Showing 6001 words to 9000 words out of 365757 words

Chapter 3 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1429

.

 hakane Munu..., karki damu, insha ALLAH munayin aure d'auke innarmu zamuyi ko Abbah ya yarda kobai yardaba wlhy!! .  ta k'arashe maganar a harzuk'e .

Murmushi Munubiya tayi, dan tasan ran 'yar uwar tata yakai k'ololuwar 6aci.

Har muka gama wankin innaro na gidan bata tafiba, bamusan uwarmi takeyiba. dayake girkin gwaggon Haleema nema ranar. ina tsaye a bayan flowers d'in d'akinmu ina goge glass d'in windows naga Abdul yafito d'aukeda tire an jera sabbin kuloli akai, nasan Abbanmu baya gari, dan haka nace,  Abdul wazaka kaima abinci haka? .

Yace,  Aunty zan kaima innaro tana falon dady .

Kai na jinjina masa kawai nace jeka, cigaba nayi da aikina ina fad'in  shidai munafurci ai dodone, maishi yakeci .

Koda na koma ciki sai nake bama Munubiya labari, innarmu dake bayanmu bamu saniba tace,  to ina ruwankine wai Munaya?, nifa banason gutsiri tsoma wlhy, wai sai yaushene zaku daina jamin fitina a gidanan ne? .

A sanyaye mukace kiyi hak'uri innarmu .

Batace komaiba tashige d'akinta, muduka da kallon tausayi muka bita, dukda tasan ita ake tauyema hak'i amma bata ta6a nuna itace mara laifi, kullum ta amince itace a k'asan kamar yanda kowa ke kallonta agidan.

https://2gnblog.blogspot.com/



&&&&&



Washe gari Abbah yadawo da yamma, duk munyi murnar ganinsa, shima kuma hakan take a garesa.

Sai da daddare suka tara iyayenmu mata meeting shida Dady da baba k'arami.

Abbanmu yay gyaran murya sannan yace,  dama wani abune yasaka muka taraku, maganace akan yaranmu mata, Ramlah da khaleesa da Rahaima da Hauwa'u kowa yasan sun fida mazajen aure harma an tsaida bikinsu nanda bayan salla .

Duk suka amsa da eh.

 yauwa to Alhmdllh, yanzu munada sauran yara 'yan mata agidanan ak'alla su 8, kuma duk kusan Kansu d'ayane, dukda su Ramlah sun girmemusu, to wani uzirine yataso na tilas zamu had'awa auren wasunsu danasu khaleesa. shin ko akwai wad'anda a cikinsu sukeda tsayayye? domin a fiddasu? .

Da sauri maman safara'u tace,  Safara'u nadashi, dan harma yanason turo iyayensa, amma nace ta dakatar dashi sai angama na yayyensu .

 to Alhmdllhi, sai kuma wa? .

Umma Ruk'ayya ma tace,  Fiddausi tanada tsayayye itama .

 masha ALLAH, to bayansu fa? .

 mamansu yaa hameed tace,  ai inaga sukenan kam Abban Hameed .

 yanzu su 6 kenan suka rage? to dama Alhaji halliru d'an majalissar datta6ai, nasan duk kunsan abokinane shak'ik'i? to shine yanemi alfarmar nemama 'ya'yansa maza biyu auren biyu daga cikin 'ya'yana, d'aya d'ansane na cikinsa, d'aya kuma d'an yayarsane tarasu tabari yacigaba da rik'onsa. to harga ALLAH nasan yaransa sunada tarbiyya dan haka na amince, amma dukda haka saida nasake dogon bincike akan yaran saboda yaron yanzu ka haifeshine baka haifi halinsa ba, to Alhmdllh suma basuda wata matsala, dan haka mun yanke magana dashi akan suzo saisu za6a acikinsu, wannan shine dalilin dayasa muka taraku kenan .



