Showing 75001 words to 78000 words out of 218703 words
hannu na”.
Cikin sauri da mamaki Moddibo ya kallesa tare da faɗin.
“Abba toh a taimaka min dasu Ummi, Innayi, da Abba zasu nemini, musamman ma Innayina zata shiga damuwar rashin jina?”.
Kai Sarki Youseef Mouley ya girgiza kana yace.
“Kada ka damu In sha Allah babu komai rashin ɗaukar wayar yana da muhimmanci, da amfanin da zaiyi Kankane yace kada a ɗauki wayar shiyasa ma ban kawo maka ba”.
A ladabce Moddibo yace
“Abba zasu shiga damuwa saboda zasuji tsoro kada abinda ya faru da Jameel nima ya faru dani”.
Cike da kulawa Sarki Youseef Mouley yace.
“Wanene Jameelun naka?”.
Idanunsa ya lumshe tare da buɗewa kana yace.
“Ai wannan Dr Jameel ɗin dana biyo, da fari ina bibiyarshi a zatona J nane sabida tsananin kamar da sukayi”.
Nan ya shiga basu labarin Jameel da duk abinda ya faru dashi.
Ya ɗaura da faɗin.
“Shiyasa lokacin da naga wannan Dr Jameel baki ɗaya na ɗauka cewa Jameelu na ne saboda kamanninsu yayi yawa, hatta maganarsu, tafiyarsu, muryar su babu abinda ya raba su sai dai ɗabi'unsu ya samu bambanci dana Jameelu na”.
Cikin raunin murya da tunowa da Jameelunsa ya basu cikekken tarihin abotarsu.
Sosai suma suka tausayawa masa tare da yiwa Jameelun fatan samun rahamar Ubangji kana ya cigaba da faɗa musu cewa aikine ya kawo sa kamfanin Baban Jameelu.
Cikin fesar da numfashi Ibraahim yace.
“Allah sarki Yah Jameel Allah ya gafarta masa”.
Cikin sanyi Moddibo yace
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.
Lalla Khadijah ce ta gyara zama tare da fuskatarsa kana a mutunci tace.
“Da fari dai kaga iya mu yamune cikin mahaifiyarmu da wasu daga cikin amintattun fadane, suka san da isowarka wacce dole labarin ya bazu cikin Faɗa, to Alhamdulillah zan haɗa taro na musamman damon gabatarda kai a tsakiyar family'nka wato zuriyar sarki Aliyu Mouley, wanda zuriyace ta tun kakannin Abbanmu da kuma kakanninmu, mu da kuma iyayenmu da ƴan bappanayenmu dama goggoninmu, in Sha Allah zayi tarone na musamman dan dan haka ka shirya fuskatarta idanu mabanmanta. Alhamdulillah na gamsu da nitsuwarka zuwa yau kuma na fahimci kasan komai na tsarin al'adunmu da nake mamakin yadda akayi ka sansu”.
Da sauri Kalla Hafsat tace.
“Ke kuwa Lalla Khadijah ya za'ayi ya rayu da jakadiya kiyi tunanin akwai wata al'adar da bazai saniba”.
Murmushi Modibbo yayi domin shi dai innayi bata taɓa alaƙantashi da labarin fadaba, sai dai yasan komai na fadar ne a cikin mafarkansa.
Abualeey ne ya gyara zama tare da cewa.
“Zuwa yanzu mun gama shiryawa komai na taron”.
Haka dai sukaci gaba da tattauna lamurran.
Washe gari ranan Asabar misalin ƙarfe uku na yamma Jirginsu Innayi yayi landing a _Rabat Sale international airport_.
Suna sauƙa a airport motocine na alfarma guda biyar suka zo ɗaukar su bisa jagoranci Dr Ahmad abokin Abban Jameel.
Mota ta farko Dr Ahmad ke driving yayin da Abban Jameel ke gefensa daga can baya kuma Innayi ce tare da Hajja Nana da kuma Khausar.
Motar dake bima sa kuwa Ummi ce da Hajiya Bunayya sai kuma ƙanwar Momyn Khausar Aunty Hajara, sai Haiydar da yake gaba gefen direba.
