Showing 18001 words to 21000 words out of 218703 words
tare da kallon Dije tace.
“Dija mu tafi”.
Numfashi Lamiɗo ya fesar kana yace.
“A'a Khausar zauna”.
Kai ta gyaɗa tare da komawa ta zauna kana ta sunkuyar da kanta ƙasa hawaye na ciko mata ido.
Ahankali Lamiɗo ya sake yin ƙasa da kansa kana yace.
“Toh Hajja Nana naji abinda yake tafe daku, akan batun Khausar da ɗan Uwanta Aliyu”.
Cikin sauri Khausar ta ɗago kanta tare da kallon Lamiɗo sai kuma tayi saurin sunkuyar da kanta hawaye na kwaranyo mata kana zuciyarta na bugawa da masifar ƙarfi.
Ahankali Abba ya cigaba da cewa.
“Ni babu wata matsala daga gareni, duk da da akwai ƙanina ɗan Yafendo na dake son Khausar tun tana ƙarama, toh amma sawun giwa ya take na raƙumi, abinda kuke ce shi za ayi domin koda inada power akan Khausar kun fini ƙarfi”.
Sai kuma ya ɗago kansa tare da kallon Hajja Nana data tsaresa da ido Ajiyar zuciya ya sauƙe kana ya cigaba da cewa.
“Amma Koda batun Naseer bazai kau da batun ku na kawo na Naseer ba, duk da cewa bamu ji ta bakin yarinya ba duk da naga alamun ta dai-dai-ta da ɗan Uwanta tun da yanzu bana ganinsu da Naseer”.
Ya kare mgnar tare da kallon Khausar da tayi ƙasa da kanta fuskarta cike da hawaye numfashin ya ɗan fesar kana yace.
“Sannan ba aji ra'ayin Khausar ba, domin yaran yanzu ba ayi musu dole sabida haka ya kamata aji ra'ayin Khausar idan tanason.
Ɗan Uwanta tofa sawun Giwa ya take na raƙumi idan kuma Naseer take so tou sai mu nemi al'farma a wurinku”.
Ƙankance ido Hajja Nana tayi kana ta shiga girgiza ƙafanta tare da kallon Lamiɗo tace.
“Lalle kam kamar yanda ka faɗa haka ne, sawun Giwa ya take na raƙumi, sannan batun so kuke ɓata ƴaƴanku mu da ai sai dai a aura maka ko kana so ko baka so, kuma hakan be hana zaman lafiya ba”.
Ahankali Lamiɗo ya sunkuyar da kansa cikin girmamawa da tausashi harshe yace.
“Ai zamani ne ya sauya Hajja Nana Da da yanzu ba ɗaya bane amman yanzu bari muji ta bakinta”.
Ya kare mgnar tare da gyara zamansa ya fuskanci Khausar cikin tausasawa yace.
“Khausar”.
Murya na rawa ta amsa, yayinda tuni hawaye ke kwaranya.
Mommy kam numfashi mai nauyi ta fesar tare da kauda kanta ranta cike da tausayin yarta.
Shi kuwa Lamido cikin kulawa yace.
“Ki dena kuka Khausar kada ki damu ki gaya min cikin mutun biyu Aliyu Dan uwanki da Naseer wa kikeso, kada kiji tsoro kinjiko Mamana gaya min”.
Jin hakane yasa Khausar ɗago kanta ahankali zuciyarta na cike da wani irin masifaffen rauni murya na rawa ido na kwaranyar da hawaye ta kalli Lamiɗo tare da cewa.
“Abba Ni dai bana sonsa”.
Cikin sauri Hajja Nana ta kalli Khausar tare da ƙankance Ido a faɗace tace.
“Don Ubanki to Naseerun kike so dangin Mayu!?”.
Sassayan kuka Khausar ta saki tare da cewa.
“Nikam shima bana sonsa”.
Kusan a tare Mommy da Hajja Nana da Lamiɗo duk suka kalleta.
Cikin tsawa da masifar isa da iko Hajja Nana tace.
