Showing 57001 words to 60000 words out of 218703 words
rauni Moddibo ya cigaba da cewa.
“J sannan koda na kasance mai taɓin hankali katari da gawarka da akayi da gawarka akace ka rasu shiya jawowa ƙwaƙwalwata matsala!”.
Ahankali Dr Jameel ya matsa kusa dashi Asanyaye yace.
“Bawan Allah ka nutsu ni bansan kaba ban san mekake nufi ba”.
Cikin fushi Moddibo yace.
“J ƙarya kake”.
Miƙewa Dr Jameel yayi tare da ɗage kafaɗa yace.
“Ok toh shikenan”.
Ya ƙarasa maganar tare da ficewa Norses suka mara masa baya.
Cikin sauri Moddibo ya mike ya fita kai tsaye wajen motarsa ya nufa ya ɗauki wayarsa ya dawo reception din ya kunna wayarsa dake ɗauke da hotonsa dana M Jameel ya nuna masa kana yace.
“Yanzu wannan ka mantani ai gaka gani”.
Kallon fuskar wayar Norses ɗin sukayi Wacce Dr Jameel ya Kira da Baby tayi saurin buɗe baki cike da Mamaki ta kalli Dr Jameel kana tace.
“Iyee Dr da gaske fa kaine”.
Harara ya watsa mata kana yace.
“Kuma dai baku da hankali”.
Ahankali Moddibo ya juya da fuskar wayarsa nan yaga takwas tara cikin sauri yace.
“Yah salam banyi maghariba banyi Isha'i ba”.
Sai alokacin Dr Jameel ya tuna da batun sallah kallon Moddibo yayi da duk kiɗima da ruɗu kana da gigita dake jikin mutumin amma ga mamakinsa sai ya juya ya nufi Masallacin dake cikin Hospital Kai tsaye Tap dake wajen Moddibo ya nufa ya ɗaura alwala har zai shiga Masallacin ya tsaya ya juya tare da kallon Dr Jameel da still Idanunsa ke kansa.
Kai ya jinjina muryarsa na rawa yace.
“Yayi kyau J nine kake cewa baka gane ba zan shiga Masallaci in faɗawa Ubangiji duk abinda ke damuna”.
Ya ida maganar tare da shiga Masallaci nunfashi Dr Jameel ya fesar kana shima yayi alwala ya nufi masallaci.
Yana shiga Masallaci yayi maghariba da Isha'i yana idarwa idanunsa suka sauƙa kan Moddibo daya tsira masa ido.
Cikin sanyin murya da rauni Moddibo yace.
“J Nine kake cewa baka gane ba”.
Kai Dr Jameel ya Girgiza cikin gaskiya da gaskiya yace.
“Wallahi bawan Allah Ni bansan kaba ban kuma gane kaba kadena cemin J Ni sunana Jameel”.
Cikin sauri Moddibo ya katsesa kana yace.
“Aina sani dama sunan ka Jameel ne”.
Dr Jameel kuwa jin wayarsa na ringing yasa ya Mike ya fita kai tsaye cikin Hospital ya nufa duba matar daya mata Theater Yana shiga Moddibo yabi bayansa bayan ya gama duba ta yafita ya kalli Moddibo kana yace.
“Yanzu ko inda zanyi aikin ma sai kabini har ciki?”.
Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.
“Eh dole sai na bika J”.
Cikin alamun gajiyawa Dr Jameel yace.
“Toh kabarni mana ina sarara”.
Kai Moddibo ya Girgiza cikin tsaresa da ido yace.
“Ai tsakanina da kai babu sararawa sai lokacin dana danƙa ka ahannun Ummi da Abba”.
Siririn tsaki Dr Jameel yaja kana ya juya yabar wajen kai tsaye Office ɗinsa ya nufa dai-dai lokacin Baby ta shiga.
Tana shiga ta tsaya daga bayansa bayan ya zauna akan kujera cike da salo ta sanya tafin hannunta tashafa sajensa zuwa kan Lips ɗinsa.
Cike da shu'uman ci ya lumshe Idanunsa cikin wata narkakkiyar murya mai tarwatsa lissafin mata yace.
