Showing 48001 words to 51000 words out of 218703 words
da Ido Mommy tayi mata alamar kar tayi magana.
Tsuke bakinta tayi tare da kawar da kanta gefe, jin lokacin sallar La'asar yayi yasa duk mazan suka miƙe suka tafi masallaci.
Bayan sun daeone suna isa afarfajiyar gida suka zauna Anutse Abba ya gyara zamansa tare da fuskantar su da kyau kana yace.
“Toh Alhamdulillah yanzu dai Kamar mun samawa tufkar hanci amma kuma dai Babban abu da yake tafe damu acikin al'amarin”.
Ya sauke ajiyar zuciya kana ya cigaba da cewa.
“Ayi ƙoƙari ayi abin cikin ƙanƙanin lokaci in Allah ya yarda ya lamunce mana komai abune mai sauƙi agaremu inhar kuma kun shirya”.
Jinjina kai Baffa Jimeta yayi kana yace.
“Bakomai in dai wannan ne mu ba matsala awajenmu tunda abin yazo na wasiyya kuma dama a wasiyyar sa ya roƙa ayi cikin gaggawa sannan ya faɗa ya kara cewa yaron nan yana ɓuƙatar aure”.
Jinjina kai Abba da Malam Arɗo sukayi alokaci ɗaya.
Cike da kamala Baffa Jimeta ya cigaba da cewa.
“Tunda har ya fadi haka to yakamata ayi ƙoƙari ayi abinda ya kamata ni awajena Insha Allah ba matsala tunda dama zan kwana biyu saboda zan samu inji da tsohuwar kasan fatanmu da Adduarmu Allah yasa mu rabu dasu lafiya”.
Kai Malam Arɗo ya gyaɗa kana yace.
“Hakane ƙwarai fatanmu da addu'ar mu rabasu da lafiya domin shi yafi al'khairi”.
Murmushi Baffa Jimeta yayi kana yace.
“Toh shine nake so in Zauna da ita Ni nan awajena duk abinda ake buƙata wanda uba zaiyiwa ɗiyarsa Insha Allah bazai gagara ba komai Ashirye muke Insha Allah”.
Cikin sauri Lamiɗo ya Girgiza kai kana yace.
“A'a Alh Muhammadu ai wannan hurumi nane don Allah dan Annabi kada kuyi min haka Khausar ɗiyace awajena tun tana wata uku nake tare da ita bata da bambanci da ɗiyan cikina inaji tamkar Ni na haifeta”.
Kallonsa Baffa Jimeta yayi cike da kamala yace.
“Anya Lamiɗo za ayi haka kuwa abar maka ɗawainiya?”.
Kai Lamiɗo ya Girgiza cike da dattako yace.
“Haba dai wace irin ɗawainiya kuma?,Meye aciki ai babu wani ɗawainiya acikin al'amarin nan”.
Numfashi Abba ya fesar kana ya fuskance su da kyau yace.
“Ni duka wannan aikin ma na ɓangaren Khausar da Moddibo zanso abarmin domin burin Jameeluna ne ni kungama yimin komai da kuka lamince zaku wanzar da wasiyyar sa bayan rayuwarsa”.
Jinjina kai sukayi kana ya cigaba da cewa.
“kungama yimin komai babu abinda zan iya yi muku tukuici dashi sai dai kubarni inyi dukkan abinda ya dace na fannin Auren nan”.
Murmushi Malam Arɗo yayi kana yace.
“Masha Allah wannan Auren yazo da al'barka Ubangiji Allah yasanya al'khairi”.
Zama Malam Liman ya gyara tare da faɗin.
“Muma kanmu duk al'amarin Khausar hakkinmu ne mu sauƙe”.
Cikin sanyin murya Abba ya kallesu kana yace.
“Ni dai dan Allah na nemi alfarma abarmin wannan aikin nayi”.
Ajiyar zuciya Baffa Jimeta ya sauƙe kana yace.
“To ai ba laifi duk zamuyi buƙatun ƴa mace suna da yawa”.
Jinjina kai Lamiɗo yayi kana yace.
“Ni dai nafi so abarmin komai na fannin Khausar”.
Dariya Malam Arɗo yayi idanunsa akan su yace.
