Showing 114001 words to 117000 words out of 218703 words

Chapter 39 - Sakayyah 2 Hausa Novel Complete

karkarwa da jikinsa keyi,
“Yah Salam”. Shine abinda ya iya furta a saman lips inshi sabida jin gaba ɗaya gangan jikinsa yana sakewa, dai-dai lokacin da ya iso tsakiya falon, wanda yake mamaye da duhu, bisa alamu, tun fitansu Lalla Khadijah ne suka kashe wutan falon.
Wayarta da ya ke cikin a'jihunsa ya zaro lokacin da yaji ya tafi ƙasa ya gaza tsayuwa, sabida wani irin fitinennen damƙa da mararsa tayi haɗi da harbawa.

Da kyar ya isa ɗan haska fuskar wayar, sai kuma ya kife wayar bisa kujerar da ke gefenshi kana shi kuwa ya miƙe plat a tsakiyar falon bisa tattausan Marocco Carpet Wanda a jikinsa ke tube MRS Aleeyu Youseep Mouleey din.

Wani irin tsuma da karkarwa jikinsa keyi tamkar mai cutar zazzaɓin da ke sa sanyi.

A can Side dinsu Asma'u kuwa.
Ita da Dija da Ummi dake waya da Mommy ne, bisa gada.
Cikin sanyi Ummin ta ɗan fesar da numfashi tare da juyowa ta kalli inda Asma'u da Dija ke kwance kana a hankali tace.
“Uhmmm ke dai bari Mommyn Khausar wlh Ni kaina, tunda muka dawo kai Khausy side ɗinta na gaza bacci, gaba ɗaya ita nake tuna, abinda baka san wahalarsa, bare da yanayin ƙarancin shekaru in dai an haɗa da na Modibbo ai Khausar yarinca tunda dudu fa yanzu suka cika shekaru sha tara.”
Cikin fesar da numfashi Mommy dake zaune bakin gadon tace.
“Wallahi kuwa Ummin Jameel, gaba ɗaya na kasa rumtsawa, bare ɗazu dana kirata, kuka tai ramin tana magoya wai dan Allah in roƙeki a bar mata Asma'u, itafa bata san kowaba a garin.
Wai da nace mata ai kowa da haka yake sabawa, sai cewa tayi. Mommy kamar bakya sona, kin san haka za'ace za'abarni ni kaɗai shine baki bani Raudat”.
Cikin sanyi Ummi tace.
“Ba komai in sha Allah, wlh Aliyu bazai tozarta zaɓin Jamilu naba, koda kuwa ace baya sonta, barema wlh Mommyn Khausar iyayen Modibbo masu mutumci ne, barema kuma ai zamu bar Innayi anan".
Cikin rauni da tausayi irin na iyayen a dararen da suka san an kaɗai ta yarsu da mijin aurenta, Mommy tace.
“Kayya Ummin Jameel wani sabawa ne, Khausar tayi da Innayi”.
Cikin bada ƙarfin guiwa Ummi tace.
“In sha Allah ba komai sai al'khairi”.
A hankali Mommy tace.
“Ɗazu muna waya da Haiydar ke cemin, wai ranar Jumma'a zaku dawo ko?".
Cikin sauƙe numfashi Ummi tace.
“Eh haka dai Abban Jameel ke cemin, amman shi Abban Jameel zai ɗan zauna sabida yanzu dole shi zai tsaya yayi aikin da ya turo Aliyun yayi. Kuma yacemin sune suka shirya komai na tafiyar namu, sun hanashi kashe ko asi”.
Cikin sanyi Mommy tace.
“Wato dai ya tabbata zaku dawo ku barmin Khausar na, can ita ɗaya, Khausar da shegen tsoro ace an barta a ƙasar da bata da kowa nata, da mijin da sonta yake ba, ko ya rayuwa zata juya mata, wlh Ummin Jameel wannan abufa yana damuna, dama ace Modibbo shine yace yana sonta da bazan shiga damuwa sosaiba”.
Cikin sanyi Ummi tace.
“Wallahi kada ki damu Khausar fa, ta samu karɓu sosai a masarautar Mouley”.

