Showing 165001 words to 168000 words out of 218703 words
ɗiba, duk inda take a duniyar nan sihiri zaije ya sameta kuma ya kamata. yanda kika san kashi nada baƙin jini awajen ko wani ɗan Adam toh haka za tayi baƙin jini a idon mijinta da dangin mijinta ke dama duk wani makusancinta aduniya hatta uwar data haifeta sai tayi baƙin jini a idanunta yanzu ke kanki idan ki kaga kashin ki kina sha'awar ki sake kallonsa?”.
Cikin matsanancin farin ciki da jin daɗi ta girgiza masa kai kai ya gyaɗa ya cigaba da faɗin.
“Toh yanda kashi keda baƙin jini kowa ke ƙyamansa ba wanda ke son ganinsa atsakiyar mutane haka zata kasance tamkar mujiya, babu wanda zaiso kasancewa da ita har yawu sai an fara zubarwa akanta yanda kika san duk wani baƙin jini na kashi to haka zata kasance.
Sai tafi mujiya bakin jini ai mujiya ana zama da ita kashi fa ana iya zama dashi?”?
Dariya ta ƙyalƙyale dashi har wani irin tsuma jikinta keyi na farin ciki kallonsa tayi tace.
“Boka an gama kuma in nayi na ƴar yayi zan dawo ayi min na uwar ma”.
Shima dariya ya ƙyalƙyale dashi wanda yafi kama da kukan alade kana yace.
“In kin gama kudin da zaki biya kuɗi dubu dari uku da hamsin da uku da ɗari uku da Naira uku da karnuka uku alade uku jakuna mata wanda zanji dadin kwanciya dasu zaki biya mu”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Boka wannan magana tazo da sauƙi”.
Kai ya jinjina tare da maida Jajayen idanunsa kan Hajiya Lami yace.
“Kee kuma kinzo batun ƴar kice?”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Eh Boka Ɗan Ilu Ina nenan temakon ka daka temaki ƴata”.
Wani ƙullin magani ya acikin baƙin ƙyalle ya miƙa mata kana yace
“Gashi ki jiƙa ki bata tasha idan har ta warke ku biya idan bata warke ba ku bari magana ta ƙare basai kun biya ba”.
Muryanta na ɗan rawa ta risinar da kai tare da cewa.
“Boka abinfa na zuba sosai”.
Kansa ya jinjina kana yace.
“Kada ki damu kije kiyi yanda na faɗa idan tasha ta samu sauƙi abiya idan bata samu sauƙi ba kada ku sake zuwa inda nake da buƙatar ku”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Nagode da muna ta jiran wanda yayi mata aikin ai”.
Wani wawan dariya yayi tare da cewa.
“Ai wannan shima yana fama da kanshi ko kun gashi bazaku ganeshiba ya fara girbar abinda ya shuka ne”.
Cikin mamaki suka zuba masa ido suna nazartar kalaman sa.
Cikin sauƙe ajiyar zuciya Hajiya Bunayya tace.
“Yanzu Boka batun auren ƴata Asiya ɗin nan yanzu saura wata ɗaya da mako uku ina so idan aka raba Auren Khausar da Moddibo mai zai hana ya Auri Asiya tunda ita Amina tuntuni anyi Aurenta da wannan Jarabebben Yaron”.
Wata mahaukaciyar dariya ya kece dashi wanda yasa suka shiga nutsuwarsu kana yana nuna ta da yatsa ya cigaba da dariya kusan minti biyu kafin yace.
“Ai Amina kam ba maganarta kwatakwata kibar batun maganarta ki daina kira min sunanta anan saboda waɗan da suke tare da ita Aminaina ne babu yanda zanyi in shiga tsakaninta dasu shin baki ga gidana kamar curuba toh ai muhallin waɗanda ke tare da Aminane”.
Hajiya Bunayya kuwa cikin rashin fahimtar abinda yake faɗa tace.
“Yanzu ba za'a samu idan Moddibo ya saki Khausar ya Auri Asiya”.
