Showing 51001 words to 54000 words out of 218703 words

Chapter 18 - Sakayyah 2 Hausa Novel Complete

tace.
“A'a ai aiken ne dole muzo da kan mu tunda iri muke nema”.
Jim yayi kana yace.
“Ikon Allah wani kalar iri kenan?”.
Ƴar dariya tayi ta gyara zamanta kana tace.
“Iyeee al'amarin ne ya sauya sheƙa”.

Gyara zama Gimbiya Dadu tayi kana tace.
“Eh aihakama shi yafi alkhairi Hausawa sunce naka sai naka daɗin zama sai bare gwara dai kome za ayi ace na kane” .
Ido kawai Lamiɗo ya zuba musu cikin rashin fahimta ko kaɗan bai taɓa fuskantar alaƙar dake tsakanin Amina da Naseer.
Ganin yanda yake kallon Hajiya Kubra tayi murmushi tayi kana tace.
“Akan al'amarin Naseeru ne da Amina”.
Cikin sauri ya kalleta ya girgiza kai kana yace.
“Ba dai Amina da Naseeru ba saidai Nasseru da Khausar dai ko?”.
Dariya tayi tare da gyara dankwalinta tace.
“A'a da Aminar dai”.
Ido ya zuba mata cike da son nazartansu yace.
“Da Amina dai?”.
Jinjina kai tayi ta kalli Gimbiya Dadu kana tace.
“Tabbas da Amina”.
Jingina Lamiɗo yayi da jikin kujeran kana yace.
“A'a baki fahimci maganarsa da kyau ba da Khausar ce kuma al'amarin ma dai gashi nan yanda yazo abirkice”.
Fuska Gimbiya Dadu ta ɓata kana tace.
“Babu abinda ya birkice sai dai sune ya birkice musu acan tunda Khausar ta nuna bata sonsa ai Alhamdulillah ga ƴar Uwarsa ta soshi”.
Cike da Mamaki Lamiɗo ya ɗago kansa ya kalleta yace.
“Da ita Aminar kenan?”.
Jinjina kai Hajiya Kubura tayi kana tace.
“Eh ai Amina da Nasseru sun daɗe da haɗa kansu soyayya suke sosai basu dai fito sun faɗa maka bane suna so sai angama shirya abubuwa komai ya kankama”.
Jinjina kai Lamiɗo yayi still da mamaki atare dashi yace.
“Allah mai iko shi kuma Naseeru ƴarsa zai Aura?”.
Cikin sauri Gimbiya Dadu ta katsesa da cewa.
“Ya haramta ne?”.
Murmushi yayi tare da girgiza kai yace.
“A'a a'a bai haramta ba na isa in haramta abinda Allah ya halatta ba wai ya haramta bane amma da yake tana sunan ƴarshi ce”.
Baki Gimbiya Dadu ta taɓe kana tace.
“To wannan dai ba wani abu bane aciki ka dai kayi fatan alkhairi Allah yasanya albarka acikin al'amarin”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Kuma haka abin ya zama kenan?”.
Kallonsa Gimbiya Dadu tayi kana ta kalli Hajiya Kubura dake murmushi tace.
“Sosai ma tunda naji Kakar Khausar tana cewa ba zata bawa Zuri'ar Mayu ba tana ƙananun surutai shiyasa nace ya janye da nemanta ya nemi Amina ƴar Uwarsa shiyafi mana kwanciyar hankali”.
Ahankali Lamiɗo ya sunkuyar da kansa ƙasa batare da yace Uffan ba.
Dariya Hajiya Kubrua tayi kana tace.
“Ai shiyasa nace bari nazo da kaina muyi magana”.
Anutse ya ɗago kansa ya kalleta ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Toh Yafendo Kubura ai wannan al'amarin Aure magana ce ta maza bata mata ba ai da Babban Naseeru ne zaizo muyi magana zai fiko sai insamu gamsuwa da sahalewar sa za ayi dukkan maganar?”.
Cikin sauri Gimbiya Dadu ta katsesa da cewa.
“Ai zaizo amma dai ta fara zuwane ta sanar maka saboda bakasan da Maganar ba”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Toh shikenan Ubangiji Allah ya mana zaɓin alkhairi”.
Gimbiya Dadu kuwa cikin sauri ta tari numfashi ta hanyar cewa.
“Shine ma alkhairi Nasseru ya auri ƴar uwarsa ita kuma taje can ta ƙarara ta auri duk wanda taga dama da masifaffiyar Kakarta”.
Murmushi yayi kana yace.
“To Allah ya kyauta”.

