Showing 192001 words to 195000 words out of 365757 words

Chapter 65 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1533

 to amma wace maganace tasa? tazama abin nazari yalla6ai? .

 game .

 game! game! nashiga fad'a ina k'ok'arin tunanowa.

 okay, wai yanda yafad'i yaci game d'in? .

 Uhhm . ya fad'a a tak'aice..

Nikuma saina murmusa,  to dukda dai bansan ma'anar d'aukar maganar da muhimmanciba amma anawa tunanin yana nufin _abinnan mabanbantane, amma saiyayi amfani dasu cikin Abu d'aya, kuma sukai masa aiki iri d'aya, sannan duk shi kad'ai ya sarrafasu akan Abu d'aya bawai yayi tarayyar da wasu mutane da yawa bane ko aikinsa had'aka,_ wannan itace fahimta ta ga zancen nasa .

Lumshe ido Galadima yayi, ya duk'o a hankali ya mannamin Sumba mai k'au a goshi. Sannan ya d'akko novel d'in ya damk'amin a hannu, yajawo laptop d'insa yacigaba da aikinsa.

Kallon mamaki kawai na zuba masa, kokad'an ban fahimci muhallin maganar tasaba da son fashin bak'i.

Batareda ya kalleni ba, idonsa akan system d'insa yace,  kallonfa? .

Janye idona nayi ina ta6e baki.

Shima saiya ta6e nasa alamar yaganni kenan. karatuna nacigaba shima yacigaba da aikinsa yana shan coffee time to time.

Yayi aiki mai tsawo kafin yasaki wani murmushi da ajiyar zuciya, ya kalli munaya da barci ya kwashe, fuskarta ya shafa yana kuma sakin wani murmushin,  tabbas gaskiya Vishnu ya fad'a, mutum d'ayane ke amfani da Numbers daban-daban wajen kiran Abba munaya, duk wadda yagama da ita bazai sakeba, tagama aikinta, a wannan karon lallai kunyi aiki da basira, wadda harta birkita tunanin Sameer, kuna kiran Abba da mabanbanta Numbers wad'anda kunrigada kun gama shirya matakan da kowacce number bazata sake aikiba, shima kansa ya d'auka mutane daban-dabanne ke kiransa. O ALLAH wannan shine bada k'afa, to ai inkunsan wata bakusan wataba kuma, Muhammad Sameer ruwane, idan bakasha yanzuba zakasha anjima, idan kak'i kuma k'ishirwa ta kasheka. Inhar tarkon dazan d'ana zai d'annu dai-dai, tabbas zan cafke kurayen daji mai duhuwa a wannan karon .  Ya k'are maganar da jan hancin munaya yana kuma sumbatar goshinta .

Kwanciya ya gyara mata sosai, ya ja bargo ya lullu6a mata sannan yaje bayi ya d'auro alwala, kamar yanda ya saba ya raya wannan dare da nafilfili da godiyar ALLAH, kafin yazo ya kwanta gefen munaya zuciyarsa na cike da annashuwa da farinciki, kaikace komai yayi done ne.

Addu'a ya musu sannan yasakata jikinsa barci ya Lula dashi shima.



Nima mai d'aukar rahoto bara nad'an rintsa my sweet sisters=� �>�)�......................
'<���













Duk Wanda yaga ban amsa massage nashiba yamin afuwa, nayi up date WhatsApp d'inane>�p�>�p�>�p�>��<���













*_ALLAH ya gafartama iyayenmu=�O�<���=�-�_**_typing=���_*





=ء� *_HASKE WRITERS ASSO....._*





*_f&RAINA KAMA.....!!f&_*

_(Kaga gayya)_







*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







~Book 2~ =�I�<���1� 8� �'1� 9�







.................Na dad'e ina barci kafin Na tashi, nayi mamakin ganina ni kad'ai, bansan time d'in da Galadima ya ficeba, sakkowa nayi daga gadon Na nufi Na watsa ruwa.

Ina tsaka da shafa mai Samha ta shigo, saida tayi sallama nabata izinin shigowa sannan, ledar hannunta Na kalla ina fad'in  mikika samo mana 'Yar Uncle? .

Cikin dariya ta zauna kan sofa tana cewa  kayan dad'i ne Aunty gimbiyarmu, alfarma nazo nema wajenki keda Uncle .

Hankalina gaba d'aya Na maido kanta,  Alfarmar mi kuma? .

 Aunty gimbiya please ki lalla6a Uncle ya barki muje birthday d'in k'awata Dhibya, ALLAH yarinyarnan tana sonki sosai, kullum hirarki .

