Showing 129001 words to 132000 words out of 218703 words
niyar miƙewa, sai kuma tayi saurin rumtse idanunta da masifar ƙarfi.
Lokacin da tayi arba da cikekkiyar kafiyarsa dake tsaye tamkar zata hudu Jallabiyar, kar-kar haka jikinta ya dauki rawa.
Shi kuwa Modibbo wani irin numfashi ya fesar tare da sunkuyowa ya kalleta, sai kuma yayi maza ya kalli jikinshi ganin yadda ta rumtse idanunta ga jikinta da ke tsuma.
Ganin yadda yake miƙene, yasashi saurin matse cinyoyinsa da son ɓoye yanayin da yake ciki.
Kana murya a daburce yace.
“Tashi muyi salla, Kinga yanzuma lokaci ya ƙure mana”.
Jin hakane yasa tayi saurin miƙewa tare da nufar ƙofar falon, tun ma kafin ya rufe bakinsa, cikkn sassarfa take tafiya da alamun rawar jiki da tsoro.
Da ido yabi ƙugunta da ke juyawa tamkar zautacce haka ya fara jujjuya kanshi.
Tare da juyawa ya nufi bedroom ɗinsa.
Ita kuwa Khausar tana shiga ɗakinta, cikin rawan jiki ta zare kayan jikinta, tare da shigewa Bathroom.
Ruwan ɗumi ta haɗa tare da shige ciki, tana mai ɗan jan tsaki dan yau tun safe da tayi wanka bata kumaba, shiyasa gaba ɗaya taji, jikin a ɗaure.
Numfashin mai sanyi ta shaƙa tare da lumshe idanunta dan daddaɗan ƙamshi turarukan wanka da suka ratsa mata jiki da zuciya.
Sai kuma ta ɗan buɗesu, sabida surar jikin Modibbo daya wulgawa ganinta, a hankali tace.
“Yah ilahi me hakan kenan”.
Sai kuma tayi saurin maida idonta ta lumshe tuno yadda ya ruggumeta, ranar da akayi bikin gabatardashi, a hankali ta fesar da numfashin lokacin da ta fara tuno yadda ya yanke mata farce, da kuma yadda ya rinƙa yi mata da ƙafarshi.
Baki ta ɗan tura a hankali tace.
“Ɗan neman mgn, haka kawai ranar ya hanani bacci, da yanayi da banma san na menene ba, gashi yauma duk ya dabaibaye min jiki da idanu mutum kamar mai mayen ƙarfe a jikinsa”.
Sai kuma ta ɗanyi shiru tuno yadda tsulɓin sajensa yake da ɗadin taɓawa.
Kusa tsawo 7 minutes tayi tana jin ɗumin ruwa da ƙamshin na ratsata, kana daga bisani tayi wonka, tare dayin burosh tare da al'wala.
Tana fitowa ta ɗan tsane jikinta da towel din dake jikinta, kana ta matso gaban dressing mirror, kuccalar sirri kaɗai ta lakata tare da mulke jikinta baƙi ɗaya dashi, domin Allah ya sani ƙamshisa nayi mata daɗin na fitar hankali.
Da sauri-sauri ta zaro wata doguwar riga After dress fari ƙal mai ɗan ratsin yellow.
Ta zura a jikinta tare da jan, zip ɗinshi, rolling kanta tayi da ɗan kwalinshi, tare da ƙara fesa jikinta da wani turare mai ni'imtaccen ƙamshi kana ta shimfiɗa Sallah.
Magrib ta farayi, tare da yin azkar, tana idarwa, ta kumayi Isha, a hankali ta ɗan miƙe tare dayi shafa'i da wutri.
Cikin sanyi ta zaro wata rigar bacci yellow mai ratsin fari fari da akayishi da zanen heart. Rigar mai sulɓice, wace tsawonta iya guiwace.
Pant ta saka red color, sai kuma ta zira rigar bacci.
Wacce daga samanta duk net ne, kana wuyanta mai fadine, daga gaban rigan kuma igiyoyine a sarƙafe haka yasa ƙirjinta ke a fili.
Sai ƙasa kuma dai-dai ƙugun shima net ne mai manyan buluka dan har cibiyarta zaka iya gani, dudu tsawonta da kaɗan ya rufe cinyoyinta.
