Showing 213001 words to 216000 words out of 218703 words

Chapter 72 - Sakayyah 2 Hausa Novel Complete

ɗan mu da kuma wa'anda zamu haifa nan gaba”.
Khausar kam wani irin kuka mai tsuma zuciya da tsananin kishi take yi.
Moddibo kuwa cikin gaskiya da gaskiya ya cigaba da cewa.
“in dai akan mulkine zan yi Miki kishiya abawa Ibraahim in yaso a Aura mishi Mata huɗu a rana ɗaya, nayi alkawarin bazan yimiki kishiya a kan mulkiba Amman ban miki alkawarin cewa wai bazan Miki kishiyaba dan bansan ne Allah zai tsara a kanmuba a gaba”.
Da sauri ta tashi kana ta buɗe Idanunta cikin rauni da shesh-sheƙa tace.
“Mata fa kace zasu Aura maka”.
Cikin kwantar mata da hankali yace.
“Ba kiji mai nace Miki bane indai mulki ne na haƙura dashi a bawa Ibrahim abarni Ni in rayu dake da ɗana da abinda zaki haifa agaba”.
Ahankali ta shiga sakin ajiyar zuciya Moddibo kuwa cike da tarin ƙaunarta ya cigaba da faɗin.
“Na tabbar kun isheni farin ciki kun isheni jin daɗin rayuwa kun isheni komai batare da mulkin nan ba Ni na yarda zan kasancewa Ibraahim mai bada shawara abawa Ibraahim mulki shine abinda yafi min kwanciyar hankali hakan ya miki kinji daɗi akan haka”.
Cikin matsanancin jin daɗi da farin ciki tace.
“Na yarda in dai har Abualeey ya yarda Bama son mulkin mun bar musu mun yafe musu mulkinsu Mukam Bama so”.
Akuma dai-dai lokacin Jaririn yasa kuka cikin sauri ta kallesa cikin shesh-sheƙan kuka tace.
“Abu J ba ka jiba yana kuka shima baya so a yiwa Mimeeinsa kishiya”.
Cikin sauri ya rungumota jikinsa kana ya haɗa da jaririn ya rungumesu tare da cewa.
“Mu bar musu mulkinsu Minha ba ruwanmu suje can su ƙarata da mulkinsu, su riƙe abinsu abarmu haka mu cigaba da jin daɗi da kwanciyar hankali yafi mana”.
Dai-dai lokacin Ibraahim yayi knowking kana ya sanar masa zuwan Momy da Didi.
Suna shiga Didi ta kallesa Babu walwala atare da ita tace.
“Yanzu Aleeyu ka kyauta kenan ɓacin ran da kasa Mahaifinka”.
Cikin sauri ya mike kana ya tsugunna gaban Didi tare da cewa.
“Didi dan Allah kuyi haƙuri”.
Cikin sauri da rashin walwala Didi tace.
“Shi ya gama yanke hukunci amatsayin sa na Mahaifin ka Sarautace an riga da an baka ita sai kayi abinda kaga zaka iya akai”.
Da sauri cikin shesh-sheƙa Khausar tace.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Didi yanzu kuma harda Mata za'a ƙara mishi?,”.
Cikin tsuke fuska momy ta harareta tare da cewa.
“Dan Allah rufe mana baki, sokuwar banza sokuwar wofi, in ba'a Aure ke aka Auro ki baza ki taya mijinki yanda zai yiwa iyayensa biyayya ba, sai ki tsaya sokonci kina kuka kina cewa an ƙara masa mata matar kashe ki zata yi, ko kuma akan ki zata zauna?”.
Cikin rauni ta fashe da kuka kana ta jingina kanta da bakin gado cikin shesh-sheƙan tace.
“Momy ba zaki gane bane bazan iya rayuwa da wata mace tare da Yah Mu'allim ba”.
Ahankali Didi ta ɗagota kana ta dafa kafaɗarta tare da cewa.
“Kiyi haƙuri Sarauta ce an bashi Mata kuma tunda yace baiso da ɗaya zai zauna shikenan tun da dama bawai shariya ɓace ta tsara haka, al'adace”.
Ajiyar zuciya mai sanyi ta shiga saki tana jin nutsuwa na diran mata shi dai Moddibo kan sa na ƙasa Didi kuwa cikin kwantar mata da hankali ta cigaba da faɗin.
“Allah da kansa ya basu Umarni suyi Huɗu, Uku, Biyu idan kuma ba zasuyi adalci ba suyi ɗaya tunda yace ba zai yi adalci ba laifi.
Mahaifinsa ya yarda an bashi Sarauta batare da anƙara mashi mata ba”.
Cike da matsanancin farin ciki ta mike ta rungume Didi kana tace.
“Nagode Didi Ubangiji Allah ya miki Albarka”.
Cikin sauri ta saki Didi kana ta tsugunna ta fuski Alƙibla tare da yin Sujudur Shukur ta godewa Allah kallonta ta mayar kan Moddibo dake Murmushi ta miƙa masa hannu tare da cewa.
“Yah Mu'allim Alhamdulillah ”.
Martanin Murmushi ya mayar mata yana mai jin wani irin nutsuwa na ratsa sassan jikinsa ganinta cikin farin ciki ahankali yace
“Alhamdulillah”
Murmushi Didi tayi tare da riƙe hannun momy kana ta kalli Moddibo tace.
“Idan ka gama murnan ka tashi ka tafi Fada ana damƙa maka sarauta”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh”.
Momy kuwa kallon Khausar tayi kana tace.
“Wuce mu tafi ”
Ta ƙare maganar suna fita.