Yayin da mota ta uku kuwa Asiya, Asma'u ce tare da Dija. Sai Aunty Ruƙayya ƙawar Mommy
Motar dake bayansa kuwa Baffa Jimeta ne da matarsa Hajiya Umma, kana da Babbar Ƴar sa mai suna Aunty Hawwa .
Yayin da motocin ke tafiya ajere cikin nutsuwa bisa Jagoranci Dr Ahmad
Bayan sun shiga cikin gari sun nufi unguwar Ben slimane, cikin sauƙe numfashi Innayi ta fesar da numfashi tare da buɗe Idanunta ta kalli cikin garin da tsarukan da kuma gine-gine suka sauya alamar garin ya sake samun cigaba fiye da da.
Cikin sanyayyar murya me cike da kewa da kuma bege ta kalli Dr Ahmad dake driving kana tace.
“Mubi ta unguwar El'gara sai mu ɓullo ta cikin Ben Ahmad dan Masarautar Rabat zamu nufa”
Cikin wani amintacciyar murmushi Abban Jameel ya juya ya kalleta kana yace.
“Kai tsaye kuma?”.
Kai ta jinjina kana tace.
“Eh can zamu nufa shine abinda yafi da cewa”
Still Idanunsa na kanta yace.
“Amma da ya kamata mu fara isa masauƙi mu huta tukunna!”.
Numfashi ta fesar tare da faɗin.
“A'a ai acan ya dace muyi hutun”.
Kai ya jinjina tare da faɗin.
“Toh shikenan”.
Shi kuwa Dr Ahmad juya akalar motar yayi, kana suma saura suma mara mishi baya.
Nan suka ci-gaba da tafiya cikin nutsuwa still motocinsu na jere.
Suna isa ƙofan Gate na farkon Masarautar Rabat ganin motoci ajere yasa cikin Sauri Hadiman dake bakin gate ɗin mutum biyar suka miƙe biyu suka tsa gefen damar motan biyu gefen hagun motar kana ɗaya ya tsaya agaba.
Cikin nutsuwa da yanayin jikin girma Innayi ta sanya hannu ta buɗe murfin motar kana ta fito yayin hannunta ke riƙe da wani abu kamar murfi kolbar Vaselin sai dai bisa ga alamu ginannene kana anyi sa da hatimin Masarautar.
Wanda ke kusa da ita ta miƙawa.
Karɓa yayi ya duba kana yayi saurin kallon fuskarta sai kuma ya juya ya miƙawa na gefensa shima ya karɓa ya duba.
Da wani irin sauri suka ɗaura hannunsu asaman ƙirjinsu kana suka sunkuyar da kansu alamar girmamawa.
Kai ta jinjina musu.
Kana cikin sassarfa suka juya tare da buɗe musu Gate ɗaya daga cikinsu ya tsaya abakin Gate yayin da sauran huɗun suka marawa moticin baya cikin sassarfa suna isa Gate na biyu ɗaya daga cikin masu binsu yayi saurin buɗe musu Gate ɗin suka shiga kai tsaye har harabar fadar suka isa, suna isa sukayi Parking atare.
Acan motarsu Hajiya Bunayya kuwa Haiydar wani irin zazzafan ajiyar zuciya ta sauƙe mai nuni da zallan mamaki kana ta kalli gabas da yamma kudu da Arewa wani irin daular duniya da suka shiga wanda ya kamata akirasa da Aljannar duniya cike da al'ajabi ta maida idanunta kan Ummi kana tace.
“Toh nan kuma ina muka zo haka”.
Lallausan murmushi Ummi ta sakar mata kana tace.
“Nan gidansu Moddibo muka zo gidan Mahaifinsa”.
Dariyar sheƙiyanci Hajiya Bunayya ta saki tace.
“Kai lallai wannan ta tsuniya yawa ne dashi nan ɗin ne gidansu Moddibo?”.
Kai Ummi ta jinjina tare da faɗin.
“Toh ki zuba ido ki gani”.
Baki ta taɓe tare da yiwa Ummi wani kallo kana tace.
“Caɓ amma Ummin Jameel banyi zaton haka daga gareki ba da girmanki”.
Ta ida maganar tare da ƙyalƙyalewa da dariya ita baki ɗaya ma maganar dariya yake bata yo ai ko amafarki Moddibo bai isa ya kasance jinin wannan ahali ba mutumin da ake kyautata zaton ɗan shegene.
