Showing 33001 words to 36000 words out of 218703 words

Chapter 12 - Sakayyah 2 Hausa Novel Complete

ai muna tare ina nan ina Marocco amma idan ya gama zai dawo ko?”.
Ta ƙarasa maganar ta sigar tambaya tana kallon Abba.

Kai Abba ya gyaɗa mata kana yace.
“Eh zai dawo Insha Allah bazai wuce sati biyu”.
Jinjina kai tayi tare da kallon Moddibo kana tace.
“Badamuwa Babana ai zamu nayin waya”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Shikenan Ummi ba matsala tunda kin amince.
Murmushi tayi still Idanunta cike da ruwan hawaye tace.
“Na amince Babana Allah Ubangiji ya kaika lafiya Allah ya dawo da kai lafiya Allah yasanya alkhairi da albarka acikin tafiyar.
Ahankali yace.
“Ameen Ummi”.

Ajiyar zuciya Abba ya sauke tare da kallonta kana yace.
“Yanzu kuma sai batun kuɗin ku da aka har haɗa”.
Sunkuyar da kai Ummi tayi Atake hawaye suka cigaba da zubowa daga Idanunta cikin raunin murya tace.
“Toni me zanyi da kuɗin nan ne Abban Jameel?”.
Kai Abba ya Girgiza cikin rawan murya da rauni yace.
“Toh nima ɗin idan kun barsu awajena me zanyi dasu ga kuɗin Aliyu ga naki kowa ya karɓi kuɗin sa kowa yana da bukatarsa motar ki da Sarƙoƙinki kika siyar ki sayi wata mota amfani dashi”.
Kallonsa ya mayar kan Moddibo kana yace.
“Kaima Moddibo ka karɓi kuɗin ka ka sayi mota sannan sauran kuɗin kayi abinda ya dace dasu”.
Kai Moddibo ya girdiza ciki rauni yace.
“Abba me zanyi da kuɗin?.
Ai kuɗi na gama abinda ya dace inyi dasu Babu abinda zanyi dasu tun da har basu tseratar min da J ɗina ba wani amfani zasu yimin?”.
Cikin rauni Abba yace.
“Bakomai Moddibo ka karɓi kuɗin nan idan ka barsu awajena kun barmin tashin hankali da damuwa”.
Jinjina kai Malam Ahmad yayi tare da faɗin.
“Kuyi hakuri duk kan tsanani yana tare da sauƙi addu'a kaɗai zamuyi wa Jameelu amma kamar yanda yace ne Moddibo ka karɓi kuɗin nan sannan kema Fatima ki karɓi kuɗin na shine abu mafi a'ala”.

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana yace.
“Yawwa shine dai ki bani account number inyi Miki transfer”.
Kai Ummi ta shiga Girgizawa hawaye na kwaranya daga Idanunta.
Ganin haka yasa Malam Ahmad ya karbi wayarta tare da fito da account number ya faɗawa Abba Atake Abba ya mata transfer kuɗinta Naira million goma da dubu ɗari takwas kasancewar yana da account number Moddibo Shima Atake ya Masa transfer kuɗinsa.
Anutse ya gyara zamansa tare da Kallonsu cikin sanyin murya yace.
“Nagode da halarcinku agareni musamman ma kai Moddibo Allah Ubangijin ya biya da mafificin alkhairi”.
Atake Moddibo yaji wani irin rauni ya mamaye sa kallon Abba yayi muryarsa na rawa yace.
“Abba akan J ne kake min godiya?”.
Numfashi Abba ya fesar tare da sauƙe ajiyar zuciya yace.
“Toh Aliyu ya zanyi kayi min halarci duk kan inda Aboki na gari ya cika ka cika Ubangiji Allah yasaka da alkhairi Nagode da halarcin ka”.
Cikin raunin murya Moddibo yace.
“Ameen Abba”.
Kallon Ummi Abba yayi kana yace.
“Toh insha Allah sammako zaiyi ya tafi kinsan akwai tazara tsakaninmu da Adamawa kuma can zai shiga jirgin zuwa Abuja”.

“Toh Allah ya kaimu Allah yakai ka lafiya Babana Allah ya kareka”.

Cikin sanyin murya yace.
“Ameen Ummi”.
Miƙewa Abba yayi tare da cewa.
“Toh bari mu tafi”.
Godiya suka masa har sun fita Ummi ta miƙe tare da bin bayansu abakin barandar ta tsaya tare da cewa.
“Babana amma ai zaka dawo daddare muyi sallama ko?”.
Jinjina kai yayi kana yace.
“Insha Allah Ummi zan zo”.
Bayan sun fita kai tsaye gidan Malam Arɗo Abba ya ajiye Moddibo zaiyi masa sallama kana Abba ya wuce gida.

