Showing 159001 words to 162000 words out of 218703 words
Nana ma cikin gyara zama ta riƙa basu labarin yanda yaje dining ya same su da Khausar filla-fillah duk abubuwan da suka faru acan sai da suka bata.
Haka nan Momy taji wani irin nutsuwa da Salama har misalin ƙarfe biyu suna zaune suna hira juyawa Ummi tayi tare da kallon Momy tace.
“Nikam Momyn Khausar kina zaune Lamiɗo fa kin barshi shi kadai”.
Dariya tayi tare da faɗin.
“A'a haba yau kam ai nace masa Hajiya Bunayya taje ta sameshi nikam ai ina tare da baƙi”.
Da mamaki Aunty Ruƙayya tace.
“Kamar ya Hajiya Bunayya taje ta sameshi ba tare sukayi tafiyar ba?”.
Still Murmushi tayi kana tace.
“Inma tare da ita akayi tafiyar ba ai bata gan shiba bai gan taba ko?”.
Haɓa Ummi ta riƙe tare da cewa.
“To ai kema baki ganshi ba”.
Momy na dariya tace.
“A'a duk da haka dai suje na turata ni kuma inji da baƙina mana”.
Ƴar dariya Ummu tayi tare da faɗin.
“Eh lallai kam hakane”.
Daren wannan ranan haka suka rabata cikin hira.
Acan Side ɗin Haiydar kuwa kwance suke da Sulaiman yana ta bashi labarin Morocco da kuma Family Moddibo da irin abubuwan da aka gabatar acikin Masarautar.
Acan ɓangaren su Asma'u kuwa bayan ta gama waya da Dr Jameel ne ta juya ta kalli Asiya dake waya da Zakariyya sai kuma ta maida idanunta kan Dija dake kwance ba tayi bacci ba cikin sanyin murya tace.
“Nayi kewan Khausar bari In kirata inji”.
Ajiyar zuciya Dija ta sauke tana gyara kwanciyar ta tace.
“Wallahi kuwa nima nayi kewarta kira mana ita muji”.
Ɗaukar waya Asma'u tayi tare da dearling Number Khausar har tayi ringing biyu ta gama bata ɗauka ba kallon Dija tayi kana tace.
“Ki gani fa har kira biyu bata ɗaga ba”.
Wayar Dija ta ɗauka ta duba lokaci ɗan ware idanunta tayi tace.
“Kina gani ƙarfe biyu na dare nefa ya za'a yi ki sameta kina ganin wannan mijin nata maƙale mata mam-man-ne mata ai da wuya idan ba suna can suna maƙale da juna ba”.
Asma'u kuwa kirji ta dafe tare da ɗan zaro ido sai kuma tayi saurin cewa.
“Haka fa”.
Sai kuma ta janyo wayar ta kashe tare da kallon Dija tace.
“Ai Yah Moddibo duniya ne wani irin kallon da yake yiwa Khausar kamar zai mai da ita cikin zuciyarsa”.
Dija na gyara kwanciyar ta tace.
“Aikuwa Soyayya ce mai ƙarfi Moddibo Namijin Duniya ne”.
A wannan daren haka suka kwana hira.
Acan ɓangaren su Khausar ma suka kwana maƙale da juna.
Washe gari da safe
*Abujan Nigeria*
Bayan fitar Uncle Naseer da kimanin minti talatin Amina ta fara jiyo gurnanin macijin na fitowa tana zaune Jingine jikin kushin wanda tun jiya daya shata jikinta ke mace ta kasa da faɗawa kowa aranta tana ji tana so ta faɗawa Ummanta amma ta gagara tayi waya da Samira Sani ma tayi niyyar faɗa mata amma sai taji bakinta yayi nauyi ta kasa sanar mata tana kwance taji gurnanin Macijin kusa da ita cikin sauri ta miƙe daga kwance ta zubawa Micijin Ido yana isowa kusa da ita kamar jiya ya shiga rigarta ya kamo kan Nipples ɗin ta ya-shash-sha kafin ya kama hanya ya fita tun jiya daya sha bata sake dawowa dai-dai ba tana jin kasala bata da kuzari yanzu ma daya sake tsotsa sai taji gaba ɗaya jikinta ya sake mutuwa ahankali ta kalli bakin Nononta na dama kana ta kalli na hagun taga ɗigon jini kamar na jiya wani irin nauyi jikinta yayi mata ahankali ta sulale ta kwanta wani irin bacci ya ɗauketa...