Cikin sauri Khausar ta miƙe tare da faɗawa jikin Moddibo tayi masa wani Amintaccen runguma sai kuma ta tallafo kansa ta haɗe bakinsu ta shiga kissing ɗin sa ahankali ta zare harshenta cikin nasa tare da riƙe hannunsa Fuskarta ɗauke da maɗaukakin farin ciki tace.
“Ina ƙaunarka Abu J My life is nothing without you”.
Murmushi yayi kana ya lakace mata hanci tare da cewa.
“Shikenan kuka ya ƙare ko?”.
Dariya ta sanya tare da ɗaukan Jaririn tabi bayansu Momy da tuni suka fice kana shi kuma ya fita ya samu su Ibraahim suka wuce Fada.

Aranan aka naɗa masa Sarautar Mouley kana aka ɗaura auren Rahama da saurayinta kana matar da za'a Aura masa aranan aka Aura wa Ibraahim ita Ibraahim kam. baki har kunne cikin jin daɗi da farin ciki aka gama Shagali da daddare aka kaiwa Ibraahim matarsa.
Tun aranan Lalla Hafsat da wasu daga cikin baƙi suka tafi da Rahama kasan cewar ƙanin mijin Lallai Hafsat ne mijinta yasa aka wuce Mexico da ita baƙin suna kuma duk an watse lfy...

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Khausar na samun kulawa mai kyau.
ranan da ta cika sati Uku Alhamdulillah Thearter yayi gwaɓi sosai suka je asibiti aka sake dubawa a ranan sukaje asibiti Alhamdulillah aka duba akace babu matsala yayi kyau saboda jikinta yana da kyau yaro yayi kuɓul-kuɓul gwanin sha'awa Masha Allah.

A ranan da suka cika wata ɗaya da yammaci Khausar bayan ta fito daga wanka ta shirya cikin wani riga da skirt na less me kyau jikinta sai ƙamshi yake ɗan ta yayi kuɓul-kuɓul Masha Allah yayi ƙato gwanin ban sha'awa.
Zaune suke Khausar Innayi da Hajja Nana suke a bedroom.
Yayin da Momy da Raudat ke zaune Side ɗin Didi tana ta shirye-shiryen tafiya nan da kwana biyar masu zuwa.

