Showing 192001 words to 195000 words out of 218703 words

Chapter 65 - Sakayyah 2 Hausa Novel Complete

da Dr Jameel zaune afalon Hajiya Bunayya tana zaune Sai murtsukuku take yi akan kujeran jin yanda tsutsotsin ke cinta yayin da Amina ke zaune gefenta bisa duk kan alamu Alhamdulillah ta fara samun sauƙi har nishinma duk ta daina .
Anutse Dr Jameel ya kalli Hajiya Bunayya kana yace.
“Akwai tests ɗin da za'a Miki.
Sai kiyi ƙoƙari kije asibitu aduba ki acan”.
Cikin sanyi tace .
“Nagode Nagode Dr Jameel Allah ya saka da Alkhairi ”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Bakomai”.
Kana suka miƙe suka fita dai-dai lokacin kuma Dr Zakariyya da Asiya ne zaune amota suna hira fitowa su Dr Jameel ne yasa Asiya yiwa Dr Zakariyya sallama ta fita kana Dr Jameel ya shiga Motar.

Moddibo kuwa bayan Khausar dake shiga Side ɗin Momy ya nufa yana shiga falon yaga ba kowa sai Raudat dake kallon Catoon yace.
“Raudy ina Addah Khausy?”.
Hankalinta na kan kallon tace.
“Tana ɗakinta”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Momy fa?”.
Still idanunta na kan tv tace.
“Tana gidan Ummin Jameel Yah Haiydar ya kaita”.
Kai ya gyaɗa kana ya shiga ɗakin Khausar zaune ya sameta agaban Weldrop ɗin ta gabanta littafaine tana ta duddubawa.
Da mamaki ta kallesa kana tace.
“Yah Mu'allim har nan kuma?”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Eh ai gidan mune”.
Kai ta gyaɗa hannunta na kan littafin tace.
“Eh nasani ai yanzu in Momy tazo ta same mufa?”.
Murmushi yayi tare da shafa sajensa kana yace.
“Eh dai-dai kenan idan Momy tazo ta ganni zata san ina buƙatar matata zata kora min ke mu tafi tun da ke yanzu kin iya gardama da taurin kai ”.