“Uhmm Toh Allah ya dawo daku lafiya”.
Mommy tace kana daga nan sukayi sallama.

Sai kuma ta miƙe ta shiga Bathroom tayi al'wala kana ta fito ta fara Nafila tare da roƙawa Khausar ɗinta samun aminci da konciyar hankali.

Ummi ma nafilan ta fara

Yayinda can cikin masarautar Mouley kuwa a side ɗin Didi.
Cikin sanyi Lalla Khadijah ta kalli Aunty Afreen wacce take ƴar Didice.
Cikin sanyi tace.
“Aunty Allah dai yasa ɗankun nan, ya bar ƴar mutane ta sarara, ta samu ta huta, domin na lura shi ɗin sai a hankali”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Ina ruwanki mutum da matarsa in banda sa ido”.
Dariya tayi tare da leƙa idon Lalla Hafsat da ke cewa.
“Gsky dai kam, Allah yasa ya barta, kinfa san in bai barta ba, muma ba hutawa za muyiba da wannan tsaraɓe-tsaraɓen al'dun wannan masarautar Mouley munnan, ni har ga Allah abin kunya yake bani da takaici”.
Cikin sauƙe numfashi Afree tace.
“Idan dai har ya kasance kamar kakanshi mahaifinmu to, babu shakka zai gyara muku masarautarku duk randa ya hau karagar mulki zai rabaku da duk wasu bauɗaɗɗun al'adu ya fuskantar daku addini, kamar yadda Sheykh Jabeer yayi gyara masarautar Joɗa”.
Cikin sauke numfashi Lalla Hafsat tace.
“Allah yasa haka”. Da Amin suka amsa, kana ita sukaci gaba hirarsu.

A can Side ɗin Khausar kuwa, cikin wahalallan baccin da takeyi a takure wanda ya jaza mata nauyin ƙirjine, ta ɗan mirgina sabida takuranda taji, cikin akasi tayi ƙasa rib kasan cewar a bakin gadon take.
Cikin wani irin raɗaɗin da ya game guiwowinta da suka sauƙa gib kan tayis ɗin ne, ta buɗe idanunta da sauri sai kuma ta sake rufesu da ƙarfi, tare da faɗin.
“Innalillahi wa innalillahi raji'un”.
Sabida ganin duhun daya mamaye ganinta, cikin gigita haɗi da kiɗima, ta miƙe tsaye tare da fara laluɓe-laluɓe tana kuma faɗin.
“Na shiga uku, innalillahi ba kowa ne a nan, wayyo Allah Ummi”.
Ta ƙarasa kiran Ummin da ƙarfi.
Sai kuma tayi saurin juyawa jin yadda ta buge kanta da jikin gini.
Kuka mai cike da tsoro ta saki tare da ci gaba da lalubawa, jin hannunta jikin labulena yasa tayi saurin yaye labulen, wanda na window ne, buɗe labulen da ta ɗanyi ne yasa ta ɗan samu hasken dake cikin correct ya ɗan haska ɗakin, da sauri ta juya ciki tana laluba ta inda wutan yake, amman ina bata ganoba sai dai tayi kamari da ƙofar fita, haka yasa ta fita da sauri, yayinda laffayar jikinta ke ja da ƙasa sabida ya warware.

Shi kuwa Modibbo tun farkawarta yaji muryarta, da motsinta, sai dai bashi da dama ko iko da ingin motsawa.
Sai karkarwar da jikinsa keyi daya ƙara tsananta. Hannunsa duka biyu ne, dafe da mararsa yayinda lips inshi suke rawa tamkar wanda aka cilla cikin dusar ƙanƙara, sabida rawar da ya tsananta har haƙoransa na dukan juna suna bada sautin gat-gat-gatt.

Ita kuwa Khausar da sassarfa ta fito falon, tana mai dannawa Ummi kira.
Dai-dai lokacin da ta iso tsakiyar falon kusa dashi laffayar ta zame tayi ƙasa ya harɗe sawunta da sauri ta daga ƙafarta da nufin ta zare samu ta cikin akasi kuma tayi tuntube da Modibbo dake kwance tsakiyar falon.