Miƙewa yayi ya fita kai tsaye sashen sa ya nufa zaune ya samu Hajiya Bunayya da waya maƙale akunnenta tana magana da Hajiya Lami ganinsa yasa tayi saurin cire wayar kana ta katse ta juya ta kallesa zama yayi tare da tsira mata ido tamkar shine rana ta farko da yafa ganinta acikin rayuwarsa.
Ganin kallon da yake bin ta dashi ne tace.
“Ya dai Mai martaba naga kana ta kallona lafiya kuwa?”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe kana cikin tsira mata Ido yace.
“Wai me yake faru tsakanin Naseeru da Amina ne?”.
Cike da farin ciki tace.
“Meye kuma yake faruwa Lamiɗo banda lamarin Aure da muke fatan zai tabbata tunda sun daidaita kansu”.
Wani irin kallo ya watsa mata kana yace.
“Sun dai-dai-ta kansu Meyesa ban sani ba”.
Zare ido tayi tare da ɗage hannunta sama tace.
“Lalala nima Wallahi ban saniba sai kwanan nan bai kai sati ba Amina take cemin wai zai aiko ya gama haɗa kayan Aure su goro da kayan gishiri da kuma sadaki”.
Ido kawai Lamiɗo ya tsira mata bako ƙyaftawa ta cigaba da cewa.
“Hatta kayan rufi ya gama haɗa komansa yana so ayi auren nan da mako biyu nanne nasan da maganar toh tsoron yi maka magana nake ta yanda zan tunkare ka da maganar”.
Cikin wani irin yanayi Lamiɗo ya tsira mata ido tamkar mai son fahimtar wani abu.
Marerece fuska tayi kana tace.
“Ya dai ka zuba min ido Lamiɗo ka yarda dani ai danasan da maganar dana faɗa maka nima abin ya daure min kai shiyasa ban faɗa maka ba”.
Sai kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa kana ta cigaba da cewa.
“Domin nasan da farko Khausar Naseeru yake so to amma shi Naseeru da kansa ya sameni yace Khausar tace bata sonsa to shi ya hakura sannan Gimbiya Dadu ma tace ya nemi Amina ƴar Uwarfashi Lamiɗo ya fesar kana yace.
“Allah ya kyauta amma batun kice baki sani ba zancene Bunayya magana kike”.
Cikin sauri ta kallesa kana tace.
“Wallahi tallahi Lamiɗo ban saniba”.
Cikin yanayin ɓacin rai da takaici yace.
“Dakata Bunayya kada ki rantse dan na lura kamar baki san girma da darajar rantsuwa ba idan kika ce baki sani ba magana ya ƙare”.
Cikin tsinkewar zuciya take kallonsa.Cike da ɓacin rai ya cigaba da cewa.
“Idan kika faɗa kona yarda ko kar nayarda wannan tsakanina ne dake akan abinda kinsan ƙaryane kinsani sannan nasani kuma inada tabbaci da yaƙinin ke kika ƙulla wannan alamarin”.
Cikin yanayin tashin hankali da damuwa tace.
“Fisabilillah taya zan ƙullah”.
Ƙwaffa yayi kana yace.
“Bunayya gani kike kamar bansan komai akanki ba ko?”.
Atake zuciyarta ya tsinke zufa ya fara wanke mata fuska duk da sanyin irin na garin Gembila cikin sauri tace.
“Toh yanzu dan Allah ni menayi?”.

