Showing 6001 words to 9000 words out of 218703 words
haddar Alkur'ani kin sauƙe sannan kinsan, Ahallari, Kinsan ishmawi, Kinsan Fiqhu, Kinsan Arbauna, Kinsan Sira da sauransu yanzu wani karatu ya rage miki”.
kallonta kawai take sai data gama jerawa kafin tace.
“Karatu kam wanda ya ragene yafi yawa aisharan fage kawai nayi acikin karatu”.
Harara Hajja Nana ta watsa mata cikin yanayin zafinta tace.
“A'a sannu Al-huda-huda sarkin karatu dole kika ce sharen fagi kikayi mana, tunda kin samu anbarki kinyi wannan ɗin”.
Sake baki Khausar tayi tare tura baki kana tace.
“Ikon Allah dana samu anbarni nayi da mekike nufi kenan, ko kuma dama kece zaki tsara min abinda zanyi?”.
Gyara zama Hajja Nana tayi cikin ƙanƙance Ido tace.
“Ke ko kunya bakya ji dube ki fa duk kin gama girma agida shekarunki kusan Ashirin ai wannan ma taumaka miki za'ayi dan kin gama tsufa”.
Buɗe baki Khausar tayi tare da kallon kanta kana ta kalli Hajja Nana cike da Isa Hajja Nana tace.
“Kalleni da kyau yo ƙarya na miki, ƙannen bayanki nawa aka Aurar wasu da yara bibbiyu wasu kuma ɗaddaya ke kam wannan wani sai dai yace bazawara ce ke dan kin gama girma”.
Wani kallo Khausar ta mata tare da cewa.
“A'a Hajja Nana ya isa haka cin fuska dan wlh bazan juraba.Wanda suka fini dubu nawa ne basuyi Aure ba, sai dai idan A Rugar kune ake irin wannan Auren, amma nikam yanzu ma nayi ƙarama da Aure.
Mommy kuwa kallon Khausar tayi tare da ɗaga mata hannu kana tace.
“Haka naki Khausar kiyi mana shiru”.
Sunkuyar da kanta ƙasa tayi batare da ta sake cewa Uffan ba kawai dai tasan in ba ita ke tare Hajja Nana ba Mommy kam ba abinda zatace tanaji tana gani za'a tauyeta.
Hajja Nana Khausar ta nunata da ɗan yatsa tace.
“Ki kiyayeni bada ke nake magana ba fitsararriya mara kunya!”.
Gyara zama Khausar tayi tare da juya mata manyan Idanunta da kawar da kai gefe.
Murmushi Dije dake gefen Khausar tayi tare da riƙe hannun ta da ido tayi mata alamar ta daina.
Gyaran murya Hajja Nana tayi tare da cewa.
“Aysha Ni dake nake magana bada Khausar ba, ya batun maganar da mukayi tunda Allah yasa tagama yanzu, sannan makon daya gabata Baffanta yazo daga Adamawa aranan daya zo aranan ya koma”.
Sai kuma ta kalli Khausar tare da watsa mata Harara kana ta maida kallonta kan Mommy dake sauraronta tace.
“Toh dama ace yazo da niyyar kwana zamu ƙara so nan, ayi magana to amma ke me kikace tsakaninta da Aliyu ɗan Uwanta!?”.
Ahankali Mommy ta sunkuyar da kanta ƙasa kana tayi shiru cikin yanayin sanyinta da Kawaici, da mutumtaka da kuma kamala tace.
“Toh Hajja Nana wannan magana duk yanda kuka zantar ai hakane Baffanta shine me Aurar da ita, dan haka duk abinda ya yanke akanta shine dai-dai”.
Jinjina kai Hajja Nana tayi tare da tura kallabin kanta kana ta gyara zamanta cikin jin daɗi tace.
“Shima yace min Insha Allah nan da wata ɗaya ko sati uku zai zo idan ya samu sarari zaizo su zanta da Uban goyon yarinyar, shima abashi mutuncinsa tunda shi ya raineta tun tana da wata wata uku shi yamata komai”.
Kai Mommy ta gyaɗa tare da faɗin.