“Lallai dai kam wannan ai sai dai ɗakuna uku za aware mata irin wannan lissafin.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Insha Allah wannan duk bazai gagara ba da ɗakuna da kuma duk abinda za'a buƙata zanyi”.
Numfashi Baffa Jimeta ya fesar kana yace.
“Allah ya temaka nima insha Allah nan da mako ɗaya zan koma”.
Jinjina kai Abba yayi kana ya gyara zamansa cike da farin ciki yace.
“Ai shi kansa Aliyu ma yanzu haka yana can ƙasar Marocco yana kulamin da ayyukan Company na to Auren ma bazata muke son yi masa”.
Murmushi sukayi jin sigar da Abba yayi magana Cike da farin ciki Abba ya cigaba da cewa.
“Idan yaso bayan an ɗaura auren da kaina zan Kai masa matarsa da izinin Ubangiji sai dai yaga mata dan yanzu ya tafi yana rayuwa shi kaɗai wasu sabbin damuwa zai sake sawa ranshi”.
Cikin sauƙe numfashi Malam Arɗo yace.
“Toh Alhamdulillah gamu da gishiri da goro na tambayar mu na forko muka zo,".
Sai kuma duk suka juyo suka kalli Malam Liman sayi gyaran murya tare fuskantarsu da kyau cikin kamala da dottaku yace.
“Tunda ga yanayin yadda abin ya kasance, mu shammaci Adda Nana, domin bata da alƙibila yanzu tace ta yarda zuwa anjima zata iya cewa ta fasa, don haka mu ɗaura auren nan yanzu-yanzu ana da goron da kuka kawo in dai akwai sadaki a hannunsu tunda ga waliyan yaro ga kuma nata waliyan”.
Ya ƙare mgnar tare da yin ƙasa da murya gudun kada Hajja Nana taji mgnar.
Cikin tsanananin mamaki da farin ciki mara misaltawa Abba Jameel yasa hannunshi cikin aljihunsa jiki na rawa ya zaro sabbin kuɗin yar dubu dubu wanda ya dauko dan yin hisani. Bandir ɗaya ya ajiye a tsakiyarsu wanda har jikinsa na rawa dan farin ciki yace.
“Gashi ina nemawa Aliyu Youseep Muhammad Mouley auren Khausar bisa sadaki dubu ɗari”.
Da sauri Bappa Jimeta ya gyara zamanshi tare da cewa.
“Na bawa Aliyu Youseep Muhammad Mouley auren ƴata Fatima Usman Abubakar Leewal bisa sadaki dubu ɗari.”
Cikin tsananin jin daɗin wannan al'amari da yazo musu da sauƙin aka ɗauka Auren Khausar da Modibbo a yau Litinin a cikin rugar Jauro yaya bisa shaidu Lamiɗo, Malam Arɗo, Malam Liman, da sauran ƙananan Hajja Nana baki ɗaya.
Bayan sun gama gudanar da ɗaurin auren kamar yadda shari'ar Muslunci ta tsara.
Cike da gamsuwa haɗin da tsananin jin daɗin ɗaurin auren Baffa Jimeta yace.
“Toh ba matsala Insha Allah duk abinda ake ciki zan gayawa Hajja Nana kuma zan taushi zuciyarta”.
Sai kuma duk suka juyo suka kalli Hajja Nana dake fitowa daga cikin rumfarta tana mai cewa.
“Uhmmm ta yara kyau take bata ƙarko, ai duk abinda kuke cewa dayi ina jinku badai kun ɗaya aurenba, toh ai hikenan maji magani”.
Cikin Sauri suka kuma kalli juna, ayi mace kunne kamar na maciji duk ƙantar sauti sai taji.
Sai kuma suka maida kallonsu kam Malam Liman dake cewa.
“Toh kisanya albarka kawai”.
Kai ta gyaɗa cike da takaici tace.
“Hmmm Allah ya sanya al'khairi Allah yasa yadda muka ɗauki mgnar marigayi da mahimmanci shima Modibbo a ɗauki mgnar da gsky”.
Bata jira cewarsu ba kuma ta juya cikin ɗakin,
Ida ta zubawa Khausar da tun lokacin da taji Hajja Nana nacewa badai kun ɗaura aurenba ta daskare a zaune, yayinda Mommy mgnar ta daki zuciyarta, dan batayi zaton abin da gaggawa haka ba. Sai kuma duk suka kalli Hajja Nana dake cewa.
