Showing 117001 words to 120000 words out of 218703 words

Chapter 40 - Sakayyah 2 Hausa Novel Complete

haɗa tayi a tare, sabida ganin wani irin zabgegen maciji baƙƙirin da yake mirgina a tsakiyar falon yana mai baza wani irin fitinennen huci da zaro harshe, abinka da babu alla a cikin rai, gaba ɗaya ta mance da addu'a sai karkarwar da ihun da takeyi, tare da dira ta bayan kujerar cikin kiɗima, ta fara lalubar wayarta, tana ɗaukan wayar ta dannawa, Unclee Naseer ɗin kira, amman bai dagaba, da gudu ta nufi bedroom ɗinta, tana shiga taci gaba da danna mishi kira babu ƙaƙƙautawa amman ko sau ɗaya bai ɗagaba.
Sai kuma ta fara kiran number Hajia Bunayyah itama waya mata ringgin amman ba'a ɗagawa.

Wani irin gigitaccen ihu ta fara kurmawa lokacin da taji hucin na ƙara matsowa bedroom ɗin nata, ga gida ita kaɗai babu ko mai gadi.

Can kuma sai taji hucin ya bari, ajiyan zuciya ta fara sauƙe tare da yarfe zufar dake ɗiga mata tako ina, dai-dai lokacin kuma taji Unclee Naseer na kiranta tare da bubbuga mata kofar.
Cikin rawan jiki tazo ta buɗe ƙofar ganinshi yasa ta faɗa jikinshi tare da sakin kuka.
“Ah Baby lfy kuwa meya faru?”.
Cikin tsoro tace.
“Uncle Naseer ƙaton maciji fa na gani, a tsakiyar falonmu, inata kiranka baka ɗauka”.
Wani irin makirin murmushi Naseer yayi tare da cewa.
“Oh my god Baby dama dan wannan macijin ne kika rufe, kilata ihun nan, ihunki nefa ya dawo dani dan dana sauƙa ƙasan na tsaya ina ɗan waya da Kesi shiyasa ban fita da wuriba”.
Cikin tarin mmki tace.
“Dama kasan da macijin ne a cikin gidan?”.
Hannunta ya kawo suka fito falon, bisa kujera suka zauna yace.
“Na san dashi mana, ai shiyasa nace karki shiga ɗakinnan dan a ciki yake, kuma babu abinda zai miki kawai dai nasan, idan kika ganshi zaki firgitane, shiyasa nace kada ki shiga, amman babu abinda zai miki shi gadin gidan yakeyi, babu wani abin cutarwar da zai shigo muddin yananan, dan haka ki kwantar da hankali ki”.
Cikin ɗan sauran taradadi tace.
“Da gaske ba abinda zaimin?”.
Cike da yaudara yace.
“Shin bakiga bamu da mai gadi a gidanba?”.
Da sauri ta gyaɗa mishi kai.
“Toh ai dan nasan ibada wannan macijinne shiyasa ban wani nemi wani mai gadiba.
Kada kiji tsoro gaba ko ya fito, kada ki gudu babu abinda zai miki ko kan cinyarki ya hau, in Kinga ya fito dai yunwa ne yakeji, ni har gado ɗaya muna kwana dashi”. Cikin bashi dukkan yarda tace.
“Da gaske ba abinda zai min?”.
Cikin son samata yarda yace.
“Wallahi ba abinda zai miki ke dai ko jikinki yace zai hau ki barshi kada ki gudu”.
Daga nan yaci gaba da rubta tunaninta saida yaga ta ɗan nitsu kana ya sake fita.


Taraba Gembulan.
Hajia Lami ce zaune bakin gadon da Samira take kwance cikin toshe hanci tace.
“Ki tashi ki shirya muje asibiti, dan wannan wari ya fara yawa, ni kaina tsoron matsowa kusa dake nake”.
Cikin zubda hawayeba Samira tace.
“Uhmmm Momy kenan, amman kuma lokacin da nake cewa bazanje boka yayi lalata da nuba, kece kikayi ta ingizani kina turani harda nuna zakiyi fushi dani in banjeba, sai gashi yanzu kuma harda ke a cikin masu guduna sabida warin da nakeyi"...






