Showing 207001 words to 210000 words out of 365757 words

Chapter 70 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1531

wasu sa'ointane a wajen? .

Uffan mama Fulani batace masaba, sai wani k'asaitaccen murmushi datayi tana kallon amintacciyar baiwarta, alamu tamata da ido na ta tambayi mi dattijuwar tazo dashi?.domin itace dama mai kawo ma mama Fulani duk wata gulma takowane 6angare a masarautar, Dan ita babu sashen dabata da 'yan lek'en asiri, kuma wannan dattijuwar baiwa itace shugabarsu, komai suka tattaro ita zasu fad'awa ita kuma takawo ga mama Fulani.

 mike faruwa tulluwa? . Amintacciyar baiwar mama Fulani ta fad'a tana kallon dattijuwa tulluwa dahar yanzu jikinta baibar 6ariba.

 Ranki ya dad'e ki gafarceni da abinda nazo fad'a, banida za6in daya wuce hakan, domin da kiji a bakin wasu gara kifara ji abakina danki tabbatar nasan aikina .

Mama Fulani ta hura hanci, yayinda izzarta ta k'aru, sosai ta tashi zaune idonta akan tulluwa.

Batareda tace uffanba tulluwa tacigaba da magana, Dan tasan ma'anar kallon ta cigaba da magana kenan.

 ranki ya dad'e yanzunnan labarin haihuwar matar Galadima ta iso wannan masarauta, ba haihuwar baceba abin girgiza abinda ta haifanne, idan kinbani izini sai na fad'a uwar gijiyata .

Wani kakkauran yayu mama Fulani ta had'iye, Wambai daya cika yay fam da haushin wannan shegiyar baiwar ya Dalla mata harara,  dalla malama kifad'a kinwani zauna cancana magana kamar wata zuma .

 ALLAH ya huci zuciyarka ranka ya dad'e, maganarce tanada nauyi. dama labari ya iso ta haifi yara uku ne maza biyu mace d'aya....

Wambai yay masifar razana harda mik'ewa, mama Fulani kam ko motsi batayiba, sai wani k'ayataccen murmushi na k'asaitattun mata masu izza da mulki tayi, ta d'ago ido ta kalli Wambai cikin harara tace  kai kuma miye na mik'ewar? .

Tunawa yay akwai kuyangi saiya saki murmushi basarwa, yace  mamaki mana Granny, 'ya'ya uku fa a 1 time, dolene na taya d'an uwana murna ai . bai jira cewarta ba yafice da hanzari.

Lumshe idanu mama Fulani tayi bayan Wambai ya 6acema ganinta, ta kalli amintacciyar baiwarta fuska d'auke da murmushi nan tace araba k'yaututtuka, takuma sallami kowa.



K'yaututtukan da mama Fulani tasaka a rabama bayin gidan yasaka zancen haihuwar munaya yakuma karad'e lungu da sak'o na masarautar, masu murna nayi masu kuka nayi, dan kowa dai yasan magadan masarautar gagara badau sun iso, tunda kowa yasan Galadima ne magaji mai jiran gado, _(karku manta haryanzu sarkin yanzu sarautarsa ta ruk'on kwaryace, Dan mahaifin Galadima tsohon Sarki bawai mutuwa yayiba, sannan ba murabus yayi da kansa yace yabarma Sarki na yanzu sarautarba, so sarautar ruk'on k'warya yakeyi, kuma ko a yanzu tsohon Sarki yasamu lafiya dolene ya sauka yabashi kujerarsa, mai guri yazo kenan, mai tabarma dolensa ya nad'e>�7�<���
@&)_.





**************



A 6angaren gidansu Munaya ma bata canja zaniba, Dan hassada k'ararace tafito a fuskokinsu da matuk'ar razanuwa, kenan arana d'aya Innarsu munaya ta wayi gari da jikoki 5 kenan? miyasa a komai sai Ai'sha ta fisu ne? bayan kuma sun fita gata sun fita dukiya, sukeda dangi da tarin 'ya'ya a gari, suke da ilimin zamani, k'asarsu ce ba karoro sukazoba?.

