Showing 87001 words to 90000 words out of 218703 words
jarabar amman ina ya gaza sabida ruɗanin da yake ciki.
Sun Khausar kuwa ahankali suka ƙaraso cikin parlorn, wasu daga cikin Hadiman dake ta hidima ne suka nunawa Asma'u Asiya da Dija, wajan zaman da aka tanada musamman domin su, haka yasa cikin nitsuwa su Asma'u suka nufi wurin zamansu, yayinda Hadiman kuma duk suka zube a ƙasa.
Yayinda su Lalla Salma kuwa suka nufo da ita wajen dasu Modibbon ke tsaye.
Da sassarfa Rahama ta taso ta biyo bayansu.
Lalla Salma ce ke rike da Khausar yayinda kowani taku ɗaya da sukeyi na kusanto inda Modibbo yake.
Hakan ke kara duk’unzuma tunanin Modibbo, wanda yakejin abubuwan suna zuwa masa awasu yanayi na daban.
Dab dashi Lalla Salma ta kawo Khausar din, tare da sakin hannunta, da sauri Rahma ta ƙaraso hannunta rik’e da wani babban glass bowl wanda cikinsa ke d’auke da kyakkyawan furanni masu fitar da sassanyan k’amshi.
Cikin tsananin farinciki ta soma watsa musu furen, Lalla Salma kuwa matsowa kusa dashi tayi, tare da ɗan ranƙwafowa ahankali tace.
“Abisa al’ada Aleey kai zaka buɗe fuskar amaryar taka ka juyata ta fuskanci family inka su ganta da kyau, kayi Bismillah ka bud’e fuskarta, idan ka juyata an ganta sai ka riƙe hannunta ku zauna bisa kujerar nan ka tabbatar kun zauna da bisimilla.”
Cikin sauri ya kalleta hadi da kallon Ibraahim dake gefensa na dama, sunkuyar dakai Ibrahim yayi kana cikin yin kasa da murya yace.
“Dan Allah Yah Aleey kayi abunda Lalla Salma tace, kada kayi abunda za muji kunya, kar kayi abunda zaisa mutane su fara tunanin babu abunda ka sani adangane al'adun masarautar da ake tunani za’a damƙa maka ragamarta a hannunka, kayi hakuri dan Allah Yah Aleey!!”
Ya k’are maganar cikin magiyan, da yasa Modibbon juyawa ya kalli Didi da ta tsura masa ido.
Sai kuma ya ɗan juya idonshi ya kalli Innayi wacce itama kallon nasa take, tare dayi masa alama akan yin biyayya.
Idanunsa ya dan lumshe tare da shakan numfashin dake kokarin kwace masa sabida tsanantan bugun da zuciyarsa keyi.
Cikin bada umarni Sheykh Jabeer ya ɗan matse hannunsa dake cikin nasa, kana ya ɗan rongofo tare da faɗin.
“Kayi abinda ya dace, umarnin kakarkace macen da tasha wuyan rainonka tsawon shekaru, kana kuma fata ne da burin mahaifiyarka data raini cikinka tsawon wata tara da kwana tara, sannan burin mahaifinka kanan”.
A hankali ya buɗe lumsassun idanunsa lokaci da yaji zuciysrsa na bashi umarni.
“Buɗe kaga wacece?”. ji yake wani abu na fusgarsa, batare da sani ko shiryawa hakan ba, sai ji yayi hannayensa na motsi, duk da karkarwar da suke.
Ganin haka yasa Rahma dake bayan Khausar ɗan turo Khausar din tare da cewa.
“Yes my Aunty jeki kusa da mijinki ya buɗe mana fuskarki mu ganki”.
Sai kuma ta ɗan ƙara ɗan tureta kaɗan da kafaɗarta, wanda haka yasa Khausar da zuciyarsa ke buga lugude tara-tara ta ɗan yi motsi kaɗan da yaɗan ƙara kusancinsu da Modibbo.
