Showing 42001 words to 45000 words out of 218703 words
numfashi tace.
“Wace Unguwar?”.
Hannu yasa tare da shafa sumar kansa kana yace.
“Tsetse amman a hotel ne”.
Kai ta jinjina tare da sauke numfashi tace.
“Ayyah Tsetse kuma kai bansan Unguwar ba”.
Ware ido yayi tare da miƙewa daga kishingiɗar da yayi da mamaki yace.
“Dama to kinsan Rabat ne bare kisan Unguwannin su?”.
Cikin sauri ta girgiza kai kana tace.
“Um-um bansani ba amma ban taɓa jin sunan bane”.
Ahankali yace.
“Ayyah yanzu ina so inyi wanka ne”.
Kai ta gyaɗa cike da kulawa tace.
“Toh shikenan ahuta gajiya”.
Daga nan ya kira Ummi da Malam Arɗo bayan sun gama gaisawa ya shiga toilet, da ido yabi turaren wanka Maclean brush towel pich colour yana kallo komai na ciki sabone Anutse ya fara wankan lokaci ɗaya yaji tsikar jikinsa na miƙewa sabida wanirin sanyin na ratsa baki ɗaya ilahirin jikinsa, cikin sauri yaja dogon tsaki Aransa kana yace.
Anya wannan aljanar yarinyar zata bar rayuwata ta nitsu kuwa, yarinya sai mata da nacin tsiya.
Towel ya janyo ya ɗaura kana ya ɗaura alwala ya fito dai-dai lokacin aka kira sallar Isha'i jikin Dressing mirrow ya nufa ya shafe jikinsa da mai kana ya fesa turare sa masu daɗin ƙamshi kana ya buɗe jakarsa ya ciro Jallabiya Sky blue me taushi kana ya ɗaura hirami kamar ɗankwali ya riƙe farin carbin sa sosai yayi kyau tun da aka sace M Jameel aka kashe sa bai sake yin wankan daya nutsu irin na yau ba yana fita ya nufi Masallaci akayi sallar Isha'i ana idarwa yayi adduo'i kana sai da aka wawwatse kafin ya fito ya nufi cikin ƙoƙarin shiga ya haɗu da mai gadin na fitowa.
Kallonsa mai gadin yayi cike da girmamawa yace.
“Aliyu Youssef Mouley?”.
Ya faɗin sunan da sigar tambaya tare da duba hoton Modibbo da Abba ya tura mishi ta whatsapp.
Kai Modibbo ya haɗa mishi tare da bashi hannu.
Cikin fara'a mutum miƙo hannunsa tare da cewa.
“Assalamu alaikum Yah Mouley”.
Rumtse ido Modibbo yaui domin tunowa da Jalaladdeen ne kaɗai ke kiransa da wannan suna. Sai kuma ya ƙara rumtse idanun da ƙarfi, sabida tunowa da tsawon lokacin da baiji motsin Jalaladdeen ba, tun kafin a sace. Jameel, ya tabbatar babban abune kaɗai zai iya ritsa Jalaladdeen da har zai iya hanashi nemansu na tsawon wannan lokacin.
Cikin sauri ya buɗe idanunsa tare da gyaɗa tsayuwarsa yana jan Carbin hannunsa jin Mutumin na cewa.
“Sunana Habibullah nine mai gadin gidan Alh Bashir kuma nike kanshi in yazo duk inda zaije nike kaishi kuma nida matata ke zaune a BQ ɗin gidan”.
Kai Modibbo ya gyaɗa masa tare da cewa.
“Eh Abba ya gaya min”.
Jinjina kai mai gadin yayi tare da cewa.
“Ganan abinci na kawo maka”.
Kallonsa Moddibo yayi da mamaki yace.
“Abinci kuma?”.
Kai mai ya gyaɗa alamar Eh.
Jinjina kai Moddibo yayi tare da kallon womers ɗin hannunsa yace.
“Toh daga ina aka samu abincin?”.
Murmushi mai gadin yayi kana yace.
“Ai akwai abokin Alh anan lokacin da Marigayi Jameel yazo har ya koma daga can ake kawo masa abinci”.
Lumshe idanu Moddibo yayi cikin sanyi yace.
