Showing 306001 words to 309000 words out of 365757 words

Chapter 103 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1440

da wuri shiyyasa suka biyo.....

Batakai k'arshen tunanintaba taji wani azababben zafi a damtsen hannunta, ko kad'an bataji k'arar wannan harbinba (dam inhar harbi zai shiga jikin mutum aishi bazaiji k'arar bindiga ba) kallon inda akayo Harbin Munaya tayi, glass d'in ya huda ga wani garjejen k'ato yayo wajen motar, a kid'ime ta kalli sarkin mota da hankalinsa shima yake a tashe, sai zufa yake yana waige-waigen ganin yanda police d'in suka fita sunason basu kariya.

Cikin k'arfin hali Munaya race,  Sarkin mota, ka kar6i Camera d'in nan ka hanzarta kaita kotu, ya tabbatar min lokacin buk'atarta tayi, karka sanar masa komai harsai shari'arnan ta kammala dan ALALH, inason burinsa yacika koda ace zan rasa raina a yau, please karka damu sarkin mota jeka, maza jeka kar Mara imaninnan ya k'ara so.

Badan sarkin mota yasoba ya kar6a ya fice da sauri cikin dabara, saboda Munaya tabashi tausayi, ga harbi ta samu, amma bata kanta takeba ta cikar burin mijinta takeyi.

Fitar sarkin mota tayo dai-dai da isowar garjejen k'atonan, ya bud'e murfin motar yana fisgo Munaya waje, fad'owa tayi kanta ya bugu da kwalta sai jini kawai, tuni numfashinta yafara fita da k'yar, dishi-dishi take hango wani Na dukan Nuren da bakin bindiga yana k'ok'arin kare kansa da kiran sunanta yana mik'o hannu, amma ina, sun riga sunci k'arfinsa, idanunta suka lumshe a hankali, yayinda wasu hawaye masu zafi suka gangara ta gefen kumatun data fad'in, fuskarta d'auke da murmushin k'arfin hali.

Nuren daketa kwala mata kira a rikice yana mik'o hannu, dukda dukansa da ake, ya zube a k'asa yana fashewa da kuka maiban tausayi da ambatar  please Munaya karki tafi kibarmin d'an uwa, ke wani yankin farin cikinsace mai matuk'ar girma ple......

Shima baikai k'arshenba ya sulale k'asa saboda dukansa da sukayi a kai.

Wani dake bincika camera d'in a motar ya juyo a fusace yana fad'in  babu camera d'in fa boss .

A rud'e Boss d'in dake tsaye gaban Munaya ya taka hannunta da mugun takalminsa yayo wajen, ko motsi kuwa batayiba alamar ruhinta yabar gangar jikinta.

Ture yaron nasa yayi yafara lalube da kansa, hankalinsa yakai gaban motar. yace,  Ina driver!!?  .

Yanda yay maganar a rikice ya saka yaran rikicewa suka hau waige-waige, sarkin mota dayay nisa a gudu yana jiyo ihun ogan, saiya k'ara k'aimi.

Wani yace,  gashi can zai gudu da camera d'in  .

Tuni suka rufoma sarkin mota baya a guje, shima yacigaba da gudu iya k'arfinsa. Cikin amincin ALLAH saiga wani mai mashin tamkar an jehoshi, ya tsaya yana fad'in  maza hau muje .

Sarkin mota ya haye, mashind'in nabarin wajen suna k'arasowa, Dutsuna suka d'auka suka dinga jifansu sarkin mota suna binsu da gudu, amma ALLAH bai basu nasaraba. Hardai ubangijin sammai ya kaisu court lafiya.

Sai lokacin Na lura Ashe Ahmad ne yaron Alhaji Bana, ya kalli sarkin mota yana fad'in  Maza kakai, yanzu haka ita kawai ake jira, kasa nutsuwa a ranka kar boss ya fahimta balle yakasa nutsuwa a shari'ar shima, yanzu haka suma police zasuje su taimakesu, muma can zamu tafi da sauran y'an uwana .

Kai sarkin mota ya jinjina, ya k'arasa gaban k'ofar kotu yay knocking yana share hawaye da tausayin Galadima. Anzo an bud'e masa aka shiga dashi, dama camera d'in kawai ake jira.