Luu ta tafi ta faɗa kanshi, ba zato ba tsammani ta jita bisa ruwan cikin mutum.
Ihu ta kurma da ƙarfi, wanda har saida Ummi dake Nafila ta jita, cikin sauri ta rumtse idanunta dan a zatonta, Modibbo ne ya rutsa Khausar ɗin a fili tace.
“Kai yaran zamani ka barta ta huta mana ko na mako ɗaya ne, ka bita a hankali”.
Ta kare mgnar cikin yin ƙasa da murya da kuma ci gaba da tasbihinta.

Shi kuwa Modibbo cikin tsakin gigitan yanayin da yake ciki ya jawota jikinshi tare da ruggume ta da masifan karfi.
Yah Salam wani irin karkarwa Khausar ta farayi kamar wacce za'a zarewa rai da ƙarfi ta daddage da nufin kurma wani ihun, sai kuma ta zazzaro idanunta waje, jin yasa tafin Hannunshi na dama ya rufe bakin nata.
Jin yadda take karkarwa da fesar da numfashi kamar mai shirin shiɗewane yasashi ɗan buɗe mata bakin.
Cikin sassayan murya ya buɗe baki murya na karkarwa yace.
“Meyasa baki da nitsuwa ne? Ki nitsumana!”.
Cike da razani tasa hannunta ta ɗan riƙe hannunsa tare da cewa.
“Waye ne kai ɗin?”.
Cikin fuzgo maganar a hankali yace.
“Nine”.

“Kai waye ɗin?”.

Cikin Lumshe ido yace.
“Mijinki ne Aliyu”.

Wani irin dogon numfashi taja mai gwaraye da tsoro da kuma sassauci murya a sarƙafe tace.
“Moddibbooooo”. Cikin wani irin sabon ruɗanin da muryarta da ɗumin jikinta ya jefa shi ne yace mata.
“Uhhhhhhhmmmmmm”.
Cikin sauri ta janye jikinta daga gareshi ya koma gefe kana murya a sarƙafe tace.
“Dan Allah ka tashi ka maidani wurinsu Ummin”.
Hannunshi yasa ya lalubo wayarta da ya kife bisa kujera, cikin sanyi ya danna hasken fuskar wayar, wanda haka yasa Khausar sakin sassayyan numfashi.
Shi kuwa cikin karkarwar da jikinsa keyi ya yunƙara da kyar ya miƙe zaune, tare da kunna tocin wayar kana ya ajiye, tare da zuba mata fitunannun idanunsa da suka sirance.

Da sauri tace.
“Dan Allah kayi haƙuri ka tashi ka kaini”.
Cikin sanyin murya dake can ƙasan maƙosjinsa yace.
“Ce miki akayi ni ɗan rakiyarki ne, ko ɗan aikenki”.
Da sauri ta turo baki tare da cewa.
“Toh Wlh ni dai bazan kwana a nan ba, cikin duhu”.
Da hannunshi na hagu yayi mata alamun ga hanya ai ki tafi mana.
Hannunshi na dama kuma Al'kebbar jikinsa ya gyara tare da rufe cinyoyinsa.

Ita kuwa cikin sanyi tace.
“Ai tsoro nakeji fita ni ɗaya”.
Kanshi ya sunkuyar ba tare da yace mata kimaiba sabida ganinta cikin shigar tayi masifar zaburar dashi.

Ita kuwa Khausar can gefe ta koma ta tsaya tana tura baki tare da mgna ƙasa-ƙasa.
“Wallahi babu inda su Ummi zasu tafi su barni a nan ƙafarsu ƙafata”.

Sai kuma tayi shiru jin, an kwaɗa kiran sallan forko a matsallacin Masarautar, sassayan numfashi ta fesar tare da cewa.
“Alhamdulillah”.
Shi kuwa Modibbo cikin ɓoye yanayin da yake ciki ya yunƙura ya miƙe tsaye tare da ɗaukar wayar tata, kana ya nufi hanyar fita da sauri tace.
“Ka bani wayata”.
Ba tare da ya juyo ya kalleta ba yace.
“Kina da ƙarfi ai kizo ki ƙwata”. Ya ida maganar tare da ficewa.