Acan gidan Lamiɗo kuwa Abualeey, Waziri, Galadima Baban Zakariyya tun da sassafe aka kai musu abinci da komai na buƙata na alfarma kuwa su Asma'u ne suka kai musu Breakfast da komai ba buƙata.
Bayan sun kammala Breakfast Ummi ta kalli Momy tare da cewa.
“Momyn Khausar mufa zamu tafi”.
Da sauri Momy tace.
“Da wuri haka Ummin Jameel?”.
Ummi na murmushi tace.
“Gidan ba kowa nayi missing ɗin ɗan Autana Bashiruna Nasan tun jiya yake tsammanin zan koma yaji shiru yayi ta kirana ma ban ɗauka ba nafi so ma sai naje ya ganni”.
Kai Momy ta jinjina tare da cewa.
“Ayyah Asma'u am ki riƙa ɗan leƙoni kafin kema a ɗauke mana ke kinga ƙawarki kam an ɗauke ta zakuje can ku haɗu”.
Asma'u kam kanta ta sunkuyar ƙasa tana murmushi tace.
“Momy gobe ma zanzo in Sha Allah”.
Cikin sanyi Momy tace.
“Allah ya kaimu”.
Miƙewa Aunty Ruƙayya tayi tana kallon Momy tace.
“Toh nima zan tafi”.
Kai Momy ta gyaɗa kafin duk sukayi mata Sallama suka tafi bayan ta basu komai na biki.
Acan ɓangaren Mazan bayan sun kammala Breakfast Lamiɗo yai musu jagora suka tafi gidan su Malam Ahmad sukayi tambayar Auren Asma'u wa Jameel gaba ɗaya malam Ahmad da yaji lbrin Jameel sai da yashiga ruɗu da tashin hankali jin tsananin kamarsa da Jameel bayan sunyi tambaya sun dawo da tabbacin Anbasu kasancewar Lamiɗo ne ya musu Jagoranci.
Bayan sun dawo Hajja Nana, Hajja Umma Baffa Jimeta suka tafi Jauro Yaya daidai lokacin da Motarsu Hajja Nana ya fita akuma dai-dai lokacin
Text ɗin Yah Ali ya shigo wayar Dija, cikin tsananin mamaki take karanta sakon nasa.
“Tun jiya da dare jikina da zuciyata suke gaya min kun dawo Nigeria kun shigo jihar Adamawa sabida wani irin ni'imtaccen ƙamshi da isaka mai sanyi da nakejin wanda ya tabbatar min kin kusa dani, shiyasa nake fata da burin in ɗaukeki daga Jauro yaya in dawo dake kusa dani a matsayin matar aurena in kin amince Dija”.
Wasu irin tagwayen murmushi take saki ba ƙaƙƙautawa ta karanta sakon a karo na uku kana ta turawa Khausar tare dayi mata bayanin wanda ya turo saƙon da kuma neman shawara, haka dai sukaci gaba da tafiya.
Motarsu Hajiya Lami da Samira Sani yayi Parking sunzo wajen Hajiya Bunayya dan jin cikekken bayanin da tsara batun tafiyarsu.
Zuwa lokacin su Abualeey sun gama komai Lamiɗo ya musu Jagoranci zuwa gidan Abban Jameel Lokacin da Hajiya Turai da Hajiya Karima suka kalli hoton Dr Jameel dasu Abban Jameel da kuma lbrun kakannisu da Jameel da kuma lbrin dangin Modibbo sosai suka shiga mamaki, musamman kamannin Dr Jameel da kuma M Jameel abin yayi masifar basu mamaki ya kuma girgiza su a washe gari suka je Juuro yaya suka gaida Hajja Nana.