Ummi kuwa da mamaki ta kalli yanda take dariya kana tace.
“Kina mamaki ne?”.
Hajiya Bunayya kuwa cikin taɓe baki tace.
“Sosai ma kuwa ai ba mamaki ba harda Al'ajabi na haɗa Moddibo fa”.
Sai ta kuma fashewa da dariyar sheƙiyanci data tuna wai Ummi tace nan gidansu Moddibo ne.
Kai kawai Ummi ta girgiza batare da tace Uffan ba tana mai bin baki ɗaya ilahirin gidan da kallo.
Acan Motarsu Asma'u kuwa cikin zumuɗi da ganin tsantsan kyawu da tsaruwan gidan Dija tace.
“Ehyeh”.
Asiya ma kallon coumpund ɗin tayi cike da shauƙi tace.
“Wowwww Masha Allah kaga wani daular duniya”.
Asma'u kuwa dogon numfashi taja tare da fesar wa tare da faɗin.
“Toh Masha Allah wannan al'amari da ban mamaki yake”.
Motocin kuwa re ras suka tsaya.
Fadawan dake tsaye bakin Fadar kuwa cikin sauri suka nufo motocin wanda aƙalla sun kai biyar isowarsu yayi dai-dai da fitowar Innayi daga motar.
Sarkin ƙofane idanunsa suka sauƙa akanta cikin sauri ya mutsi-stika Idanunsa kana ya sake kallonta sama da ƙasa cikin al'ajabi da mamaki tu'ajubi yace.
“Innare Jakadiyar Gimbiya Ruƙayya?”.
Murmushi Innayi tayi kana ta gyaɗa masa kai tare da faɗin.
“Eh”.
Duk da yawan shekaru kuwa sun gane juna
Cikin wani irin sauri ya juya tare da nufar cikin Fada yana shiga ya durƙusa agaban Sarki duk da cewa yana tare da mutane na hannun damansa suna tattauna akan al'amarin Moddibo da yanda zasu bayyanar dashi a Masarauta ga yan uwansa.
Ganin yanda ya gurfana ne yasa Sarkin zagi cewa.
“Hattara dai Sarkin Ƙofa, mene tafe da kai?”.
Cikin rawan murya tare da tsantsan farin ciki yace.
“Al'amarine mai girmane yake tafe dani”.
Duk idanu mutanen Fadan suka zuba masa ganin yanda fuskarsa ke ɗauke da tarin zumuɗin isar da labarin.
Sarkin Fada kuwa cike da kulawa yace.
“Shin wannan wani al'amari ne?”.
Aƙage Sarkin ƙofa ya sake risinar da kansa kana yace.
“Ina so abani izini ne nayiwa Innare Tsohuwar Jakadiyar Gimbiya Ruƙayya iso wacce ta ɓace tare da Alieeyu tsawon shekara talatin”.
Wani irin murmushi Sarki Youseef Mouley ya saki mai cike da zallan farin ciki da jin daɗi acikin ransa yace.
Alhamdulillah ta amsa kiranmu kenan lallai wannan ya nuna ta riƙe mana ɗanmu da amana da aminci bata kuma wofintar da al'amuran sa ba tana bibiye dashi, yanzu tsawon kwanaki biyar bataji labarinsane ta bibiyi al'amarin sa gashi ta nufo nan ne kuma da yaƙinin cewa tabbas daya shigo ƙasar nan zai dawo Mahaifarsa.
Afili kuma murmushi ya sakarwa Sarkin Ƙofa kana cike da nutsuwa da kamala kana da ƙasaita irin na sarauta ya masa alama da hannu ta shigo...
Cikin sauri Sarkin Ƙofa ya miƙe kana ya fita kallin Innayi dake tsaye jikin mota yayi tare da faɗin.
“Bismillah”.
Innayi kuwa juyawa tayi tare da kallon su Abban Jameel kana tace.
“Ku ɗan yi haƙuri ina zuwa”.
Su kuwa baki ɗaya cike da ɗumbin mamaki suke kallonta.
Cikin sauƙe numfashi Hajja Nana ta gyaɗa kai tare da cewa.
“Toh mu dai munfi karfin saiduwa, koda an kawo mu nan da za'a sayar damu ne bazamu saiduba”.