Cikin sanyin jiki Khausar ta isa Bedroom din Mommy, a hankali ta zauna agabanta cikin Muryan kuka tace.
“Mommy kiyi haƙuri kada kiyi fushi dani”.
Tsira mata Ido Mommy tayi ba tare da tace Uffan ba.
Cikin raunin murya Khausar ta haɗa hannunta waje ɗaya kana ta fashe da matsanancin kuka da sheshsheƙan tace.
“Mommy dan girman Allah kiyi haƙuri ki daina fushi dani”.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da fesar da nunfashi kana tace.
“Khausar to ni me zan ce miki?.
Bani da abinda zan ce miki tunda ai hukunci ne kin riga da kin gama yanke shi baki nemi shawarata ko izinina ba”.
Girgiza kai Khausar tayi hawaye na cigaba da kwaranya daga Idanunta.
Ita kuwa Mommy kauda kayi tayi gefe kaba ta cigaba da cewa.
“Kawai kin fadi maganarki gaba gaɗi, sannan koda akeɓance baki taɓa faɗa min tsakanina ni dake ba, sai da kika zaɓi cikin mutane sannan kika faɗa saboda ki kunya tani kin bani mamaki ban taɓa zaton haka daga gareki ba”.

Khausar kuwa kai take Girgiza cikin muryan kuka mai gunji kana Muryanta na rawa tace.
“Mommy nima ina tsoron Modibbo bafa, dan nasan baya sona”.
Kallonta Mommy tayi cikin da mmki ta tsareta da ido tare da cewa.
“Toh kina tsoron Auren Moddibo kuma, akan wani dalili zaki ce zaki Aureshi? Kuma bayan kina sane baya sonki”.
Sunkuyar da kai ƙasa tayi cikin gunjin kuka ta lumshe Idanunta tare da taune Lip ɗinta cikin raunin murya tace.
“Mommy wasiyyar Yah Jameel ne Yah Jameel ne ya roƙi al'farma awajena sannan tun lokacin daya faɗa min yace min wasiyya ya barmin yace koda ya mutu kada in manta ya nemi wannan al'farma awajena”.
Sai kuma ta kasa ci gaba da mgnar sakamakon kuka da yaci ƙarfinta hannu ta sanya ta goge hawayen fuskarta wani na sake zubowa Muryanta na rawa ta cigaba da cewa.
“Aranan da za'a ɗauke Yah Jameel bayan mun taho amota yace min yana neman alfarma awajena in na ɗauka Alfarman da yake nema awajena tamkar wasiyya ce".
Sai kuma ta kife kanta kan cinyar Mommy tana mai sakin wani irin raunataccen kuka murya na karkarwa taci gaba da cewa.
“Mommy a ranar a gabana Yah Jameel yayi ta kuka kamar yaro ƙaramin ya rinƙa haɗani da Allah da Manzonsa cikin sanyin murya da neman alfarma yace dan Allah kada ince bazan yi masa ba yana so koda bayan Ransa in Auri Moddibo”.
Kallon ta kawai Mommy keyi bako ƙyaftawa yayinda itama hawaye ke zubo mata.

Cikin sheshsheƙan Kuka Khausar ta lumshe Idanunta tana tuna lokacin da suka kasance da M Jameel amota yana faɗa mata magana da sauri ta sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta kana muryanta na rawa tace.
“Mommy alokacin Cike da damuwa na kalli Yah Jameel nace ya Jameel Meyesa kake Fadar haka Meyesa kake magana me karyar da zuciya dan Allah kada kace wasiyya nidai ka faɗi ko wace irin alfarma kake so zanyi maka domin kafi ƙarfin alfarma awajena”.
Taja hanci tare da kallon Mommy da yanayin ta ya sauya Muryanta na rawa kana numfashinta na fusga tace.
“Sai yace min Khausar koda ace kin riski labarin mutuwa ta ki tuna da Alfarman da kuma Wasiyyar da na bar miki ki Auri Moddibo idan kuma Allah yasa ina raye zanfi kowa farin cikin ganin An ɗaura Aurenki da Moddibo”.