“Toh wa kike so?, sannan me kike nufi ?,wa zaki Aura?, tunda kince bakyaso Aliyu ba kyason Naseerun?”.
Shiru batace komaiba, sai kuka.
Ganin haka yasa Lamido yin gyaran murya cikin Muryar lallashi yace.
“Toh wa kikeso Manana?”.
Kukan ne ya fara tsanantan mata kana a raunace ta ƙara sunkuyar da kanta.
Afusace Hajja Nana tace.
“Toh dan ubanki wa zaki Aura? Wa kikeso?”.
Cike da sanyi murya na rawa tace.
“Ni dai akwai wanda zan aura?”
Mommy kuwa da sauri ta kalli Khausar wacce tunda aka fara magana bata ce Uffan ba cike da mamaki tace.
“Khausar dawa ye kike soyyayya ban saniba wa kike so wa zaki Aura!?”.
Ahankali Khausar ta gyara zamanta tare da sun kuyar da kanta ƙasa kana tace.
“Ni Moddibo nake so”...!
*LITTAFIN SAKAYYAH DAI NA KUDINE KO KIN GANSHI A WASU WURAREN DA BA WURINA BA TOH NA SATANE KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI BABU HAƘƘIN WANI A GANKI LITTAFIN SAKAYYAH 1K NE KACAL DUK DA YAWANSA DA DAƊINSA DUBU ƊAYA NEFA KACAL, ki biya dubunki ɗaya ki karanta maimkyau ba sallake-sallake babu kin samu wasu PAGE ɗin baki samu wasuba ki karanta abinki one by one tura kuɗin samun damar karantawa ta asusuna na GTBank. 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 sai in tura miki karanta lfy lafiya. Mu guji yaƙin wani duk ƙanƙantarsa domin na watan nan dai na Allah ya isane atoh*
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 4*
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Zare ido Hajja Nana tayi cike da matsanancin mamaki al'ajabi haɗi da alhini.
Tayi salati tare da tafa hannu.
Muryanta na cike da mmki, takaici, haɗi da fusata ta cigaba da cewa.
“Ohh Allah ya kawo mu ƙarshen duniya, yarinya babu tsoron Allah bare aje ga babin kunya ki dubi tsabar Idona ki kuma dubi tsabar idon Mutumin dake matsayin Mahaifinki, sannan ki dubi tsakar idon Mahaifiyarki kice wai wane kike so!”.
Cikin raunin Khausar tayi ƙasa da kanta tana mai rumtse idonta tana jin wani irin yanayi mai cike da rauni azuciyarta.
Wani shegen kallo Hajja Nana ta watsa mata cikin tsananin fushi da ɓacin rai tace.
“Wanene shi Moddibo? wani gantalellen yadine Moddibon? shin inane tushensa su waye ne Asalinsa dame yafi ɗan uwanki da har kika zaɓe sa kika ƙyale ɗan Uwanki dame yake taƙama!?”.
Ta ida maganar tana me tsare Khausar da ta ɗan ɗago kanta fuska cike da rauni, ita Hajja Nana da idanun fusata ta banka mata harara.
Ita kuwa Khausar ahankali ta sake sunkuyar da kanta ƙasa batare da tace. Uffan ba yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke tsuma.
Cikin sanyi Lamiɗo ya sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi tare da jinjina kansa kana ya maida kallonsa kan Khausar da kanta ke ƙasa.
Mommy kuwa cikin yanayin mamaki da yadda maganar tazo mata abazata ta tsirawa Khausar Ido tana maimaita abinda Khausar ta faɗa aƙasan ranta.
Girgiza kai Hajja Nana tayi tare da juyawa ta kalli Mommy tare da sakin kuka kana tace.
“Yanzu Aysha Ina magana kema kinyi min banza, baza ku bani amsaba, wato ni zaku mayar gantalalliya ga tsohuwar banza tana magana dole ku shareni tunda kun mayar dani bansan abinda nake ba”.
