Showing 84001 words to 87000 words out of 365757 words

Chapter 29 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1510

musu rakkiya.

Bayan fitarsu saina shiga rera sabon kuka, saida nayi mai isata sannan natashi da nufin tafiya nawa d'akin, kallon falon nashiga yi, masha ALLAH, komai yayi a falonnan, kujerun Navy blue ne, sai labuloli da Carpet sun kasance Silver da kwalliyar k'ananun flowers blue, babu wani tarkace sosai, wani hotonsa ne yay masifar d'aukar hankalina, gaskiya hoton ya d'auku, yana sanye cikin kayan sarauta akan dokin dashima yasha kwalliya, murmushin dake d'auke a face nashi shine Yakuma k'awata tsarin hoto, ga hoton irin k'aton nanne kamar kamasa magana ya amsa maka.

Na juya na kalli d'ayan dake bangon kudu, shikam sanye yake cikin farin wando k'al da farar riga itama, ya tsuke k'ugunsa da bak'in belt, takalmansa da hularsa duk bak'ake, yana awani k'aton filine daya k'awatu da korayen ciyayi, hannunsa rik'e da wani k'arfe ga k'aramar boll a gabansa, nan ma fuskarsa washe da murmushi, har hakwaransa sun fito waje, a raina nace dama d'an wasan Golf<���<��� ne? kokuwa yasaka kayanne kawai?.>��

Da sauri na juyo jin motsi a bayana, sai kunya ta kamani ganinsa tsaye hard'e da hannayensa a k'irji yana kallona, gudun karya zaci kallon hoton nake sainayi saurin cewa  dama kana buga Golf?  .

Murmushin gefen baki yayi, yatako a hankali ya zauna a kujerar dake kallon hoton, shima idonsa na kan hoton, ya d'ora k'afarsa d'aya kan d'aya....

Jin yayi shiru yasani juyowa na kalleshi, a tunanina kobai ji baneba, ido muka had'a, kowa ya janye cikeda basarwa, saiya lumshe nasa tareda jingina da kujerar, tamkar anmasa dole yace  kinason wasanne? .

Nace,  kusan haka, duk da bansan kan wasanba har yanzun .

Murmushi naga yayi kawai amma baice komaiba.

Nima saiban sake cewa komanba na juya zan fita. idanu ya bud'e yabini da kallo harna fice.

Yana mamakin yanda bata da tsoro, zai iya cewa itace yarinya ta farko budurwa dakan iya masa magana kanta tsaye bada wani shakkuba atare da ita.

Tabbas a wannan fagen ya yaba mata, domin takafa tarihin da manyan 'yan mata masuji da mulki da Kansu suka kasayi, akwai 'ya'yan sarakuna da yawa dakesonsa amma sukan kasa fad'a masa, sunsha shan alwashi akansa amma da zarar sun had'u dashi sai alwashin nasu ya gudu, hakama 'ya'yan manyan attajirai, kuma baisan abinda yasa sukejin shakkar tasaba, shidai kawai abinda yasani baya sakar musu fuska, to ita wannan tatsitsiyar yarinyar koda fuskar tasa takai hadarin gabas murtukewa bata Shankar masa magana, ya cige lips nashi yana ta6e bakinsa wanda shiyasan dalilin yin hakan.





&&&&&&





Mama Fulani tagama cika tayi fam da rainin wayon Galadima, ba'a ta6a angon dayay abinda Galadima yayiba a masarautar, duk randa ango zai shiga d'akin amarya za'a kai farin k'yallen dasuke kira (yankin mutuntaka) a shinfid'a agado, washe gari za'a aika a d'ako domin kowa yaga mutuncin da yarinyar takawo, sannan dolene kuma kakawota da safe ta gaida matan Sarki da Sarki kafin yafita fada, saikuma sauran jama'ar gida wad'anda suka kasance iyaye.

Amma saboda rashin mutuncin fand'ararren yaron can anje d'aukar k'yallen yace zai kawo da Kansu saboda shine shugaban marasa kunya na duniya, ta aika bayi masu hidima damata CID ya korosu wai zai nemesu, gashi ana neman k'arfe uku na yamma amma har yanzu baizo gaisuwa ba shida matarsa, sai bayintane ke sanar mata sunga yarako dangin uwarsa lokacin dazasu tafi, amma ita tunda yazi bikinnan bama ta sakashi a idonta ba sai ranar da akayi Mother's and tarbar amarya event ta gansa awajen. yaron nanfa yana shigar mata hanci da yawa fa, bari taga iya gudun ruwansa da k'arshen wutsiyar iskancinsa, ai ko ubansa bai Isa mata abinda gagararren yaronnan ke mata ba a gidannan.