By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 23*

Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*


*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 08069423567 ko kuma ta wannan 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...._

🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida.

Sai kuma ta fashe da kula mai cike da rauni, murya na rawa tace.
“Momy da kin kasancemun uwa ta gari da haka bai faru da niba, mun sake Allah mun kama boka baga masifar da ta biyo bayan kauce gaskiyaba, gashi yanzu munaji muna gani Modibbo ya auri Khausar, a lokacin da ahlinsa suka bayyana da irin matsayin da ko wacce mace zasayi fatan samu, duk da ni dai Allah ya sani ba kuɗi babu ba, naso Modibbo ne har raina sabida iliminshi da kyanshi”.
Cikin zuƙar warin da Samiran keyi Hajia Lami tace.
“Yanzu dai zaki tashi mu tafi asibitin ko sai kin gama zagina”.
Cikin sharce hawaye tace.
“Kiyi haƙuri Momy bazan zagekiba, wannan zunubin dana aikata ma ya isheni ba sai na ƙara wani ba na zagin mahaifiya, ki yafe min mutafi”.
Ta ƙare mgnar da miƙewa suka fita.

Marocco
A hankali ya fito daga falon nashi yana mai zuba wani irin fitinennen ƙamshi, tare da sheƙi da ƙellin fuska.
Ware manyan idanunsa yayi lokacin da yaji ƙaran wayar Khausar da ya ajiye bisa, dinnin table a hankali ya nufi kan Dinning area ɗin.

Ido ya zubawa fuskar wayar ganin.
*My happiness* a fuskar wayar ya sashi rumtse idanunsa da ƙarfi sabida jin.
Wani irin abu mai masifar ɗaci da maƙaƙi ya tokari maƙoshinsa.
Rumtse idanunsa ya kumayi kana ya buɗesu da sauri, hakanne da kuma ganin a saman lips inshi yace.
“My happiness”.
Waye?”.
Sai kuma ya sa hannunsa ya ɗauki wayar tare da juyawa da sauri ya nufi falonta.

Can ya hangota a bakin ƙofar corridor ɗin tanata kiciniyar buɗewa amman ta gaza gane ta yaya ne ake buɗe ƙofar.
Da sauri ta juyo jin alamun takun mutun, cikin sauri tayi kasa da kanta ganin wani irin kallon da yake liƙamata shi kuwa kanta ya nufa gadan-gadan ganin hakane yasa ta fara ja da baya da baya jin ta jingina da ƙofarne yasa ta buɗe idanunta.
Da sauri ta kuma rumtse idanunta ganin yadda ya matsota gab da gab, cikin wata irin muryar da shi kansa bai tantace ta meneba yace.
“Wayeshi”. Ya ƙare mgnar tare da nuna mata fuskar wayar,
sassayan numfashi ta fesar tare da miƙa hannunta alamun zata amshi wayar, cikin tsawa yace.
“Ce miki nayi ubanwaye ne shi, baki bani amsaba kike miƙo hannu zaki amsa”.
Cikin tura baki da sauƙe numfashi tace.
“Toh ni ka bani wayata mana, me ruwanka da masu kirana”.
Wani irin gigitaccen abune yaji ya soƙi ƙahon zuciyarsa, cikin juyewar yanayi ya danna mata wani irin gigitaccen tsawa tare da ceea.
“Wane ɗan iskanne shi da zai kira m...”
sai kuma yayi shiru ganin wani kiran ya kuma shigowa.
Ita kuwa Khausar wani irin numfashi tsoro taja tare da takure jikinta wuri ɗaya sabida ganin kamar marinta zaiyi.
Amsa kiran yayi tare da liƙa wayar a kunnensa ba tare da yace komai ba.

