Showing 90001 words to 93000 words out of 218703 words
bayan sun gama suka juya suka tafi...
Aunty Ruƙayya da farin ciki ya gama cikata ganin yanda Moddibo da Khausar sukayi bala'in da cewa ga kuma yanda Moddibo ke raɗawa Khausar magana akunne wanda duk mai kallonsu a matsayin zantukan masoyane sukeyi yasa ta kalli Hajiya Bunayya wacce itace akusa da ita kana tace.
“Dan Allah Hajiya kalli Khausar da Moddibo tamkar dan junansu aka halicce su, haƙiƙa sun dace da juna Allah yayi Khausar zaɓi da mafi Al'khairi Ubangiji ya kawar da idanun maƙiya akansu”.
Yaƙe Hajiya Bunayya tayi Amaimakon tace Ameen sai ta sunkuyar da kanta tayi tare da cewa.
“Aikam”.
Wani irin zafi da ƙuna zuciyarta keyi ba zato taji hawayen hassada da ƙyashi na zuba daga idanunta ina ma ace Aminanta ce ke cikin wannan Daular duniya..
Daga can cikin falon kuwa Wasu zugan Maza da Mata manya ne suka nufi wajensu Moddibo da Khausar.
Sarkin Zaƙi na ganinsu ya ɗaga sautin muryarsa tare da cewa.
“Hattara dai Ango da Amarya ga Baffanayenku nan da Goggoninku”.
Ahankali Moddibo ya ɗaga kai yana kallonsu cikin wani irin yanayi mara misaltuwa wai yau shine acikin ahalinsa ana gabatar mishi dasu sahu-sahu.
Su kuwa cike da tarin ƙaunarsa suka riƙa yi musu liƙi da kuɗaɗe masu tarin yawa.
Aunty Hawwa ce ta kalli Aunty Hajara wacce suke daga ɗaya gefen Hajiya Bunayya kana Aunty Hauwa tace.
“Masha Allah Kinga yanda ake zubar da kuɗi tamkar ba'a cikin tsadar rayuwa”.
Dariya Aunty Hajara ta sanya tare da cewa.
“Aikam acikin wannan ahalin. Basuma san wani abu mai suna talauci ba komai nasu cikin wadata suke”.
Da ƙyar Hajiya Bunayya dake sauraransu ta haɗiye wani abu mai masifar ɗaci daya tokare mata maƙoshi Allah ne kaɗai yasan tashin hankali da ɗimuwar hassada da take ciki...
Haka aka riƙa gabatarwa Moddibo da ƴan uwansa
Abokan arziƙi, ƴaƴan Baffaninsa. Da ƴaƴan Goggoninsa sahu-sahu.
Kana bayan an gama aka shiga gabatar masa da Hadimansa wanda zasu riƙa yi masa Hidima.
Bayan an gama wannan.
Jakadiya dake tsaye gefenshi riƙe da wasu Ƙore guda uku ahannunta babban na cike da madaran Shanu fari ƙal.
A hankali ta ajiye su agaban timtim da ƙafan Khausar ke kai sai kuma ta ɗauki ƙamarin Ƙwaryan ta ajiye acikin wanda yake ɗauke da ɗanyen madaran Shanu.
Kana ta ɗauki ɗayan mai matsakaici, tare da matsowa gefen Moddibo ta risina tare da cewa.
“Bismillah zaka wanke ƙafan Amarya da madara da fatan Ubangji Allah ya kareta daga sharrin da yake cikin fadar nan kana Allah ya haɗa ta da Alkhairan dake ciki”.
Juyawa Moddibo yayi tare da kallon Ibraahim da ya dafa kafaɗarsa.
Asma'u kuwa Lumshe idanu tayi tana kallon ƙawarta cike da annashuwa kana tana mamakin tarin al'adunsu masu matuƙar kyau da tsari babu wani abu na bidi'a aciki komai bisa tsari suke gudanar wa...
Ibraahim kuwa dake dage da kafaɗarsa cike da so da girmamawa yace.
“Bismillah Yah Aleey Don Allah kayi mana”.
Lumshe idanu Moddibo yayi tare da ɗaga juya kanshi ya kalli Innayi wacce keji tamkar ta taso tazo ta ɗagashu tasa yayi dukkan abinda ya dace.