Kanta ta langwaɓar tare da cewa.
“Ayyah Yah Mu'allim ba gardama da taurin kai bane kaga idan mun koma kafin na sake ganin Momy fa zai daɗe ”.
Yana gyara zamansa gefenta yace.
“Amma Ni bakya jin tausayina tunda muka zo fa kike bari na ina rayuwa Ni kadai kamar Maraya Babu kowa kusa dani”.
Kallonsa tayi tace.
“Yah Mu'allim aima mun kusa komawa dai kayi haƙuri kwana nawa ya rage”.
Ta ƙare maganar tana cigaba da dudduba littattafan sai kuma ta ajiyesu ta gefensa kallon yanda ta hargitsa Littattafan yayi kana yace.
“Me kike nema?”.
Tana cigaba da abinda take tace.
“Wani littafi na nake nema?”.
Da mamaki yace.
“Littafi kuma?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh”.
Kamar mai raɗa ya sake matsawa kusa da ita yace.
“Toh me zakiyi dashi?”.
Kanta na kan tulin littattafan tace.
“Wani abu ne aciki?".
Da mamaki yace.
“Wani abu ne kuma aciki?,ki bari gobe sai ki duba”.
Kai ta girgiza tare da faɗin.
“Ina so ne in tabbatar yana nan ko baya nan saboda da nazo na samu Raudat tana wasa takarduna da jakar makarantana ta bubbuɗe min ban sani ba ko ta jefar min da littafin ”.
Cikin mamakin yanda take neman littafin yace
“Toh littafin na wani Subjects ne?”.
Tana ɗan tura baki tace.
“Um-um fa littafin bana karatu bane?”.
Yana ɗan ƙara matsota yace.
“Ikon Allah toh littafin na menene?”.
Ya ƙare maganar yana dudduba littattafan data tutturo gefensa yayin da take sake zaro na cikin jakar ganin basu cikine yasa ta jawo durowan ƙasan Weldrop ɗin tare da cewa.
”Toh ban sani ba bari in duba ko suna cikin nan ne”.
Dai-dai lokacin yaga wani note Book An rubuta *SPECIAL MAN* da manyan baƙi Aransa ya maimaita Special Man ahankali ya jawo littafin yana ɗan jujjuyawa Khausar kuwa baki ɗaya hankalin ta na cikin durowan Weldrop ɗin.
Ahankali ya buɗe shafin farko na littafin.
ga mamakinsa sai yaga Drawing ɗin hoton fuskarsa ne rauɗau ba abinda aka bari har sajensa.
Cikin tarin wani irin mamaki al,ajabi da kuma kaɗuwa ya kalli gefen shafin.
A gefen kuwa Drawing ɗin fuskarsa ne acikin aji hannunsa na kan Black board kamar yana rubutu cikin sauri ya kalli rubutun da akayi da kalo wanda akayi musu design yanda ya kasance na musamman haka sunansa ya kasance na Musamman _Aliyu Youseef Mohammed Mouley (Moddibo)_
da mamaki ya kalli inda aka rubuta sunansa anyi zanen ❤️ sai kuma ya maida idanunsa inda akayi Drawing ɗin fuskarsa yaga date and time ɗin da akayi rubutun Drawings ɗin.
Idanunsa ya jujjuya ya kalleta amma baki ɗaya hankalinta na kan tarin himilin sauran littafan.
Kallonsa ya mayar kan date ɗin idan har baiyi kuskure ba toh shekaru huɗu kenan ranan dasu Khausar suka fara zuwa SS3 cikin mamaki da wani irin yanayi ya buɗe page ɗin gaba sai yaga Drawing ɗin Fuskarsa ne amma ba'a fitar da fuskan sosai ba sai sajensa aƙasan ta rubuta.
_One's if I remember your face, my actionable will be change to cool, is your Breed brightly my heart always yo be sunshine , i really love you with deep voice. Uncle Aliyu Youssef Mouldy (Modibbo)_
Ahankali ya motsa laɓɓansa ya furta.
“Ya salam”.
Wani irin amintaccen numfashi ya fesar saboda jin kalaman suna Barka duk kan lakar jikinsa.
Fahimtar da yayi baki ɗaya littafin kamar akansa yake magana haka nan yaji wani abu yana sauƙa tun daga ƙwaƙwalwar kansa har zuwa babban yatsarsa a iya shafi biyu daya buɗe ya fuskanci gaba ɗaya Khausar ta rayune da soyayyar shi acikin zuciyarta shi kansa baisan meyesa ba ya dai tsinci kansa da naɗe takardan yasa cikin aljihunsa.
tare juyawa yayi mata wani amintaccen rugguma yana mai kallonta yace.
“Wai wani littafi kike nema ne?”
Batare data kallesa ba tace.
“Wani Littafina ne na musamman, nasan da wuya in Raudat bata ɓatar min da shiba dan haka taɓatar min da ɗan uwanshi da Nai ta rubutawa tun daga JSS one to 3”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Ko dai Diary kine?”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Kusan haka amma shi babban littafine ai yama fi Diary daraja awajena”.
Gira daya ya dage tare da faɗin.
“Toh tashi mu tafi da safe sai muzo na tayaki dubawa”.
Kai ta langwaɓar kana tace.
“Allah ina so ba mamaki yanzu Raudat ta ɓatar min dashi. In dai ta baddashi wlh sai na daketa dan yana tunamin abubuwa da yawa a rayuwata”.
Kai ya girgiza tare da faɗin.
“In sha Allah ma bai ɓata ba kada ki damu kizo mu tafi da safe za'a zo mu duba”.
Ya ƙare maganar da ƙaguwar so yake ya ga su ƙeɓe daga shi sai ita.
Kai ta girgiza tana cigaba da hautsina littattafan tace.
“Um-um.ni dai ina son gani ”.
Fuska ya tsuke tare da cewa.
“Mu tafi nace ko?”.
Ganin yanda ya tsuke fuska yasa ta gyaɗa kai tare da faɗin.
“Toh”.
Kana tattare littafan ta mayar cikin drawer.
Hannunta ya jawo ya riƙe kana ya kalli gyalen jikinta ganin babu laifi yasa yace.
“Mu tafi toh”.
Suna fita motarsu Dr Jameel na fita agidan motarsu suka shiga kana suka tafi gida.

