Showing 63001 words to 66000 words out of 218703 words

Chapter 22 - Sakayyah 2 Hausa Novel Complete

Office ɗin Dr Jameel ya nufa yana isa yayi Knowking ahankali idanunsa suka sauƙa akan Dr Jameel dake tsaye Atsakiyar office Rungume da wata Norse Yana kissing din sassan jikinta cikin sauri ya runtse Idanunsa tare da faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakin,J wai wani irin sauyi ne yazo maka arayuwar ka”.
Yayi mgnar cikin cushewar tunani duk da ɗabi'in wanda ake kira da Dr Jameel suna bashi cikekken yaƙinin cewa ba J dinsa bane wannan tsananin kamanceceniya ne. Toh amman kamanin da hatta muryarsu mgnar tafiyarsu komai iri ɗaya ne da na J ɗinsa yasa ya kasa amincewa kansa cewa ba J ɗinsa bane wannan.
Cikin fushi Dr Jameel ya ɗago kansa ya kalli Moddibo kana yace.
“Wai kai wani irin mutum ne tunda nace maka ba J ɗin da kake nema bane ka barni mana Meyesa zakayi ta bibiyar rayuwata?”.
Cikin sanyi Moddibo ya kallesa kana yace.
“Kaji tsoron Allah J! Shin wace irin rayuwa kasa kanka aciki J!? J mata ka fara bi ka maida kanka kamar kare wanda baisan abinda yake ba J yada ilimin ka zaka maida kanka haka cikin fushin Ubangiji kake so ka faɗa”.
Cike da ɓacin rai Dr Jameel ya juya ya kallesa kana yace.
“Anyi ɗin idan kana da iko ka hana nace maka Ni ba J ɗin ka ba kabarni inji daɗin rayuwata mana, jikinka ko jikina rayuwarka ko rayuwata matane dole in bisu inji daɗin rayuwata yoh akwai abinda ya kaisu daɗi ne”.
Cikin takaici Moddibo yace.
“J baka ji tsoron Allah ba da bakinka kake jaddada min aikin ka cewa zina kakeyi?”.
Harara Dr Jameel ya watsa masa cike da gadara yace.
“Anyi ɗin”.
Dafe kai Moddibo yayi tare da faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.
Cike da takaici Dr Jameel ya fisgo Norse din Wacce da alama ba musulma bace yana janyota ya manna bakinshi da nata.
Cikinta sauri Moddibo ya runtse Idanunsa da ƙarfi ya kifa kansa da jikin bango yana karanta duk wata addu'a da tazo bakinsa cikin sauri ya juya ya fita cikin motarsa ya zauna kasa tabuka komai yayi sai hawaye dake kwaranyo masa cikin ransa yace.
“Na gamsu wannan ba J na bane haƙiƙa ba Jameel ɗin Ummi bane.
Amman wallahi nayi al'ƙawarin in Sha Allah, zan gyara masa rayuwarsa da yardar Allah zai zama tamkar J dina na baya in sha Allah zaici albarkacin kamaninsa da J ɗina”.

Dr Jameel kuwa bayan sun gama aikata masha'arsu da wannan Arniyar ya shiga toilet yayi wanka yana fitowa yaji wayarsa na ringing Yana ɗaga wayar yayi Picking tare da kaiwa Kunnensa cike da girmamawa yace.
“Hello Unclee da kanka kuma?”.
Shiru yayi na wasu sekonni sai kuma yace.
“Toh shikenan ba matsala yanzun nan kuwa ganin zuwa.
Yana katse kiran ya gyara rigarsa tare da gyara zaman Necktie wuyansa.

Juyawa yayi ya kalli Norse din cikin bada umarni yace.
“Idan kin gama ki gyara min office ki rufe”.
Cike da yauƙi tace.
“Ok sir”.
Yana fita yashiga motarsa yaja.

Cikin sauri Moddibo dake zubda hawaye yabi bayansa duk inda ya juya akalar motarsa nan Moddibo yake bi shi kansa Moddibo baisan inda zaije ba kuma baisan me zaice masa ba, kuma baisan abinda zaiyiba.