“Bakomai duk abinda kuka tsara yayi Idan har Auren Khausar da ɗan Uwanta Al'khairi ne Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa”.
Cikin sauri Khausar ta tura bakinta tare da cewa.
“Ni dai bana sonshi kuma ke dai Mommy ayita Addu'ar alkhairi”.
Wani kallo Mommy ta watsa mata alamar rufe min baki, shiru Khausar tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa Mommy kuwa kallon Hajja Nana tayi cikin sanyin murya tace.
“Ni dai Allah ya tabbatar da al'khairi idan al'khairi ne Allah ya tabbatar ya kuma zaɓa musu abinda yafi zama al'khairi atsakanin su.
Gyara zama Hajja Nana tayi kana tace.
“Ammen,Kuma Insha Allahu ma alkhairi ne”.
Kai Mommy ta gyaɗa tare da cewa.
“Adduar da mukeyi kenan”.
Miƙewa Khausar tayi tare da riƙe hannun Dije da alamun ɓacin rai tace.
“Dije mu tafi”.
Harara Hajja Nana ta watsa mata tare da sake tura daurin Kallabinta gaba kana tace.
“Aikuwa wannan magana ya zama dole ki saurareta tunda batu ne na Aurenki akeyi”.
Cikin ƙankance Ido Khausar tace.
“Nifa bazanyi Aureba ehe ke baki da aiki sai ƙaƙale ƙaƙalen magana ina ruwanki da batun Aurena!?”.
Afusace ta kalleta kana tayi Ƙwaffa tare da cewa.
“Aikuwa dan Ubanki nike da ruwa dake kuma dole kiyu Aure”.
cikin tsirawa Hajja Nana ido tace.
“Amma dai na faɗa miki ki daina zagin mahaifina Aure kuwa idan Allah ya nufa zanyi amma ba wanda kike cewa ba kam!?”.
Ajiyar zuciya Hajja Nana ta sauke kana tana kallonta bako ƙyaftawa sai kuma ta sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.
“To wa kike so ki Aura?”.
Juya ido Khausar tayi tare da cewa.
“Aini nasan wanda zan Aura, kuma dan haka babu ruwanki dani sai kace ke lokacin da zaki yi Aure zaɓa miki wanda zaki Aura akayi ba ke kika zaɓa da kanki ba!”.
Girgiza kai Mommy tayi tare da nunawa Khausar hanya da hannu alamar tabar wajen ita har ga Allah bata so ma Hajja Nana ta tsaida Khausar a cikin mgnar ba in bana tsohuwaba taya zata tsaida Khausar bayan tasan yadda suke da juna.
Tura baki Khausar tayi tare da jan hannun Dije dake murmushi sam bata gajiya da kallon Dramer Khausar da Hajja Nana.
Khausar da Dije na isa ƙofar Bedroom ɗin zasu shiga Akuma dai-dai lokacin Asma'u tayi sallama cike da ladabi tsugunna agaban Mommy ta gaisheta Cike da kulawa Mommy ta amsa tare da tambayarta ya Umminta ta amsa da tana lafiya.
Kana ahankali ta maida kallonta kan Hajja Nana dake cin Inabi tace.
“Hajja Nana inayini fatan kunzo lafiya?”.
Kai Hajja Nana ta gyaɗa tare da cewa.
“Lafiya lau Alhamdulillah Allah ya miki albarka kar dai ki riƙa ɗaukar hallayar wasu ƙawaye na tsiwa”.
Ɗan murmushi Asma'u tayi kana cikin sanyi ta gyaɗa kanta Khausar dake tsaye bakin ƙofa ta wani ɓata fuska tare da kawar da kai gefe.
Miƙewa Asma'u tayi ta nufi wajensu Khausar suka shiga Bedroom cikin ɗan sakin fuska da sanyi Asma'u tace.
“A Dije sannu da zuwa ya gida ya mutanen Jauro yaya!?”.
Murmushi Dije tayi cikin yanayin sanyin ta tace.
“Duk lafiya lau?”.
Kallon Dije Khausar tayi kana cikin sanyin tace.
“Ayyah Dije yayan Asma'u Malam Jameel Allah ya masa rasuwa kwanan nan ƴan Kidnapping suka kashesa!”.
