Showing 60001 words to 63000 words out of 218703 words

Chapter 21 - Sakayyah 2 Hausa Novel Complete

yiba ba abinda ma ya haɗashi da likitanci”.
Yayi mgnar da cikekkiyar yaƙini da yarda da hakan sabida yanzu ya fara samun nitsuwa, ya gamsu kawai tsananin kamannine mutumin yake dashi da Jameel ɗinsa wanda hatta sautin muryarsu iri ɗaya ne da J dinsa.
“Yah Salam. Allah mai iko to waye wannan ɗin".
Yayiwa kansa tambayar da yake masifar son sanin amsarta”.

*Gembila*

Ɓangaren Asma'u da Khausar ma haka suka raba dare wajen hira har misalin ƙarfe uku suna zaune suna hiransu ta Aminai daga baya suka koma hiran makaranta wani abin idan sun tuna suyi dariya wani suyi murmushi musamman rigimar kwausar da Modibbo, rayuwa kenan shikenan rayuwar makaranta ta wuce kamar ba ayiba cikin murmushi Khausar ta gyara zamanta tare da kallon Asma'u kana ta ɗan tsuke fuska sai kuma tayi kasa da kai cikin juya murya zuwa irin ta Modibbo tace.
“Ke uwar rawar kai”. Sai kuma taja tsaki tare da cewa.
“Ko sunanafa baya kira wai ke”
Dariya sosai Asma'u keyi tare da riƙe ciki, ita kuma Khausar baki ta ɗan taɓa kana a hankali tace.
“Da jajayen lips inshi a wurin kamar balarabe da dunduniyarsa laushi kamar ta jariyai, gashin ƙeya kamar jikin Mage.”
Cikin nunata da yatsa Asma'u tace.
“Yah Salam ashe har haka akeson Ƴaƴana ban saniba”.
Harara ta watsawa Asma'u tare da cewa.
“Kamar yaya so”.
Tafa hannu Asma'u tayi tana faɗin.
“Toh fisabilillahi in ba soba mai ya kai hankalin da idanunki kan lips inshi harda ƙeyarshi duk yawan sa hulanshi, shin tukun nama ya akayi kika san dunduniyarsa da taushi, na shiga uku ashe Allah ya tsare bawan Allah da kin fyaɗeshi”.
Cikin kauda kai dan sai yanzuma taji kunyar kalamaanta a hankali tace.
“Ba wani nan kin dai san kawai ni ina son mai kyau, haka Allah yayini”.
Ta ƙare mgnar tana lumshe idanunta, a hankali ta buɗesu ganin yadda lips enshi ke motsawa in yana mata masifa.
Haka dai sukayi ta hira mafi akasari kan Modibbo ne yanayi tana kusheshi kushen da yake naɗe da cikekken yabon halittarsa da ɗabi'unsa.

Washegari da safe Misalin shaɗaya bayan sun gama yiwa Mommy Komai suka shirya suka tafi gidan Ummi suna isa suka samu komai fes-fes ta gyara har ta gama girki.

Ummi kuwa murmushi tayi ganin su yasa tace.
“Yawwa ƴan al'barka tun ɗazu nake son zamu tafi gidan Abban Jameel nida Innayi, kuma gidan shiru Bashir ya tafi sabgogin gabansa”.
Khausar na zama tace.
“Ai haka suke Ummi haka ma Haiydar shegen yawo ne da yaran nan”.
Kai Asma'u ta jinjina tace.
“Haka suke kuma idan mutum ya fita na minti biyar su riƙa cewa shine yake yawo.
Murmushi Ummi tayi kana tace.
“Yau ɗauki wannan Asma'u ki ƙaiwa Innayi yanzu na leƙa na samu tana walaha”.
Zare ido Khausar za tayi cikin sauri tace.
“Innayin tana nanne?”.
Da sauri Asma'u tace.
“Ai tunda Yah Modibbo ya tafi Marocco ta dawo nan”.
Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe ta koma ta zauna tare da faɗin.
“Au”.
Ahankali Asma'u ta jawo kular dake gaban Ummi tana buɗewa tace.
“Yau kuma mai akayiwa Innayi?”.