“Ayyah yayi kyau angode”.
Sannan yayi gaba, mai gadin kuma na biye dashi.
Bisa kujerar ya zauna shi kuwa Habib kai tsaye dining area ya nufa kana ya ajiye mishi ɗan kondon da kulolin ke ciki, kana ya dawo gabanshi tare da miƙa mishi key ɗin mota tare da cewa.
“Ga wannan da ita zamana fita, in kuma baka son draving ga number'n ta sai ka Kur'ani, zanzo in kaika duk inda kakeso”.
Ya ƙare mgnar tare da miƙa masa hannunsa alamun ya bashi wayarsa ya saka mishi number's.
Wayar ya miƙa mishi ba tare da yace komai ba.
Shi kuwa Habib number's sa ya sawa wayar Modibbo kana ya miƙa mishi.
Amsa yayi tare da ajiye wayar.
Shi kuwa Habib sallama yasa kana ya miƙe ya ficee.
Shi kuwa Modibbo a hankali ya miƙe jin yadda cikinsa ke ƙugi alamun yunwa.
Dinning table ya nufa, kujerar yaja ya zauna tare da zuba abinci kana ya fara ci bayan ya gama ne ya dawo falon.
Lumshe yayi dearling number Abba.
Bayan Abba ya ɗaga sun sake gaisawa ya sauƙe Ajiyar zuciya tare da cewa.
“Toh Abba yanzu me ake ciki idan Allah yakai mu gobe dame dame za'a fara?”.
Kai Abba ya Girgiza cikin yanayin sanyin muryarsa yace.
“A'a Moddibo gobe kam ka huta tun da kaga yau Alhamis gobe kuma jumma'a ne ba aiki a ƙasar tasu dan jumma'a da asabar ne ranakun hutun ƙarshen makonsu, shiyasa dama naso yau ka tafi ka kwana ka huta gobe ma huta sai jibi lahadi in Allah ya yarda zaka fara zuwa Company”.
Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.
“Toh shikenan Abba Allah ya kaimu”.
Ameen Abba ya amsa kana sukayi sallama.
Miƙewa yayi akan kushin ɗin ya lumshe Idanunsa a hankali yayi miƙa da alamun gajiya kasancewar yayi doguwar tafiya sannan dan kusan wuni yayi a zaune, da fari akan ƙarfe tare jirginsu zai tashi. Ashe tun dare sun mishi text sun caza lokacin tashin sun meda sai biyu zasu tashi bai ganiba, saida yazo Airport ɗin, shiko yanaga komawa ciki wani jidaline shiyasa ya zauna anan kawai.
To hakan ne yasa ya wuni a zaune, shiyasa gaba ɗaya gaɓoɓinsa ciwo suke masa ahankali ya gyara kwanciyar sa still Idanunsa na lumshe cikin sauri ya miƙe kana ya tashi ya zauna numfashi mai zafi ya fesar, tsaki yaja kana ya miƙe tare da nufar ƙofan Falon ya fita yana mgnar zuci Mayya jarabebbiya nan ɗinma sai kin adaddabeni.
Ahankali ya tsirawa coumpund ɗin ido zuwa wajen ganin yanda fitilu suka haska wajen kamar rana komai na hotel ɗin abin burgewane da ban sha'awa ne ahankali ya fara taka step ɗin farandar yana sauƙa kallon dattijon mai gadin dake zaune daga can wurinsa ya nufa,
Duk da tarin motocin dake wurin Hausa wurin ya cunkushe ba, yayinda kuma kowa harkar gabansa yake.
Hannu ya mikawa tsohon tare da yi mishi sallama.
Cikin tsananin girmamawa tsohon ma ya bashi hannu tare da zuba mishi ido cikin ƙare masa kallo.
Shi kuwa Modibbo a ya buɗe bakinsa tare da ɗan ɗaga sautin muryansa yanda zaiji yace.
“Baba”.
Miƙewa Dattijon yayi tare da da ɗan rusunawa kana ya ɗan ɗaura hannunsa na dama kan kirjinsa tare da ɗan sunkuyawa cike da tsananin girmamawar da ta fara bawa Modibbo haushi ya za'ayi dottijo kamar wannan yake kishi haka, in Habib ya mishi haka zai iya amsa sabida ya girmeshi.