Sai kuma ta juya ta kalli Khausar dake zaune gefenta wacce idanunta suka kumbura sukayi ja jawur gashin idanu suka jiƙe yayin da suka ƙara tsayi kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar tasha kuka tamkar mai isarta cikin taɓe baki tace.
“Toh kuma kukan me kikayi tunda, ai burinki ya cika, ba dai auren wanda ba'asa asalinsa ba, ai gashi dai kinga kuma wata duniyar da aka kawo mu, ko mai za'a ce mana ko mai za'a mana kuma oho domin wannan al'amari dai yafi kama da almara”.
KhausarMouleey ya jinjina tare da faɗin.
“Ai nan Fada ce mai mutunci da karrama baƙo”.
Sake sunkuyar da kanta tayi kana tace.
“Ranka ya daɗe baƙin suna da yawa”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Koda ace baƙi ɗaya Yan yanki da kuke kika ɗebo ba zasu rasa muhalli acikin wannan Masarautar tamu ba”.
Lallausan murmushi ta saki tare da jinjina kai kana tace.
“Toh abani jagora wanda zai kai mu masauƙin baƙin namu.
Kai ya jinjina kana yace.
“Toh shikenan babu damuwa”.
Kallon Jakadiyar sa yayi tare da faɗin.
“Jakadiya Bismillah akai su sashen Yamma a saman za'a sauƙi”.
Bi'ana saman inda Modibbo yake kenan
Sake sunkuyar da kai Innayi tayi tare da faɗin.
“Ranka ya daɗe Akwai maza tare kuma damu mata”.
“Baki da matsala”.
Ya faɗa tare da kallon Sarkin Ƙofa kana yace.
“Kai kuma ka kai Mazan Ƙofan Gabas”.
Kai ya gyaɗa cike da girmamawa yace.
“Toh”.
Kana suka fice yayin da Jakadiya ta yiwa Innayi, Hajja Nana, Ummi, Hajiya Bunayya, Asma'u, Asiya, Dija, Khausar, Aunty Hawwa da Hajja Umma Baki daya bayan Jakadiya suka bi tayi musu Jagora.
Yayin da Abban Jameel, Baffa Jimeta, Lamiɗo, Haiydar suka bi bayan Sarkin ƙofa wani babban Hanya suka bi kana suka hau Upstairs
Suna haura wa saiga wasu Ƙofofi biyu ɗaya aɓarin dama ɗaya aɓarin hagu Jakadiya takai su Innayi ƙofar dama yayin da Su Abban Jameel aka kaisu ƙofan hagu ta can gefen yamma wanda bata cikin falon da Modibbo yakeba suka ɓula ba sai dai in zadu sauƙo in sunbi ta ƙofar tsaki ta cikin falon zasu bulla...
Jakadiya kuwa tana fita daga masauƙin su Innayi kai tsaye ɗakin Didi ta nufa tana shiga falon ta zube agaban Didi tare da faɗin.
“Albishir”.
Fuska ɗauke da murmushi Didi tace.
“Goro”.
Sake risinar da kai Jakadiya tayi kana tace.
“Fari ko Ja?”.
Still Didi na murmushi tace.
“Faro soll Dan ƙwalele”.
Washe baki Jakadiya tayi tare da cewa.
“Toh Innare na cikin Fadar Masarautar Mouley ta iso tare da al'umma baki, daga cikinsu akwai masu tarin kamala da Alkunya kana tazo mana da kyakykyawan furanni masu haska gida”.
Didi kuwa cikin matsanancin farin ciki da jin daɗi ta miƙe kana tace.
“Masha Allah Alhamdulillah ta ina take, muje ki kaini gareta”.
Kai Jakadiya ta girgiza cike da ladabi tace.
“Amma da kiyi haƙuri ki koma ki zauna yanzu dai, farko a fara Marabtansu da abubuwan motsa baki saboda sun ɗebo hanya sannan asanar da hadimai afara yi musu girki na musamman domin maraba”.
Cike da gamsuwa Didi ta jinjina kai kana ta kalli Hadimanta dake durƙushe ƙasa tace.
“Maza kuje ɓangaren Hadiman dake Kichen kuce maza ashirya abinci na alfarma yanzu”.
Cike da ladabi suka amsa kana suka fita.
