Showing 9001 words to 12000 words out of 218703 words
da hawayenki, dan baza mu iya juran. Kallon hawayen ki na zuba ba”.
Kallonsa Ummi tayi cikin wata raunan'niyar murya tace.
“Babana idan har baka zuwa wajena ya zanyi?Kana so ka haɗa min zafi biyu alokaci ɗaya ne?
Babu Jameeluna sannan kaima baka kusa dani mekake tunanin zanji arayuwata, kana so inshiga wani hali ne?”.
Cikin sauri ya girgiza mata kai kana muryarsa na rawa yace.
“Insha Allahu bazan sake nesa da keba, zan kasance atare daku tamkar yanda J ke kasancewa atare daku, zan sanya ku farin ciki tamkar yanda J ɗina ke saku insha Allah zan kiyaye”.
Ya kalli Ummi da har zuwa lokacin hawaye ke zuba a Idanunta ya ɗaura tafin hannunsa akan nata cikin rawan murya yace.
“Insha Allah zan zame muku farin ciki kuma Garkuwa kamar yanda J ɗina ya kasance agareku Ummi. Asma'u Bashir Insha Allah bazan bari hawayenku ya zuba ba tamkar yanda J ɗina baya bari su zubo ba nayi al'ƙawarin zan zame muku farin ciki zan maye muku gurbin J ɗina”.
Ya ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka kasa rarrashin sa Ummi tayi kawai itama hawaye ya cigaba da zuba daga idanunta haka Asma'u da Bashir suka riƙa kuka harda sheshsheƙa baki daya Moddibo baya jin zai iya hana kansa kuka bare kuma ya samu kuzarin rarrashinsu hakan yasa aka rasa wanda zai rarrashi wani acikinsu.
Malam Ahmad da dawowansa kenan ya zuba musu ido cike da tausayinsu ganin yanda suke kukan kasan daga ainihin zuciyarsu yake fitowa.
Cikin sanyi malam Ahmad ya zauna gefen Ummi ya zamana yana fuskantar Moddibo, Asma'u da Bashir dake ƙasa cike da tausayawa da kuma rinƙa rarrashisu da basu baki.
Ahankali Ummi ta maida bayanta da jikin kushin ɗin ta jingina hawaye na cigaba da zubo mata Moddibo kuwa kasa yayi da kansa yana jin wani irin yanayi azuciyarsa shikenan J ya tafi ya barsa bari na har abada.
Kallonsu Malam Ahmad yayi kana ya cigaba da cewa.
“Insha Allahu da yardan Ubangiji Jameelu yana cikin rahama, salama nutsuwa da kwanciyar hankali domin Jameelu ya kasance bawa mai tsananin Biyayya ga dokokin ubangiji sannan Jameelu yaro ne me biyayya ga Iyayensa akullum burinsa yaga ya sanya Iyayensa da shalinsa acikin farin ciki”.
Jinjina kai sukayi Atare cike da gamsuwa da maganarsa tabbas ta ko wanni fanni Jameel bashi da makusa.
Ajiyar zuciya Malam Ahmad ya sauƙe kana yace.
“Jameel ya kasance mutum mai tsananin tausayi da temakon al'umma Jameel baya taɓa kallon mutum acikin halin neman temako sannan ya wuce batare daya temakesa ba, duk wanda yasan Jameel da addu'a yake binsa na Ubangiji ya jiƙansa dama mutane masu Kirki da karamci Ubangiji bai fiye barinsu tagayyaraba sam Jameelu bai cancanci kuka agare kuba, addu'a ya cancanci ku masa domin da izinin Ubangiji yana can cikin rahmar Allah da yardan sa”.
Kai Bashir ya gyaɗa tare da share hawayen saman fuskarsa kana cikin sauri yace.
“Hakane ma Abba abinda kake faɗa yanzu shine abinda.
Yah Jameel ya faɗa min acikin Mafarkina jiya da daddare yace. in faɗawa Ummi ta daina yi masa kuka domin duniyar da yake ayanzu tafi wannan duniyar da muke ciki daɗi, nutsuwa, salama, da kuma aminci”.
Cikin sharce hawaye ya gyara zamansa tare da fuskantar Ummi kana yace.