Innaro kam dai tadage sai zuba gud'a take da taka rawa, gud'artace ma ta ankarar da jama'ar anguwar mi ake ciki, dandanan aka cika mata gida ana tayata murna.

Babu kunya tasaka Shu'aibu ya kaita asibitin, bayan kwanakin munubiya biyu akan gwiwa kuma tasani amma bata ta6a nuna sha'awar zuwa dubata asibitin ba ma.=��





***************



Tunda kuyanginta suka fice tamik'e zaram itama, safa da marwa tafarayi na tsantsar tashin hankali a makeken falonta daya gama jin kayan alatu tamkar bana tsohuwa ba, zufa dukta jik'eta sharkaf, sai kuma maimaita fad'in  y'a'ya uku? Y'ay'a uku fa? wannan 'yar yarinyar ta haifa y'ay'a uku?, kai banma yardaba gaskiya, kodai k'aryane basuji d'ai-daibane?. jikinta na rawa ta jawo wayarta tayi Kiran Momma.

Momma dake cikin tsantsar farinciki saboda isowar labarin haihuwar jikokinta sabbi fil a Leda har uku, ta d'aga kiran mama Fulani.

A mutunce ta gaisheta kamar yanda ta saba koyaushe.

Mama Fulani bata amsaba, sai tambaya data jehoma Momma,  Zeenah ashe matar d'anki ta haihu? Amma aka kasa sanarmin sai dai naji a jita-jita? .

Murmushi momma tayi, tace,  ranki ya dad'e a gafarceni, amma Nima yanzunnanma nakeji, dan suna isowa Nigeria tafara nak'uda tun a mota .

Cikeda mamaki mama Fulani tace,  yo a ina ta haihun? .

 anan Nigeria ne ai mama .

 Ai nazata anan India ne shiyyasa na kira, to ALLAH ya raya, bara nasa a bincikan asibitin . bata jira cewar Momma ba ta yanke wayar, murmushi kawai Momma tayi tana girgiza kai, ta k'agara Abie ya tashi a barci ta guntsa masa wannan daddad'an labari.



Saman kujera mama Fulani ta jefa wayarta tana cije la66anta da sakin wata k'aramar k'ara hawaye na zubo mata, ita kuma tata ta k'are, Matawalle ya dace da haihuwar wad'annan 'ya'yan ba Galadima ba, dolene tanemo mafita da gaggawa kafin lokaci ya k'ure mata.



>�#�>�#�>�t�



&&&&&&&&&&





Kiran Momma daya shigo a wayar Muftahu ya saka shi mik'ama Galadima, dama shiya kirata ya Sanar mata haihuwar, ganin haka ta kirashi danya had'ata da Galadima, tunda taga suna tare.

Hakkanne yasaka Galadima fitowa harabar asibitin yana amsa mata, cikeda tsantsar farin ciki suka shiga taya juna murna, ya tambayi ina Abie, ta Sanar masa yana barcine.

Momma tace,  an sallamekune? .

 a'a Momma, har yanzu suduka barcima suke, gashi magriba ma ta gabato anan, banama zaton sallamarnan yau, maybe sai zuwa safiya .

Ajiyar zuciya momma ta sauke, tace,  to Muh'd yau fa barci bai gankaba, dolene idonka yazama abud'e tundaga kan doctors, Nurse's, da makusantanka, hankalin duk wani idon mak'iyinka yanzu akan wad'annan bayin ALLAH guda uku yake, sunsan shine kawai tarko mafi tsauri dazasu maka a yanzu, su zaituna suna hanya itada kuyangi 5 amintatu da zasu zauna daku, itama Zaitun (mom) bazata komaba sai anyi suna, anayin suna kuma Munaya zata koma gidansu tayi wanka irin na al'ada da kowa ya Sani, tunda kasan dokar masarautar taku kenan. Wannan kawai shine mafita .

Ajiyar zuciya Galadima ya sauke, muryarsa cike da damuwa yace,  insha ALLAH Momma duk za'ayi hakan, amma zama gidan nasu bak'ya ganinsa kamar had'ari? tunda za'a iya tsutar dasu a can, dan babu wani tsaro .