A hankali ya ɗan ɗago hannunsa, yatsunsa biyu yasa gefe da gefen mayafin nata ya kamo tare da d’an d’ageshi sama, yanajin zuciyarsa nayi masa wani irin duka uku uku.
Yana janye mayafin kuwa kyakkyawar fuskarta na bayyana.
Cikin wani irin baƙin al'amari ya zazzaro idanunsa cike da kad’uwa had’i da mamakin ganin fuskar Khausar, wani irin masifeffen kasalane ya rufe mishi jiki da zuciya, a take kuma yaji wani irin abu mai masifar sanyi ya tsoki ƙahon zuciyarsa, kana a take ya kuma jin wani irin abu daya harba daga tsakiyar maɗigan kansa, ya game dukkan sasanjikinsa, har zuwa kan babbar yatsarsa, wani abu me kama da mamaki, hadi da mutuwar jiki ne suka lullubeshi lokaci d’aya.
Bak’on yanayi me kama da zazzafar bege da bai tab’a jiba ya lullube dukkan jikinsa, dake wani irin tsuma.
Hadi da sanya masa wani yanayi na kaucewar tunanin.
Wanda ya sashi bud’e hannayeshi tare da ware tattausar al'kyabbar dake jikinsa.
Wanda ganin hakan yasa Rahma ɗan ƙara tura Khausar, kasancewar takalmin da ta sanya me tsinine hakan yasa ta tafiya garesa batare da ta shiryawa hakan ba.
Shi kuwa Modibbo wani irin mataccen numfashi yaja tare da fesar da sassayan numfashi mai dogon sauti.
Kana ya yayi mata Kekkyawan masauƙi a ƙirjinsa tare bata cikekkiyar kariya
da yalwatacciyar alƙyabarsa ta hanyar bata wani irin kyakkyawan runguma, me ɗauke da ma’anoni masu tarin yawa, da yafi kama da tsananin shauki hadi da zallar kewa da bege.
Rungumeta yayi tsam a cikin jikinshi ya mannata da ƙirjinsa da ƙarfi har yakai ga suna iya jiyo ɗumin jikin junansu wanda kuma tuni yayi mata garkuwa da yalwatacciyar Al'kebbar jikinsa mai cike da ni'imtaccen ƙamshi.
Lib Khausar tayi a jikinshi tare da shaƙan numfashi daya wadatu da ƙamshin turaren jikinsa wasu irin tagwayen numfarfashi take fesarwa tare da lafewa a jikinshi da kyau tamkar mai tsoron kada a janye mata shi haka nan takejin tamkar a barta ta rayu a kunshi a haka har gaban abadan haka yasa ta liƙe lip a jiki nai.
Shi kuwa Modibbo a hankali ya lumshe idanunsa tare da laso gefen lip inshi sama,
Yanayi ne na musamman a garesu, daya sanya su lumshe jujjuya kwayar idanunsu a tare, musamman ita Khausar da taji ya lulluɓeta da alkyabbarsa.
Wata duniya ce ta daban me shiɗarwa suka lula.
Cikin wani irin aminci da salama Modibbo ya ɗan sunkuyo kanta kaɗan tare da kawo bakinsa dai-dai saitin kunnenta.
Cikin sarƙafeffiyar muryarsa me kama da raɗa,cikin tsananin sanyi, ta yanda ita kadai zata iya jiyoshi atausashe yace.
“I miss you my trouble maker. I really miss you my trouble student.”
Wow gaba ɗaya falon ya kacame da tafi da sowa.
Sai kuma sarewar da ta karaɗe falon.
Ummi kuwa wani irin amintaccen numfashi ta fesar.
Yayinda Didi kuwa tayin ƙasa da kanta tana sakin murmushin.
Su Lamiɗo da Malam Arɗo kuwa duk ƙasa sukayi da kansu cikin konciyar hankali.
