Showing 105001 words to 108000 words out of 218703 words

Chapter 36 - Sakayyah 2 Hausa Novel Complete

ana haurowa kuma bisa duk kan alamu Asma'u ce dan taji muryarta kamar waya takeyi da Bashir.

Mutsu-mutsun ta fara tare da ƙoƙarin ƙwace hannunta kansa ya ɗago ya kalleta da rikitattun idanunsa.
nan taga idanunsa sun sake kaɗawa sunyi masifar Jaa kana ga alamun sun sake cika taf da hawaye sai dai hawayen basu zubo ba sai sheƙi suke suna bada kalan hazo-hazo yayin da jikinsa ke cigaba da tsuma.
Ƙoƙarin janye hannunta ta cigaba dayi, a kasalance ya ɗago kansa ya kalleta, sai kuma ya tsuke fuska tare da ɗan hararanta yace.
“Sakeni mana”.
Cikin ɗan karen kasalan daya zuba mata tace.
“Ai banice ke riƙa da kaiba, kane kake riƙe dani fa”.
A fakaice yace
“A zahiri ba”.
Sai kuma ya zare hannunshi sabida shima yaji alamun ana haurowa kan steps ɗin.
Ahankali yaja dogon numfashi mai ƙarfi kana ya miƙe tsaye tare da juya bayansa ya buɗe Labulen jikin dining ɗin ya tsirawa harabar Side din nasu ido wanda yake ɗauke da wani Kekkyawan gate golding sai farafajiyar da zata iya ɗaukan motoci bakwai sai kuma can ƙasa da ya hongu alamun BQ ne daga bakin gate kuma babban ɗakine da bayi a ciki da alamun Hadiman yankinsa ne.
Asma'u ce ta shigo ganinsa tsaye yasa tace.
“La Yah Moddibo kashigo?”.
Batare daya juya ya kalleta ba ya gyaɗa kai tare da cewa.
“Eh na shigone inga ya yanayin jikin ki dan jiya suma kikayi”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.
“Jikina da sauƙi Yah Moddibo.
Amma ni dai har yanzu gani nake Yah Jameel nane, duk da kowa ya yarda cewa ba Yah Jameel bane. Ni na kasa yarda”.
Kai ya girgiza still batare daya juya ba yace.
“Ba *J* bane Asma'u ba kiji na faɗa miki ba Jameel bane ina har rantse miki nayi”.
Kai ta gyaɗa kana ta fesar da numfashi bawai dan ta yarda ba sai dan batason yi masa musu yasa tayi ƙasa da kanta tare da faɗin.
“Toh shikenan Yah Moddibo”.
Still Idanunsa na farfajiyar gidan yace.
“Ina Innayi?”.

Ahankali tace.
“Suna can tukunna nima an turo nine inzo in faɗawa Khausar ta shirya masu zuwa yi mata lalle zasu zo su fara yi mata shiyasa nazo”
Ta ƙarashe maganar tana kallon Khausar dake ta faman lumshe idanu
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Ok”.
Daga nan ya juya yabi ta bayan Asma'u batare da ya yarda sun haɗa ido ba ya fita.
Asma'u kuwa idanunta akan Khausar tace.
“Khausar wai ki shirya masu zuwa yi miki lalle zasu zo inji Lalla Khadijah”.
Ta ida maganar tana kallon Khausar sai kuma ta juya Idanunta tsakiyar Falon ganin tuni Moddibo ya fita yasa.
Ta gyaɗa kai tana lumshe idanunta tace.
“Toh shikenan sai sunzo”.
Murmushi Asma'u tayi kana tace.
“Iyeee lalle Yah Moddibo har an fara biyo hanya kenan?”.
Hararanta Khausar tayi tare da cewa.
“Ban gane ya fara biyo hanya ba”.

