Showing 270001 words to 273000 words out of 365757 words

Chapter 91 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1428

tsaf, nasan sotake taga mina goge kona canja, ganin komai yana yanda tayishi saita kuma d'aukar soson hoda ta gyara, ta d'akko turare tana kuma fesamin, hannunta nai saurin rik'ewa ina 6ata fuska,  Wai Sweetheart bazaki barshi haka bane? Turaren nan har hawa kaifa yake, Ni wlhy kunyarma fita nakeyi .

Munubiya ta fisge hannunta tana dariya da fad'in  to kibi ta k'ark'ashin k'asa kawai mana, kuma wlhy ki nutsu, idan yauma tsiwar zaki masa saiki bada himma, anacewa mutum Idan ya haihu yana hankali kedai bakiyiba, saima rashinsa kika k'aro, malama muje yana jiranki .

Yanda kukasan na make Munubiya haka naji, amma saina k'yaleta, nima nasan ta hanyar da zanbi na rama, gyalen data samin a kafad'a nabi da kallo.

nace,  haba Munu, amma wannan d'an gyalen Dan ALLAH? .

 Okay, wajen surukinki zakine? ALLAH ki kiyayeni .

Baki na murgud'a mata.

Tace,  oho dai, kije kimasa kidawo ta cinyayyen lips, danba barinki zaiyiba .

Juyawa nayi na kalleta, amma saita d'auke kai tamkar bama itace tayi maganarba. Nayi kwafa kawai muka fito.

ALLAH ya soni babu kowa a falo sai su Aiyaan, hakkane ya sakani sauke ajiyar zuciya nad'an saki jikina.



Gwaggon Haleematu dake kaikawo a kitchen da tsakar gida saboda itace ta kar6i girki tabimu da kallo, gulma nacin ranta, daga ni har Munubiya d'auke kai mukayi tamkar bamu gantaba, muka shige falon Abba da takalman Galadima heif cover milk ke a k'ofar.

K'amshin turarensa yafara amsa mana sallama, na shak'a na lumshe ido.

Hankalinsa nakan yaransa da duk suke jikinsa, yana sanye cikin milk d'in shadda harda hular zanna bukar itama milk da d'an kwalliyar Brown kad'an, sosai yamin k'yau amma saina d'auke kai tamkar banma gansa ba.

Munubiya tace,  To Abban 3 gatanan nakawo maka .

Murmushi yayi, idonsa sanye cikin farin eyeglasses, cikin muryarnan tasa mai kama da anmasa dole yace,  Thanks you Auntynmu .

Murmushi itama Munubiya tayi, ta jinjina masa kai ta juya zata fita, har takai k'ofa ya katseta da fad'in  Su twins rowarsu akemin? .

Hannu ta saka ta dafe bakinta, saikuma ta janye tana cewa,  A'a Abban 3 zasuzo su gaida abbansu insha ALLAH .

Baice komaiba sai murmushi daya sakeyi.

Ta harareni sannan ta fice, Nina ramawa nayi.



Koda Munubiya ta fice saiya kuma maida hankalinsa ga yaran ya shareni, abin yabani haushi, jinaima kamar na fice abina, amma na danne zuciyata na matsa gabansa. Wajen tiren abincin na durk'usa, na d'auki jug d'in zo6on na zuba a k'aramin cup, d'agowar da zanyi na kamashi yana kallona, amma saiya basar, baki na tura kad'an, na mik'a masa cup d'in.

Bai kar6aba, sai wani bina da kallo yake tundaga sama har k'asa, a raina nace rainin wayo.

Idonsa ya janye daga kaina, ya fara kwantar da yaran d'ai-d'ai a gefensa, saboda a doguwan kujera yake.

Saida ya gama nakuma mik'a masa cup d'in, hannuna ya had'a da kofin ya rik'e, na d'ago ido muka kalli juna, duksai na daburce, danya cire eyeglasses d'in, kamar mai koyan magana na had'o kalmomin gaisuwar da gyar.

Nace,  i...na..yini .

Wani Munafukin murmushi yayi yana lumshe idanu, ya kuma bud'esu a kaina yana d'age girarsa d'aya da cizar lips, a hankali ya furta  ke matsoraciya Ce, miye na rikitar daga kallo uhmyim? .

Idanuna nad'an juya nace,  Tab badai niba .

Ya ta6e baki kad'an, idonsa akan hannunmu dake had'e waje d'aya akan kofin.

Nima saina kalli hannun, cikin sanyin muryar dabansan nayiba nace,  da sanyi fa .

 Really? .

Shiru nayi ban amsashiba, ya zame kofin a hankali, sannan ya koma jikin kujerar ya kwanta yana hard'e k'afafu.