Haiydar kuwa wayarshi ya zaro tare da fara musu video, hakama Rahama.
Yayinda tuni kuma masu ɗaukar hoto suka fara kebta musu.
Zakariyya ne ya ɗan zunguri kafaɗar Modibbo da tashi kafaɗar tare da cewa.
“Kai Jinin Mouley a tsakiyar mutanefa kuke, ka ritsa yar mutane kamar zaka maidata cikin ƙirjinka”.
A can sama ya jiyo muryar Zakariyya wanda ya sashi buɗe idanunsa a hankali.
Hango Lalla Khadijah da wasu mata a ƙalla su bakwai ne ya ɗan sashi sassauta rungumar da yayi mata.
Tare da ɗan jan baya kaɗan.
Fuskashi ya ɗan tsuke tare da kara ronƙofo da kanshi a hankali yasa bakinshi dai-dai iunnenta murya can ƙasa yace.
“Toh yau dai burinki ya cika ai, na ruggume ki, hankalinki ya kwanta tunda kinji ɗumin jikina ko? Kin samu abinda kikeso ko”.
Mui-mui tayi da bakinta
Kara matseta ya ɗanyi tare da cewa.
“Rashin kunya zakiyi minko”.
Baki ta ɗan tura tare da cewa.
“Ni ka sakeni”.
Ɗan haranta yayi tare da cewa.
“Kece ai kike riƙe dani mayya uwar son jiki, tashi min a jiki Mage”.
Da sauri ta ɗan janye jikinta kaɗan.
Dai-dai lokacin kuma Khadijah suka iso.
Kusan a tare suka fara yi musu wani irin....!
*Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta abinki cikin Salamah 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER'N 09097853276 in tura miki abinki ki karanta cikin salam ba tare da kin karanta na Allah ya isaba*
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 16*
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
*Dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn, masu cewa wai sun goda suga number'n nayine, ko kuma a'a bari dai in na shirya zan sake miki mgn, ko kuma yanzu dai kuɗin bai cikaba tukun sai sun cika, ko kuma a wanne gari kike, kai munyi nisa, toh in ba iyayiba ai duk nisan state da kike ba ruwan mota ba inda bazai kai mikiba, nake turawa ƴan ƙasashen wajema. Kuyiwa Allah da Manzonsa in dai in kinsan Baki shirya sayan kaya ba ku daina min mgnar ku bari sai kun shirya,kada kizo ki ɓata min lokaci a banza, wlh ni na tsani harkar karanta, duk bayani na gamayi in dai saya zakiyi ga kuɗin kaya ga account no ga numberta ai sai ki biya kawai kafin kimin mgn. Tunda dai ga alamominshi da duk illar da yakeyi na faɗi in kina dashi faƙat in babu kada ki wani zo kice min bayani dan ko kinzo iya bayanin da zan miki kenan*
Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha'awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni'ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al'ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban lissafa. Sune manyan alamomin infection.
Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.
Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni'ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya, zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.
KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni'imomin ki, da sha'awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA'AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau, duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha'awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor's suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa.
INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai Maganin na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi'izinillahi ta'ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma'ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya'ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER'N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA'AURATA.
Lalla Khadija da Lala Hafsat tare da wasu mata cousing Sister sa ne suka fara yi masu liƙi, cike da nutsuwa da kuma tarin farin ciki dake bayyane asaman fuskokinsu.
Sarkin Zagi dake can gefe riƙe da Microphone ya matso dashi kusa da bakinsa kana yace.
“Maraba da Lalla Hafsat, Lalla Khadija, Autah Rahma tare da sauran Yayyun ango da ƙannensa”.
Su kuwa cike da farin ciki suka ci-gaba dayi masa liƙi bayan sun gama Lalla Khadija ta ɗan matso kusa dashi tace.
“Kayi sauri ka buɗe fuskar Amayarka ta juya ta fuskanci dukan family”.