Dariya Asma'u ta sanya kana tace.
“A gani nayi ya fara zirya shiyasa.
Acan Falo naji Lalla Khadijah na cewa ayi agyaraki ayi miki lalle da turaraki, da sauransu dan gobe za'a kai ki Side ɗinki inda zaku zauna aima gwara ayi akai ki tunda ya fara zirya”.
Hararanta Khausar tayi tare da faɗin.
“Wani irin ya fara zirya kefa Asma'u baki da mutunci.
Yanzu ina kina ji ce miki yayi yazo ya duba ki ne da jiki ni tunda yazo ko magana ya min ne ma?”.

Dariya Asma'u ta sanya ganin duk maganar da take jikinta ba kuzari sai wani irin fitinennen miƙa da takeyi da sauƙe ajiyan zuciya, cikin dariyar tace.
“Toh waya sani abu a duhu wannan ba tsakanin ku ba, ni ƙanwar miji ƙawar amarya me nawa aciki”.
Fitowa Hajja Nana tayi daga bedroom kasancwar tana jin duk abinda Asma'u ke faɗa tana hararan Khausar tace.
“Faɗa mata dai Asma'u Munafuka ai Ni yau naga abinda yafi ƙarfin idanuna ashe-ashe yanzu ko ba muga ruwan sama ba kada muyi mamakin abinda bai kawo saba fitsaran da ake zubawa ne”.
Dariya Asma'u ta sheƙe dashi ganin Hajja Nana tsakaninta da Allah take maganar sassauta dariyata tayi tare da cewa.
“Hajja Nana me sukayi?”.
Zare idanu Hajja Nana tayi tare da kallon dining ɗin kamar dai har zuwa lokaci ganin su take kana tace.
“Menene ma basuyi ba Asma'u, yaro idanu asoye wannan ɗa yaban mamaki”.
Sosai Asma'u ke dariya kana tace.
“Yo Hajja Nana bake kike cewa ba zaki koma ba sai kin tabbatar yana sonta ko baya sonta ba”.
Haɓa Hajja Nana ta riƙe da alama har yanzu mamakin bai bar ranta ba tace.
“Eh lallai kam naga alama zai nuna min ƙashin tijara kenan”.
Kallon Khausar data zubawa dining ido Asma'u tayi kana ta maida idanunta kan Hajja Nana tare da cewa.
“Kai Hajja Nana kar kiyiwa Yah Moddibon mu sharri mutum ne mai kunya”.
Kai Hajja Nana ta gyaɗa kana tace.
“Ai kam dai ni naga kunya, ganin idona.
Ni nasan yana da kunya naga kuwa Kunya ganin Idona har gudu yake a idanunsa”.
Ta ida maganar tare da jan tsaki ta juya kana tace.
“Shegun Yara”.
Shiru Khausar tayi tare da bin Hajja Nana data shige bedroom da ido.

Asma'u kuwa har takai bakin kofa ta juya ta kalli Khausar tare da faɗin.
“Yawwa Ummi tace In faɗa miki ki ɗauki wannan sauran damun da aka miki ki ɗauka ki shanye”.
Langwaɓar da kai Khausar tayi cikin sanyi murya tace.
“Wallahi nikam na gaji da ɗure-ɗuren nan shiyasa bana iya kocin abinci aɗura ma wannan aɗura ma wancan”.
Murmushi Asma'u tayi tare da faɗin.
“Idan baza kisha ba Ni kibani in sha dan Ni gyarane tun daga yanzu sai In fara yiwa wanda zan Aura ba ruwana”.

Zama Khausar ta gyara kana tace.
“Kinji jiki wallahi, kema idan naki yazo ana ƙaƙaba miki bazaki shaba”.
Ware idanu Asma'u tayi tare da faɗin.
“Wallahi sha zanyi Ni kuma irinki ne? Kin san dama ni inaso abun zaƙi-zaki ke kuma kin fison abu mai ɗan yaji-yaji, sai ki zauna kiyi ta noƙe-noƙe baza ki shaba”.
Tana gama maganar ta juya ta tafi.

