Showing 96001 words to 99000 words out of 218703 words

Chapter 33 - Sakayyah 2 Hausa Novel Complete

zatasha, bashi da matsalar komai Maganin na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi'izinillahi ta'ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma'ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya'ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER'N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA'AURATA.


By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 18*

Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*


*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...._
🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

Ummi kuwa cikin sanyi jiki da raunin zuciya take kallonsa sam, jikinta bai faɗa mata cewa wannan ɗan ta bane, amma zuciyarta yaƙi amincewa da hakan.
Juyawa tayi ta kalli Asma'u da hawaye ke cigaba da zuba daga idanunta, kai ta girgiza kana ta maida idanunta kan Moddibo dake cewa.
“Wallahi Ummi wannan ba Jameel ɗinki bane. Nima kaina na gamsu da komai nashi na *J* ne amma ɗabi'unsa ba irin na *J* bane sam sun bambanta tako wacce siga ta hali da ɗabi'a”.
A hankali Dr Jameel dake durƙushe gaban Ummi ya kalli Modibbo tare da rausayar da ƙwayar idanunta acikin nasa alamar kada ka zubar min da mutuncina agaban idonta.

Numfashi Moddibo ya fesar fahimtar kallon Dr Jameel ɗin yamasa shi yasa yayi shiru...
Innayi, Asiya, Aunty Ruƙayya, Aunty Hajara da duk suke tsaye daga gefe suna kallon ikon Allah da Al'ajabi na tsanananin kamannin Dr Jameel da marigayi M Jameel.
Zama Ummi ta gyara tare da jan dogon numfashi kana ta sauƙe cikin sanyi tace.
“Shikenan na gamsu Moddibo, na yarda da kai saboda sanin kai nane, baka taɓa yimin ƙarya ba, kuma koda wasa kake min baka min ƙarya aciki, dan haka na yarda na gamsu wannan ba Jameeluna bane”.
Ta ƙare mgnar tare da lumshe idanunta hawaye masu zafin gaske suka zubo kana ta cigaba da faɗin.
“Amma wannan kamanni da yawa yake.
Kuma Alhamdulillah na godewa Allah daya da wannan Rahma da yayi min na nuna min mai kamannin Fuskar Jameeluna har muryarsa irin na Jameeluna da komai nashi fa”.

Dr Jameel kuwa cikin yanayin buɗe war ido, da kuma gskyar zuciyarsa ya kalli Ummi duk da kuwa yana cikin rauni da tausayinsu, a hankali ya fesar da numfashi tare da maida idanunsa kan Asma'u kana Yace.
“Ummi”.
Da sauri Ummi ta ware idanunta dake cike taf da hawaye jin ya kirata da Ummi.
Sake langwaɓar da kansa yayi idanunsa na kan Ummi ya cigaba da faɗin.
“Ummi da zan samu a bani Asma'u in Aura wlh ina so.
Kinga shikenan sai na zame miki ɗanki Jameel In maye maki gurbin shi”.
Ware idanu Ummi tayi tarexa kallonsa cikin mmkin mgnar shi da tazo mata a bazata, sai kuma taji murmushi ya suɓuce mata batare da tace komai ba ta miƙe ta shiga bedroom..

Asmau kuwa, wani irin fitinennen sanyi kalamashi suka sakar mata, so take ta yunƙu ta mike a guje ta bar wurin amman ta gaza hanan, sabida yadda gaba ɗaya guiwowinta suka sake.

Aunty Hajara, Aunty Ruƙayya, Asiya atare suka saki murmushi kana suka miƙe cike da gamsuwan cewa ba Jameel bane kawai dai kamanni ne, domin da Jameel ne bazai ce zai Auri Asma'u ba wannan kalmar kaɗai ta gamsar dasu cewa ba Jameel bane, domin idan M. Jameel ne babu ta yanda za'a yi yace zai Auri ƴar uwarsa ƙanwarsa da suka kasance uwa ɗaya kana suka sha nono ɗaya, da wannan
gamsassun hujjoji suka bi bayan Ummi zuwa bedroom.
Innayi kam murmushi tayi cike da gamsuwa cewa lalle wannan ba M Jameel bane kamanni ne kawai, fuskarta ɗauke da amintaccen murmushi ta kalli Dr Jameel tare da faɗin.
“Toh an baka”.
Saurin kallonta Moddibo yayi babu walwala atare dashi yace.
“Kece me bada Asma'u koni ne mai bada ita?”.
Still Innayi na murmushi tace.
“Kaine Mai bada ita amma kaima ai ina da iko akan ka”.
Kai ya jinjina tare da faɗin.
“Eh kina da iko akaina Innayi, amma ai shi Aure ɗan bincike ne sai na bincikesa nasan ingancin sa tukunna kafin na bashi Asma'u”.
Asma'u kuwa tun lokacin da yace yana sonta data daskare zaune, sai yanzu taji tayi azamar miƙewa sabida jin kuzarinta ya dawo,
Da gudu ta miƙe tabar wajen yayin da Khausar ta miƙe tabi bayanta.
Cikin lumshe idanu Moddibo yabi Khausar da kallo har ta ɓacewa kallonsa idonsa na kanta wani sassayyan numfashi ya fesar tare da lumshe ƙwayar idanunsa.