Wani irin ɓoyeyen ajiyan zuciya mai nauyi ya fesar jin murya Mommy Khausar ce, cikin nitsuwa kamala kawaici hadi da girmamawa yace.
“Wa alaikassalam”.
Cikin sanyi Mommyn ta fesar da numfashi dan ta gane muryarshi.
“Mommy ina kwana?”. Ya kuma cewa jin tayi shiru.
Ita kuwa Mommy cikin girmama kai tace.
“Lfy lau Moddibo ya gida”.
Wani irin amintaccen numfashi ya kuma fesarwa tare da sa hannunshi ya kamo hannun Khausar ɗin kan ya juya da ita suka nufi falonta yana mai cewa.
“Alhamdullah Mommy yasu Raudat”.

Ya kare mgnar tare da sake hannunta kana ya zauna bisa kuje.
“Suna lfy, gatama tun ɗazu take ta kuka wai in Kira mata Adda Khausy”.
Juyowa yayi ya kalli Khausar ɗin da ta matso kusa dashi tana mai miƙa mishi hannun alamun ya bata wayar, fuska ya tsuke tare da dannan mata harara.
Kana yace Mommy kuwa.
“Toh a bawa Raudat ɗin”.
Cikin kawaici Mommyn ta miƙawa Raudat ɗin waya tana amsa tace.
“Hello Adda Khausy nayi missing inki”.
“A'ah Raudat ya akayi yau bakije school ba?".
Jin hakane yasa Khausar kara matsowa gareshi cikin zumuɗi da son jin muryar Raudat ɗin dan tun shekaran jiya basuyi mgn ba, da sauri ta miƙo hannunta har tana taɓa sajenshi.
Juyowa yayi yana maiyi mata wani irin kallon mai haɗa da saƙonni masu yawa, katse kiran yayi baƙi ɗaya ya xora wayar a aljihun rigar shaddar dake jikinsa wacce iri ɗaya ne da nata.
Cikin tsuke fuska ya tsira mata ido tare da juyowa ya fuskanceta da kyau idonshi ya zira cikin nata tare da cewa.
“Na dai lura ke, in baki taɓani ba, bakya jin daɗin rayuwarki, na gama fahimtarki ban san me kikeso inyi mikiba da kike shigemin rayuwa da jiki, gaba ɗaya in kin gannin jikinki rawa yake, ji kike kamar kin cinyeni ɗanye dan rashin ta ido, yanzu ji yadda kike wani son kamani ban san uwar me kikeso inyi miki ba”.
Ya ƙare mgnar cikin ƙarfin hali.
Ita kam Khausar cikin mmki da tsoron lamarin shi ta buɗe baki tare da cewa.
“Ni dai Allah ya sani ba abinda ya dameni da kai, kawai wayata zaka bani, toh ma ni me ruwana da kai”.
Ta ƙare mgnar tana tura baki.
Da hannunshi yasa ya kamo hannunta tare da matsewa har saida tayi ƙara kana yace.
“A hakan dai kikace kina sona! Ga yadda kike kallona kamar ki haɗiyeni ni ban masan me sajena ya tsare mikiba".
Da sauri ta kwaɓe fuska tare da yin ƙasa da kanta tace.
“Toh ni ai wayata nake kalla".
Ta ƙare maganar tana tura baki.
Shi kuma cikin tsareta da ido yace.
“Jiya da dare ba biyoni kikayi ba”.
Sai kuma ya miƙe tsaye tare da motsowa kusa da ita cikin wata irin sassautacciyar muryansa can ƙasan maƙoshi yace..
“Ni kikeyiwa haka ko? Zanyi maganinki zan miki abin da kike son inyi mikin, tunda na lura a hannu kike”. Ita batama fahimci mgnar ba sai dai jujjuya ido da tayi cikin shaƙar ƙamshin jikinsa tace.
“Ni dai ka bani wayata”. Tsuke fuska yayi tare da matse jikinsa baga ɗaya kana cikin danne yanayin da yake ciki yace.
“Bazan badawa”.
Sai kuma yayi mata kallon sama da ƙasa kai ya jinjina ganin mayafin jikinta ya ɗan rufe mata ƙirji, juyawa yayi kana ya ɗan zagaya bayanta tare da cewa.
“Mu tafi Didi na kiranki". Zuwa yanzu tasan waye Didi tasan nasabarta da kuma kimarta, haka yasa cikin nitsuwa tayi gaba batare da tacemai ko ƙalaba, bayanta yabi, tare da sauƙe ganinsa kan ƙugunta dake juyawa kai kace kamar da gayya takeyi.
Kiciniyar buɗewa kofar ta fara, shi kuwa ido kawai ya zuba mata, kusan one minute tana kiciniyar, gani, ta gazane ta juyo ta kalleshi tare ɗan tura baki tace.
“Na kasa buɗewa”. Kallon gefen ido yayi mata kana yace.
“Uhmmm dama ke me kika iya banda rawan kai”.
Wasu pin number dake jikin ɗan ƙofar ya danna wanda shima Ibraahim ne ya nuna masa.
Da hannun yayi mata alamun su tafi.