Kai ya girgiza still Idanunsa na kanta yace.
“Hmmm jiki magayi tunda haka kika zaɓawa kanki, duk abinda ya kasance ku kuka da kanku acikin al'amarin nan ya kamata ace komai zakiyi kiyi shawara dani”.
Kasa cewa komai Hajiya Bunayya tayi sai zufa dake wanketa cike da takaici ya cigaba da cewa.
“Amatsayina na mijinki kuma Uba ga Amina amma bakuyi shawara dani ba sai kuka tura Iyayena ta yanda zasu tsareni acikin maganar tunda haka kuka zaɓa magana ta ƙare, kowa ya ɗeɓo da zafi bakinsa!!!”.
Cikin ɓoye tsoronta tace.
“Naseeru fa shiyace ya daina son Khausar”.
Cikin sauri ya katseta ta hanyar cewa.
“Khausar ko baice ya dena sontaba Ni kaina inada nufin bazan bashi Auren Khausar ba, tunda kuma yazo ya zagaya kukayi haka ke kika sani ƴa ƴarki ce shi kuma ɗan uwana ne babu abinda zance”.
Marerece murya tayi kana tace.
“Ni dai wallahi babu abinda na sani aciki kuma itama Amina tace in faɗa maka Babansa yace zai zo gobe”.
Wani kallo ya watsa mata Afusace yace.
“Idan kinga dama kice masa yanzu yazo aɗaure ba haka kike so ba?”.
Asanyaye ta kallesa kana tace.
“Toh fisabilillah dan Amina za tayi Aure shine zai zama laifi ko kuma so kake itama tayi ta zama kamar yanda Asiya take zaune?”.

Cikin tsawa ya ɗaga mata hannu kana yace.
“Ki kiyayi kanki kada ki yarda kijefi Asiya da mugun furuci, Insha Allah Asiya Ubangiji zai jiɓanci lamuranta Asiya zatayi Aure aure mai daraja da izinin Ubangiji baza ta taɓe ba”.
Kallon yanda yayi kicin-kicin da fuska Hajiya Bunayya tayi cikin fushi ya cigaba da cewa.
“Da yardan Allah tunda tayi haƙuri da jarabawar da Ubangiji ya mata za taci nasara baya ga haka duka-duka nawa Asiya take bare Amina dududu ba shekaran daya gabata bane ta gana Secondary ba?”.
Uffan batace ta lura aharzuƙe yake cikin rashin walwala ya miƙe yashiga Bedroom ɗinsa.

*MOROCOW*

Aɓangaren Moddibo Baki daya kansa ya ɗauki zafi aiki suke gadan-gadan Anutse ya fito daga masallacin dake cikin Company ya nufi ainihin inda ake buga Abaya, kama daga Dubai Abaya, Morocco Abaya, Saudia Abaya, da kuma Turkiya Sai kuma Veils,Bags,shoes da sauransu.
Babba wajene sosai ankafa manyan ijinina sabbi ana ta haɗa su ga manyan-manyan AC dake aiki kana ga sanyin garin dake sauƙa wajen ya ɗauki sanyi baki ɗaya aiki suke gadan-gadan babu kama ƙafar yaro da alama nan da Kwanaki biyar za'a haɗa komai gashi an dakatar da aikin komai sai sabbi dake aiki Saboda sabunta Injina da akayi Ma'aikatan na ganinsa suka nufo sa suna Cikin harshen larabci suke masa Barka cike da mutuntawa da kuma girmamawa shima sannu yake musu yana yaba aikin da suke.