“Wlh kinyi asarar ƙuruciyarki da kyanki ji yadda aka ɗaura aurenki kamar na bazawara mara gata”.
Zuwa yanzu Khausar kam bazata iya fahimtar kalaman Hajja Nana ba bare ta bata amsa. Ita kanta Mommy abin ya sata tafiya dogon nazari.
A can waje kuma
Anutse Lamiɗo ya gyara zama kana yace.
“Toh Alhamdulillah dama kwanan ake batun auren Amina nanda kwana goma, tunda an auren Khausar za'a haɗa bikin ayishi lokaci ɗaya, kana akai ko wacce gidan mijinta”.
Kusan a tare duk sukace.
“Allah ya kaimu lokacin”.
Amin Ya amsa tare daci gaba da cewa.
“Insha Allah zuwa gobe ko jibi Insha Allah zan dawo in muyi magana mahaifiyar yarinya”.
Nan dai suka gaba da tsastsara duk yadda abin zai kasance.
Sai Misalin ƙarfe biyar suka bar Jauro yaya ahanya sukayi sallar maghariba sai gab Isha'i suka isa gida.
Kasancewar ranan girkin Hajiya Bunayya ne yasa kai tsaye Mommy ta wuce Sashen ta tare da Khausar wacce take tafiya tamkar kazar da ƙwai ya fashewa, domin jin kanta take tamkar wacce aka rufe da ɗanyen fatan rago, wasu abubuwa na musamman ne ke yawo a jiki da zuciyarta ita kanta ta rasa yanayin da take ciki, kawai dai ta tsinci kanta da rayuwa da Modibbo a cikin zuciyata tun lokacin da taji wai an ɗaura aurensu.
Suna shiga kai tsaye ɗalibta ta wuce, duk da tsalle da Raudat keyi na ganinta ta gaza yi mata mgn.
Sai Mommy ce data ruggume Raudat ɗin.
Ita kuwa Khausar a hankali ta faɗa bisa gafonta, tare da rumtse idanunta da karfi.
Sai kuma ta buɗesu ganin fuskar Modibbo a ranar da sukayi robuwar ƙarshe jujjuya idonta tayi kamar yadda tayi mishi a lokacin, sai kuma ta lumshesu jin wasu tafasassun hawaye dake kwaranyo mata ba ƙaƙƙautawa.
Kamar a Film haka yanayin da suke rayuwa dashi a makaranta ya fara dawo mata, one by one, har zuwa ranar da suka kasance a mota, haka nan taji wani murmushin da batasan manufarsaba ya kumce mata, wanda kuma ya korowa hawayen da bata san ya kubce mata da kukaba.
Sai kuma ta saki sassayyan kuka jin Mommy ta zauna kusa da ita tana mai cewa.
“Toh kuma kukan me kikeyi Fatima”.
Ta ƙare mgnar da kiran asalin sunanta wanda bata cika kiranta da shiba.
Ita kuwa Khausar cikin ci gaba da sassayan kukan tace.
“Mommy kinaji fa wai sun ɗaura auren”.
Jawota jikinta Mommy da hawaye zubomata tayi tare da ɗaura kanta bisa cinyarta tana mai danne kukanta tace.
“Ba komai Mamana kiyi shiru, ai ba yau za'a tafi da keba ki share hawayenki, addu'arta bazata bari ki muzantaba a gidan aurenki”.
Ta ƙare mgnar tana share mata hawaye, daga nan taci gaba tausarta da kwantar mata da hankali dan ta lura gaba ɗaya ta ɗimauce abin ya daki zuciyarta ya kauda nitsuwarta.
Washegari Da safe Kai tsaye Bedroom din Mommy Lamiɗo ya shiga tare da yi mata bayanin duk yanda sukayi a Jauro yaya bayan sun dawo Sallar La'asar da batun auren da suka dauran.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe cikin sanyi ta ɗago kai tare da kallon Lamiɗo kana tace.
“Toh yanzu har an ɗaura Auren kuma ba jan lokacin asan yaron yana sonta, sannan kuma ace za ayi bikin cikin ƙankanin lokaci haka?”.
