Showing 30001 words to 33000 words out of 218703 words
kanki hukunci sannan ke zaki zaɓawa kanki miji wai ki kalli tsabar Idanunmu saboda tsaurin Ido kice Modibbo kike so to yaushe yace yana sonki?”.
Girgiza kai kawai tayi cikin matsanancin kuka da tashin hankali tace.
“Dan Allah Mommy kiyi haƙuri wallahi ba rashin kunya bane dolene yasa haka Mommy ki sanya mana al'barka acikin rayuwar auren da zamu yi”.
Cike da takaici Mommy ta kalleta kana tace.
“Toh Khausar tambayar da zan miki Moddibo yace yana sonki ko kuma ke kike haukanki?”.
Girgiza kai Khausar tayi cikin rawan murya tace.
“Mommy I don't know either he love me or not”.
Miƙewa Mommy tayi tare da jan dogon tsaki ta fice daga ɗakin ta nufi Falon Lamiɗo.
Khausar kuwa kanta ta kife ajikin katifa ta fashe da sassayan kuka tana sheshsheƙa Ajiyar zuciya Haiydar ya sauƙe tare da kallon Khausar cikin sanyin murya da rashin fahimta yace.
“Addah Khausi ban fahimci abinda Mommy take faɗa ba wai Malam Moddibo kike so ko kuma wa?”.
Kai ta gyaɗa masa Muryanta na rawa tace.
“Eh shi nake so”.
Zare ido Haiydar yayi tare da sanya salati kana yace.
“Toh shi Malam Moddibo yana sonki ne?,”.
Kai Khausar ta girgiza tare da ɗago Idanunta dake jiƙe da hawaye cikin raunin murya tace.
“Ban saniba Haiydar I really don't know”.
Cike da matsanancin mamaki da damuwa Haiydar yace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Khausar baki sani ba kuma?”.
Jinjina kai Khausar tayi cikin raunin murya tace.
“Bansani ba Haiydar Bansani ba Haiydar”.
Miƙewa Haiydar yayi cike da takaici yaja dogon tsaki tare da faɗin.
“Wallahi dama nasan hakane babu abinda zaisa in rakoki wajen Mommy”.
Ya ida maganar tare da ficewa cike da takaici da ban haushi.
Cikin rauni Khausar ta miƙe tare da nufar Bedroom ɗinta tana shiga ta faɗa bisa gado tare da sakin kuka mai masifar ɗaci da ƙuna.
Mommy kuwa kai tsaye falon Lamiɗo ta nufa bakinta ɗauke da Sallama tashiga falon zaune ta samu Abba akan 2sitter.
Anutse Lamiɗo ya ɗago kansa tare da sakar mata da lallausan murmushi kana yace.
“Shatu Ikon Allah mai kuma ya ɓatawa Gimbiya Aysha rai”.
Fuska Mommy ta ɓata tare da narkar da murya kana tace.
“Na lura ma al'amarin Khausar dariya yake baka, baki ɗaya tun jiya Yarinyar nan ta ɓata min rai ta hargitsa min lissafi, sam kakarta bata da kirki tsohuwa ce mai zafi ta saba da iko da gadara akan ƙannenta ta saba da maganar ta kamar yankan wuƙace”.
Kallonta kawai Lamiɗo yake yana murmushi.
Cikin yanayin damuwa ta cigaba da cewa.
“Duk abinda ta faɗa haka ne babu wanda ya isa ya musan ta mata gashi Khausar tazo tayi mata abinda bashi neba ta tafi tana zagina yanzu tana zuwa Rugar nan zata baza sunan Khausar hakan zanji daɗi ne?”.
Murmushi Lamiɗo yayi tare da gyara zaman sa kana ya miƙa mata hannunsa tare da cewa taho nan zo nan Shatuna”.
Maƙe kafaɗa tayi tare da tura baki kana ta narkar da fuska.
Murmushi Lamiɗo yayi tare da cewa.
“Ki zauna mana”.
Kallonsa kawai take amma ba tace Uffan ba.