Ahankali Moddibo ya shigo bedroom ɗin hannunsa riƙe da Jaririn dake tsala kuka kusa da Khausar ya zauna kana ya ɗaura mata yaron akan cinyarta kai ya langwaɓar cikin wata amintacciyar murya me cike da kulawa tare da tsantsar soyayya yace..
“Minha yunwa fa yake ji”.
Ashagwaɓe ta tura baki kana ta langwaɓar da kai tare da cewa.
“Yah Mu'allim ɗazu fa yasha kuma sai yaita tsotseni”.
Akasalance yace.
“Ki ƙara mishi”.
Fuska ta narkar tare da faɗin.
“Toh tunda ya daina kuka a bari sai anjima”.
Ahankali ya girgiza kai kana yace.
“A'a ki bashi yanzu”.
Miƙewa Innayi tayi tare da cewa.
“Khausar bari inje inyi Miki ɗan wake naji kina cewa kina son ɗan wanke tunda kika haihu baki ciba”.
Murmushi tayi kana tace.
“Yawwa Innayi na ayi min shi yaji yaji yayi daɗi sosai sannan asa min da ƙwai da lemun tsami akai”.
“Toh".
Innayi ta amsa tare da ficewa.
Hajja Nana kuwa ido ta zubawa Moddibo lokacin daya zuge zip ɗin rigar Khausar ta baya.
Cikin Mamaki tace.
“Ohhhh ikon Allah”. Ta faɗa asanda taga yayi ƙasa da wuyan rigar Nonon fito, kan yaron ya tallabe ya sawa yaron abakinsa.
Ta cigaba da cewa.
“Gwara ma ni in tattara mu koma in bar muku gidanku. hankalin mu ya kwanta wai nan kai Sarki ne guda".
Juyawa yayi ya kalleta kana yace.
“Toh ce Miki akayi Sarauta anayinsa atsakanin Iyalai ne?
Ai sarauta iya kacinta Fada”.
Cikin taɓe baki Hajja Nana tace.
“Ohhh Allah ya kawo mu zamani ai kai ko A Fada idan zaka samu za kayi musu taɓara”
Murmushi yayi yana shafa sajensa yace.
“Toh Matatace fa,Ko ba matata bace?
Sadaki fa na biya”.
Hararansa tayi tare da cewa.
“Ka biya ko aka biya maka?”.
Dariya maganar nata ya bashi amma sai ya murmusa yace.
“Eh koma dai menene Matatace ni wlh kin isheni da gorin biya min sadaki akayi dan haka ni yau zan biya nawa sadakin”.
Ya ƙare maganar yana jan wayarshi tare da ƴan danne-danne.
Dariya ta sanya tare da cewa.
“Ohhh baki baya mutuwa ai da kai da ita duk bakin ku ɗaya ne”.
Khausar Murmushi take musu tana cigaba da bawa yaron Nono.
Sai kuma ta kalli wayarta jin sautin shigowar saƙo.
Hannunta na hagu tasa ta ɗauki wayar tare da buɗe saƙon.
Cikin tsananin mamaki ta zaro ido ganin alert ɗin 10 million da Modibbo ya tura nata da rubu a jiki.
*Minha ga sadaki na*.
Cikin kaɗuwa tace.
“Yah Mu'allim 10 million fa ka turo min me sanyi dasu, million goma”.
Sai kuma ta ƙare maganar da kallon Hajja Nana dake cewa.
“Da gaske”. Cikin tsananin jin daɗi Khausar tace.
“Wallahi kuwa gasu kin gani”.
Ta ƙare maganar tana miƙa mata wayar da kuma yaron sai kuma ta ruggumeshi tana saki kishi sassayan kiss tako ina a jikinsa.
Ganin yadda ta ruɗene yasa Hajja Nana yarda bawai dan ta fahimci rubutun alert ɗin ba.
Haka tai ta murna tare da godiya, kukan da Keyan ya sakan ne yasa ta saki uban ta karɓi ɗan kana taci gaba da bashi Nono.
Cikin dariya Hajja Nana tace.
“Daga yau ka huta da gori, kuma dole a bani million ɗaya a ciki”.
Murmushin yayi tare da cewa.
“Kawo account inki in baki naki sadakin tunda jikarki na gudun kishi sai in haɗata dake”.
Cikin dariya tace.
“Yoh ina ni ina aure ai na gama aure kam”.
Dariya sukayi baki ɗaya.
Bayan ta gama bashi da kansa ya mayar da Nonon kana ta mike tare da faɗin.
“Kizo muje ki gyara min Siff ɗina ya hargitse”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Toh”.
Tare da miƙewa tabi bayansa da kallo Hajja Nana ta bisu sai kuma ta saki Murmushi tare da ɗaukan Jaririn tana mishi wasa.