A can kuwa suma saiga Police an k'aro, wad'anda suke tare dasu Munaya su 6 ne kawai dama, gashi bawani isassun kayan aikine dasuba, bindugun hannunsu babu mai bullet, sun daki d'aya yasuma, d'aya kuma yasamu ya sulale domin kira yasanarma ogansu abinda ke faruwa, yayinda biyu suka gudu, biyune kawai a wajen, sukuma sunyi musu yawa y'an ta'addan.

Isowar police d'in ta saka wasu a cikinsu yunk'urin guduwa, saidai ina, ALLAH yakan ara maka rana, randa kuma zai kamaka babu hanyar ku6ta, dukansu ram akayi dasu, dukda wasu sunso yin gardama, duk aka zubasu a mota, yayinda Ahmad yasake dawowa shi da Yassar tareda Ambulance, suma su Munaya da Nuren aka kwashesu=�-�.





...............................&



Tunda Galadima yaga sarkin mota ya kawo camera hankalinsa bai kwantaba, dakuma yaso had'a ido da Sarkin mota shi saiya kauda nashi, yak'i yarda su had'a idon.......

Maganar Alk'ali ta katsema Galadima tunaninsa, yayinda yake bada Umarnin a bud'e camera d'in, takardune aciki guda uku, d'aya abbane ya rubutata yanama Galadima bayanin yanda akai camera tazo hannunsa, d'aya kuma sunayen dukkan wad'anda ke bibiyar sa akan camera d'in ne, d'aya kuma wadda mutumin farko d'an uwan baba Rabilu daya bada camera d'in ne ya rubuta ce.

Ita kad'ai alk'ali yabada umarnin karantawa, yayinda masana keta k'ok'arin saita camera da TV dake kotu suma, Wanda Galadima ne ke k'ara sanar musu dukkan dabarun daya kamata suyi daga inda yake tsaye.

Abinda takarda ta k'unsa shine.....



Assalamu alaikum

Sunana Habu, wannan takarda ina fatan ta iso agareku, ko yarima, ko gimbiya ko matar Sarki mahaifiyar su yarima, Ku duba wannan camera d'in, duk yanda aka k'ulla faruwar ciwon mai martaba da wad'anda suka kulla suna a ciki, nidai nasan tawa ta k'are, dan tunda suka ganni ina d'oukar sirrinsu saisun kasheni, wata uku kenan ina 6oye-6oye, yaudai Na yanke shawarar fito fili Na baku koda hakan yana nufin zan mutu, dama can kwanana sun k'arene, koma basu nayi saisun kasheni, ballema bazan ta6a basu d'inba, ALLAH yabama mai martaba lafiya da tsawon kwana mai amfani, yakuma baku ikon hukunta wad'annan tsinannun masu jinin Fir'auna a jiki, wad'anda mulkine da tara duniya kawai a gabansu ba al'ummar k'asarsuba, duk yanda zakuyi karkubar la'anannnun nan yin mulkin al'umma, subasu cancanci zama shuwagabanniba.

Bisalam.



Kotufa tayi tsitt, ko tarin wani bakaji sai k'arar fanka, yayinda zufa tagama jik'e su Alhaji balala sharkaf, kallo d'aya zakai musu ka fahimci ruwafa ya k'arema d'an kada.



Alk'ali baice komaiba, jira kawai yake camera ta daidaita ajikin TV kowa yagani, matsalar camera Ce irin ta da, shiyyasa take bada wahala, da k'yar dai cikin amincin ALLAH ta kawo, tofa, saidai kalar da take nunawa White and black, ga wani rawa-rawa da takeyi saboda ba nutse aka d'aukaba, kuma da alama ana yayyafine.

Dagani wajen wani ke6antaccen wajene daba kowa ya isa shigaba, shikansa d'an jarida habu kota Yaya yayi hakan? ALLAH kad'ai ya Sani saishi, gashi bashida rai balle mu Sani.

Mutanene da ak'alla sunkai 20 a wajen.

Alhaji balala, Alhaji Mansur, Alhaji Lawan tanferu, Alhaji Bana, Alhaji Abdul-Naseer, Alhaji Labaran khacia, Timothy, Hajia A'i, Victoria, Miracle, Alhaji Sageer, William, Josaya bamma, Kabiru Ibarheem, Alhaji Mamman, Waziri, Sai wani Sarki daba wani k'arfin ikone dashiba, yama rasu tuni, tun ciwon Abie babu dad'ewa, sai Mahaifin Gimbiya Zulfah uwargidan Sarki, shima sarkine mai fad'a aji, Sai mahaifin Mama Fulani=�1�, sauran Biyun turawane.

