Showing 186001 words to 189000 words out of 218703 words

Chapter 63 - Sakayyah 2 Hausa Novel Complete

murya tayi cike da shagwaɓa tace.
“Ayyah ka barni in kwana mana”.
Still yi yayi kamar bai jita ba ya ma Mai da kallonsa kan Momy yace.
“Momy zamu tafi dare yayi”.
Kai Momy ta gyada tare da faɗin.
“Allaj ya bamu Alkhairi ku gaida su Didi”.
Cikin sauri da lumshe ido Khausar tace.
“Dan Allah kabarni in kwana mana”.
Juyawa yayi ya kalleta kana ya kalli Momy da tayi shiru alamar tana son ƴartata ta kwana.
Har ga Allah baison barinta ta kwana amma ganin yanda Momy tayi shiru tana Murmushi yasa shi kallon Khausar data langwaɓar da kai da kuma yanda akace tana cin abinci yasa shi fesar da numfashi tare da faɗin.
“Shikenan zo muje ki rakani”.
Da sauri ta ɗan ware idanunta tace.
“Kenan ka barni in kwana?”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Eh ba damuwa amma muje in Baki saƙo amota”.
Cike da farin ciki tace.
“toh”.
Kana ta miƙe tabi bayansa.
Cikin tsananin jin daɗi momy ta rakasu da ido domin ta samu cikekkiyar gamsuwa akan mutumunci da kulawar Modibbo da iyayensa akan ɗiyar tata.

Mazaunin Driver ya zauna yayin da ta zauna gefen mai zaman banza janyota jikinsa yayi kana ya ɗaura hannunsa akan cikinta tare da faɗin.
“Minha bana son barinki ki kwana awani waje batare dani ba amma yanda kika nuna agaban Momy ba yanda zanyi”.
Cikin sanyi tace
“Kayi haƙuri Yah Mu'allim nayi kewar Momyne”.
Cikin lumshe idanu yace.
“Shikenan ba komai”.
Ya ƙarashe maganar yana ɗaura hannunsa akan cikinta ahankali tace.
“Kayi haƙuri ”.
Kai ya girgiza tare da cewa.
“Bakomai”.
Cikinta yake shafawa kafin ya buɗe tafin hannunsa ya karanta _Ƙulhuwa³ Falaƙi³ Naasi³ Ayatulkursiyyu¹ Amanarrasulu ¹ Laƙadja'akum¹_ ya shafa mata cikinta tare da faɗin.
“Toh Allah ya kare ki ya kare min Babyna saboda banason Maƙwabtakanki da Hajiya Bunayya tsoronta na keji akan abinda tace ta miki”.
Kai ta girgiza tana sake lafewa jikinsa tace.
“Bakomai in Sha Allahu ba abinda zai samemu tunfa addu'o'inka na tare damu”.
Cikin sanyi yace.
“Dan Allah Minha kada ki kwanta bakiyi alwala ba kuma kiyi addu'a Kinga Bama tare bare inyi miki”.
Cikin shaƙar ƙamshin jikinsa tace.
“In sha Allah zan yi kuma Momy nayi min yadda kake min”.
Cikin jin gamsuwa yace.
“Ayyah Mommy Allah ya bar mana su ”.
Amin. tace tana shafa sajenshi.
Bayan sun sake taɓa hira ya rakata har ƙofan Falon Momy sai da ta shiga kana ta juya ya koma.

Ita kuwa Momy hannun Khausar ta kalla.
Ummmmm tace saboda ganin ba wani saƙo kawai so yake ya kebe da matarsa fahimta haka ya sata mgnar.
“Uhmmm kaddai in shiga haƙƙinshi shi da matarsa”.
Sai kuma ta kalli Khausar dake matsar da Raudat gefe tare da kwantawa kusa da Momy tana cewa.
“Yau dai ke zaki koma gefe ni zan kwanta kusa da Mommy na”.
Murmushi Momy tayi tare da cewa.
“Je kiyi alwala tukun”.
Toh tace kana taje tayi alwala kana tazo ta kwanta nan sukayi ta hira.

Washe gari bayan an idar da Sallar Asbah duk su Abualeey sun koma gida.