Suna shiga tsakiyar bedroom ya jawota jikinsa ya rungumeta yana shaƙan ƙamshin Kwalaccan Sirri da Humran _Aunty Aysha Aliyu Garkuwa_ da tayi amfani dashi sosai ƙamshinta ke zautar dashi yana masifar son ya riƙa shaƙar ƙamshin jinta yana masifar gigita masa tunani cikin wata kasalalliyar murya me cike da shauƙi da fitina yace.
“Minha yanzu dan Allah tsawon kwana nawa kika fara Sallah?”.
Cikin lumshe idanu da yanda lallausan tafin hannunsa ke yawo asassan jikinta ta fesar da sanyayyan numfashi tare da cewa.
“Yah Mu'allim nafi sati biyu da fara Sallah ”.
Ɗan ware idanunsa yayi kana muryansa can ƙasan maƙoshi yace.
“Kina tsoron kishiya kuma kina tsoron kyautatawa mijinki da ɗauke bukatarsa”.
Ashagwaɓe ta ƙyafta ƙwayar Idanunta cikin nasa tace.
“Yah Mu'allim nifaaaa”
Da sauri ya sake ƙanƙameta yana sakin ajiyar zuciya yace.
“Minha kin san dai ina da buƙata bazan iya jiran abinda Likitocin nan suka faɗa ba”.
Cikin sanyi da ɗan tsoro tace.
“Thearter na fa kada ya ɓalle”.
Yana yawo da hannunsa aƙugunta yace.
“Bazai ɓalle ba”.
Ya ida maganar yana zama bakin gado kana ya zaunar da ita kan cinyarsa tare da zuge zip ɗin rigar ta yayi ƙasa dashi kana shima ya cire nashi blanket ya jawo ya rufe su tare da ɗaura bakinsa akan dogon hancinta yana tsotsa kana ya mayar kunnenta yana hura mata sanyayyar iskan bakinsa.
Sai kuma ya tsaya jin tana cewa.
“Yah Mu'allim ina tsoron Theater nafa”.
Muryansa can ƙasan maƙoshi irin na wanda ke cikin tsananin buƙatuwa yace.
“Na sani zan biki ahankali”.
Bai jira jin Abinda zata ceba ya shiga sarrafa ta cike da bege da kuma shauƙi yayin da ya shiga Binta hankali cikin shagwaɓa da tsoro tace.
“Wayyo Yah Mu'allim wajen Theater na zafi fa ina tsoro kar ka ɓalle min ɗinki?”.
Cikin ficewar hayyaci yace.
“Minhaaaaa bazan ɓalle Miki ba ki nutsu dan Allah”.
Ita kam cigaba da zuba masa shagwaɓa da raki tayi tana cigaba dace masa wajen Theater ta sai da ya ɗauki kusan awa ɗaya akanta kafin ya janye jikinsa daga nata ya janyota jikinsa ya rungumeta yana sa mata albarka sai kuma yayi Murmushi yace.
“Matsoraciya sai raki ɗinki ɗinki ɗinki sai raki da tsoro".
Cikin sauƙe ajiyar zuciya tace.
“Yah Mu'allim Allah tsoro nake ji kar ya ɓalle”.
Yana shafa shafeffen cikinta yace.
“Ba abinda zai ɓalla shi Minha”.
Miƙewa sukayi suka shiga toilet sukayi wanka atare bayan sun fito suka fara jiyo muryan Raudat na cewa.
“Assalamu alaikum.
Addah khausy”.
Da sauri Khausar ta ƙarasa jan Zip ɗin rigar ta ta nufi ƙofa kallonta Moddibo yayi tare da cewa..
“Kamar Raudat ko?”.
Kai ta gyada kana tace.
“Eh Itace kuma kamar Naji kukan Keyan”. atare suka fita yana gyara wuyar rigarsa yayin da take naɗe ƙasan rigarta.
Suka fita falon idanunsa ya sauƙa kan Raudat dake rungume da jaririn.
Ware idanu Moddibo yayi tare da faɗin.
“Ya Salam Aunty Raudhiy yanzu ke aka bawa Yaron nan?”.
Murmushi tayi tare da kallon fuskar Keyan tace.
“Yah Moddibo ai na iya riƙewa bazan kada shiba”.
Murmushi yayi tare da faɗin.
“Aikam ba zaki kada shiba kawo shi nan”.
Karbansa yayi ya bawa Khausar ta zauna tana bashi Nono suka zauna gefenta suna ta hira...