Kwanan su biyu acikin Taraba suka koma Adamawa kwana ɗaya sukayi a Adamawa ya zama kwanan su uku sukayi suka shirya komawa Morocco...
A Morocco kuwa rayuwa ta fara tafiya Khausar da Moddibo sun fara samun shaƙuwa na musamman wanda su kansu basu fahimci haka ba aranan dasu Abualeey zasu dawo Khausar ce zaune a falon Didi bayan sun gama girki wanda bisa alamu sun yiwa baƙi da zasu dawo ne sun gama komai sun shirya a dining.
Ahankali Didi ta kalli Khausar tare da cewa kizo ki zauna kici abinci”.
Anutse Khausar ta ɗago Idanunta tare da shafa cikinta kana tace.
“Didi na ƙoshi bana jin yunwa”.
Juyawa Didi tayi tare da kallon Moddibo dake zaune gefe da system a gaban shi bisa alamu aikin da ya shafi campanny Abba ne yake duba, cikin kula tace.
“Taci abinci tunda gari ya waye?”.
Kai ya girgiza cikin alamun damuwa ya kalli Didi kana ya maida kallonsa kan Didi yace.
“Babu abinda taci ni kaina bansan meyesa bata son cin abinci ba kuma ba haka take ba”.
Langwaɓar da kai tayi tare da cewa.
“Nifa bana jin yunwa nasha tea ɗaxu”.
Didi na girgiza kai tace.
“Toh tea Abinci ne? Khausar ai tea ba Abinci bane.
Rahama maza ɗebo min abinci a plate”.
Miƙewa Rahama tayi ta ɗebo abincin ta kawo mata aplate karɓan abinci tayi tare da kallon Khausar tace.
“Sa hannu kici”.
Kai ta girgiza tare da faɗin.
“Allah Didi banjin yuwa cikina aƙoshe yake”.
Kai Didi ta girgiza kana tace.
“Bana son zamanki da yunwa Khausar koda bakya jin yunwa ki karɓa kici”.
Kai ta sunkuyar ta ɗauki cokali saboda batason yiwa Didi gardama.
Moddibo kuwa ahankali ya ɗago ya kalleta tare da faɗin.
“Wallahi Didi tunda gari ya waye bata ci abinci ba idan kinga taci abinci sai na matsa mata dole² bansan meyesa ba”.
Dai-dai lokacin Ibraahim dake shigowa yace.
“Toh ko dai bata da lafiya ne?,Idan baki da lafiya ne mu kaiki asibiti aje aduba ki”.
Tana cakalan abincin tace.
“Wallahi lafiyata ƙalau bana jin komai abinci kuma ina ci ina yawan shan Fruit nake gama shine yake hanani cin abinci”.
Ajiyar zuciya Didi ta sauƙe tare da cewa.
“Toh yanzu dai kici bari kuma akawo miki fruit ɗin”.
Cokali biyu zuwa uku ta sake tsakura kana ta tura plate ɗin gaban Rahama tace.
“Toh muci mana”.
Ɗan ware Idanu Rahama tayi tare da faɗin.
“Ai kina gani ɗazu naci”.
Sake langwaɓar da kai tayi tace.
“Ni ma Wallahi na ƙoshi”.
Cikin sauƙe numfashi Didi tace.
“Kici mana Khausar am”.
Ahankali ta sunkuyar da kanta tare da faɗin.
“Allah Didi na ƙoshi”.
Kai Didi ta gyaɗa kana tace.
“Toh shikenan Rahama jeki ɗauko mata fruits”.
Kai Rahama ta gyaɗa sai kuma ta miƙe ta dauko mata wani kekyawan Bowl wanda ke cike da
Inabi, Apple, Banana, Pineapple, Water millo wanda yake a yayyanki an yarayarɗa madara akai.
A hankali ta gyara zamanta tare da ɗaukan fork ɗin jin Didi na cewa.
“Bismillah”. A hankali tai Bismillah tare da soka yankan kankana kana ta buɗe bakinta a hankali tasa, lumshe udanunta tayi sabida zaƙi da garɗin madarar da ya game mata baki, a hankali take taunan kankanan tare da haɗiyewa, sai kuma tattare ƴaƴan kankanan ta haɗesu gefen bakinta.
