Showing 249001 words to 252000 words out of 365757 words

Chapter 84 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1537

fad'i tashi a kanta da yaranta, danma tak'i amincewa ne da aurenta zaiyi, anya kuwa shi yake nufi kodai wanine mai irin sunansa? .

Jiki a sanyaye Muftahu ya yarfar da hannu alamar bai saniba shima. danshi lamarin Galadima yafara bashi tsoro, mutum kamar wani tsohon aljani.



Shikam koda yabar wajensu wani office yace Sarkin mota ya kaisa, yakai tsawon lokacin a wajen tareda wani mutum dabazai gaza shekaru 56 ba a duniya, bansan mi suka tattauna ba, dan ba'a bani damar jinba.

A wajen yay sallar azhur har la'asar sannan yayo masa rakkiya wajen Motocinsa, saida yaga fitarsu sannan yakoma Office d'in.





Daga nan masarauta suka nufa, dan Galadima a matuk'ar gajiye yake,

Ya iske sashensa fes an gyara, ko ina yana tashin k'amshi tamkar yadda yake buk'ata, kayansa yacire ya watso ruwa, bai nemi kowa baya ya zauna a falo yana aiki a System, dukda yaga abincin da aka ajiye masa baiko bud'eba balle tunanin cinsa, Yakuma san Aunty Mimi ce zata saka a kawo.

Yana tsaka da aikin Sauban ya shigo, bai kallesaba koda ya gaidashi, yadai Amsa.

Sauban yace,  yaa Sam tafiyar safe zamuyine goben? ..

Ido Galadima yad'an d'ago ya kallesa, ya maida kansa ga laptop d'in yana fad'in,  Kwana 3 zamuyi ni da kai mu dawo, komanka na gameda bautar k'asa yagama kammaluwa .

Kamar Sauban zai sanya kuka yace,  Amma Yaa Sam su Momma sai abarsu babu kowa? .

 kafin ka girma dawa suke zaune?, Sauban ka kiyayeni, karka bari na fusata akanka, tashi bani waje .

Sauban ya mik'e zuciyarsa na zafi, harzai fita Galadima yace,  zonan .

Dawowa yay yana mirgina kai, batareda Galadima ya kallesa ba yace, kar6a wannan, kaje ka sakashi jikin rigar Abdurrahman ko Amaturrahman ka d'auki Wanda ka samawa d'in kaje sashen Ummu Amaan (gimbiya Zulfa) dashi .

Sauban baice komaiba ya kar6a abinda yabashi mai kama da ma6alli ya fita, ya iske Munaya na barci, yaran kuma na tare da Khaleel dake ta fama jagwalgwalasu, Abdurrahman ya d'auka ya sakamawa ya nad'eshi a showal ya fita......

��



Nikam wannan gangancin na Galadima ya isheni=�(�=�F�<���.





Bansake jin miya faruba dan banbi Sauban ba nikam, ina tsoron ganin abinda zai hanani barci=� �.





__________________________





Misalin 8:30 na dare Galadima ke shiri bayan ya dawo daga sallar isha'i, yagama tsaf cikin k'ananun kaya da jacket d'insa wadda takai masa har gwiwa, ya saka safa har a hannunsa, cikin takunnan nasa na gwarzantaka ya fito, sashen Munaya ya nufa, sukaci karo a k'ofar d'aki zata fito a rikice, sauri tareta yayi ta fad'o jikinsa saboda kad'an yarage ta fad'i, k'amshin turarensa ya sakata shaida shine, ta share hawayenta tana kallonsa a rikice, shima kallonta yakeyi, Muryarta na rawa saboda kuka tace,  yalla6ai Abdurrahman sai kuka yakeyi, jikinsa ya d'auki zafi .

Baice komaiba ya kama hannunta suka koma cikin d'akin, laraba da aunty Mimi na zaune, aunty Mimi tana zarema Abdurrahman kayan jikinsa za'a watsa masa ruwan d'umi kozaiyi shiru.

Zama yayi ya kar6e sa daga hannun Aunty mimi, ya fiddo wani kwali k'arami daga aljihun jacket d'insa ya bud'e, k'aramar kwalbar dake cikeda magani ya fiddo, ya d'iba maganin cikin tsinken da ake bama yara magani ya zubama yaran a bak'i, dak'yar ya shanyeshi.