“Ohhhh My Baby don't kill me. Cikon Office muke fa, mu tafi gida Please I need you”.
Shagwaɓe Murya tayi tare dayi masa fari da ido tace.
“But Dr Ina da Nightduty”.
Wani kallo ya bita dashi yana shinshina wuyarta kana yace.
“Toh yanzu yakike so inyi”.
Ido ta kashe masa tare da ɗage gira tace.
“Duk yanda kace haka za ayi?”.
Cike da tsanananin Mamaki Moddibo ke kallonsu Aruɗe yace.
“J wacece wannan kuma kasan abinda kake yi kuwa?”.
Cikin tsawa ya kalli Baby kana yace.
“Ke ki sake shi baki da hankali ne?”.
Juyawa Dr Jameel Yayi tare da kallon Moddibo Up anda down Cike da takaici yace.
“Ya dai bawan Allah Meyesa kake shige min rayuwa da ƙudundunai ne?,Ko kuma dan kaga bansa security sun jefa ka waje bane?Ina ruwanka da ita?”.
Araunane Moddibo ya kallesa kana yace.
“J baka da hankali ne J mekake yi haka? Shin wace rayuwa ka jefa kanka aciki J?”.
*Gembila*
Acan Gembila kuwa adai-dai wannan lokacin Mommy ce zaune abakin gadon Khausar yayinda Khausar da Asma'u ke tsakiyar gadon cikin dariya Mommy ta gyara zaman wayar dake kunnenta kana tace.
“Yau dai Ummi kiyi haƙuri nice na hana Asma'u dawowa kuma Khausar ce ta hana dan Allah kiyi haƙuri ki barta ta kwana, kinsan abokin kuka shi ake faɗawa mutuwa”.
Murmushi Khausar tayi tana kallon Mommy.
Still Mommy na Dariya tace.
“Shiyasa nace bari in kiraki in Faɗa miki kuma ɗazu nayi ta kiran wayarki yana shiga ba'a ɗauka sai yanzun”.
Acan ɓangaren Ummi kuwa murmushi tayi cikin yanayin sakin fuska da jin daɗi tace.
“Laa bakomai ai lokacin da kika kira ina tare da Babansu ne kuma nabar wayar aɗakina muna tatauna batun Khausar ne sai yanzu dana shiga ɗaki naga miss call ɗinki na kira”.
Murmushi Mommy tayi cikin jin daɗi tace.
“Toh Nagode Insha Allah zamu kwana gobe zata dawo”.
Khausar dake gefe tayi ƙasa da murya kana tace.
“Mommy kice mata dan Allah goben ma sai da daddare zata dawo zamu sake yini”.
Dariya Ummi dake jiyo sautin muryar Khausar tayi kana tace.
“Ai kwana ya isa basai anyini ba”.
Karɓan wayar Khausar tayi tare da langwaɓar da kai tace.
“Dan Allah Ummi idan mun kwana mu yini”.
Murmushi Ummi tayi tare da gyara rikon wayar tace.
“Ku kwana dai sannan kuzo da wuri Ina son tattaunawa dake”.
Kai Khausar ta gyaɗa kana tace.
“Toh Ummi”.
Sannan ta katse wayar.
Miƙewa Mommy tayi kasancewar girkinta bisa duk kan Alamu cikin shirin tafiya side ɗin Lamiɗo take kallon Khausar tayi kana tace.
“Toh kizo ki rufe muku ƙofa”.
Kai suka gyaɗa atare suka miƙe da Asma'u suka bi bayanta kana suka rufe kofar.
Zama Asma'u tayi akan 2sitter kallonta Khausar tayi ta shafa cikinta kana tace.
“Asma'u mai za muci ne?”.
Kai Asma'u ta girgiza kana tace.
“Wani abinci zanci Khausar bayan kinsan Maganar daya kawoni nake so muyi amma tun yamma kin ƙi ki zauna muyi”.
Langwaɓar da kai Khausar tayi cikin sanyin murya tace.
“Shiyasa nake so mukwana kinga yanzu ma Mommy Bata nan zamu sake muyi maganar mu”.
Jinjina kai Asma'u tayi tare da cewa.
“Toh shikenan”.