Duk suna zaune kowanne da kwalbar coca-cola a gabansa (sannan shinsa sai manya>�#�).

Alhaji Lawan tanderune ya mik'e yafara jawabi kamar haka.

Masu girma saraki dake wannan waje, da bak'inmu (turawa) sai abokaina shak'ik'ai ina muku sallama gaba d'aya

Duk suka amsa a tare. yaci gaba da fad'in,

Muduka nan mun tarune akan mak'iyinmu guda d'aya, Wanda ya tare mana gabas ya tare mana yamma, hakama kudu da arewa, mun bishi ta lallami akan yabamu goyon bayan cikar burinmu amma yak'i, yana wulak'antamu saboda yaga ALLAH yabashi k'arfin iko da izzar mulki a hannu, a daren jiya mun yanke shawarar kasheshine kowa ya huta, amma yanzu mun fasa hakan, zamuyi masa abinda saiya gwammaci yazama gawa, dan zai rayune shiba mutumba Shiba butun butumiba, ahaka naman jikinsa zai ringa ru6ewa sashe-sashe, mukuma zuwa sannan mulkinnan dai dayake ganin bazai dafa mana muyiba ya dawo hannunmu, dan mungaji da mulkin soja hakannan, gashin kanmu muke buk'atar ci koya kukace?

Hannu suka d'aga suna fad'in eh hakane hakane.

Alhaji Lawan tanderu yayi dariya yana gyara babbar rigarsa, ya d'akko wani ruwa a kwalba yana nuna musu,  kunga wannan itace gubar ruwan allurar da za'ai masa, ita cikin mintuna biyu zuwa biyar take fara tasiri koba haka kaceba Mike? .

Cikin turawa biyu dake tare dasu d'aya ya gyad'a kai yana murmushin mugunta.

Gaba d'aya suka sanya tafi, raf! Raf! Raf!, saikuma suka koma tafawa da musabaha a junansu (irin sun samu cikar burinsu d'innan).

Tanderu yacigaba da magana bakinsa a washe.

 Wannan aiki ba kowane zai mana shiba sai wazirinsa, Munaso da asubahin yau kamasa wannan allura dakagani, inamai tabbatar maka inhar ya Idar da sallar to bazai shiga gida da kansaba .

Waziri mahaifin Harun ya kar6a yana washe baki tamkar gonar auduga, da fad'in  lallai nafi kowa farin ciki da samun wannan dama, domin kobabu komai zanyi maganin mak'iyina da kaina, daga yanzu sainaga da bakin dazai kuma cin zarafina da jifana da kalaman banida hali, toshi mai halin saiya cigaba da shukashi muda bamu dashi muyita girba munakaiwa gidanmu munaci.... .

Gaba d'aya suka kwashe da dariya suna tafawa, a Na wannan dariyane Alhaji Bana idonsa yakai ga camera, alamun yaga habu kenan, ajiye k'aramin kofin silver dake hannunsa ya zuba coc yayi yana mik'ewa zumbur.

Sauran suka fara tambayarsa mike faruwa?, tuni habu daya farga dasu ya shek'a da gudu. Daga nan ba'a sake nuno kowaba, sai gudu da habu yakeyi da hakkinsa, Camera d'in Na wani shuw-shuw harma aka bar ganin komai.



Kwakwkwaran Motsi kowa ya kasayi acikin Court d'in, Galadima ya duk'ar dakai yana kallon k'asa hawaye Na zirara suna d'iga, hakama Abba Hayatuddin kuka yake saboda tausayin d'an uwansa da takaicin waziri daya kasa zama kusa dashi yanzun, ga takaicin wai harda kakansu Wanda ya haifi mahaifiyarsu, shin shikuma miye matsalarsa da d'an uwansa ne? Kenanma mama Fulani mahaifiyarsu itama tasan komai? Innalillahi wa inna'ilaihiraji'un, wannan wace iriyar masifacene hakan?.



Alk'ali daya buga gudumarsa a sanyaye ya katse tunanin mutane da yawa dake cikin kotun, cikin sauke nannauyan numfashi yace,  yanzu babu tanderu a duniya, shin ko akwai mai wakiltar wannan group a yanzu? .