Suna shiga Falonsu ya rufe ƙofan kana ya ɓalle botir ɗin wuyan rigarsa ya zare ya ajiye kana ya jawota jikinsa ya rungumeta ajikinsa cikin sanyi ya kai bakinsa saitin kunnenta kana ya shiga raɗa mata abinda ta rubuta yana cewa.
“ _One's if I remember your face, my actionable will be change to cool, is your Breed brightly my heart always you be sunshine , i really love you with deep voice Aliyu Youssef Mouldy (Modibbo)_”
Cikin sauri ta ɗaga ido ta kallesa tare da wani irin fiddo idanun duka tamkar zasu faɗo ƙasa, ido ɗaya ya kashe mata kana yace.
“Tukuocin soyayyar da kike min nake son baki a daren yau”.
Baki ta tura tare da kwaɓe fuska kana tace.
“Waye ɗin?”.
Ido ya kashe mata tare da cewa.
“Keɗin mana”.
Ɗan ware idanunta tayi akansa kana tace.
“Kamarya tukuicin soyayyar da nake maka kuma?”.
Ta ƙare maganar cikin kunya da son waskewa.
Cikin wani irin yanayi yace.
“Shekara nawa kika yi kina dakon soyayyata azuciyarki?”.
Kallonsa tayi da mamaki sai kuma ta lumshe Idanunta tace.
“Kamarya kuma nayi dakon soyayyar ka azuciyata?”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Littafin da kike nema yana hannuna fa?”
Still kallonsa tayi tace.
“Wani littafi kuma?”.
Ɗan murmushi yayi kana ya hura mata sanyayyar iskan bakinsa yace.
“Littafinki da kike nema”.
Littafin ya zaro acikin rigarsa ya nuna mata cikin mamaki ta kallesa kafin tace.
“Yaushe ka ganshi?”.
Dariya yayi tare da cewa.
“Tun ɗazu har na karanta shi ma”.
Da sauri ta kife kanta akan ƙirjinsa cike da kunya murmushi yayi kana ya shiga tura yatsunsa ƙasan ƙafarta jin haka yasa ta ɗaura ƙafanta kan rumfar ƙafansa.
A hankali ya fara tafiya da ita har suka isa bedroom.
Cikin sanyi ya kwantar da ita akan gado.
Kana yayi kissing ɗin goshinta da lips ɗin ta ahankali ya fara cire mata rigarta cikin wata kasalalliyar murya yace.
“Khausar da shin da gaske kina min soyayyar da baza ki iya furta min ita abaki ba Khausar?Meyesa baza ki faɗa min ba inji sanyi raina sai kiyita dakon soyayyata tsawon shekaru meyesa baki faɗa min ba meyesa baki nuna min ba? Da gaske kece kika rubuta littafin nan”.
Ahankali taja numfashi mai tsawo hannunta na cikin sumar kansa tana shafawa kana manyan yatsunta guda biyu na kan sajensa tace.
“Ni ba ni na rubuta ba.
Haka kawai ka'ida basona kake ba kalen ince ina sonka ka kashe ni?”.
Cikin sauƙe numfashi ya gyara ta ajikinsa tare da cewa.
“Wayace miki bana sonki? Minha”.
Idanunta ta lumshe zuciyarta na bugawa tace.
“Nasan baka soma kuma nima ba nice na rubutaba”.
Yana shafa sumar kanta yace.
“To amma tunda ke kina sona ai da kin faɗa min munyi ta cutar da juna tsawon lokaci?,bamu sani ba”.
Muryan cike da sanyi ta ɗan cije gefen bakinta tace.
”Ni dai bance ina son wanda baisona”.
Saurin girgiza mata kai yayi tare da faɗin.
“Ki daina cewa bana sonki Minha”.
Sai kuma ya shiga romance ɗin ta yana shafa saman Breast ɗin ya cigaba da cewa.
“Kinsan dalilin zamana aƙasan nan kuwa?
Naƙi na koma Jami'atul Madina nayi aikin dana samune saboda ke tun lokacin dana fara sauke idanuna akan ki Allah ya jarabceni da sonki na soki alokacin da bakisan kanki ba Minha”.
Da wani irin sauri mai nuni da zallan farin ciki Khausar ta tallofo kansa tana kissing ɗin dogon hancinsa cikin kasala da shauƙi kana da yanayin da yake ji yaci gaba da cewa.
“Sanadinki na zauna anan nasoki soyayyar da bazan iya yiwa kaina ba duk Drawing da kike yi na ki wasa ne ni duk wani motsin da kikayi a duniya idan na dawo sai nayi Drawing ɗin sa na ajiye babu abinda yake sani farin cikin gani a duniya kamar fure da kuma ke saboda furanni kansu kin fisu kyau sai dai suna ɗebi min kyewar rashin ganinki ne, kana suna cike min gurbin kallonki”.
Cikin mamaki Khausar ta ɗago ta kallesa ido cikin ido tace.
“Yah Mu'allim kenan kana sona da gaske?”.
Kai ya jinjina tare da faɗin.
“Minha ina sonki son da bansan adadinsa ba nayi Miki son da ba yiwa kowacce ƴa mace irinsa a duniya ba”.
Sai kuma ya miƙe da sauri, ya buɗe durowar dake jikin gadonshi, wasu manyan takardu masu kana da kalandu ya ja, a kan kadon ya zubasu.
Da sauri ta zubawa na forkon idanu.
Sai kuma ta kalleshi domin ta tuno yanayin da suka kasance a cikin mota a ranar daya rage mata hanya.
Da sauri yaja mata na ƙasashi.
Wani irin murmushin ne ya subce mata ganin zanenta tana rawa a gaban motarsu ranar da suka haɗu gidan Ummi.
Baki ta turo ganin na ƙasanshi ranar da take kakkaɓe ɗan kwali ne sai kuma wani da bazata manceba na ranar data fara ganinshine da ta tsaya tana kallonshi harda karkata wuya ranar da ta fara zuwa JSS one kenan sai kuma wanda ta diƙo kan bishiyar ranar da suka zo da Asma'u sai wanda suka haɗu a rugar Jauro yaya.
Ya Salam sai kuma wasu wanda bisa alamun nashine da Yah Jameel.
Kawai sai ta faɗa jikinsa.
Ture takardun yayi tare da ruggumeta da kyau.

