Showing 36001 words to 39000 words out of 218703 words
jera mata sannu da kuma ɗan bubbuga bayanta kaɗan-kaɗan yana mmkin wasu al'amuran a ranta domin ya sani tsawon zamansu da J ta hanashi zuwa Marocco wanda bai san me dalilntaba, kasancewar sa ba mutum ne mai yawan bincikeba yasa bai taɓa mata musuba ko bincike.
Ahankali ya ke mata sannu cike da tausayawa takai kimanin minti biyar kafin tarin ya lafa sannu Ahankali ta fara maida numfashi.
Tana sauƙe ajiyar zuciya ta juya ta kallesa kana tace.
“Marocco!!!! kuma Aliyu?”.
Jinjina kai yayi cikin sanyin murya yace.
“Eh Innayi Marocco zanje amma idan har kin amince, idan bakya so, bazanje ba sai in bawa Abba haƙuri”.
Ahankali ta gyara zama tare da fuskantar sa da kyau kana tace.
“Toh amma mai zakaje kayi a can?”.
Tayi tambayar zuciyarta na mai cigaba da bugawa da ƙarfi.
Lumshe Idanunsa yayi tare da sauƙe Ajiyar zuciya kana yace.
“Abba ne ya nemi al'farma da Inje in kula da Company'nsa sannan kuma jiya daya zo nayi tunanin kunyi cikekkiyar maganar ne dashi kafin ku shiga wurina, shiyasa ni ban faɗa miki ba, ya nemi taimako da Inje in taimaka masa akan batun Company sa buga Abaya, jallabiya, Carpet, Sallayu blanket's da dai sauransu”.
Kallonsa kawai Innayi keyi yayin da take ji tamkar zuciyarta zai fito saboda yanda yake bugawa.
Cikin sanyi Moddibo ya riƙe Hannunta dake cikin nasa yace.
“Akwai sabbin injinan aiki da za'a sauƙe na Company, sannan kuma za'a fara aikin dasa Injina za'a kakkafa toh akwai ɓuƙatar sa ido da kuma kula da abubuwan, amma Insha Allah bazan wuce wata biyu zuwa uku ba zan zo Innayi”.
Girgiza kai tayi tare da jingina bayanta da jikin bango ta lumshe Idanunta kana ta shiga maida numfashi.
Moddibo kuwa ido ya zuba mata kana Asanyaye yace.
“Amma Innayi idan har bakyason Inje zan kira Abba in Faɗa masa yayi haƙuri”.
Uffan bata ceba kana bata buɗe Idanunta ba daga ita sai Ubangiji kaɗai suka san mai take tunawa aranta takai kimanin minti biyar ahaka kafin ta ɗago Idanunta ta kallesa kana taja dogon numfashi ta sauƙe tare da sakin Murmushin mai tarin ma'anoni sannan tace.
“Bazan hanaka tafiya ba Aliyu, domin ko baka tafi yanzu ba, dama lokacin tafiyar ya ƙarato. na amince kayi masa duk kan abinda Jameelu zai masa daya kasance araye, domin hakan zai rage masa raɗaɗin ciwon rashin Jameelu”.
Kai Modibbo ya gyaɗa yana kallon yanayin fuskartar ahankali yace.
“Toh shikenan Insha Allah zanyi hakan”.
Innayi kuwa kallonsa tayi kana cikin sanyin murya tace.
“Amma yanzu-yanzu tafiyar kenan Aliyu?”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Eh Innayi zanbi jirgi zuwa Abuja ne, in naga komai biza na ya fito zan wuce”.
Jinjina kai tayi tare da cewa.
“Shikenan Ubangiji Allah ya sanya alkhairi Allah ya tabbatar da alkhairi sai nazo”.
Saurin Kallonta yayi cike da Mamaki yace.
“Sai kinzo kuma?”.
Sunkuyar da kanta ƙasa tayi tare da Girgiza masa kai kana tace.
“Mantawa nayi sai ka dawo nake son cewa".
A hankali ya zaro ATM ɗinshi na Zenith Bank daga al'jihunsa, cikin tafin Hannun ta yasa matashi kana a hankali yace.