Nad'an zaro ido  kai Samha yaza ai naje wani birthday da wannan cikin? kuma kema kinsan bazai bariba tunda Na 'yammatane .

 kai aunty, cikin saikace Wanda yayi wani k'ato, kumafa a cikin gida za'ayi wlhy, iyamu goma ne kawai .

 to naji, ALLAH yasa ya bari, mikika kawo mana a ledar? .

 yes my sweet aunty, wannan wani sari ne yamin k'yau a wani shagon da muke zuwa siyan kaya, shine nayi alk'awarin siya miki, Uncle Sauban ya cikamin na siya, yanzu Na kar6o please ki gwada muga .

Dariya nayi, nace,  inye kaga 'Yar Uncle Anfara jink'an iyaye, to amma ni ina na iya saka sari? .

 kowama koya yayi nidai ki saka muga dan ALLAH .

 to shike nan bara na gwada, ALLAH ya saka da alkairi, ina alfahari da d'iyata .

Samha ta fita tana dariya, nikuma na warware kayan, masha ALLAH sarin ya had'u gaskiya, farine anmasa kwalliya da pink and silver kad'an-kad'an. Na saka rigar, sai dariya ta kamani, saikace wata bafulatana>�-�>�#�.

Warware zanin nayi, tofa anan akeyinta, dan ban iya nad'awaba, na tsaya gaban mirror inata gwadawa amma na kasa, dariya ta kamani, yau naga takaina, Samha ta had'ani da aiki.



Tunda ta fara k'ok'arin d'aura zanin sarin yana tsaye a k'ofa, ya hard'e hannayensa ak'irji kawai yana kallonta, kamar zaiyi dariya saboda yanda taketa murd'e-murd'en d'aurawa.

A hankali ya taka zuwa inda take, jinai kawai andafa min kafad'u ta baya, na d'ago a tsorace muka had'a ido ta cikin mirror, fuskarsa babu walwala, ya d'agamin gira d'aya, maida idona k'asa nayi, yayinda shikuma ya juyo dani ina fuskantarsa.

Gwiwarsa d'aya ya saka a k'asa ya dogare d'aya, nidai kallonsa nake mizaiyi?. Batareda ya kalleni ko min magana ba ya zare zanin dake tattare a hannuna, nikam kamar wata sokuwa saina sakar masa.

Yiyay kamar zai warware zanin, nayi saurin rik'ewa, ya d'ago fararen idanunsa yanamin alamar na saki, ban iya musa masaba na sakar masa.

Shima sai bai yaye dukaba ya dai-daitashi, ammakina sainaga yana nad'amin, babbar magana Galadima da nad'a sari.

Dazai saka wanda a ke sokewa a gefen kugu sai yayi dawani salon daya sakani zabira saboda sak'onsa yajemin har kwalwar kai, ya d'ago ya kalleni yana wani miskilin murmushi da d'agamin gira. Sai kawai na lumshe ido dan naji kunya wlhy. Ya mik'e tsaye yana daidaitamin na kafad'ar shima, nidai harya gama ban bud'e idoba. baiyi magana ba ya warware reborn d'in kaina, da sauri na bud'e idon, yanda yawani tsareni da idanu sai nakasa jurewa na maida na rufe.

Cumb ya d'auka yahau gyaran kai, to nikma naga abinda yafi k'arfina yau d'innan, wai dama guy d'innan ya iya abin mata ne?. Bai barni ba saida ya gama yanda yakeso dani, ya zubamin ido kawai batareda yace komai ba. nikuma nakasa bud'e idona na kallesa, ahankali yafara busamin iskar bakinsa saman idona, dole nafara marmar da idanu, dainawa yayi, na bud'e idon ahankali a kansa, kuma matsoni yayi muka Zuba juna ido ko k'yaftawa bamayi, gashin dake neman shigarmin ido ya saka d'an yatsa ya matsar, na maida idanun na lumshe ina sauke k'aramar ajiyar zuciya.

Shima nannauyan numfashi ya sauke kafin yaja da baya, wardrobe d'insa ya nufa, jin yabar wajen saina bud'e idona, duk jikina ya saki, kallo d'aya namasa na d'auke kaina na juya ga mirror Dan naga yanda ya maidani, murmushi nayi ina saka hannu na gyara gashina, nima na yarda da gaske nayi kyau.

Nakuma d'ago ido da nufin sake kallon kaina sainaganshi a bayana, sark'a ya ziro a ya sakamin tareda gyara zamanta ta zauna sosai a k'irjina, ya janye gashina ta baya yana sak'ala sark'ar, nidai nawa idone, ya gama ya cire d'an kunen dake kunnena ya sakamin na sark'ar, sannan ya mannani da jikinsa yana zagayo hannunsa duk biyu saman matashin cikina, hannuna ya kama yana sakamin bangles, cikin k'asaitacciyar muryarnan tasa yake magana cikin kunnena,  haka dama sari kema Afirikawa k'yau? .