Su Alhaji balala da duk jikinsu yay lak'war kunya da nadama duk sun lullu6esu sukayi tsitt.

A fusace cikin daka tsawa Alk'ali yace,  waishin! Ba'a jini bane?!! .

Jiki Na rawa Josaya bamma ya mik'e, tsufa sosai ya kamashi, danma akwai jin dad'i tattare dashi, ko a wancan lokacin dagani ya girmi tanderun ma gaba d'aya.



Wani cikin ma'aikatan kotun yaje inda alk'ali yake suna magana k'us-k'us, komi yake fad'a masa oho, nagadai alk'ali yayi alamar a kawosu, wancan ya sakko, shikuma alk'ali ya maida hankalinsa ga Josaya bamma dake k'ok'arin shiga inda ake buk'atar ganinsa.



Josaya Yaje inda ake tsayawa ya tsaya, Alk'ali ya kallesa cike da tsantsar tsana yace,  kotu tanason jin shin minene kuka nema ga adalin Sarki mai gaskiya da son ayi gaskiya irin Sarki Saifudden yak'i baku goyon baya har kuka nakasashi? .

Josaya bamma ya gyara tsayuwa kansa a duk'e saboda kunya. Yace,  Ya mai Shari'a, mu mun kasance y'an k'ungiya d'aya masu burin kafa gwamnatin farar hula a wacan lokacin, mafi yawa acikinmu tare mukayi karatu a landan, tunkuma munacan wannan shine babban burinmu, dan haka koda muka dawo najeriya muna kan wannan buri, duk da mulkin soja shike gudana a k'asar tamu, kuma babu wani mahaluki daya Isa yin koda kwakwkwaran tarine, da farko mun fara janyo wasu mutane da yawa suka shigo jikinmu, sannan muka farabin sarakunan gargajiya Na kudanci da arewaci dan samun had'inkai, wasu sun amince mana, wasu kuma sun nuna babu ruwansu, Sarki Saifudden yana sahun farko Na manya-manyan sarakunan gargajiya da akeji dasu da girmama maganarsu a arewaci, munada yak'inin inhar ya bamu goyon baya mun gama samun abinda mukeso, wannan yasa muka fara binsa ta k'ark'ashin k'asa, wato su Mike sukaje ga wazirinsa suka gana da samun manya-manyan sirrika a wajensa, sunje da kwanaki biyu muma sai muka tunkari Sarki Saifudden bisa jagirancin Waziri. Cikin lalama da rok'o muka fahimtar dashi manufarmu, amma saiya fusata, yakuma jamana gargad'i karya kuma ganin koda masu kama damune a masarautarsa, kuma lallai shi da kansa zai nemi shugaban k'asa mai mulkin wancan karon ya sanar masa manufarmu, munta k'ok'arin fahimtar dashi amma yak'i saurarenmu, daga k'arshema saiya koremu daga masarautarsa, wannan shine dalilinmu Na shirya cewar zamu kasheshi, amma daga baya saisu Mike suka kawo mana shawarar masa allurar poison, bamusan ya akayi wannan d'an jarida ya San da shirinmuba harya biyomu inda muka ke6e dan tattaunawa, munta bibiyar rayuwar d'an jarida amma bamu sameshiba, marigayi tanderu ya k'arfafa mana gwiwa akan karmu fasa yin shirinmu, waziri zai kula da motsin kowa a masarautar, a ranar Waziri yatafi da wannan allurar guba, dakuma asubahin washe gari yacika mana aiki, bamu sakejin labarin d'an jarida ba saida Sarki Saifudden yacika watanni uku da fara jiyyasa, saigashi cikin yaranmu wani ya samoshi, sun bishi dansu kasheshi amma saiya 6oyema ganinsu, Ashe yabi motar mai dawakai ne daya gani akasuwa yazo sayen abincin dawakai. Wani bawane yaga wannan d'an jarida tareda mai dawakai a barga, shikuma bawan yana d'aya daga cikin wad'anda waziri ya baza a masarautar domin saka ido, dan yasan komai Daren dad'ewa d'an jaridarnan saiya so kawo camera d'in a masarautar, a lokacin yasaka ancigaba da bin d'an jarida, yakuma k'yale su mai dawakai har zuwa dare yaje garesu. Camera dai tacigaba da walagigi, har muka samun kashe