Yana shiga bedroom ɗinshi kai tsaye bathroom ya wuce, ruwan mai ɗan zafi ya sakarwa kansa daga bisani yayi al'wala kana ya fito tare da kmtsawa cikin wata tattausar jallabiya baƙa mai ɗan karen taushi, turare ya fesa, kana ya fara nafila.

Ita kuwa Khausar yana fita, ta kunna watan falon da sauri, kana ta shiga Bathroom dake falon tayi al'wala, laffayan ta naɗa a jikinta sannan ta fara nafila bisa Carpet din, jin an kira assalatune yasa tayi rak'atsinil fajir, kana rai ta tasbihi.

Shi kuwa Modibbo jin anyi assalatune yasa ya miƙe tare da ƙara fesa turaren ya fice zuwa masalaccin.

Jin an yada iƙamane kuma yasa Khausar miƙe itama takabbarta.

Bisa jagorancin Modibbo akayi salkan.
Koda aka idar da salla Modibbo bai tashiba hakama Ibraahim da Abualeey da kuma da yawa cikin manyan fada wasu karatun qura'an sukeyi wasu tasbihi.
Saida lokacin fitowar rana yayi kana suka riƙa yin nafila raka'a bibbiyu kamar yadda Manzon Allah ya kwaɗaitar damu, hadisi ne sahihi cewa duk wanda yayi sallan asuba, yaci gaba da zama'a wurin har rana ta fito kana yayi nafila raka'a biyu toh yaba da ladan aikin hajji.

Bayan sun fito daga cikin masallancin bisa umarni da jagorancin Abualeey da Ibraahim da Sarkin fada da su Galadima Waziri, Wambai, Ɗan Maliki Dan Muram, da dai sauran, aka rinka yagayawa dashi ana nuna mishi lungu da saƙi na masarautar kofa-kofa Part-part haka aka rinƙa kaishi ana nuna mishi ƴan uwa da abokan arziƙu.
Daga ƙarshe suka shiga part ɗin da yafi kusa da na Didi wanda nan ne Part ɗin ƙanin Abualeey wanda baida lafiya tsawon shekaru anyi neman mgnin duniya an gaji an zubawa sarautar Allah ido.
Daga bisani suka shiga part ɗin Niyna anan suka yada zango suka sha tea ƙarfe tara da kwata dai-dai suka fito, daga nan kuma part ɗin Didi suka shiga.
Shi da Abualeey da Ibraahim, yayinda duk sauran kowa ya nufi gidansa.

Suna shiga suka samu sau Lalla Khadijah a falo.
Kusan a tare suka haɗa baki wurin gaida mahaifin nasu, zama shi ya gyara bisa kujerara kana ya kalli taron ƴaƴan nashi.
Murmushi yayi jin Lalla Khadijah na cewa Modibbo.
“Ango mai jiran gadaje biyu na sarautar Mouley dana amarya.
Kanshi ya ɗan kauda gefe ba tare da yace komai ba sai ɗan gudun murmushin gefen baki da yayi, sai kuma ya kama hannun Hakim tare da cewa.
“Meya hanaka zuwa masallaci”.
Ibraahim ne ya ɗan mari ƙeyar Hakim ɗin tare da cewa.
“Baccin banza mana, in ya samu Game sai ya kai karfe biyun dare yana abu ɗaya”.
Cikin tsuke fuska yace.
“Daga yau kada in sake zuwa Masallaci ban gankaba”.
Cikin jin daɗi duk suke kallonsa,
Shi kuwa Hakim cikin jin shakka da ganin kwarjin Modibbo yace.
“In sha Allah bazan ƙaraba Unclee Aleyyh, kuma dama in a gidane wlh kullum da Abbana muke zuwa Masallaci ka tambayi Mom kaji”.
Da sauri Lalla Khadijah tace.
“A'a ba ruwana ni bazanyi shaidar zurba”.
Shi kuwa Modibbo a hankali ya kalli Rahama da Didi da suka fito yanzu Hannu Didi ta miƙa mishi alamun suyi muhabaha, murmushi yayi cike da jin kaunar ta a ranshi ya miƙa mata hannun.
Cikin so ƙauna kulawa ta kalleshi, sai kuma ta kalli gefen hagu da damanshi, cikin yanayin zazzafan shaƙuwa dake shiga tsakaninsu yayi mata kallun alamun.
“Me kike nema".
Ɗan matse hannunsa tayi tare da cewa.
“Naga banga ƴata ɗaya bane a nan ɗin. Ina ka baro min ita?”. Ciki ware manyan idanunsa yace.
“Didi bansanta ba”.
Kusan a tare duk sukace.
“Matar takace baka saniba”.
Sai kuma ya kalli Abualeey da yace.
“Ayi mishi uzuri yau dai kam, dan daga Masallaci muka wuce zagaya fada, wata ƙil shiyasa bai taho da itaba”.
Cikin ɗan tsare fuska Didi tace.
“Toh maza tashi kaje ka taho min da ɗiyata, yanzu-yanzu”.
Cikin karya wuya yace.
“Didi Rahman t..."
Da sauri ya katseta da cewa.
“Tashi maza kuje, Ibraahim nuna mishi hanyar tsakiyan nan”.
Toh Ibraahim yace kana ya miƙe yayi gaba.

