Showing 21001 words to 24000 words out of 218703 words

Chapter 8 - Sakayyah 2 Hausa Novel Complete

kai Abba yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya kana yace.
“Toh kuma gashi nima kuma ban cika lafiya ba kullum ina fama da matsanancin ciwon kai, dama can a tsarina Jameel ne zai wakilceni aiyi aikin”.
Cike da tausayawa Manager yace.
“Ayyah Allah Ubangiji ya sawwaka.
Yallaɓai sai dai a cigaba da haƙuri Jameelu kuwa Allah yajiƙan sa ya gafarta masa, amma ya kamata asamu awakilta wani tunda bana nan ga kaya sun iso gashi audugar da aka tura da Nigeria ta iso, kuma tunda tazoma bamuyi mgnar ba sabida wannan iftila'in ɓatan Jameel”.
Jinjina kai Abba yayi tare da cewa.
“Toh shikenan, amman bazan samu zuwa ba, domin nima kaina ba lafiyar bace dani amma Insha Allah zan turo Aliyu yazo zaiyi dukkan abinda ya dace”.
Kai Manager ya gyaɗa kana yace.
“Toh Allah ya bada iko dan kaya sun iso tun jiya suketa ƙoƙarin za afara aikin sauƙe kayayyakin da ayyukan su masu motocin ma sun matsa min don suna so su fita cikin Company'n dan sunce basu son su wuce kwana biyar zuwa takwas, in sun wuce haka kuma sai in za'ainta biyansu ne”.
Cikin sanyin murya Abba yace.
“Toh shikenan ba komai Insha Allah zanyi wa Moddibo magana zai zo yanzu zan kira shi in sha Allah in this week zai shigo Marocco”.

Acan gidan su Moddibo kuwa abakin ƙofa Baffa Jimeta yayi Parking din motarsa cikin sauri Hajja Nana ta buɗe Murfin motar ta fita tare da buɗe gate din gidan tashiga.
Da kallo Baffa Jimeta da Baffa Liman suka bita har ta shige cikin gidan.

Ita kuwa tana shiga tun daga ƙaramin gate da zai sadata da ɗaya sashen ta fara doka sallama tare da faɗin.
“Innare! Innare!! Innare!!!Bakya Nan ne!?”.
Cikin sauri Innayi ta fito daga ɗakinta da murmushi afuskarta tace.
“A'a wannan muryar wa nake ji kamar Hajja Nana”.
Kai Hajja Nana ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh Innare nice dai”.
Murmushi Innayi tayi tare da ƙarasawa kusa da ita tace.
“A lale maraba Barka da zuwa Maraba maraba mu shiga daga ciki”.
Kai Hajja Nana ta gyaɗa sannan suka shiga ciki cike da kulawa Innayi ta ajiye mata ruwa da abin taɓawa Sannan ta kalli Hajja Nana dake ta cika tana batsewa tace.
“Hajjia Nana mutan maka da Madina Bismillahi”.
Girgiza kai Hajja Nana tayi kana tace.
“A'a bazan iya cin komai ba barshi kawai Nagode”.

“Meye faru kuma?”.

Girgiza kai tayi cike datakaici tace.
“Ƴaƴan zamani kai Allah ya kyauta”.
Zama Innayi ta gyara tare da cewa.
“Waya taɓoki?”.
Ƙwaffa Hajja Nana tayi kana tace.
“Hegiyar yarinyar nanne fitsararriya gantalalliyar yarinya da batasan abin da ya dace da kanta ba, ana nuna mata gabas tana ga yamma.”
Sai kuma ta fesar da numfashin kana taci gaba.
“Uyumm yarinya har an kai matakin da yarinya ƙarama ana magana tana mgna ta fetsare Idanunta ta kalli idanun Magabatan ta tace wai tayiwa kanta zaɓin mijin Aure”.