Ɗan kwallin After dress ɗin ta ware ta ɗaure kanta dashi.
Sai kuma ta dawo bakin gado ta zauna, tana mai shafa cikinta a fili tace.
“Wayyo Mommy na yunwa”.
Sai kuma ta ɗan hau bisa gadon da kyau jin yadda cikinta ya bada ƙugin yunwar.
sosai takejin yunwar to amman me zataci.
tsaki ta ɗan ja a fili tace.
“Dama nan na kawo abincin ɗazun nan.”
A hankali ta jawo blanket din dake bisa gadon tana fadin.
“Bana ma son cin abu mai nauyi yanzu nan, yanzu in mutum yayi garaje in zama katuwa kamar Aunty Lami”.
Sai kuma tayi shiru jin kamar ana bubbuga ƙofa.
A hankali ta ɗan sauƙo bisa gadon tare da jawo After dress dinan ta zira a jikinta, kana taja igiyar dake tsakiyar ta daure, ba tare da taja zip din ba.
Cikin sauri ta fito falon jiyo muryar Rahama na faɗin.
“Hello my Aunty kinyi bacci ne?”.
Da sauri ta ƙaraso bakin ƙofar tare da buɗe wa.
Murmushi tayi ganin Rahama tsaye riƙe da basket a hannunta ido ta lunshs tare da miƙamata basket din cikin alamun ta fara bacci aka tasota tace.
“Gashi Didi tace, tun ɗazu take jiranku, baku sauƙo kunyi Dinner ba, har na fara bacci fa ta tadoni dole wai in kawo muku”.
Amsar basket din tayu tare da sauƙe numfashi jin daɗi Allah ya sani yunwa na ƙwaƙularta.
“Toh ki shigo mana kika tsaya a baki ƙofa”.
Cikin ɗan lumshe ido Rahama tace.
“No ai zan koma”.
Da sauri tace.
“Aa dan Allah ki shigo, dama ina tsoro kwana ni ɗaya”.
Murmushi Rahama tayi tare da biyo bayanta.
Bisa 3 sitter ta kwanta tare da cewa.
“Yoh ina mijinki”.
Ta ƙare mgnar tana kallon wayarta da kira ya shigo.
Ita kuwa Khausar yi tayi kamar bata jitaba, basket ɗin ta aje bisa senter table.
Ita kuwa Rahama amsa kiran tayi tana ɗan kashe murya tace.
“Hello sweetheart bakayi bacci ba?”.
Sai kuma ta kalli Khausar tare da cewa.
“Toh ki ɗauka ki kai mishi mana, Didi tace dan Allah kada yayi bacci baiciba.
Ke kuma tace kisha yoghurt fruits ɗinan, wai ta lura kamar bakya son cin abinci”.
Murmushi Khausar tayi yayinda a ranta kuma cewa tayi.
“Tab Didi ai baki sanni bane, toh ni ko ciwo ma ai bai hanani cin abinci”.
Ita kuwa Rahama da sauri tace.
“Dan Allah dauki ki kai mai kada yayi bacci, in kinzo fita ki kashe min wutan nan”.
Kai Khausar ta ɗan juya tare da nufar bedroom da sauri kuma ta juyo jin Rahma na cewa.
“Nifa waya nakeson yi ke kuma kina dauke min hankali ki kai mishi mana”.
Cikin taɓe baki tace.
“Yah Salam kai Rahama wannan naci haka”.
Ta ƙare mgnar tare da juyawa ta ɗauki basket ɗin ta nufi falonshi.
Tana fita Rahama ta maida ƙofar ta rufe tare da kashe wutan kana ta dawo kan 3 sitter ta kwanta tana maici gaba da yin wayarta.
Ita kuwa Khausar a hankali ta shiga falon.
Sai kuma ta ɗan tsaya ganin baya ciki.
Da alamu tunda ya shiga bai fitoba.
Ido ta ɗan jujjuya jiyo sassayan sautin muryarsa yana karanta suratul Mulki.
A hankali ta ajiye basket din kusa dana ɗazun, sai muka ta lumshe idanun tare da buɗe su.