Fuska ya ɗaure tamkar na tsohuwar biri kana ya buga mata tsawa tare da cewa.
“Asiya wannan miji shine ya dace da ita ke dai kawai tunda ga abinda kike so kije kiyi Moddibo zai sake ta magana ta ƙare”.
Kai ta jinjina tare da cewa.
“Nagode yaushe zan dawo?”.
Idanunsa ya ɗaga sama kana yace.
“Duk randa buƙatarku ta biya bukatar ku yana biya washe gari ku shirya kuzo ku biyani idan kun ki koda second ɗaya kamar inuwa haka zan biku Nasan duk motsin ku sannan in tona muku asiri a inda baku zata ba”.
Kai suka gyaɗa har suna haɗa baki wajen cewa.
“Zaka same mu masu cika alkawarin”.
Sai kuma suka miƙe zasu fita cikin tsawa yace.
“Ku fita da baya da baya sannan ku cire kayan ku tsirara zaku fita daga ciki ba'a fita da sutura anan dan kayanku shine mahadin bibiyarku”.
Jiki na rawa suka cire kayansu kana suka fita tuɓutur-tuɓutur.
Suna fita Mutumin daya rakasu ya miƙa musu kaya kasancewar yasan ƙai'idar wajen karɓa sukayi suka sa kaya ya goya su amashin kamar yanda suka zo aranan suka koma cikin Damagram suka samu masauki suka kwana washe gari suka kama hanyar dawowa Nigeria ƙarfe uku dai-dai Jirginsu ya sauka cikin Abuja, A Abuja suka kwana karfe tara Jirginsu ya tashi daga Abuja zuwa Adamawa daga nan suka hau mota zuwa Taraba.
Bayan sun dawo da kwana biyu sun huce gajiyarsu.
Yau Hajiya Bunayya ta shirya fara aikin cikin yaƙini da gamsuwa, rashin imani, da bushewar zuciya, ta shiga ban ɗakinta kana ta tsugunna ta kware takashinta ƙwallon aduwar ta ɗauka tare da turawa acikin da ƙarfi ta runtse idanunta jin wani irin azabebben zogi daya amsa cikin dauriya ta runtse idanunta tare da cewa.
“Ai ranan biyar buƙata rai ba abikin komai yake ba”.
Sai kuma ta ɗauki na biyu ta cusa shima zugine ya ratsata wanda yafi na farko atake wasu ƙwallan azaba suka zubo mata tayi saurin gogewa tana murmushin ƙeta kana ta ɗauki na ukun ta cusa da ƙarfi tana ciro ya tsar taga yatsar yayi datti da sauri ta ɗauki Morning Fresh dake ajiye ta wanke hannunta afili tace.
“Wannan ya tsata ne ma da kaina nake jin ƙyamarta ina ga Khausar?,da zatayi baƙin jini awajen mijinta da dangin ta babban farin ciki na ma ance a idanun duniya duka za tayi baƙin jini duk yanda Yayun mijinta da ƙannensa ke rawan jiki akanta duk zasu tsaneta su koreta fata-fata Ni banƙi ma ace daga Morocco ta dawo har Nigeria da kafa ba shegiya ƴar Bororon daji tana nan kamar Sadaka yalla”.
Tana gamawa ta fito tare da zama gefen gado wayarta ta ɗauka tare da dearling Number Amina tana jin ta ɗaga tace.
“Hello Amina”.
Acan ɓangaren Amina kuwa cikin sanyin murya da rauni ta sauƙe Ajiyar zuciya kasancewar dai-dai lokacin macijin ya gama shanta araunane tace.
“Umma”.
Hajiya Bunayya na gyara zama jin muryan Amina tace.
“Amina am kinyi sanyi da yawa”.
Cikin lumshe idanu da rauni Amina ta girgiza ji kai tare da cewa.
“Bakomai Umma”.
Ajiyar zuciya Hajiya Bunayya ta sauƙe kana tace.