Amman haka nan yaji wani irin amintaccen nitsuwa da salama a ranshi.
Haka nan yake jin farin ciki, tafiya mai nisa sukayi kafin suka wuce Sheikh Zayed hospital tafiya kamar na kimanin minti goma suka yi suka isa Fadar masarautar ƙasar Marocco baki ɗaya.
Ta cikin jahar Rabat suna isa Dr Jameel Yayi Hong ganin motarsa yasa aka buɗe masa gate ɗin.
farko yana shiga Moddibo ya mara masa baya tare da rumtse idanunsa da ƙarfi sabida harbawar da zuciyarsa tayi kamar zata haɗin ƙasa. Da sauri ya kuma buɗe idanunsa tare da sauƙesu can sama kan tambarin masarautar.
Lokacin ɗaya yaji jikinsa ya fara tsuma, kana duk tsikar jikinsa ta miƙe tsaye.
Da sauri ya kutsa kai cikin tare da bin Dr Jameel bamba to bamba yana shiga yaji zuciyarsa ta buga da Masifaffen ƙarfi wani irin tsuma yaji jikinsa nayi amaimakon yabi motar Dr Jameel da kallo sai ya kuma bin Cikin masarautar Da kallo daga kan dogon ginin zuwa shimfiɗeɗɗen kwalta da kuma yanda tsarin yake baki ɗaya ginin zagaye yake da bishiyoyin dabino ta ko ina masu tsawo, da sukayiwa illahirin ganinsa ƙawanya.
Ahaka suka isa wani babban gate Dr Jameel yayi hong aka buɗe masa yana shiga Moddibo ya mara masa baya.
Shi kuwa Dr Jameel sabida wayar da yakeyi yasa hankalin sa baya kai kan Modibbo ba.
Sassayyan numfashi Modibbo ya saukeganin yadda hadiman ke zirya da hidima.
Yayinda su kuwa
Fadawa da hadiman basuma ga fuskarsa amman a zatonsu tare yaje da Dr Jameel shiyasa basu hana shi shigaba.

Suna shiga gate na biyu suka isa dai-dsi kan wani RounAbout mai masifar kyau tsakiyar farfajiyar fadan. Yayinda hanyoyi guda huɗu suke zagaye dashi, kana gefe-da gefen ko wacce hanya bishi yoyin yan gajjerun dabino ne, masu ɗauke da yaya ringis a kai.
Kana tsakanin, wanda yake miƙe da ta inda su Modibbo suka fuskanta kuwa wani babban baranda ne wanda yake da staps goma sha biyu, a staps ɗin forko Hadimai ne, guda biyu gefen hagu da damansa, sai kuma a steps na shida suma hadi mai biyu sai ana sha biyu su kuma hadimai bibbiyu ne hagu da dama, wata babbar ƙoface mai kyan gani da daukar hankali da kuma taswirar manomi a cikin kekkyawar gona.
Daga nan cikin RounAbout ɗin kuwa a yalwace yake da shuke-shuke na dukkan samfurin kayyakin da ƙasar suke nomawa kasancewarsu manomane, daga tsakiya kuma
Mutun butumin wani ingarman Doki da linzaminsan cikin ado na ƙawa kasan dokin kuma zagaye yake da Grass Capet sai kuma mutum-mutumun mutane biyu da fatanya a hannunsu sai na ɗawisu a gaban dokin.
Sai kuma ƙanan tituna da suka rabu kusan kashi takwas da alamu duka cikin Masarautar yake daga saman RounAbout ɗin anrubuta Barka da zuwa Masarautar Mouley da Larabci.
Daga gefe Dr Jameel Yayi parking yana Parking ya fito shima Moddibo ahankali ya ziro ƙafarsa ya taka ƙasa, da sauri ya rumtse idanunsa tare da dafa ƙahon zuciyarsa sabida jin yadda tsikar jikinsa ya tashi yammm tamkar wanda aka watsawa ruwan ƙankara atsakiyar hunturun sanyi.
Cikin sauri Dr Jameel ya juya ya kallesa cike da mamaki yace.
“Yah Salam biyoni nan kayi bawan Allah Meyesa zaka bini har nan? Kasan inane nan kuwa? kasan meya kawo ni nan? kasan me nazo yi? Nace kama san ina ne nan kuwa? Nanfa ba cikin asibiti bane”.
Moddibo kuwa kasa cewa komai yayi saboda yanda tsikar jikinsa ke tashi baki ɗaya ya rasa yanda zaiyi sai kawai ya ƙanƙame jikinsa yana karkawar tamkar mazari.
Cikin sauri Dr Jameel
ya juya banyansu jin wata murya cikin karaji na cewa.
“Jama'a ku lura *Rinƙas* ya kunce ina Sarkin dawakai yake? *Rinƙas* ya kunce jama'a ku kauceeeeh”.
Cikin tsanani sauri fadawa da sauran jama'a dake zirya a tsakikar suka fara mannewa a jikin bishi yoyin dabinon domin sanin irin gagarumar illar da Rinƙas keyi a duk sanda ya kubce kuma babu mai iya sarrafa shi cikinsu sai sarki Dawaki ko Mai martaba Youseep Mouleey da kansa.

