Showing 144001 words to 147000 words out of 218703 words

Chapter 49 - Sakayyah 2 Hausa Novel Complete

cewa.
“Didi Azumi nakeyi”.
Kai Modibbo ya ɗan jinjina dan zuwa yanzu dai ya fara gamsuwa da sauyawar Dr Jameel, musamman yadda ya dage da azumi dan daƙushe sha'awarsa.

Ita kuwa Didi kai ta jinjina sannan ta sawa kanta suka fara cin abincin, yana ganawa ya miƙe.
Da sauri tace.
“ina kuma zakaje, kasha maganin ne?”.
Dai-dai lokacin Dr Jameel ya iso wurin kujera yaja ya zauna yana cewa.
“Eh Didi yasha”. Sai kuma ta juyo ya kalli Modibbo tare da cewa.
“Amman fa kamar ba zazzabin kawai ke damunsa ba na lura yana yawan miƙa kamar wanda jikinsa ke masa ciwo, bini bini ya dafe ƙugunsa”.
Da sauri Didi ta miƙe tare da turawa Dr Jameel ɗin womers ɗin abinci gabansa kana tayi cikin falon dan tasan ba ƙaramin aikin Dr Jameel bane yayi ɓaram-ɓarama, a gabanta haka yasa ta ma mance yace yana azumi.
shi kuwa Modibbo wani irin harara ya rabkawa Dr Jameel tare da cewa.
“Ace mutum shi bakinsa baya iya shiru”.
Murmushi Dr Jameel yayi tare cewa.
“Na lura baka taɓa sanin maceba, da alamu jiya kuma kayi yaƙin fatauci shiyasa ƙugu da jinyoyi suke ciwo, ah aini da na ɗauka kai kam ba abinda zakayi da mace yadda kake wasu abu kamar waliyi, shine tun ba'aje ko inaba kaje kai ta karya ƙugu ka kwashi Gara, yanzu kuma jiki magayi dan na lura baka sararawa yar mutaneba”.
Sai kuma yayi saurin dage kansa tare da sakin kara jin yadda Modibbo ya kaiwa bakinsa bugu.
Dariya ya fashe dashi tare da bin Modibbo da ido kana ya dawo tsakiyar falon.

A hankali ya nufi Side ɗin sa saboda wani irin bacci da yake ji ga zazzaɓin ya fara masa yawa alamar maganin ya fara kokawa da Zazzaɓin yana shiga ya kwanta bisa 3 sitter...

Jakadiya kuwa kai tsaye ɗakin Tarihin Masarautarsu takai ƙyallen budurcin Khausar.
anan aka ajiye wannan frame ɗin kana ta ɗauko sanda da Jigidan Zinare mai tambarin Masarautar Mouley sai chain na ƙafa shima na Zinare ne kuma munduwa mai tambarin Masarautar, da dai wasu kaya masu masifar kyau da ɗaukar hankali kai tsaye sashen Didi ta shiga kana ta kalli Didi dake zaune kan 2sitter daga ƙasa Carpet ta zauna tare da faɗin.
“Yawwa Didi gashi an gama haɗawa”.
Sanyayyan Murmushi Didi tayi hakan ganin abin sai ya tuna mata da lokacin da aka kai mata nata cikin sauƙe ajiyar zuciya tace.
“Toh shikenan mu tafi mu nunawa Niyna daga nan mu tafi da ita”.
Miƙewa Jakadiya tayi suka nufi Side ɗin Niyna daga nan kuma suka shiga sashin abokan zamanta suka nuna musu kana suka wuce wurinsu Ummi.
Hajja Nana, Innayi da Hajja Umma suka samu azaune suna hira.
Yayin da Ummi Khausar Asma'u Dije da Asiya ke bedroom.
Zama Didi sukayi kana suka sa aka kira su Ummi,Hajiya Bunayya,Aunty Ruƙayya, Aunty Hajara duka suka fito falon Jakadiya ce tayi musu bayanin cewa.
“Ga wannan Sandar amma yanzu dai an nuna muku ne saboda tabbacin cikekken tukuicin da aka samu daga Masarautar Mouley ce”.
Wani irin farin ciki ne ya mamaye baki ɗaya ilahirin zuciyoyinsu saɓanin Hajiya Bunayya da take jin wani sabon kunci da tashin hankali aƙahon zuciyarta.
Jakadiya kuwa cike da alfahari ta cigaba da cewa.
“Kuma yanzu za'a sake mai dashi cikin karagar masarautar tarihin gefenta sai sanda aka samu ɗa namiji ya cika Shekara ɗaya ranan za'a mallaka mata sandar ahannunta saboda sandar shine zai nuna shaidar Lalle gadon Masarautar a ɗakinta yake”.
Cike da matsanancin farin ciki Innayi tace.
“Alhamdulillah abinda ake ƙi dai shi ya tabbata in Allah yaso Sarauta dai tana nan ta tabbata a ɗakin Lalla Didi”.
Niynah kuwa murmushi take tare da faɗin.
“Alhamdulillahi burin magauta bai cika ba”