Moddibo kuwa karatun ƙur'ani ya fara daga bisani yayi Azkhar.
Takwas dai ya miƙe ya nufi gida.

Har ya nufi bedroom ɗinda sai kuma ya fasa key ɗin motarsq dake kan Dinnin table ta ɗauka, kana ya fito kai tsaye mota ya shiga.

Tare da nufan gidan Momy haka nan yake ji yayi mugun missing ɗin ta ji yake kamar ya ɗauki wasu kwanaki bai ji ɗumin baby nai ba.

Yana Parking motar aharabar gidan ya hango Haiydar da Bashir wanda yanzu ya dawo gidan da kwana saboda baƙin da suka cika gidansu.
Suna ganinsa suka isa wajensa tare da cewa.
“Yah Moddibo Barka da safiya”.
Cikin sakin fuska yace.
“Yawwa Haiydar Barka dai”.
Su Haiydar ne sukayi nasa jagora zuwa Falon Lamiɗo bayan sun gaisa Lamiɗo yace.
“Nima yanzu nake shirin zuwa wajensu Abualeey”.
Anutse Moddibo ya ɗan sunkuyar da kansa ƙasa tare da cewa
“Ayyah ai suna na tare da Abban Jameel ma da Malam Ahmad”.
Kai Lamiɗo ya gyaɗa tare da kallon su Haiydar kana yace.
“Ku isa dashi”.
Kai suka gyaɗa tare da fita kana ya miƙe yabi bayansu.

Dai-dai lokacin kuma Momy na kitchen.
Yayin da Khausar ke kwance kan 3sitter.
Suna isa bakin Falon Haiydar ya kalli Moddibo tare da faɗin.
“Yah Moddibo ka shiga ”.
Kai ya gyaɗa kana yace .
“Ok”.
Sai kuma ya kalli Bashir tare da cewa.
“Ina zakujo”.
Cikin shaƙuwa Bashir yace.
“Adda Asma'u ce ta matsa mana da kira wai muje mu amso mata ɗinkunanta”.
Kai jinjina musu, daga nan ya nufi cikin ɗakin.

Kana suka juya da alamu aikan zasu tafi.

Ahankali Moddibo ya shiga Falon bakinsa ɗauke da sallama.

A hankali ya lumshe idanunsa kana ya buɗesu sabida hango Khausar kwance bisa 3 sitter. Falon shiru ba kowa sai sassayan ƙamshi da sautin TV can ƙasa da ake addu'o'in azkar.

A hankali idanunsa suka suke yawo a kanta tana bacci cikin kwanciyar hankali wanda ga duk kan alamu tana jin dadin bacci..
Sai kuma plate dake gabanta da cup wanda ke da guntun tea a ciki sai plate ɗin dake da alamun indomei ne taci a ciki kafin tayi baccin.

Anutse ya ƙara sa tsakiyar Falon tare da zama agefenta daga ƙasa ahankali ya ɗaura hannunsa dai-dai kan fuskarsa kana yasa babban yatsansa kan gashin girarta ya kwantar.
Ahankali ta fara jin alamunsa akusa da ita yayin da take zuƙan ƙamshinsa ahankali ta buɗe ido ta kallesa fuskar ya shafa cikin wata sanyayyar murya yace.
“Barka da safiya me kyau ko Babu kwalliya”.
Idanunta ta sake lumshe jin yanda sautin muryansa ya ratsa ainihin ƙoƙon zuciyarta.
Moddibo kuwa ahankali ya kamo tafin hannunta tare da ɗaurawa asajensa kana ya motsa laɓɓansa tare da cewa.
“Na kasa juriya rai kin ka kwana tun jiya”.
Da wani irin sauri Khausar ta damƙe hannunsa dake cikin nata jin wani irin nutsuwa da farin ciki. cikin nutsuwa da zaƙin muryansa ya cigaba da faɗin.
“Ko rufe ido nayi kece kaɗai nake gaaaani kin wadaci zuciyata ba wacce zata rarrafo”.
Hannunsa ya mayar kan lips ɗin ta yana shafawa ya cigaba da cewa.
“Tattalinki zan kamar ya ƙwai”.
Cikin jin daɗi ta matso da kanta ta ɗaura asaman tafin hannunsa cikin tarin ƙaunarta ya kashe mata ido ɗaya tare da cewa.
“Duk abinda kin kaso akwai, babu wacce zata ji da kai gareni dan ni ina da Gimbiya”.
Da hannu ta nuna kanta alamar Ni ya gyaɗa mata kai yana shafa sumar kanta yace.
“In kiraki Layla ne ko Majnuniya”.
Ahankali ta ɗan mike tana jin wani irin farin ciki da nutsuwa yayin da wani irin ƙaunarsa ke fusganta ganin yanda ta kwanto jikinsa ya sanya shi kuma ahankali ya janyota tare da rungumeta tare da man....