“Ko dai cikin ne yake wahalar dake haka?”.
Numfashi Amina ta fesar tare da cewa.
“Hmmm”.
Kasancewar baza ta ita cewa komai ba duk da kuwa yanda zuciyarta ke son faɗa amma bakinta ya gaza.
Murmushi Hajiya Bunayya tayi tare da faɗin.
“Kin san shekaran jiya muka dawo daga Niger?”.
Kai ta gyaɗa tace.
“Eh munyi waya da Samira take cewa kun dawo har an bata magani ta fara sha”.
Kai Hajiya Bunayya ta jinjina tare da faɗin.
“Haka dai munje mun dawo in Sha Allah burin mu zai cika Khausar za'a korata zata baro Morocco da baƙin jini yanda babu wani ɗa namiji da zai sota kowa zai ƙyamaceta”.
Cikin sanyin Amina tace.
“Hmmmm Ummah kenan? dama dai kin haƙura ni yanzu bana son hakan ma cutarwa da wani bayi da wani riba abuma ko mun yi ba Kamasu yakeba saboda sun yarda da Allah suna da kekyawan yaƙini da riƙe ibada”.
Baki ɗaya yanzu bata da kuzari tsoro ya kamata kwata-kwata bata cikin nutsuwarta da haiyacinta tana so ta buɗe bakinta ta faɗawa mahaifiyarta amma bazata iya ba.
Hajiya Bunayya kuwa cikin bushewar zuciya da rashin fahimtar halin da ƴar tata ke ciki tace.
“Ki kwantar da hankalin ki In Sha Allah kwanan nan burinmu zai cika in Allah yaso ya yarda wannan aikin shi yafi na Kar,zu”.
Ahankali Amina tace.
“Ba komai ɗazu munyi waya da Addah Asiya ashe dai batun Aurenta ya matso har an fara shiri Abba yazo yace mata wani irin Furnitures take son a shirya mata wai baban Modibbo ne da kanshi zai mata komai ko?”.
Dariya Hajiya Bunayya tayi kana ta gyara zama tare da cewa.
“Sosai ma kuwa ayanda suka yanke bikinma ai saura wata ɗaya da mako biyu nema za'ace kin san shina Zakariyya mahaifiyarsa da baban Modibbo uwa ɗaya uba ɗaya suke”.
Cikin sanyi da lumshe Idanu Amina tace.
“Allah yasa muna raye zuwa lokacin”.
Kai ta gyaɗa Tare Da cewa.
“In sha Allahu ma muna raye yaushe zakizo”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Allah yasa haka in lokacin yayi muna rayen bikin saura mako ɗaya zanzo”.
Ahankali tace.
“Amina naji kamar bacci kike ji bari in barki kiyi bacci”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh sai da safe”.
“Allah ya kaimu ta amsa daga nan suka katse kiran...
*Jauro Yaya*
Acan ɓangaren Hajja Nana adai-dai lokacin suke zaune da Baffa Jimeta wanda tunda ya koma Adamawa bai zoba sai yau cike da kulawa da kuma girmamawa ya kalli Mahaifiyar tasa da Ƙannenta yace.
“Tunda ga yanda al'amarin Auren khausar ya kasance ga kuma Dija da Aliyu sun haɗa kansu sun fahimci juna kunga kenan abu yazo da sauki“..
Murmushi Bappa Jauro yayi cikin jin daɗi yace.
“Alhamdulillah nayi farin ciki da wannan al'amarin”.
Cikin jin daɗi da girmamawa Baffa Jimeta ya gyara zamansa tare da cewa.
“Nima naji daɗin haka saboda munyi magana da Alh Bashir Mai Dala cewa tunda Aliyu da Abba duk ya ɗaukesu aiki a Company sa acan dan haka yana so Aliyu ya Jagoranci Company's sa acan zai koma can Morocco da zama shiyasa nace In Sha Allah Aliyu bazai tafi Morocco ba sai da Matashi”.