Ganin alamun zaƙuwa tare da itane yasashi miƙewa a hankali kana ya dawo gaban Khausar ya zauna akan kujeran da aka ajiye kusa da tum-tim ɗin kujerar da Khausar ke kai kana ya zaune.
Sai kuma ya ɗan kalli Ibarahim dake cewa.
“Ɗa ƙafar dama zaka fara”.
Ɗan hararan Ibraahim yayi kana ya ɗan ronƙofo kaɗan ya sunkuya, a hankali ya sanya hannunsa na dama ya kamo ƙafan Khausar na dama tare da zare mata takalmin, tare da tsirawa fatar kafar lumsassun idanunsa,
Zakariyya ne ya ɗan yi gyaran Muryar da ya sashi,
Ɗan Lumshe ido kana ya buɗesu a hankali, yatsunta sunyi masifar kyau, kana faratun ƙafan ayanke suke fes-fes gwanin ban sha'awa.
Aransa yace ikon Allah wannan ita kuma haka tabar ƙafar nata.
Kansa ya ɗago tare da kallon kyakykyawan fuskarta dake fitar da annuri kana ya tsuke fuska ya ɗan harareta tare da cewa.
“Ko Amaryar shamuwa ana sa mata lalle. Amma ke naga alamun Amaren buzuzuma sun fiki ƙyalli”.
Jin abinda yace yasa ta tura baki da ɗan juya ido.
Ƙafanta ya jawo kana yasa cikin ƙwaryan dake gabansa wanda babu nono aciki ɗan matse ƙafar yayi har saida ta ɗanyi ƙara, shi kuwa wani murmushin da shi kaɗaine yasan ma'anarsa yayi.
Jakadiya kuwa nono ta ɗebo aƙaramin ƙwaryan ta miƙa masa.
Ita kuwa Khausar jin yadda yaja ƙafanta yasa ta risino wanda dai-dai lokacin take tura baki..
Karaf sai akan idanunsa ware manyan idanunsa yayi kana ya motsa laɓɓansa tare da faɗin.
“idanfa kina hararana, ƙwaƙule idanunki zanyi, kafin kije Lahira Ubangji ys ƙona miki su”.
Saurin kallonsa Khausar tayi jin abinda yace girarsa ɗaya ya ɗaga mata tare da cigaba da faɗin.
“Yess ai na lura bakisan daraja da girman miji bako?”...
Uffan batace masa sai ma lumshe idanunta da tayi tana jin yanda ɗumkn tafin hannunsa ke ratsata...
Hannunsa na dama yasa ya tallafi ƙafartata kana ya karɓi ƙwaryar Nonon da hannunsa na hagu ahankali yake zuba Nonon akan ƙafarta...
Yayin da aransa yake tuna tabbas ya taɓa sanin wannan al'adar amafarkinsa da yake yawanyi...
Cike da nutsu da kuma ƙwarewa yake wanke ƙafafunta daga dai-dai idon sau zuwa kan zara-zaran yatsun ta ya wanke fess.
Ita kuwa sai mutsu-mutsi take da yatsun ƙafarta ɗan ji take kamar jakul-ku-kuli yake mata,'.
Yana gama wanke wa sai ga Didi da kanta wani farin ƙyalle mai masifar haske da ƙamshi ta miƙa masa.
Juyawa yayi yaga Mahaifiyarsa tsaye da kanta take bashi.
Didi kuwa kai ta jinjina masa alamar ya karɓa.
Ba musu ya karɓa tare da gogewa Khausar ƙafanta kana ya mayar cikin takalmin ta, sai kuma ya zaro ƙafara na hagu ya wanke kamar yanda yayiwa na damar.
Wani farin ƙyalle kamar na farko mai azabar ƙamshi Didi ta sake miƙa masa ya goge mata ƙafar kana ya ajiye.
Kallonsa Didi tayi tare da faɗin.
“Toh ka matso da kyau sai ka tallafi ƙwaryar Nonon cinyaka kasa hannunta duka biyu ka wanke”.
Da ɗan sauri ya ɗaga kansa ya kalleta.
Lumshe idanu tayi alamar kayi ɗan Albarka.