By
*GARKUWAR MARUBUTA*
Tallah !! Tallah !!

Shahararriyar Marubuciyar nan Ikilima Adam (kyauta daga Allah) wacce ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *Kanwata* *kaikajawa kanka , *Rai daya janzaki*.
Yau na sake dawowa domin Domin tallata muku Littafaina mai Suna *(RUDANI )* Da kuma *Makauniyar Shari'a* littafine mai kunshe da Butulci , cin amana ,zagon Kasa , soyayya irin ta gani kasheni , aminci da saura n su basai n'a cika Ku da surutu ba Hausawa sukace Gani yakori ji.

Karku Manta *Makauniyar Shari'a* sabon littafi ne mai bibiyar Ma'anar sunan sa.
Ya zarce duk littafai na , na baya.
RUDANI littafine mai cike da Rudani da ban Al'ajabi , duk wacce kika fi buƙata zaki biya kudin sa Naira ɗari biyar kacal.

Farashin kowannen su Naira Dari biyar ne 500 kacal
Domin Karin bayani Ku tuntubeni a lambata kamar haka (09069080725 ko Kuma + 22953726162 ) wacce Bata shirya Siya ba kada mu batawa juna lokaci.
Domin aikawa da kudi kai tsaye . 3115484026 ikilima Adam first bank
Turo shaidar biya akan wannan 09069080725 sai najiku.


Ahankali ya shaƙi ƙamashin jikinta tare da kallon plate da cup dake gabanta wanda da alama akwai abinda taci kafin ta bin ba ba kwanta.
A dai-dai lokacin kuma Momy ta fito daga Kitchen idanunta suka sauƙa akan Moddibo dake zaune a hannun kujeran Khausar na zaune gefensa ta manna kanta da kafaɗarsa yayin da hannunsa ɗaya ke bayanta yana shafawa ganin haka yasa Momy saurin komawa kitchen.

Ahankali Moddibo ya ɗago kansa tare da kallon ƙofar Falon jin sautin muryan da ko agigin bacci ya farka zai gane ta muryan Hajja Nana.
Khausar kuwa cikin yanayin baccin da take ji ta buɗe idanunta ta kalli Hajja Nana sai kuma ta maida idanunta kan Moddibo ahankali ta sake maida idanunta kan Hajja Nana tare da cewa.
“Da sassafen nan?Wannan wani irin sammako kika yi?”.
Cikin sauri Hajja Nana ta kallesu tare da faɗin.
“Toh ƴar nema wato karota ma kike yi?,Ni ina nan tunda kuka zo na gaza bacci ina ta begenki ina son ganin ki shiyasa ana fitowa masallaci nace wa Baffa Liman da Abba su kawoni amma shine kike cewa nayi sammako toh ai ba gidanki naje ba sai ki bari idan gidanki naje kiyi min iyaka da zuwa”.
Murmushi Moddibo yayi kana yace.
“Toh ki zauna mana kina tsaye”.
Kai ta gyaɗa tare da ƙarasawa tsakiyar falon madadin ta zauna kan kushin sai ta zame ƙasa ta zauna tare da kamo ƙafafuwan Khausar ta fara jan yatsun sai kuma ta maida idanunta kan cikinta cikin mamaki ta riƙe haɓa tare da faɗin.
“Ohhh Allah mai iko, Allah mai kyauta da daɗi”.
Sai kuma ta maida kallonta kan Moddibo.
Moddibo kuwa kansa ya ɗan jujjuya kana ya juya ƙwayar idanunsa sai kuma ya sanya hannunsa na dama ya shafa sajensa ya fahimci kallon cikin Khausar yasa take yi masa kallon irin sannu. Jarabebbe mayatacce har ka ɗirka mata ciki? fahimtar hakan yasa ya kauda kansa.
Hajja Nana kam ganin yanda ya jujjuya idanunsa yasa ta jinjina kai tare da faɗin.
“Hmmm Allah Ubangiji ya shirye ka ke kuma Allah ya sauƙeki lafiya”.
Cike da kunya Khausar ta sake manna kanta da kafaɗan Moddibo kana ta motsa laɓɓanta ta furta.
“Ameen”.
Cikin ɗan ɗaga sautin murya Moddibo yace.
“Amin Amin Ameen ya Allah, Allah ya amsa addu'ar ki mun gode da addu'a”.
Kallonsa tayi tana mamakin yanda zamani ya sauya sukam a zamaninsu ko kusa da makamancin wannan ba'a yi ga yadda ya wani ƙwaƙumeta a farkon surka.

