Showing 99001 words to 102000 words out of 218703 words

Chapter 34 - Sakayyah 2 Hausa Novel Complete

da faɗin.
“Ke dai Amina bari wallahi dana san haka daular nan take da mu mukayi sihiri kika Auri Moddibo”.
Amina dake zaune acikin wani ƙaton falo na al'farma a Abuja tayi murmushi tare da faɗin.
“Umma kada ki damu nan ma wallahi muna cikin daula kinga gidan da aka kama nin kuwa, dan dai baki zo kinga gidan da aka kawo ni bane gidane mai masifar kyau na nunawa sa'afa”.
Sai kuma ta juya idanunta tare da kallon mashshurin falon nata kana ta cigaba da cewa.
“Kinga manyan falona guda biyu da 3bedroom atsakiyar birnin Abuja fa muke inda muke ma ai alhamdulillah kuma kin manta muma zamu tafi Indi'a ne kwanan nan da Uncle Naseer”.
Dogon tsaki Hajiya Bunayya taja kana tace.
“Ke bakiga daular dake cikin nan bane shiyasa kike faɗin hakan”.
Murmushi Amina tayi tare da faɗin.
“Umma kema fa bakisan daular da nake ciki bane ki kwantar da hankalin ki in kin dawo kinzo zaki sha mmaki”.
Cikin gaskata wa Amina ta cigaba da kwantar wa da mahaifiyarta hankali kana ta ɗaura da faɗin.
“Umma kada fa ki manta muma Indi'a zamu tare kuma Indi'a ma ai tafi Morocco sanuwa da suna”.
Kai Hajiya Bunayya ta girgiza kana tace.
“Hmmm Amina kenan ta yaro kyau take bata ƙarko, abine da baki gani ba, duk labarin da zan baki bazaki gane bane irin cigaba, da nasara, wadatar da Khausar ta riska awannan masarauta ya wuce zatonki”.
Sai kuma ta ha ɗiye wani yawu mai masifar ɗaci kana ta cigaba da cewa.
“Bazaki taɓa fahimtar abinda nake faɗa ba har sai idonki ya gane miki.
Yoh Naseer da ko Sarkin Tasha Uban sa bai taɓa mulka ba, ina za'a haɗashi da Modibbo, kina sane da cewa Khausar kuwa mijinta shine Yarima mai jiran gadon mulkin Ƙasar Morocco gaba ɗayanta fa, sannan kuma shine babban ɗa Namiji awajen Mahaifinsa”.
Amina dake zaune ta dafe ƙirji cike da ƙyashi da hasadar jin matsayi da kuma nasaran da Khausar ta samu.
Hajiya Bunayya kam cikin ƙunan zuciya da tarin hassada ta cigaba da faɗin.
“Wannan tsinanniyar tsohuwar Innayi ta cucemu data ɓoye mana wannan al'amari nasarar Modibbo da mun san da wannan nasaba da yake dashi haka ai wallahi ko zan tafi tsirara ne wlh sai kin Auri Moddibo”.

Zazzafan Ajiyar zuciya Amina ta sauƙe kana tace.
“Umma ke kam kada ki damu”.
Kai Hajiya Bunayya ta girgiza ji take kamar ta ɗaura hannu aka tayi ta zunduma ihu cikin damuwa tace.
“Ya bazan damu ba Amina dole in damu gaba ɗaya hankalina ya tashi baƙin ba, yanda ban samu ba suma su rasa Wallahi, duk yanda zanyi Amina nayi miki al'ƙawarin sai na raba Auren Khausar da Moddibo ko ana Hamaza ha mata.
In dai dawo Nigeria ne kawai yafi wuya”.
Cikin sauƙe numfashi Amina tace.
“Gaskiya dai nima yanda kike zuzuta wannan cigaban nata, da dai ta wuceni gwara a kaso Auren nata ta dawo gida ta zauna”.
Yamutse fuska tayi tare da gyara zamanta kana ta cigaba da cewa.
“Ƴar banza agola kawai tazo tafi ƴaƴan masu gida nasara”.
Ƙwaffa Hajiya Bunayya tayi kana tace.
“Ke dai bari”.
Dai dai lokacin da Asiya ta fito daga wanka kallonta tayi tare da girgiza kai cikin yanayin sanyinta tace.
“Hmmmm Allah ya kyauta”.
Alalace ta kalleta tare da faɗin.
“Toh shegiya mai baƙin hali meye?
Ƴar masu matacciyar zuciya da bakisan abinda yake miki ciwo ba sai wani yaƙe baki kike kina murmushi adole kinga nasarar wani”.