Ahankali Mommy ta sun kuyar da kanta ƙasa cikin wani irin yanayi na tsananin tausayawa da kuma tsoron Allah Mabuwayi gagara Misali tol-tol haka hawayenta ke zuba jin Khausar taci gaba da cewa.
“Mommy Yah Jameel ya faɗa min cewa ya fadawa. Kakar Moddibo cewa dan Allah ayi Aurena da Moddibo Mommy dan girman Allah ki tayani cikawa Yah Jameel Wasiyyar daya barmin bani da abinda zanyi masa a wannan duniyar wanda zaisa Yah Jameel farin ciki amakwancinsa sama da in cika masa burinsa naji na gani zan rayu da Moddibo duk da nasan ya tsaneni zan rayu dashi sabida darajar Yah Jameel da wasiyarsa zan juri dukkan uƙubar da Moddibo zaimin koda kuwa zai kasheni zan zan cikawa Yah Jameel burinsa”.
Cikin sheshsheƙan Kuka da fisgar numfashi tace.
“Mommy wannan buri da fatan Yah Jameel ne dan Allah da Manzonsa ku barni in cika masa burinsa, tun da muke rayuwa da Moddibo Amakaranta yace ko yaushe kallon mu yake amatsayin mata da miji yace bashi da buri sama da wannan Mommy yace min da ɗan Adam yana da zabi idan ajalinsa yazo to da zai roƙa ajinkirta masa ajalinsa yaga kasancewa ta da Moddibo a Inuwa ɗaya a gidan aure”.
Sai kuma tayi saurin dafe ƙirjinta jin yanda numfashinta ke fusga.
Ta sauƙe wani irin numfashi tare da dafe kanta kana ta cigaba da cewa.
“Yace min Khausy zanso naga wani irin zama zakuyi keda Moddibon.
Yace min zaiso ace Allah ya bashi Aron Rai ya rayu ya ganni gida ɗaya a Inuwa ɗaya da Moddibo yaga wani irin Rayuwar aure zamuyi koda na wuni ɗaya ne.
Allah sarki ya Jameel ashe bazai ganiba.
Dan Allah Mommy ki barni in cikawa Yah Jameel burinsa Mommy Dan Allah kiyi haƙuri ki barni in cikawa Yah Jameel Wasiyyar sa”.
Taƙarashe mgnar tare da fashewa da matsanancin kuka mai masifar ƙuna da ɗaci sai kuma tace.
“Mommy wallahi ina tsorin son Moddibo har Raina, kawai na faɗa ne domin kada Hajja Nana tace dole sai na Auri Yah Aliyu shiyasa na faɗa alokacin, amma bawai dan in kunya taki bane Mommy kinfi kowa sanin halina banyi hakan da wata manufa ba face cika wasiyyar Yah Jameel”.
Numfashi mai tsawo taja cikin Muryanta da baya fita tace.
“Mommy ina matuƙar girmama Yah Jameel Mommy Ina so in cika Masa burinsa wannan shine wasiyyar Yah Jameel na karshe kuma shine karshen maganarmu dan Allah ki tayani cika masa wasiyyar sa na roƙeki”.
Wasu irin hawaye masu zafi ne suka fara bin kuncin Mommy cikin sanyi da raunin murya tace.
“Insha Allahu Khausar da izinin Ubangiji za acikawa Jameel burinsa...!



*LITTAFIN SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama ba haƙƙin kowa a kanki 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. In dai baki biyaba kika karanta to na satane, kuma na Allah ya isane*



By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2 page 7*
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha'awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni'ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al'ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban lissafa. Sune manyan alamomin infection.
Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.
Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni'ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya Zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.
KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni'imomin ki, da sha'awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA'AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau, duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha'awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor's suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa.
INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi'izinillahi ta'ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma'ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya'ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER'N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA'AURATA.



Khausar kuwa cikin sanyi da rauni tunowa da M Jameel da ya dawo mata sabo ahankali ta kife kanta abakin gado tafashe da kuka mai cike da fargaba da kuma tsoron Allah.
Kallonta Mommy tayi cike da tausayawa tace.
“Kiyi haƙuri ki daina kuka Khausar addu'a zaki yiwa Jameelu sannan Insha Allah za acika masa burinsa da wasiyyar daya bari in Allah ya ya nufa”.
Ta ƙare mgnar tare da sauƙe numfashi.
Idanta ta tsaida kan Khausar da har zuwa lokacin kanta ke kife jikin gado cikin tausasawa tace.
“Amma kisa Aranki cewa haƙuri zakiyi da duk rayuwar da zakije ki tarar, sannan wasiyya zaki cikawa Jameel, sannan ki sani shi zaman Aure kansa Ibada ne, koda ana son juna wata ran akanji babu daɗi, bare ke da dama kin san matsayinki a wurin wanda kike ganin kina da ƙarfin guiwar zama dashi,
dan haka kisa Aranki cewa ba lallai ne kiji daɗin zama da Moddibo ba, amma tunda kince kinji kin gani zakiyi abinda Jameel ya buƙata kafin barinsa duniya zan biki da addu'a Ubangij ya tabbatar da al'khairi tunda har iyayensa duk ya gayawa kuma tuni suma sun sa baki a mgnar, kinga ni bani data cewa tunda kun mamayeni”.
Cikin rauni Khausar ta sake fashewa da sabon kuka tabbas gaskiya Mommy ta faɗa ba Lallai tayi zaman daɗi da Moddibo ba tunda baya sonta hasalima koda kallonta ne baya sonyi tuno da hakan yasa wasu hawaye masu masifar zafi suka zubo mata tama sani tabbas cikin uƙuba zata rayu dashi, to amman ya zatayi rayuwa Yah Jameel al'ƙawarin amincewa da batun auren Amininsa.