Sai kuma ta maida kallonta kan Khausar cikin matsanancin ɓacin rai da kuka tsufa tace.
“Yanzu abinda kika zaɓawa kanki kenan Khausar!?.
Yanzu abinda zaki yimin kenan? Kice ba kyason ɗan Uwanki?. Wannan dangin Mayu da kika ce bakyaso ai ban damu ba amma ki dubi tsabar Idona kice bakyason jininki ɗan uwanki yaro mai mutunci da kamala?”.
Mommy, Lamiɗo, da Dije baki ɗaya Idanu suka zubawa Hajja Nana suna kallon yadda take kukan tsakaninta da Allah Khausar kuwa still Kanta na ƙasa ita kadai tasan abinda take ji.
Cikin fushi da tsawa Hajja Nana ta kalli Khausar data ƙi ɗago kanta tace.
“Waye shin dame yafi Aliyu?.
Wato dai ya tabbata babu tsoron Allah acikin waɗannan tsayayyun idanun naki, banda lalacewa da taɓarɓarewar tarbiyarki shin har kina da bakin da Iyayenki na maganar aurenki zaki sanya naki aciki da masifar tijara?”.
Cikin sanyi Khausar ta ɗago kanta, tare da buɗe idanunta wanda tuni suka sauya launi daga farin madara zuwa jan rushi, cikin rauni ta kalli Hajja Nana dake zazzaga bala'i kamar ba gobe.
Sai kuma ta lumshe idanunta kana ta buɗe, amma ko ƙala bata ceba.
Afusace Hajja Nana dake kuka tace.
“Maza ki daina kallona da wannan.
Fitsararrun idanunki dake tsaye kamar Nonon maza tunda kin shafawa Idanunki baƙin kwalli, adole gaki ƴar tijara.
Ohoɗijam kai ni wallahi tallahi billahil-azem tunda nake ban taɓa kallon abinda ya gigitani ya ratsa ƙwaƙwalwa ta irin wannan maganar taki ba!”.
Sai kuma ta sanya bakin zaninta tare da sharce hawaye da yar majina still tana kuka tace.
“Yanzu Khausar me kike nufi dani?, kina nufin Baffanki da yayi tattaki tun daga Adamawa yazo nan yazo abanza mu taso tun daga Jauro yaya da sanyin safiya munyi a wofi kenan?.
Ki dubi tsabar Idanun mu saboda baki da kunya kice bakyason Jikana sannan ki dubi tsabar idon Baffanki kice bakyason.
Ɗansa bayan shi zai bada Aurenki?”.
Kasa ɗago kai Khausar tayi ta kalleta sabida wani irin abu take ji azuciyarta yayin da hawaye suka shiga bin kuncinta.
Mommy Kam ta gumi tayi baki ɗaya kanta ya kulle da lamarin ta rasa ta yanda zata fara misalta abin.
Lamiɗo kuwa ganin yanda Hajja Nana ke kuka haiƙan ƙadaran tana surutai yasa ya sassauta muryarsa tare da cewa.
“Dan Allah Hajja Nana kiyi haƙuri ki daina wannan kukan”.
Saurin ɗaga masa hannu tayi still tana kuka tace.
“A'a barni idan banyi kuka ba me kake so inyi tunda Allah ya haɗani da gantalalliyar jika dake son kunyatani a Idanun duniya anya yarinyar nan tana da hankali kuwa kodai akwai abinda ke damun aƙwaƙwalwar , hegiya fitsararriya”.
Cikin rauni da alamun damuwa Khausar ta ɗago Idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye ta kalli Hajja Nana muryanta na rawa cikin sanyin tace.
“Dan Allah ni. Ki daina zagina Hajja Nana ki daina Sheganta ni ke kinfi kowa sanin cewa niba Shegiya bace kuma ki daina zagin Ubana ki daina saka shi acikin wannan maganar ki barshi ya kwanta akabarinsa cikin nutsuwa da salama tun da dai ba wani mugun abu na aikata ba bare kiyita ihu kina son tara mana mutane”.