Daga nan cikin falon Didi suka bi cikin wani dogon corridor mai faɗi.
Tafiya mai ɗan tsawo sukayi, yaga sun ɓullo, ta kan steps nan da zai sadasu da saman kuma basubi, cikin babban falon nan ba.
Cikin sanyi Ibraahim yace.
“Ga hanyar dake tsakanin ka da Didi, ni inda ka zauna ɗinnan nanne Side ɗina, sai kuma ta gefen nan akwai hanyar da zaku fita ba sai kabi cikin falon nanba, tana ƙofar part ɗinka yake, ko da mota zaka fita ranan gate ɗin ka yake”.
Cikin gamsuwa Modibbo ya gyaɗa mishi kai.
Shi kuwa Ibraahim fara sauƙa yayi ta hanyar da zata sauƙa dashi ta cikin falon yana mai cewa Modibbo.
“Nima bari inje in ɗanyi wanka kafin ku fito”.
Kai kawai Modibbo ya gyaɗa mishi kana ya wuce cikin corridor insu kana ya maida ƙofar ya rufe.

Khausar kuwa tunda tayi sallan asuba ta kwanta a nan a falon tai baccinta, sai ƙarfe tara dai-dai ta farka tana tashi kuwa ta shiga wonka.

Dai dai lokacin yake haurowan kuma khausar ɗin ke tsaye gaban dressin mirror cikin wata chiga ta al'farmar da alamun yanzu ta fito wanka ta kuma fesa kolliya.
Ɗinkin doguwar rigar Getzener ce maroon color mai masifar maiƙo da sheƙi, an yiwa rigar aiki da zaren Golden color mai ɗan karen sheƙi, sai rashin fari, da kuma yellow da blue kaɗan-kaɗan wanda daga ƙasa zuwa tsakiya ne aka watsa tsaren da salon jelar ɗawisu, daga sama kuwa wasu irin duwatsun karaine masu masifar ɗaukan ido aka watsa a jiki wanda suka kuma an jerasu kamar tsarin gashin ƙirjin ɗawisu.
Cib-cib da jikinta rigar tayi wacce har ta ɗan matseta daga saman ƙirjinta da ƙasan mazaunanta da suka fito hani'an.
murza ɗaurin ɗan kwalin turban tayi ya zauna ras yayinda daga tsakiyar ɗan kwalin ta baya ta fito da jelam gashinta, wanda bata kitseshi ba.
Ƴan kunnen da sarƙa na gold masu ƙaramin nauyi tasa, sai kuma zobe.
Fuskar ta ta kalla a madubin, sai kuma ta tura baki, ganin har yanzu idanunta na ɗan kumbure kaɗan, yayinda ƙasansu dai-dai inda akesa kolli yayi ja, kamar dai kollin jambaki, hannunta tasa ta ɗauki ɗaya daga cikin hodar da aka jera mata a gaba dressin mirror, sai kuma ta maida ta ajiye tare da tura baki kana tace.
“Ba kollinyan da zanyi ma, harshenta, ta ɗan sa ta lashi pich lips inta, sai kuma dai ta ɗauki man bakin ta ɗan goga a yatsarta ma nuniya kana ta ɗan murza yatsar kan lips inta, wani irin sheƙi suka fara kamar ta samusu jambaki.
Turare kawai ta fara fesawa.