Murmushi Momma tayi har Galadima najin sautinsa, tace,  nasan abinda nakeyi ai Muh'd, bazance aturasu canba nasan zasu cutu, kaidai kawai kayi hakan, sauran bayani saika dawo zakaji komai, su zaitun nasan suna gab da isowa insha ALLAH. Papi ma yace yakira wayarka bata shigoba daga kai har Haneefa .

 tab, yoni Momma ai banmazo da waya ko d'aya ba wlhy, duk nan na mantasu a mota, kima saka khumar ya kawo miki, saidai zuwa Safiya nasamu k'arama na r'ik'e .

 to shikenan, dama haka nafad'a masa nima maybe kabar wayoyin anan, idan ta farka dai a kirani naji muryar d'iyata nima, konaji sanyi .

Murmushi Galadima yayi yace  insha ALLAH Momma .



Koda wayar ta yanke saiyayta juya maganganun momma a ransa yana musu fashin bak'i d'ai-d'ai. Haka ya koma zuwa cikin asibitin, dan anfara addabarsa da kallo, shi saiya rasama mi suke kallon? Shidai bayasha banban da sauran halitta bane, bakuma za'a kallesa ace ba bak'in fata bane, bakuma wasu kayan ado na musamman ya sakaba, hasalima k'yank'yamin kayan jikinsa yakeyi, dan sun kwana suna Neman yini a jikinsa, (tunda ba time d'inmu d'aya da India ba) yaja guntun tsaki yana k'arasawa ciki ya mik'ama Muftahu wayarsa.





***********



Sai bayan isha'i su mom suka iso, dan basu sami jirgi da wuri ba, a lokacin jama'ar gidansu Munaya suna asibitin, masu kukan zuci nayi masu murna da gaskiya nayi, hakama a wasu daga masarauta suna nan, wasu lek'en asiri kawai aka turosu, wasu ko na taya farincikine da tabbatarwa.

Yau dai yan gidansu Munaya suna kallon abin mamaki, da gaske dai inna Ai'sha tamusu fintinkau irinna jirgi, saidai hange daga nesa da harara cikin duhu.

Mom bakinta yak'i rufuwa, harda rungume Galadima, Nuren kuwa hardasu taka rawa>�#�, Muftahu na masa lik'i.

Mutane abin ya birgesu, Galadima yay murmushi yana d'an dukan kafad'ar Nuren da Muftahu kawai.

Su Munubiya basu farkaba har sannan, doctors sunce babu wata Matsala, a barsu su huta sosai yanda zasu tashi da kwarinsu zuwa Safiya.



Dole dai Galadima yasa aka zuba police a asibitinan ranar, sauran kuma anbarma UBANGINJIN TALIKAI dake kallon motsin kowa.

Masu tafiya duk suka tafi, aka bar masu kwana kawai.

Galadima da ya dage anan zai kwana shima, da k'yar dai mom ta lalla6ashi ya tafi gida kodan yasamu yad'an huta, kallo d'aya zaka masa ka gane a matuk'ar gajiye yake, jijiyoyin Kansa sunyi rad'a-rad'a, ga yunwa waddama ya manta da ita da alama.

Wannan dare dai ya kwana rayashi da bautar ALLAH ne da godiya mai yawan gaske.





Innarsu Munaya ma dai kuka sosai tasha na dad'i, itama haka ta raya wannan dare, hakama Abba, shima yamik'a godiyarsa ga ALLAH dan lokacin dayake buri da tanadi ya cika, koba komai zai sauke nauyin dake rataye a wuyansa insha ALLAH.



Washe gari...............>�)�
'<���







*_media ko bala'i, kayi turanci a novel ace ka cika iyayi da son asan ka iya turanci>�&�<���
@&, muda muke koyo muyi ace bamusan abinda mukeba>�&�<���
@&, kai jama'a babu mai iyama 'yan social media sai ALLAH, ko uwarka ka yanka kagasa tasha mai kwallan tana d'iga, da wani yagama ci zaice bataji gishiri ba=�D�, ALLAH ya shiryar damu muda bakunanmu dai.=�O�<���._*







