Showing 321001 words to 324000 words out of 365757 words

Chapter 108 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1495

ciki yana murzawa da wani salo, juyawa nayi Na kallesa muka had'a ido, idanunsa duksun wani k'ank'ance, ya sark'e nawa yanda nakasa koda motsi balle samun damar janyewa, akan la66ansa yace,  I miss you .

 Humm nafad'a nima a hankali INA kauda kaina gefe.

Hannunsa ya sak'alo ta bayan wuyana ya matso da fuskata dab da tashi, numfashinmu Na had'uwa waje d'aya, kasa jurar kallonsa nayi saina lumshe idonuna Na bamik'a masa wuya 100%, yayi duk yanda yakeso, dan da gaske missing d'in nawa mai yawa Nagano cikin kwayoyin idanunsa.



Da sauri yarima Issufu da Yaa Marwan suka koma baya, dan dama suna tare da shine aka aiko kiransu, sunata sauri su dawo dan karsu barshi cikin kad'aici, ashema yana tare da matarsa. Sunyi sallama takai 6 jin ba'a amsaba sukayi tunanin kobaijibane, shiyyasa suka shigo Kansu tsaye, dan basuyi zaton samunsa da kowaba, ALLAH ma ya sosu k'aramin gani sukayi>�-�=��.



Yareema Isaufu da mamaki ya kasheshi ya kalli Yaa Marwan yana fad'in,  wai dama duk yarannan masu kama da juna sunada aure? .

Murmushi Yaa Marwan yayi, ya dafa kafad'arsa,  biyu sunada aure mana, su tagwayene, ina auren Hasaanar, shikuma Yarima Sameer yana auren Hussaina, d'ayar itace bata da aure, dan nasan Ayusher kake nufi, tunda Feena bata kaisu girma da shekaruba, amma miyasa kamin wannan tambayar? .

Yareema Issufu yay k'aramar dariya yana cewa  zan sanar maka amma ba yanzunba, saida safe Na banbancesu .

Komai Yaa Marwan baiceba yay murmushi kawai suka cigaba da tafiya.





Mukan bama musan sun shigoba balle fitarsu, motsawar da Abdurrahman yayi yana k'ananun kukane yasamu dai-daita, duk muka kalli inda suke.

Matsawa Galadima yayi inda suke dan sunfi kusa dashi, Ashe showal d'inne ya rufe masa hanci, ya gyara masa sannan ya juyo ya kalleni yana murmushi.

K'asa nayi da kaina nima ina murmushin. Nace,  Ina yini? Kazo lafiya? .

 Kin fita daga mamakin yanzu dai kenan? . Yay maganar tamkar bayaso.

Nanma Murmusawa nayi ina 6oye fuskata.

 Humm . Ya fad'a yana gyara zama.

 Kayannan sun miki k'yau gaskiya my mata .

Nad'an d'ago ina fad'in,  Da gaske? .

Ido d'aya ya kashemin yana cizar lips.

Nima Na juya idanuna cikeda salo.

Har cikin ransa saida yaji wannan sak'on. Na katse masa tunanin da fad'in  Ya jikin Abie? .

Zamansa ya gyara sosai, ya d'auki butar shayin zai zuba nai saurin d'aura hannuna akan nasa ina girgiza kai.  Aikin ai nawane yalla6ai .

Murmusawa yayi yana sakarmin. Nima Na zuba masa fuskata d'auke da Murmushi, Na mik'a masa.

Cikin lumshe idanu yace,  Thanks .