&&&



Shi baima San tanayiba, Dan tun bayan fitar Munaya daga sashensa yatashi zuwa masallaci sallar azhur, ana idarwa ko yarda su had'u da Sarki baiyiba ya shiga gida, shigewarsa yay bedroom, yayi kwanciyarsa domin yasamu yad'an huta, jikinsa duk ciwo yake masa, saboda ainan-ainan na al'adar biki, dukda yasan ko Rabin hidimar da harun yayi shi baiyiba, saima ka rantse Harun shine angon wlhy.

Bai wani dad'e da kwanciyar ba barci ya kwasheshi hankalinsa kwance.





&&&&



A gidanmu ma dai bak'i kowa yakama gabansa, an barsu daga su sai su, da daddare Abba yace ashirya da safe kowacce abita da akwatunanta, shi baiga dalilin ajiya ba.

Duk sun amsa da to, amma kowacce burinta ace da ita aka kai nawa, Dan sunason suyo kallon kwaf, basu gamsu da labarin da 'yan kai amarya suka fad'aba akan gidana Dana munubiya, su a tunaninsu ma an aurenine domin a maisheni baiwa, yaushe nakai matsayin da har d'an Sarki guda mai sarautar Galadima zai gani yace yanaso, bayan lungu da sak'on hotunan mun gama zagaye duniya ni da shi.

K'ilama da gaske yagama lalatani d'in.

Haka dai sukaita gutsiri tsomarsu da kushe irinta masu hassada, duk da wasu abubuwan suna dawo kunnen innarmu batako damuba, ita dai babu abinda zatace ma ALLAH sai godiya, tunda 'ya'yanta kowanne yasamu matsugunni, yanzu saita maida hankalinta ga ibadar ALLAH da tarbiyar yaranta biyu maza dasuka rage, sune basu gajiba indai tozarcine.





&&&&&





Zuwa la'asar mama Fulani tafara k'ananun magana akan rashin nuna shaidar Munaya takawo budurcinta, dakuma rashin fitowarsu gaida mutane.

ALLAH Sarki Aunty Mimi sai abin ya dameta ganin yanda aketa k'ananun magana a masarautar, hakkane yasata nufar sashen Galadima, babu zancen jiran a mata iso, sarkin k'ofa yabata hanyar tashiga.

Tun'a falon farko daya raba sashina da nasa tace bayinta su jirata.

Babu kowa a falonsa, Dan haka ta zauna tad'au waya ta kirasa, dan batasan halin dayake acikiba, baikuma kamata tashiga kai tsayeba, balle yanzu yanada mata.

Fitowarsa kenan daga wanka saboda tashin dayayi a makare baisamu sallar la'asar ba, sai anan d'aki yayita sannan yashiga wanka. Wayar ya kalla yayinda yake goge ruwan fuskarsa, ganin aunty Mimi yasashi picking call d'in, saiya saka a Hans free yana cigaba da hidimarsa.

 my aunty kin 6uya fa .

 na 6uya ko ka 6uya my k'ani, gani zaune ai a falonka .

 kai haba dai? to bani kamar 5minutes na shirya nafito .

 ok babu damuwa .

https://2gnblog.blogspot.com/

Bai wani dad'eba yafito sanye cikin farin boyal mai shara-shara, yayi k'au sosai, sai zabga k'amshin turarensa yakeyi na koyaushe. daga shi har Aunty Mimi suka sakarma juna murmushi, ya zauna kujerar dake kallonta yana fad'in  sweet aunty na ni kad'ai .

 anya kuwa yanzu bamu raba da Munaya ba my k'ani? .

Murmushi yayi wadda har hak'waransa na bayyana, ya d'ora k'afafunsa d'aya kan d'aya yana gyara zama,  in haka kikeso my Aunty saiku raba ai .

dariya tayi tace,  nama bar mata. wai kasan mike faruwa a gidannan kuwa? .

 A'a saikin fad'a .

 tun kafin tafiyar su mom aka fara k'ananun magana a masarautar nan, wai anzo kar6ar yankin mutuntaka ka hana .

 mtsoww! yaja tsaki yana jingina da kujerar da lumshe idanunsa,  Aunty Mimi dan ALLAH karki biyema wannan jahilcin kema yabud'e idonsa akanta, ransa a d'an 6ace yacigaba da fad'in  kawai da Wanda yakai sanin sirrinka da Wanda ma baikaiba wai duk sai sun sani?, a wace ayar alkur'ani ko hadisi akace dan ka tare da matarka a daren farko sai duniya ta sani?. ita mai aiko a d'auki k'yallen ince agaban kowa na gidannan lokacin da abunnan yafaru take fad'in bakinta bazai iya maimaita k'azantar danayiba?, to kuma tunda tariga da tasan nayi k'azantar abaya miye na aiko da wani k'yallen banza da wofi? wlhy fa suka kaini k'arshe zan shuka rashin mutunci kinji na rantse .