Ajiyar zuciya Innayi ta sauƙe tare da kallon Hajja Nana kana tace.
“Wace yarinya ce haka”.
Cike da takaici Hajja Nana tace.
“Khausar mana”.
Cike da Mamaki Innayi tace.
“Ha'a Khausar kuma wace Khausar ɗin?".
Jinina kai Hajja Nana tayi tace.
“Eh Khausar jikata”.
Gyaɗa kai Innayi tayi tare da cewa.
“Eh na fahimta.”
Kallonta Hajja Nana tayi kana tace.
“Yanzu na fito daga gidan Lamiɗo ai”.
Cike da mamaki Innayi tace.
“Dama Khausar ɗin gidan Lamiɗo itace jikar ki?”.
Kai Hajja Nana ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh itace jikata ɗin mana”.
Numfashi mai nauyi Innayi ta sauƙe tare da gyara zamanta kana tace.
“Toh ki kwantar da hankalin ki me yayi tsanani aciki?”.
Ƙwaffa Hajja Nana tayi tare da kallon Innayi tace.
“Mun zo da batun Aurenta da ɗan Uwanta, sannan dama anan cikin zuri'ar gidan Lamiɗo kin sansu Zuri'ar Mayune to wai akwai wani yaro Naseeru da yake sonta”.
Gyara zama Innayi tayi tana kallonta.
ita ko Hajja Nana ta cigaba da cewa.
“To Ni duk atunanina ma idan batason Aliyu Naseeru zata ce tana so amma wai.
Yarinya nan tace wai wani take so, saboda rainin hankali wai Uwar ma batasan da batun ba”.
Ajiyar zuciya Innayi ta sauƙe tare da fuskantar Hajja Nana tace.
“Toh me abin tashin hankali kinsan zamanin da dana yanzu ba ɗaya bane, abinda aka mana muka jura na yanzu ba zasu jura ba, bama a isa ayi musu ba, bare kuma har aje matakin su ɗauka, amma yanzu kisha ruwa ranki yayi sanyi tukun”.

Numfashi Hajja Nana ta fesar kana tace.
“Wallahi baki daya a fusace nake yarinya tayi matuƙar ɓata min rai ta fusata min zuciya ni zata wa tsawa ƙasa a ido.
Baffanta yayi tattaki gari ya garara yazo amma tace bata son ɗan sa saboda bata da mutunci”.
Innayi kuwa ruwa ta miƙa mata tare da cewa.
“Ke dai kisha ruwa zuciyarki yayi sanyi”.
Karɓa tayi tare da kafawa abakinta ta fara sha

Acan Falon Moddibo kuwa zaune yake akan Sallaya bayan ya idar da sallar Walha hannunsa riƙe da Alkur'ani yana karanta suratul Tauba yana Aya ta ɗari da ashirin da bakwai yaji wayarsa na Vibrating Kallon screen ɗin wayar yayi ganin sunan Abba yasa ya cigaba da karatun kasancewar saura Ayoyin biyun ƙarshe yasa ya cigaba yana ƙarasawa ya shafa addu'ar dai-dai lokacin wani sabon kiran ya sake shigowa.

Anutse ya ɗaga wayar tare da kaiwa Kunnensa yayi Sallama.
Cikin sanyin murya Abba ya amsa tare da cewa.
“Aliyu”.
Ahankali Moddibo yace.
“Na'am Abba ina kwana ya ƙarfin jikin naka?”.
Cikin sanyin murya Abba yace.
“Lafiya lau Alhamdulillah ya gida? Aliyu ya kwana biyu duk ban jika ba”.
Ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauƙe kana yace.
“Wlh kuwa Abba ya ƙarfin jikin naka?”.
Ahankali Abba ya sauƙe numfashi kana yace.
“Jiki da sauƙi”.
gyara zamansa yayi tare da cewa.
“Toh Abba Allah ya ƙara sauƙi amma lafiya kuwa?”.