Ɗaya daga cikin ma'aikatan wanda yake shine Babba yace.
“Alh aiki na kyau yanda ake buƙata insha Allah nan da kwana biyar za'a gama daddasa Injinan da za'a gama aikin”.
Kallon yanayin wajen Moddibo yayi kana yace.
“Masha Allah abu yayi kyau sosai”.
Kai Engineer ya Jinjina kana yace.
“Sosai ma ai saboda ansamu zaƙaƙuran ma aikata kuma baki ɗaya cikin kwanaki Ukun nan da aka dakatar da buga Abaya's,Veils,Jakankuna da Takalma *BASJAM”.*
Ahankali Moddibo ya lumshe Idanunsa Aransa yace Allah sarki Abba gashi ya haɗa sunan sa dana J ɗina a Company sai dai bashi da ikon aiki a Company Engineer ya cigaba da cewa.
“Baki ɗaya har abin ya fara ƙaranta zuwa ƙasashen da ake kaiwa danma ansamu antanadi masu yawa suna zaune amma Alhamdulillah aikin zaiyi gaggawa tunda ansamu zaƙaƙuran ma'aikata”.
Jinjina kai Moddibo yayi tare da lumshe idanunsa saboda sanyin da wajen ke dashi kana yana jin yanda Kasan mararsa ke murɗawa ahankali ya ɗaura tafin hannunsa na dama akan maransa ya danna sai kuma ya cije Lips ɗinsa na ƙasa cikin dauriya ya kalli Engineer tun jiya ya kwana da ciwon cikin kana har yau bai lafaba na awa ɗaya mai kyauba da zaran yayi minti talatin zai sake murɗa masa ahankali ya cije Lips ɗinsa kana yace.
“Abu yayi kyau Allah yatemaka insha Allah nan kusa zamu kammala akoma bakin aiki a cigaba da aiki gadan-gadan”.

Ya ida maganar tare da juyawa ya nufi gefen dama wanda office, Office ne awajen wani Corridor ya shiga tare da buɗe makeken Office da yafi sauran kyau da tsaruwa sosai Office din ya haɗu table ne kansa ɗauke da system da takardu sai flowers kana daga jikin bango kujera ce mai juyawa daga gaban table ɗin kuma kuma jeru biyu ne sai Cottons sky blue da fari daga gefen dama Ac ne daga ɗaya gefen kuma tamkar falo ne manyan kujeru ne guda bakwai suma Sky blue sai Tv Plasmer ajikin bango da frigde sai kuma showglass dake ɗauke da kofuna ahankali ya ɗauki remote din AC yaƙara gudu duk da kuwa sanyin da ake stugawa yayin da zufa ya shiga tsats-tsafo masa agaba ɗaya ilahirin jikinsa kana maransa na cigaba da murɗawa jikinsa sai zufa yake karyo masa rintse idanunsa yayi da ƙarfi jin yanda mararsa ke murɗawa tamkar zai fita ahankali ya zauna kana ya ɗaura kansa akan Center table dake tsakiyar falon ya lumshe idanunsa sai kuma yayi saurin buɗewa kana ya lashi busassun laɓɓansa baki ɗaya jikinsa ya fara rawa jin yanda maransa ke dunƙulewa yana tsikarinsa cike da damuwa da rauni ya soma faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.
Kana yaja wani numfashi me nauyi ya yunkura da niyyar miƙewa ji yayi bashi da kuzarin da zai iya tsayawa ji yayi tamkar an haɗa maransa da bayansa ana dinkewa ga wani irin harbawa da zuciyarsa keyi da Masifar ƙarfi kwanciya yayi akan 3sitter yayi rub da ciki baki daya ilahirin jikinsa rawa yake ga zufa dake tsats-tsafo masa tamkar babu Ac saboda yanda azabebben ciwon cikin ke gallazarsa yakai kimanin minti talatin yana murƙususu akan kujera kafin ya fara lafawa sannu Ahankali ya fara maida numfashi yana fesaewa.

*Gembila*

Asma'u kuwa ta daɗe tsaye aƙofar gida bata samu Adaidaita ba jin kiran sallar La'asar yasa ta juya da niyyar koma gida tayi Sallah kuma sai tasamu adaidaita shiga tayi tana isa gidan Kai tsaye falon Mommy ta shiga bakinta ɗauke da sallama zaune ta samu Khausar da Haiydar tana riƙe da hannunsa tana yanke masa Farce.
Haiydar kuwa kallon Khausar yayi kana yace.
“Nifa ki kula kar ki yanke min hannu”.
Hararansa tayi sai kuma ta cigaba da yankewa kana tace.
“Tunda dai baka iya ba kona yankekama kai ka jawa kanka”.
Ta ƙarasa maganar tare da sauke Idanunta akan Asma'u data gama shiga falon da sauri ta sake masa hannunsa tare da miƙewa da sauri ta Rungume Asma'u cike da farin ciki tace.
“Oyoyo Asmeey ta”.
Zare ido Haiydar yayi tare da yarfe hannunsa yace.
“Wayyo ta yankeni Wayyo ya tsana”.