Ahankali Khausar ta shafa cikin tace.
“Gaskiya yunwa nake ji kema kuma naga ɗazu bakici abincin sosai ba”.
Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe kana tace.
“Toh shikenan muje kichen ɗin muga mai zamuyi”.
Suna shiga kichen Asma'u ta buɗe freezer Khausar kuwa na tsaye gefenta ganin ɗanyen kifi yasa Asma'u juyawa ta kalli Khausar kana tace.
“Toh muyi Marghi special mana”.
Kai Khausar ta gyaɗa cike da gamsuwa tace.
“Toh shikenan muyi”.
Suna aikin suna taɓa hira cikin awa ɗaya suka gama kana suka soya chips aplate Asma'u ta zuba musu sannan Khausar ta zuba musu Tea cup biyu afalo suka zauna suna ci suna kurɓan tea suna cikin ci suka ji Knowking ahankali Khausar ta kalli ƙofar tace.
“Waye”.
Haiydar dake tsaye yace.
“Nine”.
Kurɓan tea Khausar tayi tace.
“Toh lafiya har mun rufe kofa zaka zo kana mana Knowking?”.
Murmushi yayi kana yace.
“Naji ƙamshi yana ta buɗewa ne ta ko ina shiyasa nasan wani abu kuka girka Ni dai Ku sammin kawai yunwa nake ji dan nayi dogon hira”.
Hararan ƙofar Khausar tayi tare da cewa.
“Shegen kwaɗayi mutum yana nan da hanci kamar Mage duk abinda akayi baka ciki ma sai an baka”.
Dariya Asma'u tayi tare da miƙewa tashiga kichen ta ɗauki Plate ta zuba masa sauran kana ta buɗe ƙofar ta miƙa masa har ta juya yayi saurin cewa.
“Toh ni baza abani shayin bane”.
Harara Khausar ta watsa masa kana tace.
“Ohh Haiydar kinga Ni Ko Asma'u da ba kin fara bashiba”.
Murmushi Asma'u tayi tare da juyawa ta koma kichen Haiydar kuwa gwalo yayiwa Khausar kana yace.
“Oho dai abani”.
Miƙa masa Asma'u tayi bayan ta zuba.
Bayan sun kammala Asma'u tace.
“Khausar mu dan watsa ruwa mana”.
“Eh to ki fara shiga".
Cewar Khausar dake gyara zamanta.
Miƙewa Asma'u tayi tare da tattare Plate ɗin ta kai kichen kana ta dawo ta watsa ruwa bayan ta fito Khausar ma tashiga ta watsa tana fitowa ta bude Siff ta ɗauka musu sleeping dress riga da wando masu duhu ta miƙawa Asma'u ja sannan ita ta sanya fari.
Kai tsaye falon suka fito Khausar ta kunna Tv ta rage Volume Anutse Asma'u ta juya ta kalli Khausar kana cikin sanyin Murya tace.
“Khausar”.
Ahankali Khausar ta juya tare da tattara duk kan nutsuwarta zuwa gareta tace.
“Na'am”.
Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe kana tace.
“Khausar wai Maganar da naji gaskiya ne abu ya kankama wai har an ɗaura aurenku?”.
Numfashi Khausar ta fesar kana ta sunkuyar da kanta ƙasa cikin rauni ta riƙo hannun Asma'u ta mannasu da kumatunta ga mamakin Asma'u sai taga hawaye na zuba Shar-shar-shar akuncinta.
Cikin sanyi da rauni Asma'u tace.
“Haba Khausar daga na miki magana sai ki fara kuka ai mu abun farin cikine”.
Ƙasa cewa komai Khausar tayi sai hawaye da take ahankali ta fara sheshsheƙa dake fita daga ainihin zuciyarta.
Araunane Asma'u tace.
“Haba Khausar kina kuka Ni kuma ya kikeso inyi kawai daga nazo muyi magana ta tsakanin mu sai ki fara kuka ai wannan abin farin cikine ba abin kuka ba”.
Kai Khausar ta girgiza cikin rawan murya tare da ƙoƙarin hana kanta kuka tace.