Bayan kwana biyar Momy suka wuce Saudi ita da Hajjaj Nana dan Modibbo ya biya musu umra, bayan sun gama aikin umrarsu ne suka koma Nigeria bayan komawar su da sati ɗaya akayi.
Auren Amina da Baban Samira Sani cikin ikon Allah mai gadin gidansu Samira yace yana sonta fahimtar yanayin da take ciki kuma zuwa yanzu Alhamdulillah jikinta yayi sauki arana ɗaya aka ɗaura Auren Babanta ya bashi gida da jari kana ya nemi wani sabon mai gadi.
Haka suka tare abinsu Samira da maigadinsu.
ita kuma Amina tana rayuwarta da tsoho.

Hajiya Bunayya da Hajiya Lami kuwa na can Sycatry suna gallar rayuwarsu da girban abinda suka shuka.

Haka dai Rayuwa ta cigaba da tafiya Khausar kam Alhamdulillah yaronta ya kai wata shida yayi ɓul-ɓul dashi yana zama kana yana wangale baki yana dariya sosai.

A wannan lokaci kuma suka tafi aikin hajji, Ita da Modibbo da ɗan Jaririnsu da Hadimar dake kula dashi da kuma innayinsu, Asma'u da Dr Jameel, Asiya da Dr Zakariyya, Dija da Yah Ali, Yah Abba da matar daya aura wata biyu ɗaya wuce.
Sai Didi da Innayi da Abu Ali, da kuma Ibrahim da matarsa.

Watansu ɗaya a can suka dawo, bayan sun dawo da mako biyu suka je Mexico.
Sosai Lalla Hafsat da Rahama sukayi daɗin sosai.
Itama kanta Khausar Mexico tayi mata daɗi sosai.
Makonsu uku suka dawo.

Taraba. Nigeria Gembilan
Yau ya kasance labari cikin ɓadda kama Uncle Naseer ya shigo cikin garin Gembila da niyyar kwashe Mahaifiyarsa da Mahaifinsa su koma Indi'a da zama.
Cikin dare ya shiga cikin unguwar su da sauri ya buɗe musu mota tare da cewa Mamansa da Babansa.
“Kuyi sauri kushi ga mu tafi”.
Kai Maman ta gyaɗa kana tace.
“Toh ai gwara ka kwashe mu mu tafi mu huta da jaraba da Sa idon mutanen gari da gulmace-gulmace”.
Ta ƙarashe Maganar tana shiga motar.
Shikam Uncle Naseer cikin sauri ya shiga motar yaja su.
Suka fara tafiya suna gab da fita garin Gembilan motarsu tayi tambul ta riƙa juyawa tana bugawa da tsaunukan gefen titi kafin ta kama da wuta sukayi mugun ƙonewa sai ya Fuskarsu ce ta rage kana kuma b....






By
*GARKUWAR MARUBUTA*

Uncle Naseer kuwa, daga ƙugunsa zuwa ƙafafunsa ya ƙone ƙurmus kana bai mutuba yayin da fuskarsa yayi baƙiƙƙirin yanayin halittar fuskarsa ta sauya tamkar an babbaka kare. Mamansa, Babansa kuwa atake rai yayi halinsa Uncle Naseer kuwa cikin ƴan kawo agajine suka daukesa suka kaisa asibitin cikin.
Taraba.
Daga ƙarshe dai dole Lamiɗo aka kira Lamiɗo kam lokacin da akace Uncle Naseer yayi hatsari sosai yayi mamaki kasancewar baisan zuwansa garin ba kana yayi mamaki da akace iyayensa sun mutu...
Lokacin da Lamiɗo ya isa asibitin ya samu ina baki ɗaya Uncle Naseer babu abinda yake Banda jujjuya kai cikin tsananin azaba da Kiɗima sosai Lamiɗo ya tsorata da ganin yanda halittarsa ta sauya baki ɗaya jikinsa yayi sanyi ya sake jin tsoron Allah da kuma tsoron saɓawa Ubangiji.

