Showing 39001 words to 42000 words out of 218703 words
Youssef Muhammad Mouley”.
Cikin tsananin bayyanar mamaki ya zazzaro idanu waje tare da juyowa garesa da kyau cikin alamu rawan jiki ya juya harshe zuwa larabci yace.
“Yah Salam toh kuma yaushe kazo”.
Cikin ɗan sanyi Modibbo shima juya harshe ih zuwa asalin amintaccen larabci yace.
“Nazo kuma? Nida ƙasata, me zanje yi a Marocco dai zaka ce”.
Kai Jabeer bin Jabeer Joɗa ya jujjuya tare da juyawa yayi mishi mgn da hausa yace.
“Kamar yaya ƙasar kuma?”.
Ga mamakin Jabeer sai yaji Moddibon na bashi amsa da harshen hausa.
“Sabida ni ɗan Nigeria ne girman Nigeria”.
Da sauri Jabeer yace.
“A'a wannan ai ko makaho ya shafa yasan kai ba ɗan Nigeria bane kuma ma sunan da ka fadi ai ya isa shaidar inda ka nufa komawa zaka yi ba zuwaba”. Ya ƙare mgnar da iya haƙiƙanin gskyrsa da rawan jiki.
Cikin ɗan ƙosawa da surutun sa Modibbo yace.
“To sabida me?”.
Da sauri Jabeer yace.
“Sabida kafi kama da Larabawa”.
“Toh gashi kuma kaima da larabawan kake kama”.
Gyara zama Jabeer yayi tare da cewa.
“Kuma ni dai ba fullatanine”.
A hankali shima Middibo yace.
“Minfu mi pullo”.
To zuwa yanzu kam mamakin Jabeer ya tsananta.
Ya buɗi baki da niyar zaiyi wata mgnar kenan aka kirashi a baya bisa dukkan alamu Kakanshi ne da sauri ya tashi ya nufi can bayan.
Shi kuwa Modibbo a hankali ya fesar da numfashin gajiya da surutun da Jabeer ya sashin.
Tare da fara karatun Alqur'ani mai girma.
Jim kaɗan da tafiya Jabeer sai gashi ya dawo zama yayi bakinsa cike da tarin mgn to amman samun yana karatun Alqur'ani mai girma yasa dole ya haɗiye dukkan rogowar mgnarsa da tarin tambayoyinsa.
A hankali Moddibon ya ɗago manyan idanunsa tare da kallon taswirar kasar Rarat da suka iso tsakiyarta.
Wanda tuni an sanar musu.
Haka nan yake jin wani irin salama da kwanciyar hankali kana da nutsuwa tunda suka shiga yankin ƙasar Marocco yake jin wani irin sanyi da more happy Wanda har ya iya jure surutun Jabeer.
Numfashin mai sanyi ya fesar tare da ƙara ware manyan idanunsa yana kallon garin ta window'n jirgin.
Haka nan yakeji tamkar yabar damuwarsa baki ɗaya acikin Nigeria ya kuma saki dukkan ƙuncinsa a cikin Taraba.
Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yake bin tsarin dogayen benayen gidajen garin da kallo kana sassayan muryarsa na ratsa kunnuwansa yana jin sautin karatunsa da yakeyi jikin suratul Kahf.
Misalin ƙarfe shida saura minti uku rak.
Jirginsu yayi sauƙar angulu a cikin babban Airport dinsu.
Rabat Sale international airport.
Wanda dai-dai lokacin kuma ya dire ayar ƙarshe ta Suratul Kahf ɗin tuni kuma jirginsu ya dai-dai-ta da'irar tsayuwarsa.
Da sauri Jabeer ya kalleshi sai kuma yayi sauri ya mayar kallonshi gefen damanshi ganin har an buɗe ƙofar jirgin.
Juyowar da zaiyi kuwa sai ganin Middibo yayi a tsaye yana jawo jakarsa daga drower dake samansu.
Da sauri ya miƙe shima, sai kuma yaji ana kiransa a baya, da sauri ya nufi bayan.