Ahankali ya sanya hannunsa ya janyo tsintsiyar hannunta tare da zaunar da ita agefen sa cikin sanyin murya yace.
“To amma ai akwai abinda baki sani ba”.
Asanyaye ta kallesa tare da cewa.
“Toh menene ban sani ba?”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da tsira mata ido kana yace.
“Jiya Hajja Nana bata bani dama inyi mata Magana ba saboda yanda ta ɗauki abin da zafi take ta ihu da kururuwa da Masifa sannan dole mu bita ayanda taso”.
Jinjina Kai Mommy tayi tare da sauƙe numfashi.
Cikin sanyin Murya ya cigaba da cewa.
“Tun da kinga tsohuwa ce sannan tana da ƙarfin iko akan Khausar babu yanda muka iya, amma Baffanta ya fahimta domin yau kafin ya koma Ɓadamaya yabiyo nan munyi magana dashi”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana ya kalli Mommy da itama shi take kallo yace.
“Sannan yace ba zai mata dole ba kamar yanda idan Mahaifinta yana raye ba zai mata dole ba kamar yanda zai yiwa ƴaƴan sa haka zai mata saboda yana da ƴaƴa mata da yawa kamar yanda bai musu dole ba haka itama ba zai mata dole ba dan mahaifinta baya raye”.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da fesar da numfashi kana tace.
“Na sani shi yana da fahimta, amma ita tsohuwar ce gaba ɗaya ba zata fahimta ba”.
Lakace mata hanci Lamiɗo yayi kana da murmushi afuskarsa yace.
“Kada ki damu ɗan zai fahimtar da ita, dan yace ya bata haƙuri sannan idan ta huce zai sake dawowa ya bata haƙuri kuma Insha Allah zata fahimta”.
Jinjina kai Mommy tayi tare da gyara zamanta kana tace.
“Toh naji ta wannan gefen an samu fahimta amma fa Moddibo baya Son Khausar din ita da bakinta fa tace min bata san yana sonta ko baya sonta ba, ka taɓa ganin Moddibo yazo wajen Khausar ne?”.
Kai Abba ya gyaɗa tare da cewa.
“Eh na taɓa gani mana kwanaki sunzo da Asma'u”.
Girgiza kai Mommy tayi tare da fesar da numfashi kana tace.
“Zuwan da kaga yayi ta'aziyyan Ramadan yazo min domin yace alokacin da suka zo yimin ta'aziyya sun haɗu da Ori da ya muku bayani gawar Jameel toh sun fita bai shigo ya min ta'aziyya ba, shine suka zo da Asma'u yamin amma fa baice yana son Khausar ba hasalima Khausar da Moddibo basa zama inuwa ɗaya”.
Ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauƙe tare da gyara zamansa ya fuskanceta tare da cewa.
“Ki nutsu mana Ni nafi so ki nutsu Ayshatu idan kin nutsu sai in miki bayani”.
Marairaice fuska tayi tare da langwaɓar da kai kana tace.
“Toh ai yanzu ma Anutse nake ranka shi daɗe kai nake sauraro”.
Murmushi yayi tare da riƙe tafin hannunta acikin nasa kana ya lumshe idanunsa tare da cewa.
“Jiya ma hargowar Hajja Nana ce ya hana in miki bayani shekaran jiya baki ji cewa nayi baƙi ba?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh naji”.
Ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauke kana ahankali yace.
“Toh Malam, Arɗo ne da Alh Bashir mai Dala Mahaifin marigayi Malam Jameel da kuma Malam Ahmad Baban Asma'u suka zo”.
Jinjina kai Mommy tayi kana cikin sanyin murya tace.
“Ooh sune suka zo!?”..
Kai ya gyaɗa mata still hannunsa na cikin nata yace.
“Eh”.
fesar da numfashi yayi kama yace.
“Toh kinsan me yaka wo su?”.
Kai ta Girgiza kana tace.
“A'a sai ka faɗa”.
Atake yanayin fuskarsa ya sauya daga murmushi zuwa rauni cikin sanyin murya da rauni yace.
“Magana suka zo akan wasiyyar da Marigayi Jameelu ya bari”.