A hankali suka fito kana yaja ƙofar ya rufe, jujjuya kai tayi don so take ta gane ta inane inda su Ummi suke amman ta gaza ganewa kasancewar idonta a rufe suka fito, kuma ma ƙofofin wurin sunyi yawa.

A hankali ta fara taka steps din suna sauƙa ga mamakinta sai taga basu ɓullo cikin falon nanba, sai ganinta da tayi cikin corridor nan mai faɗi, kusan a jere suke tafiya yayinda suke baza wani irin fitinennen ƙamshi kamar furannin.

Da sauri tayi ƙasa da kanta lokacin da taga sun ɓullo cikin wani ƙasaitaccen falo, wanda tayi arba da Rahama dake tsaye, da sauri Rahama ta nufeta tare da buɗe mata hannun.
A hankali ta ware hannunta suka ruggume juna.
Didi kuwa murmushi ta saki tare da miƙewa, ruggume su tayi duka biyu tana mai cewa.
“A onmi jam nɓingel am". Kin tashi lafiya ɗiyata”.
Cikin mmkin yadda akayi Didi da yaranta kab da yawa da cikin mutanen makusantansu suka iya fllanci ras ta ɗan kalli fuskar Didi tare da cewa.
“Jam Alhamdulillah Didi noi Chomri".
Lfy lau Alhamdulillah Didi ya gajiya.
Murmushi Didi tayi tare da kallon Modibbo da ya zuba musu ido ko keftawa bayayi.
Sai kuma ta juyo cikin falon jin su Lalla Khadijah suna dariya tare da cewa.
“Didi kalli Ibarahim yadda ya wani zumbura baki, wai sun kwace mishi fada”.
Cikin dariya tace.
“Yoh ai bashi kadaiba kalli Yayan nashi ma yadda ya tsaremu da ido".
Da sauri Modibbo ya kauda kanshi jin abinda Abualeey ke mishi dariya.
Saita nitsuwarsa yayi cikin yanayinsa mishkilanci ya raɓa gefensu ya wuce, biyoshi sukayi a baya.
Ita kuwa Khausar a hankali ta rusuna gaban Abualeey cikin sanyi da girmama tace.
“Barka da safiya Abba”.
Cikin kula yace.
“Barka dai Khausar ya bakunta".
Cikin yin ƙasa da kai tace.
“Alhamdullillah".
Sai kuma ta miƙe sabida kamo hannunta da Aunty Khadija tayi tare da cewa.
“Bismillah zo muje muyi breakfast”.
Kai ta gyaɗa mata kana tabi bayanta.
Yayinda suma duk saura suka bi bayansu suka nufi wani tamfatsestsen Dinning table wanda a ƙalla yake da kujeru goma sha biyu.

Sai kuma duk suka tsaya, har saida Didi da Abualeey suka iso suka zauna sannan duk suka zauna.
Didi da Abualeey suna kan karshen table ɗin a jere, sai kuma Khausar dake gefen Didi forkon layin kenan sai kuma ɗaya gefen forkon layin Modibbo ne zaune wanda ya zama yana fuskarta Khausar.
Sai Ibrahim dake gefshi yana fuskarta Rahama dake gefen Khausar, sai kuma Lalla Hafsat dake fuskantar Hakim sai kuma Lalla Khadijah, dake fuskantar Ashshe.
Ya zama kujeru uku ne babu kowa a kansu.