Shi kuwa Modibbo agogon dake hannunsa ya kalla, da ɗan hanzarin sa ya nufi wajen sabida ƙaratowar lokacin sallan magrib.
A hankali ya fesar da sassayan numfashi, dai-dai lokacin da ya taka step na forko wanda ya fito da kanshi sararin garin Rarat, duk da dai duk Arfica ne amman ƙasar Marocco sunyi mana rata zarrama mai girma, sunada ci gaba na musamman.
A hankali ya furta.
“Yah Salam”.
Sabida wani irin ni'imtaccen iskane mai cike da salama ke ratsashi yana shiga duk ta inda hudar gashin jikinsa yake.
Wani rin amintaccen numfashin mai cike da yanayin sauƙe ajiyar zuciya ya shaka, like ɗan da ya daɗe baiga mahaifiyarsa ba, kuma yayi kuka.
A hankali yaci gaba da taka steps din yana sauƙo ƙasa.
Wani saurin runtse idanunsa yayi lokacin da ya dire tafin ƙafarsa kan ƙasar Marocco cikin yankin Rarat.
Wani irin tsuma yaji naman jikinsa nayi tun daga can cikin jikinsa da zuciyarsa yakejiyo wani irin tsuma.
Wanda ya ta'allaƙa hakan da tsananin yanayin sanyin garin ne.
“Alhamdulillah!!!”.
Ya furta a saman lips inshi sabida, tunda Allah ya halicce shi bai taɓajiba irin yanayin da yakeji a yanzu, ko Saudia yaje bayajin yanayin nan.
Yana mai shaƙar sassayan iskan garin ya fara bin ayarin sauran matafiya.
Yayinda can gefen kuma manyan motocine na al'farma wanda bisa dukkan alamun wani babba akazo ɗauka.
Su kuwa a cikin yanayin gajiya suka ƙaraso inda masu tarɓarsu suke.
Ɗan dube-dube ya yayi.
Da sauri ya nufi wani Balarabe dake jingina da Taxi yana riƙe da ɗan allon tarba wanda aka rubuta Aliyu Youssef Muhammad Mouley.
Yana isa yayi masa sallama.
Cike da tsananin girmamawa Balaraben yayi saurin buɗe masa marfin motar tare da cewa.
“Marhababuka”.
Kai ya jinjina masa cike da gajiya da ƙosawa.
Yasan Taxi Abba ne ya turosa.
Da sauri shima ya shiga Taxi ɗin kana yaja suka fita daga cikin Airport ɗin.
A hankali yayi miƙa tare da jingina bayansa da seat ɗin dai-dai lokacin da suka ratso ta cikin unguwar Ben slimane.
Anƙuwace ta masu alfarma, haka yasa tsarinta na musamman ne.
haka nan yaji yanayin Weather yayi masa masifar daɗi da kyau.
Gashi yanayin damuna ne Iska mai sanyi da ratsa jiki na kaɗawa gashi duk ta inda ka wulga ido bishi yoyin dabinone masu kyan tsari ke rausayawa sunyi kore shar dasu iska na kaɗawa suna rangaji ga kasar garin ajiƙe yake alamun anyi ruwa.
Ƙarfe shida da minti sha biyar dai-dai mai Taxi ɗin ya juya hancin motarsa kan wani gini mai kyau da ɗaukan indo wanda a samansa aka rubuta.
Belere Hotel Rabat.
Kai da ganin masifar kyau da tsaruwan hotel ɗin kasan zaiyi masifar tsada.
Cikin taushin murya ya kalli Balaraben dake riƙon.
Tare dayin mgn da larabcin.
“Muje wani wanda bai kaishi ba”.
Cikin sanin darajar aiki mai Taxi ɗin ya ɗan kalleshi ta madubi tare da cewa.
“Toh".
Daga nan ya juya akalar motar ya ɗauki hanyar da zata sadashi da unguwar Sidi bettache.
Tafiya kaɗan sukayi suka fito kan babban titinsu.