Kaina Na jinjina masa kawai, a nutse ya shiga bani labarin dukkan abinda ya faru, harda tsadar allurai da drugs d'in da Abie kesha, ya k'are maganar da fad'in ammafa Alhmdllh, bazan baki labarin komaiba sai kinje kinganema idonki yanda Abie yake yanzu, banta6a tafiya mai cike da nutsuwa ba irinta wannan karon, dan nasan nabaro farin ciki ne zan kuma iske farin ciki, lallai Na yarda da zancenki, HAK'URI shike bada komai, duk saurin Bawa saiya jirayi UBANGIJI, dan shine mai kowa da komai, a watanni biyu kacal da suka shud'e ganinake komai ma bazai zoba balle ya wuce, amma gashi harya zama labari, wataran muma masu bada labarin nemarmu za'ayi a rasa, mun shud'e saidai bayanmu, ALLAH ka rabamu da SON ZUCIYA, dan k'arshedai 6ACINTA, Ko'a yanzu akace babu Muhammad Sameer to naci ribar rayuwa, dan burina nason ganin mak'iyan mahaifina ya cika, Abie yasamu sauk'i, ga yarana, Na mallaki jarumar mace kamila Mumina wadda Na mallakama dukkan kaina da ZUCIYATA, To nikam minene ya ragemin kuma MATATA!? .

'Dago idanuna dake cike da kwalla nai ina kallonsa, a hankali nace,  Sai addu'ar samun aljanna my King .

Ya lumshe idanunsa yana murmushin daba koyaushe yake yinsaba yana min jinjina =�M�<���.

Nima na jinjina masa ina k'aramar dariya.

Muncigaba da hirarmu a tsanake cikin so da k'auna da nunama juna kulawa.

Yauma langaremin yayi saida nabashi abinci da kaina yaci, nima dai haka ya ciyar dani da kansa.

Ban bar sashenba sai wajen 12, shima su Yaa Marwan muka tausayamawa, dukda kowa da d'akinsa, falone kawai ya had'asu.

Da kansa ya d'akkomin Absurraheem da Amaturrahman, ya rakoni, aiko muna fitowa yace,  ya salam, my mata dama haka wajennan keda sanyi? .

Cikin tausayawa Na kallesa, dan nima Na manta kayan dake jikinsa k'ananune, dan ciki akwai d'umi sosai, bama zaka tuna ana sanyiba,  kawosu kawai ka koma, kar mura ta kamaka .

 No muje da sauri Na rakaki, dan sunmiki yawa ai .

Har k'ofar sashen da muke ya min rakkiya, Na lek'a Na kira Wanda ke kusa danya taimaka min, Ayusher Ce ta fito itada Zuhuriyya, Na kar6esu d'ai-d'ai daga wajensa ina mik'a musu, yayinda suke gaisheshi sukuma yana amsawa da kulawa.

Suna shigewa ya jawoni jikinsa, waige-waige Na fara dan gudun kar wani ya gammu, shikam ko'a jikinsa, ya mannani da gini yana yanda yaso, kusan mintuna 2 sannan ya sakeni yana fad'in  Good night . A hankali tare da d'agamin yatsunsa biyu.

Kasa magana nayi harya 6acema ganina, Na sauke ajiyar zuciya ina shiga ciki a sanyaye tamkar wadda tama sarki k'arya.

Duk sunyi barci, sai Ayusher da Maryamu da Zuhuriyya ne kawai ido biyu, sai bina da wani kallon tuhuma suke.

Na zauna ina fad'in,  waiku lafiya kukemin kallon har hanji? .

Dariya suka sanyamin, Ayusher tace,  Hajiyata ina janbakin Dana Sanya miki? .

Harara Na zuba mata nace,  oho miki sa idiniyya . Natashi nai shigewata.

Aiko mizasuyi inba dariyaba, nima Na shige ina k'unshe tawa. Shirin barci nayi nai kwanciyata, har suka shigo suka kwantar da yaran ban kulasuba saima nayi tamkar barci nakeyi.

Dama Laraba Na iske tayi barci abinta ita tuni, Na dad'e banyi barciba, kasancewata tare da Galadima ta tsayamin arai, kai wannan Bawa akwai iya salon d'auke zuciya iri-iri, duk hanyar dazaibi ya dabaibayeki ya Sani.