_Ayshan sadiq sak'onki ya iso gareni, nakuma gode kwarai da gaske, saidai ina mai baki hak'uri da sauran fans d'ina, a gaskiya weekend d'inan ina muhimman abubuwane a cikinsa, bazan iya alk'awarin typing ba, sannan ni kaina idanuna =�A�=�A�da Brain >��� d'ina suna buk'atar hutu, inada aure, akwai wasu hak'k'oki a kaina bana typing kawai ba, kunga yadace suma na basu lokacina, dan Ku gamsu nake zaman yin typing mai tsawo, insha ALLAH idan mukai hak'uri kamar yaune raina kama zaizo k'arshe abarma yayinsa Ku manta dashi saikuma wasu dazasu 6ullo daga sauran writers namu, dan haka muringa hak'uri da abinda ALLAH ya k'addara namu a lokacin da ya tsara, kar muyi gaggawa domin aikin shaid'ance, nima Ku duba nawa buk'atun amatsayina na mutum kuma mace mai rataye da igiyar auren. Ina godiya kwarai da gaske da k'aunar da kuke nunama wannan buk, bammasan yanda zan nuna muku farincikina ba kusan inajin dad'in Comments naku nima, amma ina sonku irin sosai d'inan a raina, kumuje zuwa guys, duk Nisan jifa k'asa zai fad'o=�N�<���_





I love you mazga-mazga all.=��=��>�p�>�p�=�
�=�
�=�
�>��<���.







Ayshan sadiq, ina miki fatan alkairi a duk Inda kike=��=��=��=��>��<���.

















*_ALLAH ka gafarma iyayenmu_*=�O�<���=�-�

[7/9, 11:05 AM] d'y'ar K'asad': *_typing=���_*





=ء� *_HASKE WRITERS ASSO....._*





*_f&RAINA KAMA.....!!f&_*

_(Kaga gayya)_







*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







~Book 2~ =�I�<���2� 3�





...............Koda Muftahu ya sauke Galadima saiya sake shiri Yakoma asibitin, tunda ya shigo idon Nuren a kansa, sai mamaki ya kamasa, shin miya maido Muftahu asibitin? bayan kuma tare suka tafi da Galadima.

Bai masa maganaba dan karma yasan ya gansa, saiya saka ido a dukkan wani motsin Muftahu d'in, shidai Muftahu baisan yanayiba, dan baima je d'akinda su Munaya sukeba, sai zagaye-zagaye dayaketa famanyi har ALLAH ya wayi gari lafiya.

Wannan lamarifa ya zaune a zuciyar Nuren yanata kaikawo, anya kuwa ba suna zargine akan abinda ba haka yakeba?, dukda jami'an tsaro dake wajen Muftahu Nada damar aiwatar dadukkan abinda yay k'uduri tunda kowa namasa kallon makusancin Galadima, amma har ALLAH ya wayi gari baimayi wani yunk'uri na shiga d'akinba balle alamun rashin gaskiya, saima aikinsa dayay kama dana mai k'ok'arin bama wani abu kariya,  ya ALLAH ka warware wannan lamari cikin sauk'i kodan wannan bawa naka yasamu nutsuwa shima . Nuren ya fad'a a fili yana d'aga hannayensa sama alamar rok'o.

Muftahu dake kallonsa yay murmushi yana amsawa da amin a la66ansa, daga nan yafice abinsa ya koma masarauta, saboda anata kiraye-kirayen sallar asubahi





****************



Misalin 7:30am Munaya ta farka, kamar a kunnen Munubiya itama saita farka, su mom dake d'akin suka shiga musu sannu, cikin tsantsar farin cikin farkawar tasu, dandanan aka kira doctor.

Alhmdllh babu wata matsala a tattare dasu, aka kikkimtsasu dagasu har yaran daketa barci irinna jinjirai, daga Munu... Har munaya dai kallon y'ay'a biyar sukeyi, amma tunaninsu ko cikin y'ay'an y'an uwansune.

Doctor Farida data lura da hakan tayi murmushi kawai. umarni tabama Nurses d'in abama kowa nata, kallon kallo akeyi tsakanin Munaya da Munubiya, amma kowa bakinsa yagaza furta komi, saisu kalli juna sukuma kalli jariran gabansu.