Ta ƙare mgnar cije da rauni.
Jinjina kai Abba yayi yana kallon yanayinta yace.
“Toh me za ajira Aysha ai abune na wasiyya kuma akwai damar yi sannan Already Khausar ta gama Secondary kawai tayi Aurenta tunda Alh Bashir yace a Marocco zasu zauna kinga shida kanshi yace zai kaita wurin mijinta”.
Kallonsa kawai Mommy keyi sabida tama rasa abincewa.
Ahankali Abba ya cigaba da cewa.
“Saboda ya lura yaron bayan son zaman nan sannan yana so yabar masa ragamar Company ahannunsa kinga idan sunje can sai ta cigaba da karatunta acan tunda dama yanayin makarantar su akwai cikekkiyar larabci kinga zata iya karatu a can, ta kuma yi zaman aurenta cikin aminci”.
Sunkuyar da kai Mommy tayi tana wasa da yatsun hannunta yayinda tausayin yarta yasa hawaye cika mata idanu A hankali tace.
“Kuma ba wanda ta sani a canfa, ya zatayi”.
Abba ya cigaba da cewa.
“Kada ki damu, ɗan naji Abban Jameel yace in Malam Ahmad ya yarda da rakiyar Ummin Jameel da Asma'u zasuje, ga kuma Hajia Bunayyah itama zan biya mata su kaita tare”.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe kana tace.
“Hmmm abin ne naga kamar anyi sa da gaggawa Khausar fa yarinya ce, wlh tsoron yaronan ne fal zuciyarta jiya kwana tayi batayi bacciba”.
Murmushi Lamiɗo yayi tare da riƙe tafin hannunta acikin nasa yace.
“A ba wani yarinta aciki ai Insha Allah komai zai tafi dai-dai zakiyi alfari da Aurenta da Moddibo ke lokacin da aka aurar dake ai bakima kaita shekaruba, mijinta kuma bar tunanin tana tsoronshi a a bata sonshi ke dai ku zuba ido zakusha mamakin yadda al'amarin zai kance in dai Khausar ta ɗauke ki ai kiyi shiru kawai yaro zayi mubaya'a”.
Ya ƙare mgnar da cikin sigar wasa da son kwantar mata da hankali.
Kai ta gyaɗa kana cikin sanyi tace.
“Allah yasa”.
Amin yace tare da miƙewa ya fita.
Acan ɓangaren Ummi kuwa bayan Sallar Azahar bayan Malam Ahmad ya dawo daga gidan Abba ya zayyanewa Ummi duk yanda Abba ya faɗa masa.
Ajiyar zuciya mai nauyi Ummi ta sauƙe tare da fesar da numfashi cikin tsananin jin daɗin kana tace.
“Alhamdulillah yau dai burin Jameeluna ya cika sannan wasiyyar daya bari ta kasance kai baki daɗin wannan al'amarin”.
Jinjina kai Malam Ahmad yayi cike da farin ciki yace.
“insha Allah”.
Numfashi Ummi ta fesar kana tace.
“Toh Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya kaimu lokacin tafiyar, shiru zanyi bazan gayawa Asma'u ba tukun sai naga yadda Khausar ɗin ta nufeta da mgnar”.
Ameen ya amsa kana ya fice.
Ahankali Asma'u ta fito daga Bedroom tare da kallon Ummi kana tace.
“Ummi wai maganar me naji kuna yi kamar batun Aure?”.
Kai Ummi ta jinjina da alamun farin ciki afuskarta tace.
“Hmmm”. Sai kuma tayi shiru, ita kuwa Asma'u cikin son tabbatar da abinda kunnuwanta suka jiyemata cike da kaɗuwa tace.
“Dan Allah Ummi ki gaya min na tuba”.
Cikin tsanananin jin dadin ɗaya kasa biya a saman fuskarta tace.
“Eh maganar Auren Moddibo mukeyi”.
Zare ido Asma'u tayi kana tace.
“Ummi Yaya Moddibo zaiyi Aurene?”.
Jinjina kai Ummi tayi tana kallonta tace.
“Eh yanayi Aure dai”.
Murmushi Asma'u tayi cike da farin ciki tace.
“Ummi Wacece matar?”.
Ummi na murmushi tace.