Kanta ta kwanta ajikinsa tana jin yanda hannunsa ke yawo a sassan jikinta tace.
“Amma kuma Yah Mu'allim kullum dukana kake yi ya za'a yi na yarda dagaske cewa kana sona”.
Yana sakin ajiyar zuciya yace.
“Dole ne yasa nake Miki wannan yanayin saboda na fahimci kamar J yana sonki so kuma irin na aure”.
Saurin kallonsa tayi ya jinjina mata kai yana cigaba da cewa.
“A duniya ban taɓa son abu J yaƙi shiba.
Kana J bai taɓa son abu naƙi shiba sai nazo na fahimci akan mace ma zamuyi tarayya akan soyayya kuma hakan zai zame mana masufa a amintakarmun shiyasa nasawa raina hantarar ki da nisantarki da ƙin kasancewa kusa dake saboda in yakice ki azuciyata J ya mallake ki dan nayi alkawarin mace bata isa ta shiga tsakanin amintakarmu ba”.
Idanunta ta lumshe tana jin wani irin ƙaunarsa na huda duk wani magudanan jinin jikinta ahankali ya cigaba da cewa.
“Abinda J ya faɗa min kenan a voice ɗin sa na ƙarshe yace min ya fahimci ina sonki yamin voice da ace alokacin yana raye zance J ai kaima kana sonta amma tun a voice ɗin yace min kana tunanin kamar ina son Khausar ko? Shiyasa kake hantararta dan ka yakiceta a zuciyarka.
Wai sabida zaka bar min ita ko?.
To ni ba sonta nake ina taya ka son abinda kake sone A.J ka Aureta dan naga zanenta da kayi a takardu, in su ka ɓoyesu shin zaka ita ɓoye na zuciyarta da ƙwaƙwalwar kane, AJ. Ka aureta. abinda J ya faɗa min Kenan ”.
Duk da nasan ya faɗane kawai Amman J ya soki Minha ya soki irin so na aure ashe ya gane ina sonki”.
Idanu ta tsira masa kana tace.
“Dagaske Yah Mu'allim?”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Sosai ma”.
Daga nan ya cigaba da romance ɗin ta ya dauki Kimanin minti arba'in da biyar akanta kafin ya jawota ya rungumeta yana sa mata albarka tare da cewa.
“Alhamdulillah ashe son da nake baso bane soyayya ce?”.
Tana sauƙe Ajiyar zuciya tace.
“Kamar ya?”.
Murmushi yayi tare da faɗin.
“Eh so na gefe ɗaya shi ake cewa so amma tunda kema kina sona kinga soyayya ce”.
Sake shiga jikinsa tayi kana tace.
“Dagaske Yah Mu'allim maganar daka ke faɗa?".
Cikin tabbarwa yace.
“Ki daina kokonto Minha Vidaa Ana uhubbuki kubban axeem”.
Wani irin farin cikine mara misaltawa ya mamaye gaba ɗaya ilahirin zuciyarta.
Awannan daren haka suka kwana cikin farin ciki da kwanciyar hankali...