Murmushi Hajja Nana tayi cike da ƙasaita ta gyara zamanta tana kallon ɗan nata Baffa Jimeta kuwa cikin sauƙe numfashi ya cigaba da cewa.
“Shiyasa nazo akan atsaida batun maganar Aurensa da Dija ya ɗauki matarsa su tafi kunga itama Khausar ta samu ƴar Uwarta sannan ga Asma'u da take Aminiyarta za tayi Aure su koma can kana ga Asiya da suka zauna gida ɗaya yanzu ma kafin nazo nan sai da na biya ta wajen Alh Bashir Mai Dala na bashi mukayi mgnar”.
Cike da gamsuwa Baffa Liman ya jinjina kai tare da cewa.
“Wannan abu yayi munyi farin ciki, abu ya zama tuwonmu Manmu magana yaƙare in Sha Allah nan kusa kuma za'a yi ɗaurin Aure”.
Baffa sadu dake gefen Hajja Nana ya sauke ajiyar zuciya yace.
“In sha Allah kuwa In yaso Auren mu ajiyeshi nan da wata ɗaya mana”
Ajiyar zuciya Baffa Jimeta ya sauƙe tare da cewa.
“A'a da yake Alh Bashir ɗin yace Modibbo ma zasu zo Auren Asma'u mu bari ya kasance ahaɗa bikin gaba ɗaya idan an tashi sai atafi da Amaren”.
Cikin gamsuwa Baffa Jauro yace.
“Haka ma yayi Allah ya nuna mana da rai da lafiya”.
Daga nan suka ci-gaba da tsara bikin yanda zai kasance”....
Bayan kwana uku Hajiya Bunayya ce tsugunne a Bathroom ɗin ta yayin da ta cika Bocket da ruwan ɗumi ahankali ta sanya tsarta ta zaro wannan abu mai kama da ƙwallon aduwa ta ɗaura akan Tissue data ajiye gefenta ahankali ta sake cusa ya tsanta ta zaro na biyu ta ajiye ajiyar zuciya ta sauƙe kana ta sake danna yatsarta da niyyar ciro na uku taji babu sake cusa wa tayi bata jiba akiɗime tare idanunta tare da faɗin.
“Ha'a to ina yake?".
Sai kuma ta sake danna yatsarta akaro na uku da ƙyar taji kansa cikin sauri ta cusa yatsanta da ƙarfi ta fisgoshi.
Ajiyar zuciya ta sauƙe da karfi ba ƙaramin tsorata tayi ba domin tayi zaton koya ɓace acikinta tana cirowa kuwa wani irin azabebben ƙaiƙayi na fitar hankali ya game wurin cikin sauri ta shiga kwara ruwan zafi ahankali taji ƙaikayin ya ragu miƙewa tayi tare da naɗe su acikin Tissue ta fito kana ta shanya a Balcony inta ƙasan dish ɗin ta yadda ba wanda zai lura dashi komawa ɗaki tayi ta zauna tana sakin ajiyar zuciya jin har yanzu ƙaiƙayin na damunta.
Bayan kusan kwana biyar ya bushe ƙermes ne ta ɗaukoshi ta daga a turmi ƙarfe tare da haɗawa da garin maganin kana ta haɗa da yashin tsikayar gidan nasu sannan ta watsashi tsakiyar dare yadda bokan yace mata a hankali ta turo ƙofar falonta ta shigo cikin jin daɗin ta gama haɗa aikinta tana sauke numfashi ta zauna bakin gadonta sai kuma tayi saurin miƙe da masifan sauri sabida wani irin masifeffen ƙaiƙayin da taji takashinta ya fara yi irin kaiƙayin da yayi mata randa ta zaresu da gudu ta nufi bathroom sai kuma ta kwaye zanenita tare da cusa yatsarta ciki tafara mishi wani irin kwakwasusa.
“Shhhhuuuwwwyyyooo Allah na wayyyyyoohhhh duwawuna ƙaiƙayi-ƙaiƙayi”.