“Aminiyar kice matar”.
Asma'u kuwa cike da matsanancin mamaki da al'ajabi ta zare Idanunta waje kana tace.
“Khausar!?”.
Kai Ummi ta jinjina tare da faɗin.
“Tabbas kuwa da izinin Ubangiji Itace”.
Tafa hannu tayi tare da buga still da Mamaki da kuma al'ajabi tace.
_“Lahailah ha Illallahu Muhammad Rasulullahi (S.A.W)”_ Yah Moddibo da Khausar.
Kallon yanda ta zare ido da sallami Ummi tayi kana tace.
“Haƙƙun kuwa dan tuni an ɗaurama”.
Dafe kunci Asma'u tayi da matsanancin mamaki gani da kaɗuwa ɗoki da bai sake taba tace.
“Dan Allah Ummi yaushe aka fara wannan maganar?”.
Hannunta Ummi ta riƙe tare da zaunar da ita agefenta yace.
“Ki nutsu mana Asma'u me wannan kamar wanda akace an haɗa Auren mutum da Dodo!?”.
Sake baki Asma'u tayi cikin Mamaki tace.
“Tabb Ummi ai kusan Auren Dodo da mutum za ayi dan wallahi Khausar matsayin Dodo take kallon Yah Moddibo”.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauke kana tace.
“Aikuwa da saninta”.
Zare ido Asma'u tayi tamkar zasu zubo tace.
“Ummi Khausar ɗin ta sani?”.
Kai Ummi ta gyaɗa kana tace.
“Eh”.
Dafe ƙirji Asma'u tayi Idanunta akan Ummi tace.
“Shine kuma bata faɗa min ba iyeee Kam bala'i bari Inje in sameta”.
Ta Ida maganar tare da miƙewa.
Cikin sauri Ummi ta riko tsintsiyar hannunta tace.
“Zauna ai zuwa ta ƙarshe naji tana cewa tazo kuyi wata magana kuma ta samu kuna aiki sannan fitowar ku kenan taga Moddibo yazo kinga ai jikinta na rawa ta fita”.
Jinjina kai Asma'u tayi still Hannunta na cikin na Ummi tace.
“Eh dan na kirata awaya ma nace ta faɗa min shine tace idan inaso Inje gidansu inji labari ashe dama wannan ne maganar amma Ummi tasan maganar kuma ta yarda?”.
Cikin sanyi Ummi tace.
“Eh ta sani ta yarda kuma ta amince”.
Dafe kunci Asma'u tayi kana tace.
“To amma Ummi garin ya akayi haka?”.
Kallonta Ummi tayi tare da gyara zamanta kana ta sauƙe numfashi cikin sanyi tace.
“Wasiyyar Yayanki zata cika?”.
Cikin sauri Asma'u ta kalleta fuskarta ɗauke da mamaki tace.
“Wasiyya kuma Ummi ya bar mata?”.
Jinjina kai Ummi tayi tare da fesar da numfashi kana ta jingina bayanta da jikin kushin ɗin tace.
“Idan baki manta ba Ranan da yazo gidan nan na ƙarshe itama Khausar tazo sannan tare suka tafi”.
Cikin sauri Asma'u ta jinjina kanta kana tace.
“Ƙwarai kuwa Mommy na tuna aishine tace suna tafiya taga wata mota na binsu”.
Kai Mommy ta Jinjina kana tace.
“To awannan ranan ne ya bar mata wasiyar. Mommy ta ke sanar min yanda suka yi”.
Jinjina kai Asma'u tayi cike da tausayawa Aminiyar tasan yanda Khausar ke masifar tsoron Moddibo tabbas ta ɗauki al'ƙawari mai girma cikin sanyin murya tace.
“Allah sarki Khausar!, Allah sarki Aminiya!!, Ubangiji Allah yabar ƙauna Allah yabar ƙauna tsakaninta da Yah Moddibo”.
Sai kuma ta kalli Ummi da fuskarta ke ɗauke da murmushi tace.
“Ummi inshirya inje”.
Kai Ummi ta gyaɗa kana tace.
“Kije mana Asma'u wa zai hana ki zuwa wajen Aminiyarki”.
Cikin sauri Asma'u ta miƙe tashiga Bedroom ta sanya hijabinta kana ta fito tayiwa Ummi Sallama.