Shiru Aunty Mimi tayi tana kallonsa, tasan ransa yakai k'ololuwar 6aci, dan Galadima yanada hak'uri sosai, gudun kar matsala ta biyo saboda ciwonsa saita kwantar da murya,  haba my k'ani kwantar da hankalinka mana, ai abun bana 6acin rai baneba kaji, haba my habibi .

 Aunty Mimi nagaji ne wlhy, rashin mutuncin masarautar nan yafara isata, nifa komai zan iya kawoshi karshe a wannan karon .

Tasowa tayi ta zauna kujerar gefensa, ta kama hannunsa  please cool down mana my man, kaci gaba da hak'uri tamkar yanda kakeyi abaya, ALLAH yana tare da masu hak'uri, Momma bazataji dad'in wani Abu yabiyo bayaba, hakama Abie duk da yana a kwance zuciyarsa zatayi kunci, kansu ai sukema wa, yanzu ina k'yallen?  .

Iska ya furzar daga bakinsa, sannan ya nuna mata bedroom d'insa da hannu.

Tashi tayi tashiga, a saman sofa taga k'yallen dan haka ta d'akko ta fito. zama takuma yi a kusa da shi,  my K'ani ina zamu samu syringe? .

Idonsa yabud'e ya kalleta,  syringe kuma? mizakiyi dashi? .

 Sameer duk abinda zamuyi mu kare mutuncin mahaifanmu da lafiyarka muyishi mu zauna lafiya. yanzu dai kasa wani ya kawo mana .

Baice komaiba yajawo wayarsa yakira Muftahu, buk'atarsa ya fad'a masa sannan ya yanke wayar batareda yajira cewar Muftahun ba.

Wata hirar Aunty Mimi ta d'akko masa, tun yana basar da ita, har ya fara tanka ta, daga nan suka cigaba da hira.

Knocking d'in k'ofar akayi, Galadima yace,  waye .

Sarkin k'ofa yace,  ranka ya dad'e yalla6ai Muftahu ne yazo yace amasa iso .

 kace ya shigo .



Da sallama Muftahu ya shigo, ya rissina ya gaida Aunty Mimi sannan yabama Galadima hannu suka gaisa cikin musabaha.

Ledar hannunsa ya mik'ama Galadima,  no kabama aunty mimi .

Aunty Mimi ta kar6a ta fiddo da Syringe ta 6are daga ledar, had'awa tayi tare da Allurar sannan ta janyo charger ta d'aure tsintsiyar hannunta, Galadima da Muftahu dai kallonta sukeyi, allurar zata tsira Galadima ya rik'e  mizakiyi hakane Aunty Mimi? .

 Sameer! wannan itace kawai mafita, kabari kawai na d'iba a saka musu, da safe saika basu .

lips d'insa ya cije da k'arfi, yashiga kwance charger data d'aure hannunta,  ki barsa zan saka musu nawa, yanzu ma koda an saka zai bushene, dan yayi wuri ai .

 karfa kazo ka shukani .

 karki damu zanyi, kema kin sani ai, tunda na amsa to zanyin .

Mik'ewa tayi tana fad'in  shikenan to, bara na duba k'anwata itama .

Kansa kawai ya jinjina mata, yayinda muftahu yamata sallama ta fice.



 wai mike faruwa? ranka ya dad'e .

Tsaki Galadima yaja, yay shiru kusan minti 2, har Muftahu ya yanke tsammani da samun amsa. labarin komai yabashi.

Shima Muftahu tsuka yaja,  wai dan ALLAH yaushe za'a daina jahillar al'adarnan a masarautar nan? abinda ba addini ya wajabtaba sun kama sun rik'e, kuma duk matsalar tsohuwar nan ce wlhy, masarautu nawa ne suka daina wannan abun, amma mu takafa ta tsare, ALLAH lokacin da akayi na Uncle Hayatudden, kunya abinnan yabani saboda shi kawai nata6a gani, sashe-sashefa haka akaita nuniyar abinnan a masarautar nan wlhy .

Wani mugun tsuka Galadima yaja saboda haushi da abin yakuma bashi, fitarma da yay niya saiyaji yafasa.





&&&



Ni bansan mike faruwa ba ma, ina d'aki kwance duk kewa da kad'aici sun gallabeni, ga wayata babu caji saboda na manto cajan a gida.

Nayi zurfi a tunani naji ana sallama. firgigit nayi sannan na amsa, hijjab d'ina najawo na saka, ina k'ok'arin tashi tashigo. da Sauri na mik'e ina mata sannu da zuwa, dan nariga da na shaidata itace aunty Mimi. rissinawa nayi na gaidata, ta amsa cikeda fara'a sannan ta zauna. mik'ewa nayi na nufi freight domin bata ruwan amma saita dakatar dani ta hanyar kamo hannuna.

 no k'anwata barshi kinji, yi zaman ki, ya zaman kad'aici da bak'unta? .