A hankali ta nufi ƙofar bedroom ɗinsa sabida tunowa ba abinda yaci tun safe, wanda Didi tasa ta kawo mishi ɗazunma gashi ba abinda yaci, .
Cikin sanyi ta tura ƙofar a hankali tare da kutsa kanta ciki.
“Hhhhhh Wow Yah Salam”.
Ta hade mgnar duk wuri ɗaya lokacin da idanunta sukayi arba da ƙasaitaccen ɗakin nasa da fidda wani irin amintaccen ƙamshi da sanyi mai masifar ratsa jiki da zuciya, wanda ya haifar mata da wata iriyar fitinenniyar kasalar datasa ta gaza karasowa ciki.
Ido ta zuba mishi hongoshi zaune bisa sallaya ya fuskanci ƙofar ɗakin bisa alama nanne alƙibla, wata tattausar jallabiya ce royal blue mai masifar sheƙice a jikinsa, idonta ta liƙa sumar kansa, da zata iya cewa yaune kacal karo na forko da ta ganshi babu hula, wani irin sheƙi sajensa da gemunsa zuwa gashin kan nasa suke zubawa da ƙelli.
Shi kuwa Modibbo a hankali ya ɗan ɗago idanunsa ya kalli ƙofar jin motsi alamun an buɗe ƙofar.
A hankali ya lumshe idanunsa jin numfashin sa yayi ƙasa.
Sai kuma yayi mata alamu ta shigo mana da
hannunsa.
A hankali ta kutso kanta cikin dakin.
Gefenshi ta ɗan matso tare da ɗan yin ƙasa da kanta.
Dai-dai lokacin kuma yazo ƙarshen suratul Mulk ɗin tare da shafawa, sai kuma ya ɗan juyo idanunsa da har yanzu suke a fitine ya kalleta a saman lips enshi yace.
“Yah akayi?”.
Cikin jin sanyin tayis ɗin na ratsa tafin sawunta da ba takalmi tace.
“Didi ce, ta bawa Rahama abinci ta kawo wai dan Allah kaci kafin kayi bacci”.
A hankali yasa hannunsa ya shafa cikinsa tare da cewa.
“Toh kawo min shi nan”.
Toh tace kana ta juya
Idanunsa ya liƙa bisa mazaunanta da ke juyawa kasancewar ta daure ƙigunta da igiyar rigar ya ƙara bayyana su.
Shyyyhhhhh ya fesar da sautin tare da tanƙwashe sawunshi.
Ita kuwa a hankali ta fita.
Jim kaɗan ta dawo da basket din duka biyu.
Cikin tsareta da ido yace.
“duka wannan ya zamuyi dashi”.
Tana ajiyewa tace.
“Ɗayan na dazune da na kawo maka ka ƙi cine”.
Cikin tsareta da ido yace.
“Toh ba ke bace kika sani bacci”.
Da sauri ta kalleshi sai kuma tace.
“Ni ɗin”.
Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.
“Toh zauna ki samin min”.
Zaman tayi bisa Carpet ɗin dake shinfide gaban gadon.
Sai kuma yace.
“Buɗesu mu gani”.
Toh tace tare da fara buɗe wanda ta kawo ɗazun.
Jolof ɗin Couscous ne mai masifar kyau wanda yaji Vegetables da kifi sai kuma Yan bolls da ya Sha ƙwai sai tururi suke bisa alamu kulilon masu riƙe zafine sosai sai kuma wani Bowl dake dauke da inabi da Apple.
A hankali yace.
“Rufesu, buɗe wannan mugani”.
A hankali ta jawo basket din da Rahama ta kawo yanzu.
Kular ta buɗe, wani irin haɗiyar yawu tayi ganin wata iriyar danƙwaleliyar kaza da tasha gashi na musamman sai tururi take zuba, ga Sultan chips dake zageye da ita, wanda yaji Vegetables sai wani irin fitinennen ƙamshi yake zubawa, sai kuma robar dakekken yaji dake gefe bisa Mug din dake cike da yughort fruits wanda yake ta zuba nason sanyi.
Plate ta ɗauka, tare da fara kokarin yagar kazar.
“Dagoshi duka kawai”.
Kai ta ɗago ta kalleshi da alamun duka kuma?