“Sannan yace bayason wannan kukan da Ummi ke masa, shikam addu'a yake buƙata duk wannan koke koken bayaso adaina yi masa.”
Kallonsa ya mayar kan Moddibo tare da cewa.
“Sannan kaima Yah Moddibo acikin mafarkin da nayi da Yah Jameel yace in Faɗa maka ka cigaba da yimasa addu'a sannan kayi ƙoƙari ka cika masa wasiyyar da yayi maka ta gefen Innayi ya jadda min kuma ka taya Abbansa kula da lamuran kasuwancinsa”.
Saurin ɗago kai Moddibo yayi tare da cewa.
“Ummi wani wasiyya kuma J ɗina ya bari akaina??”.
Girgiza kai Ummi tayi tare da fashewa da matsanancin kuka batare da tace Uffan ba.
Ajiyar zuciya Malam Ahmad ya sauƙe tare da kallon Ummi dake sheshsheƙa kana yace.
“Fatima yanzu kuka za kiyiwa Jameelu? shin kinsan Rahman da Ubangiji ya tanadar wa da duk wa'anda aka zalunta da rabasu da rayuwarsu?
Kada fa ki manta Ubangiji ya tana dar da rahma wa duk rayukan da aka kashe batare da hakkinsa ba”.
Ahankali Ummi ta ɗago kanta kana ta sanya tafin hannunta ta share hawayen ta Numfashi malam Ahmad ya fesar kana yace.
“ki tuna ni'imomin da Allah yayiwa muminai tanadin su.”
Lokaci ɗaya Ummi ta saki murmushi wanda tun bayan sace M Jameel ba tayi irinsa ba wani irin nutsuwa da salama taji yashigeta lokaci ɗaya tabbas tana ji ajikinta Jameelun ta na cikin rahmar Ubangiji.
Moddibo ma murmushi yayi wanda ya fito daga ainihin zuciyarsa in sha Allah J dinsa yana cikin kwanciyar hankali da salama da izinin Ubangiji addu'a kawai J dinsa ke buƙata atare dashi Insha Allah kuwa zai cigaba da masa hakan yasa suka cigaba da hirar rahmar da M Jameel zai kasance da izinin Ubangiji cikin sakin fuska suka cigaba da hira.
Acan gidan Lamiɗo kuwa ƙarfe biyar dai-dai Hajja Nana ta mike tare da kallon Dije dake zaune gefen Khausar suna hira tace.
“Ke Dije tashi mu tafi”.
Kai Dije ta gyaɗa tare da miƙewa cike da girmamawa Mommy ta haɗa mata tsaraba sannan ta bawa Khausar ta riƙe suka fito.
Suna fita coumpund ɗin Hajja Nana ta kalli Khausar tare da cewa.
“Insha Allah idan Baffa Jimeta yazo zamu zo tare”.
Ko uffan Khausar bata ce da ita ba haka zalika Mommy, bayan Khausar sun koma falon ta kalli Mommy cikin sanyin murya tace.
“Mommy yanzu dan Allah biye mata zakiyi?”.
Ahankali Mommy ta zauna tare da kallon Khausar cikin sanyi tace.
“Yanzu Khausar idan ban biye mataba wa kika tsayar? sannan tsohuwar nan tunda ta rantse akan dole sai anmiki aure tofa babu makawa, sannan babu yanda zanyi dole sai an Aurar dake ke dai kiyi fatan Allah ya miki zaɓin alkhairi, sannan ya baki mijin da zai barki ki cigaba da karatunki ki kuma cika burin ki”.
Wani abu mai masifar ɗaci Khausar ta haɗiye cikin raunin murya tace.
“Mommy nifa Banason sa”.
Kallonta Mommy tayi kana cikin tsareta da ido tace.
“To idan bakya sonsa wakike dashi ko kuma wa kika tsayar babu wani saurayi dake zuwa wajenki Naseer da ake maganar sa yanzu ya fita sabgarki kuma hakama yafi min.
Ni yanzu abinda na fahimta ma kamar soyayya suke da Amina”.
Khausar kuwa kallon Mommy tayi tare da tura baki kana tace.