Tana zama gaban dreesing mirror tace.
“Umma idan har bakayi baƙin ciki da nasarar wani ba kaima Allah zai kawo maka naka narasan”.
Ahantare Hajiya Bunayya ta harareta tare da cewa.
“Dalla can rufe min baki,Ki ɓace min daga ɗaki”.
Kai ta gyaɗa tare da ficewa daga dakin kasancewar tasa kayanta kai tsaye ɗakin su Khausar ta nufa...

Acan ɓangaren Moddibo kuwa bayan sun Sheykh Jabeer sun tafi. suka cigaba da gaisawa da Manyan baƙi.
Har aka kira La'asar bayan an idar da sallar La'asar baki ɗaya baƙi suka tafi anci ansha wasu irin abinci na alfarma aka dafa wanda ma'aikatan manyan restaurant aka ɗebo sukayi girkin gargajiya dana zamani domin afita kunya.
kuma Alhamdulillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Moddibo kuwa gaba ɗaya wunin yau ɗin duk abinda yake Khausar ce ke faɗo masa arai da Zaran ya lumshe Idanunsa zai tuna sanda ya rungumeta yana budewa kuwa lokacin da yake wanke mata hannu acikin Madarane ke masa gizo duk wani abu da yake dauriya kawai yake.
Yayin da wani ɓangare na zuciyarsa ya tafi ga halin da Asma'u ke ciki kasancewar har suma tayi a daren jiya kana ko bayan barinsa sashen da sukenma bata cikin nutsuwarta, tun safe yaso zuwa dubata amma bai samu ba saboda hidindimu da suka yi masa yawa...

Acan Falon su Khausar kuwa suka zaune Jakadiya ta shigo bayan sun gaisa ta kalli Innayi tare da cewa.
“Innayi Didi na buƙatar ku baki ɗaya asashenta amma banda Khausar sannan abarta da mutum ɗaya kada ta zauna ita kaɗai”.
Kai Innayi ta jinjina tare da cewa.
“Toh ba damuwa sai abarta da Hajja Nana”.
Ta ida maganar tare da miƙewa ta nufi ƙofa yayin da Hajiya Bunayya,Aunty Ruƙayya, Aunty Hawwa, Aunty Hajara Asiya, Dije suka mara mata baya.
Kai tsaye suka nufi sashen Didi bakinsu ɗauke da sallama suka shiga tangamemen Falon suna shiga idanunsu ya sauƙa akan Wasu Mashahuran Akwatuna set biyar ko wannen kalansa da ban.

Lalla Khadijah ne ta ɗaga kai tare da kallon Innayi kana tace.
“Ku shigo ku zauna mana”.
Murmushi Innayi tayi kana suka shiga suka zazzauna akan lumtsa-lumtsan kujerun na al'farma.
Ɗaya daga cikinsu ne Yayar Didi wacce ta kasance ƴar farinsu ce Mai suna Afreen wacce kira da Ashshe matsawa tayi suka gaisa kana cikin sakin fuska tace.
“Toh Alhamdulillah ga lefe nan mun gama haɗawa na.
Amaryanmu so mun kira kune kuzo ku gani in Sha Allah za'a bawa Hadimai su kaishi Side ɗin da zasu zauna ne”.
Cike da tarin farin ciki Innayi ke kallon Set ɗin akwatunan kana tace.
“Masha Allah Alhamdulillah”.
Ummi kuwa cikin yanayin farin ciki tace.
“Kai masha Allah wannan duka lefene!?”.