Shi kuwa Modibbo ta gefen idonshi yake kallonta,
yanka na biyu ta kuma kaiwa bakinta ba tare da ta haɗiye ƴaƴan kankanan ba, sai kuma ta sake harhaɗe ƴaƴan kankanan ta tarasu gefen bakinta sabida bata iya haɗiyesu, sai kuma ta jujjuya kwayar idanunta alamun tana neman wurin da zata zuba ƴaƴan kankanan ne.
A hankali ya miƙo mata hannunshi tare da buɗe mata tafin hannunshi, cikin fidda idanunta waje ta ɗan jujjuyasu alamun tambaya.
“In zuba?”.
A hankali ya ɗan juyo ya ɗan kalleta tare da ɗaga mata girarsa ɗaya alamun yess zuba ya ƙare ɗaga girar da ƙara manna hannunsa ƙasan bakinta kaɗan a hankali ta tattarosu tare da ɗan sunkuyowa ta zuba mishi su cikin tafin hannunshi.
Cike da mamaki Rahama ta buɗe baki da hanci tana kallon su kamar wasu tattabaru.
Ibraahim ma ido ya zuba musu, ita kuwa Rahama kai ta kuma juyawa ta kalli Didi data kauda kanta gefe tana mgnar zuci.
“Uhmmm ai in dai ya ɗauki mahaifinku zai yi abinda yafi hakama”.
ta ƙare mgnar zuci da kallon Ibraahim da ya saki baki yana kallon Modibbo ganin ya afa ƴaƴan kankanan cikin bakinsa tare dasa hannunsa ya tsinki inabi guda ɗaya ya haɗa da ƴaƴan kankanan ya ci.
Ita kuwa Didi murmushin tayi tare da maida kanta kan TV.
Shi kuwa Modibbo hannunshi ya kuma miƙa mata a karo na biyu ta kuma sa mishi ƴaƴan kankanan.
A nutse taci gaba da ci, a hankali ta juya ta kalli Ibraahim dake cewa.
“Yah Aleey in Sha Allah nima gobe zan koma Turkey”.
Kallonsa Moddibo yayi kana yace.
“Ha'a har zaka koma kuma?”.
Ya ƙare maganar da sawa Khausar tafin hannunshi ƙasan bakinta sabida ganin ta kuma tara wasu ƴaƴan kankanan, zuba mishi su tayi tare da zuba mishi idanu,
Shi kuma shu'umin murmushin gefen baki yayi tare da watsa ƴaƴan kankanan a baki domin shi yasan amfanin ƴaƴan kankanan a jikin namiji, domin babu wani abu cikin fruits dake ƙarawa wa maza ƙarfin kamar ƴaƴann kankanan shiyasa duk wani mgnin ƙarfin tattalin lafiya mazantaka zaka samu da sinadarin ƴaƴan kankanan a ciki.
Ya tabbatar bata san amfanin da zasuyi mishi a jikinsa bane da bazata bashi ba.
Yoh shida ko azumin rage ƙarfin sha'awa yayi muddin ya kuskura yayi buɗa baki da kankana to ranar ba bacci, bare ba azumin yayi ba, kuma gata kusa dashi.
Shi kuwa Ibraahim cikin kallon yadda yayan nashi ke amsar ƴaƴan kankanan daga bakin matarsa yana ci ya ɗan gyara zama yace.
“Eh wasu kaya zan sake kaiwa kasan ban cika zama anan ba saboda yanayin kasuwanci na”
Murmushi yayi tare da faɗin.
“Yaro Ƙarami da neman kuɗi”.
Yaaje mgnar yana kallon Khausar data tura baki alamun ya kawo hannunshi ya amshi ƴaƴan kankanan, miƙa mata hannun yayi tare da lasar gefen lip inshi na sama.
Didi dake sauraron tace.
“Wallahi fa kadai faɗa masa kayi masa faɗa ko zai rage Ibraahim da zirga-zirga firr yaron nan yaƙi zama sai jaraban son Kuɗi”.
