Showing 81001 words to 84000 words out of 218703 words
dole ya fito ko domin girgiza zuƙatan sauran ɗan burbushi magauta duk da dama suna zaton haka tunda kowa yasan labarin wasiƙar da Innayi ta bari kafin tafiyar kuma a san shi ba a tsinci gawarsa ba kamar yadda ake tsinta na yayunshi da suka gabata, masu fariyar dole sarauta ta bar hannun ahlin Aliyu Mouley, su san cewafa ga wani Aleey mazan”.
Murmushi mai ɗan sauti Sheykh Jabeer yayi dan shi kansa al'amarin yana tsumashi yana tuna mishi irin magautan da suka fuskanta a masarautar Joɗo, shida har tsuntsuwa aka meda mahaifiyarsa. *A Littafin GARKUWA sai gashi kuma ƴar shima ta faɗa irin gidan*
Innayi kuwa cikin yaƙini tace.
“Da izinin Allah su da Aliyu na sai dai kallo basu da zarrar iya cutar dashi”.
Cikin gamsuwa Sarki Youseep Mouleey ya gyara zamansa tare da fuskatarsu kana yace.
“Aje a fara shiri”. Daga nan aka watse taro cike da jin daɗi.
Didi ce zaune a bakin gadon ta na alfarma yayinda
Lalla Khadijah da Hafsat dake zaune a gabanta cikin tsananin happy tace.
“Didi kin ko tuna cewa gobene birthday ɗin Aliyu”.
Kai ta jinjina tare da kallon Rahama da ta miƙe zaune tana mai danna wayarta tace.
“Didi kice inyi gayyata ta mu samman”.
Ta ƙare mgnar tana shiga group ensu na Mouley family.
Didi kuwa cikin jin daɗi tace.
“Ai kuwa Rahama ki gayyata ta musamman domin bikine na musamman.
Sai kuma ta kalli Hafsat tare da cewa.
“Ki kira ƙawarki Islam kuje Ryad square shopping mall. Ku ɗebo dukkan abinda ya dace, kama daga na amarya da shi Aleey.
Daga nan in kun taso ku biya Marocco Mall ki ku zaɓo dukkan abin buƙata na al'adun amaren masarautar Mouley, Hafsat so nake komai ya zama na musamman ne”.
Cikin sanin manufar mahaifiyar tasu ta ce yanzuma kuwa Didi.
Khadija kuwa da sauri tace.
Amman sai munje munga amaryar kafin mu tafi”.
Gyaɗa musu kai Didi tayi tare da cewa.
Nima yanzu zan tafi sashin Niyna dan ance min su Goggonku Salma da Zakariyya sun iso”.
Daga nan ta miƙe ta fita.
Rahama kuma tana gama fesa labarin hidimar da za'ayi a masarautar tasu gobe misalin ƙarfe huɗu na yamma.
Ta kuma shiga group ɗin na ƙawayenta.
Nan ta fesa musu.
A masauƙinsu Khausar kuwa bayan su Ummin da Innayi sun dawo cikin farin ciki Ummu ta zauna kusa da Khausar dake riƙe da kwanon ƙasaitacciyar mace da Ummin ta dama mata tun kafin su tafi.
Ƙwaffa tayi tare da cewa.
“Wai Khausar har yanzu baki shanye damun nan ba?”.
Fuska ta ɗan kwanɓe tare da cewa.
“Allah ko Ummi abun babu daɗin”.
Da sauri Asma'u tace.
“Ni dai Wlh yayi min daɗi gaba ɗaya gumbunan da da garukan ɗaɗine dasu, wani garɗi kamar na dabino da aya da kwakwa harda ɗanɗannon zumafa a ciki, Ummi gashi da zaƙin su ƙungiyar alewa da kuma mazarƙwaila”.
Da sauri Ummu tace.
“Toh sha zumami kice mana wanda aka ɗan sha ɗin ma kece kika shanye. da kike koro jawabi haka”.
Yar dariya tayi tare da rufe idonta kana tace.
“Sai daifa gsky kuma duk da kayan dadin akwai itatuwa da jijiyoyi dan naji ƙamshi jijiyar ilanwaddihi ma da ma kwaranyi wanda kike yawan aikena in amso miki wurin Innayi”.