Cike da tausayawa Dije tace.
“Ayyah Ubangiji Allah yajiƙan sa da rahma sukuma Allah ya tona musu asiri”.
Atare Asma'u da Khausar suka amsa da.
“Ameen”.
Asma'u kuwa Idanunta ne suka ciko da ruwan hawaye.
Cikin sanyi Khausar ta dafa kafaɗar ta kana tace.
“Dan Allah Asma'u kiyi haƙuri kin sani babu abinda Yah Jameel ke buƙata awajenmu face addu'a Insha Allah Yah Jameel na cikin rahamar Allah”.
Jinjina kai Asma'u tayi kana cikin sanyin murya tace.
“Insha Allah muna yi kuma zamu cigaba dayi”.
Miƙewa Asma'u tayi tare da kallon khausar cikin sanyin murya tace.
“Toni zan tafi”.
Da sauri Khausar ta ɗago kanta cike da kulawa tace.
“Sauri-sauri haka”.
Kai Asma'u ta gyaɗa tare da lumshe Idanunta cikin sanyin murya daya zame mata jiki tace.
“Wallahi gidan Innayi nake son zuwa dama na biyo ne akan ince muje ki rakani kuma sai na ganki da baƙuwa, shiyasa nayi shiru bance komai ba”.
Ajiyar zuciya Khausar ta sauke tare da tsira mata ido cikin fesar da numfashi tace.
“Ayyah wallahi kuwa badan baƙuwar ba ai da naje na rakaki amma lafiya kuwa?”.
Kai Asma'u ta gyaɗa tana gyaran zaman hijabinta tace.
“Eh Ummi ce ta aikeni wajen Innayi akan Inje wajen.
Yaya Moddibo yau kusan sati kenan bai sake zuwa gidanmu ba sannan kuma Innayi ma ta kirata tana faɗa mata ko cikin gida baya fita”.
Jinjina kai Khausar tayi cike da tausayinsu tace.
“Allah sarki Malam Moddibo dole ya shiga cikin tashin hankali da alhinin rashin.
Yah Jameel insha Allahu jinin Yah Jameel da hakkinmu ba zai taɓa bari wannan mutanen su samu salama acikin rayuwarsu ba!”.
Kai Asma'u ta gyaɗa cikin sheshsheƙan Kuka tace.
“Tabbas sun cutar da rayuwar mu, cuta mafi muni sun zalunce mu kana sun ɗauke mana duk wani farin ciki da walwalarmu. Yah Jameel shine Komai namu Yah Jameel shine fitilar dake haska zukatanmu amma dare ɗaya suka rabamu da wannan hasken kuma jigonmu”.
Cikin sanyi da tausayawa Dije tace.
“Asmau'u kiyi haƙuri Allah baya zalunci sannan baya bari ayi zalunci da sannu Ubangiji zai fallasa asirin wanda suka aikata wannan ta'asar sannan sai sun wulaƙanta wulaƙanci mai muni insha Allah”.
Cikin sanyi da Khausar da su kaji mutuwar ya dawo musu sabo suka hada baki wajen cewa.
“Ameen”.
Miƙewa Asma'u tayi tare da faɗi.
“Bari na tafi dan Ummi tayi ta kiran wayarsa baya ɗauka sannan itama Ummi baki daya bata jin daɗin jikinta sosai ta dawo tamkar majinyaciya.
Khausar sai kinga gidanmu baki ɗaya duniyar bata mana daɗi”.
Cikin sanyin da rarrashi Khausar tace.
“Ayyah Asma'u am haka rayuwa ta gada Ubangiji Allah ya jikan Yah Jameel da rahma mu kuma Ubangiji yasa mana dangana azuciyarmu sannan mu cigaba dayi masa addu'a gatan da zamu nuna masa kenan”.
Kai Asma'u ta gyaɗa kana tace.
“in sha Allah, na tafi”.
Kai Khausar ta gyaɗa sannan ta kalli Dije tace.
“Muje mu rakata”.
Miƙewa Dije tayi sannan suka fita bayan Asma'u ta yiwa Mommy da Hajja Nana sallama har bakin hanya suka rakata saida ta samu adaidaita ta hau sannan suka koma.