Acan ɗaki kuwa Asma'u ce ta kalli Khausar tare da ƙyalƙyalewa da dariya kana tace.
“A'a manya gari yane duk bakinki ya mutu. Yah Moddibo yayi aiki kenan”.
Kallonta Khausar tayi tare da tura baki cikin yanayin jin bacci saboda magungunan data sha ta harareta da kumburarrun idanunta sai kuma ta murguɗa baki.
Ware idanu Asma'u tayi tare da faɗin.
“Eh lallai yarinyar da sauran ki har yanzu Yah Moddibo bai ladab tar dake ba tunda har kika samu idanun harara da bakin tsiwa”.
Wani kallo Khausar tayi mata cikin dishsheyar murya mai cike da sanyi da rauni alamun ko yanzu tana iya kuka a hankali tace.
“Hmmm Ladabtuwa na nawa kuma, sai dai kuma in kasheni ya rage yayi”.
Sai kuma ta lumshe idanunta hawaye masu zafi suka zubo ahankali ta taune lips ɗin ta na ƙasa tare da cewa.
“Naji azabar da tunda Uwata ta haifeni ban taɓa ji ba, salon mugunta kuwa babu wanda Yah Moddibo bai haddace ba bayan makarantar Hadda da yaje ina ga har da na koyon mugunta da zalumci yaje yayi Mater's ya iya salon mugunta iri da kala, Ni dai Allah ya sani ba abinda zance sai Allah ya saka min kuma inyi ta Addu'a Allah ya tsareni da sherrin muguntarsa”.
Ta kare mgnar murya na rawa, da kuma iyakar gskyar zuciyarta.

Wani sabon dariya Asma'u ta ƙyalƙyale dashi harda riƙe ciki kana tace.
“Uhm lallai su Fattanah anji maza wato har Master's Yah Moddibo yayi a fannin mugunta”.
Cikin kauda kai Khausar ta runtse idanunta tare da cewa.
“Ayyah am Asma'u kiyi dariya son ranki kema kwana nawa ne zaki zo irin wannan Matsayin?”.
Murmushi Asma'u tayi tare da miƙa mata wayar kana tace.
“Gashi naga Mommy ke kiran”.
Tana karɓan wayar ta fashe da kuka.
Shiru Mommy tayi tana jin shesh-sheƙan kukanta kusan minti biyu ta ɗauka tana kukan kafin cikin rawan murya tace.
“Momy ina kwana”.
Ajiyar zuciya Momy ta sauƙe tare da cewa.
“Kin gama kukan?”.
Kamar jira take sai kuma ta sake fashewa da sabon kuka cikin sauƙe numfashi Momy tace.
“Meyesa bakya girma ne Mamana. ai rayuwar nan da kike gani hakuri ake musamman mace dole abubuwa suzo maka ayanda ba kayi zato ba, ki koyi dauriya Khausar agaban surkunan ki kike fa, kinga za'a barki agarin da babu kowa naki ki iya dauriya ke macecefa wata rana ma haihuwa zakiyi”.
Kuka ta kuma fashewa dashi cike da rauni tare da cewa.
“Wallahi Mommy ni nafasa Auren zan biyosu in dawo wallahi ni na fasa bazan zauna ba zan biyosu bazan zauna a garin nan ba kasheni zaiyi”.
Sai kuma taja ajiyar zuciya tare da cigaba da faɗin.
“Dama shi mugune sannan kuma an kawo ni inda ba kowa nawa zai cigaba da yimin mugunta”.
Cikin sauƙe numfashi Momy tace.
“Kul kada In sake Jin kin faɗi haka abakin ki bana so, ce miki akayi aure wasa ne, ina Umminki?”.
Cikin Muryan kuka tace.
“Tana falo”.
Kai Mommy ta gyaɗa tare da faɗin.
“Toh bawa Asma'u ta kai mata”.
Miƙawa Asma'u wayar tayi ta karba kana ta fice ta kaiwa Ummi.