Harara Ummi ta cilla wa Asma'u tare da cewa.
“Dama ai mgni kam bazai yi ɗaɗiba, maza Khausar kafa kai ki shaye”.
Cikin rumtse idanun ta kafa kanta ta fara sha.
Saida tasha kusan rabi kana ta janye kwanon tare da kwaɓe fuska tace.
“Wlh Ummi ni dama can kayan zaƙi bai cika dakuna ba, nafi son abun yaji-yaji kiga mana kazar nan da kika dafa min duk da babu daɗi amman dana zumbuɗa yaji na cinyeshi fes. Kuma Kinga Wanda Aunty Hajara ma ta kawo min na cinyeshi. Shi kam ma yafi rashin daɗi dan da ƙyar naci tanata zagina wai dubu ashirin da takwas ta biya AYSHA ALIYU GARKUWA ta dafa minshi wai zuciyar farin ragone”.
Haɗe fuska Ummi tayi tare da cewa.
“Kuma wannan ɗinma sai kin shanyeba”.
Jin haka yasa ta kafa kai ta shanye, tare da ajiye kwanon kana tace. “Alhamdulillah na gama”.
Cikin sauƙe numfashi Ummi tace.
“Yanzu muka dawo daga sashin kiran da akayi mana, munje bisa jagorancin innayi”.
Da sauri Asma'u tace.
“Ummi kunga Yah Modibbo?”.
Kai ta jujjuya mata tare da cewa.
“Bamu ganshiba, baima san munzoba, innayi ma sunce ta bari sai gobe zata ganshi”.
Taɓe baki Khausar tayi tare da cewa.
“Uhmm me ake ta ɓoyeshi sai kace kuɗine shi ko zinari”.
Zura mata ido Asma'u tayi tare cewa.
“Yoh ba doleba, sun san akwai mai ƙar mishi kallo har gashin ƙeyarsa ta iso”.
Harara ta cillawa Asma'u tare da cewa.
“Waya ma damu da dashi”.
Murmushi Ummi tayi tare da faɗin.
“Yanzu dai tashi kiyi Wonka, tunda dilken ya kai awa biyu a jikinki”.
Da sauri tace to, tare da miƙewa ta nufi bathroom din.
Asma'u kuwa falo ta nufa jin innayi na kiranta.
Zaune ta sameta dasu Hajia Bunayyah da kuma su Aunty Hauwa duk dai waɗanda suka zo tasu.
Gyara zama tayi tare da kallon su ɗaya bayan ɗaya kana tace.
“Idan Allah ya kaimu gobe za'a fara hidimar bikin Khausar da Modibbo kamar yadda al'adar masarautar Mouley takeyi.
Dan haka ku shirya karfe huɗu na yamma ne za'a fara.
Zuwa Maggarib an gama na gobe sai kuma zuwa jibi.
Cikin tsinkewa da lamarin cigaban da Khausar ta samu Hajia Bunayyah tace.
“Uhmm Allah ya kaimu”.
Sai kuma ta yunƙura zata tashi.
A hankali ta koma zaune jin muryar Hajja Nana na cewa.
“Bisa alamu dai Khausar taci ribar ƙin auren ɗan mayu, abu ya haɗu, sunna ta haɗu da farilka, sakekke ya haɗu da sakekkiya, wato bazawari ya samu bazawara ɗan maye da ƴar Mayu, jikar tsarki da jikan sarki”.
Cikin takaici Hajia Bunayyah tace.
“Kamar yaya kuma Sunan ta hadu da farilla?”.
Kai Hajja Nana ta jinjina cikin isa kasaitar data motsomata yau tace.
“Eh ɗan babban Sarkin Mouley na kasar Marocco ya auri jikar babban Sarkin Gombawa na ƙasar Nigeria jihar Gombe, kin san su dama su Khausar kirarinsu Gombawa ɗiban fari ba'a kwana dasu ba a tashi dasu, Gombe doma hamadar sarki lahirar sulaimanu”.
Da sauri Innayi ta kalleta cikin rashin fahimta ita kuwa Hajja Nana cikin ƙasaita tace.