Lokaci ɗaya Hajiya Bunayya ta nemi ƴar nutsuwarta ta rasa atake yanayin fuskarta ya rikiɗe afili zuwa hassada da ƙyashi ta kasa ɓoye baƙin cikinta.
Cikin fusata taja wani dogon tsaki tare da sauƙe numfashi wanda yaja hankali da yawa daga cikin mutanen falon suka kalleta.
Asiya dake gefenta tayi saurin dafa kafaɗarta ganin yanda ake kallonsu yasa tace.
“Umma lafiya?”.
Kai ta gyaɗa tare da yamutse fuska kana tace.
“Ƙirjina ne yake ciwo sai to kareni yake”.
A yatsine Lalla Hafsat ta kalleta tare da cewa.
“Ok ba matsala bari na kira Dr Jameel yazo ya duba ki da jiki sai ya baki magani”.
Ta ƙare mgnar a yaysine dan har ga Allah matar bata konta mata a raiba....



Littafin SAKAYYAH dai na kuɗi ki biya ki karanta cikin Aminci.


By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 19*

Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha'awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni'ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al'ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban lissafa. Sune manyan alamomin infection.
Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.
Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni'ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwatanta Zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.
KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni'imomin ki, da sha'awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA'AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau, duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha'awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor's suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa.
INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi'izinillahi ta'ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma'ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya'ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER'N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA'AURATA.



Cikin sauri ta girgiza kai tare da faɗin.
“A'a Nagode inada magani in mun koma zansha”.
Baki Lalla Hafsat ta taɓe kana ta fara buɗe musu Set ɗin akwatin farko na ƙasan idanunsu suka sauƙa akan wasu EGYPT Abaya masu masifar kyau da tsada baki daya cikin akwatin cike take da Abayas kala daban-daban kama daga Turkey Abaya, Itally Abaya, Dubai Abaya Wanda aƙalla zasu kai arba'in sai kuma ɗaya akwatin dake ɗauke da wasu Samfarin laffaya masu masifar kyau da tsada wanda zasu kai hamsin, sai mai binshi kuma Jakankuna da takalma masu shegen kyau da tsada sunfi set shabiyar ɗayan kuma mayafaine da mai binshi Sleeping drees masu shegen kyau da ɗaukan hankali yayinda da mai bi masa ɗan ƙaramin ke ɗauke da sarƙoƙin Gwal da ɗan kunnayensa da, kuma murjani irin na Masarautar, haka aka riƙa buɗe musu Set ɗin farko har ƙarshe ana shiga na biyun suka sake gyara zama domin ganin abin na yine, nan sukaci gaba da kallo...

Dai-dai lokacin kuma Moddibo suka dawo shida Ibraahim da Zakariyya suna shiga Falonsu kai tsaye bedroom Moddibo ya nufa kallonsa Ibraahim yayi tare da faɗin.
“Ya dai Yah Aleey?”.
Cikin fesar da numfashi Moddibo ya kallesa kana yace.
“So nake in ɗan watsa ruwa ne baki ɗaya yau atakure nake”.
Kai ya gyaɗa da faɗin.
“Toh ba matsala”.

Cike da kasala Moddibo ya nufi toilet ya watsa ruwa ya fito bayan ya fito ya shafa mai tare da feshe jikinsa da turaruka masu daɗin ƙamshi kana ya sanya Jeans Blue da Farin Riga mai guntun hannu yalwataccen sumar kansa zuwa kwantaccen sajensa yasha gyara yayin da jikinsa ke fitar da wani sihirtaccen ƙamshi.