“Eh lfy lau. Yanzuma nayi waya da.
Mgnar Company na dake Marocco, to dama akwai kayan da mukayi Order sabbbin Injuna, sabida tsoffin sun fara samun matsala kasancewar sun kwana biyu to an kawo sabbin kuma Manager baya nan yaje duba lafiyarsa, kuma yanzu dole ana buƙatar sai akwai sahalewar wani da kuma sa hannu na kafin afara sauƙe kayan dole kuma akwai buƙatar tsayeyye da zai sa ido kan aikin kafa musarrafan da za'ayi”.
Tunda Abba ya fara magana Moddibo ya lumshe idanunsa yana cigaba da sauraron sa.
Abba ya cigaba da cewa.
“To yanemi da Inje, to ni kuma bazan iya ba, kullum ina fama da ciwon kai kuma kaga ga yanayin da nake ciki har yanzu ana zuwa min gaisuwa, shiyasa nake so ka shirya ka wakilceni, kaje ka fuskanci aikin idan yaso idan komai ya dai-dai-ta aka fara aiki in anyi rukunin forko saika dawo ba zaka daɗe ba”.
Moddibo kuwa shiru yayi tare da jingina bayansa da jikin Cushing.
Daga ɗaya ɓangaren Abba yace.
“Hello! Aliyu Hello!!, Hello!!! Aliyu kana jina kuwa?”.

Shi kuwa Moddibo cije Lip ɗinsa na ƙasa yayi Aransa yace bana son garin Gembila baki ɗaya jihar Taraba ta fitar masa ji yake tamkar wuta ake watsa masa aduk lokacin daya tuna shi kaɗaine ke rayuwa babu J ɗinsa, babu wani akusa dashi idan zai tafi masallaci shi kaɗai sannan idan zai dawo shi kaɗai kana idan zaici abinci shi kaɗai baki ɗaya ilahirin garin ya masa duhu kana ya masa ƙunci sam baya son zama acikinsa Nigeria kanta ta fice masa arai.
To amma kuma idan ya tafi Ummi ya zatayi.
Cikin sauri ya buɗe Idanunsa dake lumshe jin Abba na cewa.
“Aliyu ya dai kayi shiru baka ce komai ba?”.
Numfashi mai tsayi yaja kafin ya sauƙe ahankali cikin sanyin murya yace.
“Abba Ummi idan na tafi nayi nesa da Ummi ba zata ji daɗi ba sannan Innayina, da waye zan barta?”.
Ahankali Abba ya sauƙe Ajiyar zuciya tare da sauƙe dogon numfashi kana yace.
“Ba komai Aliyu Insha Allah za ayi ƙoƙari akula da duk kan al'amurran su sannan ba daɗewa zaka yiba”.
Cikin raunin murya Moddibo yace.
“Abba Ummi tace idan banje wajenta ba hankalinta na tashi damuwarta na tsananta. Abba bana son ganin Ummi cikin wani yanayi, Innayi na kuma bata da kowa a duniya saini in nayi nesa da ita ya zataji”.
Ajiyar zuciya Abba ya kuma sauƙe kana yace.
“Bakomai Insha Allah za muyi magana da Malam Ahmad za'a kwantar mata da hankalin ta, sannan dama inaso zamuyi magana dakai Innayi kuma kada ka damu zata iya dawowa gidana kafin ka dawo ko gidan Ummin”.
Ahankali Moddibo ya gyara zaman wayar akunnensa.
Yayinda Abba kuma ya cigaba da cewa.
“Akan kuɗin da aka har haɗa aka turo wanda Fatima ta saida Sarƙoƙinta da kuma motarta kazo zamuyi maganar ka karɓi kuɗin Asiya mata wata motar sannan sauran ta ajiye idan zata sai wasu kadarorin ma ta ajiye”.
A hankali ya gyara zamansa tare da rintse idanunsa kana ya cigaba da cewa.
“Sannan kaima naga motar da kake Amfani da ita tsohuwar mota ce ya kamata ka siya wata sabuwar motar ka riƙa hawa”.
Girgiza kai Moddibo yayi cikin raunin murya yace.
“Abba me zanyi da wata sabuwar mota Abba bana son Kuɗin dan Allah kadaina maganar Abba ni dai bana son Kuɗin Abba bana son su”.