Sai kuma maza ta haɗa ruwan zafi still dai tana yagunan wurin wanda tuni yayi jazir.
Koda ta shiga cikin ruwan zafin kuma sai ta daka tsalle tare da miƙewa tsaye sabida yadda taji wasu abubuwa suke cin takashin nata wanda sunfi ƙarfin a kirasu da cucuka ko mude.
A wannan ranar dai haka ta kwana a tsaye tana susa har farshen yatsar ya karye sai asuban fari taji kaiƙayin ya lafa sannan ta samu bacci.
*Morocco*
Yau kwanan Khausar hamsin Cif da tarewarta sashen Moddibo bayan sallar Asbah Khausar ce zaune a bedroom ɗin Moddibo tun da ita idar da Sallar Asbah bata motsa ba tana kan sallayar yayinda gaba ɗaya jikinta ke a saluɓe kasalar data zame mata abokin rayuwa a jiya da yau ta tsananta mata wata ƙil hakan baya rasa nasaba da rashin cin abinci wanda ta kai kwana biyar sai ruwa tea da fruits domin abin ƙaruwa yakeyi.
Bayan Moddibo ya dawo daga Masallaci kai tsaye bedroom ɗin sa ya wuce ganinta zaune kan sallaya yasa ya nufeta tare da zama gefenta ya zuba mata ido gaba ɗaya ta rame ta ɗanyi fiyau sai wani irin fari mai kamar yellow da tayi wanda har jijiyoyin jinin jikinta suka ɗanyi kore kaɗan suka bayyana.
Ganin kamar azkar takeyi ne yasa shina ya janyo Alkur'aninsa dake kan Starm.
Cikin lumshe idanu da nutsuwa yayi A'uziyyah kana ya fara karatu cikin Suratul Ibrahim daga forko.
Yayinda ita kuma taci gaba da yin azkar ɗinta bayan ta gamane ta shafe jikinta da addu'ar kana a hankali ta ɗan yunƙuro ta matso kusa dashi a dai-dai lokacin kuma yazo aya ta (39)a hankali ya ɗan juyo ya kalleta tare dasa hannunshi ya kamo nata, cikin sanyayyar muryansa yaci gaba da karantun kamar haka.
_“Alhamdulillaziy wahabli alalkibri Isma'iyla Wa Ishaƙ,Inna rabbi lasami,Uddu',a.”_
Sai kuma ya janyota jikinshi a hankali ya rungumeta,
Ita kuwa Khausar cikin kasala ta daura kanta akan kafaɗarsa hannunta ɗaya na bisa ƙirjinsa idanunta na kan Alkur'anin tana mai jin zazzaƙan sautin muryarsa.
Shi kuwa Modibbo hannunsa na dama na kan Kur'anin na hagu kuma na rungumeta da ita yana cigaba da karatun,
A hankali ta kuma manna kanta da ƙirjinsa sai kuwa ta lumshe Idanunta jin yana karanto aya ta(40) yanda sautin karatun ke ratsa dodon kunnenta yasa itama buɗe bakinta muryarta a sanyaye a hankali ta fara binshi suna karatun a tare sai dai muryarshi ya ɗanfi nata fita a jere suke karanta harufan ayata 40.
_“Rabbij Alniy Muƙiymassalati wamin zuriyyatie.Rabbana wataƙabbwl du'aaa”_.
Cikin lumshe idanu da sauƙe numfashi ta kuna zamewa ta kwanta kan cinyarsa tana fuskantar qura'an ɗin sabida duk yadda tayi bata jin daɗin jikinta ga azabar yunwa da kasala ga alamun zazzaɓin da take ji,
Shi kuwa Modibbo still dai yana karatu ya ɗaura hannunsa aƙugunta yana shafawa yana cigaba da lumshe idanunsa yayinda ita kuwa Khausar tayi lamo a jikinsa, sai kuma ta miƙe zaune tana ɗan fuskantarsa, cikin sanyi ya ɗaura bayan tafin hannunshi bisa kuncinta na dama yana ɗan shafa har lau kuma idanunsa na kan qura'an ɗin.