Moddibo kuwa jin yadda ake gudu da kuma ganin yadda kowa ke neman mafaka ne yasashi cewa *Rinƙas*
Yayi mgnar a fili a cikin ransa kuma ya kuma sake cewa.
“Rinƙas a na”.
Yayi mgnar tare da saurin juyawa sabida jin wani irin takun aukuwar ingarman doki lafiyeyye ya nufo kanshi gadan-gadan yana wani irin gigitaccen suƙuwansa da harba iska tare da barbaza gezan kwataccen dogon gashin dake kan wuyansa.
Gab-gagab Gab-gagagab Gba-gab, ya nufosa haiƙan ƙadaran.
Dr Jameel kuwa wani irin gigitaccen kara ya sake tare da artawa a guje, ya nufi kam ƙofar fadar.

Yayinda gaba ɗaya hadimai da bayi kuwa duk suka ɗaɗdaura hannayensu a kai tare da rumtse idanunsu baki ɗaya sabida gaba ɗaya sun gama sadaukarwa sai dai a dauke nuƙurƙushesshen gawar Modibbo.

Shi kuwa Modibbo juyawa yayi ya kalli gabas da yamma Kudu da Arewa na cikin masarautar gaba ɗaya jama'ar da ke ziryar duk sun manne da jikin bishiyoyin kai kace kadangarune.
Wanda ke gefen damansa ya kalla yadda ya zare ido tamkar zai fiddasu waje.
Bayanshi ya juya ya da sauri jin kukan wani mutun.
Da sauri ya juyo kan zaburarran dokin da yaji an kira da Rinƙas ɗin da yayiwa farin sani a mafarkansa.

Sai kuma ya kuma kallon dottijon da kallo ɗaya zakayi mishi kasan cikekken mahaukacine tubran.

Rinƙas kuwa wani irin gigitaccen haniniya da sukuwa mai bada sautin takunsa mai jawo hankalin mutane, yayinda daga can baya kuma mai gadin sashin dawakanne ke ihu da kururuwa tare da yin mgn cikin tashin hankali yake cewa Modibbo.
“Ka gudu! Nace ka gudu zai kasheka fa".
Sai kuma ya ƙara ɗaga murya tare da cewa.
“Sarkim Dawaki taimakon gaggawa”.

Dai-dai lokacin kuma Rinƙas yayi wani iri-iri haniniya tare da harbin iska kana ya baza gashin kan wuyanshi tare da zura ƙafafunsa na gaba suka tafi suuuwwwh kan Modibbo.