Momy dake kitchen kuwa jiyo kaman muryan Hajja Nana yasa ta leƙo.
Ganin tabbas Hajja Nana ce yasa cikin sauri ta fito tare da cewa.
“A'a Hajja Nana, dama naji kamar Muryar ki na dan kasa kunne ashe dai ke ɗin ce”.
Murmushi Hajja Nana tayi kana tace.
“Wallahi fa tun randa mukayi waya kika cemin tazo nake ta son zuwa washe garin ranan kuma Mashin ɗin Abba ya samu matsala shine malam Liman yace na bari sai yasa mai a mota kafin muzo, tunda zai zo ya marabci su Abualeey yanzu ma tare muke suna falo da Lamiɗo”.
Kai Momy ta gyada tare da faɗin.
“Kai Masha Allah sannun ku da zuwa.
Ahankali Moddibo ya juya da naiyyar gaisheta
Sai ya ga har ta shige kitchen Momy kuwa already ta gama haɗa breakfast Sultan Cheaps ta soya wanda yaji Vegetables da naman rago mai laushi sai kuma Ƙosai data soya wanda keta tururi wanda Khausar ce tace tana so sai kuma Koko wanda duk zaɓin Khausar ne sai kuma tea dake ƙamshin Kanunfari, Citta Na'a'na'a ta fito dasu.
Anutse. Moddibo ya sunkuyar da kansa kana yace.
“Momy Barka da safiya".
Cike da kulawa tace.
“Barka dai Moddibo ka iso?”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Eh Momy ina kwana”.
“Lafiya lau Alhamdulillah ya gida”.
Kallonta ta mayar kan Khausar tace.
“Ki tashi ki samu ku abinci kuci”.
Juyawa Khausar tayi tare da kallon Momy kana tace.
“Momy kinyi min ƙosan?”.
Kai Momy ta gyaɗa cike da tarin ƙaunarta tace.
“Nayi miki mana ai dole na inyi miki”.
Hajja Nana dake cigaba da matsawa Khausar Kafa tayi dariya tare da faɗin.
“Aikam dole kiyi mata naga abin na musamman ne”.
Baki Khausar ta ɗan tura tare da hararan Hajja Nana kana ta ɗan janye jikinta daga na Moddibo wanda shi har ga Allah yama manta Momy na wajen jin ta ɗan matsa ne yasa ya kalleta.
Ganin yana kallonta yasa ta juya mishi ido alamar yaga Momy na nan.
Fahimtar hakan yasa ya gyara zama sai kuma ya zame ya zauna akan tattausan Carpet ɗin ya zamana suna fuskantar juna yayin da Hajja Nana ke gefensu.
Kulan farkon ta jawo ta buɗe idanunta suka sauƙa akan ƙosan dake zuba wani irin tururi da ƙamshi ajiyar zuciya mai sanyi ta sauƙe irin yanda duk wata mai ciki keji asanda ta samu abinda take so.
Flaks din dake gefe ta jawo ta buɗe sai taga tea.
Fuska ta kwaɓe kamar za tayi kuka tace.
“Momy kunun fa?”.
Momy na ƙoƙarin janyo Flaks din gabanta tace.
“Gashi nan ki buɗe mana ki gani ke kina da ci da zuci”.
Ɗan Murmushi tayi kana ta buɗe tare da cewa.
“Kai Momy Ubangiji Allah yabar min ke Allah ya miki Albarka Ubangiji ya miki sakayya da gidan Aljanna”.
Murmushi momy tayi tare da faɗin.
“Ameen ya Allah Mamana”.
Murmushi Hajja Nana dake gefe tayi kana ta kalli Khausar sai kuma ta kalli Momy ahankali tace.
“Ubangiji Allah ya rabaku lafiya”.
Cikin sanyi Khausar tace.
“Ameen”.
Moddibo kuwa fuskarsa ɗauke da murmushi ya gyara zama tare da cewa.
“Ameen ya Allah aini ina ga yau tukuici na musamman zan banki tunda kika zo kike mana addu'a da fatan Alkhairi ”.
Baki Hajja Nana ta taɓe tare da cewa.
“Allah yasa dagaske kake”.
Cikin tabbatar wa yace.
“Dagaske nake mana ai ina ga ke tare zamu tafi dake kiyi ta mana addu'ar nan sannan kiyi ta kula mana da ita”.
Ɗan zare idanu Hajja Nana tayi kana ta hararesa tace.
“Kunyi ƙarya nikam bazan zama mai aikin kuba kuda gacan innare kuna tare da ita ai magana ta ƙare duk kular da kuke buƙata zaku samu”.
Kai ta jinjina kana tayi Murmushi tare da faɗin.
“Aikam itama munzo dasu jiya ma take cewa tana son zuwa wajen ki sai Khausar ke cewa ai kema zaki zo shiyasa bata jeba”.
Ɗan gyara zama Hajja Nana tayi tare da faɗin.
“Aikam toh shikenan”.
Khausar kuwa ƙosai ta zuba kusan guda goma kana ta zuba Kokan sai kuma ta zuba wa Moddibo Sultan Cheaps da Perpe Chicken mug ta ɗauka ta haɗa masa tea mai kauri.