Bayan sun gaisa da Ummi fuska ɗauke da yalwataccen farin ciki Ummi tace.
“Kai Alhamdulillah Momyn Khausar yau muna cike da farin ciki in Sha Allah gobe zamu dawo, zamu dawo da tukuici mafi tsada da daraja na munduwar masarautar Mouley shaidar yarmu ta kawo budurcinta ”.
Wani banzan kallo Hajiya Bunayya ta watsa mata Ummi kuwa cikin farin ciki ta cigaba da cewa.
“Khausar ɗin mu ta kai budurcinta gidan miji sannan Sarauta wanda muke da yaƙinin in Sha Allah aɗakin Khausar zai kasance”.
A wannan karon ƙwaffa mai ƙarfi Hajiya Bunayya tayi ta sunkuyar da kanta ƙasa yayin da idanunta suka kada sukayi Jawur cike da takaici bakin ciki da hassada tace.
“Uhmm ai duk gaggawar asara ta dai jira samu”.
Da kallonta suka bita sabida su dai fulanine ba wata cikekkiyar hausace garesu ba dan haka basu wani fahimceta ba bare su damu.

Mommy kuwa cikin hayaniyar da take jiyowa tace.
“Naji kamar kina cikin mutane”.
Kai Ummi ta gyaɗa tare da faɗin.
“Wallahi ina cikin mutane farin cikine ya hanani in haɗiye abun da zamu tattauna”.
Mommy na murmushin Farin cikin tace.
“Toh ki bari sai kin nutsu zamuyi waya amma ya jikin ƴar taki?.”
Zama Ummi ta gyara tare da faɗin.
“Jiki da sauƙi anzo an bata magunguna yanzuma ina ga bacci zatayi su Asma'u ne suka hanata bacci da surutu”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da faɗin.
“Toh shikenan Allah ya ƙara sauƙi”.
Ameen Ummi ta amsa kana sukayi sallama.