Kallon kulan Ummi tayi kana tace.
“Tuwo nayi mata nasan tanason tuwo”.
Kai Asma'u ta gyaɗa kana tace.
“Ayyah aikam dai”.
Ta ƙare mgnar tare da nufar ɗakinta da kular don nan innayi take.
Anutse Ummi ta maida kallonta kan Khausar cike da kulawa tace.
“Khausar”.
Cikin sanyi ta ɗago kanta tace.
“Na'am Ummi”.
Ido Ummi ta tsira mata kana tace.
“Ahaka za ayi zaman auren?”.
Khausar kuwa da sauri tayi ƙasa da kanta batare da tace Uffan ba yayin da hawaye ke cika mata kwarmin ido.
Ahankali Ummi ta sake kiran sunan da faɗin.
“Khausar”.
Shiru Khausar tayi sake kiran sunanta ta kuma yi.
Still Bata dagoba numfashin Ummi ta fesar tare da cewa.
“Khausar ɗago mana ki kalleni”.
Ahankali ta ɗago Idanunta dake cike da ruwan hawaye cikin sauri Ummi ta girgiza mata kai kana tace.
“Kar kiyi kuka Khausar insha Allah inaji Ajikina akwai al'khairi a alaƙarki da Moddibo Ubangiji Allah ya miki albarka”.
Cikin rauni da zubda hawaye ta amsa da Ameen asaman laɓɓanta.
Cikin rarrashi da son kwantar mata da hankali Ummi ta cigaba da cewa.
“Sai kuma batun tsoro ki daina mutumin da kike ƙoƙarin kasancewa ƙarƙashin inuwar Aurensa ai bai canci irin wannan tsoronba, shi ba Dodo bane Aliyu da kike ganifa yana da mutunci, Kara, tausayawa, da kuma karamci tsoron da kike nunawa akansa ya tsananta”.
Cikin sanyi ta girgiza kanta muryan ta na rawa tace.
“Ummi baki sanshi bane ba fa”.
Itama Ummi cikin sanyi tace.
“Nasan shi mana Khausar”.
Araunane Khausar ta girgiza kai cikin son Hana kanta kuka tace.
“Ummi baki san saba yana da mugunta fa”.

Kai Ummi ta girgiza kana tace.
“Ba zai miki mugunta ba Khausar in Allah yaso ya yarda Babana bazai miki mugunta ba saboda kin masa duk kan halarcin duniya”.
Lumshe Idanunta tayi cikin raunin murya tace.
“Ummi baya sona ya tsaneni koda kallon fuskatane baya so tunda muke tare Amakaranta da zaran mun haɗu zai nemi laifin da zai lika min kawai dan ya dake ni”.
Ta share hawayen da suka zubo mata cikin sanyi ta cigaba da cewa.
“Ummi ina tsoron rayuwa dashi sannan kuma Ummi ina so in cikawa Yah Jameel burinsa Ina so ciki wannan al'ƙawarin dana ɗauka”.
Ahankali Ummi ta matsa kusa da ita ta janyota jikinta ta Rungume cikin ƙarfafa mata gwiwa tace.
“Kar kiyi kuka Khausar! Kada jiki tsoro! Kada ki damu ki daina tsoron Babana babu abinda zai Miki”.
Ta ƙare mgnar dasa hannunta, amshi wayar Khausar tare da cewa.
“Yanzu bani wayarki in sa miki number's, ko kinada ita?”.
Cikin sauri ta jujjuya kanta.
Ita kuwa Ummi cikin kulawa yace.
“Toh bani wayar, in sa miki, yanzu dai kin san ke matar aurece, igiyoyin aurensa na kanki, banda yawan yawo, dukda dama nasan baku da yawan yawo".
Ta ƙare mgnar da fara sa mata number Modibbo dan wayarta ba pin, tana gama sa number's ɗin ta miƙa mata waya.
Amsa tayi tare da kife wayar bisa cinyarta. Ita kuwa Ummi da sauri ta kalleta jin tana cewa...



Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER'N na 09097853276. Kana in tura miki shi kisha karatunki cikin aminci.