Da sauri Modibbo yace.
“Masha Allah”.
Dai-dai lokacin da
Idanunsa suka sauƙa akan tamfatsetsen masha'hurin hotel mai masifar kyau da tsari daga can sama tsololuwan ginin an rubuta.
Welcome to Sofitel Youssef Mouley hotel.
Da sauri yace.
“Tsaya mu shiga nan”.
Yayi mgnar still idanunsa na kan sunan hotel ɗin da yayi kama da sunanshi hakan don sunan hotel ɗin yaji yana son sauƙa a nan.
Murmushin mai Taxi ɗin yayi tare da cewa.
“Toh ai wannan yafi wancan tsadama”.
Da sauri ya gyaɗa mishi kai tare da cewa.
“Eh shi yayi”.
Ya ƙare mgnar da lumshe idanunsa jin sautin kiransan salla a masallacin dake cikin hotel ɗin.
Haka yasa shima mai Taxi ɗin saurin shiga.
Numfashi mai sanyi ya fesar tare da buɗe Idanunsa daya lumshe kana ahankali.
Wani irin hotel ne mai masifar kyau da tsari da girma duk da cewa a farfajiyar akwai masallaci sai dai ba wani Babba bane, amma farfajiyar babbe ne me kyau da tsari daga gefen dama wajen Parking din Motoci ne wanda aƙalla zai ɗauki motoci settu zuwa saba'in da biyar kana daga jikin doguwar kantamgar kuwa bishiyoyin kwakwane zagaye da ginin daga can gefe kuma wasu irin flowers ne dake wadace da damshin ruwa haka yasa jikinsu sai sheƙi kayi, tafiya kaɗan zaka samu side ɗin shiga Reception ɗin.
Atsakiya daga gefe da gefe kuma hanya ce kana daga baya wani ƙaton gardin ne wanda yana iya hango bishiyoyin dake ciki kana yana jiyo sautin kukan tsuntsaye kala da ban daban.
Ahankali ɗago daga jingina da seat din da yayi.
Yana Jin zuciyarsa na harbawa kaɗan kaɗan cikin sauri mai taxi ɗin ya rufe marfin gefensa cikin sassarfa ya zagoyo gefen da Modibbo yake tare da buɗe masa murfin motar kana fuskarsa ɗauke da murmushi yace.
“Lalle marhaba fatan an ka isa Marocco lfy”.
Cikin sanyin murya da tarin gajiya yace.
“Yawwa”.
Kana ahankali ya ziro ƙafafunsa waje ya sauke aƙasa.
Da sauri ya rumtse idanunsa tare da kuma buɗesu a lokaci ɗaya yaji wani irin abu mai masifar sanyi ya zira masa tun daga tafin ƙafansa har zuwa ƙwaƙwalwar kansa irin dai abinda yaji daya taka ƙafarsa a Airport. cikin sauri ya kuma lumshe idanunsa tare da furta.
“Yah Salam”.
Kana ya fito dai-dai lokacin da mai kira sallah a masallacin hutel ɗin yazo dai-dai wurin kalmar shahada.
Cikin sanyi ya fara bin kalmar shahadar, wanda hakan ya ankarar da mai taxi dinma ya amsa, tare da bin addu'a'o'in da yaji Moddibon yanayi.
Cikin sanyin murya Mutumin yace.
“Sannu da zuwa”. Lokacin da yaga ya ɗan juyo ya kallesa.
Kai Modibbo ya gyaɗa masa tare da buɗe bayan motar ya ɗauki Breafcase ɗinsa tare da jakarsa, da sauri mai taxi ɗin yasa hannunsa ya amshi jakar kan nasa tare da kuma miƙa masa hannun zai amshi Breafcace ɗinma.
Kai Modibbo ya girgiza tare da faɗin.
“Barshi, zasu yi maka yawa ai”.
Cikin jin daɗi yayi gaba tare da
cewa.
“Bismillah kashiga ciki gashi ma Maghariba ta tayi”.