Cikin narkewan jiki ta langwaɓar da kai tare da ƙara matsoshi sosai ganin haka ne, yasashi sa hannun tare da ɗan tura katakon da Qura'an yake a kai, kana ya jawo ta ya rungumeta tsam a jikinshi da hannunsa duka biyu a hankali yake ɗan shafa bayanta da hannunsa na dama da yake saman na hagun alamun yana son ta samu nitsuwane yasa yaci gaba da karatun cikin zazzaƙan muryansa ya ɗauko ayata (41) kamar haka.
_“Rabbanagfirliyy,Walilwalidiyya Walilmu'uminiyna Yauma Yaƙuumulhisab”_.
Ahankali ta ƙara rungumesa tare da ɗan ɗago kanta ta kalleshi idanu cike da alamun hawaye sai kuma ta sauƙe numfashi mai zafi, wanda yake sauka acikin kunnensa.
ba tare daya kai ƙarshen Surar ba kasancewar yazo ƙarshen Ayar ya rufe Kur'anin tare da gyara mishi zama kana ya janyota jikinsa ya rungumeta da kyau yana goga sashen sa afuskarta ya motsa laɓɓansa tare da cewa.
“Ya dai?”.
Ahankali tayi miƙa tare da lumshe idanunta wani irin kasala da yunwa takeji baki ɗaya jikinta yayi nauyi ba tada kuzari ko kaɗan zuwa yanzu ta gama fahimtar baki ɗaya yanayinta ya canza ta rasa meyesa meta cikin sanyi ta girgiza masa kai tare da cewa..
“Ban sani ba”.
Yayin da idanunta suka canza launi saboda yanayin da take ciki.
Sake jawota jikinsa yayi kanaya cusa kansa tsakanin wuyanta muryansa can ƙasa cike da kasala yace.
“Minha yau baki da lfy me yake damunki ne?”.
Kai ta girgiza tare da cewa.
“A'a nima ban sani ba fa?”.
Cikin rauni, kulawa, tausayi, gami da jinƙai da damuwar yadda yaga yauɗin gaba ɗaya ta sake yace.
“Minha Vidaa yunwa cefa take son lahanta min ke”.
Bai jira jin abinda zata ce ba ya mike tare da ɗaukarta cak a jikinsa, batayi musu ba, sabida bata da ƙarfi a hankali ta lumshe udanunta ganin side ɗin Didi ya nufa da ita.
Da sauri Didi dake tsaye a dinning area ta zuba mishi ido cike da tsoron da yasa jikinta mutuwa tace.
“Aliyu lafiya kuwa”.
Ta ƙare maganar tana nufi tsakiyar falon ganin ya kwantar da ita bisa kujera murya cike da damuwa yace.
"Didi yau kusan kwana biyar bataci abinciba yau kuma kinga duk ta sake na rasa meke damunta Didi”.
Ya ƙare maganar yana zama gefenta, ita kuwa Didi da sauri ta koma dinning ta haɗa tea mai zafi kana ta dawo,
Cup ɗin ta miƙa shi tare da cewa.
“Gashi bata”. Da sauri ya tallabota ya zaunar da ita tare da amsar cup ɗin yasa mata a baki, ba musu ta kafa kanta ta fara sha saida ta shanye a janye cup ɗin dai-dai lokacin kuma Innayi ta shigo da sauri ta ƙaraso gabanta kusan a tare suke mata sannu ganin wani irin zufa daya keyi mata.
Ita kuwa Khausar cikin wani irin gigitaccen yunƙurin amai daya taso nata, ta damƙi hannun Modibbo tare da niyar miƙewa wanda tuni ta fara kakari da sauri Didi ta maida ita zaune, shi kuma ya tallabota.
Aiko nan take ta fara zuga.....