Ta ida maganar tare da juyawa suka bar wajen.
Shi kuwa Moddibo hankali ya ɗan ƙara matsota, cikin yanayin da shi kansa ya gaza ta tacewa, ya ɗago lallausan tafin hannunsa tare da ware ƴan yatsunsa ya kama kafaɗar ta kana ya juyar da ita ta fuskanci Al'ummar cikin falon baki ɗaya.
Lokaci ɗaya cikin falon ya kaure da tafi Raf-raf-raf yayin da duk wanda yayi arba da fuskar Khausar suke kallonta cikin tsananin farin ciki da ganin baiwar kyau da Ubangji ya zuba mata suke faɗin.
“Wowwww Masha Allah”. Shine abinda mafiya yawansu suke faɗi.
Lokacin guda kuma wasu zugan matasa wanda sun kai goma sha biyar suka nufo kansa cike da izzah, nutsuwa, ƙasaita suke musu liƙi yayin da sautin busar sarewa da ƙaran algaitu ke tashi da sassayan kiɗan jita...
Moddibo kuwa ahankali ya ɗan juya kwayar idanunsu, ya kalli Khausar, sai kuma ya fesar da wani irin sassayyan numfashi, tare da matse hannun ta dake cikin nasa, cikin wata irin sassautacciyar muryansa yace.
“Toh Mazari Sarkin rawa.
ba kinji Busar sarewa da kiɗaba, kiyi rawa na.
Kiga abinda zanyi miki”.
Cikin narke fuska tace.
“Toh ni nace zanyi rawane”.
Ɗan juyo fuskarsa yayi ya ɗan kalleta tare da hura mata iskar bisa idanunta ganin yadda take jujjuyasu, numfashi mai nauyi ya fesar tare da cewa.
“Uhmm kimayi mana ki gani in ban karya ƙugun naki ba!”.
Kallonsa tayi da shanyayyun idanunta wanda yasa bai san lokacin da ya ƙara rumtse tafin hannunsa da nataba.
Ita kuwa cikin yin mui-mui da da bakinta kana ta tsukesu Pinch lips ɗin ta tana ɗan motsawa ahankali alamar magana take ƙasa-ƙasa sai dai baya jin abinda take faɗa.
Sunkuyawa kanta kaɗan yayi tare da cewa.
“Ni kike turawa baki ko?”.
Ɗan kallonshi zuciya cike da ganin girmansa kimarsa gami da darajar da kuma wani matsayi na musamman da takeji a jikinta wanda yake sakar mata kasala da son ƙamshin jiki nai,
Hararanta ya ɗanyi kana a hankali yace.
“Ci gaba da tura min baki, zanyi mgnin lips en nan, idan na tsinkesu zanga dame zaki kuma yimin rashin kunya kije ƙiyama kuma Allah ya ƙonasu tunda mijinki kikeyiwa tsiwa”.
Wani irin lumshe idanunta tayi sabida yadda taji kalmarsa ta karshe ta ratsa mata jiki da zuciya har yasa tsikar jikinta tashi.
Yanayin yanda suke magana ƙus-ƙus ne da yadda suke kallon juna yasa Ummi dake can wajen zamanta, ta saki amintaccen murmushi cike da jin daɗi, mgnar Jameel ɗinta ya tabbata, domin duk wanda ya kallesu zaiyi zaton hirar soyayya suke.
Yayin da zugan matansa suka cigaba dayi masa liƙi wasu baza su wuce sa'annun saba wasu kuma baza su gaza shi ashekaru ba Zakariyya da Ibraahim dake tsaye suma suka shiga cikinsu suna musu Liƙi...
Sarkin Zagi dake riƙe da Microphone ya gyara masa zana tare da kaiwa bakinsa kana yace.
“Duk wa'anan Cousing Brother's ɗin Ango ne, Ƴaƴan Baffanunsa,da kuma ƴaƴan Goggonninsa”.