“Asma'u na amince ne saboda wasiyyar da Yah Jameel ya barmin kenan, amma ke kinsani kinsan waye Moddibo kinsan yanda tsakanina dashi yake kuma ni wlh banyi zaton da sauri-sauri haka zasu liƙa mishi niba”.
Hawaye na bin kuncinta ta cigaba da cewa.
“Bansan wace irin rayuwa zanyi atare dashi ba bansan wani iri zama zanyi ba bansan wani irin ƙakubalen zan fuskanta ba amma ina cikin taraddadi da tashin hankali Asmau”.
Atake idanun Asma'u suka cika da hawaye cike da tausayin Khausar.
Araunane Khausar ta cigaba da cewa.
“Ranar ma abinda ya kaini gidanku kenan naje ne muyi maganar amma sai in rasa ta yanda zan fara maganar ta ina zan kama mgnar ma”.
Cikin matsanancin kuka da tashin hankali tace.
“Asma'u shin menene makomata Yah Jameel ya barni da nauyi mai tarin yawa inaso in wanzar masa da wasiyyar sa gashi ya kasantu to amman ni menene makomata”.
Cikin rauni da tarin damuwa Asmau tace.
“Khausar ki daina kuka in dai kin gamsu Saboda farin cikin Yah Jameel amakwancinsa kikayi to ki daina kuka na tabbatar da Yah Jameel yana raye ba zaiso kukan kiba”.
Kasa da kai Khausar tayi hawaye na cigaba da zuba daga idanunta cikin zubda hawaye Asma'u ta cigaba da cewa.
“In dai har kinyi haka saboda farin ciki da kuma Wasiyyar Yah Jameel ya bar miki toh kada kiyi Kuka Yah Moddibo ai Namiji, ke kuma macece, kuma zuciya tana son mai kyau tata mata ke kuma mace cefa cikekkiya mai ababen muradin dukkan namiji”.
Ta sauƙe Ajiyar zuciya still Hawaye na bin fuskarta ta cigaba da cewa.
“Ina da tabbaci Khausar ko Yah Moddibo muddin yaji wasiyya ce Yah Jameel ya bar miki sannan saboda wasiyyar sa kika ce kinji kin gani zaki auresa nasan bazai zalunceki ba muddin bai kyautata miki ba to bazai zalunceki ba”.
Kai Khausar ta girgiza ta tare da ƙara danne sheshsheƙan Kukan ta haka ma Asma'u cikin sauri Khausar ta fara share mata hawayen fuskarta murya na rawa Asma'u tace.
“Khausar ban san da wani irin baki zan miki godiya ba, Ubangiji Allah ya biya ki da mafi kyawun sakamako saboda wasiyyar ɗan uwana kika amince da mgnar duk da ba yayanki bane”.
Cikin sauri Khausar ta sa hannu ta rufe mata baki muryan ta na rawa tace.
“Asma'u meyesa zaki ce haka Yah Jameel kike cewa ba Yayana bane?”.
Kai Asma'u ta girgiza kana cikin raunin murya tace.
“Ba haka nake nufi ba Khausar”.
Araunane Khausar tace.
“Toh meyesa haka Yah Jameel Yayana ne kuma Malami nane sannan Al'farma ya nema ya haɗani da Allah da Manzon ranan rabuwa ta na ƙarshe da Yah Jameel”.
Sai kuma tayi saurin rufe fuskarta da tafin hannunta kana cikin rauni ta cigaba da cewa.
“Yah Jameel Yana Kuka fa Asma'u yake cemin Khausar nasa zaiyi wuya inyi tsawon rayuwa alokacin daya faɗa min hankalina ya tashi na gigice bansan lokacin da hawaye ya fara zubo minba”.
Asma'u kuwa lumshe idonta tayi tana mai jin ƙaunar Khausar aranta.
Cikin sheshsheƙa Khausar ta cigaba da cewa.
“Ganin ina kuka sai ya fara yimin dariya yana cewa dan yace min zai mutu shine xan fara kuka ai bawai dan ya faɗa yana nufin mutuwa zaiyi ba, sannan yace min akwai Alfarma da temakon da yake nema awajena”.
Ta lumshe Idanunta hawaye masu zafi suka zubo kana ta cigaba da cewa.