Hummm yaufa anzo da Sabon al'amari a gidan namu, nanafa iyayenmu mata suka hau tsugunne-tsugunne, kowa burinta ace d'iyarta aka za6a, harma da iyayensu safara'u dakeda mijin a hannu, ganin sunji gidan maik'one kowacce tafara k'ok'arin gani da fatan 'yarta ta kasance acikin gidan, aiko sai shirye-shirye kowa keyi a asirce, aka fara gyara 'ya'ya.

Mudai a 6angarenmu babu abinda innarmu kemana, hasalima inda taji maganar anan ta barta, komu bata sanarma ba, sai abakin Fauziyya mukejin komai.

Yanda ake shirye-shiryen bak'i takowanne 6angare saika d'auka 'ya'ya. Shugaban k'asane zasuzo, ni abinma mamaki yabani dan kowanne d'aki da nasu shirin, dayake kowane d'aki akwai budurwa d'aya, mu 8ne, su shida kowanne d'aki 1 kenan, saimu mu biyu a d'akinmu, 'ya'yan abbanmu mu 4 kenan, na baba k'arami 2 na Dady 2, gashi biyu za'a za6a acikinmu amma saika d'auka mu duka za'a za6a saboda shirye-shiryen da iyayenmu keyi.



Ranar Asabar (Saturday) kenan takama zasuzo, dan haka muduka 'yan Matan 8 baba k'arami yace muhad'u muyi girkin tarbarsu.

Ni Munaya, Munubiya, Safara'u, Fauziyya, Haleematu, Fiddausi, Zarah, Siyama.

A kitchen d'in 6angarenmu muke girkin, dukda dai iyayenmu sun d'an saka mana hannu wajen tsara kalolin abincin daya dace a tanada. Ni abunma haushi yabani, yanda naga 'yan uwana NATA rawar kai, sai wani k'alk'ale-k'alk'ale akema abinci da drinks na gargajiya damuka had'a.

A raina nace Kodai sune iyayen cin tsiya, ai bazasuci ko quarter d'in abincinnan ba, wannanma ai almabazzaranci ne wlhy, mutun biyu kawai amma anmusu abinci wajen kala 6, banda kuma kayan ciye-ciye irinsu snakes da nau'in nama da aka sarrafa zuwa daban-daban. haka dai muka gama aka kai falon baba k'arami aka shirya, sannan kowa takoma 6angarensu danta kimtsa........
'<���







Anan ne za'ayi kece rainin=�L�<���=��<���<���
@&







Guys kumuje zuwa=� �=�N�<���











One luv>�p�>�p�













*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=�O�<���=�-�

[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing=���_*







*_HASKE WRITERS ASSO...=ء�_*

_(Home of expert and perfect writer's)_









*_f&RAINA KAMA......!!f&_*

_{Kaga gayya}_









*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







=�I�<���4�



.......Daga ni har Munubiya babu wata kwalliya damukayi, hasalima ni ko mai k'in shafawa nayi, danayo wankanma sainayi kwanciyata na hau barci. sai wajen 1 munubiya ta tadani wai sun iso, dama lokacin duk fashin salla muke nida munu.... (zakusha mamaki idan nace muku dai-dai da prioud yakanzo mana rana d'aya nida hassana ta, kuma musami tsarki tare), tashinai ina yatsine fuska, dan naji haushin tadanin datayi, toilet nashiga domin kimtsa jikina, sama-sama nadinga jiyo maganar Ikram tana fad'in  Aunty wai innaro tace kuzo .

Cikeda mamaki munubiya ta amsa da to. nima abin yabani mamaki, dan haka nafito da Sauri,  wai Munubiya minake jiyowa ina toilet?  .

Maganarta d'auke da mamaki tace,  wai innaro ke kiranmu .

 ni da ke? kokuma mu duka? .

 wlhy ban saniba munaya, sai dai munje d'in magani .

Innarmu tashigo d'akin tana cewa  waishin Baku naji innaro ta aiko kira bane? .

Muka amsa da  eh innarmu, mune .

 to mi kuke jira, kuwuce kutafi mana .

Babu Wanda yay magana acikinmu muka fita muna mamakin wannan kira Na innaro.