Kai ya jinjina hakan yau yake jinsa wani irin farin ciki mara misaltuwa tamkar wanda aka yiwa bushara da gidan aljanna.
Kujeran yaja ya matsa kusa da Khausar sosai yayin da Gwiwoyinta ke gugan Gwiwoyinsa.
Bakajin saurin komai sai busan sarewa da tashin jits, Yayin dasu Ibraahim kuwa suka koma ta bayansa suka tsaya, gudun kada su tsaya agaba su tare wa ƴan baya,
Hotuna yimusu ake yi babu tsayawa tako wacce kusurwa hoto ake musu, yayin da Yayunsa ke zuba musu Liƙi.
Ahankali ya kamo lallausan tafukan hannunta ya riƙe acikin nasa kana ya tsunduma su acikin ƙwaryar Nonon da Jakadiya ta ɗaura masa akan cinyarsa wanda aka zuba wasu Jajayen Flowes masu kyau da tsari.
Cikin nutsuwa ya fara wanke hannun, tare da ɗan jan ƴan yatsunta, a hankali, ya ɗan ƙara ware idanunsa lokaci da ya ja ƴar ƙaramar yatsarta ta hannun hagu, gani yadda ta tara faratunta sunyi zaƙo-zaƙo irin dai yanda ƴan matan zamani keyi, sai dai sunyi masifar kyau musamman ma na ƙaramin yatsanta na hagu duk yafi sauran faratun tsawo, matse hannun yayi acikin nasa.
Runtse idanunta tayi cike da raki da shagwaɓa ta furta.
“Wash! Allah”.
Ta faɗa tare da sunkuyo da kanta haɓarta na taɓa goshinsa ahankali ya ɗago kanshi, wanda hakan ya bawa hancinsa damar gogan hancinta.
Cikin tsuke fuska ya sanya ƙwayar idanunsa cikin nata tare da faɗin.
“Meye amfanin wannan farcen da kika bari ajikin ki?”.
Cikin sanyi tace.
“Dan yin susa in ƙaiƙayi ya dameni”.
Sosai ya daure wurin danne yanayin da muryata ta sashi a ciki, a hankali ya ɗan matse yatsar kana a hankali yace.
“Shin bakisan cewa shi farce shine rumfar shaiɗan ajikin ɗan Adam ba?”.
Shiru tayi ba tare da ta cire idonta daga kan sajenshi da takeyiwa kallon kurillaba.
Shi kuwa numfashi ya fesar tare da cewa.
“Ya za'a yi ki tarawa sheɗan Mafaka ajikin ki?No wonder shiyasa kika cika rawan kai ashe muhalli kikayi ibilis a jikinki”.
Bakinta ta tura tana kallon yanda yake matse mata hannu.
Shi kuwa Moddibo cikin sanyin murya ya cigaba da cewa.
“Shiyada duk rashin ji da neman mgn duk kece a gaba ashe-ashe muhalli kika tarawa sheɗan agangar jikinki. Toh kiji da kyau, ko kiyanke faratun nan ko kuwa idan na tashi da kaina zan haɗa da ƴan yatsunki in yanke kana na wurgawa karnuka su cinye”.
Cikin yanayin tsoronsa da sanyin murya tace.
“Dan Allah ka sake min hannuna zafi fa yake min”.
Sake matsawo kusa da ita yayi tare da faɗin.
“Bazan sake ba”. Da sauri tace.
“Afwan”.
Cikin kasala yace.
“Sai kinyi al'ƙawarin zaki yanke farcen”.
Da sauri ta gyaɗa masa kai cikin narke fuska tace.
“Nayi al'ƙawari zan yanke amma zan bar ɗaya”.
Fuska ya ɗaure tare da faɗin.
“Ban yarda ba duka zaki yanke”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Na yarda zan yanke toh ka sake min hannu”.
Wani irin murmushi mutanen dake wajen sukayi yayinda wasu ke binsu da kallon sha'awa.
Asma'u kuwa hannu ta miƙawa Dije dake gefenta suka tafa cikin yanayin farin ciki Dije tace.
“Asmeey kinga wata Madarar soyayya kamar a Indi'a muke, lallai na yarda cewa Ustazan nan sunfi kowa iya soyayya”.