Cike da salama Moddibo yace.
“Bismillah”.
Yayi mgnar tare da nuna masa gabanshi alamun yayi gaba.
Cikin sauri yashiga gaba kana Moddibo yabi bayansa.
Cikin hanyar da flowers ke ajere gefe da gefe sai ɗan mawadacin hanya dake tsakani sukabi.
Ahankali Moddibo ya taka step ɗaya biyu ana ukun ya hau kan barandar Kofar falon.
Ya sanya ƙafarsa na dama aciki tare da furta.
“Masha Allahu laƙuwwata Illah billahi”.
Sosai komai na hotel ɗin keda tsari na Muslunci da burgewa.
Cikin yanayin gajiya ya ƙarasa gaban ma'aikatan dake binsa da kallon ƙurilla.
Bayan sun gaisane ya kama ɗaki, cike da mutuntaka da martabawa suka gama komai, ɗaya daga cikinsu, ya amshi jakarsa dake hannun mai taxi ɗin.
Kana yayi gaba tare dace masu bismillahi.
Cike da gajiya yabi bayanshi.
Lifter suka shiga cikin minti biyu suka isa hawa na biyu inda na ɗakin daya kaman yake.
Ma'aikacin hotel ɗin ne da kansa ya buɗe ɗakin ya shiga kana ya shimfiɗa beshit tare blanket, kana ya wuce da sauran kayan kamarsu Towel da Bathrobe da makilin da Brush sabulu ya ajiyesu bathroom tare da feffesasa Air freshner kana ya fito tare da cewa mishi.
“Sir akwai abinda kake buƙatane?”.
Kai ya jujjuya mishi alamun a'a.
Ganin haka yasa ya fice.
Shi kuwa Modibbo cike da gajiya ya ajiye woyoyinsa yana mai shaƙar ƙamshin Roomfreshner tare da kallon tsarin komai na ɗakin, komai na cikin falon Ash & maroon colour ne mai masifar kyau kama daga Cottins carpet dama kujerun.
Cike da gajiya a shiga bathroom al'wala yayi tare da fitowa da sassarfa.
Lifter ya shiga ya sauƙa kana kai tsaye masallacin dake cikin hotel ɗin ya shiga da sassarfa jin an tada iƙama.
Ya samu tuni sahu forko da na biyu duk sun cika sai ana uku suka tsaya
Suna shiga suka tada kabbara dai-dai lokacin kuma aka tafi ruku'un Farko.
Bayan anyi Sallah an idar Moddibo.
Yayi Adduo'insa na yau da kullum, ya kara da na neman aminci cikin wakilcin da zaiyiwa Abba tare da samun nasara da roƙon Allah yayi riƙo da hannayensa ya bashi ikon riƙe amana.
Yana so ya jira Isha'i amma saboda yanayin gajiya da yake ji bazai iya jira ba yana so yayi wanka duk da cewa garin akwai sanyi,
Amma yana son yayi wanka dan yaji daɗin jin kinsa da sauƙin gajiyar hanya.
A hankali ya yunƙura da niyyan tashi, cikin sauri ya juya bayansa tare da fito da Idanunsa cike da tsananin son tabbatar da ganinsa ya miƙa da sauri saboda gani fuskar da bashi da hauki ko kokonta a kai cewa fuskar J...!
*Littafin dai na kuɗi 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... page 8*
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
*Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha'awa.* Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni'ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al'ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban lissafa. Sune manyan alamomin infection.
Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.
Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni'ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya Zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.
KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni'imomin ki, da sha'awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA'AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau, duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha'awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor's suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa.
INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi'izinillahi ta'ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma'ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya'ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER'N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA'AURATA.
Da sauri ya juya baki ɗayansa kana ya nufi hanyar ƙofar masallacin ta waje yana ida fita yaga anja motar dake gefe ta wajen masallacin antafi dashi cikin sauri ya sanya hannunsa duka biyu ya dafe kansa yana maimaita duk wata addu'a da tazo bakinsa.