Sudai sunyi jugum-jugum suna kallonsa.

Yunk'urin amai da yaron keyi yasaka Galadima d'agashi daga jikinsa dan kar yay masa, baimayi amanba, hakanne yasaka Galadima sauke ajiyar zuciya ya mannashi da k'irjinsa yana hura cikin kunnen yaron a hankali.

Tun yana kukan kad'an-kad'an ya koma ajiyar zuciya, sai gashi yayi barci. Kwantar dashi yayi kusada y'an uwansa ya lullu6esa.

Ya kalli aunty Mimi yana mik'ewa,  insha ALLAH zai sauka zaza6in ..

Yanda Aunty Mimi kebinsa da kallon tuhuma saiya janye idonsa yakama hanyar fita, da sauri tamik'e tabi bayansa a fusace. Dan Sauban ya sanar mata Galadima ya sashi kai yaron sashen mai martaba d'azun.

 Dakata Sameer .

Cak ya tsaya yanajan hular rigar bisa kansa, amma bai juyoba.

 Sameer wai mike damun kankane haka? da zaka ringa wasa da rayuwar yaranka da kanka? .

Lips d'insa ya ciza, ya juyo yana kallonta, amma ita bata ganin idanunsa saboda hular ta rufe, murmushin takaici yayi, yace,  Ni ba wasa da rayuwarsu nakeba aunty Mimi, komai kikaga nayi nasan abinda nakeyi, zuwa nangaba kad'an kuma zaku fahimci komai .

 ALLAH yasa to, amma ni yanzu na zone muyi maganar komawar Munaya gida kafin mu wuce goben, tunda jirgin rana zamubi .

Agogon hannunsa ya kalla, yace,  yanzu kam inada uzirin fita? .

 fita? Inakuma zakaje a wannan daren? .

Batareda ya tanka mataba yajuya yakama hanyar fita, saida yaje bakin k'ofa sannan yace,  Farauta . yay ficewarsa.



Kasa motsi aunty Mimi tayi a wajen, sai maimaita Sunan Galadima kawai takeyi akan la66anta.





******



Tacan baya yabi shikam, hanyar akwai k'arancin mutane sosai, yana zuwa ta wani waje yagamu da wani Wanda ke sanye da irin kayan hadiman masarautar, rissinawa yay yabashi keys d'in mota. ya kar6a batareda sunma juna maganaba ya wuce.

Can sashen su Harun naga ya nufa, dukda tazarar dake tsakaninsu baiji tafiyarba, motar dake fake a wajen ya bud'e ya shiga ya zauna, zamansa da mintuna uku Harun yafito ad'an hanzarce, motar yabud'e seat d'in baya ya shiga ya zauna, cikin bada Umarni yace, lawandi muje, kasan d'an bala'innan yanada securitys dake kaimasa rahoto .

Murmuahin gefen baki Galadima yayi yatada motar yafice daga masarautar................
'<���









 Hummmm! Reader's harna sauke numfashi, babbar magana, yau dai ga Galadima ga Harun, sauran abinda zai faru kuma sai a buk 3 na raina kama .

Miya faru da Abdurrahman lokacin da Sauban ya kaisa sashen gimbiya zulfah ne>��? Yaya batun kama SD?, wad'anne sarakuna ne Galadima yake zargi? Kodai dama can Galadima yasan wanene Harun yabashi damane kawai?>��, Yaya batun warkewar Abie da Auren Contract tsakanin Galadima da Munaya?, mi suke shiryawa itada Momma da suka damu da zuwanta wankan gida? Ko Galadima zai amince? .



Yaya batun gano asalin innarsu Munaya? Da ita Munayar ta d'auki alwashi?.



Tofa wannan amsar dai duk zatazo a littafi na 3 kuma na k'arshe da izinin ubangiji, dukkan wasu tambayoyinku amsarku na cikinsa, zan had'a muku da albishirin zan dingayi a weekend rana 1, kodai asabar ko lahadi, kowacce rana nasamu dama aciki, dan buk 3 inason kammalashi ne a gaggauce saboda uzirin danake dashi insha ALLAH.