Kai Asma'u ta jinjina tana mai binsu da kallon sha'awa yayin da aranta take musu addu'ar samun dawwa-Mam-miyar farin ciki tace.
“Ai kam ko tattabaru bazasu gwadawa su Khausy zama da junaba, kinaga wani irin mayataccen kallon da Yah Modibbo keyi mata, ko me yake gaya mata?”.
Da sauri Aseeya tace.
“Sai Allah gashi dai tun ɗazu suketa wani ƙus-ƙus ji Khausar yadda take lumshe ido”.
Dariya sukayi dukansu
Zakariyya kuwa cikin sarawa salon Modibbo ya ɗan sunkuyo daf da kunne Moddibo kana yace.
“Dan Allah ka riƙa tunawa, cikin mutane da kuke.
Na lura gaba ɗaya ka zauce ƙa kauce hanya baki ɗaya, ka wani gigice daga ganin yarinya kana ƙoƙarin taɓarewa acikin tsakiyar taron al'umma duk kuma wani narkewa”.
Khausar kam kanta na ƙasa Zakariyya kuwa cike da sheƙiyanci ya cigaba da cewa.
“A cikin Family fa kake ba cikin falonku kuke ba”.
Shi kuwa Modibbo Numfashi ya sauƙe mai nauyi A ransa yace.
ohhh ni Aliyu na lura Zakariyya magana ne abakinsa shida. Dr Jameel sai dai Allah ya shirye su.
Hannunsa na dama yasa ya damƙe nata da ƙarfi, sai ya zama na kamar sunayin musabaha ne.
Sai kuma yayi shiru tare da rintse idanunsa da sanya haƙoransa ya cije gefen lips ɗinsa na ƙasa kana ya sunkuyar da kansa ƙasa, wani irin abu yake ji tun daga tsakiyan maɗigan ƙwaƙwalwar kansa, har zuwa tsakiyar tafin ƙafarsa, lokaci ɗaya yaji gangar jikinsa ya fara tsuma baki ɗaya jikinsa ya fara tsuma amma ta ciki yanda babu wanda zai fahimta sai shi...
Ibraahim ne ya tsugunna kansa tare da faɗin.
“Bismillah Yah Aleey, Continue”.
Jin muryan Ibraahim yasa ya fesar da sanyayyan numfashi sai alokacin ya fara dawowa hayyacinsa.
Ahankali ya buɗe Idanunsa da suka kaɗa sukayi Jawur ya kalli Khausar yana mai jan wani dogon numfashi da ɗan ƙarfi ya sauƙe numfashin kana ya ɗago idanu ya kalleta.
Da sauri ta fito da idanunta waje ganin yanda ƙwayar idanunsa suka sauya launi baki ɗaya.
Khausar kuwa ahankali tace.
“Ayyah kasake min hannu na zafi”.
Numfashi ya fesar tare da sakin hannu kana ya kamo yatsunta.
Didi dake tsaye ta dauki wani ƙyalle me kyau kamar farko ta miƙa masa karɓa yayi kana ya goge mata tafin hannun zuwan ƴan saffa-saffa yatsunta.
Rahma kuwa kaskon turaren wuta dake fitar da wani Masifeffen ƙamshi ta miƙa masa.
Ƙamshin da ya fara gigita masa tunaninsa lokaci ɗaya ya fara jin wani irin yanayi yana game masa gangar jikinsa da ruhinsa baki ɗaya.
Kaskon turaren wutan ya ɗaura akansa kasancewar gindin Kaskon nada faɗi sai ya kamo hannayenta ya kife akai.
Ahankali hayaƙin turaren wutan ke ratsa yatsunta yana buga fuskanta.
Mai busa Algaita ne ya cigaba da busawa dare da haɗawa da kirari.
Sarkin Zaƙi kuwa hura Microphone yayi tare da cewa.
“Idan akwai ƙanin Amarya ko ƙanwar amarya ta fito, ta amshi kaskon bisa al'adarmu”.
Cikin sauri Haiydar dake ta faman Video ya miƙe ya fita kana ya zare Kaskon turaren wutan kasancewar haka Al'adarsu take.
Shi kuwa Haiydar sunkuyowa kan Khausar yaui tare da faɗin.
“Kai Addah Khausi kunyi kyau.