“Eh Mommy soyayya suke to amma.
Ni me ruwana dasu ni dai bazan Auri Yah Aliyu ba Naseer kuwa bana sauraron maganarsa bare insa shi araina”.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da gyara zaman ta cikin sanyin murya tace.
“Toh Allah ya mana zaɓin alkhairi”.
ta faɗa tare da miƙewa tashiga Bedroom ɗin ta Khausar kuwa jingina bayanta da jikin kushin tayi tare da lumshe Idanunta.
Da yammaci Misalin ƙarfe biyar da rabi Hajiya Bunayya da Hajiya Lami ce zaune agaban Boka Kar'uzu.
Cikin farin ciki Hajiya Lami ta gyara zamanta tare da kallon Boka Kar'uzu dake taune laɓɓansa na ƙasa duk yayi muni ba kyan gani cikin sassauta murya tace.
“Na gaishe ka Boka Kar'uzu Uban bokaye La'anannen Uban La'anannu ina mai farin cikin sanar da kai shekaran jiya Alhj ya tafi Saudia kaga yanzu sai ka shirya ka koma gidana kaje kayi sati ba matsala”.
Wata mahaukaciyar dariya Boka Kar'uzu ya fashe dashi wanda yasa ganyen bishiyar dake wajen suka soma zubowa yana mai ƙara wangale wawakeken bakinsa yace.
“Anjima da daddare zanzo, maza ku tashi ku tafi da ƙafar hagu yanzu zanyi manyan baƙi da kukar bulikiya Ɗan Jaƙunana mai ƙaho Atsakiyar kai da da jela zai ƙaraso”.
Ai cikin sauri suka miƙe suka fita daga wajen kamar yanda ya faɗa.
Acan gidan Innayi kuwa zaune suke da Malam Arɗo asaman baranda Moddibo.
Cikin nitsuwa Innayi ta kalli Malam Arɗo cikin sanyin murya tace.
“Toh kaji yanda mukayi dashi, yanzu abinda nake so idan Allah ya nufa zaka je kasamu Abban Jameelu kayi masa bayani idan yaso sai mu isar da manufarmu ga mahaifin yarinyar”.
Jinina kai Malam Arɗo yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya kana yace.
“Insha Allahu idan Allah ya yarda zan shiga wannan maganar da iyakacin ƙarfina zan shigeta da izinin Ubangiji”.
Kai Innayi ta jinjina tare da cewa.
“Toh ba matsala Insha Allah Nagode matuka”.
Acan gidan Ummi kuwa bayan fitar Malam Ahmad Moddibo ya kalli Ummi cikin sanyin murya da damuwa yace.
“Ummi nayi al'ƙawari da izinin Ubangiji da yardan Allah sainayi duk yanda zanyi sai an gano waɗanda sukayi mana wannan cuta.
“Domin duniya tasan irin baƙin zunubin da suka aikata, sannan akamasu ayi musu hukunci dai-dai da zunubinsu, domin wasu su tsira agaba kada su sake cutar da wasu kamar yanda suka cutar damu, da zukatanmu da kuma ahalinmu”.
Numfashi Ummi ta fesar tare da sauƙe ajiyar zuciya kana tace.
“Hummmm?".
Cikin sauƙe numfashi Asma'u tace.
“Toh ammn ta ina zamu fara Yah Modibbo!?”.
Ahankali Ummi ta kalleta kana ta kalli Moddibo ta sauke ajiyar zuciya mai sanyi tace.
“Nima abinda nake tunani kenan, ta ina zaku fara wannan ba ƙaramin case bane dole yakasance mutum nada ƙwararan hujjoji kafin ya tun kari lamarin mu kuma bamu da sahihiyar Hujja dan haka mu barwa Allah lamarinsa”.
Jinjina kai Asma'u tayi tare da gyara zaman ta tace.
“Makama ɗaya muke da shi batun Khausar”
Cikin zurfafa nazari Moddibo yace.
“Kin tabbata Asma'u zata bamu haske kan batun?”.
Kai ta gyaɗa masa kana cikin gaskiya da gaskiya tace.
“Na tabbatar Yah Moddibo”.