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 11*

Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*


*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...._


🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,


Araunane tace.
“Ummi dukana fa yake sawa ayitayi kawai dan mugunta”.
Cikin sassauta murya Ummi tace.
“Khausar Rayuwar makaranta da ban, sannan rayuwar da zakuyi yanzu shima daban bazai da keki ba”.
Kai ta girgiza still Hawaye na bin kuncinta tace.
“Wallahi Ummi mugunune kobai dakeni ba, zai ta cin zalina, nasani koma mene zaimi. Allah zai saka min zan jure domin cikawa Yah Jameel Wasiyyar sa”.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauke cike da ɗan murmushi tace.
“Kada ki manta Shifa ba jahili bane yana da ilimi kuma shi Modibbo mutum ne da yasan darajar ɗan Adam. dan haka ki kwantar da hankalin ki, kinji ki daina jin tsoron dubi yanda baki ɗaya kika rame nasan harda maganar nan yasa kika rame to ki cire abin ki sa a ranki abokin ne yanzu bawai malaminki ba”.

Numfashi Asma'u dake fitowa ta fesar tace.
“Ummi haka jiya ma tayi ta kuka da daddare nima tayi ta sani kuka”.
Still tana jikin Ummi tace.
“Kada kiyi kuka ki saki ranki rayuwar inci zakije kiyi.
ki fara shirye-shiryen ki da zuciya ɗaya Insha Allah zakiyi al'fahari da wannan auren”.
Cikin tura baki tace.
“Ummi ni kuma wani shirye-shirye zan fara”.
Ɗan murmushi Ummi tayi kana tace.
“To ai dole kiyi shiri Khausar dudu yanzu saura kwana gomane dama abinda zai kaimu gidan Abban Jameel kenan”.

Zare ido Khausar tayi tare da dafe ƙirjinta tace.
“Kwana goma kuma Ummi da sauri haka dama dagaske ne?”.
Cikin murmushi Ummi tace.
“Dama da wasa kika ɗauka ne Khausar?”.
Kai ta girgiza tace.
“Bada wasa na faɗa ba Ummi amma kuma ai da anbari sai na gama karatuna”.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauke tare da riƙe tafin hannunta tace.
“Karatu zakiyi agidan mijinki Khausar kada kiji tsoro kinji ko munyi magana ma da Mommy ki kafin ki iso, akwai wasu kayan turarukan wuta dasu Humra da kullaca, da dai wasu abubuwa da na saya miki a wurin AYSHA ALIYU GARKUWA, in sha Allah nanda kwana biyu zata gama haɗa miki kayan zasu taho daga Adamawa, tam ce ta gama komai dahuwar kazane bata gama da kuma zuciyar farin rago su sabida da rubutu ake haɗasu”.
Shiru Khausar tayi batare da tace Uffan ba, sabida Allah ya sani batayi zaton da gaggawa haka za'ayi abinba.
cikin dabara Ummi ta riƙa kwantar mata da hankali tana mata nasiyya sai da taga ta nutsu kafin ta Miƙe da nufin shiga ɗakin innayi ta kirata su tafi.
Sai kuma ta gyara mayafinta juyowa jin Khausar na cewa.
“Ina yini”.
Murmushi tayi ganin innayi take gaisarwa, ita ma Innayin murmushi tayi ganin yadda Khausar ɗin ta sunkuyar da kanta.
Cikin kula da kauna tace.
“Lafiya lau kishiya ya gida".
Guntun murmushi dake iya sama lebe Khausar tayi tare da miƙe ta kama hannun Asma'u suka nufi kitchen.
Ummi kuwa ƴar dariya tayi tare da cewa.
“Yauwa Innayi tunda kin fito tafi ko”.
Gyara mayafi Innayi tayi tare da cewa.
“Eh muje”. Nan suka fice suka tafi gidan Abban Jameel a sabuwar motar da ya sayawa Ummi.

Asma'u da Khausar kuwa suka ci-gaba da hiransu.