Batare da yace Uffan ba ya juya kansa ya nufi cikin hotel cikin raunin murya yace.
“Meyesa idanuna ke yimin gizo yau kuma J ɗina nake gani”.
Haka yaci gaba da mgnar zuci har ya shiga ɗakinsa.
Baki ɗaya abin ya fara bashi tsoro anya kuwa bai far zaucewa ba. Ya ƙare mgnar zuci tare zamewa ya zauna bakin gadon.
Wayoyinshi guda biyu dake gefen jakarshi ya ɗan juya ya kalla sabida jin ƙaramar tana ruri.
Hannunsa yasa ya zarosu, duk da kiran ya katse. Numfashi mai sanyi ya fesar ganin tarin miss call ɗin Abba, Innayi, Ummi da Malam Arɗo ahankali ya fesar da numfashi tun da yabar masauƙinsa na Abuja gaba ɗaya mancewa yayi da wayoyin suna cikin jaka bai buɗe ba sai yanzu da yaji kiran. Da sauri yayi picking call ɗin Abba da ya sake shigowa.
Cikin sanyin yayi sallama tare da cewa.
“Barka da dare Abba”.
“Barka dai Aliyu ya gajiyar hanya tun ɗazu nake ta kiranka, shiru”.
Cikin lumshe ido yace.
“Alhamdullah Abba phones ɗin ne suna cikin jaka”.
Ajiyar zuciya Abba ya sauke cike da kulawa yace.
“Amma to ya hanya”.
Murmushi Moddibo yayi kana yace.
“Lafiya lau hanya Alhamdulillah Abba gashi har na isa nayi sallar maghariba, yanzu wanka zanyi kafin sallar Isha'i ta gabato”.
Jinjina kai Abba yayi kana yace.
“Alhamdulillah ahuta gajiya amma kafin nan ka kira Innayi da Malam Arɗo da kuma Ummin ka dan hankalinsu ya kwanta”.
Kai ya gyaɗa cikin alamun gajiya yace.
“Toh Abba Insha Allah zan kira”.
“Wanne hotel ka sauƙa”.
Abba ya tambaya.
Ɗan guntun numfashi ya fesar tare da cewa.
Sofitel Mouley Youssef na sauƙa Abba dan naga Hotel yanada Kekkyawan tsari kuma a binciken da nayi naga yafi kusa da Companyn' namu”.
Cikin gamsuwa Abba ce.
“Sosai ma kuwa, anan kusa da shine ma gidana yake inda nake sauƙa in nazo. Kaima dan ba'a gyarashi bane shiyasa”.
Miƙe tsaye yayi da wayar saƙale a kafaɗarsa yace.
“Amman yanada tsada kam”.
Shi kuwa Abba gyara zama yayi tare da cewa.
“Ka zauna anan zuwa lokacin da za'a gyara gidana dake nan bayan hotel ɗin ƙadan, sai ka koma can, zan turo maka mai gadin gidan zai zo ya kawo maka key ɗin motar da zaka rinƙa zirya dashi, zai kuma nunnuma maka duk abubuwan da suka dace”.
cikin gamsuwa yace.
“Toh Abba sai yazo”.
Daga nan sukayi sallama.
Yana katse kiran yayi dearling number Innayi lokacin da kiran ya shiga Innayi na kan Sallaya bayan ta idar da sallan maghariba tana ganin kiran tace Alhamdulillah kana ta ɗaga tare da kaiwa kunnenta tace.
“Moddibo”.
Lumshe Idanunsa yayi tare da komawa yayi bakin gadon ya kishingiɗa kana yace.
“Na'am Innayi”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe cikin sanyin murya tace.
“Fatan ka isa lafiya?".
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Lafiya lau Alhamdulillah”.
Numfashi ta fesar kana tace.
“Masha Allah cikin Rabat kake ko kuma cikin gefenta kake?”.
Cikin alamun gajiya yace.
“A'a cikin Rabat nake a tsakiyar garinma kuwa”.
Kai ta gyaɗa cikin sauke