Ibraahim da idanunsa ke ƙofar bedroom yace
“Wowww Yah Aleey dama haka ƙananan kaya ke masifar yi maka kyau tun da na kazo ban gaba da ƙananun kaya ba sai yau ni nai zatonma ko baka sawa ne”.
Murmushi Moddibo yayi tare da shafa sumarsa kana yace.
“Ina ɗan sawa time to time, so nake in ɗan sake dan naji yanayin garin yau kamar akwai ɗumi”.
Ya ida maganar tare da nufar kofar fita a falon yana mai ƙara matse jikinsa da Jeans ɗin da yasa don ya ɓoye yanayin da yaje ciki.

Zakariyya dake zaune yayi saurin cewa.
“Ya dai ina zaka je”.
Lumshe idanu Moddibo yayi tare da buɗe su akansa kana yace.
“Zan ɗan fita ne dama ina so zan duba Asma'u”.
Ajiyar zuciya Zakariyya ya sauƙe tare da cewa.
“Ok dama ina so mu ɗanyi magana ne dan gaskiya gobe nake tunanin zan wuce amma yanzu akwai dalilin da zai tsadani”.
Anutse Moddibo ya gyara tsayuwar tare da faɗin.
“Wace magana ce?”.
Zakariyya na kallonsa yace.
“Naga kamar kuma sauri kake”.
Kai Moddibo ya girgiza tare da cewa.
“A'a In ba mai daɗewa bane ina jinka”.
Zama Zakariyya ya gyara kana ya kalli Moddibo tare da cewa.
“Toh kazo ka zauna mana”.
Baya Moddibo ya dawo kana ya zauna gefensa.

Numfashi Zakariyya ya fesar kana yace.
“Gaskiya nima fa naga matar Aure acikin ƙwayen Amaryanka”.
Da mamaki Moddibo ya kallesa kana yace.
“Wacce fa?”.
Hannu Zakariyya ya buɗe tare da faɗin.
“Naji dai jiya kamar ana kiranta me ma? Na dai manta sunan amma wata ƴar doguwa haka dai fara mai sanyi”.
Ahankali Moddibo yace.
“Ko dai Asiya?”.
Yatsu Zakariyya ya ƙyasta da murmushi afuskarsa yace.
“Yes of course ita, Ita nake nufi naga ta kwanta min dan tana da nutsuwa ni gaskiya yanzu bani da wani tunani in ba nata ba”.
Murmushi Moddibo yayi wanda ya sake bayyanar da kyawun fuskarsa kana yace.
“Toh Lallai dai kam toh ba laifi in Sha Allah zanyi nazari akai.
Amma yanzu bari inje idan na dawo zanyi nazari akai sai muyi maganar”.
Numfashi Zakariyya ya fesar tare da faɗin.
“Toh shikenan ba matsala amman dai ka sani ni ba irin Dr Jameel bane da zakace sai kayi nazari”.
Dariya kawai Modibbo yayi
Kana ya mike ya tafi...

Acan Falon su Khausar kuwa Hajja Nana ce kaɗai zaune adining area yayin da Khausar ta fito daga bedroom rabonta da abinci tun Breakfast har zuwa yanzu babu komai acikin sai tarin damun gumbuna da kuma garuka dasu tsumin masu ratsa jiki da cire yunwa da Ummi ka bata.
Sanye take cikin wani tattausan material Blue Black me ɗan ratsin Pinch daga saman rigar atsuke atake yayin daga ƙasan kuwa abuɗe yake daga ƙirjin rigan net ne haka ma hannun net ne tayi ɗaurin ɗankwali as-down yalwataccen sumar kanta ya kwanta luf-luf bisa goshinta ,duk da cewa ba tayi makeup ba Amma tayi masifar kyau farar powder ce kawai a fuskarta sai kwalli da ta zizara aƙwayar idanunta mai haske kaman Madaran sai kuma laɓɓanta yake shiƙin Man baki sai tafi to tamkar wata tauraruwa.