Suna na isa gidan Abban ta samu Malam Arɗo bayan sun gaisa Malam Arɗo yace.
“Toh jiya da daddare Lamiɗo ya kirani yace biki za'a haɗa dana ƴar wajensa kuma sunce Jumma'a na sama nema suke so aɗaura auren kunga yau saura kwana takwas nema, toh yace za ahaɗa dana Khausar”.
Jinjina kai innayi keyi cike da gamsuwa Malam Arɗo ya cigaba da cewa. “Sannan mun gama tattaunawa da Abban Jameel akan ayi kawai agama tunda dama Jameelu yayi ta jaddadawa cewa ayi ƙoƙari ayi shi cikin ƙanƙanin lokaci”.
Gyara zama Ummi tayi kana tace.
“Sosai ma ayi kokari ayi haka shiya dace”.
Gyara zama Malam Arɗo yayi kana yace .
“Sannan Alh Bashir yace kada ayi masa batun Auren”.
Kai Ummi ta gyaɗa cikin gamsuwa, shi kuwa Abban Jameel gyaran murya yayi tare da cewa.
“Innayi kada a faɗa masa fa, dan so nake muyi mishi ba zata”.
Cikin gamsuwa Innayi ta jinjina kai tare da cewa.
“Ai kuwa bazata kam suna da yawa kuma ɗin kanku akwai bazatar da zan muku.
Tunda in an ɗaura auren kai mishi ita za'ayi ko?".
Da sauri Abba yace.
“Ni zan kai mishi ita”.
Murmushi Innayi tayi tare da cewa.
“A'a kada ka damu a gayawa dangin amarya su shirya yan rakiyar amarya da basu gaza goma”.
Da sauri Ummi ta juyo ta kalleta tare da cewa.
“A'a Innayi bafa ƙasar nan bane, har Marocco nefa, ya za'ayi ace har mutun goma ai ɗawainiyar zatayi yawa, wurin sauƙesu ma ai jidali ne”.
Cikin sauri Malam Arɗo yace sosai ma kuwa.
Abba kuwa ido kawai ya zuba musu.
Ita kuwa innayi gyara zama tayi cike da yaƙini da kuma tabbaci tace.
“Kada ki damu Ummin Jameel, ai tuwon girma miyansa nama, kuma in dai masauƙine koda Gambulan baki ɗaya zamuje bazata rasa masauƙiba. Kana kema zakije Asma'u, Abban Jameel Malam Arɗo, dama Lamiɗon kansa zaije”.
Murmushi mai cike da nazari Abban Jameel yayi tare da tuno abubuwan da Jameel ya gaya mishi akan tarihin Modibbo da yace Innayi ta bashi.
Cikin gamsuwa yace.
Kada ki damu Fatima a gayawa mahaifiyar Khausar a samu mutun goma daga gefen dangin kausar na uwa da uba da ni kuwa zan gayawa Lamiɗo”.
Kai kawai Ummi ta iya gyaɗa musu, domin abin ya bata mmki tunda Modibbo fa ya gaya mata kuɗin tickets insa na business class 1,303,000 suku tum toh fisa bilillahi wannan kudi ai yawa garesu ace kusan mutun goma.
Jin Malam Arɗo yace.
“Ai akwai economic tickets, kudinsa bazai kai hakaba ni dashi nake amfani duk inda nake zuwa”.
Jin hakane yasa ta gane ashe mgnar zuci da tayi ya fito fili.
Innayi kuwa kai ta jinjina tare da cewa.
“In sha Allah dai ba abinda zai gagara”.
Abba kuwa cikin nitsuwa yace.
“Kayan lefenta kuwa nasa matar aminina Dr Ahmad zata haɗa komai, wata ƙil ya iso kafin muje".
Da sauri innayi tace.
“A'a a barsu sai munje can mu haɗa ai tunda zamuje da zuriyarta duk zasu gani”.
Da sauri Ummu tace.
“Ayi haka kuwa innayi a tafi da amarya ba lefe, ai za'ayi ta surutai”.
Cikin jinjina kai innayi tace.
“Barsu suyi lokacin sune”.
Nan suka ci-gaba da tattaunawa yadda komai zai wakana.
Tun daga wannan rana suka fara shirye-shiryen biki babu kama ƙafan Yaro.