“Yasa na mishi al'ƙawari koda bayan ransa zan cika masa wasiyyar Asma'u kuma nayi nasa al'ƙawarin idan har ban auri Moddibo ba kenan ban cikawa Yah Jameel Wasiyyar sa banyi masa taimakonba shiyasa nace Moddibo zan aura amma ke kin sani tsoron Moddibo nake hasalima babu wacce Moddibo ya tsana arayuwar sa sama dani kinsan shi baya sona ni kuma ina tsoronsa”.
Cikin sanyi da son ƙarfafa mata gwiwa Asma'u tace.
“Insha Allah ba zaki taɓe ba Ummi ma tayi farin ciki da wannan auren kowa kin sashi afarin ciki Insha Allah Ubangiji zai dawwamar miki da farin ciki agidan Auren ki”.
Ajiyar zuciya mai nauyi Khausar ta sauƙe kana yace.
“Ni dai zanyi wannan al'amarin saboda Yah Jameel ne kuma na yarda zan jure duk kan ƙunci, Haranta, Cin fuska, Tozarci, Cin zali da duk wani salon wulaƙanci da Moddibo zai min saboda cika burin Yah Jameel”.
Asma'u kuwa kai ta girgiza kana tace.
“Insha Allah ma ba zai miki ba da yardan Allah ba zaki ƙuntata ba rayuwa ba zata miki ƙunciba tunda Mommy ta sanya Albarka aciki komai zai tafi dai-dai”.
Ta ida maganar tare dasa hannu tana share mata hawaye murmushi tayi ko kaɗan bata son ganin hawayen Khausar cikin son ƙawar mata da damuwarta tace.
“Keda kike amarya wayasan amarya da kuka kuma amaryar ma ango mai tsada matar Yah Moddibo?”.
Harara Khausar ta watsa mata da jiƙaƙƙun Idanunta da Eyelashes ɗinta suka sake zara-zara dasu sai kuma ta tura baki tace.
“Ba wata amarya amarya ko kuma wahalalliya dai!?”.
Dariya Asma'u tayi kana tace.
“Ba wata wahalalliya amarya dai”.
Cikin sanyi Khausar tace.
“Hmmm Asma'u Ni dai hankalina atashe yake ina tsoron Moddibo bansan wani irin zama zamuyi ba”.
A dai-dai lokacin kuwa Samira Sani ce, da Amina ke waya tana gaya mata batun auren MODIBBO DA Khausar, Ya Salam wannan labarin ya girgiza Samira, haka yasa bta cilla wayar bisa gado ma tare da ta katse kiranba.
Da gudu ta nufi ɗakin Hajia Lami, tana shiga ta ganta zaune bakin gado da waya a kunne tane cewa.
“Haba dai Hajia Bunayyah wanne irin aure kuma, innalillahi ya za'a mana haka muna nan muna shiri mun rasa nitsuwa dan jawo hankalin wannan yaro kuma azo ace wannan shegiyar yarinyar ya aura, ya zasu fito mana a bazata”.
Sai kuma ta katse wayar tare da ruggume Samira da ta faɗa jikinta tana kuka wui-wui tare da cewa.
“Mommy shike nan ni kam nayi batam ɓaka tamtam, ni ba budurcinaba, ni ba Modibbo ba, ni ba lafiyata ba ni da zunubin zina da boka, ga ruwa mai wari da ke bibiyata”.
Ta ƙare mgnar da fashewa da matsanancin kukan da yasa Hajia Lami ruggume mata cike da takaici ta fara lallashinta.
Acan Falon Lamiɗo kuwa kallon Mommy dake zaune gefensa yayi ahankali ya sauke ajiyar zuciya kana yace.
“Ɗazun Alh Bukar suka zo maganar Amina da Naseeru to kuma har angama magana anbawa Naseer Amina since Ashirye suke nan da kwana goma suke so dan Ashirye suke”.
Murmushi Mommy tayi kana tace.
“A'a Masha Allah Abu yayi kyau Allah yasanya al'khairi”.
Anutse Lamiɗo ya gyara zamansa kana yace.
“Toh kuma tunda sakaranar yazo abakin gaba kawai za ahaɗa da ɗaurin bikin Khausar”.