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da girgiza kai kana yace.
“A'a Aliyu ya za ayi kace haka?”.
Moddibo kuwa rumtse idanunsa yayi tare da taune Lip ɗinsa na ƙasa kana yace.
“Toh Abba me zanyi da kuɗin da suka kasa ceton min J me zanyi da kuɗin da suka kasa temakon ceto mun rayuwar J Abba bana son Kuɗin Abba dan Allah kada kayi min maganar kuɗin”.

Numfashi Abba ya fesar cikin sassauta murya yace.
“Aliyu kayi haƙuri dole muyi maganar kuɗin nan kaima kace baka son maganar kuɗin nan to ni kuma me zanyi dasu Aliyu kayi haƙuri kaji sannan dan Allah kayi ƙoƙari ka shirya ka tafi Marocco E PASSPORT naka zaka fitar dan Allah, mu fara neman damar fitan ko ta online zakayi komai, cikin makon nan nakeso ka tafin in Allah yasa ka samu buse”.

Shiru Moddibo yayi lokaci da yaji maganar Bashir ya dawo masa kunne na cewa yayi mafarki da M Jameel sannan yace ya faɗa masa cewa ya taya Abba harƙan kasuwancin sa dogon numfashi yaja mai sanyi duk da cewa baya so ya tafi ya bar Ummi da Innayi amma ji yake ya tsani zaman cikin Taraba da Gembila baki ɗaya Jahar Jaligo ta fita Aransa ga kuma tuno da abinda Bashir di ya faɗa ya sauƙe numfashi cikin sanyin murya yace.
“Toh shikenan Abba bari nayi magana da Innayi da Ummi”.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Toh shikenan idan kunyi maganar dan Allah ka kirani yanzu yanzu ina jiranka”.
Cikin sanyin murya Moddibo yace.
“Toh shikenan ba matsala”.
Sannan ya katse kiran ya miƙe.

Acan ɗakin Innayi kuwa Hajja Nana na gama shan ruwan ta ajiye Cup ɗin tana sakin ajiyar zuciya.
Ahankali Innayi tace.
“Toh kici abinci”.
Girgiza kai tayi tare da faɗin.
“A'a bazan iya cin abinci ba barni kawai”.
Kallonta Innayi tayi kana tace.
“Toh Wai me ya tsananta ne har ya tayar miki da hankali haka?”.
Ƙwaffa Hajja Nana tayi tare da riƙe haɓa cike da takaici tace.
“Wai fa Khausar cewa tayi bata son Aliyu wai wani take so”.
Gyara zama Innayi tayi kana tace.
“Wai wani waye shi wanda take son?”.
Cikin fushi Hajja Nana taja dogon tsaki tare da cewa.
“Wai wani wai shi Moddibo take so Malamin Makarantar su inji Lamiɗo”.
Cikin sauri Innayi ta kalleta tare da jan dogon numfashi kana ta lumshe Idanunta tare da buɗe su cikin sanyi ta kalli Hajja Nana kana tace.
“Moddibo?".
Kai Hajja Nana ta gyaɗa tare da faɗin.
“Eh Moddibo?”.
Jinjina kai Innayi tayi kana tace.
“Kuma wai malamin su?".
Still Kai Hajja Nana ta gyaɗa mata.