Tun a k'ofar falon baba k'arami mukaga wasu k'yawawan takalma, ga wani k'amshi yacika wajen, wicewa mukayi batareda mun shigaba, dukda mun hango Zarah da Siyama da Fiddausi natahowa cikin matsanancin gayu, saika rantse fita zasuyi wani gagarumin biki.

A k'ofar gidama munci karo da motoci uku duk bak'ak'e wulik, sai dai ta tsakiyar tafi k'yau da d'aukar hankali, garadan samarine majiya k'arfi kusan su 7 tsaitsaye ajikin motocin, duk suna sanye da bak'ak'en suit, daka gansu kasan babu sauk'i, hakan yasa muka fahimci bodyguards d'in bak'inne.

Gida biyu ne tsakanin gidan innaro da gidanmu, dan haka muka Isa da wuri. a tsakar gida muka isketa tana shanyar lawashin albasa. muka gaidata.

Yanda ta saba haka ta amsa mana, amma tace mushiga ciki tana zuwa.

Kusan mintuna 40 muna falon innaro zaune, amma bata shigoba, hakan yasakani tunanin tabas akwai wani lauje cikin nad'i a kiran namu, tashi nayi nalek'a tsakar gidan ta window, amma bata nan.  Munubiya kinsan Innaro bata gidanan kuwa? .

Cikeda mamaki tad'ago tana kallona,  kamarya bata nan? .

 Munu... Wlhy ko rantsuwa nayi babu kaffara aciki, akwai dalilin kawomu nan .

A sanyaye Munubiya tace,  karki damu Sweetheart, ko mai suke nufi ALLAH ya fisu, dama naga mamansu ya hameed tafito d'azu bayan mungama girki, ai d'an hakkin daka raina shike tsolema ido, *_RAINA KAMA KAGA GAYYAFA_* inji masu iya magana.

Hakane dear.

Daga nan muka zauna shiru kowa da abinda take tunani, har barci ya sace Munubiya, nukuma nahau chart kawai.



A gidanmu kuwa su Siyama ne suka fara Isa falon, tundaga k'ofar falon daddad'an k'amshin turaren bak'in yafara rikitasu, sun shiga da sallama, yayinda sukuma bak'in suka amsa.

Gaskiya masha ALLAH dan kuwa matasan samarine k'yawawa masu aji da gayu, suna kama da juna, hakan zai tabbatar maka da cewa jininsu d'aya. sunci ado cikin wasu rantsatstsun shaddoji gizna, sai maik'o sukeyi, d'aya yafi d'aya sakin fuska.

Su Siyama sun gaidasu cikin shauk'i da zumud'in fatan kowaccensu ta kasance abar za6i.

Sun amsa musu cikeda jan aji da nazartar su, ahaka Fauziyya da Safara'u da Haleematu suka shigo suma, suma dai gaidasun sukayi. Fauziyya da Zarah ne kawai sukayi hankalin tashi su zuba musu ruwa da lemo, sannan suka musu bismillar abinci.

Mai d'an yawan fara'ar ne yamusu godiya, sannan yace,  to ya sunan k'annen namune? .

Cikeda yanga kowacce tafara gabatar da kanta agaresu, yayinda sukuma suka maida hankali sosai wajen nazartarsu, bayan sun gama suma suka gabatar musu da kansun.

 Ni sunan Sulaiman, brother d'ina kuma Sa'eed, munji dad'i kwarai da gaske Na tarbar damuka samu daga gareku .

Murmushi duk sukayi suna nuna farin cikinsu suma, sund'an ta6a hira.

Babu Wanda yadamu da rashin ganinmu acikinsu sai Fauziyya, iyayenmu kuma basusan babumu ba, dansu suna falon Abbanmu suna hira.

Kusan awa d'aya sannan duk suka fito suka barsu dan sud'anci abinci.