Shi kuwa Modibbo cikin tariyo yanayin da yake rayuwa da dokin a mafarkansa na tsawon rayuwarsa.
Ya ture hular kansa tare da girgiza kansa yayi yadda dokin yayi, kana ya saita ƙwayar idanunsa, cikin tsakiyar idanun dokin.
Tare da ɗaga tafin hannunsa na dama ya saita kan goshin dokin.
Wanda hakan ne kuma yasa dokin sakin wani hargitstsen haniniyar da saida ta ratsa kunnuwan tsarki da tawagarsa dake cikin fadar suna zaman yiwa Sarki Jabeer Nuruddeen Gwadabe sallama dan yau yake shirin komawa Nigeria.

Juyowa mai martaba sarki Youssef Muhammad Mouley yayi tare da kallon gefen da Sarkin Dawaki yake tare lunshe idanunsa wanda hakan kaɗai ya wadatar ya gane nufin Sarkin.

A can waje kuwa gaba ɗaya jama'ar idanu suka zubawa Modibbo da Rinƙas suna kallon sarautar Allah, shi kuwa Modibbo.
Lumshe idanunsa yayi tare da buɗasu cikin na dokin.
Wani irin ɗaga sawu sama dokin yayi alamun sarawa da kuma cikekkiyar sanayya yayi Modibbo, kana yayi ƙasa dasu a hankali ya manna goshinsa da tafin hannun Modibbo.

Shi kuwa Modibbo shafa sumar gaban goshin yayi tare da fesar da sassayyan numfashi.

Mutumin dake gefen sane yayi wani irin sake baki tare da furta Yah Salam.
Dan sai lokacin ya samu damar ƙarewa fuskantar Modibbo kallo.

Dokin kuwa cikin nuna alamun shaƙuwa da sanayya mai tarin yawa, ya rinƙa karkaɗa jelarsa tare da baza gashin wuyansa da sakin haniniya kana ya fara zaga Modibbo tamkar maiyin ɗawafi.

Shi kuwa Modibbo wani irin mataccen murmushi yake tare da jujjuyawa yana kallon duk inda dokin yayi.

Saida ya zagayashi sau uku, sai kuma ya dawo gabanshi.
A hankali ya sunkuyo haka yasa Modibbo sumbatar wuyan dokin.

Dai-dai lokacin kuma sarki Dawaki ya buɗe ƙofar fadan ya fito da sassarfa ya fara taka steps din.

Shi kuwa Modibbo ɗan buge goshin dokin yayi sai ga dokin yayi ƙasa a hankali ya kwanta tare da karkarɗa jelarsa alamun so yake Modibbo ya hau kanshi.

Ya ilahi ya mujibatda'awato. Yah Salam, shine kaɗai abinda gaba ɗaya al'ummar dake kewaye da bishiyoyin suka fara faɗa tare da sauƙowa suka nufo Modibbo.

Shi kuwa Modibbo gashin saman wuyan dokin ya kamo tare da ja,
Haka yasa dokin miƙewa tsaye cike da biyayya.
Shiko Modibbon a hankali ya lumshe idanunsa, sai kuma yayi gaba dokin na biye dashi tamkar raƙumi da akala.
Duk da babu linzami a wuyan dokin.

Shi kuwa Modibbo ido a lumshe ya juya gefen hagunsa ya fara tafiya yana mai kallon taswirar hanyar inda zaije ya ɗaure dokin na dawo masa filla-filla kamar yadda yake gani a mafarkansa.

Wannan al'amari yayi masifar sa mamaki da kaɗuwa a zuƙatan al'ummar waje.

Dr Jameel kuwa ido ya zubawa Modibbo.
Yayinda sauran Hadiman kuwa gaba ɗaya hannun suka rinƙa ɗaurawa a ƙirzansu suna ɗan ronƙofowa kaɗan sunayiwa Modibbo wani irin gaisuwar ban girma.

Sarki Dawaki kuwa cike da al'ajabi da ta'ajjudin ganin yadda wani ke sarrafa Rinƙas ban ya sani duk duniya shida Abualeey ne kaɗai ke iya sarrafa dokin wato sarki Youseef, ko Ibrahim Mouley baya matsowa kusa dashi, kana ya sani kusan mutum uku ya kashe a cikin masarautar.