Asma'u na isa gidan direct Sashen Innayi ta nufa zaune ta hango Innayi kan barandar ta tayi tagumi da hannunta na dama jin anɓude ƙofa yasa tayi saurin ɗaga kanta ganin Asma'u yasa ta saki Ajiyar zuciya.
Cikin sanyi Asma'u ta ƙarasa tare da zama agefenta cikin sanyin murya tace.
“Innayi”.
Numfashi Innayi ta fesar tare da tsira mata ido cikin alamun damuwa tace.
“Na'am Asma'u kin zo ya jikin Umminki!?”.
Kanta aƙasa tace.
“Innayi da sauƙi Ina Yah Moddibo fa?”.
Ajiyar zuciya me nauyi Innayi taja kafin ta sauƙe cike da damuwa tace.
“Asma'u bansan wani irin yanayi Moddibo yake ƙoƙarin shiga ba baki ɗaya ya zama wani iri ya dawo tamkar mara lafiya ya zama abin tausayi koda fitowa bayayi”.
Sai kuma ta runtse Idanunta cike da damuwa kana ta buɗe su tare da cewa.
“Ko abinci idan bana nuna masa ɓacin raina ba baya ci banda ruwan tea Babu abinda yake sha baki ɗaya ya sauya duk hankalina ya tashi na rasa yanda zanyi.
Gaba daya ƙasar nan tafi raina duniyar ta isheni”.
Sunkuyar da kai Asma'u tayi tana jin hawaye na cika kwarmin Idanunta.
Cikin raunin murya Innayi ta kalli Asma'u tare da cewa.
“Na rasa yanda zanyi da Moddibo ɗazun nan ma Abban Jameel ya fita dalilin zuwansa da yayi masa.
Nasiyya da kwantar masa da hankali shine ma muka samu ɗazun yasha kunu”.
Numfashi mai zafi Asma'u ta fesar tare da kallon Innayi tace.
“Ummi ma tace tana som ganinsa baki ɗaya ta damu da rashin zuwansa kuma koda ta kira wayarsa baya shiga bare taji muryarsa, Innayi barin shiga wajensa”.
Kai Innayi ta gyaɗa kana tace.
“Shikenan ba matsala muje”.
Miƙewa Asma'u tayi tare da nufar Sashen sa Innayi na biye da ita.
Innayin ce ta tura ƙofar falon suka shiga ahankali Idanun Asma'u suka sauƙa akan Moddibo dake zaune kan 1sitter Ƙirjinsa Rungume da Alkur'ani yayinda idanunsa ke lumshe suna tsiyayar da hawaye kana dashash-shiyar muryarsa na rera karatun Alkur'ani.
Cikin mutuwar jiki Asma'u ta zauna daga gefen ƙafafunsa Innayi kuma ta zauna daga saman kujeran.
Ganin yanda hawaye ke fita Shar-shar-shar a idanunsa yasa Asma'u fashewa da kuka mai gunji hadda sheshsheƙa.
Jin sheshsheƙan Kukan Asma'u yasa Moddibo da idanunsa ke lumshe saurin buɗewa ganin yanda Asma'u ke kuka da sheshsheƙa yasa yayi saurin sanya tafin hannunsa yashiga goge hawayen dake saman kuncinsa.
Cikin sanyi Innayi ta kallesa tare da cewa.
“Moddibo!, Moddibo!!, Moddibo!!!”.
Ahankali ya ɗago kumburarrun Idanun sa da suka jiƙe da hawaye kana Eyelashes ɗinsa sun kwanta cikin sanyi ya kalleta.
Innayi kuwa cikin tsaresa da Ido tace.
“Moddibo za kayi fushi da hukuncin Ubangiji ne?”.
Cikin sauri ya girgiza mata kai tare da cewa.
“Astagafirullah³”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe kana ta tsira masa Ido tace.
“Toh Meyesa Moddibo baka fita, baka cin abinci sannan baka walwala, kenan fushi kake da Ubangijin daya bamu Jameelu sannan ya ɗaukesa!?”.