Aranan da daddare aka kawo kayan Auren Amina kaya sunyi kyau sosai su Hajiya Lami ne suka tarbi kayan Auren Bayan anwatse Amina ta kalli Samira dake gefenta tayi tagumi wacce baki ɗaya ta rame ta sauya ta dawo shiru-shiru.
Kallon Samira tayi kana tace.
“Samira wallahi da gaske kin fara wari dan ina jin warin”.
Cikin zubda hawaye Samira ta kalleta Muryanta na rawa tace.
“Allah Amina kina ji ko?”.
Kai Amina ta gyaɗa cikin gaskiya da tace.
“Wallahi Ina ji Amina sai kinji kamar warin Baragurbin ƙwai”.
Cikin raunin murya tace.
“Na sani dole za aji warin kawai Mommy na Idan na faɗa mata sai tace bata ji amma nasan dole za aji warin”.
Yamutse fuska Amina tayi kana tace.
“Gaskiya dai kam kina warin Baragurbin ƙwai wallahi ki dage ki koma wajen Boka ya baki magani”.
Kai Samira ta Girgiza.
Dai-dai lokacin Hajiya Bunayya ta shigo Harara ta watsawa Amina tace.
“Ke dai Wallahi Amina baki da hankali amaimakon ki kwantar mata da hankali sai ki ƙara tayar mata”.
Baki ta tura tare da kallon Hajiya Bunayya tace.
“Mommy wannan ba maganar tada hankali bane gaskiya ne kawai ku koma wajen Boka Kar'uzu yayi ƙoƙarin nemo mata magani”.
lokacin kuma Hajiya Lami ta fito daga toilet dake Bedroom din tace.
“Boka Kar'uzu har yau bai dawo ba daga tafiyar da yayi nima jira nake ya dawo Inje ko shekara jiya naje ban same shiba.
Cikin rauni Samira ta kallesu muryanta na rawa tace.
“Ni dai da an haƙura da neman Magani awajen Boka Kar'uzu kawai anema min maganin Islamic medicine ko Allah zaisa adace”.
Atare Hajiya Bunayya da Hajiya Lami suka ce me kike faɗa haka ki dai bari asake gwadawa agani.
Shiru tayi ba tare da tace musu uffan ba.

*Morocco*

Motar Moddibo ce tsaye abakin Mouley Yussef Hospital Rabat kusan kullum sai yazo amma da zaran security dake bakin gate din ya ga shine zai ki buɗe masa yau kwana biyu kenan yana sintirin zuwa cikin sanyi jiki ya juya ya koma gida yana so ya faɗawa Abba to amma ta ina zai fara faɗa masa zaice Jameel ɗinsa ko kuma yaya zuwa wannan lokacin hankalinsa ya gama tashi ya rasa shin wani irin tunani zaiyi cikin wannan tunanin ya koma gida.
Washe gari: alhamis haka ya tashi cikin matsanancin kasala saboda yanda aka kwana ana zuga ruwan sama gari yayi sanyi cikin damuwa da ciwon kasala da jin bugun zuciya ya kwana adaddafe ya tashi ya shirya kai tsaye Company ya nufa ya dudduba aikin da akayi zuwa yanzu gaba ɗaya angama daddasa Injinan da za ayi aiki dasu alissafinsu Insha Allah ranan Monday za afara bubbuga Nauikan, Abaya, Laffa, Jallabiya, Sallayu, blankets, Jakankuna, takalma za a cigaba da sarrafa kaya.
Kai tsaye motarsa ya shiga har ya nufi gida sai kuma ya sinci kansa da juya alamar motarsa kai tsaye Mouley Youssef Hospital Rabat ya nufa yana isa bakin gate ɗin dai-dai lokacin da security ya buɗe wa wata mota gate wannan damar Moddibo ya samu yayi saurin cinna hancin motarsa ciki.

Yana isa yayi Parking security na ganinsa yace.
“You again”.
Iya abinda ya iya faɗa kenan domin haiba da ƙwarjinsa yasa ba zai iya korinsa ba cike da nutsuwa Moddibo ya nufa cikin reception duk ido mutanen da Norses ɗin suka zuba masa suna kallon baiwar kyau nutsuwa da kamala da kuma ƙwarjini da yake dashi.

Kai tsaye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login