Kai ya gyaɗa mata, sanan nesa ta ɗago kazar dake bajewa don tayi lugub ta ajiye tsakiyar plate ɗin kana ta zagayeshi da Sultan chips ɗin kamar yadda take cikin kular fork and knife ta sako mishi gabanshi.
Tare da ɗan tura mishi plate ɗin gabanshi.
Juyowa yayi da kyau ya fuskanceta kana ya tanƙwashe sawunshi, tare da ɗan tura plate din tsakiyarsu.
“Matso muci”. Ya faɗi yana sa fork da knife yana ɗam saluɓe tsokokin, sai kuma ya kalleta jin tana cewa.
“Na ƙoshi”. Fuskarsa ya ɗan tsuke tare da cewa “Toh me kikaci?”. A hankali tace.
“Bana jin yunwane”. Cikin nazartan yanayinta yace.
“Ƙarya kikeyi, kuma kina sane cewa ita ƙarya haramunce, kuma kin dai san duk ƙanƙantar ƙaryar da zakimin zan gane ko”.
Shiru tayi tana ɗan wasa da yatsun hannunta ai kam tabbas ƙaryarce ta kuma tuna tabbas yana saurin gano ƙaryarta.
Shi kuwa fork yasa mata a gabanta tare da cewa.
“Kin dai ga Didi ma fork biyu tasa, dan haka matso muci”.
Kai ta kuma jujjuyawa tare da cewa.
“Nifa bazan ciba”.
Da sauri yace.
“Ko ki matso ki ci, ko kuma ki tashi yanzun nan ki shiga Bathroom kiyita kaɗe ɗanwalinki daga nan har asuba”.
Cikin tsoro ta zaro ido tare da kallonsa.
Girarsa ɗaya ya ɗaga mata tare da cewa.
“Yes ba kince a ƙoshe kikeba, ai wanda ya ƙunshi shi aikine ya dace yayi”.
Cikin sanyi ta amshi fork ɗin daya miƙa mata.
Shi kuwa bismillah yayi ya fara ci, sosai abinci yayi mishi ɗaɗi gashi ba yaji ko kaɗan, kallonta yayi a lokacin ganin yadda take jujjuya fork din yayi a lokacin da ya kai lomata na uku.
“Wai meyasa ne kike da taurin kai, kinci kin tsaya kina jujjuya manyan idanu”.
A hankali ta kai fork ɗin cikin plate ɗin ta ɗan yagi farar tsokar kazar tare da ɗan haɗawa da chips guda ɗaya.
Kana ta ɗago hannunta sai kuma ta tsaya tana jujjuyawa.
Gaba ɗaya lamarin a baƙon da ba'a zato yazo mata, wai itace zaune da Yah Modibbo yana cewa suci abinci tare.
“Ok kaɗe ɗan kwalin kike so ko?”.
Da sauri ta jujjuya kanta ganin yadda ya tsareta da idonsa, yasa ta kai loman bakinta.
Sosai yayi mata daɗi ya kuma tada tsohowur yunwar da take ƙwaƙularta.
A hankali take sarrafashi a baki kana daga bisani ta haɗiye, cikin jin daɗi ta kalli robar yajin daya miƙo mata.
“Amshi kisa yajin kici”.
Cikin ɗan sunkuyar da kai ta amsa kana ta buɗe robar tare da baɗa yajin a gabanta.
Cikin tsinkewar yawun ta fara ciki.
Shima cin yakeyi wanda tuni yaci kusan rabin kazar da Chips din.
Goran ruwan dake gefenshi ya dauka ya ɗan sha kana yaci gaba daci.
Saida yaci rabin kana, ya janye hannunshi.
Sai kuma ya kalleta ganin tun ɗazu data ajiye fork din Bata kuma ɗaukaba gane kallon da yake matane yasa tace.
“Na ƙoshi fa”.
Kai ya jinnina dan yaga ta ɗanci mai ɗan dama, sai kuma ya ja Mug ɗin nan mai cike da yughort fruits, a ƴan madai-dairan bowl dake cikin basket ɗin ya zuba tare dasa tea spoon a cikin, miƙamata ɗaya yayi kana ya fara shan nasa.