Kallon Ummi dake Kallonsu yayi kana cikin ƙarfin gwiwa yace.
“Ummi”.
Cikin sanyi da tausayinsa tace.
“Na'am Babana”.
Cikin alamun samun nasara da jin daɗi yace.
“Ummi zamu fara bincike”.
Kai Ummi ta gyaɗa kana cikin wani irin yanayi tace.
“Nikam ina tsoro Babana ina tsoron kada kaima Azo acutar mana da kai ina tsoro kada wani abu ya sameka kawai abar maganar nan”.
Cike da mamaki da kuma sanyi Moddibo yace.
“Ummi tayaya”.
Girgiza kai Ummi tayi kana tace.
“Babana Abar Maganar kawai”.
Kai ya gyaɗa mata sannan suka dauka wani hiran sosai kowannen su ya samu nutsuwa sosai sukaji damuwar suya fara raguwa kaɗan sai bayan da Moddibo yayi sallar maghariba kafin yayiwa Ummi Sallama ya tafi.
Bayan Sallar Isha'i Malam Arɗo ne zaune gaban Abba wanda baki ɗaya ya rame yayi wani iri dashi.
Kallonsa Malam Arɗo yayi kana yace.
“Toh Alh kaji yanda akayi kuma shine abinda ya kawo ni”.
Jinjina kai Abba yayi cikin yanayin sanyinsa yace.
“Nima nasani Jameelu ya faɗa min”.
Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe tare da faɗin.
“Masha Allah abu yazo da sauƙi kenan”.
Jinjina kai Abba yayi kana cikin sanyi yace.
“Ba matsala Insha Allah zuwa jibi zamuyi kokari muyi maganar”.
Kai Malam Arɗo ya gyaɗa tare da cewa.
“Ayyah Jameelu Insha Allah zamu cika masa burinsa tunda har yayiwa Amininsa zaɓin mata yayi fatan ya haɗa wannan Auren kafin ya tafi zamu cika masa burinsa da izinin Ubangiji zamuyi ƙoƙarin cika wasiyyar daya bar mana”.
Kai Abba ya gyaɗa cikin sanyi ya gyara zamansa tare da lumshe idanunsa kana yace.
“Insha Allah zan tsaya akan lamarin sannan zanyi iyakacin bakin ƙoƙarina ganin ancika masa duk kan wasiyyar daya bari”.
Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe tare da jinjina kai yace.
“Insha Allah babu damuwa idan Allah yakai mu jibin zanzo ba matsala”.
Godiya Abba ya masa sannan Malam Arɗo ya masa Sallama ya tafi.
Bayan kwana biyu: Moddibo ya fito daga gida jikinsa sanye da Gezner fari soll yayin da kansa ke sanye da hula tangaran baƙa yalwataccen sumar kansa irin na Fulanin Usul yana kwance aƙeyarsa fuskarsa tayi fayau manyan Idanunsa na lumshe yayinda jikinsa ke fitar da sanyayyan ƙamshin tularen Oud Khareem kai tsaye gidan Ummi ya nufa bakinsa ɗauke da sallama ya shiga coumpund ɗin Abaranda ya hango Asma'u na Morping Jin ƙaran buɗe ƙofa yasa Asma'u ta juya ganin Moddibo yasa tace.
“Yah Moddibo sannu da zuwa ka iso mana”.
Ahankali ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.
“Ummin fa naji gidan shiru?”.
Tana matse mopan dake hannunta tace.
“Bata nan”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Ke kaɗai ce agida?”.
Girgiza kai tayi kana tace.
“A'a Bashir na ciki?”.
Kai ya gyaɗa tare da gyara zaman hular dake kansa kana yace.
“Ina Ummi taje?”.
Ahankali ta jinginar da Moper kana tace.
“Ummi ta tafi asibiti saboda kwanan nan ciwon kai yana yawan damunta taje adubuta”.
Cike da kulawa da kuma sanyi yace.
“Subhanallah toh Allah ya sawwaƙe”.
Ahankali Asma'u tace.
“Ameen”.
Moddibo kuwa gyara tsayuwar sa yayi cike da nutsuwa da kuma sanyi yace.
