Showing 189001 words to 192000 words out of 218703 words

Chapter 64 - Sakayyah 2 Hausa Novel Complete

juya ta kalli Hajja Nana itama Hajja Nana kallonta tayi sai kuma ta juya ta kalli Moddibo cikin sanyi tace.
“Yah Mu'allim nace maka batun jikin Umma da Amina ayi musu addu'a sannan ka turo Dr Jameel yazo ya duba su amma Yah Mu'allim har yanzu baka ce komai akai ba”.
Ahankali Moddibo ya dafe kansa da hannunsa na hagu yace.
“Wallahi na manta, koyie haƙuri mantawa na keyi Minha”.
Kamar za tayi kuka tace.
“Yanzu fa kaji abinda Asiya tace”.

Hajja Nana da batasan meke faruwa ba ta kalli Khausar tare da cewa.
“Meke damunta?”.
Cikin rauni Khausar tayi ƙasa da kanta kana ta kwashe labarin duk yanda ta faɗawa Moddibo ta faɗawa Hajja Nana.

Ajiyar zuciya Hajja Nana ta sauƙe tare da jinjina kanta tace.
“Ai dama haka duniya take idan kace tukunyar wani bazai tafasa ba naka ko ɗumi bazai yiba arayuwa ka taka ahankali kada ka shiga hurumin da bana kaba duk lokacin daka shiga hurumin da bana kaba sai ka samu abinda zai shiga huruminka”.
Araunane Khausar ta risinar da kanta Hajja Nana kuwa cikin jimami ta cigaba da faɗin.
“Ya hanaka zaune ya hana ka tsaye yanzu wa gari ya waya ita wancan ta haukace ƴarta ta zama mai wari ita gata nan ƴarta ta zama wata halitta daban gashi ita kuma yanzu ƴarta tazo tana cewa tunda gari ya waye bata zauna ba ta isa ta zauna tsutsotsi na cinta”.
Ahankali Khausar ta rausayar da kanta hawaye na kwaranyowa daga idanunta tace.
“Hajja Nana Ni tausayi suke bani musamman Amina tana bani tausayi gaba ɗaya sai kinga yanda ta dawo ita ma Umman na ban tausayi bata isa ta zauna bafa Hajja Nana wlh ko jiya data shigo nan mu gaisa tsutsotsin har bin ƙafarta suke yi sai in taji kiga tana ta buge-bugen ƙafart kamar itama so suke su haukatata gaba ɗaya ”.
Cikin sauƙe numfashi Hajja Nana ta gyara zama tare da cewa.
“Dama haka duniya take”.
Still idanunta na zubda hawaye ta kalli Moddibo tare da faɗin.
“Ni dai ina so a samar mata magani ayi mata addu'a ane ma mata sauƙi awajen Allah”.

Acan Side ɗin Hajiya Bunayya kuwa Momy na shiga ta sameta atsaye sai bubbuga ƙafa take saboda yanda tsutsotsin ke cinta yayin da Amina ke gefenta tana zazzaro harshenta waje.
Da sauri Momy ta ƙarasa wajenta ta riƙe hannunta kana tace.
“Yaya ki zauna mana”.
Kai ta girgiza cikin tarin damuwa tace.
“Ina Momyn Khausar bazan iya zamaba idan na zauna ji nake har cikin hanjina tsutsotsin suke ci suna gigitani na rasa yanda zanyi na cutar dake arayuwa gashi nima yanzu na samu abinda yake cutar dani na rasa yanda zanyi a rayuwata”.
Cike da tarin tausayinta Momy ta girgiza kai tare da faɗin.
“Bakomai in sha Allah zaki samu lafiya”.
Kai ta girgiza tana cigaba da buga ƙafarta kana tace.
“A'a nikam nasan na nemowa kaina abinda yafi ƙarfina Momyn Khausar ki yafe min ki cewa Khausar ta yafe min”.
Cikin sauri momy ta juya tare da faɗin.
“Ki kwantar da hankalinki Yaya bari naje na kira Lamiɗo yazo ya kai ki asibiti ”.
Ta ida maganar tare da nufar Side ɗin Lamiɗo.