Hakane yasa ya fara sassarfa, amman ina ya kasa iso Modibbo da dokin domin shima da sassarfan yake tafiya ganin dokin na sonyin sukuwa.

Kana gaba ɗaya mutanen kuma yuuuh sukayi suka bi bayan Sarki Dawaki domin al'ajabin wannan al'amarin.

Tafiya mai nisa sukayi kana Modibbo yayi kwanan gefen yamma nan ma tafiya mai tsawo sukayi kana suka ɓullo kan wani ƙaton farfajiya wanda a ƙalla dawakai sun kai ɗari uku zuwa huɗu ke wurin.
Duk inda ka wulga idonka iya ganinka dawakaine a wurin. Shi kuwa Modibbo wata yalwatacciyar hanya yabi tare da ratsa tsakiyar dawakan ya wuce.
“Iko sai Allah”. Mutumin nan dake ya shelanta tsinkewar Rinƙas da gudu ya nufosu tare da maɗaukakiyar mamaki a fuskantar.

Shiko Modibbon ratsawa ya rinƙayi har ya isa inda nanne tirken dokin. Ɗaureshi yayi kana ya juyo.
Juyowarsa kuwa itace tasa numfashin Sarkin Dawaki kusan ɗaukewa a fili yace.
“Yah salam”. Sabida ganin kamannin fuskantar Modibbo tayi masifar girzashi, kawai sai ya ɗaura hannunshi na dama kan ƙirjinsa ya ɗan rusunar da kai, yayinda gaba ɗaya sauran ma haka sukayi.

Shi kuwa Modibbo ratsasu yake a hankali tare da bin hanyar da bata nan ya zo ba, tafiya kaɗan yayi ya ɓullo kan fadar.
Wanda tuni wasu hadiman sun kuma maye gurɓin waɗancan da suka tafi wurin dokin.
Jiyo alamun takun mutanene yasa ya ɗan juyo, ainkuwa zugar tawagar da ya barine suke biye dashi cike da girmama.
Bai fahimci komaiba a cikin abinda suke mishi, kawai dai yana bin hanyoyin da ya saba gani a mafarkansa ne, hakan yasa ya fara taka steps ɗin.
Da sauri wanda yake bakin ƙofar ya tura ƙofar tare da sa hannun sa ɗaya a ƙirji ya ɗan rusunar da kai, ɗai hannun kuma yayi masa alamun bismlillah ga hanya ka shiga.

A hankali yake takun cike da kamala da haiba, ya kutsa kanshi cikin tamfatsestsen falo na al'farmar da ƙasaita. Wanda komai na cikinsa ja ne, sai ratsin baƙi, bisa alamu kalan tutar ƙasarsu ce.

Babban falone wanda a ƙalla zai iya ɗaukan mutun sama da ɗari.
Yana shiga Sarkin Dawaki na biye dashi a baya.
Da sauri ya kalli gefen damanshi jin muryar yaron nan da suka haɗu a jirgi na cewa.
“Alhamadullah Abeey kaga ga wanda nacema mun haɗu dashi a jirgi, mai kama da Ibrahim”.
Faɗin hakane yasa duk suka kalleshi sai kuma suka kalli inda yake nuna musu.
Da sauri wani Kekkyawan Mutun mai cikar haiba, kamala, haɗi da ƙasaita ya miƙe tsaye cikin shiga ta al'farmar dake nuni da shine Sarkin masarautar ƙasar Marocco.
Miƙewarsa tsayence tasa dukkan sauran mutanen kama daga Waziri, Galafima, Wambai, Ɗan Maliki, Sarkin gida, Sarkin fada, dama gyara kimtsi Sarkin zagi kab suma suka miƙe tsaye cike da zubawa Modibbo idanu tamkar zasu ɗagashi sama da idon.
Dr Jameel kuwa, muƙut ya haɗiye wani yawu mai haɗe da mmki dan jarabar neman mata shi bai barshi yayi wani tunani kan kamannin Modibbo da Ibarahim ba koma yace da kawunshi ba.
Sai kuma yace.
“Har nan”.
Moddibo kuwa Jabeer bin Jabeer daya dawo gabanshi yana miƙa mishi hannu ya zubawa ido tara da bashi hannun.