“Yoh da ji kikeyi ku kadaine keda masarauta, to idan baki saniba, Sarki Buba Yero shine tsohon mijina kuma kakansu Khausar, barina Gombe da mahaifin Khausar da bappanta Muhammad, ne yasa masarautar ta koma hannun kaninsu ɗan abokiyar zamata, kuma shi har yanzu jira yake Yayanshi bappan Khausar yaje ya karɓi ragamar mulki dan su masarautarsu sunada imani da ƙaunar juna babu wani tsaface-tsaface, nice na hana sabida ni kwanciyar hankali ƙannena yafi min”.
A hankali Ummi dake jiyo Hajja Nana ta fesar da numfashi tare da cewa.
“Haba sai haka mana ƙasaita da isar Hajja Nana tayi yawa, ita kanta Khausar ƙasaitarta da kwarjinin ba irin na normal mutane bani, kwarjinin ta yawa gareshi.
Sai kuma ta kalli Khausar da fitowar ta kenan daga Bathroom.
“Masha Allah”. Shine abinda Ummi ta faɗa sabida ganin wani irin sheƙi da ƙellin da fatar Khausar keyi kai kace tarwaɗace, tsabar farin da tayi kace balarabiyace.
Gashin kanta dake tubke ta zubawa ido.
Sai kuma ta kalli Khausar ɗin dake tsane jikinta tare da miƙa mata.
Man shafawa, da dauko handdryer kana ta dawo ta bayanta.
Tare da fara busar mata da gashin dan ya ɗan jike. yaje mata tayi tare shafa mata mai.
Ita kuwa Khausar mai take shafawa a jikinta kusan a tare suka gama.
Ajiye handdryer ɗin Ummi tayi tare da juyowa gefen gadon inda akwatuna set ke jere, ɗaya pink ɗaya blue, wanda Ummi ce ta bada aka haɗawa Khausar ɗin Kayan lefe, kana kuma shine aka kai gidansu dangi da abokan arziƙi suka gani.
Wanda suma Hajia Bunayyah dai bata samu abin kushewa ba.
Na forkon ta buɗe wanda tun a gida Asma'u ta haɗa dukkan abin buƙata da kuma kayan da Khausar ɗin zata saka har gama bikin.
Wata Dubai Abaya Ummi ta zaro mata, Black color sai kuma zare golding color da aka yiwa rigar aiki zuɓi na musamman mai masifar kyau da ratsin fari kaɗan rigar irin mai ɗan faɗin nanne musamman daga sama. sai kuma ta zaro mata wani tattausan mondo Wanda bazai wuce iya guiwarta ba, sai bra su duka fararare, turare ta zaro kusan kala uku ta feshesu dashi. Kana ta ɗauko Kulaccar sirri wacce ta saya wurin AYSHA ALIYU GARKUWA, miƙa mata tayi tare da cewa.
Gashi ki shafa wannan.
Amsa Khausar ɗin tayi tare da cewa.
“Ayyah Ummi a tubke min gashin nan”.
To Ummin tace tare da fara tubke mata shin.
Tana gama ta nufi falo tare da cewa.
In kin gama kizo, kai kawai Khausar ɗin ta gyaɗa mata.
A can Falo kuwa Hajia Bunayyah ce ta miƙe jiki a salube ta shige ɗakin da nanne masauƙinsa inta da Aunty Hajara da kuma Aunty Ruƙayya.
Da sauri ta maida ƙofar ɗakin ta rufe tare da dannawa Hajia Lami kira a wayarta.
Bugu ɗaya ana biyu Hajia Lami ta ɗauka tare da cewa.
“Mutanen Marocco yaya akayi?”.
Cikin fesar da numfashi mai zafi Hajia Bunayyah tayi kwafa tare da cewa.
“Wllhi Allah Hajia Lami munyi babbar asara daba Samira wannan yaron ya auraba. Na rantse miki da Allah munyi asarar samun daular duniya.
Wannan shegiyar yarinya mai idanu kamar na mujiya ko yaushe suna lunshe kamar mai jin bacci anya ma kuwa ba idanun dunane da ita ba.
Kinga tayi nisa ta barmu da Naseer ɗin da ubansa ko Sarkin tasha bai taɓa samuba, ke kuwa ta bar miki ƴa da wari da yoyon ƙazanta”.
Nannauyan numfashi Hajia Lami ta fesar tare da cewa.