Acan gadon Khausar kuwa ganin ta samu bacci ne yasa Asma'u, Asiya Dije fitowa.
Fitowar su yayi daidai da ɗaga wayar Lalla Hafsat ta manna akunnenta maganar minti biyu tayi kana ta janye tare da kallon Asma'u da shigowanta Falon kenan tace.
“Asma'u kizo mu tafi kina da baƙo A Side ɗin Didi”.
Kai ta gyaɗa tare da kallon Ummi batare data bita ba.
Ummi data fahimci tsayuwar da take yasa tace.
“Kije mana”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da bin bayan Lalla Hafsat da ta fara ta fiya tana isa Falon ta saki ɓoyeyyen ajiyar zuciya ganin Dr Jameel dake zaune kan 3sitter Lalla Hafsat kuwa direct bedroom ɗin Didi ta wuce.
Cikin tsira mata ido da tarin ƙaunarta dake ratsa duk wani magudanan jinin jikinsa wanda yake uzzura jabarsa ɗaya danne yayi alƙawarin tsakaninsa da Allah bazai ƙara kusantar zinaba, ganinta ya sashi sauke numfashi mai sanyi tare da lumshe idanunsa kana ya buɗe su akanta tare da cewa.
“Ƙaraso ki zauna anan”.
Ya faɗa yana nuna mata gefensa cikin wani irin yanayi mai tattare da kunya ta nufi gefensa ta zauna kana ta gaishesa amsawa yayi yana mai tsira mata idanu tare da shaƙar daddaɗan ƙamshin hunran data shafa Cikin sauƙe numfashi yace.
“Albishir My Asmeey”.
Idanunta aƙasa ta motsa laɓɓanta tare da faɗin.
“Goro”.
Yana binta da wani sihirtaccen kallo yace.
“Fari ko Jaaaaa”.
Murmushi ne ya subce mata asaman laɓɓanta jin yanda yaja kalmar Jaaa ahankali tace.
“Fari ƙall”.
Zamansa ya gyara fuskarsa ɗauke da ƙayataccen murmushi dake bayyana farin cikin dake ciki yace.
“In sha Allah gobe, da Abualeey, Galadima, Waziri da Abban Zakariyya da ƙanin Abbanshi zaku tafi, saboda za'a je ayi tambayar Aurenmu”.
Tafin hannunta ta sanya ta rufe fuskarta kana ta saki murmushi mai ɗauke da kunya kafin ta ɗago kanta tare da cewa.
“Allah ya kaimu Allah kuma ya mana zaɓin abinda yafi Alkhairi”.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum amma dai kinyi farin ciki ko?”.
Kai ta gyaɗa still hannunta na saman Fuskarta.

Cikin son janta da hira ya gyara zamansa tare da cewa.
“Kuma harda batun Asiya da Zakariyya ma duk za'a yi tambayar kinsan shi Zakariyya ya riga ya koma Indi'a amma in Sha Allah yace bazai daɗe ba zai dawo saboda yana so ayi abin cikin ƙanƙanin lokaci in Allah ya yarda”.
Ahankali tace.
“Ayyah Allah dai ya mana zaɓi mafi Alkhairi”.
Cikin tarin ƙaunarta yace.
“Ameen nan suka ɗan ci gaba da hira”.

Lalla Hafsat da Lalla Khadijah kuwa, duk suna ɗakin Didi hadimai na shirya musu kayansu dan yau da dare Lalla Khadijah zata koma gidanta. Lalla Hafsat kuwa ƙarfe shida na safe na safen gobe jirnsu zai tashi zuwa Mexico.

Su Ummi kuwa ƙarfe sha daya zasu tashi.
Wanda kuma da pravate jet zasu tashi so kai tsaye Adamawa jirginsu zai sauƙesu, wanda tunima sun samu amincewa da sahalewar sauƙansu a Yola international airport, kassn cewar abune na manya ga kuma su Sheykh Jabeer da sune masu Jihar.


Acan ɓangaren Khausar kuwa bacci ne mai nauyi mai cike da gajiya takeyi.

Yayin da aɓangaren Moddibo ma hakan ne ya kasance sosai yayi bacci kiran sallar la'asar ne ya tashe sa yana tashi yaji jikinsa yayi sakayau alamar zazzaɓin ya sauƙa, cikin jin daɗi yasa hannunsa bisa mararsa yana shafawa jin maransa tayi sakayau wani makirin murmushi ne ya subce mishi sai kuma ya lumshe idanunsa wani irin farin ciki yake ji mara misaltuwa gami da nitsuwa salama kwanciyar hankali da cikekkiyar lafiya sai kuma zazzafan shauƙi.
Da Zaran ya tuna wasu abubuwa da suka gabata sai ya saki murmushin.
A fili yace.
“Wai Wayyo Didi zai kasheni Yah Mu'allim zan mutu”.
Sai kuma ya ɗan jujjuya idanunsa tare da cewa.
“Farar kura ba, *Minha Vidaa* ga tsoro ga ban tsoro, ga tsiwa ga raki ”.
ahankali ya shiga toilet ya sakaraa kanaa ruwan ɗumi kana ya daura alwala ya fito cikin wani tattausan yadi fari ƙall ya shirya kana ya feshe jikinsa da turarukansa masu daɗin ƙamshi a bedroom ɗinsa yayi sallan azahar daya riskeshi yana bacci, kana ya wuce masallaci yana mgnar zuci.
“Sai na hukuntaki da sani makarar samun jam'i da kikeyi kuwa”.