Da sauri Mommy ta fito daga Bedroom ɗinta Idanunta akan Haiydar tace.
“Lafiya kuwa”.
Yarfe hannu Haiydar yayi kana ya Marerece fuska yace.
“Mommy ki kallafa Addah Khausi ta yanke min yatsana daga kallon Asma'u”.
Langwaɓar da kai Asma'u tayi kana tace.
“Ayyah Haiydar Sorry sannu bata sani bane”.

Hararansa Khausar tayi tace.
“Rabu dashi ƙato dashi tunda dai har yanzu bai iya yanke Farce ba sai dai in yanke masa aikuwa nata yanke masa hannu”.
Kallonta Mommy tayi kana tace.
“Wato ma da saninki kika yanke sa?”.
Cikin sauri ta girgiza kai tare da langwaɓar da kai tace.
“Wallahi Mommy ban sani ba ganin Asma'u ne yasa na tashi da sauri ashe na yanke sa”.

Kai Mommy ta gyaɗa tare da kallon Haiydar tace.
“Sannu Babana mu gani”.

“Mommy Ummina tace in gaisheki”

Jinjnna kai Mommy tayi kana tace.
“Ina amsawa”.
Hannun Asma'u Khausar taja suka shiga Bedroom ɗinta suna shiga Khausar tace.
“Fisabillah baki zoba sai yanzu ko dai kwana zamuyi?”.
Zare ido Asma'u tayi kana tace.
“Mu kwana kuma wa zai taya Ummina aiki da safe?”.
Langwaɓar da kai Khausar tayi sai kuma tace.
“Don Allah Asmeey mu kwana zan kira Ummi mu roƙeta”.
Kai Asma'u ta girgiza kana tace.
“A'a keto muje mu kwana mana”.
Ware ido Khausar tayi tare da sanya dariya tace.
“Caɓɓ lallai kam”.
Murmushi kawai Asma'u tayi kana ta zauna abakin gadon.
Khausar kuwa fridge ta buɗe ta ɗauki Plate ta sanya Faro water da Ayaba ta mikawa Asma'u.
Karba Asma'u tayi tana ɓare Ayaban tace.
“Ke dai bakya rabuwa da Ayaba aɗaki kina nan kamar biri”.
Murmushi Khausar tayi kana tace.
“Wallahi kuwa Ina son Banana yana min daɗi”.
Jinjina kai Asma'u tayi tare da faɗin.
“Ai lallai dai kam”.

*Morocco*

Aɓangaren Moddibo kuwa haka yaita fama bayan minti talatin cikin yake sake Murɗansa yana kallon gari yayi duhu maghariba ta kawo kai har wasu massallatai sun fara kiran sallah amma ya kasa miƙewa saboda yanda ciwon cikin ke kartansa jin ciwon ya lafa yasa ya miƙe tare ya fita yaga wajen shiru alamar duk ma aikata sun tattafi sai securities da mai bawflowes ruwa kasancewar karfe biyar da wasu Mintuna ake tashi ma tsaye wajen motarsa yashiga yaja ya fita a gate one.
Ya miƙe titin ya fito gate ɗin La riva restaurant dake Opposite da Company yazo Dai-dai wajen Traffick sun tsaida shi saboda sauran motoci da suke wucewa ahankali yasa hannunsa ya dafe fuskarsa ta gefe yatsunsa na dafe da kuncinsa ya tsansa ɗaya kuma na cikin bakinsa kana ya fito da fuskarsa ta wajen motar yana ɗan shan Iska jikin katangar Company sa yana shaƙan iskar bishiyar dabino dake zagaye da Company wanda ta ko ina sune da gudu yaga wata mota ta gilma ta gabansa wacce ta fito daga gefen yamma zata yi gabas kana shi kuma yana gefen kudu ne idan ya samu dama zaibi arewa ganin wulgawar motar yaga fuskar J ɗinsa ne aciki cikin sauri ya zare Idanunsa sakamakon kallon fuskar J ɗinsa aciki Motar cikin wani irin sauri ba tare da anbasa hanya ba ya figi motar ya karya kwana yabisa har ya kusa bige wata mota.

