.
“Haiydar Ina tsoro”.
Kai ya Girgiza tare da sassauta muryarsa yace.
“Toh idan baki bata haƙuri ba so kike tayi ta fushi dake?”.
Be jira cewar ta ba ya riƙo tsintsiyar hannunta suka fita, ganin Mommy bata falon yasa suka nufi kichen still Nan ma bata nan kai tsaye Bedroom ɗinta suka nufa zaune suka sameta abakin gado da alamar bata daɗe da fitowa daga wanka ba ta gama shiryawa tana ɗaure yalwataccen sumar kanta da Ribont.
Tsugunna wa Haiydar yayi agabanta tare da jan hannun Khausar itama ta tsugunna cikin sanyin murya da neman yafiya Haiydar yace.
“Ayyah Mommy dan Allah kiyi haƙuri Addah Khausi tace kinyi fushi da ita tun jiya bakya mata magana”.
Kallonsu Mommy tayi tare da kawar da kanta gefe Khausar kuwa da hawaye ke kwaranya daga Idanunta yayin da kanta ke ƙasa.
Miƙewa Mommy tayi kana ta cigaba da shirinta ba tare data tanka suba ta ɗauki turare ta feshe jikinta.
Cikin sanyi Haiydar ya mike tare da ƙarasawa gaban Dressing mirrow ya durƙusa kana Cike da ladabi yace.
“Dan Allah Mommy kiyi haƙuri Idan akwai abinda tayi miki mu baki haƙuri”.
Banza Mommy tayi dasu ta cigaba da shirinta.

Cikin raunin murya da tsanananin tashin hankali Khausar ta shiga Girgiza kanta tana sakin kuka, kana Idanunta na zubar da hawaye Shar-shar muryanta na rawa tace.
“Dan Allah Mommy kiyi haƙuri ki yafemin, kinsan fushinki masifa ce agareni”.
Uffan Mommy bata ceba ta koma bakin gado ta zauna cikin sanyi jiki Haiydar da Khausar suka bita da rarrafe suka durƙusa a gabanta, ido ta zuba Khausar tana kallon yadda take kuka,
Ita kuwa Khausar ta kasa ɗago kanta, sai hawaye dake cigaba da zuba shar-shar.
Cikin muryar dake nuna ɓacin rai Mommy tace.
“Toh Kuma kukan me kike yi bayan kinyi abinda ranki keso.
Ai dariya ya kamata kiyi tunda har kin kai matsayin zaɓawa kanki miji, kin iya fetsare idanu gaban manya kice ke ga wanda kikeso. kin jamin tashin hankali da zagi awajen kakarki”.
Haiydar kam ido ya zubawa Mommy don bai taɓa ganin tsananin ɓacin ranta irin na yau ba.
Mommy kuwa cikin fushi ta cigaba da cewa.
“Tsohuwar da kinsan ba kirki da kara bane da ita, ta fita tsakiyar gida tana min ihu da haushi tana tara min mutane, Kina sane da cewa duk abinda kika yi laifinsa kaina yake dawowa, sannan duk abinda kikayi Ni bansan dashi ba bansan yaushe kika tsara ba ban isa ki gaya min sirrinki mu biyuba sai kin bari a tsakiyar mutane”.
Ajiyar zuciya Haiydar ya sauƙe tare da cewa.
“Dan Allah Mommy me tayi miki ne?”.
Cike da ɓacin rai Mommy ta kalli Khausar kana tace.
“Ai ita tasani ta faɗa maka me tayi”.
Ahankali Haiydar ya juya tare da kallon Khausar yace.
“Addah Khausi me kikayi?”.
Kallon Mommy Khausar tayi Muryanta na rawa tace.
“Dan Allah Mommy kiyi haƙuri?”.
Girgiza kai Mommy tayi babu walwala atare da ita tace.
“Toh me kike nufi da kalmar da kika faɗa?
Kince ba kyason Naseer na gamsu domin Ni kaina bana son Naseer tunda nasan abinda ke tafiya, sannan na fahimci yanzu Ameena yake so”.
Kuka kawai Khausar keyi Allah ne kaɗai yasan me take ji aranta.
Mommy ta cigaba da cewa.
“To amma shi Aliyu Meye lefinsa ɗan uwanki ne sannan zai riƙe da amana da gaskiya kamar yadda ya riƙe yar uwarki. Baffanki bazai bari ya to zarta kiba sannan kinzo min da wata magana wai Moddibo kike so ko kunya baki jiba”.
Ahankali Khausar ta ɗago kanta kana ta rumtse idanunta dake zubar da hawaye Muryanta na rawa tace.
“Mommy dan Allah kiyi haƙuri abar batun Yah Aliyu ayi batun Aurena dashi Mommy wlh ni Moddibo nake...!




Ikon Allah sai kallo wai fa Modibbo takeso.

*Littafin SAKAYYAH dai na kuɗi ki biya ki karanta cikin Aminci yafi ki karanta na sata kuma na Allah ya isa, 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Sai in tura miki littafin*


By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2 page 6*
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

*Alamomin infection sune kamar haka*. Rashin sha'awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni'ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al'ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban lissafa. Sune manyan alamomin infection.
Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.
Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni'ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin yana kwaranya. Zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.
KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA sai ya gama yi miki illah. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni'imomin ki, da sha'awarki, duk kyan kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA'AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau, duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha'awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor's suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin sherrin chronic infection ne yar uwa.
INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi'izinillahi ta'ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa dole kema ki nace masa da maganin mu, set ɗin10k ne kuma maganin kala biyarne nasha kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin indai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma'ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya'ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba dan kun kai mishi amarya a rarake bayan kun san kuɗin sadaki ya ƙara sama. Saboda yanayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi a 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER'N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA'AURATA.


Cikin yanayin ɓacin rai Mommy ta ture kanta dake kan cinyar ta babu walwala atare da ita tace.
“To ai shikenan Khausar hankalinki ya kwanta, zagine da abin kunya kunja min, kukan me kuma zaki zo kina min, in banda rashin hankali dama rashin kunya Khausar yaushe Moddibo yace yana sonki yaushe Moddibo ya taɓa zuwa wajenki?”.
Kasa cewa komai Khausar tayi sai hawaye dake cigaba da kwaranya a Idanunta Shar-shar.
Cike da takaici Mommy ta cigaba da cewa.
“Mutumin da ko Amakaranta tsakaninki dashi sai dai faɗa kyara da hantara. Duk abinda ke faruwa ina sane ai ana bani labari amma saboda tsabar shashanci ki rasa wanda zaki ce kina so sai mutumin da bakwa zama inuwa ɗaya!”.
Kuka sosai Khausar ta fashe dashi cikin sheshsheƙan Kukan tace.
“Wallahi Mommy ba haka bane dan Allah ki tsaya ki saurareni”.
Kai Mommy ta Girgiza tare da tsira mata Ido tace.
“Hmmm Khausar kenan me zan saurara kuma, ai babu abinda zanji daga gareki tunda ke kika haifi kanki ke zaki yankewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login