Bayan sun gama Liƙin suka juya suka fita kana suka koma wajen zamansu.
Ibraahim kuwa kallon Moddibo yayi kana ya mishi alama da hannu su zauna.
Anutse Moddibo ya gyaɗa masa kai kana cikin nutsuwarsa ya koma ya zauna itama Khausar ta zauna gefensa kasancewar 2sitter ne.
Hakan yasa suka samu kusanci tsananin su bayansu flowes ne masu kyau da ƙamshi sai kuma Hadimai da suma ke tsaye bayansu.
Wani irin yalwataccen murmushi mai cike da Aminci Innayi ke saki tana mai cigaba da kallonsu.
Acan ɓangaren Lamiɗo kuwa mamakine ya kamashi aransa yace.
“Toh dama yaran nan suna soyayya da junansu ne? Koko yaya”.
Sosai yake mamakin yanda suke gudanar da komai tamkar akwai da ɗaɗɗiyar soyayya da shaƙuwa atare dasu.
Haiydar kam hotuna da Video yake ɗaukar su, kai tsaye yake turawa cikin groups ɗinsu na family.
Cikin nutsuwa da ƙasaita kana da yalwataccen farin ciki Abualeey da Didi suka tasu,Yayin da Waziri, Galadima, Sarkin Fada, da sauran manya suka mara musu baya, daga can bayansu kuwa Hadimai ne ke biye dasu.
Suna isa dai-dai mazauni Moddibo da Khausar suka fara yi musu Liƙi cike da girma, sai kuma aka ƙara ssutin Busa sarewa da kuma sautun jitan daya karaɗe baki ɗaya ilahirin wajen...
Didi dake cikin wata shiga na alfarma cikin jin daɗi ta ɗan sunkuya tare da sanya hannunta na dama ta ɗan ɗago Fuskar Khausar ta kalleta.
Ido ta lunshs sabida jin lokaci ɗaya yarinyar ta kwanta mata arai, tana jin masifar ƙaunar yarinyar sake sunkuyawa tayi ta rungumeta, sai kuma ta ɗago tare da tallabe fuskan Khausar kana ta sanya laɓɓanta akan goshinta tayi mata kiss.
Fuskarta ɗauke da amintaccen murmushi tace.
“Allah ya miki albarka, Ubangji Allah yasa kin shigo da ƙafar dama, Allah ya baku zaman lafiya mai amfani, mai albarka”.
Lumshe ido Khausar tayi yayin da take jin nutsuwa da ƙaunar matar na ratsa sassan jikinta...
Abualeey kuwa hannunsa na dama dake ɗauke da Zoben azurfa ya ɗaura akan Moddibo tare da faɗin.
“Allah ya maka albarka Ubangji Allah ya albarkanci rayuwarka. Allah ya baka zaman lafiya da matarka!”.
Haka nan Moddibo yake jin wani irin farin ciki ji yake yau kamar ranan Sallah ne, sabida wani irin nishaɗi da yakeji tamkar wanda aka yiwa bushara da Aljanna asaman lips ɗin sa yake amswa da.
“Ameen Ameen”.
Haka nan yake jin farin cikin addu'ar da Mahaifiyar sa da Mahaifinsa keyi masa...
Liƙi suka cigaba dayi musu suna zuba musu kuɗi kamar ba'asan darajar su ba...
Sarkin zaki kuwa hannunsa riƙe da Microphone yace.
“Hattara dai manyan bisa kanku wan'nan sune manyan ƙasar Morocco baki ɗayanta. Jiga-jigan manyan cikin birnin Rarat baki ɗaya manyane bisa kanku ku amsa da Ameen dan addu'a ce ta manyan Ameen.
Baki ɗaya mutanen falon suka amsa da.
“Ameen”.
Saboda sun san cewa addu'a da fatan Al'khairi iyayensa ke masa