Suna fita Sa'eed ya kalli Sulaiman a yatsine,  my man nida yaran nan nakula sunada rawar kai, garama mai farin kayannan naga kamar tafisu nutsuwa (Fauziyya) .

 wlhy gskyarka bro... Amma Kasan dolenefa mucika umarnin dad, tunda yayi rantsuwa akan dolene muza6a acikinsu, kai wlhy mun jama kanmu, ni dama tun maganar farko da dad yamana Na maida hankali naza6o da duk hakan bata faruba gareni .

Cikin ta6e baki Sa'eed yace,  wannan kuma kaika Sani malam. amma basuma 8 akace manaba? .

 eh hakane, amma kamanta ance biyu acikinsu sunada samari .

A nanma bakin Sa'eed Yakuma ta6ewa. sun d'anci abinda aka ajiye musu, sannan su Abba suka shigo suka gaisa, cikeda girmamawa suka gaida su Abba, hakan yayima Dady da baba k'arami dad'i, sun kuma tabbatarwa yaran sunada tarbiyya, dama basa kokwanto akan zance yayan Nasu.

An musu rakkiya duka Sassan gidanmu, sun Haida iyayenmu mata. ganinsu Yakuma rud'ar da iyayenmu, kowacce addau'arta ALLAH yasa d'iyarta aka za6a, yo wad'annan zuk'a-zuk'an samari haka, ga kud'i ga ilimi, kowacce saida suka ajiye mata kud'i suke fitowa, har innarmu ma.

Tun aiko kiranmu Innarmu taji ajikinta da biyu aka turamu can, amma baiwar ALLAH hakan bai dametaba, tasan dai wata bata aurar mijin wani, dan haka ko'a fuska bata nunama wani bama cikin wad'anda suka je wajen bak'inba.



Saida Innaro takusa awa d'aya sannan tashigo gidan, yinai tamkar ban gantaba, Munubiya kam tanata barcinta, itama sai bata kulaniba tashige bedroom d'inta.

Shigarta baifi da mintuna 3 ba mukajiyo sallama a k'ofar d'akin, nice Na amsa, Basheer yafara shigowa, sai kuma Sulaiman da Sa'eed, irin k'amshin damukaji a k'ofar d'akin baba karami yasani d'agowa dan jinsa anan, hakan ya tabbatar min da sune sukazo gaida Innaro.

Tunda suka shigo idonsu ya sauka a kanmu, sun kasa d'auke kai daga kallonmu.

Cikeda jan aji nace,  ina yininku .

Duk suka amsa da  lafiya big girl .

Basheer yace,  kai Aunty dama kuna nan Ku? .

Kallonsa nayi nace,  eh, ana nemanmu ne? .

 a'a, amma dai ba'asan badaku akaje wajen bak'iba .

Hararsa nayi, saboda sanin halin shegen surutunsa,  malam kaje ka kira musu Innaro ka zauna kana zubama mutane shegen surutu uwa aku .

Baki ya zum6ura sannan yanufi bedroom d'in Innaro.





Wanda tunda suka shigo yakasa d'auke kai daga kallona, saima zama dayayi kujeraf dake kallona yace,  ok dan bakwa buk'atar ganinmu kuka gudonan kenan? Sai kuma gashi ALLAH ya kawomu mun ganku, dama ance rabon kwad'o...... koko my man? .

Murmushi Sulaiman yayi, yace  hakane wlhy bro, hakanma dasukayi yamana dai-dai .

Magan ganinmu yasaka Munubiya tashi, Sulaiman yace,  sleeping beauty kin tashi? .

d'an waro idanu Munubiya tayi, sai kuma ta kalleni dan neman k'arin bayani.



Innaro takatsemu da fad'in  toku kuna ganin bak'i basai Ku tashi Ku basu wajeba .

 cikin tsokana Sulaiman yace,  a'a Granny idan sun tashi wazamu kalla? Sun gudo wajenki dan karmu gansu kuma sai gashi ALLAH ya kawomu har gida .

Ba k'aramin k'ona ran innaro maganar tayiba (dama an kawomu nanne dankar bak'in su gammu balle su za6emu, amma kuma sai gashi sun gammu anan d'in. Anyi gudun gara kenan.....>�#�=�J�).