Saurin Kallonsa Mommy tayi cikin sanyin murya da damuwa tace.
“Wasiyya kuma!?”.
Jinjina mata kai Lamiɗo yayi tare da fesar da numfashi kana yace.
“Eh”.
Ahankali tace.
“Wasiyya kuma Jameel ya bari akan me!?”.
Zamansa ya gyara tare da janye hannunsa ɗaya daga cikin na Mommy ya dafe goshinsa cikin raunin murya yace.
“Jameel yabar wasiyya ne akan Moddibo da Khausar”.
Lokaci ɗaya idanun Mommy suka ciko da Hawaye cikin raunin murya tace.
“Wasiyya akan Moddibo da Khausar kuma to akan me?”.
Jinjina mata kai yayi still muryarsa Araunane yace.
“Tabbas Mahaifinsa ya faɗa min cewa akwai ranan da suka je shi da Moddibo gidansa alokacin saura kwana uku asace sa har yake faɗa masa yafa zaɓawa Moddibo matar da zai Aura Amma shi kansa Moddibo bai sani ba domin koda Jameel ya faɗa murmushi Moddibo yayi alokacin har yake cewa Alhaji Bashiru. Abba kaji fa wai ni J zai za ɓawa mata kamar wani yaro ko makaho”.
Lumshe ido Lamiɗo yayi cikin rauni ya cigaba da cewa.
“Alokacin Abban sa yace ya faɗa masa wace mata ce sai Jameelu yayi dariya yace sai ya dawo asirri zai faɗa masa to bayan da ya dawo sai yace wa mahaifinsa dan Allah Abba ina neman alfarma acikin kwanakin nan domin wata ƙila akwai abinda zai iya faruwa acikin kwanakin nan wataƙil agaban ido na wataƙil kuma abayan Idona”.
Cikin sauri Mommy ta rintse Idanunta Hawaye masu zafi suka zubo mata ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauƙe kana yace.
“A lokacin sai mahaifinsa yace.
“In sha Allah a gaban idon ka nema Jameeluna ina zakaje”.
Sai yayi murumshi tare da sunkuyar da kansa murya a sanyaye yace.
“Wata ƙil kafin nan na tafi Marocco ko wata duniyar. Dan haka ga mata na zaɓawa Moddibo koda bayan bana nan Abba ayi ƙoƙari ahaɗa auren Moddibo da Khausar sai Abban sa yace to Meyesa kace haka sai yace wa Mahaifinsa shi dai yana fata kuma yana buri ahaɗa auren Moddibo da Khausar domin Moddibo yana ɓuƙatar Aure fiye dashi shiyasa ya fara yi masa zaɓin mata”.
A hankali Lamiɗo ya fesar da numfashi mai zafi kana ya cigaba da cewa.
“Sannan Marigayi Jameelu ya sanar da mahaifiyarsa maganar kana ya sanar da Kakar Moddibo maganar har ta kira Malam Arɗo ta sanar dashi maganar domin wasiyya ce alokacin yake cewa ayi ƙoƙari ayi auren cikin gaggawa domin Moddibo yana bukatar aure shiyasa yake so ayi kokari ayi auren cikin gaggawa koda baya nan babu wanda baisan da maganar ba sai Moddibo shiyasa shekaran jiya suka zo akan neman alfarma ga Uzurin da suka zo dashi”.
Sai kuma ya numfasa kana yaci gaba da cewa.
“Akan wasiyyar da yabari toh na faɗa musu lallai Nine mariƙin Khausar Kuma Khausar tamkar ƴa take awajena, saidai bani da iko da kuma ƴan cin da zan bada Auren Khausar garesu batare da izinin Yayan mahaifinta ba da kuma sahalewar kakarta”.
Gyara zama tayi tare da kallon Mommy da tayi sanyi hawaye na zuba daga idanunta numfashi ya fesar kana yace.
“Toh nace suje bayan kwanaki zasu jini, toh dana niyyata zamu je Jauro yaya muyi wa Hajja Nana bayani sannan mu faɗa mata wasiyya ne duk abinda ake ciki dama nace idan muka dawo zan faɗa musu”.