Shiko Jabeer jawoshi yayi har zuwa gaban Sarkin tare da cewa.
“Ganshifa ko makaho ne ya shafa fuskarsa ya shafa taka ko ta Ibrahim yasan wannan mallakinmu ne shi, Abeey ba dama na gaya makaba”.
Ya ƙare mgnar da kallon Sheikh Jabeer .
Shi kuwa Sheikh Jabeer wani Gwauron numfashi ya fesar tare da yiwa Ɗan aminin nashi nuni daya zauna.
Cike da kaɗuwa Sarkin Mouleey ya zauna kana yayiwa dukkan fada alamun su zauna.
Haka kuwa duk suka zauna.
Dr Jameel ne ya ɗanyi gyaran murya tare da rusunar da kai cikin ladab yace.
“Ayi min izini in tashi zan shiga wurin Didi in duba Rahman".
kai Sarkin fada ya gyaɗa masa tare da nuna masa hanya alamun yaje.
Cikin sauri Dr Jameel ɗin ya miƙe da tare da kamo hannun wani ɗan yaron da bazai gaza shekara gomaba yace “Muje”. Ya ida maganar tare da jan hannunsa suka juya zasu fita.
Da sauri Modibbo ya miƙe tare da bin bayan Dr Jameel.
Cike da mmki ya tsaya ganin fadawan da suka zagayeshi da sauri kana sunkayi mishi zobe tare da baza manyan rigunansu.
Suka tareshi baya iya ganin Dr Jameel.
Cikin sanyin murya yace.
“Yah haka Ku buɗe min hanya mana zan tafi”.
Da sauri ya juyo jin Muryar Sarkin Zagi na cewa.
“Gyara kimtsi bisa umarnin mai martaba kuyi mishi jagora sashi na musamman”.
Kafin ya fahimci mai kalaman Sarkin zagin ke nufi, sai ji yayi anja hannunsa ba tare da an cire ƙawanyar da ankayi masaba, yaji sun fara tafiya dashi.
“Ikon Allah wai na zaune ya daɗi".
Shine abinda yake faɗi a ransa yana mai ƙoƙarin ɗago kanshi sama, wai ko zai samu yaga gabanshi amman ina.
A hankali ya fesar da numfashi sabida tariyo masa da mafarkansa da kwakwalwarsa tayi masa.
Taku yaci gaba dayi da bin sawun Sarkin gida dake jansa wanda ta cikin ƙaton falon sukabi ta wata babbar ƙofa, tafiya mai tsawo sukayi kana yaji sun fara hawa steps jim kaɗan kuma yaji sun ɓulo ta wata kusurwar, ɗan gajeren tsaki yaja.
sabida jin tafiyarfa taƙi ƙarewa, kuma mutumin nan yayi mishi riƙon babban ɓarawo, ga ƙattin fadawa da suka zagayeshi.
“Toh wai me haka”.
Ya faɗa dai-dai lokacin da yaji, an ajiyeshi bisa wata ƙasaitacciyar kujera.
Sai kuma yaga duk sun janye ƙawanyar da sukayi mishi kana suka juya suka fita.
Da ido ya rakasu har suka je bakin ƙofa ga mmkinsa sai yaga mutumin nan da ya riƙo hannunsa yaja ƙofar da ƙarfi ya ruf....


Muje zuwa, wasa ya jiƙa, karatu dan aka biya kuɗin laranra Littafin yafi ɗadi ba haƙƙin kowa a kanki 1k ne fa kacal ki biya kada ki kiranta na sata 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER'N na 09097853276 ki biya in tura miki littafin ki karanta abinki cikin Salam kana in saki a Group ɗin littafin kusha comments,



By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 12*

Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*



*TSAYA! TSAYA!!! NACE ki TSAYAKO Sister's* duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login