Hajja Nana ma ƙosan Khausar ta zuba mata tana kallon ƙosan da yayi kyau a ido ta kalli Momy tace.
“Ƙosan ya isa haka, asamin shayi sai ahaɗa min da biredi”.
Kai Momy ta gyaɗa kana ta miƙe ta ɗauko Bread Mai yanka-yanka Karɓa Hajja Nana tayi ta shiga haɗa breading, ƙosai da tea tana sha.
Khausar kuwa Ƙosai da Kokon ta shiga sha cikin tsananin mararin abin.

Ahankali ta gutsiri Ƙosan da cikin tsakiyarsa ke ɗauke da diddigin nama kana ta kuma kurɓan kokon daya sha kayan ƙamshi yawun bakinta sai tsinkewa yake saboda yanda ya mata masifar daɗi.

Moddibo kam cike da mamaki yake kallon yanda Khausar ke cin ƙosai da Koko tsakaninta da Allah.
Hajja Nana dake kai biredi da Ƙosai baki ta kalli Moddibo daya zubawa Khausar idanu yana cew.
“Ni mamaki nake bata cin abinci fa agida”.
Murmushi Hajja Nana tayi tana kallon yanda Khausar ke shan Koko tsakaninta da Allah tace.
“Ai dama haka wani yake in dai yana da ciki baici agidansa amma da zaran yaje unguwa zai ci abinci”.
Kansa ya girgiza tare da cewa.
“To ai can ko munje gidan Lalla Khadijah bata cin abinci amma kinga tunda muka zo nan cin abinci fa takeyi”.
Momy dake fita zata kaiwa Abba da Man Liman nasu tayi Murmushi tare da faɗin.
“Sosai ma kam tunda aka zo nan abinci take ci babu kama hannun yaro taci ta ƙara ɗayan daren ma munyi hira mun gama tace min yunwa take ji sai da naje na dama mata Quaker oats tasha kafin tayi bacci”.
Cike da farin Moddibo ke sakin murmushi yana kallon Khausar dake ɗan Cunno baki gaba Momy kuwa idanunta akan Hajja Nana ta cigaba da cewa.
“Sannan da safe kafin ta kwanta plate da kuka zo kuka samu shima indomei taci tasha tea kafin ta kwanta tayi bacci anan gashi yanzu ma tana ta ɗurawa”.
Langwaɓar da kai Khausar tayi tare da faɗin.
“Toh Momy yunwa nake ji na daɗe bana cin abinci fa”.
Dariya Momy tayi kana tace.
“Keee dama haka kike da cin abinci nayi mamaki ma da akace wai ciki ya hanaki cin abinci.
Don banyi tunanin akwai abinda zai hana ki cin abinci ba, tunda ke ciwo ma baya hana ki cin abinci”.
Kanta ta sunkuyar ƙasa ta cigaba da cin ƙosanta kallonta Moddibo yayi ganin ta gama cinye duk ƙosan hannu tasa ta sake janyo kular ɗan ware idanunsa yayi tare da faɗin.