“Ga ATM ɗina na Zenith Bank, kin san pin number ɗin, akwai kuɗi a ciki kusan 5 Million”.
Da sauri tace.
“Ina ka samosu?”.
Gyara zamanshi yayi kana yayi mata bayanin yadda sukayi da Abba sannan ya ɗaura da cewa.
“Akwai wasu a wurina, wannan ki riƙe kiyi dukkan abinda kike buƙata kafin in dawo, in haɗasu muyi ƙoƙarin barin garin nan, domin ya fita raina”.
Yayi mgnar yana tuno kalaman Hajja Nana ita kuwa Innayi cike da sanyi tace.
“Uhmmm Aliyu in Sha Allah kamar ma mun barima ai kama barin kai kam”.
Cikin sanyi ya jinjina
Kai tare da miƙewa yace.
“Toh shikenan Innayi amma dai bakiyi fushi dani bako?”.
Da sauri tace.
“La la la Aliyu banyi fushi da kaiba”.
hannunta ya riƙo tare da ɗaurawa a kanshi kana yace.
“Toh kuma baki samin Albarka ba”.
Cikin sanyin Murya tace.
“Allah yasan ya Albarka Ubangiji ya tsare gabanka da bayanka Allah maidakai lafiya ya kuma tsareka da lafiyarka, Ubangiji ya rabaka da sharrin duk kan abin ƙi walau mutum ko aljan ko wani irin abune ya *Tsareka da Tsoffin magauta ya hanasu ganeka bare cutar da kai kafin isarka tushenka”.*
Lumshe Idanunsa yayi kana yace.
“Ameen ya Allah Innayi ni zan tafi”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh ka tsaya bari na zo".
Kai ya gyaɗa sannan ya tsaya ɗaki tashiga ba daɗewa ta fito sanye da hijabi, suka nufi wurin motarsa,
“Yau innayi zafa ki koma gidan Abba ko Ummi dan zamani ke ɗaya a nan bai minba”.
Cikin sauri tace.
“Eh toh gsky k nima ina tsoro Ni kaɗai a nan to amman, gsky gwara min gidan Ummin Jameel kaga ita kamar ɗiya take a gareni gidan Abba kuwa ba wani sabawa nayi da matansa ba, amman can zamu zauna ɗakin Asma'u nasam Malam Ahmad kuma baida matsala”.
Cikin gamsuwa da haka yace.
“Gsky kam hakan yafi, zan gaya Abban in kin gama haɗa kayanki Asma'u zata zo ku tafi”.
Kai ta jinjina cikin gamsuwa tace.
“Ba laifi”.
Jingina yayi da jikin motar bayan yasa jakarsa gefen mai zaman banza.
Ita kuwa Innayi a hankali ta matso kusa da marfin motar zira hannunta tayi ta ciki, zip ɗin jakarsa tabuɗe tasa jim kaɗan kuma ta maida ta rufe kana sukayi sallama ya mota ya tafi.
Kai tsaye gidan Ummi Moddibo ya nufa cikin nutsuwa yake Driving yayin da yake sauraran ƙira'ar Ahmad Sulaiman cikin suratul An'am yana isa gidan Ummi yayi Parking aƙofar kana ya fita ya shiga coumpund ɗin yana tafiya ahankali yana ɗaura ƙafarsa akan farandar sautin muryar Khausar ya ratsa Dodon Kukensa cikin sauri ya tsaya tare da rumtse idanunsa.
Sabida jin yadda tsikar jikinsa ya fara tashi tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar ƙwaƙwalwan kansa, ahankali ya jingina bayan sa da jikin bango yayin da zuciyarsa ta shiga bugawa da kaso Cassa'in da tara cikin ɗari.
Aransa yakeji kamar ya koma domin gaba ɗaya ya rasa meke sashi shiga wani yanayi da zaran yaji sautin Muryanta zaiji tamkar ana tsikara masa allura yama rasa ta wani irin yanayi zai misalta yanda yake ji akan yarinyar shin kunyarta yake ko kuma tsoronta yakeji, ko shakkarta shi kansa ya kasa tantancewa, taune Lip ɗinsa na ƙasa yayi da ƙarfi tare da buɗe idanunsa da suka sauya launi kana ya tura ƙofar falon tare da sallama yana mai tsare fuska.