Bayan tafiyar Asma'u da minti talatin masu yiwa Khausar Lalle suka zo.
Cike da ƙwarewa da sanin aikinsu suka fara Cancaɗa mata jan lalle cikin tafin hannu da baya kana suka yi mata manyan flowes abinka da faran fata atake tayi wani masifar kyau.
Kana sukayi mata atafin ƙafa zuwa sama wani irin kyau na ban mamaki yayi tun kafin a wanke ita kanta Khausar kallon lallen take tamkar wata sarauniya.
Ɗaya daga cikinsu ta dawo bayanta cikin harshen Larabci tace.
“Kiyi haƙuri zamuyi abayanki”.
Ɗan ware idanu Khausar tayi kasancewar tana jin larabci tace.
“Harda baya kuma?”.
Kai mai Lallen ta gyaɗa mata tare da faɗin.
“Eh harda baya ma”.
Ta faɗa tare da zuge zip ɗin rigar ta fara zana mata wani irin zanen ɗawisu mai masifar kyau da ƙawa kana ta dawo ta gaba asaman ƙirjinta ta zana mata wani siririn star kamar Tatu nan kyawunta ya sake fitowa ta zamo tamkar sarauniyar kyau...
Sai gab Maghriba su Innayi suka dawo dai-dai lokacin da masu lallen ke shirin fita kallon Innayi tayi tare da cewa.
“Idan lallen ya bushe baku zaku wanke mata ba ku bari zamu zo mu haɗa mata ruwan wankewan”.
Kai Innayi ta gyaɗa kana suka shige.
Bayan sallar Maghriba suna dawo suka wanke mata lallen...

Acan Abuja Birnin tarayya kuwa Amina ce zaune a tangamemen Falon ta yayin da Uncle Naseer ke gefenta ba suyi sallar Maghriba ba kuma basu shiryawa tashi yiba.
Ahankali ya shafo fuskarta tare da cewa.
“Nayi missing naki”.
Hannunsa dake shafa fuskar tasa ta riƙe tare da faɗin.
“Nima nayi missing ɗin ka Uncle Naseer yau fa tun safe daka fita baka dawo ba”.
Yana binta da wani shu'umin kallo yace”.
“Na ɗan yi tafiya ne Shiyasa”.
Ashagwaɓe ta marairaice fuska tare da faɗin.
“Uncle Naseer ina kaje?”.
Fuskanta ya tallafo kana ya motsa laɓɓansa kusa da kunnenta yace.
“Wajen abokaina naje”.
Kafin tace wani abu ya janyota jikin tare da kissing ɗin wuyanta yana shinshina sassan jikinta kafin ahankali ya zuge mata zip ɗin rigar ta tare da kama Breast ɗin ta yana sarrafata cikin ƙwarewa tashiga mayar masa da martani ƙasa ya zamo daita kana cikin zafi-zafi suke romance juna har suka biyawa junansu buƙata anan falon yana gama ya tashi ya shiga dakin da tunda suka zo bai barta ta shiga ba ko fita zaiyi saiya rufe wanda kuma lokuta da dama tana jin huci daga cikin ɗakin amman koda ta gaya kishi bai kulataba, da wannan tunanin itama ta miƙewa ta nufi ɗakinta...

*Morocco*
Bayan an idar da sallar Maghriba matan da sukayi mata lallene suka shigo suka haɗa mata ruwan da zatayi wanka ruwane me masifar kyau da ƙamshi koda tayi wankan ta fito wani irin sheƙi da ƙamshi take bazawa lallen ya kwanta akan farin fatar ta da yayi smooth ta dawo kamar wata tarwaɗa fatan ta sai haske da ƙyallin Amarci yake.
Already tayi alwala kafin ta fito zama tayi awani kujera suka fara turara mata jikinta da turare bayan sun gama suka fara turara mata gashinta da wasu masu daɗin ƙamshi nan da nan gashin ya dauki sheƙi da haske..
Kai tsaye ta nufi bedroom ta gabatar da sallar Maghriba kana tana zaune har aka kira Isha'i ta idar Misalin ƙarfe goma Ummi ta kalli Khausar hannunta riƙe da Damun data dama kana tace.
“Gashi ki karɓa kisha”.
Ahankali Khausar ta ɗaga idanunta ta kalleta cikin yanayin kasala da baƙon lamarin dake ratsa jikinta ta fesar da numfashi tare da cewa.
“Ummi wallahi cikina ya ƙoshi bazan iya shaba”.
Ummi na kallonta tace.
“Bana son haka Khausar kar kiyi min musu tun bayan la'asar nace Asma'u ta faɗa miki kisha.
Ni nayi tsammanin kinsha ashe baki sha ba”.
Karɓa tayi cikin kasala da sanyi ta motsa laɓɓanta tare da cewa.
“Wallahi Ummi baki daya shi yake cika min cikina shiyasa ko abinci bana iya ci aɗuramin wannan aɗuramin wancan abarni haka mana In huta”.
Harara Aunty Hajara ta watsa mata cikin ɗaure fuska tace.
“Zaki karɓa kisha ko kuma saina ɓata miki rai”.
Cike da tsoronta ta karɓa tasha kamar zatayi kuka...