Ngd sosai da had'in kan da kuke bani, muje zuwa my guys�&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&>�p�>�p�>�p�>�p�>�p�>�p�=�
�=�
�=�
�=�
�=�
�=�
�d'd'd'.





Barkanku da juma'a=�K�<���.



Musha weekend lafiya�&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&













*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*=�-�=�O�<���

*_typing=���_*





=ء� *_HASKE WRITERS ASSO....._*





*_f&RAINA KAMA.....!!f&_*

_(Kaga gayya)_







*_Bilyn Abdull ce>��<���_*

__________________________



*_Kai jama'a yau dai kun Sani typing dole saboda munafurcin y'an bani Na iya, wannan karon kuma kurasa k'ullin da zakuyi sai akan Uwa da 'Diya?, nikam yau koda mamana (mamu gee) kwaikwayar RAINA KAMA tayi to wlhy birgeni zatayi, ai baiwace ma wani yayi Abu kabishi daki-daki kana kwaikwayo. Irin wannan shirmen naku baya cikin kan Bily, ba mamu gee ba koda watace aka jingina da hakan bazanji komaiba wlhy, sannanma nifa abinda yabani mamaki a writeup d'in da mamana tayi bata ambaci sunan RAINA KAMA ba aciki ko wani littafi daban, to tayaya y'an bani Na iya da tsugunne-tsugunne su anasu writeup d'in suka saka sunan RAINA KAMA? (Wlhy halin wasu daga cikin writers namu ko kad'an bashida k'yau, neman sunane kokuwa son asanine niban saniba>�&�<���
@&)._*

_Reader's kuma da naku, sometimes bakunanku basuda linzami, irin wannan abubuwan kune ke fara tsirarsu saisuzo kuma su buwayeku, Ku ke karanta RAINA KAMA DA TARAYYA Ku kusan banbancin abinda ke cikin kowanne, amma dayake Ku irin wannan dama shine farin cikinku saikuyita k'irk'irar abinda dolene daga k'arshe saiya zama rikici, to nikam zan sanar muku, awanan karon sai had'in naku baiyiba, Dan MAMU GEE DA BILYN ABDUL duk Abu d'ayane, daga tarayya har Raina kama buks d'inmu ne, mu muke rubuta abunmu, babu wata munafukar writer ko reader da mukayi shawara da ita kafin mu d'aura alk'alaminmu a takarda, masu had'a husuma kuma sai kusha fetur Ku had'iyi ashana kuyi bombing d'in kanku, ina dai shikenan ko?=�E�<���_.

*Daga k'arshe inamai muku nasiha da kuji tsoron ALLAH, wlhy bashin naira 10 kacal yana hana bawa kwanciyar kabari, karo tsakanin rago da rago kawai akwai hisabi tsakaninsu, aranar kiyama bayan an tsaya hisabi duk Wanda kasani koya sanka saika Ganshi kakuma ganeshi, bawai kaitsaye za tantanceka akaika wuta ko aljanna ba, wlhy sai an tsidaka, ancire hak'in mutane a kanka, ka zagi wane babu hak'k'insa, ka harari wane, kama wane zind'e, ka cinye kud'in wane, ka had'a fad'a tsakanin wane, ka 6ata sunan wane, ka cuci makwafcin, ka...ka...ka...da yawan gaske, duk wani cin amana ko zalunci dakama wani inhar bai yafe makaba a wannan ranar sai an cire masa hak'insa a cikin ayyukanka, (Dan sune kad'ai guzirinka) komai tarin aikin alkairin daka tara inhar kanada irin wad'annan bashishshikan d'aya bayan d'aya sai an zaresu daga gareka, koda dabba da kafiri ka zalunta kuwa, idan dama bakada komai, sai ayita kwashe nasu zunubai ana lafta maka, sai angama tas, kabiya an biyaka saikuma a gwada ayyukanka a kan mizani, miyarage kuma? Saika koma gefe jiran sakamako. Wlhy y'an uwa babu babban tashin hankali irin kar6ar sakamako, a wannan lokacin uba baya gane d'ansa, y'a bata gane uwarta, miji baya gane matarsa saboda tsantsar tashin hankalin da ake ciki, da wane hannu xaka amsa, ina ne zaizama mazauni Na dindindin, duk baka saniba, haba y'ar uwata, kinada wannan babban aiki a gabanki amma kika shagala wajen had'a husuma irin ta social media wadda bansanki ba, baki sanniba, maybe ma har Abadan bazamu ta6a sanin junanmu ba, muji tsoron ALLAH wlhy, yakamata irin wannan abubuwan su tsaya hakanan, daga ni har mamana badan Neman suna mukeba, domin Isar da sak'o mukeyi a cikin tarayya da raina kama, burinmu kuma ko mutum d'aya ya amfanu da manufarmu ya wadatar, bawai tarin masu karantawa ba, ni miyasa babu Wanda yata6a tarata yacemin tarayya copy d'in raina kama ne? to Ku kama kanku please, kodan tsoron ALLAH.*