Ummi dake zaune ta tsira masa ido tare da cewa.
“Babana har ka shirya kenan?
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Eh Ummi”.
Kana ya zauna agefenta ya zamana yana facing ɗin kichen.
Kallonsa Ummi tayi cike da kulawa tace.
“Amma dai ba kayi breakfast”.
Kai ya girgiza kana yace.
“Uhm-Uhm”.
Da Mamaki tace.
“Toh ya za'a ayi ka tafi da yunwa ba zaiyu ba Babana ba zaka tafi da yunwa ba”.
Langwaɓar da kai yayi tare da Marerece murya yace.
“Ummi bana jin yunwa fa”.
Fuska ta ɓata kana tace.
“Bafa zaiyu ba Babana baza ka tafi da yunwa ba”.
Khausar na fitowa daga kichen ta girgiza kai tare da kallon Asma'u tace.
“Toh ni zan tafi sai anjima”.
Da mamaki Asma'u ta kalleta kana tace.
“Bangane ba kamar ya sauri kike?
Dama ba nan kika zoba ne?”.
Khausar kuwa kai ta girgiza tare da kallonta kana tace.
“A'a ba nan nazo ba dama gidan Aunty Ruƙayya naje to da naje sai na sameta tare da baƙi shine na kira Mommy nace zan ƙaraso nan mu gaisa.
Mommy kam cewa tayi wai da safiyar nan zanzo”.
Moddibo kuwa tunda yaji sautin Muryanta akusa dashi ya kasa ɗauke idanunsa akanta duk da cewa kallon Kasan ido yake mata.
Cikin sanyi Khausar ta cigaba da cewa.
“Toh shine nace tayi hakuri ba daɗewa zanyi ba shine fa tace inzo amma kada in daɗe saboda mune da aikin rana zan koma in ta yata nazo muyi wata mgna ce, kuma nafasa”.
Da sauri Asma'u tace.
“Dan Allah muyita”.
Kai ta jujjuya tare da cewa.
“Ba damuwa in kin samu dama kizo zamuyita, yanzun sauri nake”.
Ta ida maganar tare ɗago kanta.
Idanunta ne suka sauƙa cikin idanun Moddibo.
Atsorace ta zira Idonta cikin nasa tare da juya su acikin nasa wanda hakan ya zama kamar hararansa tayi ita kuma cikin mamakin yadda ya rame ya wani zama shiru, ne yayi matuƙar bata mamaki da tausayi domin da dane da tuni ya danna mata harara.
Cike da tsoro ta janye kwayar idanunta daga garesa, tana mai mamakin sauyinsa rayuwa, cikin wani irin sauri ta nufi ƙofar falon yayin da jikinta ke tsuma Muryanta na rawa tace.
“Ummi ni na tafi”.
Kallon yanda ta nufi ƙofar Ummi tayi kana ta kallo Moddibo da har zuwa lokacin idanunsa ke ƙasa da mamaki tace.
“Ya da sauri kamar kinga Dodo?”.
Kai ta girgiza batare data juya ba tace.
“A'a Ummi nikam na tafi”.
Cike da kulawa Ummi tace.
“Toh ki tsaya Kiyi breakfast mana”.
Kai ta girgiza still jikinta na tsuma tace.
“A'a Ummi Allah Mommy na za tayi faɗa idan na daɗe”.
Jinjina kai Ummi tayi kana tace.
“Toh shikenan nagode ki gaida Mommy ki gashi kin ki kitsaya kiyi breakfast”.
Da sauri tace.
“Allah Ummi sai da nayi breakfast agida kafin na fito”.
Kai Ummi ta gyaɗa kana tace.
“Ki gaida Mommy naki da Raudat dasu Haiydar”.
Cikin sauri ta fice daga falon bayan tace zasuji.
Moddibo kuwa ahankali ya jinginar da kansa da jikin kujeran tare da lumshe Idanunsa kana ya cije Lip ɗinsa na ƙasa, sai kuma yayi saurin buɗesu sabida ganin surar jikinta da yayi ziraran miraran.