Hajja Nana dake kallonsu tace.
“Hmmm Allah ya kawo saukin wato wai yanzu duniya ta kai duniyar da har ɗuwawu yana da kwallinsa wai in zaku Aurar da ƴaƴa kuyi ta musu shungullah da hidima”.
Murmushi Innayi tayi tare da faɗin.
“Toh ai tun zamanin mu da ɗin ma ana gyara kam sai dai inke bakiyi gyara ba amma tun da kam ana gyara”.
Wani kallo Hajja Nana ta watsa mata tana gyara zama tace.
“Kyanuna min gyara kema Baiwa kikace kinsan gyara bare mu matan Sarakuna”.
Dariya Innayi tare da shewa ta tafa hannu kana tace.
“Da ne nake baiwa yanzu kin manta agaban idonki aka ƴantani ai yanzu dai-dai nake dake”.

Zare idanu Hajja Nana tayi tare da cewa.
“Za dai kiyi dai-dai dani amma bazaki taɓa dai-dai dani ba ai wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa”.
Kallon Hajja Nana Khausar tayi kana tace.
“Kiyiwa Allah da Annabi Hajja Nana kada araba hali dake a ƙasar da ba naki ba nan fa ba muhallin ki bane ba kuma cikin ƙannenki kikeba”.
Cikin sanin halin Hajja Nana Innayi ta kalli Khausar cike daso tace.
“Yi shiru abunki barni da ita, ai in da sabo tuni na saba”.

Baki sake Hajja Nana ke kallon Khausar kafin ta harareta da faɗin.
“Iyyeee kaji shegiyar Yarinya.
Toh naji ke kam muhallinki ne ai nan ɗin gidan Ubanki ne ko da zakice ba muhalli na bane”.
Lumshe idanu Khausar tayi tare da tura bakinta kana tace.
“To ko ba gidan Ubana bane ai gidan mijinane kam”.
Tafa hannu Hajja Nana tayi tare da Salati ta sanar da Ubangji kana tace.
“Eh ba shakka ba ƙarya wato ɗazun da yazo zugaki yayi ya Fom-famkaki ya zizzira miki”.
Cikin lumshe ido Khausar tace.
“Me kuma zai zira min?,Ya ziramin kamar wata rijiya”.
Ummi da Aunty Rukayya da Hajja Umma kam dariya sukeyi dramer Khausar da Hajja Nana baya ƙarewa.
Hajiya Bunayya kuwa Ayatsine ta kalli Khausar tare da jan tsaki kana ta kawar da kai gefe...

Asma'u kuwa ka faɗan Khausar ta dafa tare da faɗin.
“Allah yaja da Zamanin Matar Sarki”.
Murmushi Khausar tayi tare da Fari da idanu kana tace.
“Aaa faɗawa tsohuwa dai taji”.
Cikin mamaki da sarewa da halin Khausar Hajja Nana tace.
“A lallai kin samu baki Munafuka, ai ɗazu kam kuka kika tayi sai da na rarrasheki.
Amma yanzu saboda kinga kuna tare shiyasa kike min haka toh zasu tafi kuma har nima tafiya zanyi na fasa zama, tunda kwaye min baya zakiyi”.
Dariya Asma'u ta sanya tare da faɗin.
“A'a Hajja Nana baza ayi haka ba dan Allah kiyi haƙuri ki zauna”.