Khausar kuwa kafin akira La'asar ta farka tana tashi Ummi ta sake bata abinci taci kana tace.
“Toh tashi kiyi wonka kiyi salla”.
Kai ta gyaɗa tare da miƙewa tsaye ga mamakinta sosai ciwon yayi sauƙi sai kaɗan-kaɗan da takeji alamun mgni yayi aiki.
Bayan tayi wanka ta sauya kaya tayi sallan azahar da la'asar ɗin.
Tana bisa sallayar Ummu ta ɗauko mata Magungunan _Aunty Aysha Aliyu Garkuwa_ ɗan bokatjn wata gumbar madara mai haɗe da kwakwa ta miƙa mata, ba musu Khausar ta karɓa ganin yadda Aunty Hajara ta tsareta da idanu.
A hankali ta fara ci tana haɗawa da kwakwar gumbar nada ɗan karen daɗi shiyasa ta ci mai ɗan yawa.
Sai kuma ta amshi gorar da take miƙamata wanda na tsumin riɗine da kuma tsimi zuma a cup ta haɗa mata su.
Cikin tura baki tace.
“Ayyah Aunty Hajara cikina ya cika fa”.
Da sauri ta ɗan sa cup ɗin a baki sabida hararar data watsa mata.
Ajiye kofin tayi bayan ta shanye.
Sai kuma ta kalli Ummi dake cewa ki shiga Bathroom na haɗa miki ruwan ɗumi ki zauna a ciki, kai ta gyaɗa kana ta shiga.

Toilet ta tayi tsarki da ruwan ɗumi kana ta shiga cikin wanda Ummi ta haɗa matan.
Wanda yaji turaren tsarki ta fito.
Tana baza ƙamshi ita kanta in ta ɗan sunkuyo da kanta sai ta Lumshe idanu sabida yadda take baza ƙamshi ga kuma kullacar sirri da yafi komai mata daɗi, shiyasa take nace masa wurin shafawa ganin ba kowa a ɗakin ne yasa ta fita falon tana jin zazzaɓin ya sauƙa kana zugin da ƙasanta ke mata ma ya ragu sosai.

Haka dai yinin wannan ranan Khausar da Moddibo sukayi yinin jinya kuma Alhamdulillah jiki yayi sauƙe...

Moddibo kuwa yana dawowa masallaci part ɗin Didi ya wuce.
Allah ya sani so yake ya ganta yaga yanayin jikinta amman ya rasa ta yadda zai nematan haka yasa ya miƙe da nufin zuwa side ɗin dasu Ummin suke kuwa sai ya sauya hanya tare da komawa side ɗinsu Allah ya sani kunyasu Ummi yakeji, kuma tsoron wannan tsohuwar mai Shegen baki yakeji kada ta kunyatashi.

Bayan sallan isha akazo aka ɗauki Lalla Khadijah ta koma gidanta.

Misalin ƙarfe tara da kwata, Ummi ta kalli Khausar dake kwance gefenta tace.
“Khausar kada kiyi bacci anan fa, tashi ki tafi dakin mijinki”.
Cikin tsinkewar zuciya ta zazzaro idanunta waje, tare da saurin kallon Ummi tana mai girgiza kai kana tace.
“Na shiga uku Ummi dan Allah, ki barni in kwanan ni bazan koma canba wlh anan zan kwana”.
Kai ummi ta girgiza tare da faɗin.
“Nan kuma Khausar bayan gacan ɗakin mijinki a'a bazai yiwuba. maza tashi ki tafi”.
Da sauri Ummi ta zuba mata ido jin ta fashe kuka tsakaninta da Allah kuwa take kukan. dashi tana yarfe hannu tace.
“Ni dai dan Allah Ummi ki barni mu kwana anan, wlh tallahi bani da lafiya dan Allah ki barni in kwana kusa dake”.
Asma'u dake gefe tayi murmushi tare da gyara kwanciyar ta.
Ummi kuwa ganin yanda take kuka da faɗin baza ta je bane yasa tayi shiru...
Sai kuma ta jinjina kai jin Innayi na cewa.
“Ba komai Ummin Jameel barta ta kwana a nan ɗin, gobe ina zata ganku”.
Ita kam Khausar ido ta rufe tana mgnar zuci.
“Yoh ai tarema zamu tafi dan wlh ni dai bazan zaunaba”.