“Toh yanzu me abinyi?".
Cikin tsananin hasada Hajia Bunayyah ta buga hannunta da jikin gini tare da cewa.
“Wallahi Allah ni dai na rantse da Allah, sai na kashe auren nan, koda zan tafi tsirarane sai na watsa aurenan, muddin ina raye wlh Khausar bazata ji daɗin rayuwarta a gidan nan ba, idan zaki zo mu haɗa hannun da ƙarfe mu tumɓuke auren nan, mu shiga da Samira gidan to ki fara shiri, domin ina dawowa zamu bazama".
Cikin ƙeƙashewae zuciya Hajia Lami tace.
“Ai ke dai Allah ya dawo dake lafiya, Ƙawata na sama mana labarin wani ƙasurgumin boka a ƙasar Niger cikin dajin Damagaran ance min aikinshi kamar yankan wuƙane, babu haufi shi bazama ka biyaba sai buƙatar ka ta biya”.
Cikin yaƙini tace.
“Ke dai ki shirya ina dawowa zamu tafi”.
Daga nan suka katse kiran kana ta fito.
A falon kuwa da sauri su Ummi suka ƙali ƙofar falon jin sallamar Jakadiya da kuma su Lalla Khadijah da Hafsat.
Cikin sakin fuska Ummi da Innayi suka amsa tare da nuna musu wurin zama.
Zama sukayi cikin sakin fuska da cikekken fulatancinsu da suka iya ta sanadin Didi suka kalli su gaisa cikin mutumtaka.
Jakadiyace ta kalli Lalla Hafsat tare da juyowa ta kalli innayi kana tace.
“Dama yayun Aliyu ne suka zo ganin ƙanwar tasu tare da marabtanta.
Cikin jin dadi Ummi tace.
“Ayyah to babu laifi barin in kirawota”.
Sai kuma ta mike ta nufi dakin da Khausar take.
“Masha Allah diyata kinga yadda kikayi kyau kuwa". Murmushi tayi tare da rufe fuskarta da tafukan hannunta.
Ita kuwa Ummi kamo hannunta tayi ta ajiyeta tare da cewa.
Zo mu je ki gaisa da yayun Modibbo.
Da sauri ta sunkuyar da kai ganin yadda Ummi ke gyara mata tarhan da tayi da gyalen abayar sosai tayi masifar kyau ta fito cas da ita a matashiyar budurwar yar kimanin shekaru 19 zuwa 20. Duk da rigar nada faɗi bai hana kyan surar jikinta bayyana ba.
A hankali suka fito falon.
Khausar kam kanta a ƙasa take wani irin amintaccen taku mai cike da nitsuwa.
Da sauri Lalla Khadijah ta miƙe tsaye lokacin da suka iso tsakiyar falon.
Hannunta ta buɗewa Khausar tare da faɗin.
“Wow Masha Allah, Didi dai ta samu ƙarin diya wannan ai in an ganta da Rahama kai kace tagwayene". Murmushi mai yelwa Lalla Hafsat ma tayi tare da miƙawa Khausar hannun a hankali Khausar ta ɗan janye jikinta dan jikin Lalla Khadijah ta ɗan saketa.
Ruggumeta Hafsat tayi tare da cewa.
“Masha Allah, Khausar muna farin ciki da shigarki Mouley family. Allah ya baki hikima da basirar zama tsakiyar wannan Fada”.
Kusan a tare suka amsa da Amin ita kuwa Khausar yatsun hannunta take ɗan murza tare da ɗan rusunawa kana ta gaidasu.
Amsawa sukayi suna mai ƙare mata kallo. Cikin ɗan sakin fuska Hafsat tace.
“Ai wannan komai nata kamar na Rahama zaiyi mata dai-dai”.
Cikin girmamawa Jakadiyarsu tace.
“Sosai ma kuwa”. Ita kuwa Hafsat hannun Khausar ta kamo tare da cewa.
“Takalmi sise nawa kike sawa”.
Cikin sanyin murya tace.
“37”. Da sauri Khadijah tace.
“uhm jinjina sise ɗin Rahama kenan”.
Sai kuma ita Khadijah ta kamo hannun Khausar tare da ajiyeta gefen Innayi kana tace.