Gashi da zaran yaji muryan yarinyar zai riƙa jin wani irin abu mai wuyar fassarawa kana lokacin da ƙwayar idanunsu suka haɗu babu abinda suka hango masa face.
Ƙirjinta tamkar zasu tsole mishi idanu.
Asma'u Mommy tasa ta kawo masa ɗan waken da sukayi sai ruwan Tea ba laifi yaci danwaken da ɗan dama kana yasha ruwan Tea.
Malam Ahmad ne yashigo tare da yi masa addu'ar Allah ya tsare miƙewa yayi ya fita kana yaja tsohuwar motarsa zuwan gidan Abba yana isa yayi Hong mai gadi ya buɗe masa Parking Yayi aharabar gidan kana yashiga sashen Abba bakinsa ɗauke da sallama ya shiga falon Cike da kulawa Abba da Hajiya Turai dake zaune gefensa suka amsa masa.
Anutse ya ƙarasa tare da zama gefen Abba cike da kulawa Abba yace.
“Aliyu ka ƙara so?”.
Jinjina kai Moddibo yayi cikin sanyin murya yace.
“Eh Abba ina kwana ya ƙarfin jikin”.
“Jiki da sauƙi Aliyu”.
Bayan sun gama gaisawa Abba yayiwa Moddibo duk kan wasu bayanai kana ya bashi wasu takardu da duk wani abu daya kamata sai da Abba ya masa bayani.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe kana yace.
“Toh Abba ni zan tafi”.
Ahankali Abba ya sanya hannu a aljihu tare da ciro key mota sabo dal ƙiran PRADO ya miƙa Masa tare da cewa.
“Ga wannan Aliyu za'a kaika Airport dashi, in Manu driver ya dawo kuma gidan ku zaije ya ajiye maka ita”.
Cikin sauri Moddibo ya ɗago kansa tare da Kallonsa.
“Abba mota kuma?”.
Kai Abba ya gyaɗa masa alamar eh.
Cikin sanyi Moddibo ya sake kallon key motar kana yace.
“Abba to ai ina da mota”.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana yace.
“Uhm-Uhm Aliyu kenan. Ɗan Allah kada kayi min gardama ka karɓa kawai ka sanya albarka aciki”.
Sunkuyar da kai Moddibo yayi batare da da yace Uffan ba.
Kallonsa Hajiya Turai tayi kana tace.
“Ka karɓa mana Aliyu ai yanzu kam an zama ɗaya”.
Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.
“Toh shikenan Abba Nagode Allah yasaka da Akhairi Ubangiji Allah ya mayar maka da dubunsa”.
Murmushi Abba yayi kana yace.
“Ameen”.
Nan take ya ɗauko takardun motar ya miƙa masa tare da cewa.
“Jiya mukayi magana da Alhj Abubakar nasa ya kawo min da yamma gatanan lafiyarta ƙalau anyi mata dukkan abinda ya dace”.
Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.
“Nagode Abba Allah yasaka da alkhairi ni zan tafi”.
Ahankali Abba yace.
“Allah ya tsare Aliyu Allah ya bada abinda akaje nema”.
Ameen ya amsa kana ya miƙe Abba ya rakasa da kansa ya buɗe masa bayan motar ya shiga, sabuwar motarsa sosai motar ta burgesa duda bai wani damu da bakin abuba, amman collor bakin yayi masifar kyau dan sai sheƙin sabunta takeyi,
Manu ne ya shiga yaja motar suka fita.
Kai tsaye gidan Malam Arɗo ya wuce dashi bisa umarninsa.
Sallama yayi masa kana daga nan suka ɗauki hanyar da zata sadasu da cikin Taraba Jaligo ja gari na Baba Abasu babban birnin Gembila kenan wanda kuma tsakanin local government ɗin nasu zuwa cikin ƙwaryar birnin Taraban tafiyace ta musamman.
Koda suka isa cikin Taraba, basu tsayaba suka nausa hanyar Adamawa Yola.