Cikin fushi da takaici Mommy ta Kai hannunta na dama tare da kwaɗawa bakinta mari kana ta watsa mata Harara tare da cewa.
“Rufe min baki fitsarariya mara kunya. Wallahi Khausar kin bani mamaki sam ban taɓa zaton haka daga gareki ba agaban idanun mu Khausar yaushe kika zama haka ni zaki kunyata?”.
Da sauri Khausar taja baya tare da fashewa da matsanancin kuka me tsuma zuciya.
Cikin sanyi Lamiɗo ya kalli Khausar dake kuka tamkar ranta zai fita kana yace.
“Khausar tashi ki tafi ɗaki”.
Da gudu ta miƙe ta nufi ɗakinta, kana Dije ta mara mata baya. Khausar na shiga ɗaki ta faɗa kan gado tare da fashewa da matsanancin Kuka me tsuma zuciya da ban tausayi yayin da hawaye wani ke bin wani suna kwaranya daga Idanunta.
Acan Falon kuwa ta inda Hajja Nana ke shiga ba tanan take fita ba, baki ɗaya Idanunta sun rufe sai Masifa take zazzaga musu musamman Mommy ganin yanda take zazzaga Masifa ba Full stop bare commer yasa Lamiɗo kasa fadar abinda ke ransa cikin sanyin murya da ladabi yace.
“Dan Allah Hajja Nana kiyi haƙuri, muyi mgnar a tsanake, kinfa san shi Aure fa rabone, sannan nufi ne na Ubangiji sannan matar mutum kabarinsa, idan har Allah ya ƙadarta cewa Aliyu shine mijin Khausar to fa duk duniya idan za'a haɗu babu wanda ya isa ya raba wannan auren”.
Wani irin kallo Hajja Nana ke binsa dashi tana mai tafasa dan masifa.
Cike da ladabi da kuma sanyin murya Lamiɗo ya cigaba da cewa.
“Idan kuma har Allah bai ƙadarta cewa Aliyu shine mijinta ba, tofa babu wanda ya isa yasa hakan ya kasance, dan haka dan Allah kiyi haƙuri Insha Allah komai zai dai-dai ta”.
Girgiza kai Hajja Nana tayi tare da juyawa ta kalli Mommy da kanta ke ƙasa cikin fushi tace.
“Lallai Aysha dama irin wannan tarbiyyar kika bawa ƴarki kenan?
Yanzu mu awajen mu wace yarinya ce ta isa ta kalli tsabar idon magabatan ta tace wai ga wanda take so wannan abin kunyar har ina?”.
Cikin sanyi da alamun damuwa Mommy ke kallonta baki daya ta rasa wani kalma za tayi amfani dashi wajen bawa Hajja Nana haƙuri.
Hajja Nana kuwa ƙwaffa tayi cikin rawan murya ta cigaba da cewa.
“Tirrr da wannan rayuwa wai yarinya ƙarama kamar Khausar har tasan ta tsaya agaban manya tace ita ga wanda take so, watoma kenan itace zatayiwa kanta zaɓin mijin da zata aura.
To mu azamanin mu koda ya rinya itace Sarauniyar kyau idan magabatan ta suka zaba mata miji koda kuma shine Sarkin munin duniya haka zata zauna dashi bare me Khausar zata nunawa Aliyu?Mutumin da koda kyaune ya fita”.
Ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauke tare da gyara zaman sa kana ya tsira mata idanu yana mamakin yanda ta ɗauki al'amarin da zafi kawai dan Khausar tace Moddibo take so shine ta kafa aƙota sai kace wacce akace tayi cikin shege shi kam baiga abin tada jijiyoyin wuya akan maganar ba.
Numfashi ya fesar tare da sassauta muryarsa yace.