Numfashi ya fesar tare da ɗan sakin fuska jin dottijon na cewa.
“Na'am Alh ya aka yi?”.
Gyara tsayuwar sa yayi kana yace.
“Baba kana zaune kai kaɗai ne?”.
Kai Dattijon mai gadin ya gyaɗa kana yace.
“Eh Alh gacan abokan aikina yanzu sune a bakin gate, ni sai da safe zan koma can kuma, yanzu anan nake”.
Ya ƙare mgnar yana buɗe wani mutun da yazo shiga, saida mutumin ya shiga kana ya kuma rufewa.
Girgiza kai Moddibo yayi yana kallon kalimin Dattijon numfashin ya fesar tare da cewa.
“Sunana Aliyu Youssef Muhammad Mouley, daga Nigeria amma kakata tana kirana da Moddibo zaka iya kirana Modibbo”.
Jinjina kai Dattijon mai gadin yayi yace.
“Ayyah Alh yayi kyau”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe cikin sanyin murya yace.
“A'a ba sai kace min Alh nan ba ka kirani da sunana kawai”.
Kai ya gyaɗa yana jinjina karamcinsa Aransa yace yana nan kamar ƙaninsa Ibrahim Youssef Muhammad Mouley. Ibrahim bashi da girman kai sai dai shi Ibrahim yafi wannan dariya afili kuma sai yace.
“Toh Moddibo”.
Murmushi Moddibo yayi kana yace.
“Yawwa ai yafi sannan kuma akwai abinci da aka kawo min so naci yamin yawa, kaje ka ɗauka mana sai kaci sabida kada ya lalace!”.
Cikin tsananin mamaki da ganin tsananin karancin Dottijon ya haɗa kai, tare da amsar key ɗin ɗakin da Moddibo ke miƙa masa, cike da yarda aminci yace.
“Ngd Ngd matuƙa Modibbo, Allah ya kara girma ya kare zuriyar Mouley baki ɗaya”.
Gyara tsayuwa yayi tare da girgiza kai yace.
“Amin Ya Allah”.
Gefensa mai gadin yabi kana yace.
“Bari na ɗauka to”.
Ya faɗi tare da nufar cikin, cikin nitsuwa Modibbo yabi bayanshi.
Yana shiga falon ya dauko Warmers din sannan ya fita.
Cike da girmamawa Moddibo yace.
“Toh saida safe Baba”.
Mai gadin na fita yace.
“Allah ya tashe mu lafiya ahuta gajiya”.
Sannan ya fice.
Ahankali Moddibo ya rufe ƙofar falon tare da kashe wutan falon da Ac kana ya nufi Bedroom ɗinsa Kallon AC bedroom din yayi jin kamar yayi mishi yawa ne yasa hannun ya ɗauki rimot ɗin kana ya rage gudunshi.
Kwanciya yayi akan gadon tare da lumshe Idanunsa cikin sauri ya buɗe Idanunsa tare da dafe ƙasan lokaci ɗaya zuciyarsa da jikinsa sunka harba a tare, baki ɗaya ya fahimci wannan muguwar yarinya haka zatayi ta addabar rayuwarsa kenan.
awannan rana dai haka ya kwana cikin wani irin yanayi bacci rabi da rabi yayi.
Washe gari Jumma'a haka ya wani cikin hotel din sai sallan jumma'a da ya fita ana isarwa ya dawo, daga nan ko bakin titin hotel ɗin bai leƙaba.
masallaci ne kaɗai ke fitar dashi.
Hakan yayi kwana biyu yana hutawansa.
Yau Lahadi a bisa tsarin ƙasar Marocco yau ɗin ne forkon sati.
Ƙarfe takwas ya samu Moddibo acikin Company Abba bisa jagorancin Habib.
Yana isa suka fara aiki gadan-gadan aiki ake tako ina babu kama ƙafar yaro domin dama sa hannunsa kawai ake kira da sahalewarsa a matsayinsa na mataimakin MD duk sabbin Injina da aka kawo aka shiga daddasasu da duk wasu gyare-gyare daya kama suka shiga yi domin samun asabunta Company da habaƙashi don har buga atamfofi, Laces, Mayafain laffaya da duk sauran abubuwan buƙata suke so farawa.