6oyayyar ajiyar zuciya na sauke, bansan miyasa inhar Galadima zai kasance kusa dani daf irin haka koya kafeni da ido nake rikicewa ba, haka kawai sainaji jikina yana tsuma...

Yay wani luuu da idanu saboda ajiyar zuciyar da tayi, zo6on ya kai bakinsa ya kur6a kad'an, dad'insa ya sakashi lumshe idanu ya had'iye.

Da hannu yamin nuni da kujera, tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki na mik'e, harzan bar wajen naje ta nesa dashi saiya rik'o hannuna. Juyawa nai na kallesa, ya nunamin kujerar kusa dashi da ido cikin tsare gida.

Banida za6in daya wuce bin umarninsa, na zauna tamkar mai shirin guduwa da ance ar.

Zo6on yakuma sha yana kallona, kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru.

Ganin haka sai nace,  yaya jikin Abie? dasu Momma? .

Yaji dad'in ganin ta damu da ahalinsa, ya ajiye kofin yana gyara zama, yace,  jikin Abie Alhmdllh munata k'ara ganin haske, duk since na gaidaki dak'yau .

Nace,  ina amsawa .

Daganan mukai shiru, kowa yana tattaunawa da zuciyarsa, Idan ka gammu saika d'auka wasu saurayi da budurwane, irin had'uwar farko d'innan=��.

Abimda na fahimta dai kamar yana tattare da damuwa ma, nad'an kallesa ta gefen ido, idonsa nakan yaransa, nace,  Abinci fa? .

Maido da kallonsa yay gareni, yad'an yamutsa fuska yana girgiza kai.

Kallonsa nayi, cikin marairaicewar da bansan nayiba nace,  please mana yalla6ai, yanzu haka bakaci komaiba ka fito gida .

Wani Abu dabaisan miyeba yaji ya tsarga cikin kansa har zuwa tafin k'afa, idonsa k'yam akan Munaya ko k'yaftawa bayayi, itama gareta hakanne, ta zuba masa ido batare da ta shirya hakanba, sai tsantsar tausayinsa dayake hangowa cikin idanunta, hannunta ya kamo cikin nasa, yana fad'in  kinaso naci? .

A sanyaye na jinjina masa kai alamar eh.

Murmushin gefen baki yayi, ya matsa hannunta kad'an,  indai kinason naci akwai sharad'i .

Batareda nasan mi bakina ya fad'aba nace,  kafad'a kona miye na amince .

Kansa ya jinjina yana janye hannunsa, ya gyara zamansa yana fuskantata sosai, akan la66a ya furta,  saidai idan zaki bani da kanki .

Babu shiri na waro manyan idanuna ina dafe baki alamar mamaki, ya had'e fuska yana ta6e baki da kwantar da kansa jikin kujerar. Yace,  Ashe ba sokike nacinba, kuma yunwa nakeji .

Harga ALLAH inason yaci, dan na fahimci yanada buk'atar abincin, amma yana azabtar da kansa saboda bai yarda yaci na kowaba amasarautarsu, idan kuma ya fito inhar ba birnin gayu yajeba bazai ta6a cin komaiba inba ruwa ba harya koma gida kuwa...

Na sauke ajiyar zuciya, idona cikeda kwalla nace  to amma...

Idonsa ya bud'e ya d'agamin hannu, amma baice komaiba.

Nima ban sake yunk'urin cewa wani abunba, na sakko daga kujerar na durk'usa a k'asa ina bud'e kulolin.

Mamaki ya kamani, dan ganin masa, a ina Munubiya ta samo masa haka? A lokacin da tasan zaizo yayi k'arancin da har za'ayi Masa. ganin babu mai amsamin tambayar na zuba hud'u a plate d'in, na d'ago ido na kallesa, Ashe shima ni yake kallo, idanu ya lumshe alamun ya Isa. Nima saina jinjina kai, kwanon da zansa miya na d'akko, amma saiya rik'e hannuna yana girgiza kai, na kalli plate d'in masar sannan na d'ago Na kallesa, ya kad'amin kai.

Fahimtar mi yake nufi da nayi saina zuba miyar gefen masar, sannan na mik'e da nufin komawa inda na taso, tiren abincin ya janye gefe, ya jawo center teble d'in a gabansa sosai.

Kallon teble d'in nayi shima na kallesa, saiya d'auke idonsa, a yanda ya janyo teble d'in inhar na zauna dolene k'afafunmu suke gogar juna, amma ya zanyi tunda na d'auki alk'awari.

Zama nayi, na d'ora plate d'in saman cinyata, na d'ebo masar da spoon na nufi bakinsa, baki ya ta6e yana girgiza kai.