Shima a 6angaren Galadima da k'yar yay barci, da badan kar ace yayi abin kunyaba da babu inda matarsa zata ta barsa, yana buk'atarta a kusadashi ainun, amma ya zaiyi, dolene ya had'iye kwad'ayinsa harsu dawo kusa dashi. Haka yayta juye-juye harya samu barci ya d'aukesa.









Washe gari





Ban samu damar ganin Galadima ba har a zuhur, dama gashi an tashi da sanyin daya hana kowa sukuni, sai a waya muka gaisa dashi, bayan Azhur aka kaimasa yaransa dai, sunsha gayu cikin kayan sanyi.



Bayan sallar la'asar mukad'an fito ni da sauran y'an uwana domin mud'ansha iska dai, saidai kowa a cikin kayan sanyi yake, ina goye da Meenal, yayinda suma sauran yaran su Badeera duk suka goyasu.

Mun shiga sashen matan sarki mun gaishesu mun fito muka had'u da su Galadima sun fito daga masaukinsu zasu shiga mota, da alama dai fita zasuyi.

Ido muka had'a dashi ya sakarmin Murmushi da d'agemin gira d'aya.

Nima murmushin namasa ina juya idanu.

Da yake d'an nesa damu suke, basu zoba muma bamu k'arasaba, suka shiga motar da aka bud'e musu. Har suka fice inabin motar da kallo.





****



Tarbar da Galadima ya samu ta girma da mutuntawa tamasa dad'i ainun, Dan shima har wata sarauta suka bashi, sun Nuna farincikinsu Na had'a jini da babbar masarauta irintasu Galadima, shima kuma yayi farincikin kasancewarsu cikin yankin ahalin matarsa, shikam bashida abun fad'a sai godiya.



Washe gari Sarki da Kansa yasa aka kirani, naje har turakarsa Na samesa, nasiha yaymin mai ratsa jiki, ya k'ara nunamin Girman daraja da Kimar masarautar su Galadima dayake gani, dukda basu had'a k'asa d'ayaba, inhar Na aikata k'yak'yk'yawa martabarsu da darajarsu Na kare, domin su ahalinane, kuma dole ace daga tsatsonsu Na fito, Na kare musu mutuncinsu, shima bada dad'ewaba zai shigo Nigeria insha ALLAH.

Cikin girmamawa da share hawaye nace,  Insha ALLAH bazan baku kunyaba, zan zama d'iya tagari mai ado da tarbiyyar ahalinta Na kowanne 6angare,, da izinin ALLAH saikunyi alfahari dani .

 ALLAH yayi miki albarka, Yakuma tsareku da dukkannin sharri keda y'an uwanki, yabaku zaman lafiya Na har abadan a gidajen aurenku .

Nace,  Amin Abba mun gode sosai, ALLAH ya k'ara girma .





A gurguje please>��







*******





Kwanakin Galadima uku a masarautar muka fara shirin tafiya, dan mura ta kama shi ram, gashi bata masa da sauk'i, a lokacin mu kwanakinmu 10, kowa yana cike da kewar tafiyarmu, jisuke kamar karmu tafi, mu kanmu a kewar rabuwa dasu muke ji sosai, dan Sabone maiban mamaki da shak'uwa ta shiga tsakaninmu, ba k'aramar hidima suka manaba, lamarin harma yayi yawa, sukace suma insha ALLAH suna tafe garemu nan kusa. Mussamman da kowa ya fahimci alak'a mai k'arfi dake tsakanin Yareema Issifu da Ayusher, wadda kowa yake cikin tsantsar farinciki da fatan ALLAH ya tabbatar da wannan had'i.



Yanzu kam tafiyar ta canja salo, dan Munubiya da Yaa Marwan, ni da Galadima.

Innarmu da Abba, mama Rabi'a da abbansu Ayusher, Feena da Ayusher, innaro, laraba, Yaa Fadeel dasu Aryaan aka had'asu a babbar mota guda d'aya (gwauraye kenan>�-�>�#�).