_My Sweet mah-mah mamu gee wannan page d'in sadaukarwane a gareki, kiyi yadda kikeso dashi nabaki, ALLAH yabarmu tare, I love you irin trillions d'innan, kisamun albarka nakuma zama gagara badau=��=��._



Bilyn Abdull & Mamu gee RAINA KAMA ne mu, sannan munyi TARAYYA NE akan Isar da sak'o mai muhimmanci, mabiyanmu Na gaskiya a KAFTA kawai�&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&=��=�M�<���.



HARUN da GALADIMA kuma Ku KAFTA naku wasan>�#�>�#�>�#�>�8�<���
@&>�8�<���
@&
'<���=��.

__________________________





~Book 3~ =�I�<���1� �'2�





...............Saida suka fara tafiya sai Harun yafara jin tamkar k'amshin turaren Galadima yakeji, mamaki ya kamasa, ya kalli gaban motar yana fad'in  lawwali nikam kaji minakeji kuwa? k'amshin Sameer fa .

Murmushi Galadima yayi, baice komaiba sai  Uhmm .

Hakan yakuma d'aure kan Harun, kamar zai sake magana saiya fasa, ya d'auki wayarsa domin son kira yaji ina Galadima, yasan Abu dolene ke fiddashi da daddare daga masarauta, amma sai kira ya shigo a wayarsa, k'aramin tsaki yayi Dan ba'a ko'ina yake d'aga wayaba, ya yarda da lawwali drivern babansa waziri amma bakomai yake barin ya saniba, ganinfa an damesa da kiran saiya d'aga. Da sauri ya janye wayar a kunnensa yana lek'o kansa gaban motar danya tabbatar. shin ina tunaninsa ya tafi dahar ya iya gaza banbance lawwali da Sameer?.

yace  Sameer! .

Galadima dake tuk'insa hankali kwance yana kuma sauraren wayar Harun ta abinda yasa akunne, saboda ya saita duk wayar dazata shiga ta Fita a war Harun saiya shigo wayarsa shima kota fita yace,  Uhmyim .

A tsorace Harun yakoma baya ya bigi seat da k'arfi, babu abinda zuciyarsa keyi sai dukan 100-100, wayarsa ya jawo jiki Na rawa yafara k'ok'arin kiran wani.

Galadima yay murmushi, cike da izzar k'asaita yace,  bar wahal da kanka my dear friend, duk wata waya dazaka kira a yanzu wayata zata shiga .

Harun yay jifa da wayarsa a kujera jiki yana rawa, batare da wani tunaniba ya mik'e kawai ya shak'e Galadima, da hannu d'aya Galadima yake driving, hannu d'aya kuma yana k'ok'arin kare kansa daga shak'ar da Harun ya masa.

Da k'yar yasamu ya gangara gefen titi, yasaka hannunsa d'aya ya bigi gefen cikin Harun daya samu damar shak'esa da k'yau, Dan numfashin sa harya fara fita afisge.

Dukan cikinsa da Galadima yayi yasakashi sakinsa da sauri, Galadima ya juya yakuma naushin bakin Harun saiga jini, dama bai gama dawowa hayyacinsa ba daga dukan cikinsa da yayi.

Harun ya fad'a saman kujera yana rik'e ciki da shafar hancinsa dayaji yana yoyo, kallon hannunsa yayi saiyaga jini, ya zaro ido cikin matuk'ar mamakin shi Sameer ya fasama baki, yo ko danbe zasuyi ai babu abin zai d'auka a jikinsa, (Dan shima Harun d'infa ba bayaba).