Murmushi Ibraahim yayi yana mai lallon salon so mai zafi da darasi a wurin ustzun yayansa da ya dasa mai son aure farat ɗaya cikin fesar da numfashi yace.
“Toh Didi Idan ban nemi kuɗi ba mai zanyi nayi karatu na gama kuma Ni ba ayi min Aure ba sannan kuma abubuwan nan abune daya kamata asame su a inda babu tunda dabino ne mutane da dama suna bukatar shi acan shiyasa muke kai musu”.
Kai Didi ta girgiza tana gyara zamanta tace.
“Toh lallai kam wato ba'ayi ma aurena ba?”.
Kanshi ya ɗan sosai tare da sunkuyar da kai dan baisan mgn ta subce mishi ba.
Ita kuwa Didi cikin kulawa tace.
“Toh Amman ai bashi kaɗai kake yi ba inka dawo nan ɗinma komai na hotel ɗin Mouldy ka ciki”.
Ƴar dariya yayi tare da faɗin.
“Toh Didi ba dole inne mi kuɗi ba sune abokan rayuwa”.
Murmushi tayi tace.
“Yanzu kayi magana”.
Cikin sauƙe numfashi yace.
"Da Yauma nayi niyyar tafiya amma ina jira su Abualeey su dawo ne Shiyasa”.
“Allah ya dawo dasu lafiya”.
Cewar Moddibo.
Da ya kuma miƙa Khausar hannun a karo na barkai ita bashi ƴaƴan kankanan da sai yanzu ta cinye sai kuma ta kalli bowl ɗin tuni ya cinye mata inabi.
Zama Didi ta gyara tare da faɗin.
“Aima In Sha Allah nan da awa biyu zasu iso”.
Atare suka hada baki wajen cewa.
“Masha Allah Allah ya kawo su lafiya”. Kana sukaci gaba da hirarsu Rahama kam zama ta gyara tana bin Modibbo da Khausar da kallo domin Ita dai darasi take ɗauka.
Aranan su Abualeey suka dawo sun dawo kuma da labari mai daɗi cewa Mahaifin Asma'u ya bawa Dr Jameel Aurenta sannan Mahaifin Asiya ma ya bawa Zakariyya wanda ansa bikin Auren nanda wata uku ne masu zuwa.
A daren ranar misalin ƙarfe biyu da rabi.
A hankali Khausar ta saki wani irin raunataccen kuka mai cike da gajiya kasala gamida fara galabaitar da ita da Modibbo yayi.
Wanda tun sha ɗaya ya rsitsata, hutun awa ɗaya ya bata tana cikin bacci ta kuma jin ya kwaƙumeta.
Shine har yanzu bai sararamata ba kusa 50 minutes kenan, cikin yarfe hannun ta kuma saki sassayan kuka bawai dan zafiba sai dan gajiya duk da kuma cikekkiyar nitsuwa da yake samar nata.
“Wasshhhhhhhhh Yah Mu'allim na gaji”.
Cikin tsananin farin ciki gamsuwa salama da wadatacciyar ni'amarta ya tallabota jikinshi tare da fara sa mata albarka da yiwa J ɗinsa addu'a da Abbanta.
“Wow Minha vidaa Jazakillahu khairan wa yatta ƙinallahu jami'an kin bani dukkan jin daɗi da na miji kema, Allah yayi miki albarka Yayiwa Mommy gafara duniya da ƙiyama ya killace mata farin ciki ta kamar yadda ta killace min budurcinki Allah yayi mata tukuici da jannatul firdausi”.
Cikin gajiya da narkewa a jikinsa da jin daɗin addu'ar da yake wa iyayenta tace.
“Amin Yah Mu'allim”.
Sai kuma ya tallabota suka shiga bathroom sukayi wanka kana suka fito liƙe da juna.
Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya wani shaƙuwa na musamman ne yashiga tsakanin Khausar da Rahama wacce ta zame mata kamar Asma'u, sannan Didi na nuna mata soyayya na musamman mai nutsarwa da kwantadar da hankali Hakama Niyna, Innayi kuwa tuni ta dawo ɗaya daga cikin ɗakunan dake falonta, kana an kawo mata komai na girki tare da hadimai uku, biyu masu girki ɗaya kuma maiyi mata dan gyaran ɗaki.
A banƙaren Modibbo kuwa sosai yake baza hutun amarcin da aka bashi, sai dai time to time yana leƙa fada, domin Abualeey nada burin yin murabus nan kusa shiyasa yake nuna mishin komai na masarautar Alhamdulillah kuma yana gane komai sosai.
Alhamdulillah Abban Jameel kuwa ya ɗauki Yah Ali aiki a Company sa wanda yakeso shi zai maye mishi gurbin Modibbo, sosai karar da Abban Jameel yayiwa su Bappa jimate ya sasu farin ciki ya kuma ƙara dangon zumunci
Aɓangaren Amina haka rayuwa ta cigaba da tafiya tsakaninta da Macijin nan kullum zai fito yasha Nononta wanda zuwa yanzu ta fahimci jininta yake ɗan zuka kasancewar duk sanda yasha nono taɓa ganin jinin kaɗan tana so ta faɗa amma ta kasa idan ta fadawa Uncle Naseer cewa tana ganin jininta yake zuƙa sai cewa yayi ai da jininki yake zuƙa da tuntuni kin mutu kawai yana tayani shan abu nane, ahaka yake sha-shantar da ita.
Haka tsakanin Dr Jameel da Asma'u soyayyarsu ke tafiya gwanin ban sha'awa.
Haka ma Dr Zakariyya da Asiya soyayyarsu ke tafiya cikin kwanciyar hankali.
Hakama Yah Ali da Dija.
Wanda tuni mgnar ta isa ga Bappa jimate.
Tuni shirye-shiryen aure ya kankama sosai dan Abualeey da kanshi yace ya ɗauki nauyin gidan Jen angawaye da komai na amare Abban Jameel kuwa shine ya ɗauki nauyin komai na auren Yah Ali da Dija tuni yasa an fara gyara gidan cikin sama kuwa Yah ɗauki Yah Abba ma aikin sabida shima CB inshi sunyi kyau.
Aɓangaren Hajiya Bunayya da Hajiya Lami ma sun shirya zuwa Niger wajen sabon bokan da suka samu...
Yau kwanan su Ummi goma sha biyu kenan da tafiya.
Ahankali Khausar ta tura ƙofan Falon Moddibo ta shiga saboda tana so tayi wasu da Ummi dan tunda suka tafi ba tayi waya da kowa ba kasancewar Moddibo ya riƙe wayarta shiyasa ta shiga ahankali saboda tana so zata roƙesa ya bata wayarta ta kira Ummi Momyn ta harma da Hajja Nana in tayi sa'a ta sameta.
A hankali ta shiga tsakiyar Falon sai kuma ta ɗan jujjuya idanunta ganin ba kowa,
ha yasa ta nufi cikin bedroom ɗinsa tana shiga ta hango wayoyinsa da nata akan dreesing mirrow cikin sanɗa ta ƙarasa jikin dreesing mirrow jin alamun yana wanka a ban ɗaki.
Da sauri ta ɗan sunkuya ta ɗauki wayar dai-dai lokacin kuma, ya buɗe ƙofar tare da fito ƙugunsa ɗaure da towel cak ya tsaya yana kallonta ganin yanda take sanɗan ɗaukar wayar tana juyawa ta ganshi tsaye a gabanta,
cikin sauri ta runtse idanunta ganin faffaɗan ƙirjinsa awaje cikin wata sanyayyar murya yace.
“Mene?”.
Cikin tura baki tace.
“Baka da riga”.
Da mamaki ya kalli yanda ta runtse idanunta ya lura ganinshi na tsokanon kuran karfenta cikin yin murmushin gefen baki yace.
“Yau kika fara ganina bani da riga ne?”.
Muryanta na rawa tace.
“Ni dai ka rufe jikinka”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Ok na rufe”.
Ya ƙarashe maganar tare da since towel ɗin ta