Tunda Na shigo motar k'amshin turarensa ya faramin sallama, sanye yake cikin milk d'in shadda datasha ainahin aikin masu sarauta harda hula, yayi k'yau, Dan yau a sarakinsa ya fito, muka kalli juna kowa yay murmushi, saida Na zauna sosai su Deejama dake rik'e da yaran suka mik'ominsu, ganin zasumin yawa yad'an matso ya d'auki Abdurraheem da Abadurrahman, idona dukya cika da k'walla, haka suma su Maryamu hawaye sukeyi, haka suka rufemu suna d'aga mana hannu.

Saida motar ta fara tafiya sannan hawayena suka sami damar zubowa.

Galadima da tun shigowata idonsa Na kaina yay murmushin gefen baki, tissue ya Ciro a bayanmu ya matso jikina sosai da d'ago fuskata. Kallonsa nayi, idanunmu suka sark'e cikin Na juna, ya lumshe nasa dake cike da barci da mura wadda ta k'ara musu girma da canja kalarsu jaa kad'an yana girgizamin kai alamar nabar kuka.

Bance komaiba, sai kuma matso hawayen da nayi, yasaka tissue d'in ya gogemin, sannan ya sumbaci saman la66ana kad'an yana jingina kaina da kafad'arsa.

Shiru nayi ina sauke ajiyar zuciya kad'an-kad'an, yayinda shikuma yake d'an shafa gefen kafad'ata daya d'oro hannunsa wajen, saida nasami nutsuwa sannan Na d'ago, kallona yayi muka had'a ido, cikin salon rashin son yayi magana ya kad'a kwayar idonsa alamar yadai?.

Da hannu Na nuna masa yaran nima, dukda bai fahimci minake nufiba baice komaiba.

Hulunan su Amaturrahman Na fiddo a handbag zan saka musu, dan sauri bai barni nayi hakanba dazamu fito, anafa fitowa daga sallar Asubahi akaita mufito-mufito, kuma duk Yaa marwan ne da wannan azalzalar.

Amaturrahman dake jikina Na sakamawa, shima gogan da mura taima murus ya kar6a yasakama mazan yana magana tamkar an masa tilas,  kai garinnan da dad'in zama da wahala, wannan sanyin nikam shiya hanani sukuni .

Dariyar data tahomin Na had'iye da k'yar ina fad'in  Ai sanyin kam babu sauk'i, sunce idan zafima yazo yashin yaji rana haka suke azabtuwa, garama sanyin, kaji kuwa muryarka fa ta canja gaba d'aya .

Murmushi yayi ya jingina kansa dake masa ciwo jikin seat batareda ya amsaminba.

Nima sai ban sake magana ba, Na nad'e yaran sosai a showal dukda glasses d'in duk a rufema suke, driver dai nata tuk'insa, ni idan son samunema Na kwanta, Dan barci nakeji sosai, jiya bamuyi wani barcin kirkiba anata hirar bankwana, muna kwanciya babu dad'ewa innaro tafara tashinmu mu shirya.

Seat d'in gaba Na kalla, tunanin maida yaran can yazomin, nakuwa d'aukesu d'ai-d'ai ina maidawa, tunda suna cikin kayan sanyi, kuma barcinsu sukesha, nima ai saina huta ko.

Zamewa nayi Na kwanta tareda d'ora kaina a cinyarsa, ido kad'an ya bud'e ya kalleni da mamaki,  Ina yaran? ya fad'a yana kallona.

Da hannu Na nuna masa gaban motar,  Amma ai zasu takura a can? .

A shagwa6e nace,  ALLAH bazasu takuraba, barci nakeji har kaina yafara ciwo .

Kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru, Dan bayason yawan maganar saboda kansa ciwo yake sosai. Nima ban sake cewa komaiba Na gyara kwanciyata ina lumshe ido, hannunsa ya d'ora a jikina daganan motar ta d'auki shiru, Dan barci tuni yayi awon gaba dani, shima a hakan barcin ya kwasheshi.