Kallonsa kawai Mommy take bako kyaftawa tana sake jin tsoron Allah Mabuwayi gagara Misali aranta cikin sanyin murya Abba ya cigaba da cewa.
“Kuma tunda kika ji Khausar ta furta haka wataƙil itama akwai abinda ta sani acikin wannan al'amarin”.
Dogon numfashi Mommy taja tare da fesarwa kana ta lumshe Idanunta hawaye masu zafi suka zubo ahankali ta sunkuyar da kanta cikin raunin murya tace.
“Allah sarki toh Ubangiji Allah ya jikansa da rahma idan al'khairi ne Allah ya tabbatar idan kuma ba al'khairi bane Allah ya sauya musu da mafi al'khairi”.
Jinjina kai Lamiɗo yayi tare da sauƙe numfashi kana yace.
“Yawwa Aysha yanzu kika gane addu'ar da zaki yi kenan, sannan kada kiyi fushi da Khausar fadan nan dakike yi bashi da amfani zama zakiyi da ita ki fahimci Meye dalilinta na fadar haka”.
Kai ta gyaɗa kana cikin sanyin murya tace.
“Toh shikenan Insha Allah zan kiyaye”.
Sai da aka kira sallar azahar Lamiɗo ya fita ya tafi masallaci kana Mommy ta miƙe ta nufi sashenta tana shiga falon ta fara jiyo sheshsheƙan Kukan Khausar abakin ƙofar Bedroom ɗinta ta tsaya tare da ɗaga labulen ta kalli Khausar ba yabo ba fallasa tace.
“Idan kin gama kukan ki tashi kije kiyi al'wala kiyi sallah”.
Cikin sanyi ta gyaɗa mata kai kana ta miƙe tashiga toilet ta ɗaura al'wala ta fito Anutse ta gabatar da sallah.
Mommy ma na shiga Bedroom ɗinta ta ɗaura al'wala sannan ta gabatar da sallah.
Bayan Khausar ta idar da Sallah kai tsaye ɗakin Mommy ta nufa.
Acan ɓangaren Hajiya Lami kuwa zaune take akan kujera taji ƙa garin magani da tsamiya da kuma ruwan zafi ta kalli Samira dake zaune gefenta ta zabga ta gumi cikin sanyi tace.
“Gashi ki karɓi maganin kisha dama wannan yace sai da rana-rana zaki riƙa sha wanda kika sha jiya da daddare kuma dare-dare zaki sha”.
Karɓan kofin Samira tayi tare da tsira masa Ido ganin yanda ta tsirawa kofin Ido yasa Hajiya Lami cewa.
“Kisha mana”.
Cikin raunin murya Samira tace.
“Mommy nifa na jiya da daddare nan ma dana sha babu abinda ya ragu saima zubar ruwan daya ƙaru”.
Ahankali Hajiya Lami tace.
“Toh Sokuwa wataƙil ruwan ai zai zube ne ya gama ƙarewa idan ya gama zuba shikenan magana ya ƙare”.
Cikin raunin da tashin hankali Samira ta kalli mahaifiyar ta da Idanunta dake cike da ruwan hawaye kana tace.
“Toh Mommy ruwan fa da ƙarni da wari yake zuba yanzu ma bakiji yanda nake ƙarni ba?”.
Cikin tsinkewar zuciya ta kalli Samira sai kuma ta basar domin bata son bawa ƴartata tsoro amma baki ɗaya hankalinta ya tashi kar dai ƴarta ta samu wata matsala numfashi ta fesar tare da kallonta kana tace.
“Ni dai banji wani wari ba hancin kine dai da shegen jiye-jiye kina nan da hanci kamar na kule ke dai kisha magani tunda yace kisha na tsawon sati biyu kafin mu koma”.
Zare ido tayi cike da tashin hankali tace.
“Mommy har sati biyu kuma?”.
Kai Hajiya Lami ta gyaɗa kana tace.
“Eh saboda zaiyi tafiya so koda munje baza mu same shiba”.