Jauro yaya
Baffan Liman ne zaune agaban Hajja Nana cikin sanyi murya da ladabi yayi ƙasa da kansa tare da cewa.
“Hajja kiyi haƙuri bai kamata ace kina fushi akan abinda bai kai ya kawoba, wannan al'amari ba wani al'amari mai girma bane bai kamata ace ki ɗauki zafi akansa har haka ba”.
Kallonsa kawai Hajja Nana keyi tana girgiza ƙafa tare da girgiza kai.
Ajiyar zuciya Baffa Liman ya sauke kana ya cigaba da cewa.
“Idan kin lura Khausar fa jika ce agareki ba ƴa bace, kinga kuwa duk ikon ka akan jika yana zama mai rauni, bare wannan zamanin da muke ya bambanta dana baya dan Allah Addah Hajja kiyi wa wannan al'amarin Kyakkyawan fahimta”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da fesar da numfashi kana tace.
“Na lura sannan na fahimci Liman da kai dasu Garga, Sadu, Jauro baki ɗaya bakin ku ɗaya akan al'amarin Khausar tun da haka kuka ce ni bani da abinda zance kuje kuyi duk yanda kuka ga dama”.
Ahankali Baffa Liman ya ɗago ya kalleta kana ya sake sunkuyar da kansa.
Cikin alamun ɓacin rai ta cigaba da cewa.
“Amma fa kusa ni ba zata Auri wannan yaron ba, tunda har ta iya buɗe baki ta kalli tsabar idona tace bata son. Aliyu jikina kuma ɗan Uwanta toni babu hannu na akanta kuyi mata yanda take so amma banda Auren mara tushe da asali”.
Gyaran murya Baffa Garga yayi kana yace.
“Dan Allah Addah Hajja kiyi haƙuri shikansa. Muhammadu Jimeta yace zai zo amma yafi so yazo ya sameki cikin farin ciki kada akan batun Khausar ranki ya dinga ɓaci abanza a wofi”.
Fuska ta ɓata tare da Kallonsu ɗaya bayan ɗaya kana tace.
“Idan yayi niyyar zuwa yazo idan kuma baiyi niyyar zuwa ba yayi ta zama tunda shi kansa bayanta yake bi, tun da wai har cewa yake bazai yi mata dole ba”.
Baffa Liman ya sake sassauta muryarsa yace.
“Dan Allah Addah Hajja kiyi haƙuri ki bi lamarin asannu da izinin Ubangiji komai zai dai-dai-ta amma bama son ganinki cikin damuwa”.
Haka suka riƙa Rarrashinta tare da kalamai masu kwantar da zuciya.
Acan ɓangaren Moddibo kuwa tafiya tsakanin Taraba da Yola tafiya ce mai zaman kanta sai dai bata wuce awa biyu zuwa uku, tuƙi Manu keyi cike da ƙwarewa ga samun sabuwar mota.
Shi kuwa Modibbo a hankali ya fesar da sassayan numfashi.
Sabida ji yake wani irin yanayi yana lullubeshi gaba ɗaya tunanin J ɗin sa ya dawo masa ji yake tamkar idan ya juya gefen damansa zai ga J ɗin sa, ahankali ya zira hannunsa ya kara volume din ƙira'ar da yake ji acikin Suratul Nisa'i, sai kuma ya koma baya ya jingina bayanshi da jikin Seat ɗin.
Domin idan har ba karatu yake jiba ko kuma yake yi sam baya taɓa samun nutsuwa, saidai kuma ta wani ɓangaren haka nan yake jin wani irin farin ciki da yabar garin Gembila, ji yake tamkar yabar wani yanki da yake da tarin ƙunci, ji yake tamkar yabar wani waje mai duhu da zafi ji yake tamkar ana zare ransa da ruhinsa daga waje mai ƙunci da azaba, kana kamar ana nufar dashi awaje mai tarin nutsuwa da salama yakeji.
Domin tun bayan rasuwar Amininsa garin Gembila tayi masa zafi da ƙunci kana tayi masa duhu baya kallon haskenta gaba ɗaya ya tsani garin, to dama Meya rage masa da garin Innayinsa ce kaɗai sai kuma Ummi dasu Asma'u.