Dai-dai lokacin Moddibo ya isa bakin barandar ɗakin Innayi yana son ya mata bayanin Abba ya kira sa akan yaje yasa yazo wurinta, yana taka step ɗin firko ne.
Ya jiyo sautin Muryan Innayi na cewa.
“Toh Moddibo ai jika nane Hajja Nana.”
Sai kuma tayi murmushi mai cike da jin dadi kana taci gaba da cewa.
“kinga shikenan faɗuwa tazo dai-dai da zama Aliyu jikana aishine Moddibon kinga sai muyi tuwonmu manmu”.
Cikin sauri Hajja Nana ta miƙe tare da kallon Innayi kana ta zare ido sannan ta buga hannunta aƙirji tare da cewa.
“Ji kanki?”.
Jinjina kai Innayi tayi tare da faɗin.
“Eh jikana ne Aliyu”.
Still Hajja Nana na tsaye cikin zare ido tace.
“Shine Moddibo kenan?".
Kai Innayi ta gyaɗa mata cikin tabbatarwa.
Ita kuwa Hajja Nana cikin wani yanayi tace.
“Sannan kuma shine Malamin nasu?”.
Kai Innayi ta kuna gyaɗa mata kana cikin sanyi tace.
“Tabbas shine jikana Moddibo”.
Cike da mamaki Hajja Nana tace.
“Kenan jikanki ne Moddibo wanda Khausar ke so?”.
Still Kai Innayi ta gyaɗaa karo na barkatai tare da cewa.
“Eh".
Cikin wani irin masiyacin kallo Hajja Nana ta kalleta tare da cewa.
“Aikuwa baza ta saɓu ba bindiga aruwa, ai wannan ma ta tsuniyace mara wanzuwa ai wannan ma zancen banza ne, wannan ƙarya ne wlh. Khausar bata isa ba mu zata lalatawa tushe da asalin zuri'a”.
Cikin sauri Innayi ta mike tare da zare ido ta kalli Hajja Nana cike da mmki tace.
“Wannan wace irin kalma kike faɗa?”.
Gyara tsayuwa Hajja Nana tayi kana tace.
“Toh Innare waye bai san cewa jikanki bashi da asali ba, wani mahaukacin ne zai ɗauki ƴa ya baku? waye zai so haɗa zuri'a da jikan ki da bashi da asali! ɗan shege da kika samu akwararo ɗan da ba'asan tushe da Asalinsa ba!!!”.
Cike da matsanancin mamaki Innayi ke kallonta Hajja Nana ta cigaba da cewa.
“Ɗan da ba asan tabbacinsa ba asan asalinsa ba. Yaron da ake da tabbacin cewa ba ɗan sunna bane ɗan zina ne. Shine za ahaɗa zuri'a ta dashi ai wallahi wannan ba zata yuba”.
Ta ƙarashe mgnar cikin yanayinta na ba shina ba sabo.
Cikin fushi da ɓacin rai Innayi ta watsa mata wani irin kallo tare da cewa.
“Ke dakata Hajja Nana ki kama kanki".
Dogon tsaki Hajja Nana taja tare da cewa.
“Bazan kama ba, tabbas abinda na faɗa gaskiya ne, idan har yana da uba to waye Ubansa tun da kuka zauna tsawon rayuwarku shekaru talatin da acikin Garin Gembila waya san Asalinsa wayasan Ubansa wayasan tushensa na faɗa na ƙara fada da ƙarfi shi ɗan shege ne ke kuma magajiya”.
Moddibo dake baranda atsaye ne, yayi wani irin jan numfashi tare da rumtse idanunsa domin tamkar sauƙan aradu haka maganganunta suka ratsa ƙwaƙwalwarsa zuwa dodon kunnensa.
Hajja Nana kuwa cikin fushi da ɓacin rai tace.
“Shegene jikan naki na faɗa zan kuma faɗa”.
Wani irin kallo Innayi ke binta dashi zuciyarta na wani irin tafarfasa ta kalli Hajja Nana kana tace.
“Tabbas babu wanda yasan asalin Jikana sannan babu wanda yasan ina ne tushen jikana amma ke dai baki isa ki jefe mu da mugayen kalamai irin wannan ba”.
Taɓe baki Hajja Nana tayi tare da watsa mata Harara kana tace.
“Na nawa kuma ance da kuturu Allah ya la'ance ka, jikan ki dan kwararo ne ɗa mara tushe da galihu”.
Cikin tsanananin tashin hankali da ruɗu da wani irin tsinkewar zuciya mai tafiya da nunfashi Moddibo ya dafe kansa da hannu bibbiyu tare da rintse idanunsa...!