Didi kuwa cikin wani irin farin ciki da annashuwa kana da jinjina girma da mutuntaka irin na Innayi ta kalli Jakadiya tare da faɗin.
“Maza ashirya musu drinks, Fruits, Snack's,da ɗan gashshen nama sannan akwai nono mai sanyi da kwakwa ahaɗa musu”.
Ta ƙare mgnar tare da kallon Lalla Khadijah sai kuma tace.
“Khadija keda Hafsat ku jagoranci aikin”.
Kai suka jinjina kana atake suka haɗa suka kai sashen su Innayi da kuma sashen su Abban Jameel...
Acan ɓangaren su Hajiya Bunayya kuwa tunda tashiga tangamemen Falon da yaji komai na more rayuwa take kallon komai cikin ƙunan zuciya mamaki da kuma tarin takaici....
Innayi kuwa suna zama ta kamo hannun Khausar da har zuwa lokacin take shesh-sheƙan kuka kana ta riƙo Asma'u yayin da Ummi ke biye dasu suka nufi ɗaya daga cikin ɗakin da yake 3bedrooms ne.
Ƙofar da shine na tsakiya suka shiga.
Suna shiga ta saki sassayyan numfashi tare da sakin hannun Khausar sai kuma ta zaunar da ita gefen gadon kana ta juya ta fita.
Fitanta yayi daidai da shigowar Hadimai mata suka shigo da Fruits suka ajiye cike da girmamawa suka gaishesu kana suka ce...
Gimbiya tace ayi muku sannu da zuwa sannan ga abubuwan motsa baki kuci kafin ta iso.
Godiya sukayi kana sukuma suka fice ba daɗewa suka sake dawo wasu hannunsu riƙe da drinks,wasu Snack's wasu dambun dabbi da soyayyu.
Yayin da Lalla Khadijah da Lalla Hafsat ke riƙe da wasu Bowls manya da yaji Kindirmo da kwakwa da ayaba suka ajiye.
Cikin tsura musu ido Innayi ta kalli Lalla Khadijah kana ta juyo ta kalli Lalla Hafsat.
Sai kuma ta saki murmushi gani sun ruggumeta cikin bege da kewarsu Innayi tace.
“Allah mai iko da buwaya Khadijah kune kuka girma haka”.
Sai kuma ta kalli Lalla Hafsat dake faɗin.
“Innayi ashe dai rai kanga rai, baki wani canza ba”.
Cikin mamaki dai Hajja Nana Hajia Bunayyah da dukkan su suka zuba masu ido.
Gaisawa sukayi bayan sun zauna.
Cikin kula Lalla Khadijah tace.
“Hafsat muje ko, mu barsu susha ruwa".
Kai Hafsat ta gyaɗa kana suka juya suka tafi hadimansu na taka musu.
Kana acan ɓangaren su Lamiɗo suma haka aka kai musu.
Cikin sauƙe numfashi Baffa Jimeta ya kalli Abban Jameel bayan fitar Hadiman kana yace.
“Toh Alh Bashir wannan al'amari dai da ban mamaki da kuma ɗaure kai yake toh shi wannan yaro na rasa tantance inda al'amarinsa ya nufa”.
Murmushi Abban Jameel kana ya yace.
“Nan shine gidansu Modibbo kamar yadda kakarsa ta labarta min shi ɗan wannan ahlin ne, gidansu ne kuma tsatso kuma jigo sannan kuma tushen sa mahaifarsa kenan”.
Kai Baffa Jimeta ya gyaɗa cike da gamsuwa yace.
“Ikon Allah wannan al'ajabi da yawa yake,ita kuma daga wannan ƙasa ta tashi ta koma Nigeria har Lungunmun can taje ta zauna dashi.
wannan wani irin al'amari ne yasa ta ficewa daga nan ta koma can”.
Zazzafan ajiyar zuciya Abban Jameel ya sauƙe kana ya gyara zamansa tare da cewa.
“Al'amarine mai girma mai kuma ban mamaki”.
Numfashi Lamiɗo ya fesar wanda tunda aka fara magana bai ce komai ba ya muskuta kana yace.
“Ai wato sha'ani Masarauta sai ahankali idan bakayi Sa'a ba sai a saubata maka rayuwa! A banza”.