Cikin kiɗima tace.
“Wallahi Lamiɗo Yaya ce babu lafiya gaba ɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye ta kiɗime ta gigice ga Amina ma ita ma baki ɗaya yau jikinta nata abin ya sake motsa wa”.
Anutse Lamiɗo ya juya ya kalleta kana yace.
“Hmmm shine baki ɗaya kika gigice haka?, Mutanen dake suka cutar Sakayyah ce ta sauƙa akan su shine zaki gigice haka?”.
Kai ta girgiza kana tace.
“Nikam basu cutar dani ba kuma koda sun cutar dani na yafe musu Duniya da lahira”.
Gyaran murya Man Liman yayi tare da cewa.
“Wayene ba lafiya?”.
Zama Momy tayi muryanta ɗauke da damuwa tace.
“Uwar gidata ce babu lafiya Baffa Liman jinyan kuma ya kiɗima mu”.
Kai ya jinjina yace.
“Toh kunje asibiti ne?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Munje asibiti. Likitocin da kansu sunce bana asibitinba ne na gidane sai kaga yarinyar mijin da aka Aura mata ne bisa duk kan alamu tsafi yayi da ita ita kuma Yayan dai baza ka tantance ba”.
Zama Lamiɗo ya gyara kana yace.
“Ki daina cewa ba za'a tantance ba ki fito kice sihiri tayi Miki keda Khausar ya dawo kanta haka zaki faɗa masa ki fito fili ki faɗa masa abinda ta miki Saboda ko baki faɗa ba Allah ya sani kuma taga Sakayyar abinda ta aikata”.
Kai Momy ke girgiza masa shikam cikin tsanar Muguwar ɗabi'ar Hajiya Bunayya ya cigaba da cewa.
“Ita kuma Amina dama ai ƙulle ƙulle sukayi Ni kaina tsoron Al'amarin Naseer nake yi suka nuna dole-dole sai Naseer ya auri Amina yaje yayi tsafi da ita ya dawo da ita me zance musu su suka jawa kansu jiki magayi.
Ai dama sai dana ce duk abinda ya faru babu Ni aciki ba hannuna bare ƙafata aciki”.
Cike da nutsuwa Man Liman ya kalli lamiɗo tare da faɗin.
“A'a Lamiɗo baza ayi haka ba ai ita rayuwa rai da lafiya ita ake bibiya ake duban Lamarinsu kuma komai lalacewan Amina jinin kace tsatsonka ce kana Hajiya Bunayya komai lalacewan ta Matarka ce Uwar ƴaƴan kace”.
Da sauri ya girgiza kai yace.
“Uwar ƴaƴana ne babu yanda na iya amma Ni na saketa na saki Hajiya Bunayya tun wata ɗaya daya wuce Ni yanzu babu alaƙa tsakanina da ita na barta dai ta sauna a gida nane albarkacin Asiya da Sulaiman, taje can rayuwarta da ban rayuwata da ban”.
Mommy kam kallonsa take cike da matsanancin mamaki jin cewa ya saki Hajiya Bunayya ko kaɗan batayi farin cikin jin haka ba sai ma damuwarta ɗaya karu.