Zakariyya kuwa tunda suka shigo idonshi na kan Aseeya gaba ɗaya ya gaza ɗauke idanshi a kanta.
Ibraahim kuwa shiru yayi yana kallonsu kawai.

Ganin duk sun watse yasa Innayi maida kallonta kan Moddibo kana tace.
“Bismillah kuje kuci abinci naga kamar abinci kuke ci na tada daku”.
Kai suka gyaɗa tare dayi mata sallama kana suka tafi.

Suna shiga Falon Dr Jameel ya kamo hannun Moddibo tare da langwaɓar da kai kana cikin sanyin murya da neman alfarma yace.
“Na roƙeka da girman Allah Moddibo kada ka faɗi wani abu da zai zubar min da kima da daraja a idon Ummi”.
Kallonsa kawai Moddibo, Ibraahim, Zakariyya sukeyi Shi kuwa cikin sanyi da neman alfarma ya cigaba da cewa.
“Na lura tana kallona da kima da daraja kuma Wallahi har cikin raina ina ƙaunar Asma'u kuma Aurenta zanyi”.
Cikin sauri Moddibo ya tari numfashinsa ta hanyar cewa.
“Gaskiya ayanayin kan nan dana lura da kai. Wallahi bazan baka Asma'u ba, Asma'u nine nan mai bada ita,Tana da mahaifi, Lallai Mahaifinta shine zai bada ita.
Amma bisa yaƙinina zai bada ita. Ni kuma bani da yaƙini akan ka”.
Sai kuma ya ɗan furzar da iska mai zafi yana tuno yanayin munanan halayyar Dr Jameel kai ya girgiza kana yace.
“Baka da tsarkakan da zan baka tsarka-kakkiyar yarinya saboda Asma'u tsarka-kakkiyar ce.
Kallonsa kawai Dr Jameel keyi cikin rauni da nadama ɗabi'unsa da yakega zasu kasance mihsi barazana daga mallakar ƴarinyar da yakeji in bai setaba zai zauce.

Moddibo kuwa cikin yaƙini da gaskiya ya cigaba da faɗin.
“Saboda Faɗin Allah ma ɗaukakin sarki ne, cewa. Mazinaci baya Aure sai Mazinaciya ƴar uwarsa Asma'u kuwa tsarka-kakkiya ce ba Mazinaciya bace kai kuma kafi kowa sanin kanka”.

Ahankali Zakariyya da tausayin Dr Jameel ya gama cikawa zuciya ya kamo hannun Moddibo suka zauna kana cikin nutsuwa yace.
“Kayi haƙuri Moddibo ai abu da yawa yana zama sanadin shiryuwar mutum kada kayi mamaki Auren Asma'u ya kasance hanyar shiryuwan Dr Jameel”.
Kai Ibraahim dake gefe ya jinjina tare da cewa.
“Hakane Yah Aleey tunda har yace yana sonta da dai ashige masa gaba ba ba mamaki wannan abin da yake rashin mata ne”.

Dr Jameel kuwa cikin gaskiya da gaskiya ya kalli Moddibo kana yace.
“Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! In dai za'a bani Asma'u Ni dai nayi al'ƙawari zan rabu da duk wata ƴa mace”.
Ganin gaskiya acikin ƙwayar idanunsa yasa Moddibo fesar da numfashi tare da cewa.
“Shikenan ka fara rabuwa dasu tukunna idan na gamsu ka rabu dasu.
Ni kuma zan baka ita In dai har na gamsu”.
Cike da farin ciki Dr Jameel ya gyaɗa kai kana yace.
“Ni kuma nayi maka al'ƙawari daga yau daga yanzu na rabu dasu”.
Ya ida maganar tare da zaro wayarsa kana ya shiga contact tare da blooking ɗin Number duk ƴan matan sa kana ya nunawa Moddibo.
Murmushi Moddibo yayi kana yace.
“Toh Allah yasa kayi iya deleting ɗin su acikin Mind ɗin ka da zuciyarka kamar yanda kayi awayarka”.
Asanyaye Dr Jameel ya furta.
“In sha Allahu babu kowa a raina”.