Alhamdulillah haka rayuwa ta cigaba da tafiya ranan Alhamis akayi walima ranan juma'a aka ɗaura auren.

Malam Liman da yazo ɗaurin Aure ya kawowa Amina da Samira magani da yayi alƙawar kamar yanda ya faɗa zuwa yanzu Alhamdulillah jikinu da sauƙi amma dan Amina har abinci takeci.
Samira kuwa ruwan ya rage zuba sosai a wuni haifi sau uku zai zuboba.

Hajiya Bunayya kam abin nata babu sauƙi kullum gaba-gaba yake.

A ranan jumma'a akayi Dinner mai rai da lafi.

Alhamdulillah ranar Litinin sufa dawo Adamawa da amarensu Zakariya da Aseeya Asma'u Da Dr Jameel Dija Yah Ali Su Didi sunje har falon bappa Jimeta.

Washe gari talata jirginsu ya ɗaga zuwa Morocco.
Misalin ƙarfe 2:00pm suka sauƙa acikin Morocco anan suka samu motoci daga Masarautar Mouley na jiransu suka shish-shiga kana suka tafi motocin ajere ajere suke tafiya a sai da sukayi nisa Khausar taga motarsu ta fita cikin sauran tawagar motocin ahankali ta kalli Moddibo dake gefenta kana tace.
“Yah Mu'allim ya naga su sunyi can mu munyi nan?”.
Yana ɗan shafa cikinta yace.
“Gida zamu tafi”.
Idanunta ta zare kana ta langwaɓar da kai tace.
“Yah Mu'allim gida kuma?
Baza muje inga gidansu ba? Ai kamata inyiwa Asma'u rakiya aminiyata fa”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Za kije amma ba yau ba sai kin huta”.
Kai ta gyaɗa direct motarsu Masarautar Mouley ta nufa.
Yayin da Amare aka wuce dasu gidajen su batare da rakiyan kowa ba daga Nigeria kasancewar ga Didi da Innayi sun sai Goggo Asma'u ta wadatar dan a cewarsu ai Asiya ga Khausar dijama ga Khausar ga Yah Abbanta.