Bamu tsaya sauraren abinda innaro zata ceba mukayi fitowarmu zuwa gida.

Su Sa'eed sun gaida innaro, anan take tambayarsu kosun za6a acikin wad'anda sukaje gaishesu acan gidanmu.

Sa'eed yace,  eh mun za6a Granny, amma wad'annan dasuka fita yanzu .

Caraf innaro tace,  ai wad'annan anmusu miji shiyyasa su basujeba, sai dai cikin wad'ancan .

Bahaka sukasoba, amma yazasuyi, sai dai har sukabar gidan basu sanar da wa suka za6aba.



Koda muka sanarma innarmu cewa tayi babu ko mai, karma hakan ya damemu.







&&&&&&&&



Har tsawon kwana 5 babu wata magana data fito akan suwa bak'in suka za6a, su Abba basuce da kowa komaiba.

Hankalin iyayenmu mata duk atashe yake, kowa takasa kunne taji wacece aka za6a, sai dai babu mai iya tunkarar iyayenmu maza da zancen, dan duk ba suga fuskar hakanba.



Satinsu guda da zuwa saiga bak'i sunzo wai an kawo kud'in aure.

Hankalin iyayenmu fa yakuma tashi, dan ganinsu wani munafurcin akayi shiyyasa aketa k'unbiya-k'unbiya. Nanfa suka shiga 'yan tsugunne-tsugunne Na gulma irinta gidan yawa.

Kwana biyu dayin haka su Abba suka sanar da cewa nida Munubiya sukace sun za6a.

Innaro ce tafara k'aryatawa, sannan tace, Sam bata aminceba, ina jikokin talakawa 'ya'yan bak'in haure suka kai matsayin auren 'ya'yan babban mutun irin sanata halliru, ai k'aryane sannan munafuncine, agabanta su Sa'eed sukace Zarah da Siyama suka za6a. (Zarah k'anwar ya hameed Ce, babanmu d'aya, Siyama kuwa d'iyar momy Hadiza Ce d'iyar dady).

Jin wannan zance yasa kowa ya fahimci akwai munafunci a lamarin, kowa yasan yanda mamansu ya hameed suke da momy Hadiza a gidan, kansu had'e yake. aikam matan gidanmu suka harzuk'a sunata yada magana, harma abin yaso yazama fad'a, innarmu ce batace komaiba, ita cewama Abbanmu tayi dan ALLAH amaida zancen auren kansu Siyamar tunda innaro tace dama su suka za6a.

Banza abbanmu yamata dan yasan innaro tayi hakanne danta k'untatama innarmu, amma tabbas dabakin su Sulaiman sukace 'yan biyunnan suka za6a, shin sai yaushene inna zata bar muzgunama Aisha da munanata a gidannan?, shekara kusan Arba'in ana Abu guda babu sassauci, tunda yake baita6a ganin rana d'aya da innarmu tama innaro koda kallon banzaba bare rashin kunya, sa6anin sauran matan gidan da basa kunyar ya6a mata magana koda ta habaicine.



Kwana kusan hud'u ana d'auki ba dad'i akan wannan zance, saboda akawo k'arshen maganar sai Abbanmu yace su Sa'eed suzo su nuna wad'anda suka za6a da kansu.

Hummm bamusan miya faruba, (konace mi innaro dasu momy hadiza suka k'ulla ba) munga dai sunta murnar zuwansu Sa'eed d'in, sai rawarkan had'a abincin tarbarsu sukeyi, dan ranar su biyu kacal sukayi, kuma abin mamaki wannan karon agidan innaro aka saukesu.

Bayan isowarsu dakamar mintuna 20 sunci abinci sai akace duk muje gidan innaro.

Su Haleematu duk sun rigamu tafiya, mune k'arshen zuwa muda Fauziyya, saidai muna shiga gidan Innaro ta samu mukabi ta k'ofar kitchen nida Munubiya kawai, Fauziyya kuma aka barta tashiga ta falo.

Yanda sukaita


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login