“Zauna abinki. Didi da Niyna sunyi miki Barka da zuwa, masarautar Mouley. Yanzu mu zamu fita ne.”
A hankali tace.
“Allah ya kiyaye hanya."
Amin sukace a tare sai kuma suka ɗan kalli Asma'u tare dayi mata murmushi suke.
“Ke me sunanki?”.
“Asma'u”.
Murmushi Khadijah tayi kana tace.
“Yauwa toh in ba matsala innayi zamu tafi da ita, ai kin san sise ɗin Khausar da kalanta ko?”.
Cikin fara'a Asma'u tace.
“Sosai ma kuwa, Nama fita sanin abinda yake mata kyau”.
Dariya sukayi ganin hararar da Khausar ta cilla mata..
Ummi kuwa murmushi kawai tayi.
Daga nan suka fita da Asma'u.
Sune basu dawoba sai gab da Maggarib.
Acan Side din da Modibbo yake kuwa.
Zaune yake shi da Ibrahim da Dr Jameel.
Cikin tsuke fuska ya kalli Dr Jameel dake zoro wayarsa daga aljihu.
“Baby”. Ya faɗa a saman lips enshi.
Sai kuma ya tsaida idonsa kan Modibbo da ya wani irin tsaresa da idanu.
A hankali yace.
“Yah dai Malam kallon nan fa?”.
Fuska Modibbo ya kuma tsukewa tare da cewa.
“Kaji tsoron Allah, Dr J kasani. Abinda kakeyi kana tafiya cikin fushin Ubangiji ne, kuma masifar zunubinka zaiyi ta bibiyarka tun anan gidan duniya, kasan cewa abinda kayiwa ƴaƴan wasu za'ayiwa ƴaƴan ka, shin me ribarka a cikin in har ka jazawa ahlinka. Ka tuna shifa zina tsananin muninsa yasa Allah baice kada kuyi zinaba, cewa yayi kadama ku kusaceshi fa. Shifa mazinaci baya zina har sai an zare mishi imaninshi. Kasan kuwa abinda Allah ya tanadarwa mazinata abinsha a cikin jahannama?”.
Cikin tsananin sanyin jiki Dr Jameel ya rumtse idanunsu tare da cewa.
“Nifa shiyasa badon Abualeey da kansa yace min dole in kasance kusa da kaina wlh bazanzoba sabida na lura kai mutumne mai tsaraɓe-tsaraɓen halal da haram”.
Cikin takaici Modibbo yace.
“Koda baka zo inda nakeba kasa a ranka in dai ina cikin ƙasarnan, sai na kasance tare da kai, na kuma yi al’ƙawari zan ƴaƙi shsiɗanin dake tare da kai, in Sha Allah sai ka dawo managarci tamkar J na”.
Murmushi Dr Jameel yayi tare da kallon hadimai guda huku da suka shigo da manyan jakukkuna guda biyar masu ɗauke da tambarin Anfaplace mall Marocco.
Da sauri Ibraahim ya miƙe tare da cewa.
“Ku shigo dasu cikin bedroom kada ku barsu a nan”.
Jin hakane yasa suka bishi a baya.
Kusan a tare suka shirya kayan cikin wodurob.
Daga bisani suka fito falon, a tsaye ya samu Dr Jameel.
“Mujeko Ibraahim”. Cewar Dr Jameel.
Kai Ibraahim ya gyaɗa tare da bin bayanshi sai kuma ya juyo ya kalli.
Moddibo dake cewa.
“Wai dan Allah Ibraahim sai yaushe za'a buɗeni in samu zuwa jam'in salla, wlh abinfa yana damuna.
Sassan numfashi Ibraahim ya fesar kana a hankali ya juyo ya dawo gaban Modibbo tare da cewa.
“Kayi haƙuri Yah Aleey in Sha Allah gobe dai a jam'i zakayi sallan magarib. Akwai babban dalilin ne da yasa ba'a barka ka fitoba.
Ƙwaffa Modibbo yayi tare da lumshe idonsa Allah ya sani suna ƙona mishi rai da batun hanashi jam'i da wotoyinsa.
Shi kuwa Ibraahim juyawa yayi yabi bayan Dr Jameel suka tafi.