Kinga yanda kika zama kamar wata acikin taurari baki ɗaya ke kike haska wajen nan”.
Kallonsa tayi cikin yanayi gajiya, sai kuma ta ɗan hararesa kana tace.
“Dole mana kace haka tunda ni kaɗai ce ƴar Uwarka”.
Murmushi yayi kana cikin gaskiya da gaskiya yace.
“Wallahi ba haka bane Addah Khausy kinyi masifar kyau fa”.
Ya ida maganar tare da miƙawa Jakadiya Kaskon.
Jakadiya kuwa da ido ta yiwa Moddibo alamar ya tashi ya koma kan kujera.
Kai ya gyaɗa tare da komawa mazauninsa.
Haka ma Didi da yayunsa suka koma wajen zamansu...
Sarkin Zaƙi kuwa cike da rakaɗi yace.
“Alhamdulillah da wannan al'adar tamu mu kazo ƙarshen wannan taro na yau, sai kuma gobe idan Allah ya kaimu bisa dai da lafiya, za'a fitar da Aleeyu Youseep Muhammad Mouley atsakiyar fada, domin gabatar dashi atsakiyan Fada a matsayinsa na sarki mai jiran gado”.
Daga nan aka tashi kasancewar ƙofofine da dama cikin falon, yasa lokaci ɗaya duk aka fita cikin nutsuwa batare da wani cunkuso ba duk da kuwa yawan mutanen.
Acan ɓangaren Innayi kuwa cikin sauri ta nufi wajensu Moddibo tare da riƙe hannun Khausar ta juya.
Moddibo kuwa baki ɗaya Cousing Brother's ɗin sa ne suka riƙa bashi hannu suna rungumesa cike da ƙaunarsa tare da gabatar mishi da sunayensu da dangatakar su.
Shima cikin yalwataccen farin ciki yake rungunarsu.
Kafaɗarsa Zakariyya ya dafa tare da faɗin.
Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta abinki cikin Salamah 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER'N 09097853276, in tura miki ki karanta abinki salamun Salam.
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 17*
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Assalamu alaikum mutanan arziki masoya kamshi ma abota kamshi Amaren kamshi masu jargon kamshi Yammata wadanda sukasan darajar kamshi ni Aysha Aliyu Garkuwa na kawo muku tallan wasu Amintattun turarukana masu matukar kamshi da Kama jiki
Masu saukin farashi sannan ga biyan bukata
Yarhjya_incense_and_more
Ta shirya tsaf domin ta gwangwajeku da Turaruka na alfarma
Farar khumrah
Bakar khumrah
Turaren Wanka
Oil 6ml 1
Oil 12ml 1
Turaren fesawa 100ml 24 hours guda 1
Duka Akan 8k kacal
Sannan kayanta suna tafiyane da guarantee duk wacce tasiya taji babu kamshin nan na alfarma ko kuma basuda lasting to tayi alkawarin mayar muku da kudinku
Wannan garabasar zata kare on 5th September insha Allah
Ku hanzarta ku mallaki naku domin kayan yarhjya babu Danasani a cikinsa saidai kuyi alfahri da siyan kayanta
Account number 1419787445 Amina Umar usman access bank
Kitura evidence of payment to
08092664954
Kuyi saving number TA domin ci gaba da ganin Turaruka Kala Kala
Normal price
Bakar khumrah 1500
Farar khumrah 2k
Turaren Wanka 1500
Oils 6ml 800
Oils 12ml 1500
Turaren fesawa 100ml 3500
Turaren fesawa 50ml 2k
Kayanmu available ne a koda Yaushe
Akwai turarukan wuta na jiki na Kaya Dana daki duka sai Wanda kika zaba
“Kazo mu koma ciki Maghriba tayi muje muyi alwala mu tafi masallaci”.
Cikin gamsuwa ya gyaɗa kai,
Ibraahim kuwa hannun Moddibo ya riƙe tare da faɗin.
“Yah Aleey daga yanzu zaka riƙa zuwa jam'i yanda kake buri da fata da marari”.
Sanyayyan numfashi Moddibo ya fesar kana yace.
“Alhamdulillah, dan babu abinda nafi bege kamar zuwa sallah jam'i da kuma Innayi na”.