Kaina a k'asa nayi murmushi kawai, sannan nace  Alhmdllh aunty .

 masha ALLAHU k'anwata, babu dai wata matsala ko? .

Kai na na d'aga mata alamar babu, daga nan mukayi shiru saboda rashin sabo.

Zuwa can nace,  ina Samha?, tun d'azu tace zata dawo amma har yanzu? .

Murmushi tayi, tace,  sun fitane itada Sauban tun d'azun, amma nasan suna hanyar dawowa kam .

 Ayya ALLAH ya dawo dasu lafiya .

Ta amsa da amin tana mik'ewa. har falona namata rakiya, inajin dad'in yanda take nuna tana sona.





*******



A can kuwa bayan Muftahu yafito daga wajen Galadima sai yayi murmushi, tabbas yasamu hanyar dazata zame masa tsanin *CIKAR BURINSA*, da wannan kawai zai iya cin galaba akan Galadima.

Da wannan tunanin ya hau mota yabar masarautar gaba d'aya.





Mikake k'ullawa ne Muftahu?=�1�





&&&&&&





Bayan sallar isha'i ina zaune ina karatun Alkur'ani Galadima ya shigo, ban daina ba saida na kai aya sannan, na d'ago domin gaidashi sainaga idonsa a kai na.

Janyewa nayi nace  barka da dare .

Bai amsaba cewa kawai yayi  tashi ki shirya zamuje gaisuwa cikin gida .

Nima sai ban amsa shiba namik'e kawai na maida Alkur'anin inda na gansa. tashi yayi yafita danya bani damar shiryawa. banja wani lokacin mai tsayiba nafito cikin Alk'yabba, tsaye na iskeshi a falona, batareda yace uffanba yafara k'ok'arin fita, nima sai nabi bayansa batareda na tanka d'inba.................
'<���











>�s�mun tafi sashen mama Fulani, maison jin yanda zata kaya saiya biyoni.

�&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&









Barka da juma'a=��=�L�<���











*_YA ALLAHA KA GAFARTAMA IYAYENMU_*=�-�=�O�<���

*_Typing=���_*







*_HASKE WRITERS ASSO...=ء�_*

_(Home of expert and perfect writer's)_









*_f&RAINA KAMA......!!f&_*

_{Kaga gayya}_









*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







=�I�<���2� 4�





............ Tunda muka fito masu hidimar sashensa suketa zubewa suna gaishemu, hannu kawai yake d'aga musu, nikam ma ba amsawa nakeba.

Wata mota aka bud'e mana muka shiga, mamaki ya kamani, shin ba'a cikin gidan bane?. banida mai bani amsa dan haka nayi gum.

Duk da darene muna ganin bayi dake yawo tsilli-tsilli, ga ko'ina kwanyar da haske, a k'ofar wani sashi ya tsaya da motar.

Kallona ya juyo yayi, cikin muryar nan tasa ta k'asaita yace,  basai na fad'a mikiba, kinsan yanda ya kamata ace kowa ya ganmu, nan sashen kakarmu ne mai suna mama Fulani  .

Kai na na gyad'a masa, sannan muka fito saboda anbud'e mana dama tuni.



Tunda muka fito ake kwasar gaisuwa, nikam sai binsu da kallon tausayi nakeyi, su shikenan a bautama wasu zasu k'are, basu da wani 'yancin Kansu......

Tunanina ya kakare, lokacin danaji tattausan hannunsa cikin nawa, kowannen mu saida yaji shock, nad'an rumtse idanuna, yayinda shikuma ya cije lips.

Saida aka mana iso sannan muka shiga. kata faren falone na alfarma, iyakar k'yau da tsaruwa yayi, saikace ba falon tsohuwa ba, ga k'amshin turare na musamman na tashi,.

Bafulatanar tsohuwace mai jikin fulanin asali, dankuwa akwai k'yawu iya k'yawu, tabbas wannan a zamanin k'uruciya anyi asalin k'yak'yk'awa, sai dai gajarta tamata tsiya kam>�#�>�-�.

A kishin gid'e take, yayinda hadimai ke zagaye da ita, kowanne da aikin dayakeyi. Shigowar mu tasakasu kowa tasaki tanemi hanyar fita kamar yanda tabasu umarni. Bai saki hannuna ba har muka k'arisa gabanta, yayinda ita kuma idonta ke akan hannayenmu dake sark'e dana juna ko k'yaftawa batayi.

Saida ya taimaka min na zauna bisa tattausan carpet d'in dake falon, gaf da mama Fulani kad'an, sannan shima ya zauna kusa dani.

 Ranki ya dad'e barka da hutawa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login