Domin shine Company na farko da aka buɗe sa acikin Rabat wanda aka haɓakasa sannan ake inganta kayyakinsu.
Bai bar cikin Company ba sai shida saura kwata kai tsaye masauƙin ya wuce yana isa yayi Hong mai gadi ya buɗe masa gate yana Parking suka gaisa.
Kana ya wuce yayi ciki. kai tsaye Bedroom ya wuce ya watsa ruwa kana ya ɗaura alwala ya fito Masallaci kasancewar ankira Maghariba bai fito ba saida akayi Isha'i kafin ya dawo yaci abinci da Habib ya kawo masa. bayan ya kammala ya ɗauko system ɗin sa ya tura Abba duk yanda sukayi tsare-tsaren abubuwan da kuma hotunan yanda abubuwan suka tafi sosai yayiwa Abba bayanin sannan Abba ya kara masa haske akan sauran abubuwan sai misalin shaɗaya ya tashi yana jin wani irin kasala bini-bini zaiyi miƙa tare da hamma kai tsaye toilet ya nufa ya watsa ruwa.
Anutse ya fito tare da kumtsaawa, kana ya kwanta akan gado tare da lumshe idanunsa tsikar jikinsa na tashi sanyin AC da ƙamshin Roomfreshner da kuma ƙamshin tularensa shi yasake haddasa masa jin wani masifaffen kasala cikin wani irin yanayi ya ƙudundune tamkar yaro lokaci ɗaya bacci yayi awon gaba dashi.
A hankali yake juye-juye yana mai jin da ganin abin kamar a mafarki kamar kuma a zahiri.
Kanshi longwaɓar cikin narkekkiyar murya yace.
“Zakeeh kasheni fa”.
Cikin tsoro tace.
“Ana asped Yah Mu'allim”.
Kai a jujjuya mata tare da cewa.
“Kije keda Allah, kiyi ta dakon zunubi, kina sane dai in har ban yafe mikiba cikin fushin Allah zaki kwana”.
Da sauri ta ƙara kwaɓe fuska, tare da cewa.
“Dan Allah Yah Mu'allim kayi haƙuri ka yafe min, nayi maka al'ƙwari ina nan tafe zanzo gare cikin aminci da rakiyar amintattu a ranar nayi al'ƙawarin gujewa fushin Ubangiji a ranar kada ka ɗaga min ƙafa ka mallaki dukkan ƙudurinka”.
Wani irin mataccen murmushi yayi tare da cewa.
“Yaushe ne ranar?”.
Da sauri tace.
“Nan kusa take”.
Wani irin kallo yayi mata tare da cewa.
“Ranar yaushe ce”.
A hankali tace.
“Raanar larabace ce”.
Cikin wani irin kallo yace.
“Na'amin ce, tunda al'ƙawari kikayi”.
Cikin sauri ta miƙe ta nufi toilet cikin mawuyacin hali ya ɗago idanunsa dake cike da feeling kana muryarsa na rawa yace.
“Pleaassss Hayatieee kada ki saɓa min al'ƙawarin dan idan kika saɓa min a wannan ranar”.
Girgiza kai Khausar tayi cikin kuka da raunin murya tace.
“Bazaka mutuba”.
Amatuƙar galabaici ya yunƙura da niyyar binta tayi saurin rufe kofar toilet.
Akuma dai-dai lokacin ya farka da wani irin azabebben kasala dafe kansa yayi da hannu bibbiyu yayin da Idanunsa suka cika da ruwan hawaye haka ya kwana cikin mawuyacin hali Allah ya sani ya fara ganin yarinyar aljana.
Washegari da sassafe ya tashi yayi wanka kana ya shirya cikin gezner fari ƙal da ya fito da ainihin kyawunsa Anutse ya fito falon hannunsa riƙe da Breafcase a dining area ya tsaya tare da buɗe Warmers din da Habib ya jere Wainar shinkafa ce da miyar taushe sai kuma soyayyan Arish da tea Wainar yaci kana yasha tea bayan ya gama ya mike tare da ɗaukar Breafcase ɗinsa da wayoyinsa da kuma mukullin motarsa kai tsaye Company ya nufa.