Uncle Naseer kuwa Cikin matsanancin kuka da radaɗin azabar daya game jikinsa ya kalli Lamiɗo kana ya riƙe hannunsa tare da cewa.
“Na ƙulla sharri na kulla rashin imani na ƙulla shirka da riya da yawa gashi Allah ya kamani lokacin da banyi zato ba lokacin da nake tsaka da shirya makirci na zama abin tausayi kuma abin ƙonawa cikin wanan azabebuyar wuta”.
Kai Lamiɗo ke girgiza wa cikin tsananin tausayi da son kwantar mishi da hankali Amman ina.
Cikin ihu da kururuwa Uncle Naseer ya cigaba da cewa.
“Gashi tun daga nan duniya Allah ya fara ƙonani da wuta ina ga naje lahira nayi tsafi na sadaukar da mutane da yawa nasha jini”.
Kai Lamiɗo ya girgiza cikin sanyi da mamaki yace.
“Babu amfanin wannan maganar Naseer kawai ka tuba zuwa ga Allah kayi ta Istigfari”.
Cikin kururuwa da azaba Naseer ya girgiza kai tare da faɗin.
“Bazam iya ba bana jin zan iya tuba Ni mushrikine na haɗa Allah da wani saboda duniya wayyo nashiga uku na lalace kaicona wayyo Ni wayyo kaina”.
Kallonsa Lamiɗo yayi cikin mamaki yace.
“Baka iya tuba kuma toh kana so ka mutu da zunubi ne?”.
Kai kawai Uncle Naseer ke girgizawa ya gaza buɗe bakinsa ya nemi gafarar Ubangiji alamar Allah ya hana shi samun rahamar sa haka sai ya cigaba da surutai yana kururuwa tare da faɗe-faɗe da kuma abinda yake aikatawa cikin azaba da zugin da jikinsa ke masa yace.
“Ni nake zama Maciji na tsotsa jinin Amina naso in kashe ta Allah bai ƙaddara ba kwananta yana gaba ita. Asirinta ya ruhu naso in cutar da ita Allah bai nufa ba amma laifin Mahaifiyarta su suka nuna kwaɗayin kuɗinsu ga yanda rayuwa ta zamo mini”.
Ya ƙare maganar cikin tsananin kururuwa da firgita yayin da yake fisge-fusge yana zabura kana idanunsa suka zazzago cikin ihun azaba yace.
“Ka gani ko zan mutu kuma in na mutu cikin wuta zan shiga kaga wutar da ake nuna min kalletafa sai ci take tamkar ba abinda zai kashenta”.
Cikin rashin sanin madafa da tarin tsoron Allah Lamiɗo yace.
“Naseer ka daina kururuwa ka tsaya kayi salati da istigfari”.
Yana cigaba da ihu tare da firgita yace.
“Inyi salati kana ganin wutar da ake nuna min cikin wutar nan wai za'a jefani? Kuma kace inyi shiru”.
Haka dai ya ci gaba da tona wa kansa asiri ɗa'a fade-faɗe abubuwan d yake ganin, yinin wannan ranan ya mutu aka tattarasu dasu da iyayensa aka binnesa...

A cikin wannan kwanakin kuwa Baffa Jimeta yace Hajja Nana ta tattara kayanta su koma Yola ya gaji da zamanta a Jauro Yaya haka ya ɗaukota ta dawo Adamawa da zama ba don ta soba, Amman bini-bini zatace ya kawota haka kuwa dole yake kawotan tai kwanaki azo a ɗauleta tana komawa bazata rufa wataba zatace a Kaita.

Amina kuwa Alhamdulillah rayuwa ta cigaba da tafiya mata cikin kwanciyar hankali tana ta Istigfari tana zaune Lafiya da Mahaifin Samira wanda har ta samu ciki.
Wata rana ta fito daga gidan Samira kasancewar basu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login