Murmushi nayi, na d'ago idona muna kallon juna ta cikin mirror, haryanzu hannayena na cikin nasa yana saka bangles d'in da guda d'ai-d'ai.

Ya lumshe idanu yana shanshanar wuyana, jikina yafara rawa, babu shiri na saka hannuna d'aya daya gama saka bangles d'in na shafo gefen kumatunsa, cikin rawar murya nace  please kabari yalla6ai .

Batareda ya dainaba cikin sark'ewar harshe yace  mizaisa na daina? yalla6iya .

Yanda yake min akan dokin wiya da yanda hannunsa d'aya ke canja salo a jikina sainayi k'ok'arin juyowa garesa, ko hakan zaisa yabari d'in. Ashe dama ma na sake bashi, gaba d'aya yawani rikice kamar ba Galadiman Dana saniba. Hannunsa ya sak'alo kuguna yana kuma matsoni jikinsa sosai, yasaka d'ayan hannun ya tallafo kaina tareda d'ora la66ansa akan nawa.

Kasa jurewa nayi, na mik'a masa wuya kawai, harda bada gunmawa nima........





Tofa munga idi, daga gyaran sari=�F�<���=�9�.





Samha tataho da karsashinta dantaga ko Munaya ta saka, daga nan ta nuna mata yanda zata nad'a zanin sarin, tunda tasan bata iyaba, ko kad'an babu Wanda yaga shigowar Galadima, Dan babu kowa a falon, jakadiya ta tafi asibiti itada Sauban da innarsu munaya, aunty Mimi kuma barci takeyi, Dady kam yanacan baya inda ya maida lambun tunaninsa, itako Samha tana bama Munaya sari takoma d'aki danta bata lokaci ta shirya a tsanake. Sallama d'aya kawai tayi ta turo k'ofar tana kwala kiran  Aunty gimbiyarmu kin saka? .

Galadima dayake Neman fara zirmawa yay hanzarin sakin Munaya, da sauri naja baya nima, dan kamar a sama mukaji muryar Samha.

Itama Samha baya ta koma da sauri gabanta na fad'uwa, Dan ganin Wanda batayi zatoba a d'akin. ALLAH ma yaso bataga komaiba, lokacin datake sako k'afarta a d'akin Galadima ya janye bakinsa yana k'ok'arin matsawane baya.

Wata uwar harara mai kad'a hanji da hanta ya zubama Samha, hakanne yasakata yin baya da sauri ta koma.

Nikam kasama d'aga ido nayi balle na kalleshi dagashi har Samhar, saima wani yaam nakejin jikina tamkar zan fad'i.

Lura da hakan da yayine yasakashi azamar rik'o hannuna, na shige jikinsa ina sauke tagwayen ajiyar zuciya, dagani harshi idanu kowa ya lumshe, tsawon lokaci muna a haka munkasa sakin juna, ahankali na shiga k'ok'arin janye jikina, bai hananiba yabani damar barin jikinsa, ra6awa nayi ta gefensa na wuce, na koma saman sofa na zauna ina dafe kai, juyowa yayi yana kallona, kafin yatako shima zuwa bakin gado ya kwanta, k'afafunsa na k'asa duka, yayinda yay filo da hannayensa yana lumshe idanu.

Duk munyi shiru d'akin tamkar babu wata halitta mai numfashi a cikinsa, kowannenmu shiyasan mi yake sak'ama zuciyarsa.

K'arar wayarsace ta sakamu d'an firgita mu duka, duk sai muka zubama wayar ido tamkar wani ojuju. harta tsinke bai d'aukaba, saida aka sake kira sannan ya cirota daga aljihun wandonsa yay picking.

Muryarsa vary low yace,  Nuren Yaya dai? .

Mamaki da al'ajabi ya cika Nuren, yakuma Ciro wayar daga kunnensa ya duba Dan tabbatar da Galadima ne kuwa?, lallai shine, maida wayar yayi a kunne yana fad'in  brother lafiyarka kuwa? .

Taune lips nashi yayi, ya yanke wayar, dan indai ahaka zasuyi wayarnan bazai fahimci komaiba, ajiye wayar yayi yatashi ya shige bathroom.

Da kallo k'asa-k'asa kawai na iya binsa, amma nakasa ko kwakwkwaran numfashi.