Doctor Farida dai dataga basuda niyyar d'aukar yaran tace  y'an biyu wannan itace k'yautar da ALLAH ya baku, Munubiya 2, Munaya 3.

Duk waro ido sukayi, Dan Na Munaya ne yabasu mamaki, tunda dukansu sunsan Na Munubiya dama.

Munubiya ta sakko daga gadonta batareda ta d'auki ko d'a d'aya anata ba, gadon Munaya ta nufo, ta durk'usa k'asa tana rungumo yaran, ga hawaye ga dariya tanayi, saikace sokuwa.

Munaya ma dai batabi takan nata d'inba, saita nufi Na Munubiya ta d'auka duk ta sakasu a jikinta, k'aunarsu Na ratsa dukkan 6argonta kamar yanda take k'aunar mahaifiyarsu.

Galadima da Yaa marwan dake tsaye a bakin k'ofa suka kalli juna suna murmushi, kowanne yana mamaki a ransa, anacewa y'an biyu akwai shak'uwa, sukam suna mamakin ta wad'annan Matan nasu, soyayyar dake tsakaninsu tanada ban mamaki da birgewa.

Galadima ya k'arasa ga Munaya da har yanzu take a tsaye idonta arufe y'an biyun Munubiya na jikinta, had'ata yay itada yaran ya rungume.

A firgice tabud'e ido, saitaji k'amshin turarensa, tayi baya kad'an yay saurin ruk'ota. Idonsa ya saka cikin nata yana wani murmushin dabata ta6a ganiba daga garesa. Ahankali ya furta haba  Maman y'an biyar a hankali mana .

K'aramar harara ta sakar masa, ya saka k'aramar dariyar da tadawo da Yaa marwan daga duniyar daya tafi=�3�, danshifa mutunmin naku har yana Neman sakin layi>�-�>�s�.



Mom dake bayansu tayi gyaran murya, kowa saiyaja baya daga jikin matarsa>�#�, suna wani susar k'eya.

Munubiya da Munaya sai suka koma kusa da juna, Munaya ta kama hannun Munubiya a cikin nata. ita mom dariyama suka bata, Dan haka tad'an dara tana fad'in  An sallamemu to yanzu ya za'ayi? .

Munubiya da Munaya suka kalli juna, da alama dai basa buk'atar rabuwa, sudai su Galadima kallonsu suke kawai.

Ganinfa zasuyi daru sai mom tai murmushi, da ido taima Galadima da Yaa marwan magana akan su fita.

Babu musu suka fice, itakuma takama hannun Munaya da Munubiya ta zaunar a bakin gado. Magana take musu k'asa-k'asa wadda (banajin=�D�).

Sai naga duk sunyi murmushi suna 6oye fuska. Itama murmushin tayi tana saka musu albarka. Dan murmushin nasu ya tabbatar mata dasun amince.



Daga nanfa shiri aka fara, kowacce aka had'a mata kayanta da y'ay'anta.

Gayyar gidansu Munubiya su mama Rabi'a suka kwashi nasu, nasu Galadima ma haka.

Manne da hannun juna suka fito, mutane sai kallonau sukeyi abin sha'awa da birgewa. Harda masu musu hotuna daga gefe..

Su doctor Farida ma saida suka matso akayi musu hoto danya zama acikin tarihin wannan asibiti.

Saida Munubiya ta saka munaya a mota sannan takona tashiga wajen mijinta itama, kowanne Na share hawaye, ba'a San ransu za'a rabasuba.





Saikace wad'anda za'a raba gaba d'aya>�#�, kai ALLAH yabamu 'yan biyu=���&<���
@&�&<���
@&.







&&&&&&&&&&&&





Tarba ta musamman su Munaya suka samu a masarauta, harma abin yaso basu mamaki, hakan dai baisa Mom tayi sake da yaran ba, duk wani motsi dai idonta Na Kansu, an musu rakkiya har sashensu dayasha gyara, yayinda Galadima keta kar6ar barka ga ahalin wannan masarauta, tun daga hadimai zuwa y'an uwansa na jini, maza da mata yaro da babba.

Za'ayi walimar cin abinda data


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login