Saurin Kallonsa Mommy tayi Asanyaye tace.
“Mai martaba da sauri haka?”.
Kallon yanda tayi da fuska yayi kana yace.
“Toh ke Meye damuwarki aciki?”.
Cike da damuwa tace.
“Toh Babu abinda muka shirya wa bikin nan fa”.
Numfashi ya fesar kana yace.
“Toh na saki ne ko kuma nace kishirya ne?,Ko cokali bansa ki siyawa Khausar ba kibar min ƴata Ni zan mata komai”.
Ya ƙarasa maganar cike da kara, mutuntaka, da kuma dattako.
Cike da kunya da jin daɗin karansa Mommy tayi murmushi kana tace.
“Nagode Allah yasanya musu al'khairi duk abinda kace haka za ayi”.
Murmushi yayi kana yace.
“Haka nake son ji ke dai ki sanya Albarka acikin wannan al'amarin”.
Jinjina kai tayi cikin sanyin murya tace.
“Allah yasanya alkhairi”.
*Morocco*
Cikin fushi Dr Jameel ya watsa wa Moddibo Harara kana yace.
“Haka kawai zaka zo kana takura min rayuwa dan bansa ankore kaba?”.
Cikin wani irin yanayi Moddibo yace.
“Korana?,Kasa akoreni J ni kake cewa zaka kora?J Bismillah in baka koreni ba baka amsa sunan ka Jameel ba”.
Afusace Dr Jameel yaja hannun farkarsa yace.
“Mu tafi Baby”.
Cikin sauri Moddibo yabi bayansa kafin ya fita tuni Dr Jameel yashiga mota, Cikin sauri yashiga motarsa zaiyi reverse yaga wasu motoci biyu sun taresa dole sai anja daya daga ciki kafin ya samu ya fita Dr Jameel kuwa tuni yaja motarsa ya tafi.
Da sauri Moddibo ya fito daga motarsa yace.
“Waye wannan yazo ya tare min mota ta ina zan fita”.
Dai-dai lokacin mamallakin Motar yazo cikin sanyin murya yace.
“Ayyah Bawan Allah kayi haƙuri na ajiye mota abayan naka banyi tsammanin zan daɗe ba abu kawai zan karba”.
Uffan dai Moddibo bai ce da mutumin ba yashiga motarsa yaja ya tafi sannan Moddibo ya shiga nasa yaja ya fita sai dai ba motar Dr Jameel ba labarinsa gefe da gefen Asibitin ya zagaya amma koda wasa baiga alamunsa ba.
Komawa yayi da niyyar shiga asibitin security suka hanasa duk yanda yaso shiga sunƙi barinsa cikin takaici ya juya akalar motarsa kai tsaye Mouley Youssef Hotel Rabat ya nufa cike da tunani iri-iri, yana isa yayi Parking kana ya fito yashiga cikin harabar Hotel ɗin ya shiga reception kai tsaye ya wuce masauƙinsa yana ya sa key ya buɗe ya shiga bakinsa ɗauke da sallama
Zama yayi akan 1sitter ya dafe kansa da hannu bibbiyu cikin sauri ya janye hannu ya ɗauki wayarsa ya kira Number Abba amma har ya katse ba adauƙa ba.
Lokacin da kiran yashiga wayar Abba tuni yayi bacci miss call uku Moddibo yayi ganin bai ɗauka ba yasa ya haƙura ya jinginar da kansa da jikin kushin yasani koda ace J zaiyi ko wani irin basaja ne aduniya ba zaiyu ace anyi masa Aure Iyayensa basu sani ba kuma ga duk kan alamu ma wancan karuwa ce domin tafi kama da karuwai wannan ne ya fara ɗarsa mishi shakku anya wannan J ɗin shi ne kuwa a fili yace.
“Ina inada tabbacin J na ba mazinaci bane, kuma bazai aikata zinaba, shin toh in ba J na bane waye wannan”.
Kanshi ya daddafe da duka hannunsa yana mai rumtse idanunsa da ƙarfi da kuma ƙarfin yace.
“No J bazai kasance haka, ina ba J ɗina bane kuma J na ko allura bai iya