Daga can kuwa Nuren kwashewa yayi da dariya saboda tuno wani Abu, (to su Nuren dai dama bariki sune manyanta>�#�), dariya yakeyi iya iyawa yana dukan kansa, daya fara tsagaitawa saiya kuma saka wata, saida yayi ta ishesa sannan ya daina, ya rik'e ha6a yana fad'in  oh ni su brother ansan takan tsiya, ina ganinsa lab-lab Ashe d'anba sauk'ine, toma uwar miye na d'agamin wayar tunda yasan yafara sauka a network>�#�, yakuma saka dariya saikace wani sabon kamu.=�,�



Galadima kam ruwa ya sakarma kansa kawai, ya dafe bango da hannu biyu ruwan na kwarara saman kansa, sai faman taune lips yakeyi shi kad'ai, yayi da zuciyarsa ke sak'awa da kwancewa, saida ya ji k'arfi-k'arfi sannan ya kashe shower d'in yaja bathrobe d'in ya saka yana faman sauke 6oyayyar ajiyar zuciya.

Inda yabarta anan ya fito ya isketa, kallo d'aya yamata ya d'aukekai, bakin gadon ya zauna yana goge kansa da k'aramin towel, yajawo wayar da d'ayan hannun ya danna kiran Nuren.

Bugu d'aya Nuren d'in ya d'aga, da k'yar yasamu ya danne dariyarsa,  brother wai miya farune naji muryarka haka? nifa ka tadamin hankali .

 Ba komai, shin kajene? .

Nuren ya toshe bakinsa gudun kar dariya ta kufce masa, Sameer d'an rainin wayone ALLAH, wai babu komai, to naji babu komai aje a haka.

 wai kana jina kuwa? . Galadima yafad'a.

 Oh sorry brother network nayin wasa, gani a gidan, amma bankai ga shiga inda takebane .

 ok tom kaje, amma kabar wayar a kunne, inason naji komai .

Nuren yace  to .

Da sallama ya shiga d'akin, sai wani ciccin magani yake.

Farhat dake zaune bakin gadon d'akin ta zabga tagumi ta d'ago kai tana kallonsa, yayin da wasu hawaye ke shirin zubo mata.

Kujera guda d'aya dake d'akin ya jawo ya zauna.

Farhat ta share hawayen kumatunta, murya a sanyaye tace,  yayana dan ALLAH kayi hak'uri, wlhy ina missing d'in families d'ina da karatuna, dan ALLAH idan kasheni zakayi ka kasheni kawai na hutama rayuwa ma ni gaba d'aya .

Murmushi Nuren yayi, idonsa a kanta yace,  bazan kashekiba Farhat, dan bakimin komaiba, kamar yanda na sanarmiki mahaifinkine yaja miki, ki kwantar da hankalinki, insha ALLAH zaki koma gidanku kwana kusa, yanzuma dukba wannanba, wata tambaya nazo yimiki, ALLAH yasa zaki bani had'in kai? .

Kanta ta jinjina masa tana kuma share sauran hawayen,  insha ALLAH inhar nasani zan fad'a maka .

 good girl  .  cewar Nuren yana gyara zama .

 Farhat nasan kinsan duk yaran Abbanki ko?, ina nufin masu masa hidima a office ko a gida? .

 Eh nasan mafi yawansu, dan ina zuwa wajensa a Office, kuma wasu acikinsu sukanzo gidanma .

 Masha ALLAH, kokin san SD? .

 SD!? .

 eh shi .

 gaskiya a yaran Abbana dana sani babu wani mai suna SD .

 okay, amma ko wani mai Something sunan dazai iya kasancewa full name bazaki iya hasasowa ba? .

Shiru tayi ta lula duniyar nazari, shidai Nuren ya zauna mata idanu yana kuma jinjina ma ubangiji akan yin k'yak'yk'yawar hallita, dan Farhat black beauty ce masha ALLAH.

A jiyar zuciya ta sauke,  yaya inaga kamar dai akwai wani Sagir dauda dana Sani, amma bansan aikin da yake a k'ark'ashin Abbanmu ba, sai kuma ya Shareffudden k'anin Aunty Umma, sai Steven Daniel .

 shi Steven d'in wanene shi a gidanku, itama Aunty Umman haka? .

 Driver d'insu Mom ne, shike kaisu anguwa, ita kuma Aunty Umma matar Abbanmu ce ai, itace amaryarsa .

 Uhyim . Nuren yafad'a yana jinjina kai.

 Dan ALLAH yayana in tambayeka mana? .

 ina saurarenki .

 laifin mi Abbana yamuku hakane? .

murmushi Nuren yayi,  karki damu nangaba kad'an komai zai wuce, kuma bashi yay laifinba, wanine yayi na kusa dashi .

 to ALLAH yasa Ku kamashi, amma dan ALLAH karkuma Abbana komai .

 insha ALLAH babie .

Murmushi Farhat tayi, Nuren kuma ya mik'e tsaye idonsa a kanta.  babu dai wata Matsala ko? .

Cikin shagwa6ar data saba tace,  please ko TV ka samin, banajin dad'in zaman hakanan .

 Am sorry to say dear, har kibar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login