“Dan Allah Hajja Nana kiyi haƙuri Insha Allah komai zai dai-dai ta akwai yarinta atare da Khausar har yanzu bata mallaki hankalin kanta ba, amma bawai dan baki isa da ita bane yasa tayi magana”.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da ɗago kanta kana cikin sanyin murya ta kalli Hajja Nana dake matsar kwallar da taƙi fitowa tace.
“Dan Allah Hajja kiyi haƙuri wallahi Ni kaina ban taɓa jin wannan kalmar abakin Khausar ba, sai yau da ace tun farko naji to wallahi bazan bari ya fito fili ba zan dakatar da ita”.
Wani irin kallo Hajja Nana ta watsa mata tare da ƙankance ido tace.
“Wallahi ƙarya kike Aysha Babu ta yanda za ayi ƴarki na soyayya da wani amma baki sani ba, kawai dai so kike kinuna min iyakata akan Khausar kuma kisani duk abinda zakiyi ke dai baki isa ki canza matsayina ba”.
Kai Mommy ta girgiza cikin sanyi da ladabi ta cigaba da bata haƙuri haka zalika Lamiɗo hakuri kawai suke bata.
Miƙewa Hajja Nana tayi tare da ƙankance Ido ta kalli Lamiɗo da Mommy kana ta ya mutse baki tare da cewa.
“Ni dai Wallahi Allah wannan maganar jinta nake kamar saɓon Allah”.
Cike da damuwa Mommy tace.
“Dan Allah kiyi haƙuri ki zauna. Khausar tayi kuskure amma zamuyi wa tufkar hanci”.
Cikin sauri Hajja Nana ta kalli Mommy tare da faɗin.
“In zauna fa kika ce? Inani ina zaman nan? Ina sam nikam banga wajen zama ba. Subhanallah Allah ya tsareni ai sai Girgiza ƙasa ya rufta dani aciki yarinya budurwa yarinya ƙarama har tanada tsaurin idon da zata zauna tsakanin magabatan ta masu aurar da ita, ta iya buɗe baki tace bata son zaɓin su sai zabinta”.
Ta ida maganar tare da ficewa tana mita, da korwa da kororowa haɗi da kormoto.
Cikin sauri Lamiɗo da Mommy suka bi bayanta cike da girmamawa suke bata haƙuri amma firr wannan fitinenniyar tsohuwa taƙi sauraronsu tafiya kawai take tana kumfar baki, har ta isa Farfajiyar gidan.
Dai-dai lokacin Hajiya Bunayya ta fito tare da kallon Hajja Nana sai kuma ta maida kallonta kan Mommy dake aikin rarrashin Hajja Nana tana bata haƙuri tace.
“Aysha lafiya kuwa yau nakeji hayaniya naga kamar ran Hajja Nana aɓace".
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe cikin sanyin murya tace.
“Dan Allah Hajiya ki tayamu bata haƙuri fushi tayi”.
Kallon Hajja Nana. Hajiya Bunayya tayi da murmushi afuskarta tace.
“Ayyah Hajja Nana kiyi haƙuri dan Allah”.
Ko kallonta Hajja Nana ba tayi ba bare ta tanka ta ta nufi jikin mota.
Baffa Jimeta da Baffa Liman dake zaune Falon Lamiɗo kuwa jiyo hayaniyarta yasa sukayi saurin miƙewa tsaye, sai kuma suka nufi wajan jin Muryan Hajja Nana na tashi cikin sauri suka fito tsaye suka hangota jikin motar tana ta sababi kallon Baffa Liman Baffa Jimeta yayi cike da mamaki yace.
“Yau kuma waya taɓo Hajja Nana haka?".
Girgiza kai Baffa Liman yayi tare da faɗin.
“Allahu a'alam amma dai baya wuce Khausar ba”.
Suna isa jikin Motar Baffa Jimeta ya matsa kusa da ita tare da sassauta murya yace.
“Hajja lafiya kuwa me yafaru?”.
Kallonsa tayi cikin fushi tace.
“Wuce mu tafi ina Liman maza ku wuce mutafi wannan gida ba gidan zuwa bane gidan fitsararru da rashin tarbiyya”.