Galadima daketa huci ya dafe sitiyari da kife kansa ya kuma tada motar a harzuk'e ya fara tafiya cikin tsananin gudu.

Cikin hakki da fidda numfashi a wahalce Harun yace  Sameer n..n..ni ka daka? harda fidda jini? .

Banza Galadima yamasa yacigaba da tuk'insa, Harun ya kuma yunk'urawa zai tashi amma saiya kasa, saboda ba k'aramin duka Galadima ya masa a gefen cikiba, wajen ya k'ulle, dole ya koma ya kwanta yana cije baki da matse ido, hannunsa rik'e da wajen har yanzu.



Suna isa inda ya nufa yay horn, saiga Nuren da kansa yazo ya bud'e masa k'ofa, a fusace ya shiga gidan, shi Nuren ma har yana tsorata.

Yana tsaida motar ko kashewa baiyiba yabud'e ya fito a harzuk'e, inda Harun yake ya bud'e ya jawoshi, yakuma kai masa naushi, shima ya kai masa dukda azabarda cikinsa ke masa.

Nuren da Muftahu sun iso wajen a hanzarce, Dan ganin danbe Na Neman hark'ewa tsakanin aminai guda biyu, Nuren yaja Harun, shikuma Muftahu Galadima.

 Waishin mikukeyi ne haka brother? Da girmanku da ajinku kuke danbe? danbe fa? Wannan wane irin kuma abin kunyane? Lallai da y'an jarida zasu samu labari gobe dasunci kasuwa sosai.....

Hankad'a Muftahu Galadima yayi baya, yay taga-taga zai fad'i, bai kuma kallon ko wanne a cikinsuba ya nuna Harun da d'an yatsa,  Mara kwakwalwa kawai, kafin ni ka kasheni ninan zan kasheka daga kai har munafikin ubanka, dak'ik'i kawai . yana gama fad'ar haka yabar wajen zuwa cikin gida, taku yake kamar wani bajimi ya fito za6en sarauniyar k'yau.

Daga Nuren har Muftahu da kallon mamaki suka bisa, shi kansa Harun maganar Galadima tasakashi girgiza, kardai guy d'innan yana sane da wanene ni tun tuni amma ya k'yaleni? da k'arfi ya fisge shima daga jikin Nuren yana kaima Muftahu duka,  Munafiki dakai zan fara .

Saurin kare kansa Muftahu yayi, Nuren yakuma yunk'urin rik'e Harun, danshifa abin yafara d'aure kansa, kowa yasan Harun aminin Galadima ne Na kusa, yau kuma miya had'osu haka? harda zancen kisa? Galadima yanada matuk'ar zuciya, idan ransa ya 6aci babu ubanda ke gane kansa....

Fad'a dai Neman komawa yay ga Muftahu, saida su Ameer sukazo suka rirrik'e Harun, cak suka d'aukesa yana fisge-fisge da fad'ama Muftahu magana suka shiga dashi ciki.

Nuren ya kalli Muftahu dake murmushi yana gyaran kwalar rigarsa.

 Amma mike faruwa kuma haka? Yau Sameer ne ke fad'a da Harun? .

Muftahu ya dafa kafad'ar Nuren,  'Dan uwa akwai abinda baka Sani bane, amma Na tabbatar yanzu zama sanshi . Yana gama fad'ar haka yayi gaba abinsa, shima da kallon Nuren ya bisa, kenan shima yasan dalilin fad'an nasu ashe? jiki a sanyaye ya nufi wajen motar ya kashe sannan ya nufi gidan shima, a yanzu kam lamarin wanan case yafara rud'ar dashi, dan yanda Sameer keta abubuwa a tsakaninnan basuyi kama da nasa zarginba shi.

Galadima Na kwance cikin kujera doguwa, tunda ya shigo anan yazufe, duk yanda zuciyarsa taso 6aci sai kalaman Munaya su danne su (mata kunga amfanin hikimar zance ga mazajenmu ko), zantuttukanta suka shiga dawo masa a rai daki-daki, tabbas a yanzu ba fushinsa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login