Kai ya girgiza mata batare da yace Uffan ba!.
Cikin sanyi da rauni Innayi ta zuba masa Ido baki ɗaya Garin Jahar Taraba da maƙasar Nigeria yafi ta ranta, fesar da numfashi kana tace.
“Toh Meyesa sai dai ka ɗauki Kur'ani ka rungume kana karatu kana kuka”.
Cikin wata dashash-shiyar murya me cike da rauni da tashin hankali yace.
“Innayi mai zan fita nayi acikin garin Gembulan? Innayi da waye zan fita? Innayi baki ɗaya garin nan ya fita raina bana son garin nan na tsani garin nan garin nan ya fita min araina”.
Sai kuma ya runtse Idanunsa da ƙarfi yayin da jijiyoyin kansa suka tashi ruɗu ruɗu dasu kana zuciyarsa ta shiga bugawa da masifar ƙarfi cikin dauriya ya buɗe idanunsa da suka yi masifar Ja yace.
“Innayi duk inda na wulga acikin garin Gembulan zanga kamar J ɗina na akusa dani, shin Innayi taya zan fara fita da waye zanyi yawo da waye zanje masallaci da waye zanyi dariya da wa zan dawo gida da wa zan zauna inci abinci!?”.
Asma'u kuwa kife kanta jikin kushin ɗin da yake zaune tayi tare da fashewa da wani irin kuka tabbas sunyi rashin da baza su sake samun kwatankwacin saba sannan kuma anzalince su zalinci mai muni da raɗaɗi.
Jin yanda Asma'u ke kuka kamar ranta zai fita yasa Moddibo juyawa ya kalleta cikin sanyi da tausayinta yace.
“Asma'u ki daina kuka ki yiwa J addu'a domin shine abinda yake buƙata atare damu”.
Innayi kuwa kallonsa tayi har zuwa lokacin hawaye na zuba daga idanunsa ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.
“Toh Moddibo kaima fa kukan kake ya za ayi Asma'u ba zatayi kuka ba”.
Kallon Innayi yayi tare da lumshe idanunsa wasu hawaye masu masifar zafi suka zubo masa.
Anutse ya goge tare da cewa.
“Innayi idan har bana samu na rungume Kur'ani ina karatu ba bana samun damar hawaye suna zubo min, sannan aduk lokacin da hawayena ke zuba inaji kamar ana zare min wani abu mai nauyi ne acikin ƙoƙon raina, shiyasa nake rufe kaina ni kaɗai nayi ta kuka”.
A tausashe ya kalli Innayi data tsaresa da ido ya cije Lip ɗinsa kana yace.
“Innayi idan har banyi kuka ba menene amfanin Idanuna da hawayena? idan ban zubar dasu arashin J ba J fa Innayi J ɗina”.
Numfashi Innayi ta fesar cikin sanyi tace.
“To ai addu'a zaka yi masa Moddibo”.
Cikin dashash-shiyar muryarsa daya dishe da kuka da tashin hankali yace.
“Innayi to ai ina masa addu'a”.
Asma'u kuwa ahankali ta ɗago Idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye ta kallesa cikin sanyi tace.
“Yah Moddibo Meyesa ka daina zuwa wajen Ummi?.
Baki ɗaya hankalinta ya tashi ta dawo kamar mara lafiya?”.
Girgiza kai yayi tare da kallonta kana cikin sanyi yace.
“Asma'u ki cewa Ummi tayi haƙuri insha Allah zan zo amma ina jin wanin irin yanayi ne taya zan kalli al'amarin tayaya zan iya zuwa wajen Ummi ba tare da J na kusa dani ba?”.
Numfashi mai zafi ya fesar da karfi kana yace.
“Baki ɗaya rayuwa tayi min ƙunci na rasa madafa, komai ya min duhu acikin duniyar nan na rasa yanda zanyi da kaina baki ɗaya na rasa yanda zan fuskanci al'amarin”.
Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe tare da fesar da nunfashi ta kallesa tare da faɗin.
“Ni dai Yah Moddibo mu tafi, idan har baka jeba Ummi na cikin tashin hankali da damuwar rashinka, koda magana da Ummi ba tayi idan ba mun matsa mata ba amma sai ta zauna shiru ita kadai afalo baki ɗaya gidan ya daina yi mana daɗi”.