Na dafe kaina irin naga ta kaina d'innan, na kallesa a marairaice,  yalla6ai to ya kakeso nayi please?, kaifa kace zakaci .

Da d'an yatsa ya nuna hannuna. Cikin mamaki nace,  da hannu? .

Yanda tai maganar tana zaro ido saiya so bashi dariya, amma ya had'iye kayarsa.

 O ni Munaya naga ta kaina . Nafad'a a hankali.

A ransa yace zadai ki gani yarinya.

Dole na mik'e nakuma wanko hannuna a bayin falon Abba, na dawo, gyalena na zame dole na shinfid'a masa saman cinya gudun karna 6ata masa kaya, na fara d'ibar masar kamar yanda yake buk'ata na nufi bakinsa, saida ya kama hannuna sannan ya k'arasa dashi cikin bakin, ALLAH sai da tsigar jikina ta tashi, amma na daure nakuma d'ibowa, haka naita bashi har ya cinye, na bashi nama ya girgiza kai, alama namasa a k'ara?. Da d'an yatsa ya nunamin wai d'aya, bud'e kular nayi na d'auka, sauran miyar plate d'in ta isa, zan gutsura ya rik'e hannuna, a mamakina sainaga ya d'an ja hannun rigarsa sama ya saka hannu a plate d'in, idanu na waro da bud'e baki Dan mamaki, sai kawai naji hannunsa cikin bakina ya sakamin masa, ya d'agamin gira d'aya damin alamar inci, tamkar sokuwa haka na shiga taunawa, harna had'iye idonsa nakan bakina, saida ya rage saura lauma d'aya ya dakata da bani, na ida d'aukar laumar k'arshen na saka masa nima, ina niyyar tashi na wanke hannu ya maidani zaune, hannun dana bashi ya kamo yana sud'ewa, salon dayake lashe miyar saiya haifarmin da kasala, na rumtse idona harya gama sannan ya sakarmin hannu. Nima saina kama nasan na tsotse sannan na mik'e, ina toilet zan wanke hannuna zan d'ibo shima nakawo ya wanke sai na jishi a bayana, juyowa nayi na kallesa, ya mik'amin hannunsa. Bance komaiba na kama na wanke masa, na zuba masa ruwa ya kuskure bakinsa. Nidai gaba d'aya mamaki dukya nemi halakani.

Koda muka fito ina niyyar komawa inda na fara zama sai naji an fisgoni, jikinsa na fad'a, bance komaiba dukda naji zafi. Shima baice uffanba.

Lallai akwai abinda ke damunsa da gaske, hannuna na d'ora a kan k'irjinsa saitin zuciyarsa, ya bud'e ido sosai yana kallon hannun nawa, cikin aro jarumta nace,  Autan Momma mike damunka wai? .

Murmushin dabai shiryaba ya saki, ya kalleni ido cikin ido yana fad'in,  kin rainani ALLAH kuwa, wannan autan bazai bar bakinkiba dai ko? .

Murmushi nayi mai sauti, har hak'orana na bayyana, na had'e hannayena a waje d'aya alamar ban hak'uri, cikin langa6e kai nace,  tuba nake to na tsakkiya nefa kai ashe .

Rankwashi yamin a kai, na dafe wajen dukda d'ankwali yasa banji zafiba sosai, amma na 6ata fuska ina k'ak'alo hawayen k'arya.

Gira d'aya ya d'age yana kallona alamar yadai?.

Na tura baki gaba ina fad'in,  da zafifa .

Murmushi yayi yana kauda idonsa yana kallon yaransa.

Na yunk'ura da nufin sauka a jikina amma ya rik'eni, ba tare da ya kalleniba yace,  yakamata kisan kin girma .

Bakin na kuma tunzurawa nace,  hu'im ina nan a babyna wlhy .

Shi kansa baisan k'aramar dariya ta kufce masaba, ya d'an dara yana girgiza kai da kallona.

Ganin ya fara sakin jikinsa saina kuma cewa  Please yalla6ai bakada lafiya ne? .

Tafin Hannunsa ya sanya saman kumatuna, a hankali tamkar mai rad'a yace,  mikika gani? .

Na d'an kuma kwantar da murya ina janye idona daga cikin nasa,  Ba komai, kawai yanayinka ne ya nuna .

Baice komaiba ya matso da fuskarsa gab da tawa ya had'e bakinmu, dukda na tsorata kar wani ya shigo ya gammu haka na barsa, yayi yanda yake so inhar hakan zai kauda damuwar dake ransa, nidai fatana na cika alk'awarin dana d'aukarma Momma a duk sanda na gansa cikin damuwa.