Mutsike idanu Hajja Nana tayi tana hararan Khausar tace.
“Wallahi bazan zauna ba tafiya zanyi waɗannan fitsararrun ai in mutum ya zauna babu abinda ba zasuyi agaban idanunsa ba”.
Jin abinda tace yasa Khausar langwaɓar da kai cikin sanyin Murya tace.
“Don Allah dan Darajar Annabi Hajja Nana na mu zauna mana kada ku tafi ku barni ni kadai”.
Sai kuma ta maida idanunta kan Ummi tare da cewa.
“Ayyah Ummi dan Allah za'a bar Asma'u anan ina?”.
Sai ta kuma juyawa ta kalli Hajiya Bunayya kana tace.
“Umma dan Allah ki barmin Addah Asiya”.
Cike da tsanarta Hajiya Bunayya tace.
“Eh dole abar miki su dole sai tunda su ba aure zasuje suyi ba”.
Araunane ta girgiza kai tare da faɗin.
“Ayyah ba haka bane dan Allah Ummi ku bar min su”.
Kai Ummi ta girgiza kana tace.
“A'a Khausar kada muyi haka dake.
Kada ma mufara haka dake”.
Rau-rau tayi da idanunta yayin da ruwan hawaye suka cika alamar gan take da fara kuma.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da faɗin.
“Um-um ki kwantar da hankalin ki kada kiyi kuka ai Asma'u kuna tare”.
Murmushi tayi Ummi kuwa miƙewa tayi ta nufi bedroom ɗin ta...

Agefen Moddibo kuwa tun da ya koma sashen sa ya samu Ibraahim da Zakariyya suna zaune batare daya kalli inda suke ba ya wuce bedroom ɗinsa ya kwanta akife kana ya runtse idanunsa baki ɗaya ilahirin jikinsa rawa yake wani irin Masifeffen feeling yake ji na fitar hankali.
Ji yake tamkar ya ɗaura hannunsa aka yaita zunduma ihu ko zaiji sassaucin abinda yakeji.
Wani irin tsuma jikinsa keyi da dama da zai iya yin sex da katifar koda zaiji sassaucin abinda yake ji juyi kawai yake akan katifar cikin tsananin feeling dake addabar sa yayin da *A* ɗin sa ya miƙe tunda yake bai taɓa jin azabebben feeling irin na yau ba baki daya na yau ya bambanta da duk na sauran lokutan da yake ji.

Dr Jameel ne ya shi lokacin alwalan sallar Maghriba ganin yanda yake murƙususu yace.
“Ya dai tun ɗazu nazo Ibraahim suka cemin kashiga ciki kana kwance lafiya dai?”.
Shiru Moddibo yayi dan ya tabbatar idan yace zai buɗe baki yayi magana kuka ne zai kufce nasa koda kuka bai kufce masa ba to Muryansa bazai fita.
Sake matsawa jikin gadon Dr Jameel yayi kana yace.
“Lafiya kuwa? Na tafi na Barka ɗazu lafiya kalau kuma yanzu tunda nazo kana kwance”.
Ya ƙara sa Maganar tare da taɓa wuyan zafi rau ya ratsa hannunsa.
Cike da kulawa yace.
“Subhanallah baka da lafiya ne?”.
Araunane Moddibo ya kallesa kana ya girgiza kai tare da cewa.
“Nima ban sani ba”.
Ya ƙare maganar cikin ruwar murya.
Da mamaki Dr Jameel yace.
“Kamar ya baka sani ba baza ka rasa sanin meke damunka ba mana?”.
Shiru Moddibo yayi yana murƙususu.
Ganin yanayin da yake ciki sai ƙaruwa yake yasa Dr Jameel cewa.
“Ko dai zamu tafi asibitine, kaga yanayin ka baki ɗaya jikin ka rawa yake ga zufa da kake fitarwa duk da sanyin da ake”.
Still shiru Moddibo ya masa.
Dr Jameel kuwa hannu yasa tare da yaye blanket ɗin daya rufu ware idanu yayi ganin yanda *A* ɗin sa ya miƙe kamar zai fasa wandon Jeans ɗin ya fito.