“Asma'u zo muje ki rakani gidansu.
Khausar akwai tambayoyin da nake so nayi mata”.
Kai Asma'u ta gyaɗa cike da jin daɗin hukuncin da yake son ɗauka tace.
“Toh Shikenan Yah Moddibo bari in kira Ummi in Faɗa mata”.
Cikin sauri ya girgiza mata kai kana yayi ƙasa da muryarsa yace.
“A'a kada ki faɗawa Ummi, zata hana mu binciken idan kika faɗa mata zata hana amma yanzu kiyi sauri muje kafin ta dawo yanzu zamu dawo”.
Jinjina kai tayi tare da faɗin.
“Toh shikenan”,Sannan tashiga ta dauki Maroon hijabinta har ƙasa kana ta kalli Bashir dake karatun wani littafi na addini tace.
“Bari muje gidan su Khausar nida Yah Moddibo”.
Ta Ida maganar tare da fitowa.
Miƙewa Bashir yayi tare da fita kana yace.
“Laa Yah Moddibo Sannu da zuwa”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.
“Yawwa Bashir koda Ummi ta dawo kada ka faɗa mata can mukaje kace gidan Innayi muka je”.
Ahankali Bashir ya gyaɗa masa kai kana yace.
“Toh shikenan Yah Moddibo sai kun dawo”.
Suna fita suka shiga mota kana Moddibo yaja suka tafi.
Acan gidan Lamiɗo kuwa cikin sauri Khausar ta fita daga side dinsu ta nufi sashen Gimbiya Bunayya tun kafin ta ƙarasa shiga tace.
“Ummah!, Ummah!!Ummah!!!”.
Daga ciki Hajiya Bunayya tace.
“Na'am”.
Khausar na karasa shiga tace.
“Ummah Raudat tashigo?”.
Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa kana tace.
“Eh tashigo”.
Ƙarasa shiga Khausar tayi tare da Hararan Raudat dake ɓuya tace.
“Raudat kizo muje in miki wanka amma sai wani bauɗewa kikeyi tun ɗazu kina ta gudu”.
Maƙale ka faɗa Raudat tayi tare da tura ƙaramin bakinta tace.
“Ni dai na faɗa miki bana son wankan nan akwai sanyi”.
Cikin rarrashi Khausar tace.
“To ai da ruwan ɗumi zan miki”.
Girgiza kai Raudat tayi tare da tura bakinta tace.
“Ni dai Banason gaskiya”.
Ganin tana son ɓata mata lokaci yasa Khausar ta shiga tare da janyo hannunta tace.
“Maza wuce muje in miki zan baki waya kafin fito kiyi game”.
Bubbuga kafa Raudat tayi cike da Shagwaɓa tace.
“Addah Khausi Ni dai ki ƙyaleni bana so”.
Ahankali Khausar tayi ƙasa da muryanta tace.
“Harda Game ɗin bakya so?”.
Ware Ido Raudat tayi tare da ƙyalƙyala dariya kana tace.
“Allah dagaske Addah Khausi zaki bani?”.
Murmushi Khausar tayi tare da lakace mata hanci tace.
“Eh”.
Suna shiga Bedroom ɗin Raudat ta zauna gefen gado sannan Khausar ta mika mata wayar bayan tasa mata game ɗin _Subway surf_ ta bata murmushi Raudat tayi kana ta fara buga game ɗin.
Khausar kuwa dogon rigar jikinta ta cire tare da ɗaura towel iya ƙugunta ta shiga toilet.
Akuma dai-dai lokacin Moddibo yayi Parking afarfajiyar gida dai dai nan Lamiɗo ya fito da motarsa ganin Moddibon yasa Lamiɗo yayi Parking din motarsa ya fito cikin sauri Moddibo ya ƙarasa kusa dashi tare da basa hannu sukayi Musabaha cike da kulawa Lamiɗo yace.
“Moddibo bar kadai ya gida ya kuma Ƙarin haƙurin rashin Jameelu?”.
Cikin sanyin Murya Moddibo yace.
“Alhamdulillah hakuri mungode Allah”.
Cike da kulawa Lamiɗo yace.
“Allah ya gafarta masa ayi ya masa addu'a”.