Juyowa Modibbo yayi ya kalli Ibarahim dake miƙa mishi woyoyinsa,
Murmushi Ibraahim yayi tare cewa.
“Tun da safe Abualeey ya bani su yace amman in bari sai dare in baki”.
Murmushi Modibbo yayi tare da cewa.
“Ummm yayi kyau”.
Cikin wasa Ibraahim yace.
“Nasa maka caji ne dan naga sun mutu sabida kiraye-karen da akayi ta maka”.
Miƙewa yayi tare da cewa.
“Yoh ba dole su mutuba moko guda”.

“Eh amman ai yanzu duk a cike suke”.
Cewar Ibraahim.
Kai Modibbo ya gyaɗa mishi yana mai kunna woyoyin nasa.

Acan ɓangaren su Khausar kuwa tunda suka shiga bedroom take sakin murmushi idanunta akan Asma'u da duk tayi zuru-zuru da ita kana tace.
“Asma'u Wallahi wannan ba Yan Jameel bane”.
Kallon mamaki Asma'u tayi mata Still hawaye na bin fuskarta tace.
“Kamar ya zakice ba Yah Jameel bane”.
Hannunta Khausar ta riƙe tare da cewa.
“Asma'u jikina ya faɗa min ba Yah Jameel bane.
Ki sani da Yah Jameel ne ko cutan hauka yayi ba zai kalleki yace yana sonki amatsayin matar Aure ba”.
Sai kuma ta sake damƙe hannun Asma'u acikin nata cikin son tabbar mata da gaskiya ta cigaba da cewa.
“Ki tuna fa Nono ɗaya kuka sha mahaifiya ɗaya ce ta haife ku fa wallahi Asma'u ba Yah Jameel bane, kawai ni inajin farin ciki araina ne. Alhamdulillah bazan rayu Ni kaɗai aƙasar nan ba zan rayu tare dake, zai ɗakko min ke ya dawo min dake ƙasar nan mu rayu tare”.

Zazzafan Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe idanunta akan Khausar tace.
“Wallahi nifa Khausar har yanzu ban gamsu cewa ba Yah Jameel bane”
Kai Khausar ta girgiza tare da cewa.
“Wallahi Asma'u ba Yah Jameel bane ya za'a yi Yah Jameel yace yana sonki zai Aure ki, Asma'u kiyi tunani mana hakan bazai taɓa faruwa bafa”.
Haka dai sukaci gaba da tattaunawa.
A daren wannan ranan haka suka cika da alhini da al'ajabi...

Acan Side ɗin Didi kuwa zaune suke da ƙannenta da kuma Yayyanta da suka zo.
Baki ɗaya hirar tasu akan Khausar ce suna yabon kyawu da kuma haibar da Khausar tayi kowa na faɗin albarkanci bakinsa.
A wannan ranan haka duka ahalin suka kwana cikin yalwataccen farin ciki.

Washe gari aka shirya taro na alfarma wanda baki ɗaya manyan Fada da kuma manyan Masarautar Morocco ne taro ne wanda yafi na jiya sai dai wannan taro ne na maza zalla saboda an gabatar da Moddibo amatsayin Sarki mai jiran gado kana ana gabatar dashi a baki ɗaya idon Fada sosai Moddibo yayi jawabi daya ratsa zukatan mutane kasancewar shi aka bawa Microphone ya rufe taron da addu'a.
Al'amarin da ya gigita jama'ar masarautar jin yanda ya dinga zazzago addu'oi yana rerawa cikin zazzaƙan muryansa.
Wani irin farin cikine ya mamaye zuciyar Abualeey ya tabbatar da cewa ɗan sa ya samu kyakkyawan tarbiyya da jigon da zai iya mulkar masarautar Mouley.
Cikin jin daɗi yake kallonsa,

Shi kuwa Modibbo addu'oin daya ta jerawa na yayi dai-dai da lokacin da aka kira Sallar Azahar.

Limamin masallacin Fadan dake zaune gefe wanda tsohone tukuf ya tsufa sosai bisa alamu kuma sa yanayin jinya na tsufa.
Cikin jin dadin ya sauke A tare da karɓan Microphone ɗin kana yayi jawabin cewa,
Shi ya fahimci wannan Yariman yana da cikekken ilimin addini dan haka daga yau ya sauƙa daga kan karagata na limanci shine zai cigaba da limanci masallacin masarautar su kasancewar tsufar da ya cimasan da kuma sanyin da muryasa keyi wacce wasu lokutan bata isarwa mabiyan jam'inshi.
koda Modibbo yaji haka yayi ƙoƙarin maida tayin da limamin yayi mishi amman ina yaƙi sabida da gskyarsa sufa tacin mishi.
Sai kallon Modibbo yake cikin so da
Amintaccen murmushi mai cike da yarda da yaƙini kamilin dattijon yake bin Modibbo da Addu'o'i kana ya ɗaura da cewa.
Hakan za'a yi kuwa domin Modibbo ya cancanta sai dai ko in baka kusa ko kayi tafiya ko wani abu dai to sai in jamu.
Daga haka taron ya tashi da yaƙin cewa an bar mishi Limanci...