Man Liman kuwa cike da nutsuwa yace.
“Ai baza ayi haka ba yanzu idan babu matsala kayi min jagora muje in gansu Babu abinda yafi ƙarfin Ubangiji zanyi musu abinda Allah Ubangiji ya sanar dani”.
Kai Lamiɗo ya girgiza kana yace.
“Baffa Liman ka barsu baka san su bane”
Cikin rauni Momy ta kallesa kana tace.
“Dan Allah Lamiɗo kayi haƙuri ka taushi zuciyarka”.
Ahankali Lamiɗo ya ɗago ya kalleta kana ta girgiza kai ganin yanda ta tashi hankalinta yace.
“Kina jifa da bakinta tace ita tayi sihiri ta kashe Ramadan ”.
Cikin sauri Momy tace.
“Innalillahi wa'inna alaihi raji'un yanzu kai Lamiɗo sai ka yarda ita tayi sihiri ta kashe Ramadan?”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Ehem ita ta faɗa da bakinta ai ”.
Cikin sauƙe numfashi ta kalli Man Liman ta kalli Lamiɗo tace.
“Amma ka manta tun lokacin da Ramadan yayi accident an gaya mana cewa yana da brein Cancer tun lokacin daya karye ka manta cewa Likita ya faɗa mana kuma ko kai kanka kasan cewa ciwon kan da Ramadan yayi dare ɗayane sannan kuma an tabbatar mana da cewa ciwon ne ya kashe sa”.
Kai Abba dake gefe ya jinjina Momy kuwa cikin rauni ta cigaba da faɗin.
“Ko Sihiri da tace tayi Ni banyi Imani Sihirinta da tayi shi ya kashe min ɗana ba imma shine ya kashesa tsakaninta da Ubangijinta kuma ko cikina da take cewa ita tayi sihiri ya zube wallahi bata isa tayi Sihiri cikina ya zube ba face dama Allah ya ƙadarta waɗanan cikin bazan haifesu su taka doron ƙasa ba, shine kaɗai amma Ni bata isa ta kashe min ɗa ba bata isa zubar min da ciki ba wa'adin sa ne yayi”.
Cikin sanyi ta ƙare maganar tana mai zubda hawaye ta cigaba da cewa.
“Kuma ai ita in tayi zalunci mu bai kamata mu saka mata da zaluncin ba sai mu barta da Allah shi yasa Sakayyar da zaiyi mana”.
Jikin Lamiɗo ne yayi sanyi jin abinda ta faɗa sai kuma ya kalli Man Liman dake cewa.
“Kayi haƙuri muje mu dubata”.
Ahankali Yah Abba ya gyara zamansa tare dasa baki acikin tattaunawar su yace.
“Ayyah Lamiɗo ayi haƙuri adubasu ai rai da lafiya ake dubawa”.
Kai ya gyada tare da cewa.
“Shikenan”.
Momy ce ta fara miƙewa ta fita Lamiɗo na biye da ita sai kuma Man Liman da Yah Abba Abaya.

Suna shiga falon Hajiya Bunayya suka sameta atsaye sai bubbuga ƙafanta take tana tsalle ga ƴan mili-milin tsutsotsin nan na bin ƙafafunta yayin da Amina ke kwance kan 3sitter tana karkata kanta tare da zaro harshenta Man Liman na ganinta yace.
“Innalillahi wa'inna alaihi raji'un”.
Juyawa yayi ya kalli Hajiya Bunayya kana ya kalli Amina sai kuma ya sake juyawa ya kalli Momy tare da faɗin.
“Momyn Khausar akwai Zam-zam?”.
Kai ta gyaɗa tace.
“Eh akwai”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da faɗin.
“Toh ki temako min dashi”.
Da sauri tace.
“Toh”.
Kana cikin hanzari taje ta dauko Zam-zam Babban gora ta kawo karɓa yayi kana yace.
“Allah yasa kuna da ganyen Magarya ko ɗanye ko bushesh-she amma idan akwai ɗanye anfi buƙatar shi”.
Ajiyar zuciya Momy ta sauke kana tace.
“Alhamdulillah akwai ɗanye abayan window na adan kwai bishiyarsa”.
Cikin sauke numfashi yace.
“Toh Alhamdulillah aje atsinko akawo min”.
Cikin sauri ta juya taje ta tsinko ganyen Magarya ta kawo masa tana kawowa ya karɓa kallon Asiya dake kuka yayi kana yace.
“Asiya idan akwai sabon roba mai haske ki kawo min”.
Cikin sauri tace.
“Toh”.
Kana ta shiga kitchen ta ɗauko roba mai ɗan girma karɓa yayi yasa rabin Zam-zam ɗin aciki zama yayi ya Tofa Ayatul Shifaa gaba ɗaya aciki idan ya gama tofawa yasa ganyen Magarya guda bakwai aciki kallon Asiya yayi yace ta kawo masa karamin kofi cikin minti ɗaya ta kawo kofin ruwan addu'ar ya ɗebo ya bawa Amina yace.
“Karɓi kishi”.
Akarkace Amina ta miƙe tare da kauda kai gefe.
Cikin tausasa murya ya sake cewa.
“Karɓi kisha”.
Still juyawa tayi alamar bazata shaba.