Ajiyar zuciya Samira ta sauƙe tare da cewa.
“Toh bari in sha”.
Aɓangaren Naseer kuwa zaune suke afalon Mahaifiyar sa da Addarsa Hindu da kuma Mahaifiyar su Hajiya Kubra yayin da akwatuna ke jere agabansu cikin su sanye da Atamfofi, Leshuna, Shadda, English wear, Turaruka, Mayuka,Takalma.
Gyara zama Naseer yayi tare da kallon Addah Hindu murmushi ya sakar mata tare da ɗage mata gira ɗaya kana yace.
“Insha Allah Addah Hindu burina ya kusa cika”.
Murmushi tayi tare da jinjina masa hannu kana tace.
“Ƙwarai kuwa nan da ƙanƙanin lokaci ma kuwa”.
Gyara zama Hajiya Kubra tayi tare da kallon Naseer tace.
“Toh yanzu me yarage acikin kayan Auren nan ba asaba!?”.
Ajiyar zuciya Naseer ya sauƙe tare da cewa.
“Kayan Aure kam yanzu ai kusan an gama komai kawai yanzu gishiri da goro za asiya sai kuma sadaki i think suka ɗaine suka rage”.
Kai Addah Hindu ta gyaɗa tare da faɗin.
“Eh saura kayan rufi ba ahaɗa ba”.
Kai ya jinjina kana yace.
“Toh badamuwa yaushe za akai?”.
Kallon akwatunan tayi kana ta kallesa numfashi ta fesar ta da sakin murmushi tace.
“Idan Allah ya yarda nan da sati za akai saura gyalullulka dana aika akawo min daga Kano basu iso ba tukunna”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Toh ba matsala sai sun iso”.
Bayan Moddibo da Abba sun idar da sallar Azahar Amasallacin Kofar gidan Abba kai tsaye gidan Ummi suka nufa bayan sun isa Moddibo yayi Parking suka fito daga motar kana suka tsaya daga coumpund ɗin Moddibo yayi sallama daga ciki Malam Ahmad ya amsa kana ya fito ganin Abba yasa ya faɗaɗa Murmushin fuskarsa tare da cewa.
“A'a Alh Bashir yau har da kaine agidanmu sannu da zuwa sannu da zuwa maraba lale ku iso mana”.
Kai Abba ya girgiza kana yace.
“A'a nan ma yayi”.
Ahankali malam Ahmad yace.
“A'a bakomai Abban Jameel mu shiga mana ai an zama ɗaya haba dai mushiga dan Allah”.
Murmushi Abba yayi cikin sanyin murya yace.
“Toh shikenan Nagode”.
Sannan suka nufi falon Ummi Asma'u dake zaune ta miƙe tare da yi musu Barka da zuwa kana ta koma kichen ta dauki Plate ta kawo musu ruwa da drinks da kuma Fruit ta ajiye masu kana ta Gaishe su cike da ladabi.
Ahankali Moddibo ya jingina bayansa da jikin kujera ya lumshe idanunsa baki ɗaya ya tsani garin Gembulan da jahar Taraba ji yake tamkar ana yayyafa nasa garwashin wuta ajiki baiƙi ace ko yaushe yana ɗaki baya fita ko ƙofar takashi ba.
Ummi dake Bedroom zaune kan Sallaya ta miƙe ta fito jin muryan Asma'u na gaishe da Moddibo kana tace.
“A'a Moddibo ne”.
Ganin Abba zaune yasa ta tsaya cike da Mamaki tace.
“A'a Alhaji Bashir”.
Cikin sanyin murya Abba yace.
“Na'am Fatima”.
Kallonta Malam Ahmad yayi sanye take da hijabi har ƙasa hannunta riƙe da Carbi cike da kulawa yace.
“Ki ƙara so mana ku gaisa”.
Kai ta gyaɗa tare da ƙarasawa ta zauna daga gefe.
Anutse Moddibo ya daga kai ya kalleta kana yace.
“Ummi ina yini”.
Kallonsa Ummi tayi ba tare data amsa gaisuwar ba tace.