Abban Jameel na taunar Inabi yace.
“Hakanne ma yaso kasancewa shiyasa ta gudu da Moddibo domin tseratar da rayuwarsa”.
Baffa Jimeta na kurɓan drinks Mai sanyi yace.
“Allah mai iko”.
Daga nan kuma sai suka rufe maganar tare da cin kayan maƙulashen da aka kawo musu bayan sun gamane Dr Ahmad da sauran masu jan motocin suka sakkamesu suka tafi.
Ɗaya daga cikin Hadiman dake sashin ne ya shigo cike da ladabi ya kallesu kana yace.
“Ga banɗaki sannan ga ɗakuna akwai duk wani abin buƙata da zaku buƙace”.
Murmushi Lamiɗo yayi kana yace.
“Mumgode”
Daga haka ya juya ya fice.
Bayan awa ɗaya, sun ci sun sha Hajiya Bunayya ta kalli Hajja Nana dake goge baki da Tissue tace.
“Wannan al'amari dai da ɗure kai yake”.
Cikin taɓe baki Hajja Nana tace.
“Toh Ni dai fatana dai Allah yasa basayar damu akazo yi ba ehee”.
Dariya mai sauti Innayi ta sanya ganin yanda Hajja ke magana tsakaninta da Allah cike da kamala tace.
“Babu Sai dawa sai karramawa wanda gadon mune, kuma ma in banda abinki a saidaku a nemi me, ki dai dubafa duk wata ɓukata da ɗan Adam yake dashi muna dashi a masarautarmu”.
Ummi kam murmushi kawai take, dan talura Hajja Nana da innayi har yanzu ba'a shiryaba.
Suna cikin haka sukaji sallama, tare da ganin jagorancin Hadiman Didi
Cike da zaƙuwa ta tashigo tare da Jakadiyar ta da kuma Kakar Moddibo Niyna sai kuma su Rahama bakinsu ɗauke da sallama.
Innayi na ganin Didi tayi saurin miƙewa tare da durƙusawa agabanta kana ta sunkuyar da kanta ƙasa batare da tace Uffan ba.
Didi kuwa cikin yalwataccen farin ciki ta tsugunna tare da sanya hannunta akafaɗar Innayi kana ta ɗagota ta tsayar da ita suna fuskar juna, sai kuma kawai ta ruggumeta tare da faɗin.
“Kin gama min komai Innayi kiyi min duk kan abinda ɗan Adam zai yiwa abokin zamansa na halacci, daga yau na ƴan taki kin tashi daga Baiwa kin zama ƴa ƴan tacciya kuma Uwa amintacciya kuma kamila kuma cikekkiyar jakadar sarki mai jirangado”.
Dariya mai sauti Innayi ta sanya wanda ke nuni da zallan farin ciki kana tace
“Alhamdulillah Nagode wa Allah ina tahowa zuciyata na tsinkewa ina tunanin shin ya rayuwa ta kasance shin ana raye ko kuma anbar duniya zuciyata ta cika da fargaba”.
Baki ɗaya mutanen falon kallonsu suke cike da tsantsar mamaki musamman Hajiya Bunayya da wani irin zufan hasada ke fita agoshinta.
Innayi kuwa cike da annashuwa ta cigaba da faɗin.
“Amma Alhamdulillah nayi katari da Youseef akan karagar mulki kana kema nayi katarin dake acikin shigar Gimbiyya amma banga Ubangida naba Sarki Muhammad Aliyu Mouley”.
Kai Jakadiya ta girgiza kana tace.
“Allah yayiwa Sarki Muhammad rasuwa yanzu ɗanki ne Youseef akan Mulki”.
Cikin sanyi Innayi tace.
“Allah sarki, Sarki Muhammad Mouleey. Ubangji Allah yajiƙan sa da Rahma”.
Amin suka amsa a tare,
Ita kuwa innayi juyawa tayi tare da kallonsu Hajja Nana da suka zubo musu idanu sai kuma ta maida idanunta kan Didi tace.
“Yanzu dai idan na fahimta Moddibona Aliyuna shine Yariman Masarautar nan? kuma Sarki Mai Jiran gado?”.
Yalwataccen murmushi Didi ta Saki kana tace.
“Tabbas kuwa shine ɗa Namiji babba