Da mugun gudu yake bin motar kana ga cunkoson ababen hawa kasancewar maghariba ta kawo kai ƴan kasuwa sun taso ga kuma ma'aikata sun tattaso daga Office kowa na burin komawa gida wasu kuma na ƙoƙarin su samu masallacai dan kada su rasa jam'i hakan yasa cunkoso yayi yawa ga kuma duhun gari gudu yake yana bin bayan motar ga kuma cun kuson motoci da suka taresa ya cusa ta nan yaga antaresa baki ɗaya ilahirin jikinsa rawa yake tun lokacin daya zare idonsa har yanzu bai maidasu daidaiba saboda idanunsa sun gane masa Allah ya nuna masa fuskar Jameel ɗin sa ne yasani Koda amagagin mutuwa yake ya tabbatar fuskar Jameel wulgawa daya zaiyi ya gane yasani wannan fuskar Jameel ɗinsa ne baki ɗaya ilahirin jikinsa rawa yake kana yana maimaita kalmar Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n yana cigaba da dannawa motocin gabansa hon baki daya mutane Kallonsa suke wasu kuma na cewa wannan kam lafiyarka ina zakaje haka kamar zaka tashi sama shidai haka ya cigaba da tafiya ya kutsa tanan ya kutsa tacan garin hakane ya bigewa wani motarsa mutumin na cewa Kai lafiya amma ina tuƙi kawai yake da gudu baki ɗaya hankalinsa baya jikinsa wani mai Napep ne ya tare gabansa madadin ya kalli gabansa amma baki ɗaya idanunsa na kan motar daya yaga J ɗinsa aciki yana samu ƙaramar ɗin ya kauce masa ya cigaba da bin bayan motar yanda yake gudu da masifaffen ƙarfi haka zalika motar da yake bi ɗin ma take gudu hakan yasa yasake tabbatarwa kansa J dinsa ne kenan gudunsa yake ko kuma yaya ahaka suka isa wani roud about nan yaga ya ɗauki hanyar da zata sa dashi da flyover gudu yake da ƙarfi haka shima wancen ke gudu duk da gudun da yake amma ya kasa kamo wancan motar saboda shima gudun yake ga kuma motoci dake tsakaninsu amma yana iya hangosa kasancewar be wuce motoci biyu zuwa uku bane agabansa sunzo daidai kan Flyover yasamu yabi sama Shima Moddibo cikin sauri yabi sama kasancewar ba cunkoso sosai numfashi mai karfi ya sake kana ya hau kan Flyover yabi sana kafin ya isa tsakiyar Flyover shi kuma wannan har ya sauƙa ya ɗauki hanyar Unguwar Mellila shima Moddibo cikin sauri yabi wannan hanyar tafiya kaɗan sukayi yaga motar ta wuce wani asibiti cikin gudu shima ya wuce tafiya kaɗan suka ƙara yaga motar taja kwana adai-dai wani tamfatsetsen gini mai masifar kyau da girma bisa duk kan alamu asabiti ne saboda sunan dake manne asaman ginin idanunsa ya ɗaga yaga sunan dake manne ajikin ginin *Youssef Mouley Hospital*.
Mai motar kuwa yana danna hong aka buɗe masa gate yashiga kafin ya juya akalar motarsa ya ƙarasa wajen kuma a maida gate din ana ƙoƙarin rufewa da wani irin sauri ya danna hancin motarsa cikin gate din.

Cikin sauri securities dake bakin gate din suka taso suka yo Kansa.
Shi kuwa mutumin cikin motar tuni yayi Parking ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login