“Babana jiya duk baka leƙoni ba”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Eh Ummi”.
Cikin sanyin murya tace.
“Kuma na kira wayarka baka ɗaga ba sai nayi tunanin ko kana bacci ne?”.
Kai ya girgiza tare da sunkuyar da kansa ƙasa yace.
“Kuma Ummi ban kulaba ban miss call ɗin ba”.
Jinjina kai tayi tare da fadin.
“Ayyah”, Kana suka gaisa.
Anutse Abba ya kalleta tare da cewa.
“Fatima ina yini”.
Ahankali ta gyara zamanta tare da faɗin.
“Lafiya”.
Cikin sanyin murya yace.
“Ya muka ƙara ji da haƙuri”.
Lumshe Idanunta tayi kana tace.
“Haƙuri ya zama dole”.
Jinjina kai yayi tare da cewa.
“Toh Allah yajiƙan Jameelu Ubangiji ya masa rahama”.
Baki ɗayan su suka amsa da Ameen ya Allah.
Gyara zamansa yayi kana yace.
“Fatima kada ki yiwa Jameelu kuka ki tayi masa addu'a shine abinda ya dace kinji ko?”.
Kai ta gyaɗa tare da sunkuyar da kanta ƙasa tace.
“Insha Allahu bazan yiwa Jameelu na kuka bai Insha Allah zan ta binsa da addu'a”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Hakan yafi”.
Anutse ya gyara zamansa tare da kallon Moddibo da kansa ke ƙasa kana ya kalli Ummi da itama still Kanta ke ƙasa ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Dama nazo da Moddibo ne inne ma masa uzini awajenki”.
Cikin sauri ta ɗago kanta tare da Kallonsa tace.
“Izinin me kuma?”.
Numfashi ya fesar tare da cewa.
“Dama Abune da yashafi kasuwanci na acan Company mu na Marocco wanda Jameelu ne yake komai na Company nin toh kuma yanzu kin gani Allah ya dauke mana Jameelu”.
Cikin sauri Ummi ta lumshe Idanunta tare da gyara wuyan hijabinta.
Abba ya cigaba da cewa.
“To Kuma Manager company shima ba shida lafiya toh sun nemi da Inje kuma nima bana jin daɗin jikina bazan iya zuwa ba”.
Ahankali Ummi ta ɗago kanta tare da kallon sa gani tayi baki ɗaya ya rame ya zama wani so silent dashi.
Cikin sanyin murya da tausayawa tace.
“Toh Abban Jameel Idan bamu sa haƙuri aranmu ba ya zamuyi ka kwantar da hankalin ka Ubangiji Allah yajiƙan Jameelu shine kawai fatan mu da addu'ar mu”.
Kai ya gyara tare da sauƙe numfashi yace.
“Insha Allah zan kiyaye.
Yanzu mshawan jinin ne baki ɗaya yasani agaba duk kan magungunan da nake sha sai yazama kamar basa min aiki”.
Jinjina kai tayi cikin sanyin murya tace.
“Allah ya sawwaƙa amma ka rage tunani koda kana shan magani idan baka rage tunani ba ba zaiyi aiki ba”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana yace.
“Toh Fatima ya zanyi idan banyi tunani ba!?”.
Ahankali ta sunkuyar da kanta hawaye na zuba daga idanunta.
Gyara zama Abba yayi cikin sanyin murya yace.
“Toh dama shine nake so Moddibo ya wakilceni yaje shine yake cemin bawai zuwan bane baya so amma baya so yayi nesa da Umminsa”.
Ahankali ta ɗago Idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye ta kalli Moddibo murmushi tayi kana tace.
“Ba komai Babana kaje wannan ma ai abin farin ciki da al'fahari ne zaka cika burin da Jameeluna yake son cikawa. Ubangiji Allah yakai ka lafiya ya dawo da kai lafiya Allah ya maka albarka”.
Cikin sanyin murya da tausayawa Moddibo ya amsa da Ameen asaman laɓɓansa.
Ahankali Ummi ta cigaba da cewa.
“Insha Allah zanyi ta binka da addu'a ba komai Babana