Sai Misalin ƙarfe biyu da rabi ya shiga cikin Adamawa suna isa cikin Adamawa.
Manu yayi Parking A dai-dai Masallacin jum'ae dake cikin Atiku Abubakar shopping mall ɗinsu nan sukayi Al'wala sukayi sallar Azahar Kasancewar hanya zai kama, ɗan tafiya yasa a gaba shiyasa yayi niyar ƙasaru ya haɗa da sallar La'asar domin karfe uku dai-dai jirginsu zai tashi.
Baya jin zai iya cin wani abu haka yasa ya kalli Manu cikin mutuntaka yace.
“Manu sannu da yunwa”.
Cikin girmamawa Manu yace.
“Laa ba komai ai kafin mu fito ma naci abinci”.
Kai ya jinjina kana yace.
“Muje ka kaini cikin Airport ɗin, sai kayi sauri ka juya, kada kayi dare a komawa”.
Cike da gamsuwa Manu yace.
“Toh”.
Daga nan ya kaishi Airport sannan shi kuma ya fito, ya ɗan samu abin da ya taɓa kana ya kama hanyar komawa Taraba, Gembila.
Ƙarfe uku Dai-dai jirginsu Modibbo ya tashi daga Adamawa zuwa birnin tarayyar Nigeria Abuja.
Alhamdulillah cikin kwanaki huɗu bizi'nsa ya fito da yake business bisa ne ba wuya.
Alhamdulillah ranar Al'hamis da misalin ƙarfe biyu dai-dai jirginsu ya ɗaga daga Abujam Nigeria.
Zuwa Rabat babban birnin ƙasar Marocco kenan
A hankali ya fesar da wani irin zazzafan numfashi dai-dai lokacin da tayun jirginsu ke raɓuwa da ƙasar Nigeria, rumtse idanunsa yayi da karfi sabida wasu irin zafafan hawaye da yaji suna tsastsafo mishi ta cikin dukkan jijiyoyin idanunsa.
Wani irin yanayin da bai taɓajiba duk tafiye-tafiyen da yakeyi yaji yana dabaibaye rayuwarsa haka kawai yakeji kamar ya bar kasar kenan bari na har abada.
Lokaci ɗaya tunanin Jameel ya dawo masa, wanda hakan yasa yayi saurin jingina bayansa da kujerar jirgin.
Yana mai jin wani irin sassayan kuka na taso mishi daga can cikin ƙahon zuciyarsa, hakanne yasa ya fara karatun Alqur'ani mai girma a hankali.
Yayinda mutanen cikin jirgin kuwa kowa keta hidimar gabansa.
Shi kuwa Modibbo tunda ya zauna bai ɗago kansa ya kalli kowaba.
Sabida yanayin da yakeji.
A hankali dai tafiya ta fara nisa, tuni sun kutsa cikin sararin samaniya jirgi ya kama hanyarsa.
Koda akazo tambayarsu me yake buƙata.
Cewa yayi baya buƙatar komai.
A ƙalla sunyi tafiyar awa uku a sararin samaniya.
Zuwa yanzu kam mafi akasarin matafiyan kowa ya nitsu hada-hadar ta ragu matuƙa, wanda zuwa lokacin kuma sauran musu 57 minutes su dira cikin birnin Rabat sabida daga Abuja zuwa can tafiyar awa uku da minti hamsin da bakwai ne cib-cib.
A hankali ya gyara zamansa tare da kallon farin matashi da ya zo ya zauna gefensa wanda bazai wuce sa'anan ba.
Murmushi matashin yayi tare da miƙa masa hannun yana mai mishi wani irin kallo mai cike da tambayo al'ajabi da kaɗuwa.
Shima ɗan murmushin yayi tare da bashi hannu sukayi musabaha.
“Jabeer bin Jabeer Joɗa. Wanda ya kira kansa da Jabeer ɗan Jabeer Joɗa ɗin ya kare mgnar cike da masifar mamaki da zurawa fuskar Modibbo idanu yana matuƙar mamakin kamanninsa.
Shi kuwa Modibbo cikin yanayin sanyi yace.
“Aliyu