Gembila
Aɓangaren Abban sosai hankalinsa ya dan kwanta fahimtar lallai Moddibo yana aiki gadan-gadan bisa tsari da hikima komai na tafiya dai-dai.
Numfashi ya fesar tare da ciro wayarsa yayi dearling number Malam Arɗo bayan ya dauka sun gaisa.
Abba ya sauƙe Ajiyar zuciya kana yace.
“Yau kusan kwana shida kenan da zuwan mu gidan Lamiɗo akan maganar Aliyu da Khausar amma har yau bamuji ya sake neman muba amma tunda mu muke da buƙata yakama muji ta bakinsa”.
Ya gyara zamansa wayar akunnensa kana ya cigaba da cewa.
“Musamman ma da yanzu na tura Aliyu Marocco yana rayuwa shi kaɗai ya kamata ace anyi ƙoƙari anyi batun auren nan saboda kaɗai ci da damuwa zaiyi masa yawa”.
Jinjina kai Malam Arɗo yayi cike da gamsuwa yace.
“Nima abinda nake tunani kenan amma Insha Allahu gobe zamuje da daddare idan Allah ya kaimu rai da Lafiya”.
Ahankali Abba ya jingina bayansa da jikin kujeran kana yace.
“Toh Allah ya kaimu bisa rai da Lafiya”.
Ameen malam Arɗo ya amsa kana suka katse kiran.
*Jauro Yaya*
Hajja Nana ce zaune ta tanƙwashe ƙafafunta Baffa Garga dake gefenta yayi Murmushi yana kallonta yace.
“Addah Nana ɗazu nayi magana da Hammadu”.
Kallonsa tayi tare da kawar da kai gefe tace.
“Ya masa kyau”.
Murmushin Baffa Garga ya faɗaɗa yana kallon yanda tayi kicin-kicin da fuska sassauta murya yayi kana yace In gaishe ki”.
Taɓe baki tayi ba yabo ba fallasa tace.
“Idan ya damu da gaisuwar ai sai yazo inda nake”.
Gyara zama Baffa Garga yayi kana yace.
“Addah Nana ai yace ma zai zo In sha Allahu gobe da safe zaiyi sammako yazo”.
Sassauta fuskarta tayi kana tace.
“Toh Allah ya kawo shi lafiya”.
Ameen Baffa Garga ya amsa tare da ɗauko mata wani hiran.
Washe gari:Asuban fari Baffa Jimeta yayi sammako ya ɗauko hanyar Taraba duk da sammako da yayi sai ƙarfe biyar da rabi ya isa Jauro yaya Aka shiga gaishe-gaishe da tambayar juna koda wasa bai kawowa Hajja Nana maganar Khausar ba sai bayan sallar Isha'i bayan sun ci abinci sun zauna da mahaifiyarsa da kuma Kawunnansa ana hira.
Ahankali ya gyara zamansa kana ya tanƙwashe ƙafafunsa agabanta ya karyar da wuyarsa cikin sanyin murya yace.
“Hajja Nana alfarma nake nema awajenki”.
Kallon second ukun tayi masa kana tace.
“Ni kuma wace alfarma zanyi maka ai da har ina da abinda zaka nemi alfarma awajena Umarni na zaka bi”.
Ahankali ya sassauta muryarsa yace.
“Ai yanzu ma Umarnin ki nake bi Hajja Nana Ni dai temako nema”.
Kallonsa tayi kana tace.
“Taimako akan me?”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da yin ƙasa da kansa yace.
“Taimako akan Marainiyar Allah”.
Baki ta buɗe tare da kallon ƙannenta sai kuma ta kallesa tace.
“Ai kowa ma Maraya ne sannan kowa ma zai iya kasancewa Maraya”.
Kai ya gyaɗa yana kallon yanda take jijjiga ƙafa yace.
“Eh nasani amma akan Khausar nake magana Hajja Nana nazo ne in sake Baki haƙuri akan laifin data aikata sannan muyi mata uzuri matsayinta na yarinya ƙarama”.
Kai ta gyaɗa ba yabo ba fallasa tace.