Shi kuwa Modibbo a hankali yake takawa har ya iso, dai-dai bakin ƙofar falonta, ƙofar na buɗe amman kuma ba kowa, sai tv data kunna ana karatun qura'an.
Wucewa yayi ya shiga falonsa, kai tsaye Bathroom ɗinsa ya shiga, ya shiga wanka.

A Side dinsu Ummi Innayi kuwa Ummin Jameel ce ke waya da Mommyn Khausar cikin ɗan yin ƙasa da murya tace.
“Wallahi nima tun ɗazu nake kiran wayarta yana shiga amman bata ɗagawa, na rasa ma ta ina zan fara na kirata yafi sau shida”.
Wani irin numfashi tausayi Mommy taja kana cikin sanyi tace.
“Ni nayi mata kira yafi goma, yanzuma saida na kira bata ɗayaba, Ummin Jameel kiyi ƙoƙarin zuwa inda take”.
Da sauri tace.
“Ok ba matsala in Sha Allah yanzu zanyuwa innayi mgnar”.
Daga nan suka katse kiran kana ta juyo ta kalli Innayi tare da cewa.
“Innayi ko zamuje wurin Khausar? Tun ɗazu muje kiranta bata ɗagawa”.
Murmushi Innayi tare da cewa.
“Ai in da buƙatar zuwanmu sashinta Jakadiya zata sanar mana.
Yanzu babu mai zuwa inda take, kuma itama ƙofar Didi kawai zataje, shima dan wannan zuwan shine madubin da za'a gane cewa, ya ta kasance tare da mijinta, kuma in akwaida abinda ya faru za'a nemu. Kiranta kuwa bari zuwa anjima ku sake gwadawa”.
Innayin ta kare mgnar a dungule, wacca kuma tuni Ummi da Aunty Rukayya sun gane ma take nufi.
Haka yasa Ummi sauƙe numfashi kana ta kira Mommy ta ɗan kwantar mata da hankali toh kawai Mommy tace amman taci gaba da kiran.

Nigeria
Abuja, cikin Maitama. Amina da Unclee Naseer tsaye a bakin falonsu, bisa alamu fita zaiyi, cikin salo na musamman, ya ɗan jawota jikinshi tare da ruggume ta cike da yaudara yace.
“My Dear Kada ki damu bazan daɗeba zan dawo, bazan wuce awa biyu ba”.
Cikin yauƙi tace.
“Ni da mu tafi tare”.
Kai jujjuya tare da ɗan janye jikinshi kana yace.
“Baby mitin fa zamuyi, kuma duk mu ya mune maza. Ki dai yi haƙuri kinji, bari in tafi kada in makara”.
Cikin kwarkwasa tace.
“Toh sai ka dawo”.
Ɗan shafa fuskarta yayi kana ya fice.
Ita kuwa ƙofar ta maida ta rufe.
Tare da komawa cikin falon, bisa 2 str ta kwanta tare da ci gaba da chating.

A hankali ta ɗan juya kanta, jin kamar alamun an buɗe ƙofar ɗakin nan da bata taɓa shigaba, kai ta maida ta jingina taci gaba da latsa wayar, sabida ganin ƙofar nan a rufe.
Sai kuma ta ɗan dakata da latsa wayar sabida jin kamar hucub numfashin mutun, haka nan kuma wani irin kasala da tsoro ya diro nata, a hankali ta juya idonta zuwa kan A.C wanda a zatonsa hushin fesar da sanyinsa ne.
Da sauri ta tashi zaune jin hucin ya karuwa da kuma ƙara matsota. Wani irin gigitaccen kara da tsalle ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login