d'an jarida, a lokacin bamusan Alhaji Rabilu munafuki bane yasan komai, har yazo ya shiga jikin mu da cewar yazo shiga tafiyarmune, Ashe munafuki yasan komai, dan bamuga fuskarsa ba lokacin damukaje fadamar bayan gari, shi Badi shikad'ai muka gane tunda dama waziri ya sanar mana. Muncigaba da Neman Badi har tsawon shekaru 4 amma ko labarinsa babu, saidaga baya cikin shekara ta biyarne muka samu labarinsa a wani k'auye, munta bibiyar rayuwarsa daki-daki, har randa yabaro k'auyen muka cigaba da binsa, lokacin daya farga damu shine ya gudu Alhaji Auwal Fharuk ya bigeshi da besfa, lokacin da yaranmu sukazo shi Alhaji Auwal Fharuk saiya gudu, dan haka basuga fuskarsa ba, shikuma Badi ya suma, a tunaninsu ya mutu, suka daddike gawarsa suka dawo suka sanar mana babu camera d'in a hannunsa, sannan kuma ya mutu, amma suna k'yautata zaton yabama wani kafin zuwansu, kilama mai besfa d'in daya bigeshine, bamu hak'uraba, mun cigaba da lalube dukda bamusan wanene ba, ana cikin hakane kuma muka samu damar kar6ar mulki, burinmu ya cika, Alhaji Labaran Khacia yazama shugaban k'asa kamar yanda muka tsara, dan dukya fimu arzik'i a lokacin, saidai kuma yana shekara biyu kacal da hawa mulki Alhaji Lawan tanderu ya rasu sakamakon had'in mota, shugabanci k'ungiya yadawo hannuna, Tanderu bai dad'e da rasuwa ba shima Alhaji Labaran yakwanta jiyya, kwanansa baifi 6 ba ya mutu shima, lallai wad'annan rashin sun girgizamu matuk'a, har yanzu kuma mun kasa mantawa. Tun daga wancan lokacin duk Wanda zaiyi shugabanci a k'asarnan da taimakonmu yake yinsa, kuskuren da mukayi shine mantawa da Sarki Saifudden nada d'a namiji, kuma komai Nisan lokacin zai iya Girman da zaibi ba'asin ciwon mahaifinsa, gaba d'aya sai hankalinmu ya k'arkata ga son samun Camera kawai, a tunaninmu damun sameta dukkan magana ta k'are. Har lokacin da muka fahimci Alhaji Rabilu shima munafukinmu ne, shine muka titsiyeshi akan camera, amma yace bai saniba, Alhaji Shehu ya d'auki mataki a kansa, dan dukkan Wanda yasan da zancen camera burinmu mu kaudashi kawai magana ta k'are, Bamu farga da yarima Sameer ba sai lokacin da ya fara bibiyarmu, Ashe a time d'in shi C.I.D nema, mukuma duk bamu saniba, da taimakon d'an waziri Harun muka samu bayanan sirrin Documents d'in shi yarima Sameer, dan haka Kabiru Ibraheem da shima masanin Computer ne ya shiga yimasa kutse, dan munason musan shin yarima Sameer yana sane da mune? Inhar yana sane damu mukaudashi shima. Saidai kuma yaron ya wuce da dukkan tunaninmu, yanda muke bashi wahala haka shima yayta bamu wahalar, aka cigaba da yak'in sunk'uri, kowa baya ganin kowa kenan, kwatsam saiga Alhaji Shehu Darma yazo mana da labarin Camera fa Na hannun Alhaji Auwal Fharuk, wannan yasa muka koma bobiyarsa, mun masa tayin dukiya mai yawa sau babu adadi amma yak'i saurarenmu, munma rayuwarsa barazana nanma a banza, daga k'arshe muka nemi kasheshi shima, amma ya tsira bai mutuba, Yarima Sameer ma ya d'aukeshi zuwa India, dukda a India d'inma bawai mun barsa bane, canma musha bibiyarsa da barazana, amma taurin kansa yahanashi bamu har zuwa yau d'inan, munsha kaima rayuwar Sameer hari shima ta 6angarori da dama amma yana shallakewa cikin tsarewar Ubangiji, wannan shine abinda ya faru yamai shari'a .



Babu abinda kakeji a kotunnan sai sauke ajiyar zuciyar jama'a, alk'ali


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login