Cikin sanyin murya Mommy ta cigaba da cewa.
“Sanin bake kaɗai Jameelu ya barwa wasiyya ba yasanarwa da Kakar Moddibo sannan ya sanarwa Umminsa da kuma Abbansa nima da farko hankalina ya tashi.
Amma yanzu barina ɗakin Abbanku yake cemin shekaran jiya da daddare Abban Jameel da Malam Ahmad da malam Arɗo sunzo da batun, abinda yasa baiyi mgnar ba Hajja Nana bata bashi dama bane daya mata bayani”.
Wani irin rauni, Kunya,damuwa da rasuwar Jameel ne suka dawowa Khausar alokaci ɗaya.
Cikin sanyi jiki ta miƙe ta nufi ɗakinta tana shiga ta faɗa kan gadonta kana ta cigaba da kuka cikin rauni tasan dai iyaye keyiwa ƴaƴansu auren dole a tarihin duniya, sai gashi ita dai itace zatayiwa kanta da kanta auren dole bisa wasiyar Yan Jameel malami na musamman mai matsayin babban Yaya wanda ita dai da fari har ranta shi takeyiwa kallon mai iya jiɓantan lamuranta.

Washe gari da safe Misalin ƙarfe 8:00 Anutse Moddibo ya fito daga falonsa cikin wani ɗanyen Boyel Sky blue Fuskarsa tayi fayau manyan Idanunsa dake lumshe sun sake girma sabida ramar da yayi, sajensa ya sake yawaita yayi fadi da cika, yana kuma ɗan hargitse alamun an kwana biyu ba'a gyarashi.
Kafadarsa na dama rataye da jakar laptop ɗinsa daga zip ɗin gefen wayoyinsa ya zira, sai hannunsa dake riƙe da jakar kayansa, a hankali yake tafiya, yayinda jikinsa ke fitar da sanyayyan ƙamshin tularen sa.
Kai tsaye sashen Innayi ya nufa ahankali Innayi dake breakfast ta ɗago Kai ta kallesa Anutse ya ƙarasa tare da zama gefenta.
Da mamaki take Kallonsa ganin kamar alamar cikin shirin tafiya yake.
Cikin sauri tace.
“Aliyu”.
Kallonta yayi da sauri domin bata fiye kiransa da Aliyu ba sai da babban dalili.
Cikin sanyin murya yace.
“Na'am Innayi”.
Hannunta riƙe da kofin tea tace.
“Ya haka? ya na ganka kamar mai yin tafiya?”.
Kai ya gyaɗa mata tare da tanƙwashe ƙafafunsa kana ya fuskanceta cikin ƙoƙarin danne damuwarsa kana yana mai jin farin cikin zai bar garin Gembila haka nan ya tsinci kansa da jin farin cikin yau dai zai bar Jahar Taraba domin baki ɗaya garin ya fice masa arai cikin sanyin murya yace.
“Innayi ba kama bace tafiyar ce”.
Cike da mamaki ta ɗago kanta kana tace.
“Aliyu tafiya zaka yi amma ban sani ba sai dai in ganka kana fita da jaka haka?”.
Ahankali ya riƙo tafin hannunta acikin nasa cike da mmkia yace.
“Kiyi haƙuri Innayi tafiyar ce nima tazo min a bazata kuma ba jiya Abban Jameel ya gaya mikiba”.

Kai ta girgirza tare da cewa.
“A'a bai gaya minba zakayi tafiya ba, ya dai cemin yana neman al'farma ni kuwa nace umurni kawai zai baka kamar yadda yake bawa Jameel ni na amince duniya da ƙiyama, ban bari yamin bayaniba sabida kar yaga kamar zan hanaƙa yaji ba daɗi. To waima Tafiya zuwa ina zakaje?”.
Cikin kwantar da murya yace.
“Tafiya zuwa Marocco!”.
Cikin tsananin kaɗuwa ta zaro idanunta baki ɗaya lokacin ɗaya ta ƙware tare da fara tari sakamakon ƙwarewa da tayi da dankalin dake bakinta”
Moddibo kuwa ganin yanda ta ƙware yasa yayi saurin daukan kofin ruwa ya miƙa mata tare da cewa.
“Sannu”.
Amsa tayi tasha amma still tarin bai tsaya ba lokaci ɗaya Idanunta yayi ja zufa ya shiga tsats-tsafo mata agaba ɗaya ilahirin jikinta shi kuwa Modibbo ido ya zuba mata tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login