Ya ida maganar tare da bin bayan Ibraahim suka fara tafiya.
Tuni ƴan Uwa sun fiffita falon ya rage babu mutane sai ɗaɗ-ɗaya.
Innayi dake riƙe da hannu Khausar ta nufi wajensu Ummi tare da faɗin.
“Kuzo mu koma masauƙinmu sai kuma gobe idan Allah ya kaimu, za'a cigaba da hidima”.
Sheikh Jabeer kuwa da kansa ya nufi inda su Abban Jameel ke zaune yace.
“Kuzo mu tafi Maghriba ta ƙara to”.
Kai suka gyaɗa kana suka miƙe suka bi ta ɗaya ƙofar suka tafi.
Moddibo da su Ibraahim kuwa a hankali suke tafiya cikin nitsuwa auka shiga Corridor da zai sada su da falon Side da suke.
Su Khausar kuwa sun fara haurawa kan steps din.
Asma'u ta juya da sauri ta kalli Ummi tare da faɗin.
“Ayyah Ummi bari inje na gaida Yah Moddibo in faɗa masa saƙon Bashir”.
Ƴar dariya Ummi tayi kana tace.
“Bismillah keda ɗan Uwanki”.
Kai ta gyaɗa cikin sauri ta juya ta nufi wajensu Moddibo tana faɗin.
“Yah Moddibo! Yah Modibbo”.
Moddibo kuwa Already sun riga sun shiga falon da Dr Jameel ke ciki.
Shi kuwa Dr Jameel jiyo motsinsu ne yasa ya sassauta murya cikin wani irin yanayi da yake ciki bisa ga duk kan alamu hirar batsa suke awayar cikin lumshe idanu yace.
“Please Baby kiyi haƙuri muna cikin wani Uzuri ne fa na Fada”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Ok bye bye Amma please kazo Ina jiranka, kasan cewa kwana biyu bamu haɗu ba ina kewarka”.
Ta ida maganar tare da katse kiran.
Dr Jameel na miƙewa su Moddibo na shiga....
Cikin yanayin takaicin halayyarsa Zakariyya ya maka masa harara tare da cewa.
“Wallahi kai dai kam Jameel kayi asara, komai aka shirya da kai da zaran mace tashiga ciki saita ware ka cikin mu, musamman wannan shegiyar Baby na rasa yanda zanyi in raba ka da ita”.
Moddibo dake jinsu ne ya girgiza kai kana yace.
“Alhamdulillahi kaima kenan abin na damunka Zakariyya?”.
Kai Zakariyya ya gyaɗa yana mai cigaba da hararan Dr Jameel dake murmushi yace.
“Sosai ma kaga an tsara fitan nan dashi amma dayake shi Mamajone mayen mata, ni wlh ban na lura da lokacin daya zame ya dawo ciki ba, sai da muka shiga na gane baya tare damu”.
Sai kuma Moddibo yayi saurin juyawa jin muryan Asma'u na cewa.
“Yah Moddibo”.
Da murmushi afuskarsa yace.
“A'a Asma'u”.
Asma'u kuwa idanunta ta zare tare da ɗaura hannunta ɗaya akai kana ta buga ɗaya hannunta a ƙirjinta tare da faɗin.
“Yah Jameel”.
Tayi maganar idanunta na kan Dr Jameel dashi ma ita yake kallo.
Cikin sauri Moddibo ya juya ya kalli Asma'u sai kuma ya juya ya kalli Dr Jameel.
Cikin yanayin kaɗuwa, mamaki, Al'ajabi ta fara takowa har ta isa gaban Dr Jameel ta tsaya cikin sarkewar murya ta furta.
“Yah Jameel”.
Kallonta Moddibo yayi tare da girgiza kai yace.
“A'a Asma'u”.
Cikin ficewar hayyaci ta ɗaura hannunta akai tare da faɗin.
“Ummiiii kizo ga Yah Jameel”.
Sai kuma tayi baya luuu idanunta sukayi sama.
Cikin wani irin sauri Dr Jameel da tun time data kira sunansa ya zuba mata idanu yana kallon ƙiranta da kuma yanda Ubangji ya ƙawata surarta, lokaci ɗaya yaji wani irin yanayi da