“Shikenan komai ya wuce tunda Ni ban kaiba Ni kaka ce kun nuna min bani da matsayi sannan banida ikon faɗa aji”.
Da sauri Baffa Jimeta ya kalleta amma baice komai ba ta cigaba da cewa.
“Acikin maganar rayuwar Khausar to ba matsala na cire hannuna ta Auri duk wanda taga dama take so Ni bani da damuwa aciki na janye hannu na tunda haka kuke buƙata”.
Numfashi Baffa Jimeta ya fesar cikin kwantar da murya yace.
“Toh shikenan kiyi haƙuri ki sanya Albarka aciki”.
Taɓe baki tayi kana tace.
“Zansa al'barka ai tunda bazan sa tsinuwa ba Ni dai babu bakina aciki sannan babu batub aurenta da wancan ɗan gaba da fatihan kam”.
Kai ya girgiza cikin sassauta murya yace.
“Mu dai kiyi haƙuri dan Allah kiyi haƙuri kiyi mana fatan alkhairi aciki”.
Ahankali ta kallesa kana tace.
“Toh Allah ya kyauta ya kiyaye gaba dama maganar data kawo ka kenan??”.
Cikin sauri ya girgiza mata kai kana yace.
“A'a bashi bane ya kawoni kewar ki nayi shine nace bari nazo in gaisheki”.
Hararansa tayi tare da kallon sauran ƙannenta tace.
“Oho dai”.
Akuma dai-dai lokacin Malam Arɗo,Malam Ahmad da Abba ne zaune afalon Lamiɗo bayan sun gaisa sannan suka yimasa jawabi kan cewa sunji shiru shiru bai sake neman suba yasa suka dawo.
Anutse Lamiɗo ya gyara zama cike da dattako yace.
“Badamuwa Insha Allahu dama nima ina shirin zan ne meku ɗin saboda bani da ikon bada ita akaran kaina amma munyi magana da Baffan yarinya yau ɗin nan ma yazo daga can Adamawa zai nemi sahalewar kakar yarinya”.
Ajiyar zuciya suka sauƙe atare Kallonsu Lamiɗo yayi kana ya cigaba da cewa.
“Dake Itace taso kawo tangarɗa acikin al'amarin amma yace zaiji da lamarin duk abinda ake ciki yace min Insha Allahu gobe muyi ƙoƙari muje gamu gashi gata ya zama na munje neman Auren ne”.
Numfashi Malam Ahmad yafesar kana yace.
“To ai wannan duk mai sauƙi ne badamuwa za'ayi hakan”.
Kai Abba ya gyaɗa kana tare da faɗin.
“Bakomai Insha Allah goben zamuje”.
Murmushi Lamiɗo yayi cike da kamala yace.
“Eh zamu bari gobe idan munyi sallar Azahar sai muje kafin nan ya tattauna da mahaifiyarsa idan anyi sa'a abin zai zo da sauƙi dake shi yana da kyakkyawar fahimta sannan bashi da son zuciya”.
Jinjina kai Malam Arɗo yayi idanunsa akan Lamiɗo yace.
“Ba matsala Insha Allah nima ina da ƙafa agarinsu dan Malamin dana ke zuwa ɗaukan karatu awajensa ai ƙanin Kakarta ce kuma sunzo wajena tare shima nasan yana da kawaici, kara da dattako”.
Jinjina kai sukayi tare da tsaida magana akan washe gari Bayan Sallar Azahar zasu tafi.
Washe gari baki ɗayansu suka shirya har Mommy da Khausar Lamiɗo yace su shirya atafi dasu Khausar da Mommy suna motar Lamiɗo Malam Arɗo da Malam Ahmad suna motar Abba kai tsaye suka dauki hanyar Jauro yaya suna isa Jauro yaua kai tsaye gidan Hajja Nana suka nufa dai-dai lokacin dasu Baffa Jimeta suka fito daga sallar La'asar Malam Liman na ganin Malam Arɗo ya faɗaɗa fara'ar fuskarsa kana yace.
“A'a Malam marhaban lale sannunku da zuwa”.
Baffa Jimeta kuwa cikin sauri ya nufi Lamiɗo tare da miƙa masa hannu yace.
“A'a Sannunku da zuwa har kuzo kenan?”.
Murmushi