A hankali Lalla Khadijah ta miƙa tsaye tare da fara savin dinsu ɗaya bayan ɗaya duk da kowa da irin kalan abinda ta zuba mishi.

Abualeey masace mai haɗa da miyar daddageggen nama, sai kuma Modibbo da Ibarahim da ta zuba musu soyayyan dankali, da dege-dege da yaji naman kaza da kuma fararen tsokokin kifi sai kuma wadatacciyar albasar da take sa ɗan sauran gwaninta, sosai yajin yayi meɗeu a cikin domin Ibarahim na son yaji sosai sai kuma soyayyan kwai da yaji vegetables wani iri daddaɗan ƙamshi mai tada tsohuwar yunwa dege-dege ke gazawa, shi ta zubawa Khausar ma da Rahama, sai kuma ta sawa Ashshe da Lalla Hafsat masa da miyan ita kuma irin nasu Khausar Hakim ma Masa da miyarsun ta saka mishi.
Da sauri duk suka juyo jin muryar Dr Jameel da Zakariyya da kusan a tare suka shiga.

Bisa kujeru dake gefen Lalla Khadijah suka zauna bayan sun gama hausawa.
Suna ta zuba musu abincin.

Bismillahi suka kana duk suka fara ci.

Yayinda Khausar kuwa ke riƙe da fork din tana ɗan jujjuyawa tana ganin yadda miyar taji nama da kifi.
Da sauri Didi ta kalleta tare da cewa.
“Bismillah ɗiyata kici abinci”.
Murmushi ta ɗanyi tare da cewa.
“Toh”. Sai kuma ta ƙare mgnar tare da kallon Modibbo dayi loman forko, da sauri ya lumsh idanunsa, yana maijin ɗan-ɗanon abincin mai gamsarwa na ratsa mishi harce, sai dai kuma wani irin gigitaccen yajin da yaji yana gama gaba ɗaya jijiyoyin bakinshi manya da kananan. Allah ya sani shi dai yana masifar tsoron yaji.
Rahama ce ta kalleshi cikin murmushi tace.
“Yah Aleey yayi daɗiko nice nayi mana girkin da kaina”.
Cikin danne azabebben yajin dake gab da gigitashi yace.
“Yes kinci a baki tukuici”.
Sai kuma ya ɗan kalli Ibarahim dake cewa.
“Wow masha Allah ai ɗaɗi kam sosai ma, wannan girki ko yau aka aurar da ke ai bamu da haufi”.
Kai Khausar ta ɗan sunkuyar tare da soka dankali ɗaya ta haɗa da kifin kadan tasa a baki.
Wani irin zar taji yawun bakinta ya tsinke Allah ya sani tana da masifar cin yaji, shiyasa taji abinci yayi mata yadda takeso, sai dai duk da haka yajin ya fitini harshenta.
A hankali ta kalli Lalla Hafsat da kuma Lalla Khadijah dake cin abinci cike da kwanciyar hankali alamun suma manyan askarawa ne a cin yaji.

Sai kuma ta kalli Dr Jameel ta ɗan kalli Abualeey tare da jan plate gabansa ya fara cin masa da miyar Abualeey da aka sa mishi.

A hankali ta dawo da kallonta kan Modibbo da ya kai hannunsa kanshi yana ɗan shafawa tare da yin ƙasa da hannunsa har zuwa ƙeyarsa.
A hankali ta kuma kai loma na biyu wanda zuwa lokacin Ibrahim dasu Kalla Khadijah har sun kusa cin kaso ɗaya bisa ukun na abinci da ke kan plate dinsu.
Shi kuwa Modibbo cikin sanyi ya kai loma ta huɗu wanda tuni idanunsa sun cika da hawaye sabida azabar yaji daya fitini bakinsa.
A hankali ta tsaida idanunta kanshi tana mai tuno wasu kalaman Yah Jameel a ranar da sukayi rabuwar ƙarshe a cikin Shopping mall da suka shiga, a lokacin da yaga ta ɗauki robar dakekken yaji yace mata.
“Na lura kina son Yaji matuƙa, MJ

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login