Kallon Lamiɗo Man Liman yayi tare da cewa.
”A danneta Abata tasha”.
Cikin takaici Lamiɗo ya girgiza kai kana yace.
“Ta karɓa tasha sai adanneta ai jiki magayi lafiyarta ne ko lafiyanmu”.
Man Liman na gyara alkyabbarsa yace.
“Ayi haƙuri Abata ai sihirin da aka yi mata ne an haɗa mai tafiya da siffar maciji bayin kanta bane bazata sha ɗinba”.
Cikin rauni Asiya ta kalli Lamiɗo tace.
“Ayyah Abba don Allah Abata ”.
Ta ƙare maganar tare da karban kofin ta matsa kusa da Amina.
Amina na ƙoƙarin ture kofin Lamiɗo yayi saurin kama hannayenta kana ya rike kanta Asiya ta ɗura mata ruwan Tofi da ganyen Magaryan tasha mai ɗan yawa amma sauran ya zube.
Ahankali ta fara yin gyatsa lokaci ɗaya jikinta ya saki ta koma ta kwanta kan kujeran atake bacci ya ɗauke ta.

Tana yin Bacci Man Liman ya sauƙe ajiyar zuciya yace.
“Alhamdulillah tunda har tayi bacci in Allah yaso ya yarda zata rabu da abinda ke tare da ita amma wannan yaron da kuka Aura mata ya cika taƙadirin Jahili makirin mutum mushirki”.
Kai Lamiɗo ya girgiza tare kana yace.
“Su suka siyawa kansu”.
Cikin kuka da nadama Hajiya Bunayya ta durƙusa gaban Man Liman tace.
“Dan Allah nima ataimaka min mana abani abinda zansha inji sauƙi atemaka min”.
Kai Man Liman ya gyada yace.
“Ba matsala in Sha Allahu”.
Sai Kuma ya tsiyayi ruwan Zam-zam daban akofi yasa ganyen Magarya aciki yayi mata Tofi kana ya bata yace ta taune ganyen Magarya Zam-zam ɗin shi kai ta gyaɗa kana tayi kamar yanda yace tana gama yi taji kamar fitsari take ji cikin sauri ta nufi bedroom ɗin ta ta wuce Bathroom.

Man Liman kuwa kallon Asiya yayi tare da cewa.
“Idan ta farka wannan ruwan daya rage ta samu tayi wanka dashi awajen da babu najasa”.
Kai Asiya ta gyaɗa tare da faɗin.
“Toh In Sha Allahu”.
Yana kallon Aminan dake bacci yace.
“Kuma in sha Allah akwai tofin da zan mata amma da Zam-zam ɗin ne sai dai zai ɗauke Ni tsawon kwana biyu in sha Allah idan anyi shi in zamu zo daurin Auren su Jameelu zamu zo dashi da izinin Ubangiji zata samu sauki”.
Kai Asiya ta gyaɗa kafin cikin sanyi tace
“Umman mufa?”.
Ɗan gyara tsayuwar sa yayi kana yace.
“Toh bamu san mai Ubangiji zaiyi ba amma itama in sha Allah muna kyautata zaton Allah zai bata lafiya”.
Cikin sanyi da ɗan jin nutsuwa tace.
“Allah yasa mun gode”.
Nan Lamiɗo da Man Liman da Yah Abba suka fita.
Momy kuwa cikin jin sassauci tace.
“Alhamdulillah Amina ta samu sauki”.
Kai Asiya ta gyaɗa.
Momy kuwa ganin Hajiya Bunayya ta tafi daki yasa tayi zaton sauki ta samu tana kallon Asiya tace.
“Barin tafi ina da baƙi kinsan Hajja Nana nacan”
Cikin ƙaunarta da sake jinjina kyawun halinta Asiya tace.
“Toh Mun gode”.
Lamiɗo Man Liman da Yah Abba kuwa Side ɗin Lamiɗo suka koma...