Jujjuya tea spoon din tayi, sai kuma ta ɗan ɗiba ta kai bakinta.
Wow tace a ranra jin yadda ya wadatu da Banana da kuma Apple tare da inabi sai ɗan gogeghiyar kwakwa, ga gardin Yughort da madarar gongoni.
Kallonshi tayi ganin ya gama shanye nashi ya aje bowl din sai kuma ta kalli natan ga mamakinta itama ta shanye,
Mug din ya miƙata, tare da cewa.
“Sha da kyau ƙarbi wannan ɗinma”.
Ai kam ba musu ta ƙarɓa tana ɗan tura baki Allah ya sani bazata iya barin shiba.
Juyewa tayi kana ta fara sha.
Sassayan gyatsa tayi tare da gyara zamanta.
Shi kuwa Modibbo dake cije da lips in na ƙasa yana maiyi mata wani irin kallan mayata yana mai jin zuciyarsa na raɗa mishi gudurin tabbatar da aurenshi, Allah ya sani bazai iya jumrewa abinda yakeji ba, yanajin muradin tabbatar da ita a matsayin matar da J ɗinsa yayi mishi zaɓi haka nan yakeji bazai iya jumre wannan yanayin na yau ɗinba.
Ita kuwa tattare plete din tayi da Bowl din ta zuba a basket ɗin kana ta yunƙura tare da miƙewa dasu a hannunta ta nufi ƙofar fita.
A hankali yace.
“Ki kawo min phones ɗina”.
Toh tace kana ta fice, jim kaɗan kuma ta shigo, tare da miƙa mishi woyinsa da hannunta na dama yayinda ta maida hannun hagunta kuma baya.
Amsa yayi tare da cewa.
“Bani wanda kika ɓoyen”.
Cikin kwaɓe fuska tace.
“Waya tace fa”.
Ido ya zuba mata cikin subcewar mgnar ya tsinci kansa da faɗin.
“Dake da wayar ai duk nawa ne”.
Baki ta ɗan tura tare da ƙara maƙe hannun a bayanta.
Miƙewa tsaye yayi tare da cewa. “Baneeyhh”.
Da sauri ta miƙa mishi tare da ɗan jan baya ganin yadda ya matsota.
Amsar wayar tata yayi tare da ajesu kan bed side drower, kana yace.
“Shiga nan kiyi al'wala kizo”.
Ya ƙare mgnar yana nuna mata Bathroom inshi.
Cikin sauri tace.
“Nayi sallah fa”.
Fuska ya kauda gefe tare da cewa.
“Na sani ai kije kiyi al'wala nace ko”.
Kai ta ɗan langwaɓar cikin rashin fahimtar manufarsa tace.
“Ina da al'wala”. Kai ya gyaɗa kana yace.
“Ok to shiga ki kuskure bakinki”.
Toh tace kana ta shiga Bathroom ɗin.
Shi kuwa ƙofar bedroom ɗin yaje ya rufe tare da zare key ɗin yasa a aljihunsa.
Tana fita shima ya shiga ya sabunta al'wala.
Yana fitowa ya ƙara fesa turaren wanda al'adarsa ce in dai zaiyi salla sai ya fesa turare.
Kan salla ya tsaya tare da cewa.
“Bismillah”.
Kai ta ɗan jujjuya tare da cewa.
“Banda hijabi”.
Da yatsarsa ya nuna mata gyalen after dress din jikinta tare da cewa.
“Ki rufu dashi”.
“Toh ai ni nayi salla ma fa”.
Cikin kauda kai yace.
“Eh na sani ai zamu ƙara ne dan samu lada mai yawa, ko bakya son ƙarin ladan?”.
Kai ta ɗan jinjina kana tace.
“Ina so mana”.
Da hannun ya nuna mata alamun to muyi salla.
Toh kawai tace kana ta dawo bayanshi kaɗan.
Tsayuwarsa ya gyara kana ya tada iƙama.
Nafila sukayi raka'a biyu.
Bayan sun sallamene ya ɗanyi tasbi, yayinda ita kuma take karanta Addu'o'i kwanciya bacci a lissafinta daga ta koma ɗakinta sai kwanci.