Dariya Dr Jameel ya fashe dashi harda riƙe ciki kana yace.
“Ashe dai bani kaɗai bane mayen matan, kaiɗin ma gashinan ka gaza haƙura, yanzu ka dubi yanayin da kake ciki to kai me matsalar ka tunda ga mata an kawo maka zuwa anjima dai kuna tare”.
Hararansa Moddibo yayi kana yace.
“Kai fa ɗan Iska ne”.
Still Dr Jameel na dariya yace.
“Ƴan Iska dai zakace.
ai kai kam ma wa ɗan'nan shaiɗanun idanunka masu cike da shu'umaci sai ka casani, toh ni nama isa inyi ko rabin abinda idonka ke nunawa ne ko amafarki ban isa in aikata abinda zaka aikata ba dan wlh in ka ritsar ƴar mutane zata gane kurenta”.
Lumshe idanu Moddibo yayi tare da hararansa kana yace.
“Kamar yaya mene aikata? yanzu Jameel kai duk abinda kake aikatawa kace ko rabin abinda zanyi baza ku aikata ba ko amafarki amman wlh ka cuceni?”.
Kai Dr Jameel ya jinjina tare da cewa.
“Sosai ma kuwa”.
Cikin yanayin gajiya da maganar da kuma feeling dake addabar sa ya miƙe dare da yin miƙa atake *A* ɗin sa ya kuma miƙewa duk da wandon Jeans ne ajikinsa saida ya nuna.
Dariya Dr Jameel ya sheƙe dashi kana yace.
“Toh da ace baka da mata ne sai ince zan baka magani ko kuma In maka allurai dan wlh in ace zaka rayu na wata ɗaya a haka Allah ne kaɗai yasa adadin matan da zaka danne.
to amma Alhamdulillah ba wannan duk cikin biyun tunda ga matarka nan shikenan nan magana ya ƙare”.
Hararansa Moddibo yayi yana ƙoƙarin dai-dai-ta nutsuwarsa.
Murmushi Dr Jameel yayi kana ya ɗage masa giransa tare da cewa.
“Kamayi Sa'a ɗazun na biya sashen Didi naji tana cewa gobe In Sha Allah za'a kai maka matarka sashenta dama already an gama gyarawa”.
Hararansa Moddibo yayi kana ya wuce ya shiga toilet bayan ya fito suka tafi Sallah koda aka idar da Maghriba basu dawo ba sai da akayi Isha'i.
Haka ya kwana baiyi bacci ba sai juyi yake saboda tsananin feeling da fitinar dake addabar sa baki daya ya rasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali da Zaran ya lumshe idanunsa zai tuna moment ɗin da suka kasance a dining sai ya riƙa jin tafin hannunsa kamar yana yawo acikin nata wani irin azabebben tsuma jikinsa keyi baki daya *A* ɗin sa ya takura sa a duk sanda ya tuna yadda take shafa hannunta bisa sajenshi sai yaji kamar zai zauce...

Acan ɓangaren Khausar kuwa kwance suke a bedroom su uku Khausar, Asma'u sai Dije.
Juye-juye Khausar keyi tare da jan tsaki bini-bini zataja tsaki.
Ahankali Asma'u ta janyo wayarta tare da duba time taga 1:00am juyawa tayi ta kalli Khausar tare da faɗin.
“Khausar ya dai?,Lafiya kuwa naga tun ɗaxu sai tsaki kike ba kiyi bacci ba?”.
Kai Khausar ta girgiza cikin sanyi murya tace.
“A'a bakomai”.
Ido Asma'u ta tsira mata tare da cewa.
“Ya zakice ba komai gashi tun ɗazu sai juye-juye kike”.
Lumshe idanu Khausar tayi kana tace.
“Da gaske bakomai kawai dai bacci be bai zo idona ba shiyasa”.
Kallonta Asma'u ta kuma yi kana tace.
“Amma kuma dai lafiyar ki ƙalau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login