Momy na shiga falon Moddibo ya mike kana yace.
“Toh Momy Ni zan wuce”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh mun gode”.
Khausar kuwa cikin sanyi ta kallesa kana tace.
“Dan Allah Yah Mu'allim kada ka manta Dr Jameel yazo ya duba Umma”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“In sha Allahu bazan manta ba Minha baza ki rakani bane”.
Kanta ta langwaɓar tare da ƙyafta ƙwayar idanunta ciki nasa sai kuma ta daura hannunta na dama kan ƙafarta tace.
“Ayyah kayi haƙuri baki ɗaya Ƙafafuna rawa suke”.
Lallausan murmushi ya sakar mata tare da motsa laɓɓansa cikin ƙasa da murya yanda ita kaɗai zata ji yace.
“Toh sai nazo da daddare”.
Kallonsa tayi da sauri tace.
“Me kuma za kazo yi da daddare?”.
Yana ɗan lumshe Idanunsa cikin nata yace.
“Bakyaso in kawo Dr Jameel ɗin ne?”.
Ahankali tace.
“Ina so mana”.
Kai ya gyaɗa yana gyara tsayuwar sa yace.
“Toh idan nazo kuma ki shirya zamu tafi tare”.
Langwaɓar da kai tayi tare da faɗin.
“Ayyah Yah Mu'allim ka barni in kwana mana”.
Kai ya girgiza tare da faɗin.
“Bazan iya ba dole fa yau zamu tafi muje mu kwana tare”.
Sake langwaɓar da kai tayi tare da marairaice fuska tace.
“Dan Allah Yah Mu'allim ”.
Cikin sauri ya ɗan tsuke fuska yace.
“Kada ma ki haɗani da Allah ki cuceni”.
Shiru tayi ganin kallon da Momy ke mata me nuni da alamun gargaɗi.
Shi kuwa Modibbo Hajja Nana ya kalla jin tana cewa.
“Idan Allah ya kaimu gobe ko jibi in ba matsala zamu tafi jahar Gombe muje kaga asalin masarautar su Khausar kuna mahaifarta”.
Cikin murmushi Khausar tace.
“Gobe dai zaifi dan Allah Yan Mu'allim kace gobe”.
Kai ya jinjina cike da jin yana son yaje yaga Masarautar su yace.
“Allah ya kaimu goben in ya samu in kuma bai samuba sai jibi, za dai muje kafin ayi bikin”.
Amin suka amsa kana shi kuma ya juya fita.

Yana isa gida kai tsaye Side ɗin su Dr Jameel ya shiga nan yasa masu suna ta maganar abinda za'a yi kasancewar yau saura kwana huɗu ne ɗaurin Auren kasancewar yau ya kasance Litinin.
Talata Laraba Alhamis juma'a za'a ɗaura Auren.
Nan dai suka cigaba da hiransu.

Acan gidansu Asma'u ma shirye shiryen biki ya kankama.

Alhamdulillah washe gare suka tafi Gombe.
Harda Dr Jameel da Lallai Khadijah da Rahma harda Didi da Innayi da Galadima suka je dan ya gabatar da masarautar su.
Kwana su biyu suka dawo Gembilan.

Alhamdulillah zuwa yanzu Amina ta fara samun sauyi dan yanzu ta daina zare harshenta.

Hajia Bunayya kuwa abu kam sai gaba gaba.
Samira Sani kuwa jin Amina ta samu sauƙine da yadda akayi yasa itama ta zo ta kokawa Momyn kuma Alhamdulillah yau dasuka dawo daga Gombe.
Man Liman yayi mata tofi, ya bata ya bawa Amina.

Alhamdulillah cikin kuɗirar Ubangiji kafin zuwa la'asar Samira ta fahimci zuban ruwan nan ya ragu sosai.
Amina kuwa sosai itama mummurɗewa da jikinta keyi ya fara raguwa.