“Minha bazai Miki yawa ba?”.
Kallonsa tayi sai kuma ta girgiza kai tace.
“Um-um kaɗan zan ƙara naji cikina ya ƙoshi amma bakina bai gaji dashi ba”.
Yana rufe kulan yace.
“Toh ki bari sai anjima”.
Marairaice fuska tayi ganin haka yasa Momy cewa.
“Ki bari na rage Miki ƙullu a fridge idan kina so anjima zan sake soya miki ”.
Gyatsa tayi kana ta gyaɗa kai tare da faɗin.
“Toh shikenan”.
Ta ida maganar tana jingina bayanta da jikin kujera.
Ahankali Moddibo ya matsa kusa da kujeran da take ya ɗan jawota jikinsa tare da cewa.
“Zo, Zo zonan kada ki kwanta, ki ɗan zauna tukun mu samu abincin yabi jikinki”.
Ya faɗa yana manna kanta da kafaɗarsa yayin da hannunsa ɗaya ke kan cikinta yana shafawa shi kuma yana cigaba da cin abinci da hannunsa na dama.
Ahaka suka gama cin abinci suna taɓa hira jefi-jefi.

Suna gama cin abinci Momy ta shigo idanunta akan Khausar tace.
“Toh tashi ki tattare wurin”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Toh”.
Kana ta yunƙura zata miƙe.

Ahankali Moddibo ya kalli Momy kana yace.
“Momy bari na tattare”.
Ɗan ware idanu Momy tayi kana tace.
“Ta isa tana zaune ka tattare mata kwanika”.
Cikin sanyi yace.
“Momy toh ta gaji ne kuma ta cika cikinta da yawa bata son motsi”.
Kai Momy ta girgiza tare da faɗin.
“Aikuwa dole tayi motsi maza tashi ki tattare su”.
Ta ƙare maganar tana kallon Khausar.
Hajja Nana dake kallonsu ta ɗan taɓe baki tace.
“Kai dai kai dai kam wannan akwai ka da tsirfa iri-iri yo in Mai ciki bata motsa jiki ba mai za tayi!? Ko kaine zakayi mata naƙudar”.
Ɗan hararan Hajja Nana Khausar tayi sai kuma ta kalli Momy tare da cewa.
“Nima fa bance yayi ba shi yace zaiyi”.
Ta ƙarashe maganar tana kwashe kwanukan ta kai kitchen kana ta dawo ta zauna bayan ta dawo sun zauna Momy suka gaisa da Hajja Nana bayan sun gaisa suna cigaba da hira.
Asiya ta shigo cikin sassarfa kamar an jefota cikin yanayin tashin hankali tace.
“Momy dan Allah kizo kiga Ummana baki ɗaya yau tunda gari ya waye atsaye take bata zauna ba kona minti ɗaya fa gaba ɗaya yau jikinta ya tashi!”.
Da damuwa Momy ta miƙe cikin sauri tabi bayan Asiya suka nufi Side ɗin Hajiya Bunayya.
Khausar kam ahankali ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login