Kallon Hajja Nana dake zaune da.
Fruits agabanta tayi cikin sanyi jiki ta nufi ɗaya daga cikin kujerun Falon zata zauna cikin tsira mata idanu Hajja Nana tace.
“Zo nan?”.
Ɗan tura baki tayi cikin yanayin sanyin da tunda aka ɗaura aurenta ya ziyarceta tace.
“Menene?”.
Hararanta Hajja Nana tayi tare da cewa.
“Bace miki nayi kizo ba, toh kizo mana tunda na kiraki, ai in kinzo koma menene zakiji, ke da Allah yayiki ba'a miki abin arziƙi, sai yiwa mutum gardama?”.
Batare da tace Uffan ba ta nufi dining ɗin kana taja kujera ta zauna gefenta.
Cike da kulawa Hajja Nana tace.
“Meyesa bakya son cin abinci?”.
Langwaɓar da kai tayi tana wasa da yatsun hannunta, baki ɗaya tayi sanyi ahankali ta ɗago Idanunta dake ƙyallin hawaye ta kalleta.

Haɓa Hajja Nana ta riƙe kana tace.
“Ikon Allah kuka kuma zakiyi keda kika ce shi kike so? an kawo ki gidansa ai sai dai kiyita dariya da farin ciki bawai kuka ba”.
Kai ta girgiza Muryanta cike da rauni ta kalli Hajja Nana tare da faɗin.
“Baza ki gane bane Hajja Nana Ina kewar Momyna sannan ina kewar Raudat, kuma yanzu gashi Haiydar ma wai ance idan antashi tafiya dashi za'a yi akace”.
Kai Hajja Nana ta jinjina kana tace.
“Eh tafiya za'a yi dashi mana, dukansu ma tafiya zasuyi nice dai zan zauna”.
Jin abinda tace yasa farin ciki ya mamaye zuciyar Khausar ahankali tace.
“Da gaske zamu zauna Hajja Nana?”.

Kai Hajja Nana ta gyaɗa cikin yanayinta na ƙasaita da zafi tace.
“Toh badole in zauna ba tunda kece kika ce kina son shi, bashi bane yace yana sonki, ai dole in zauna In jira inga wani irin tarba zai miki, inga kamun ludayinsa,dan wlh Allah kenan In naga ya Miki abinda bai min ba duk da ke kikace kinji kin gani kina so wallahi ɗaukarki zanyi mu tafi tare”.
Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe tana kallonta cike da jin daɗi dan harga Allah ta fara tsoron a tafi a barta ba kowa nata tare da mutumin da in baici zalinta ba baya jin daɗi ta kuma san baya sonta.

Hajja Nana kuwa cike da izzah da ƙasaita ta cigaba da cewa.
“Na faɗawa Baffanki ma tun jiya ya fara cewa inyi haƙuri kuma Wallahi babu abinda zai tafiyar dani, zama daram anan sai naga yanayin kamun ludayinsa mutumin da an bani labarin tun a makarantar ma ba shiri kuke ba kinga ko nida tafiya sai naga abinda ya turewa buzu naɗi”.
Kai Khausar ta girgiza tare da sunkuyarwa ƙasa ita kanta ta san.
Moddibo baya ko ƙaunae ganinta kuma tafi kowa sanin tsanar daya mata baya son alaƙa da ita koda kallonta ne baya son yi”.
Hannu Hajja Nana ta sanya ta ɗago haɓarta kana ta tura mata Bowl ɗin dake ɗauke da Fruits ɗin gabanta da Mukara dake ɗauke da Juice kana tace.
“Gashi kici wannan koda baki ci Abinci ba shi zai ɗan taimaka miki, kinga gaba ɗaya ki rame”
Akuma dai-dai lokacin suka ɗaga kansu suka kalli ƙofan Falon jin Antura ƙofar an shigo...
Da sauri Khausar ta sunkuyar da kanta ƙasa ganin Moddibo Hajja Nana kuwa sallamarsa ta amsa tare da zuba masa ido.
Cikin ranta tace.
“Uhmmm

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login