Washe gari tun safe Dr Jameel da Jabeer bin Jabeer da kuma Ibrahim suka shigo wurin Modibbo.
Tare da wani Kekkyawan matashi wanda bazai wuce sa'an Modibbo ba.
Cikin sakin fuska matashin ya bawa Modibbo hannu tare da cewa.
“Sunana Zakariyya Khallin”.
Cikin ɗan sakin fuska Modibbo yace.
“Masha Allah”.
Ibrahim ne ya amshi mgnr da cewa.
“Yah Aleey Wannan ɗan Goggo Salma ne ƙanwar Abualeey. Shi a India yake shima likitane, taron gabatar da kaine ya kawoshi.”
Murmushi Modibbo yayi tare sake bashi hannun, shi kuwa Zakariyya ruggume Modibbo yayi tare da faɗin.
“Duk da zumuɗin Mami na rigata ganin ɗan yayanta”.
Shi kuwa Modibbo Ibraahim ya kalla jin yana cewa.
“Dr Jameel ma ɗan Goggonmu ne Aunty Sahrah itake bin Goggo Salam, kuma babanshi Aminin Abualeey ne ɗan ƙasar Turkey, duk dangin babanshi suna can”.
Dr Jameel kuwa numfashi ya ɗan fesar kana yace.
“Ni ya labarin Yusuf ne, kwana biyu bamuci wayaba”.
Da sauri Zakariyya yace.
“Ya tafi Mexico kasanshi ya nacewa Zeeyada yar Lalla Hafsat”.
Sai kuma ya kalli Modibbo tare da cewa.
“Yusuf ɗan Unclee Haroon Mouley ne, ƙanin Unlee Youseep Mouleey”.
Cikin fahimta Modibbo yace.
“Na fahimta, toh amman kuma tunda nazo banga Unclee Haroon ɗinba”.
Cikin sanyi Dr Jameel yace.
“Dashi da Mamina, da Abbana duk rana daya sukayi haɗari, su sun rasu shi kuwa har yau baida lfy tsawon shekaru ashirin da biyar kenan”.
Cikin sanyin jiki da tsananin tausayi Modibbo yace.
“Allah sarki Jameel Allah ya jiƙansu da rahama yasa sun huta shi kuma Unclee Haroon Allah ya ya bashi lfy”.
Da Amin suka amsa baki ɗayan su.
Shi kuwa Modibbo cikin sanyi ya kalli Dr Jameel tare da cewa.
“Dan J kabar abinda kakeyi ka zamewa Aunty Sahra da Abba al'waladussaliha ko dan basa raya ka zame musu sanadin samun lada”.
Cikin sanyi jiki Dr Jameel yayi ƙasa da kansa yana mai taunan lips inshi na ƙasa.
Shi kuwa Modibbo a raunace yace.
“Mu kuwa zamuci gaba dayi maka Addu'o'i Allah ya shiryeka”.
Amin suka amsa a tare.
Sai kuma Ibrahim yace.
“Yauwa mu shiga daga ciki masu gyara zasu shigo gyara nan ɗin".
Toh sukace kana suka shiga Corridor nan tare suka shiga ƙofar nan ta dama inda Modibbo yake, a falon suka zauna.
Zamansu ba jimawa Rahman ta shigo da hadimai da sunka kawo musu breakfast.
Acan Side ɗin dasu Khausar suke kuwa, suma tuni an kawo musu breakfast, dama dukkan abin buƙata.
A nan wannan falon kuwa, zuwa bayan an isar da sallam la'asar duk an gama ƙawatashi da shiryashi irin shirin nan na al'farmar da kamala.
Kujerun gaba ɗaya an mannasu da ginin duk da girman falon wai dan a samu ya ƙara girma.
Wata kujera mai zaman mutum biyu aka ajiye daka san tsakiyar falon. Sai kuma wasu datsa-datsan Turkiy Carpet masu masifar kyau da taushi. Da aka shimfiɗa a gaban kujerar, wacce duk ta inda ka shigo zaka kalli waɗanda ke ka kujerar. Sai kuma wasu tukwanen kasa masu zanen ɗawisu da aka jere gefe da gefen kujerar yayinda daga sama tukwanen kuwa, gashin gezan ɗawisunne a cikin mai cikekken launi daban-daban, sai