Cikin sanyin yace.
“Ameen Mai Martaba Nagode.
dama munzo wajen Khausar ce”.
Cike da kulawa Lamiɗo yace.
“Toh ba matsala Asma'u ku isa”.
Ahankali Moddibo yayi ƙasa da kansa tare da cewa.
“A mai Martaba baza'a a bari daga nan ba”.
Girgiza kai Lamiɗo yayi kana yace.
“Ku shiga ba matsala bari na kira Aysha in Faɗa mata”.
Hannu ya sanya a aljihunsa tare da ciro wayarsa yayi dearling number Mommy tana ɗagawa yace.
“Aysha ga baƙi Moddibo da Asma'u zasu shigo”.
Cike da kulawa Mommy tace.
“Toh ba damuwa su shigo mana”.
Katse wayar Lamiɗo yayi tare da yi musu Sallama kana ya shiga motarsa ya fita.
Moddibo da Asma'u kuwa suka nufi sashen Mommy suna isa bakin barandar Moddibo ya tsaya Asma'u ta ƙarasa shiga falon tare da cewa.
“Assalamu Alaikum”.
Shiru falon ba Kowa sai dai ko ina tsaf-tsaf kana ga ƙamshin dake tashi. Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe tare da nufar Bedroom din Mommy tana cewa.
“Mommy!, Ta ƙarasa tare da shiga Bedroom din Mommy dake sanye da hijabi tace.
“Asma'u kun ƙara so Ina Moddibo?”.
Kai Asma'u ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh amma yana waje”.
Mommy na zama gefen gado tace.
“Toh kice masa yashigo mana ya zaki barshi atsaye”.
Kai Asma'u ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh Mommy”.
Sannan ta juya tare da fita falon ta leƙa ƙofan Falon cikin sanyin Murya tace.
“Yah Moddibo wai kashigo”.
Ahankali ya ɗago kansa tare da buɗe Idanunsa dake lumshe yace.
“Toh”.
Sannan ya shiga falon da komai ke kintse yana fitar da sanyayyan ƙamshin ahankali ya zauna akan 1sitter dake fuskantar ƙofar Bedroom din Khausar.
Asma'u kuwa juyawa tayi tare da kallon Moddibo kana tace.
“Yah Moddibo bari in sanarwa Mommy ka ƙara so”.
Bata jira amsar saba ta nufi Bedroom ɗin Mommy.
Khausar kuwa ahankali ta fito daga toilet tare da juya kanta yalwataccen sumar kanta dake jiƙe ya mannu da wuyanta da kuma gefen fuskarta dake da damshin ruwa fararen cinyoyinta masu haske da santsi na ɗauke da damshin ruwa.
Ware Ido Raudat dake Game tayi tare da kife wayarta akan gadon kana ta dira tare da ficewa da gudu saida ta isa kofar Bedroom din kafin ta tsaya.
Cike da mamaki Khausar ke kallonta kana tana tafiya ahankali tace.
“Raudat ina kuma zaki je?”.
Tura baki Raudat tayi tare da juya Idanunta tace.
“A ni dai Banason wankan nan da kwai sanyi”.
Sake baki Khausar tayi wato ita Raudat zata yiwa wayau, ɓata fuska tayi tare da cewa.
“Aikuwa baki isa ba kisa in. Baki wayata kiyi game sannan yanzu kinga na fito kice zaki gudu”.
Gwalo Raudat ta mata tare da fita da gudu.
Ware ido Khausar tayi tare da bin bayanta da gudu dariya Raudat ta ƙyalƙyale dashi tare da nufar hanyar fita sai kuma ta karya kwana ta nufi Bedroom ɗin Mommy.
Khausar kuwa garin zata karya kwana ta nufi Bedroom din Mommy santsin ruwan dake ƙafarta da kuma santsin tlyes ya jata tayi baya Suuuuuu ta faɗi a ƙasa kana towel ɗinta ya since ya zame yayi ƙ...!
Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA.
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2..... Page 3*
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
*LITTAFIN SAKAYYAH DAI NA KUDINE KO KIN GANSHI A WASU WURAREN DA BA WURINA BA TOH NA SATANE KI