Saida ya gaji da kansa sannan ya bari tareda rungumeni yana sauke ajiyar zuciya, muryarsa can k'asan mak'oshi yace,  haka kike son ganina .

Kaina na girgiza masa, ya d'agoni da sauri yana kallona, yace,  to yaya? .

Murmushi nayi nafad'a k'irjinsa ina 6oye fuskata saboda kunya, shima saiya saka hannuwansa ya zagayeni yana murmushin, a hakanla ya furta  Thanks .

Bance komaiba, amma naji dad'i daya godemin.

Kiran wayarsa da akayi ya sakani tashi daga jikinsa, zan tashi gaba d'aya ya rik'eni, a haka yay picking call d'in, na fahimci da papi yake waya, dukda kakansa ne yanda yake magana cikeda tsantsar girmamawa saiya birgeni, Mai dawakai danaji yana ambata da bayanin d'ansa mai suna Badi ne yaja hankali na, tsaf na fahinci zancen dukda bansan mafariba, yakuma yanke maganar bai k'arasaba yana fad'ama papi sai yazo zasu k'arasa zancen.

Yanke wayar yayi yana huremin ido saboda kallonsa dana keyi, tunda ya fara wayar.

K'asa nayi da kaina dan naji kunya ya kamani ina kallonsa, ya ajiye wayar yana fad'in  Zamukai Abdurrahman asibiti ne? .

Kaina na girgiza masa. nace,  A'a aiya warke bama sai an kaisa ba .

Yace,  Okay . Idonsa akan yaran, Abdurraheem ya fara motse-motsen tashi, sauka nayi a jikinsa nakoma gaban kujerar na durk'usa ina d'an bubbuga bayansa, dan banason ya tashi, inhar ya tashi saiyasha nono, sauran kuma suma duk tashi zasuyi, bada nono a gaban Galadima shine abinda nake gudu ni kuma.

Shikam tsura musu ido yayi cikeda sha'awa daga ita har yaran, ya d'auki wayarsa yamusu hoto batare da ta saniba.



Saida naga ya koma barci sannan Na dawo kujerar dana fara zama, shima zamansa yagyara yana kallona, magana yakeson yi amma yanata juyata a zuciya, nidai bance dashi komaiba, saida ya gama k'asaitarsa da basarwa sannan yace,  Abba fa? .

Nace,  yayi tafiya yau kwana biyu .

 zuwa ina kenan? .

 wlhy ban saniba, amma miya faru? .

Kansa ya girgizamin alamar babu komai, yad'an furzar da huci yana kallona agogon hannunsa.  Shikenan ni zan wuce, zan iya dawowa a kowane lokaci inhar Abba ya dawo .

Kaina na jinjina masa, ya mik'e, nima saina mik'e ina fad'in  yaa Sauban fa? .

Bai tankaminba saida ya duk'a yayma yaransa kisses a kumatu sannan ya d'an kalleni ya d'auke kansa,  Tare muka dawo, amma zai wuce masarautar su papi gobe, dan a can zai zauna harya gama .

 ALLAH ya bada nasara . Nafad'a ina sauke ajiyar zuciya.

A kan la66a ya amsa da amin.

Harya kusa nufar k'ofa nace,  bakace komai game da maganarmu bafa .

Cak ya tsaya amma bai juyoba, a haka yace  wace magar? .

Wani yawu na had'iye da k'yar ina fad'in,  Maganar rabuwa, nifa gaskiya bazan komaba .

Saida yaja kusan seconds 20 kafin ya juyo yana fuskantata, kallon da yakemin yasani janye idona daga kallonsa, cikeda k'asaitarsa yatako ya dawo inda nake tsaye, hannayensa ya cusa cikin aljihu yay matuk'ar d'aure fuska, cikin izzarsa yace,  wai nikam miyasa kikeda naci? .

Nima fuskar na tamke. Nace,  Neman y'ancina nake, tun farko a wannan tubalin ka gina auren, mizaisa kuma lokacin rugujeshi yayi bazakayi hakanba? .

Lips d'insa ya ciza yana kallona da k'ank'ance idanu, cikin salon Basarwar tasa yace,  So what idan nine na gina a haka d'in? Kinsan dai bazaki ajiyemin yara ba koda abinda kikeson ya kasance, dan yarana bazasu sha madaraba bayan sunada abinci .

 Humm na fad'a cikin takaici. na gyara tsayuwa idona na cikowa da kwalla,  Yalla6ai karka manta a randa na kwana biyu gidanka da bakiknka ka tabbatar min baka zalunci? daga ni har kai mun amince cikin yarannan ya zone cikin k'addarar dabamu shiryama


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login