Nan ya sake yi musu tofi cikin zam-zam ɗin na wasu keɓantattun ayoyi da sauri kamar haka.
*Al-araf ayata 117, 118, 119, 120, 121 da kuma 122. Sai Suratul Yunus daga ayata 79, 80, 81, 82, Sai kuma suratul Ta-ha aya ta 65 66, 67, 68, 69, 70, Sai kuma suratul al-Kafurune gaba ɗayanta, da kuma suratul al-ikhlas dukanta sai suratul al-falaq itama dua da kuma suratul An-nas itama dukanta da forko zaki samu zam-zam ki zuba mai yawa a tsabtacecen mazubi ko roba ko kwarya, ki tabbatar zam-zam ɗin zai ishe ki sha da kuma yin wanka, sai zuba a robar kana kisa kanyen magariyar guda bakwai an fison ɗanye Amman busheshenma ba matsala zaki daka guda bakwai in ɗanyen nema ki daka bakwai, sai ki zuba a Zam-zam ɗin kana ki karanta ayoyin Alkur'ani mai tsarkin dana lissafa Miki da surorin ki ɗan motsashi zakiga ya ɗan buga kumfa sai ki ɗiba a cup wanda zakisha ki ƙoshi kuyi gyatsa, sai ki zauna bisa yaƙini da niyar Allah ya yaye Miki matsalarki ko wacce iri yace Sihiri, ko tsafi, Sammu, ko kambun baka, ko cutar da ba'a gane kantaba ko sharrin iska. Kisha koyi hamdala kana ki ɗauki sauran na cikin robar ki samu sarkakekken wurin da babu najasa kiyi niya da duk matsalarki kiyi wanka. Wlh da izinin Ubangiji zakiji sauƙi ki samu sauyi anaso na farko dai kiyishi da Zam-zam inda hali duk bayan wata shida ko shekara ɗaya kiyi kiyiwa yaranki da mijinki dan makarine mai girma in ba hali saboda tsadar da Zam-zam keyi in kinyi na forkon da Zam-zam to na biyu kiyi da ruwan sama na uku da duk ruwan da ya sauwaƙa gareki, inda hali ko yaushe da Zam-zam in ba hali ayi na forkon da Zam-zam in bai samuba ayi da ruwan sama na roƙon da na biyun da na ukun, kiyishi maƙo maƙo ko wata wata ana dai son duk bayan wata shida ko shekara ɗaya kiyi, yar uwa ko ɗanki, ƴarki mijinki ƙanwarki ƴaƴan yar uwa ki ko ɗan uwa duk inda kukaga yaro ko yarinya sun cika rashin ji gagara rawan kai gardama da alamun kwaucewa hanya kuyi masu yanada matuƙar fa'ida da falala, sadakace fisabilillahi idan kinji daɗinshi kiyi niya kiyiwa Mahaifiyata Fatima Dedde na ƙu'huwa ƙafa uku da fatan Allah ya jiƙanta ya kai haske da ni'ima Qabarinta. Ni kuma inada wata buƙata mai girma da falala da daraja a wurin Allah kuyi min addu'a kisa yaranki suyi min addu'a kice su roƙawa Aysha Aliyu Muhammad Garkuwa Allah ya biya mata buƙatarta akan alkhairi, ya raya mata ƴaƴanta Muhammad Jabeer da Maimuna Ikhram da Ibraahim ya shirye su ya basu ilimi mai amfani da albarka yasa su zama abin alfahari ga Musulunci da Musulmai mazan ya basu mata na gari da zuraya ɗaiyi ba, macen ya bata miji na gari da zuri'a ɗaiyiba, kana Allah ya bani wasu ƴaƴan masu albarka da nisan kwana tagwaye inyiwa Deddena takwara da Babana in samu Aliyu Haiydar da Fatima Khausar in samu auta A'isha takwarar kakata mafi soyuwa*

Man Lima da Hajja Nana ma bayan sunyi sallar la'asar da Baffa Liman da Yah Abba suka kama hanyar komawa Jauro Yaya.

Acan ɓangaren Hajiya Bunayya ma tunda tasha wannan ruwan tofin sai tsutsotsin suka yawaita fita yayin da suke cinta da gasken gaske sai dai tana shiga ruwan ɗumi zai lafa amma bazai wuce awa biyu zuwa uku ba zai sake dawowa haka tayi wannan yinin ranan zunibi da sakayyan aikinta na bibiyarta.

Daddare bayan sallar Isha'i Moddibo ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login