Aɓangaren Hajiya Lami kuwa miƙewa tayi daga Bedroom ɗinta ta nufi ɗakin Samira zaune ta sameta Idanunta sun kaɗa sunyi jawur tamkar garwashi alamar tasha kuka sosai cikin sauri ta ƙarasa kana ta zauna gefenta cike da kulawa tace.
“Samira wai lafiya yau baki fito ba meya faru?”.
Ahankali ta ɗago kanta Idanunta da suka sauya launi ta kalleta Muryanta na rawa tace.
“Mommy ni baƙi ɗaya wari nake ji idan na tambaye ki kinajin wani sai kice min bakya ji Mommy kullum warin nan ƙaruwa yake ya zanyi da raina”.
Cike da tausayawa Hajiya Lami ta janyota jikinta cikin sanyin murya tace.
“Haba Samira ki kwantar da hankalin ki mana idan ya dawo sai mu sake komawa wajensa”.
Cikin raunin murya tace.
“Mommy wani irin in ya dawo zaku koma wajensa ni dai ina ganin mutumin nan ya lalata min rayuwa ne yanzu ayanda nake warin nan ko maigadin gidansu Modibbo ma zai yarda ya aurenki ne bare Modibbo da ɗan karen tsabta”.
Sai kuma sharce hawaye masu masifar zafi kana tace.
“Yanzu Mommy wani namiji ne zai kalleni bare yace yana sona! ga ruwa mai wari da ƙarni yana ta bina ko yaushe ina tare da ƙunzugu kamar mai jego”
Cikin sanyi Hajiya Lami tace.
“Bakomai Samira kasa ki damu Insha Allah yana dawowa zamu koma wajensa”.
Cikin muryan kuka da tashin hankali tace.
“Mommy Ni dai ina ji ajikina wannan al'amari ya zama min bala'i arayuwata na saɓi Ubangiji gashi ya kamani tun ba aje ko ina ba Wayyo Allah! Kaico na! Ni Samira”.
Asanyaye Hajiya Lami tace.
“Haba Samira kar ki karyar min da zuciyata mana Insha Allah burinki zai ciki”.
Kai ta girgiza kana tace.
“Mommy ni kam hankalina bai kwanta ba burina inga na samu lafiya wannan ruwan ya daina zuba shine kwanciyar hankalina”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da dafa shoulder ta tace.
“Kada ki damu Insha Allah Samira Zaki samu sauƙi”.
Jinjina kai tayi kana tace.
“Allah yasa Mommy Ina fatan hakan Allah na tuba Allah kayafemin Allah kaji ƙaina ka gafarta min”.
Acan ɓangaren Lamiɗo kuwa bayan ya fita ɗakin Mommy Kai tsaye sashen Gimbiya Dadu yashiga bakinsa ɗauke da sallama zaune ya ganta da ƙanwarta Hajiya Kubra.
Anutse ya ƙarasa tare da zama kana da murmushi afuskarsa yace.
“A Yafendo Kubra kin zo ne?”.
Kai ta gyaɗa tace.
“Eh Lamiɗo kana gida kenan?”.
Kai jinjina kana suka gaisa bayan sun gaisa Hajiya Kubra ta gyara zamanta tare da kallon sa tace.
“Toh yau dai kam nazo da aiken Ƙaninka duk da yace min iyayenshi maza sunzo”.
“Wanne ƙarin nawa”. Yayi tambayar a bauɗo domin babu wanda ya taɓa mishi mgnar.
Shi kanshi mahaifin Naseru cewa yayi yaji suna mgnar ne bakwai sun gaya mishi bane, to kuma shima sai abin ya kwanta mishi musamman da yasan Nasiru na biye-biyen mata shiyasa ya nemi alfarma a bashi Amina kuma ayi auren cikin gaggawa.
Murmushi tayi tare da Kallonsa tace.
“Naseeru mana”.
Kai ya jinjina kana yace.
“Ikon Allah Naseeru kuma ko ɗazun ma muna tare kuma bai faɗa min ba shine sai ya aiko ki? ai da kin kirani ma zanzo har gida in sameki”.
Kai ta girgiza kana ta kalli Gimbiya Dadu sai kuma ta kalli Lamiɗo