Zuwa lokacin karfe goma harda kota....

Washe gari da asuba ana fita masallaci Aka kai Lalla Hafsat da Hakim Airport.
Bayan ta sallami su Ummi.
Bakwai dai-dai jirginsu ya ɗags zuwa Mexico.

Abujan Nigeria, karfe takwas dai-dai Unclee Naseer ya bar gidan.
Tun fitansa kuwa Amina ke konce a tsakiyar falon bisa Carpet.
A hankali take sauke numfashi sabida ɗan baccin ɗaya fara fizgarta.
Cikin baccin da ya fara nisan, ta rinƙa jin hucin macijin nan, sai kuma tayi saurin buɗe idanunta sabida jin sanyin jikin macijin yana ratsa cikinta yana ɗan jujjuya kanshi tare dayin sama da kan nashi da ya shigar ta ƙasar ƴar rigar dake jikinta.
Wani irin fitinennen karkarwa jikinta ya fara, tare da zazzaro idanunta baki ɗaya lokacin da taji macijin nan ya manna bakinshi kan nimple dinta na hannun dama yayiwa nimple din wani irin damƙa da karf....


*Littafin Sakayya dai na kuɗi ki biya karanta cikin aminci da salama ba haƙƙin kowa a kanki 1k ne kacal 0661110170 gtbank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276 in tura Miki ki karanta cikin aminci*


By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 28*

Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*


Tallah !! Tallah !!

Shahararriyar Marubuciyar nan Ikilima Adam (kyauta daga Allah) wacce ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *Kanwata* *kaikajawa kanka , *Rai daya janzaki*.

yau na sake dawowa domin Domin tallata muku Littafaina mai Suna *(RUDANI )* Da kuma *Makauniyar Shari'a* littafine mai kunshe da Butulci , cin amana ,zagon Kasa , soyayya irin ta gani kasheni , aminci da saura n su basai n'a cika Ku da surutu ba Hausawa sukace Gani yakori ji.

Karku Manta *Makauniyar Shari'a* sabon littafi ne mai bibiyar Ma'anar sunan sa.
Ya zarce duk littafai na , na baya.

RUDANI littafine mai cike da Rudani da ban Al'ajabi , duk wacce kika fi buƙata zaki biya kudin sa Naira ɗari biyar kacal.

Farashin kowannen su Naira Dari biyar ne 500 kacal
Domin Karin bayani Ku tuntubeni a lambata kamar haka (09069080725 ko Kuma + 22953726162 ) wacce Bata shirya Siya ba kada mu batawa juna lokaci.
Domin aikawa da kudi kai tsaye . 3115484026 ikilima Adam first bank
Turo shaidar biya akan wannan 09069080725 sai najiku.



Lokacin daya damƙi nipple ɗin ta akuma dai-dai lokacin itama ta runtse idanunta da masifar ƙarfi jin yanda yasa harshensa yana ɗo bakin nipples ɗin ta ya mata wani irin zuƙa wanda taji tun daga cikin Faratun ƙafarta wani irin abu yana biyowa har bakin nipples ɗin ta.
Macijin kuwa zuƙa ya cigaba da yayi.
Ita kam wani irin zogin azaba take ji duk da cewa bata taɓa Shayarwa ba amma ji take zafin yafi ƙarfin zafin jariri na zuƙan, baki ɗaya ta kasa motsawa dan duk jikinta ya narke koda ya tsanta ta gagara motsawa bare kuma tayi yunƙurin ceton kanta haka yayita zuƙa tsawon minti biyu da rabi kafin ya zare harshensa.
Sai alokacin ta iya sunkuyar da kanta ƙasa kaɗan ta kalli

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login