Bamu kuma sanin halin da ake cikiba saida tafiya tai nisa sosai, yara suka farka suna k'ananun kuka, shine ya fara farkawa, ya bud'e ido a hankali bakinsa d'auke da addu'a, agogon hannunsa yafara kallo, sannan ya maida kaina danabi dukna kanainayeshi, yad'an murmusa yana janye gyalen jallabiyar jikina daya rufe rabin fuskata, barcina nake hankali kwance, shi saima yaga Na k'ara k'yau a hakan. Kukan yaran daya fara k'arfine ya sakashi dawowa hayyacinsa, ya shafa fuskarta a hankali yana kiran sunanta.

Munaya batada nauyin barci dama, idanma aka cika surutu a kusa da ita takan farka, tad'anyi mik'a tana bud'e ido, hannunsa nakan fuskata ya zubamin idanu, ni saima kunya ta kamani, naja gyalen Na rufe ina tashi zaune. Murmushi yad'anyi yana fad'in  Duk kin samin ciwon jiki .

Fuskata Na bud'e ina tura baki kad'an da kallon kaina, ina naga nauyin dazan saka masa ciwon jikin?.

Fahimtar abinda nakeyi dayayne ya sashi cewa,  kina kokwanto ne? .

Nace,  sosaima . Nai maganar ina d'akko yaran.

Yanzuma kar6ar biyu yayi, Na dungure kan Abadurrahman ina fad'in,  kun ishi mutane da k'ananun kuka, nima yunwar nakeji ai .

Galadima dake kallonmu cikeda sha'awa yay murmushi mai sauti dahar ya bayyana hak'oransa a waje, amma baice komaiba.

A nutse Na shayar dasu su duka d'aya bayan d'aya.





Munzo cikin babban wani gari Galadima ya Umarci driver da cewar yasama mana wajen abinci mai k'yau, Dan karsu Aiyaan suji yunwa.

Cikeda girmamawa driver ya amsa masa.

Abinka da driver manya, dukkan wani wajen girma sun sanshi, kansa tsaye ya kaimu wani had'ad'd'en wajen cin abinci, saima kayi gaddamar ba'a Niger d'in yakeba, duk fitowa mukayi, amma Galadima yak'i fita, saida su Abba suka shige sannan, Ayusher da feena sukazo kar6ar yaran, Dan can Yaa Fadeel da Laraba sun kar6i Ameen da Meenal.

Mik'ama Ayusher Abadurrahman nayi, Na bud'e inda Galadima yake Na rank'wafo ina d'aukar Abadurraheem, shima mik'ama Feena nayi, itama Amaturrahman Na d'akkota Na rik'e, ganin ko motsi baiyiba nace,  yalla6ai yadai? .

'Dan yatsinamin fuska yay saikace wani mace. Na kuma rank'wafowa ina d'ora hannuna saman goshinsa, tausayinsa ya kamani, dan kan akwai zafi alamar bayajin dad'i. Nace,  Sorry my king .

Idonsa yad'an lumshe yana murmushi.

Nakuma cewa  ka daure muje ciki, sai a nemi maganin mura .

Nanma baice komaiba, saida yaja wasu seconds sannan ya ziro k'afa, nad'an matsa baya nabashi hanya ya fito.

A raina dai ina jinjina jinin masu mulki, k'asaita da izza tarigada tazama jinin jikinsu, babu yanda za'ayi ka iya rabasu dashi.

Da hannu yayma Drivers d'in alamar su shiga suma.



Mune k'arshe. Shiga.

ALLAH Sarki Yaa Marwan, harya tanadar mana wajen zama, gaskiya babu k'arya wajen yayi tsari, mukam mund'an shiga daga lungu kad'an, su Abba basa ganinmu bama ganinsu,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login