Khausar kuwa suna isa abinci suka ci kasancewar an shirya musu komai kana ko wanne yayi wanka ya kwanta dan huce gajiya.


Bayan kwana biyu Moddibo ne zaune akan sallaya gabansa ɗauke da starm da Kur'ani ke kai, bayan ya dawo daga sallar Asbah yayin da Khausar ke gefensa ahankali ta ɗago kanta jin ringing ɗin wayarta kallon Moddibo tayi kasancewar ya fita kusa da wayar da ido ta mishi alamar ya dai wake kira?.
Juyawa yayi kana ya kalli screen ɗin wayar sai kuma ya kalleta yace.
“Asma'u ce”.
Da ɗan sauri ta miƙe ta karɓi wayar tare da amsawa takai kunnenta tare da cewa.
“Hello Besty na kiyi haƙuri laifin yayanki ne. Yah Mu'allim ne ya hanani zuwa wai in barku ku gurji amarc...
Sai kuma tayi shiru ba tare da ta ƙarasa mgnar ba, sabida jin muryan Asma'u a disashe kana yayi sanyi alamun taci kuka ta godewa Allah cikin raunin murya tace.
“Khausar”.
Da damuwa Khausar ta ɗan jingina bayanta da kafaɗar Moddibo kana tace.
“Subhanallah Asma'u meke faruwa”.
Cikin rauni da zubda hawaye Asma'u tace.
“Khausar zan mutu dan Allah ki cewa Yah Mudibbo kuzo ki ɗaukenu, wannan mutumin mungu ne ya kasheni ”.
Dariya mai sauti Khausar ta fashe dashi har tana ɗan bubbuga kanta da jikin kafaɗar Moddibo kana tace.
“Ya kashe ki kuma kike magana?”.....






By
*GARKUWAR MARUBUTA*

https://chat.whatsapp.com/Ke5tcPxlatRGeO2qeSdR8s



Group ne na musamman na Ƙasaitattun mata da suka san darajar gyara. Kana group na mata na musamman masu daraja.

Hajia ko sau ɗaya kika taɓa sayan kayana, ina maraba dake.

Please idan kin san baki da ra'ayin sayan kayan ɗa'a ko na ƙamahi bi ma'ana baki bukatar gyara kada ki shigo group na domin na kayyakin Matana dana ƙamshi.
Kamarsu. Set ɗin uwar gida, Amarya, budurwa ko bazawara, mai jego, mgnin infection sadidan kayyakin ƙamshi kamarsu Humra kala-kala kullacca kala-kala Turaren wuta kala-kala Turaren wanka turaren carpet, na kujeru da labulaye hodar hammata mai hana zufa.
*Idan dai kina buƙatar kayan to ƙofa a buɗe take ki shigo group ɗin ina maraba da tsoffin Customers na da kuma New Customers, ina lale marbin da kuma masu sayan ƙanana set da kuma masu sayan manya, domin da rarrafe taro ke tashi tsaye.

Set ɗina hawa hawa ne, akwai manya daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k sai ƙananan set ɗin daga 40k 35k 30k 25k 20k 15k 10k sai ɗan ƙaramin haɗina na ƙarshe Hajia 5k bani da haɗin ƙasa da haka Amman zaki samu na ɗan dubunki biyar ina saida mgnin infection sadidan ba haufi set 10k half 5k akwai daɗi har maɗiga 5k maliƙi mai masifar matsewa 7k in son samune ki haɗasu biyu, akwai kwanon Ƙasaitacciyar 7k akwai sahuwar zuciyar farin rago 25k akwai haɗin dahuwar kaza da rubutu 20k akwai mara rubutu 15k akwai ɗayan 12k ku'accar siri 7k shu'umar Humra 5k ƙanan roba kenan duk gumbunana ƙananan roba 3-3k ne sai na riɗi da uku alkhairi da gumbar kwalli ƙanan robar su 5k ne sai ƴan botikayen gumbunan su 9-9k ne hakama garuka, haka tsumuka sai dai a garuka akwai na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login