Ahankali Moddibo ya taune Lip ɗinsa kana yace.
“Insha Allah zan zo ki cewa Ummi tayi haƙuri”.
Girgiza kai Asma'u tayi kana tace.
“A'a Yah Moddibo nidai gaskiya Ummi tace sai dai muje tare”.
Gyara zama Innayi tayi tare da fuskantar Moddibo cike da kulawa tace.
“Toh ka tashi kuje matuƙar kana son farin ciki da kwanciyar hankalin Ummin ka, kada ka haɗa mata ciwo biyu Moddibo kasan rashin ka awajen Ummi babban matsala ne”.
Cikin sauri Asma'u tace.
“Wallahi kuwa Yah Moddibo baki daya ƙuncin ya mana yawa, ba kai babu Yah Jameel. Baki ɗaya zuciyarmu acunkushe yake da damuwa amma ganinka zai ɗebe mana kewa”.
Cikin sanyi da rarrashi Innayi tace.
“Ka daure kaje ko hankalinsu zai kwanta kuma kaima za kaji sauki acikin ranka”.
Ta ida Maganar tare da miƙa masa key tsohuwar motar data fara saya mishi.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da karɓa kana ya miƙe cikin sanyi ya Murɗa handle din ƙofar
tare da fitowa wajen, cikin sauri ya lumshe idanunsa rabonsa da ganin haske irin haka ko kuma ya taka kofar falon yau tsawon kwana biyar kenan ko da sallah agida yake baya fita jam'i kai tsaye inda Motarsa yake ya nufa ya shiga sannan yaja suka tafi.
Innayi kuwa na ganin tafiyarsu ta kira Number Malam Arɗo bayan ya ɗaga tace.
“Dan Allah Malam Arɗo idan babu damuwa kazo ina da magana da kai”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Toh badamuwa Insha Allah zan zo”.
Modibbo kuwa suna isa memory sa ya shiga tariyo masa hoton fuskar J ɗin sa cikin sauri ya juya gefen damansa jin kamar sautin murya J ɗinsa cikin dariya yana cewa A.J tsayuwar me kakeyi Please kazo mu shiga inga Ummina kasan dai nayi missing dinta da yawa.
afili ya furta.
“J kai ko nima ainayi kewarta kuma dan na tsaya jiranka ne da tuni na taho”.
Murmushi yaga M Jameel ya sakar masa sannan ya janye hannunsa daga cikin nasa ya juya ya fara tafiya yana jujjuya masa hannu alamar Byebye.
Da sauri Moddibo ya juya tare da cewa.
“J ina kuma zaka je ba kace ka matsu kaga Ummi ba?”.
Cikin sauri Asma'u dake Kallonsa ta tashare hawayen dake kwaranya a Idanunta kana tace.
“Yah Moddibo Yah Jameel fa baya nan sannan bazai taɓa zuwa inda muke ba”.
Moddibo kuwa ido ya tsirawa Asma'u kamar mai son fahimtar abinda take faɗa sai kuma yayi saurin dafe kansa tare da maimaita Kalmar Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n shi kansa yasan zuwa zuwa yanzu dai kamar zautacce yake.
Numfashin ya fesar sannan ya nufi falon bakinsa ɗauke da Sallama Asma'u na biye dashi.
Ahankali idanunsa suka sauƙa akan Ummi dake zaune kan 3sitter ta daura guiwar hannunta duka biyu akan cinyarta tayi tagumi tare ta tsirawa waje ɗaya Ido baki ɗaya ta rame fuskarta yayi fayau.
Cikin sauri Moddibo ya ƙarasa shiga falon tare da zama agefenta kana ya janye tagumin da tayi ya maida hannunta kan gwiwoyinta.
Ummi kuwa cikin sauri ta sunkuyar da kanta nan take hawaye suka fara zuba Shar-shar-shar cikin sanyin murya ya kalleta kana yace.
“Ummi dan Allah kiyafemin. Insha Allahu bazan sake nesa dake ba, kinji Ummina ki daina zubar