A hankali ya juyo gareta wanda hakan yasa suka kasance gab da juna, kusan a tare zuƙatansu ke bugawa, da sauri ta ɗan ja da baya.
Shi kuwa Modibbo cikin nitsuwa ya ɗan kauda kanshi tare da ƙara matsota har guiwowinsu na gogan juna, ganin tana kuma ƙoƙarin matssawane ya ɗan juya fuska ba sauƙi kuma ba zafi yace.
“Tsaya mana”.
Ya ƙare mgnar tare da ɗaga hannunshi na dama tare da ɗaurawa kan goshinta zuwa saman kanta kaɗan ya riƙe da babbar yatsarsa na kan jijinyan gefen goshinta na dama sai kuma yatsarsa ta tsakiya dake kan jijiyar kanta na hagu.
“Hhhhhhhm”. Ta fidda sautin daga ƙasan zuciyarta sabida wani irin yam taji tsikar jikinta da zuciyarta sun amsa a tare.
Shi kuwa Modibbo lumshe idanunsa yayi sabida yadda yaji jijiyar goshinta na harbawa haka yaji A ɗinsa ya harba da masifarƙafi hankali ya fara karanta Addu'ar da Manzon Allah ya koyarwa maza danyi a dararen forkonsu.
*“Allahumma inni As'aluka min khairi ha wa khaira ma jabaltaha alaihi, wa a uuzu bika min sharri ha wa sharra ma jabaltaha alaihi".*
Ma'ana
"Ya Allah ina roƙon ka Al'khairin ta, da Al'khairin da ka Halicce ta akan shi.
Kuma ina neman tsarin ka daga Sharrin ta, da kuma sharrin da ka Halicce ta da shi ko akan shi.
Amfanin Addu'ar
Idan ka yi ta.
Allah zai cike Soyayyar da ke tsakanin ku 100%. Zai tsare Shaiɗanu da Miyagu daga cutar da zaman Auren ka da ita da sauran su...
*Iyaye muke koyawa yayanmu maza ita musamman in sun tasa dan tana da mahimmanci a rayuwar aure kuma mazan ba kowa ya iya ba*
A hankali ya koma baya kaɗan ya jingina da jikin gadon,.
A hankali ya buɗe idanunsa da ke lumshe tare dasa hannunsa ya ɗan jawo bowl ɗin fruits din dake gefenshi sai kuma ya ɗan kalleta ganin alamun zata miƙe yace.
“Ina zakije?”.
“Zan tafi in kwanta bacci nakeji”.
“Zo ki zauna kiyi karatu tukuna inji bitar haddarki”.
Da sauri tace.
“Ai ina muraja'a a gida”.
Ba tare da ya kalletaba yasa hannunsa na dama ya riƙo hannunta tare da jawota, dole ta zauna gefen damanshi.
Shi kuwa Modibbo a hankali ya ɗan murza tafin hannuntan dake cikin nasa kana a hankali yace.
“Bismillah kiyi muji”.
Ɗan sunkuyar da kai tayi kana tace.
“Nifa bacci nakeji”.
Matse hanun nata yayi da ɗan ƙarfi har saida ta ɗanyi ƙara.
Hararanta ya ɗan yi tare da cewa.
“Yaushe makika tashi a bacci, baccin awa huɗu cib fa kikayi, dan haka ba bacci ba kam sai dai ko tunda kuka gama makaranta kin daina muraja'a ko? Shiyasa kike tsoron yi”.
Da sauri tace.
“Wlh inayi fa”.
“Toh kiyi mu ji, in kin bata ki ƙwana kaɗe ɗankalinki”.
Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa kana tace.
“Wacce surar zanyi maka?”.
Yana ɗan matse cinyoyinsa yace.
“Suratul Khaf”.
Cikin sauƙe numfashi ta ɗan yi gyaran murya tare da yin basmala kana ta fara jam ayoyin”.
Wani irin amintaccen nitsuwa salama haɗida shauƙi mai zafine ya fara ziraro mishi, wanda hakan yasa ya ɗan ƙara matsota da kyau, ita kuwa cikin fesar da numfashi taci gaba da kawo aya ta uku.
“مكشين فيه ابدا.
Sai kuma ta ɗan yi shiru tare da jan numfashi, tana mai jin wani irin