Dai-dai lokacin Gimbiya Dadu ta fito daga sashen ta jin hayaniyar babu walwala afuskarta ta kalli Hajja Nana tare da cewa.
“Dakata!, Mukam ba fitsararru marasa tarbiyya bane Jikar kice dai fitsararriya mara tarbiyya”.
Afusace Hajja Nana ta kalleta tare da ɗaga mata hannu cikin fushi da ɗaga murya tace.
“Keee dakata kada kice zaki faɗa min magana”.
Cikin sauri Lamiɗo ya juya ya kalli Gimbiya Dadu cikin sanyin murya yace.
“Dan Allah Mama kada kiyi magana, ki taya mu bata haƙuri baki san meye ɓata mata rai ba”.
Taɓe baki Gimbiya Dadu tayi kana tace.
“Yo aiji nayi tana haɗa mana Jami'n zuriya gaba ɗaya ne tana aibanta mu”.
Tafe hannu Hajja Nana tayi tare da ƙankance ido kana tace.
“Toh Zuri'ar taku ta arziƙi ce? Nace zuru'ar taku har wata kayan gabas ce? Kin sani dai na sani. ko kuma wata tsiyace da ita zuri'ar Mayu”.
Girgiza kai Baffa Jimeta yayi tare da cewa.
“Inalillahi Ash'sha haba Hajja Nana dan Allah kiyi haƙuri mana”.
Kusa da ita Baffa Liman ya matsa cike da rarrashi yace.
“Dan Allah Addah Hajja am kiyi haƙuri ki kwantar da hankalin ki kizo muje mu zauna”.
Girgiza kai tayi tare da faɗin.
“Inaaa zan zauna mutafi kawai nifa bazan zauna awannan gidan ba wallahi banga wajen zama ba wannan abin kunya da tashin zuciyar ba dani ba”.
Ganin yanda ta tashi hankalinta yasa Baffa Jimeta ya buɗe mata bayan mota tashiga sannan ya zagaya yashiga mazaunin Driver Baffa Liman ya zauna gefensa.
Ahankali Lamiɗo ya matsa jikin motar ta Side din da hajja Nana ke zaune cike da ladabi yace.
“Dan Allah Hajja kiyi haƙuri akan abin da ya faru”.
Girgiza kai tayi tare da cewa.
“Ba komai Lamiɗo ai ba laifin ka bane, ai kai baka da laifi aciki laifin uwarta ne da ita kanta”.
Mommy Kam da kallo tabi motar har ya fice daga gidan.
Bayan sun fita Baffa Jimeta ya juya tare da kallon Hajja Nana da tayi kicin-kicin da fuska kana yace.
“Toh Hajja yanzu gida zamu tafi kenan?”.
Girgiza kai tayi tare da cewa.
“Kaini gidan ƙawata Innare”.
Jinjina kai yayi kana yace.
“Toh”.
Kai tsaye gidan su Moddibo ya nufa da motar.
Acan gidansu Abba kuwa zaune yake afalonsa cikin yanayin shiru-shirun daya saba ya tallafe haɓarsa da hannunsa na dama baki ɗaya ya rame dan bai cika Lafiya ba ahankali ya kalli center table dake gabansa jin wayarsa na ruri ɗauka sunan Manager company sa dake Marocco ne ya bayyana Picking Yayi tare da kaiwa Kunnensa sannan yayi sallama.
Bayan sun gaisa Manager ya fara mishi mgn da larabci kamar yadda suka saba yace.
“Yallaɓai sabbin kaya da mukayi Order daga Chaina sun iso gaba ɗaya sannan ana bukatar kai ko ni wani ya zamana yana wajen domin aikin sabbin na'uran sarrafa Arabia Gawn da mukeson fara sabbin samfurin.
To gashi kuma ni yanzu ba na nan, kasan ina India naje aduba min lafiyar ƙafana to dole since sai an wakilta wani kafin asauke kayan aga yanayin da abubuwan suka iso lafiya”.
Jingina