Aranar Modibbo ne yaja limancin sallar Azahar, wanda baki ɗaya sautin zazzaƙan muryarsa ya cika masarautar.
Wanda baki ɗaya al'umma cikin Masarauta ke yaba zaƙin muryansa.

Bayan an idar da sallar Azahar Direct sashen Didi Ibraahim ya nufa cike da farin ciki ya zauna gefen Didi tare da riƙe hannunta kana yace.
“Didi kinsan waya ja mana jam'i?”.
Kai ta girgiza tare da faɗin.
“A'a sai ka faɗa?”.
Cike da matsanancin farin ciki yace.
“Wallahi Yah Aleey ne Kai Didi wlh Innayi ta gama mana dukkan gata na duniya”.
Fuska ɗauke da yalwataccen farin ciki Didi tace.
“Kai Alhamdulillah”.

A ɓanƙaren su Modibbo kuwa, Sheiyk Jabeer ne tare Modibbo sai Jabeer bin Jabeer cikin kulawa Modibbo yace.
“Sheiykh yau yau kuma zaku koma?”.
Gyaran murya Sheikh Jabeer yayi tare da cewa.
“In Allah kuwa yanzuma zamu tafi airport dama kafin mu tafi masallaci nayi sallama da kowa na Fada harma da Didinku munyi sallama.
Tafiyar ce ta gaggawa ta sameni zan koma ne saboda gobe da yamma muna da zama da ƙungiyar *MI YETTI ALLAH* Akam matsalolin Garkuwa da mutane ƙasarmu ke fuskanta.
Toh yadda ake maida akalar zargin kan cewa Fulani ne keda alhaƙin hakanne yasa ƙungiyar *TABITAL POOLAKU* shiga mgnar da keɓance ƴaƴanta Fulani da wonkesu daga zargin da ake musu domin suma fulanin basu tsiraba, anayi musu wannan zalumcin su a ƙara da kashesu ma”.
Cikin sauƙe nannauyan numfashi Modibbo yace.
“Gsky wannan ƙudurine mai kyau, domin abune daya addabi ƙasarmu, kaga wala Allah cikin haka a gano masu aikata hakan”.
Cikin kulawa Sheiykh yace.
“In sha Allah kuwa, domin fulanin zamu wakilta mu naɗasu aikin bamu rahoton duk abinda ke gudana cikin dajukan za mu rabasu ko wanne state na Nigeria”.
Sai kuma suka kalli Jabeer bin Jabeer dake cewa.
“Musamman Zamfara Sokoto Katsina abun yafi tsamari a can”.
Moddibo ne ya ɗan fesar da numfashin mai zafi kana yace.
“Ni kuwa ina so a ruɓanya masu binciken Taraba yankin Gembulan domin anayi musu illa sosai, a sanadin su na rasa J na”.
Sheykh ne ya ɗan kali agogo dake hannunsa tare da cewa.
“Eh nima da batun Jameel da kayi mana bayani na kuduri aniyar in sha Allah, sai na gano waɗanda suka yi masa wannan kisan gillan, in ban mantaba kace min akwai wacce taga mota bibiyarsu kuma har ta ɗauki number'n ko?”. Da sauri Modibbo yace.
“Eh Khausar ce”.
Cikin samun cikekken yaƙini kan binciken Sheykh yace.
“Toh ba matsala idan kun nitsu, ka nemi min cikekken bayanin a wurinta, sai ka tura min komai, in Allah ya yarda jininshi bazai tafi a banzaba”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“In sha Allah kuwa”.
Daga nan sukayi sallama, Abualeey da kanshi yayiwa surkin nashi da ƙanin matarsa rakiya zuwa Airport, bai dawoba saida jirginsu ya tashi.

Acan ɓangaren su Khausar kuwa zaune take kan sallayar tun bayan data idar da sallar Azahar bata motsa ba.
Innayi dake gefe ta saki murmushi tare da faɗin.
“Kai Alhamdulillah naji daɗin nagartar Moddibo ina farin ciki da hakan”.
Kai Ummi dake gefenta ta jinjina kana tace.
“Ai dai kam Alhamdulillah”.
Daga haka suka cigaba da hira wanda mafi yawa akan Moddibo ne...

Acan ɓangaren Hajiya Bunayya kuwa zaune take a bedroom ita kaɗai yayin da Asiya ke toilet tana wanka.
Hajiya Bunayya kuwa wayane maƙale a kunnenta tana magana da Amina dogon tsaki taja tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login