Littafin SAKAYYAH dai na kuɗi Hajia ba free book bane dan haka ki saya ki karanta cikin Aminci da salama 1k ne kacal kuɗin samun damar karantawa 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar
biyanki ta WHATSAPP 09097853276



By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 5*

Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*


Runtse idanunsa yayi da karfi, tare dasa hannunsa duka biyu ya matse kansa, sabida yadda ya fara jin kansa yana juyawa tare da sarawa, yayin da kalaman Hajja Nana ke dukan tsakiyar ƙoƙon kansa yana ratsa ƙwaƙwalwar kansa tare da jin suna ratsa kunnuwansa suna yawo tamkar yanda aradu ke yawo asararin samaniya, baki ɗaya idanunsa sun juye sun kaɗa sunyi Jawur, kab ilahirin jikinsa rawa yake kar-kar-kar tamkar mazari cikin wani irin sauri zuciyarsa ke bugawa da kaso Cassa'in da tara cikin ɗari, tana mai wanzar da jini litter-litter a cikin dukkan daƙiƙu yana watsashi wa jijiyoyin jikinsa.
Hakan yasa tuni rigarsa ta fara jikewa da zufa, duda yanayin garin Gembila da ba'a musu zafi.
Sai ga tashin hankali ya sashi tsats-tsafo zufa sabida yadda zuciyarsa ke bugawa da Masifaffen ƙarfi yayin da numfashinsa ke fusga tamkar zai bar ganganar jikinsa, cikin tsanananin tashin hankali da wani irin masifaffen juyi da kansa keyi ya ƙara matse kansa da hannu bibbiyu, da ƙyar ya iya daga ƙafarsa ya sauka daga barandar ya nufi side ɗinsa yana tafiya tare tangaɗi tamkar ɗan maye yayin da kuma jiri ke ɗibarsa.

Yana cikin tafiya tamkar zai faɗi ya tsinkayo muryar Innayi cikin tsananin fushi da takaici cikin zafin zuciya tace.
“Zaki sha mamaki kuwa.
Hajja Nana zan nuna miki ƙarfin iko da isan ɗan shegen da kike faɗi. Zaki gane kinyi kuskure ambatonsa da wannan sunan da yafi ƙarfinsa. Auren nan kuma da izinin Ubangiji tamkar anyi sa angama ma, in dai wannan auren nen kika tashi ki kace zaki yaƙesa sannan kika ce zaki hana toki sa. Aranki anyishi an ɗaura shi angama domin ke dai baki isa ki haramta abinda Allah ya halastaba wlh muddin ina raye toh in Sha Allah kamar ma anyi auren nan an gama zan shayar dake mamaki”.
Wani irin kallon rainin hankali me ɗauke da zafin zuciya Hajja Nana tabi Innayi dashi.
Ita kuwa Innayi. Cikin fushi ta cigaba da cewa.
“Babu wani mahaluki na duniya daya isa ya hana wannan ɗaurin Auren sai Ubangiji daya halicci sammai da ƙassai. idan har kinga wannan Auren bai kasance ba to daga Rabbus Sanawati ne amma ba daga ke Hajja Nana mai kaɗa kai kamar Ƙadangariya ba”.
Wuhuhu ina wuta Hjja na ta faɗa ciki.
Cikin fushi da hatsala Hajja Nana dake ƙoƙarin fita ta tsaya tare da juyawa ta kalleta sai kuma tayi murmushi tare da gyara tsayuwar ta kana tace.
“Wani ƙarfin iko ko kuma isa. Ɗan shege ke dashi? Ai sai dai kuje kunemi watsatstsiya ƴar gaba da Fatiha ku Aura masa, amma dai ba jikata dake da asali da tushe ba zuri'ata tayi miki nisa sai dai hange daga nesa?”.
Afusace Innayi da Idanunta suka kaɗa tamkar garwashi tace.
“Tabbas zaki ga isa da kuma ƙarfin Iko irin na ɗan shegen da kike faɗa agaban idanunki za'a ɗaura Aurensa da Khausar sannan ya ɗauketa su tafi ke babu yanda kika iya, zakisha mmkin ganin tushensa daya girmi tunaninki ya kuma zarta zatonki. domin ke ba kowa bace a kansa, Allah ya wadaran aminiyar da bata mutunta amintaka, kin kasance mara ɗa'a da sanin ya kamata!”.
Ita kuwa Hajja Nana mugun kallo ta watsawa Innayi tare da nuna kanta da tsaya kana tace.
”Ni kika faɗawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login